Showing 33001 words to 36000 words out of 75493 words

Chapter 12 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt

tsaye ya yi 'yar tafiya nesa kaɗan da inda sauran abokan tafiya suke ya zauna ya shiga sabon tunani. Abinda ya fara fado masa a rai shi ne, tunowa da wasiyar da Aljani Marhabul Zaurus ya yi masa kafin ya mutu cewar ya yi hankali da Boka Muzaffar lallai mayaudari ne shi kuma azzalumi".Shaharan na cikin wannan tunani ne yaji an dafa kafadarsa ta baya. Cikin firgici ya waigo da sauri sai ya ga ashe Zarina ce don haka sai ya yi murmushi a gare ta itama ta maida masa da martanin murmushin sannan ta zauna daf da shi suna masu fuskantar inda sauran abokan tafiya ke kwance, wato can bakin kogin tundun tsira.

Tsawon 'yan dakiku dayansu bai ce uffan ba daga can sai Zarina ta yi gyaran murya ta ce, 'Ya kai masoyina, ka yi sani cewa masu iya magana sun ce, 'Ruwa baya tsami banza' Tabbas akwai abinda ke damunka shi ya sa ka baro cikinmu ka dawo nan ka zauna kana tunani. Idan har son da kake yi mini na gaskiya ne kada ka ɓoye mini komai. Ka tuna cewa na rasa dan uwana Sarkin Farisa yanzu bani da sauran kowa a duniya. Kai ma ka rasa dokinka wanda da shi ne kaɗai za ka cika babban burinka na duniya, ba ka da wani abu da yai saura wanda ya fi ni daraja. Lallai ya zama wajibi a gare mu mu hada kai mu taimaki juna tunda muna bukatar junan namu". Sa'adda Gimbiya Zarina ta zo nan a cikin zancenta sai jarumi Shaharan ya yi ajiyar zuciya sannan ya kwashe labarin duk abinda ya faru tsakaninsa da Aljani Marhabul Zaurus ya zaiyane ma ta.

Koda jin wannan labari sai hankalin Zarina ya

dugunzuma ainun, ta yi shiru tana mai tunani. Daga can sai ta kawo gwauron numfashi ta ajiye sannan ta ce, "Hakika Biri ya yi kama da Mutum. Inda Boka Muzaffar ya kasance adali kuma mai gaskiya da ya nuna matukar damuwarsa bisa duk irin abubuwan da suka rinka faruwa a gare mu mu duka. Ni na rasa dan uwana amma ko jaje bai yi mini ba. Shadira ta rasa dan uwanta bai tausaya mata ba. Kai ma ka rasa dokinka bai ce da kai komai ba. Haiman da kai kun rasa hannayenku dai dai amma duk bai nuna tausayinsa ba. Wannan yana yi mana nuni da cewa Boka Muzaffar bai damu da rayuwarmu ba alhalin kuma shi ne ya dora mu akan wannan TAFARKI zuwa kogon Darul Iksina kuma mun dade muna jiransa akan yin wannan tafiya. Ko shakka babu Muzaffar yana da wata manufa a Karkashin zuciyarsa kuma yana da wani buri na musamman akan shiga cikin kogon Darul Iksina. Lallai ya yi amfani da mu ne kawai a matsayin Karukan farautarsa. Ya kai masoyina shawarar da zan ba mu ita ce duk irin umarmin da Boka Muzaffar zai ba mu a cikin kogon Darul Iksina kada mu yi amfani da shi kuma idan da hali mu hana sauran abokan tafiya aiki da wannan umarni nasa." Lokacin da Zarina ta zo nan a zancenta sai Shaharan yai ajiyar zuciya sannan ya ce, "Ya ke masoyiyata ki yi sani cewa abokan tafiyarmu sun yarda da Boka Muzaffar dari bisa dari, koda za mu ba su labarin wasiyyar da Aljani Marhabul Zaurus ya bayar ba za su aminta ba. Idan kuma muka sanar da su a yanzu za su yi mana tawaye, wata kila ma su hada kai su yake mu. Abin da zai fiye mana alheri shi ne kawai mu bar wannan al'amari a cikin zuciyarmu. Wanda duk yake da rabon fitowa a raye daga cikin kogon Darul Iksina lallai zai fito. Yanzu ki tashi mu koma can wajen abokan tafiya domin idan muka ci gaba da hira anan Boka Muzaffar zai iya zarginmu har ma ya yi tunanin daukar mataki a kanmu".

Gama fadin hakan ke da wuya sai duk su biyun suka mike tsaye suka koma can wajen sauran abokan tafiya. Nan take aka shiga kafa tantuna gami da shirya abincin da za a ci.

Kamar yadda Boka Muzaffar ya shirya haka al'amura suka kasance, wato sai da su Shaharan suka shafe kwana uku cur suna jinyar raunikan jikinsu a nan bakin kogin tudun tsira sannan suka kintsa aka kama hanya aka durfafi kogon Darul Iksina.
Haka dai suka wanzu suna tafiya, ba sa ya da zango face idan dare ya yi sannan su tsaya a kafa tantuna a kwanta ayi barci.

Wani abin mamaki da ya faru shi ne, a iya tsawon kwana ukun da suka yi wannan tafiya ko maciji ba su kara gani ba akan hanyarsu bare ya kawo wa dayansu hari.

Da la'asar sakaliya suka iso bakin kogon Darul Iksina. Kogon na Darul Iksina ya kasance abin al'ajabi ga dukkan wanda ya yi arba da shi, domin ya wanzu ne tamkar ginin gida akan wani dan karamin tsuburi, wanda ruwa ya kewaye shi kuma ruwan ba shi da zurfi domin komai gajartar mutum bai fi ya kawo masa iya kaurin kafarsa ba.

Kogon na Darul Iksina an yi shi ne cikin siffar gida na ginin jan dutse na Murjani, wanda tun daga nesa mutum zai ga yana ta kyalkyali da daukar ido sannan haskensa ya haskake dajin gaba daya.

Girman gidan ya kai na dan karamin gari yana da fadi da tsawo sosai domin idan aka fuskance shi ba a iya hango karshen katangarsa. Idan mutum ya daga kai ya dubi saman ginin kogon sai ya ga kamar bashi da karshe kwai dai ya lmtokare da sararin samaniya ya kule a cikin gajimare. Ko kadan babu alamar kofa ko taga a jikin gidan kuma ko ina a mulmule yake a shafe tamkar wani abu bai taɓa shiga cikinsa ba.

Lokacin da su jarumi Shaharan suka iso daf da kogon Darul Iksina sai gabadayansu suka ja suka yi cirko-cirko suna kallon kogon cikin tsananin al'ajabi. Shi kansa Boka Muzaffar an batar da tunaninsa domin yadda duk yake tsammani zai ga kogon ba haka ya gan shi ba.

Bayan sun dan ɓata dakiku masu yawa suna kallon kogon sai Boka Muzaffar ya wuce kan gaba ya shiga cikin wannan ruwa ya durfafi tsuburin da kogon Darul Iksina ke kai ba tare da fargabar komai ba yana ta kyalkyala dariyar farin ciki kuma yana yafito sauran abokan tafiya da hannu.

Koda ganin haka sai Haiman ya bi bayansa yana goye da matarsa Lumaira, sannan Imran dauke da mahaifiyarsa, Shadira na binsu daf da daf Shaharan da Zarina na biye sannan Gimbiya Rahila, Sarki Laffaru ne na karshe.

Kamar yadda Shaharan da Zarina ke da shakku akan Boka Muzaffar, haka Sarki Laffaru ya kasance domin shi ma ya lura da take-takensa tun daga farkon tafiyar tasu har izuwa sa'adda suka iso bakin tekun tudun tsira don haka sai ya aiyana a ransa cewa duk irin umarnin da Boka Muzaffar ya bayar a cikin kogon Darul Iksina ba zai yi aiki da shi ba koda kuwa zai rasa rayuwarsa.

Bayan kowa ya haye wannan ruwan sai aka hau kan tsuburin aka iso daf da kogon Darul Iksina aka tsaya aka yi cirko-cirko kowa ya zubawa Boka Muzaffar idanu.

Yayin da Muzaffar ya ga shi kaɗai ake sauraro sai farin ciki ya lulluɓe shi nan take ya shiga yi wa kansa kirari yana mai cewa;

"Ni ne Bokan zamani wanda ya gagari dukkan Bokaye.

Ni ne murucin kan dutse ban fito ba sai da na shirya.

Ina matsafa da jaruman duniya, yau ga Bokan farko da zai zamo sanadin da za a shiga kogon Darul Iksina.

Na bata hankali Dare na sami suna da daukaka, kuma na samu.

In banda Aljani Maruful Dauwaz babu wanda zai riga ni shiga kogon Darul Iksina, lallai na bar wa duniya abin tarihi.

Ko yanzu na mutu na kasaita kuma na gawurta, lallai duniya ba za ta manta da ni ba." (OH ni Maiboko! Ka ji ďan egiya mayaudari macuci)

Gama fadin hakan ke da wuya sai Muzaffar ya fiddo wata 'yar karamar wuka daga jikinsa ya kama suturar jikinsa dai-dai ciayarsa ya kwaye ta, sai ga wadansu dalasiman tsafi rubuce akan ciyar

Nan take ya fara karanto dalasiman tsafin cikin daga murya. Faruwar hakan ke da wuya sai wata irin iska mai karfi ta fara kadawa tana zagaye gaba dayan kogon na Darul Iksina, gaba daya yanayin sararin samaniya ya sauya daga fari fat ya koma kore shatar.

Al'amarin da ya firgita gaba dayan abokan tafiyar ke nan, dukkaninsu suka ji tsigar jikinsu ta tashi, kuma tsoro ya baibaye su.

Boka Muzaffar na gama karanto wadannan dalasiman tsafi sai wannan iska ta dauke dif, yanayin sararin samaniyar ya dawo dai-dai yadda yake a da.

Ba zato ba tsammani sai suka ga wata katuwar kofa ta bakin mulmulallen karfe ta baiyana akan ginin kogon Darul Iksina, sannan sai suka ji karar zare sakatu a jikin kofar har guda casa'in da tara. Daya bayan daya sakatun suka rinka zare kansu. Ta casa'in da taran na gama fita sai kofa ta bude wanwar.

Koda suka yi arba da cikin kogon sai gaba dayansu suka cika da tsananin al'ajabi. Ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin abin da ke cikin kogon.

Wadansu gidaje ne kala-kala a cikin kogon har guda bakwai. Kowanne gida guda daya ya kai girman unguwa guda, kuma dukkan gidajen anginasu ne daga dangin su Zinare, Lu'u-lu'u, Jauhar, Murjani da sauransu. Duk wanda ka kalla sai ka ga kamar ya fi wanda ke kusa da shi kyau da ginuwa

Ba tare da fargabar komai ba Boka Muzaffar ya kuna kai izuwa cikin kogon suma sauran abokan tafiyar sai suka bivshi da sauri duu! Da yake Sarki Laffaru ne na karshe yana shiga sai kofar gidan ta rufe kanta wadansu sakatu guda casa'in da tara suka mayar da kansu cikin ramukansu, sanann kofar ta sake rufe kanta.

Faruwar hakan ke da wuya sai Boka Muzaffar ya bushe da dariyar mugunta. Lokaci guda kuma ya hade rai ya ce, "Ni ne kadai zan iya sake bude muku kofar wannan gida ku fito in ba haka ba kuwa sai dai ku mutu a cikinsa".

Gama fadin hakan ke da wuya sai Boka Muzaffar ya sanya hannunsa a cikin aljihunsa ya fiddo wata 'yar karamar jemammiyar fata. Babu. komai a jikin fatar face taswirar gidajen da ke cikin wannan kogo gaba dayansu guda casa'in da taran. A jikin kowanne gida akwai rubutun wadansu kalmomin tsafi.

Nan take Boka Muzaffar ya ajiye wannan jemammiyar fata a kasa, gaba dayan abokan tafiyar suka kewaye ta suna kallonta cikin mamaki.

Muzaffar dube su daya bayan daya ya ce, Shin a cikinku akwai wanda zai iya karanta mini kalma daya daga cikin kalmomin da aka rubuta a jikin wannan fata?"

Koda jin wannan tambaya sai kowa ya duru-duru aka rasa wanda zai ce kala. Da ganin haka sai Boka Muzaffar ya sake bushewa da dariya sannan ya ci gaba da kuri yana mai cewa, "Ku duka a yanzu rayukanku a hannuna suke. Wanda duk ya bi umarnina zai kuɓuta ya sami cikar burinsa. Wanda kuma duk ya bijire mini kuwa zai hallaka anan cikin kogon Darul Iksina.

Koda gama fadin hakan sai Boka Muzaffar ya Kurawa wannan fata idanu sannan ya dago kai ya dubi Haiman da Imran ya ce, "Ku je ku bude kofar wancan gida na uku ku shiga cikinsa kai tsaye. Lallai a cikinsa ne za ku riski ruwan albarka da za ku yiwa masoyanku magani da shi su warke".

Ba tare da gardamar komai ba kuwa Haiman da ke goye da matarsa Lumaira ya nufi kofar wannan gida. Imran goye da mahaifiyarsa ya mara masa baya.

Nan take suka bude kofar wannan gida na uku suka kunna kai ciki. Suna shiga sai kofar gidan ta rufe kanta. (Allah wadaran mai hali irin na boka Muzaffar)

Daga nan sai Boka Muzaffar ya dubi Zarina da Shadira ya ce, "Ku kuma kun rasa masoyanku don haka ba ku da sauran bukatar ruwan albarka. Kai ma jarumi Shaharan baka da bukatar wannan ruwa, saboda haka ka bi Zarina da Shadira ku shiga cikin gida na biyu. Duk abin da kuke so na duniya wanda ya dunganci dukiya za ku samu a cikin wannan gida, ku shiga ku debo iya muradinku akwai hadiman da za su yi muku dako har izuwa kasashenku."

Koda jin wannan batu sai Shadira ta nufi wannan gida na biyu, amma sai Shaharan da Zarina suka toge. Al'amarin da ya matukar bai wa Boka Muzaffar mamaki ke nan ya dube su ya ce, 'Me kuka tsaya jira? Ko kuwa kuna so ku bijirewa umarnina ne?"

Sa'adda Shaharan ya ji wannan tambaya daga bakin Boka Muzaffar sai ya yi murmushi ya ce, "Ya kai wannan Boka ka yi sani cewa ni yanzu tsakanina da kai babu sauran yarda da amana, saboda jikina ya ba ni cewa so kake ka yaudare mu ka cutar da mu. Ina tabbatar maka da cewa duk inda ka shiga ni ma nan zan shiga tunda na san cewa ba za ka kai kanka inda za ka hallaka ba".

Koda jin wannan batu sai Boka Muzaffar ya bushe da dariya ya ce, "Tabbas ka yi dabara ya kai wannan jarumi, b." amma ka kama hanyar da ba za bulle ba

Boka Muzaffar ya dubi Sarki Laffaru ya ce, ya kai abokina, maza ka ruga izuwa cikin daki na hudu domin anan ne za ka sadu da Aljani Maruful Dauwaz wanda zai cika maka burin rayuwarka. Sarki Laffaru ya toge ya ce, "Kai ba zai yiwu ba. Haba abokina! Ai ilimin tsafi ka fi ni amma ba wayo ba ko sanin tuggun duniya. Ina tabbatar maka da cewa kafarka-kafata. Duk inda ka shiga nan zan shiga. Idan har ma gaskiya ne cewar zan sadu da Aljani Maruful Dauwaz a cikin gida na hudu ta ya ya zan iya sarrafa shi ya aminta da ni har ya biya mini bukatata?"

Koda jin wannan tambaya sai Boka Muzaffar ya ce, "Ai ga Gimbiya Rahila nan amfanin tahowa da ita kenan a cikin wannan tafiya muddin Aljani Maruful Dauwaz zai yi arba da ita duk abin da kake so zai yi muku tunda kamanninta iri daya ne sak da na masoyiyarsa wadda ya rasa."

Kafin Muzaffar ya gama rufe brakinsa tuni Gimbiya Rahila ta tari numfashinsa ta ce, "Kai! dakata tsohon banza! Mayaudari, ai kama da wane ba ta wane. Ni mutum ce, masoyiyar Aljani Mauruful Dauwaz kuwa aljana ce, kuma ta mutu. Wanda duk ya mutu ba zai dawo ba, Mauruful Dauwaz ya san da haka. Abin da na ke so da kai kawai ka kai mu inda Maruful Dauwaz yake mu gana da shi ni na san abin da zan gaya masa ya aminta da bukatarmu, idan kuma ba za ka yi haka ba sai dai KAIFIN TAKOBI ya raba mu da kai yanzu".

Koda jin wannan batu sai Boka Muzaffar ya bushe da mahaukaciyar dariya wacce ta cika kogon gabadaya da amsa kuwwa sannan ya ce, "Ai ni yanzu na gama dahuwa bana tsoron konewa. Ina mai sanar da ku cewa yanzu karfin sihirin tsafina zai yi aiki don haka idan ma za ku taru ku duka ba za ku iya hallaka ni ba har sai na cika burina. Ku sani cewa gabadayanku yaudararku na yi babu wanda na kawo shi nan domin samun biyan bukatarsa sai don biyan tawa bukatar. Tuni na yi bincike a cikin hallarar tsafina na gane cewa dole sai da ku zan iya ratsa wadannan dazuzzuka guda biyar domin sihirin tsafi ba zai iya kuɓutar da mutum daga sharrin da ke cikinsu ba. Batun ruwan albarka da na gaya muku cewa idan ku ka yi amfani da shi masoyanku za su warke, duk karya ce na shirya muku kawai na yi amfani da ku a matsayin Karnukan Farauta na.

(Boka Muzaffar da yan siyasa ba su da maraba a gurin dadin baki da bakar yaudara. Allah ya kyauta)

Ya kai Laffaru, kai ne kadai za ka iya cika burinka idan ka sadu da Aljani Maruful Dauwaz idan har ya amince da kai. Ni kam abu daya ne ya kawo ni cikin wannan kogo, ba komai bane face wani MASHI wanda ake kira GALILUL HARAS. Yau shekara arba'in ke nan ina ta bincike akan yadda zan zo na mallake shi sai yau na sami wannan dama. Da zarar na dauki wannan mashi na Galilul Haras na fita da shi daga cikin kogon nan na mallaki duniya gaba dayanta.

Idan duk mutanen dunuiyar nan da dukkan aljanun duniya za su taru ba su isa su hana ni shiga wannan gida na farko ba don dauko wannan mashi.

Da wannan furuci nake yi muku bankwana sai mun sake saduwa nan gaba a lokacin da kasashenku da Sarakunanku suka dawo karkashin mulkina".

Koda gama wannan bayani sai Boka Muzaffar ya ɓace bat! yana mai kyalkyala dariyar farin ciki. Nan take kofar wannan gida na farko ta bude sannan ta kulle kanta.

Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin su Sarki Laffaru da Boka Muzaffar a farkon shigarsu cikin kogon Darul Iksina.


Al'amarin Haiman da Imran kuwa wadanda ke goye da masoyansu lokacin da suka shiga cikin wannan gida na uku sai suka tsinci kansu a cikin wata makekiyar fada wacce ta kasance akwai komai a cikinta na sarauta sannan ga Dakaru nan kimanin su dubu a tsaitsaye rike da makaman yaki amma dukkaninsu sun kasance gumaka masu kirar mutanen farko wato manya-manya. Sun kasance masu tsawo da kaurin gaske domin kuwa kowane dayansu tsawonsa ya ninka na su Imran sau uku.

Akan karagar mulkin fadar kuwa gunkin wani dan karamin yaro ne kafafuwansa a tankwashe a kansa akwai dan gajeren rawani kuma fuskarsa cike take da annuri kamar ace kyat ya yi magana.

Lokacin da Imran da Haiman suka ga yanayin tsarin wannan fada sai suka cika da mamaki. Haiman ya dubi Imran cikin alamun damuwa ya ce, "Anya kuwa Boka Muzzafar ba yaudararmu ya yi ba. Yaya mu da muka zo neman ruwan albarka zai shigar da mu nan, ga shi ko alamar danshi babu a wajen bare a sami ruwa sai gumakan banza kawai".

Da jin wannan batu sai Imran ya yi ajiyar zuciya sannan ya kwance mahaifiyarsa daga bayansa ya ajiye ta a kas gefe daya shi ma ya zauna ya dubi Haiman ya ce, "Tabbas biri ya yi kama da tutum, akwai alamun yaudara da cin amana a cikin wannan al'amarin, yanzu kenan duk wahalar nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login