Showing 69001 words to 72000 words out of 75493 words
Chapter 24 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt
nan ya dakawa Maruful Dauwaz harara ya ce, "Kai kuma mene ne ya ba ka dariya?"
Maruful Dauwaz ya ce, "Gani na yi za ka ba mu kunya a matsayinka na ďa namiji.
Ka tuna cewa Ramlatul Siyam yarinya ce kankanuwa a kanka, tunda shekarunka sun ninka nata.
Ka tuna cewa manyan mazajen duniya sun mutu da bakin cikin rashin mallakar Gimbiya Ramlatul Siyam, amma kai ga shi yanzu za ka mallake ta a karon banza saboda kawai ta ce ka kawo kan rikakken Zaki a matsayin sadakinta shi ne za ka karaya?
To ka sani cewa ba ka da wani zabi wanda ya fi ka kawo wannan sadakin in ba haka ba kuwa, har abada ka rasa ta, kuma sai makiyanka sun sami nasarar hallaka ka a cikin kankanin lokaci.
Ina tabbatar maka da cewa ni ma ba zan taimaka maka da komai ba akan samo wannan sadakin domin idan har ka kasa samo sadakin da kanka 'yar da za ku haifa ba za ta zamo gagarumar jaruma ba saboda ba a samu sadauki sai daga tsatson sadaukai.
Duk da cewar kai GWARZON SADAUKI ne ada, ai a yanzu ka zama rago, kuma sadaukantakarka ba za ta dawo ba sai bayan ka haifi wannan 'ya taka har ta girma".
Koda gama fadin hakan sai Aljani Maruful dauwaz ya ɓace ɓat, ya sake baiyana a bakin tantin Gimbiya Ramlatul Siyam ya yi gyaran murya. Nan take Ramlatul Siyam ta fito daga cikin tantin ta dubi Maruful Dauwaz ta ce, "Me kake da bukata?"
Maruful Dauwaz ya risina cikin biyayya ya ce, "Ina son na ji lafiyar Gimbiya Rahila ne domin na san matsayin da nake ciki".
Koda jin wannan batu sai Ramlatul Siyam ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Rahila ta farka daga barci har ma na ba ta ruwa ta sha, amma fa har yanzu ba ta iya bude bakinta ba bare ma ta yi magana, kuma idanunta ma da kyar take iya bude su. Yanzu dai na sake ba ta wannan digon magani ta sha ta koma barci. Ka kara hakuri wata kila nan da kwana uku ta sami sauki sosai har ta iya magana".
Koda Maruful Dauwaz ya ji haka sai hankalinsa ya dan kwanta ya yi godiya ga Ramlatul Siyam kuma ya roke ta akan ta ci gaba da kula da Rahila har izuwa sa'adda za ta sami lafiya. Gimbiya Ramlatul Siyam tayi masa alkawari cewar lallai za ta bata kyakkyawar kulawa iyakar yadda ya kamata.
****
Ba tare da ɓata lokaci ba Sarki Laffaru ya mike tsaye ya fara kafa nasa tantin. Bisa mamaki sai ya ji ya sami dan kwarin jikinsa amma bai ji rabin karfin dantsensa ba irin na da ba.vNan take farin ciki ya lullube shi har ya fara tunanin cewa zai iya shiga dajin ya yi farautar rikakken Zaki.
Haka dai ya ci gaba da aikin kafa tantin nasa cikin murna har ya kammala sannan ya shiga ciki ya yi kwanciyarsa ya ci gaba da tunanin zuci har barci ya sace shi bai sani ba.
Ya yin da dare ya soma yi sosai sai mugayen dabbobin daji suka fara zarya a kusa da inda tantin su Ramlatul Siyam yake.
Amma duk dabbar da ta yi arba da Aljani Maruful Dauwaz sai ka ga ta firgita ta koma da baya guje izuwa cikin daji tana koke-koke. Wato dai sai Aljani Maruful Dauwaz ya bayar da cikakken tsaro a a gare su.
****
Kashe gari da safe Sarki Laffaru ya farka daga barci sai ya mike zumbur! Ya fito daga cikin tantinsa domin ya ga lafiyar abokan tafiyar tasa yana fitowa sai ya iske Ramlatul Siyam a zaune tana buda baki. Aljani Maruful Dauwaz na zaune a gefe daya kusa da ita cikin nishadi suna ta hira har da dariya. Nan take Laffaru ya gangara izuwa cikin wata korama da ke bayan inda suka kafa tantunansu ya tube kayansa ya fada cikin koramar domin ya yi wanka.
Kash! Rashin sani yafi dare duhu. Ashe akwai wata katuwar Kada a cikin wannan korama bai sani ba. Ai kuwa yana cikin wanka sai ya ga wannan Kada ta taso masa. Ya yunkura domin ya ruga waje daga cikin koramar sai ya ga ai ba zai iya gujewa Kadar ba.
Cikin tsananin tsoro Sarki Laffaru ya kurma uban ihu. Ai kuwa sai Ramlatul Siyam da Aljani Maruful Dauwaz suka rugo izuwa bakin koramar. Da isowarsu suka iske katuwar Kadar ta wangame bakinta za ta hadiye Sarki Laffaru.
Cikin zafin nama Laffaru ya goce bai san sa'adda ya rungumi Kadar ba suka fara kokawa a cikin ruwan tana danna shi kasa, shi ma yana kokarin tasowa sama, kuma yana ci gaba da ihu gami da kiran taimako.
Har Maruful Dauwaz ya yunkura zai kai masa dauki sai Ramlatul Siyam ta hana shi ta ce, "A haka ne zai iya samo sadakina? Wannan fa kada ce ba rikakken Zaki ba.Mu kyale shi kawai ya fara bai wa kansa horo tun kafin ya yi arba da rikakken Zaki.
Nan fa aka ci gaba da gumurzu tsakanin wannan kada da Sarki Laffaru a cikin wannan ruwa. Sarki Laffaru ya ci gaba da rukunkume Kadar iya karfinsa ya ki yarda ya sake ta.
Da yake Kadar ta ruku sosai sai kuwa ta kasa kwacewa amma sai ta yi amfani da jelarata ta rinka dukan jikin Laffaru.
Duk sa'adda ta maka masa jelarta sai ka ga kamar da takobi aka yanke shi, take jikinsa ke darewa jini ya yi tsartuwa ko feshi yana mai fwalla ihu, amma duk da haka ya ki yarda ya saki Kadan duk da cewa wani lokaci tana danna shi izuwa karkashin ruwan numfashinsa na daukewa.
Da zarar kadan ya taso sama sai ka ga sun ci gaba da gumurzu.
Kafin a jima jikin Laffaru ya yi kaca-kaca da raunika. Ita kuwa Kadan sai ta ji ta fara gajiya don haka sai tayi nutso kasa taki dagowa sama.
Koda Laffaru ya ga numfashinsa na neman daukewa gaba daya sai ya saki Kadan babu shiri ya fara iyo da sauri don ya kaj bakin gaɓar koramar.
Ai kuwa sai kadan ya juyo da sauri suka kasa sabon tsere.
Yayin da Sarki Laffaru ya auna ya ga cewa kafin ya isa bakin gabar koramar sai kadan ya cim masa sai kawai ya juya ya tare shi.Wannan karon sai Kadan ya kai wa kafarsa hari. Laffaru ya goce cikin zafin nama, amma duk da haka sai da Kadan ya wawuri tsokar nama mai kauri a cinyar Laffaru.
Laffaru ya kurma uban ihu a lokacin da yai wuf ya sake rungumar Kadan suka ci gaba da kokawa a kan ruwan.
Da kyar da sidin goshi Laffaru ya samu ya zare wata siririyar wuka a jikinsa ya daga sama ya kirɓawa Kadan. Bisa sa'a sai ya soke ido guda na Kadan.
Take idon ya fashe, sai ga jini yana bulbula. Laffaru ya sake daga wukar ya luma ta a kan daya idon na Kadan.
Ai kuwa sai Kadan ya yi wata irin gagarumar kara yai kasa ya lume izuwa karkashin koramar bai sake tasowa sama ba.
Nan fa Laffaru ya fara iyo da kyar har ya samu ya fito bakin gaɓar koramar. Yana fitowa ya baje a kas sumamme.
Koda Gimbiya Ramlatul Siyam da Maruful Dauwaz suka ga irin raunikan da wannan Kada ya yi wa Sarki Laffaru sai suka kamu da tsananin tausayinsa.
Nan take Ramlatul Siyam ta ruga da gudu izuwa bakin koramar ta dauko Laffaru ta kai shi cikin tantinsa. Da kanta ta shiga yi masa magani ta dinke raunikan da suke bukatar dinki.
Wannan rauni da ke kan cinyarsa kuwa sai magani ta zuba masa sannan ta nannade shi da kyalle mai kyau saboda wajen ba shi da kyan gani.
A sannan ne Sarki Laffaru ya farfado daga dogon suman da ya yi. Yana bude idanunsa ya yi arba da Gimbiya Ramlatul Siyam tsugune a kansa tana yi murmushi kawai sai ta dube shi ta ce, "Tabbas ka yi Namijin kokari, Akwai alamun cewa za ka iya kawo sadakina amma fa sai ka yi matukar jajircewa."
Koda gama fadin haka sai ta mike tsaye ta ce, "Ga abincin kalacinka nan na ajiye maka, lallai sai ka yi jinyar kwana bakwai sannan za ka sami kwarin jikinka har ka iya fita faratar sadakina.
Nan take Ramlatul Siyam ta juya ta fice daga cikin tantin tana waigen Sarki Laffaru tana yi masa wani irin murmushi mai kama da na mugunta.
Al'amarin da ya fusata shi ke nan ya ji kamar ma ya hakura da aurenta, amma da ya tuna cewa idan bai aure ta ba duk wahalar nan da ya sha a baya ta zamo ta banza sai ya ga batun hakura bai taso ba, koda zai rasa rayuwarsa, don haka sai ya ji ya karfafi zuciyarsa akan cewa lallai sai ya kawo sadakin auren Gimbiya Ramlatul Siyam ta kowane hali ko da kuwa shi ne sanadin ajalinsa.
Lokacin da Ramlatul Siyam ta fito daga cikin tantin Laffaru sai ta hango Aljani Maruful Dauwaz zaune a can gefe daya ya yi tagumi, hawaye na zuba daga cikin idanunsa. Cikin tsananin mamaki Ramlatul Siyam ta karasa gare shi ta zauna daf da shi ta dube shi ta ce, "Ya kai Sarkin sadaukan aljanu me ya faru kake tunani mai zurfi haka har da zubar da hawaye?"
Koda jin wannan tambaya sai Maruful Dauwaz ya yi ajiyar zuciya sannan ya share hawayensa ya ce, "Ya ke tauraruwar taurarin mata ta duniya, ki yi sani cewa, ba komai ne ya sa ni wannan zubar da hawaye ba face tsananin takaici bisa halin da muke ciki a rayuwarmu ni da ku.
Zaman da na yi anan yanzu na tuno da irin labarin su Lafaru bisa tsananin wahalar da suka sha a cikin wadannan dazuzzuka guda biyar kafin su iso kogon Darul Iksina, da yadda wasunsu suka rasa masoyansu, ga shi kuma shi kansa wanda ya yaudare su ya jefa su a cikin wannan bala'i ya tashi a tutar babu, karshe ma ya rasa rayuwarsa a banza bai cika burinsa ba.
Hakika abin da na fahimta a rayuwa shi ne, kowane mahaluki ya kan mutu da burinsa ne, domin buri ba ya yankewa face ajali ya riske shi. Babu mamaki mu ma nan da burinmu duk za mu mutu.
Sa'adda Maruful Dauwa ya zo nan a zancensa sai Gimbiya Ramlatul Siyam ta yi ajiyar zuciya, a lokacin da idanunta suka ciko da kwallah sannan ta ce, "Ya kai sadaukin aljanu na duniya ka yi sani cewa, ita wannan rayuwar babu wani abu madawwame a cikinta, walau farin ciki ko bakin ciki. Yanzu dai ka dauki misali a kaina.
Tun da na taso ina karama ban san wata wahalar duniya ba, kuma ban san kowa ba sai mahaifina tunda sa'adda uwata ta mutu ban fi shekara uku ba.
Babu mahalukin da na shaku da shi sama da ubana amma yau ga shi mutuwa ta raba mu.
Na rasa daular da nake ciki, yau ni ce a cikin daji ina rayuwa shigen irin ta dabbobi wacce ba ni da tabbacin tsaro na lafiyata kuma abin da zan ci ma sai na nema, Komai ni zan yi wa kaina.
Koda jin haka sai Aljani Maruful dauwaz ya kamu da tsananin tausayin Gimbiya Ramlatul Siyam har hawaye ya sake zubo masa. Koda ganin haka sai ita ma Ramlatul Siyam ta fada kan kirjinsa ta rungume shi kuma ta fashe da matsanaicin kuka yana mai rarrashinta.
Kamar yadda Ramlatul Siyam ta fadi haka al'amarin ya kasance, wato sai da Sarki Laffaru ya kwana bakwai yana jinyar jikinsa sannan ya samu lafiya gami da kwarin jikinsa.
A ranar kwana na bakwai ne da hantsi Ramlatul Siyam ta kawo wa Sarki Laffaru takobinta gami da garkuwarta ta yaki ta mika masa ta ce, "Ga shi ya kai mijina na gobe, ka yi sani cewa lokaci ya yi da za ka tafi neman sadakina saboda haka, daga nan zuwa faduwar rana ina sauraron dawowarka tare da sadakin nawa sai ka kama hanya ka nausa cikin daji".
Sa'adda Ramlatul Siyam ta zo nan a zancenta sai Sarki Laffaru ya ji tsoro ya baibaye shi kuma ya ji kamar ya ce ya fasa auren nata amma sai ya daure bai ce kala ba.
Cikin sanyin jiki da alamun karayar zuciya ya karbi takobin da garkuwar sannan ya ce, "Shin za ki iya ba ni aron Maruful Dauwaz ya yi mini rakiya?".
Ramlatul Siyam ta yi murmushi irin na mugunta ta ce, "Babu mai yi maka rakiya face takobinka da garkuwarka. Idan har rana ta fadi gari yai duhu muka ga ba ka dawo ba mun san ka mutu sai mu jira izuwa ranar da Rahila za ta gaya wa Maruful Dauwaz inda wasiyyar masoyiyarsa take sannan mu tashi mu bar wanan daji. Koda gama wannan jawabi sai Ramlatul Siyam ta juya ta tafi izuwa cikin tantinta.
Cikin fushi da kunan rai Sarki Laffaru ya juya ya durfafi cikin daji yana tafe yana huci kai ka ce zai iya tarwatsa rundunar mayaka guda saboda kwarjininsa da kirarsa irin ta sadaukai amma ga wanda ya sani, banza ce ta kori wofi, domin ba zai iya tsinana komai ba, abu ne ma mawuyaci ya iya tsira da rayuwarsa.
Sarki Laffaru ya ci gaba da tafiya har ya yi nisa a cikin daji, duk da cewa ya san cewa ba shi da wata jarumtaka a jikinsa wacce zai iya kashe rikakken Zaki har ya ciro kansa amma sai ya ji dukkan tsoro ya kau daga cikin zuciyarsa ko mutuwa ce ta tare shi ba zai gudu ba saboda ya fusata ainun kuma zuciyarsa ta kekashe.
Sau tari a rayuwa dakewar zuciya shi ke haifar da samun nasara ba wai karfin jarumtaka ba.
Sai da Sarki Laffaru ya yini a daji yana farautar rikakken Zaki amma bai gan shi ba.
Wani abu da ya daure masa kai shi ne, ko daga nesa idan wadansu mugayen dabbobin suka hango Laffaru kamar su Damisa, Kura da sauransu sai ka ga suna komawa da baya ko su sauya hanya. Abin da bai sani ba shi ne, tsananin kwarjinin sa ne ya sa dabbobin suke tsorata da shi.
Lokacin da Laffaru ya gaji da yawo a cikin dajin har ya ji kishirwa ta kama shi sai ya je karkashin wata doguwar bishiya ya zauna sannan ya fidda dan guzurin abincinsa ya fara ci. Abin da bai sani ba shi ne, ashe akwai abin da ya fito nema akan wannan bishiya da ya zauna a karkashinta.
Wani murtukeken rikakken Zaki ne kwance akan bishiyar yana barci. Zakin bai dade da cinye wata barewa ba da ya make.
Bayan ya ci ya koshi kuma ya je ya sha ruwa sai ya zo ya hau can saman bishiyar ya kwanta. Yana kwanciya kuwa sai barci ya sace shi. Da yake barcin nasa bai yi nisa ba ko munshari bai fara ba.
Koda Laffaru ya fara cin abincin sai sautin taunarsa ya sa Zakin ya farka. Ai kuwa yana lekawa kasa ya yi arba da Laffaru sai ya kwarara uban gurnani mai tsananin firgitarwa.
Gurnanin nasa ya cika dajin gaba daya da amsa kuwwa. Hatta Maruful Dauwaz da Ramlatul Siyam da ke can tsakiyar dajin sai da suka jiyo wannan ruri na Zaki.
Cikin tsananin farin ciki Ramlatul Siyam ta daka tsalle ta fada kan Aljani Maruful Dauwaz tana mai cewa, "Na sami miji!"
Bisa mamaki sai ta ga Maruful Dauwaz ya sunkui da kansa kas cikin alamun karayar zuciya sannan ya ce, "Wannan rurin Zakin da kika jiyo ba na fitar rai ba ne, ruri ne na tsoratarwa.
Tabbas Laffaru ya yi MUGUN GAMO da murjejen Zaki kuma rikakken gaske domin sai zakin da ya haura shekaru talatin a duniya shi ne yake irin wannan ruri".
Koda jin wannan batu sai hankalin Ramlatu!Siyam ya dugunzuma ainun ta ji kamar ta ruga da gudu izuwa cikin dajin domin ta kai wa Laffaru dauki amma sai ta dake.
Lokacin da wannan Zaki ya yi wannan ruri sai Laffaru ya mike zumbur a matukar tsorace domin ya gudu, ai kuwa sai Zakin ya duro a kansa ya turmusheshi a kas suka kama kokawa suna mirgine- mirgine.
Zakin ya fara kokarin ya kafa hakoransa akan makoshin Laffaru shi kuwa sai ya dage iya karfinsa yana gabzawa Zakin naushi suka ci gaba da turmutsutsu da birgima a kas.
Nan da nan Zakin ya karkarce jikin Laffaru da faratan hannayensa da na kafafunsa. Albarkacin mirginawar da suke yi ne shi ma Zakin fuskarsa ta rinka gwaruwa a jikin duwatsu da bishiyoyi har ya sami raunika, jini ya cika fuskar tasa.
Ai kuwa suna cikin birgima a kasan ne da mirginawa suka fado izuwa asan wani rami wanda ruwan kogi ne ke azababben gudu a cikinsa. Suna fadowa cikin ruwan sai kowannensu kansa ya bugu akan duwatsu duk suka suma. Igiyar ruwa ta tafi da su izuwa can gaɓar kogi tayi watsi da su.
Sai da iska ta bugesu sannan Laffaru ya fara farfadowa. Koda ya yunkura domin ya mike tsaye sai ya ji ya kasa saboda ji ya yi kamar ba shi da kafar dama.
Koda ya dubi kafar tasa sai ya ga ta karkarce kuma ta kumbura suntum! Nan take ya gane cewa karyewa ya yi. Al'amarin da ya matukar dugunzuma hankalinsa ke nan.
Kwatsam! Sai wannan Zaki ya farfado daga dogon suman da ya yi. Ai kuwa yana bude idanunsa ya yi arba da Laffaru zaune a gabansa sai ya daka tsalle gami da wangame bakinsa zai afka masa.
Cikin tsananin zafin nama Laffaru ya cisgo wata 'yar karamar bishiya da ke daf da shi yai sama ya tari Zakin. Bisa sa'a kuwa sai tsinin reshen bishiyar ya shige cikin hancin Zakin ya bullutso ta wuyansa.
Suna fadowa kasa shi da Zakin sai Zakin ya kama matagungun da shure-shuren mutuwa. Sai da Zakin ya dade yana shure-shure sannan ya mutu.
Nan fa tashi ya gagari Laffaru. Dole ya ci gaba da zama a bakin wannan koramar da wanan karamar bishiya wacce ya kashe Zakin da ita ya samu ya kakkarya rassanta ya gyara karayar tasa ya daure kafar a jikin rassan da taimakon tsumman rigar jikinsa da ya yayyage. Sai da ya kwana uku yana jinyar kafar tasa a bakin wannan kogi ya zamanacewa, ba shi da abincin ci sai danyen naman wannan Zaki da ya kashe, har ma Zakin ya rube ya fara tsutsa amma a haka yake cin naman nasa don kada yunwa ta kashe shi, tunda babup kyastu a wajen wanda zai kunna wuta ya gasa naman. Ruwan wannan kogi kuwa shi