Showing 30001 words to 33000 words out of 75493 words
Chapter 11 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt
sai ta fusata ainun, ta kara kaimi, ta mai da hankalinta akan kai musu munanan sara. Ai kuwa nan da nan ta lalata dukkan garkuwoyinsu suka yi ta jifa da su, bisa dole suka ci gaba da yakarta da takubba.
Kaico! Tashin hankali ba a sa masa rana. A wannan lokaci ne Kunamar ta sami lagon jaruman ta fara samun nasarar saran jikinsu. A lokaci guda ta sari Shadira da Zarina a damtsen hannayensu wurin ya yi rami mai zurfi jini yai feshi suka kwalla ihu suka fadi can gefe daya a matukar
galabaice. Haiman, Imran da Zarina, Rahila da Shaharan kuwa a kafafunsu ta sassaresu ta yi watsi da su can gabanta.
Boka Muzaffar da Sarki Laffaru gami da Aljani Marhabul Zaurus kuwa wani irin wawan mangari tayi musu suka yi sama kamar an cilla su daga cikin Baka sannan suka fado a kasa a sume kuma a warwatse. Nan take Kunamar ta ruga izuwa inda su Shaharan ke zube a kas domin ta karasa hallaka su. Suna ji suna gani aka rasa wanda ai iya mikewa tsaye ya kare kansa. Tuni a wannan lokaci mahaifiyar Imran, Lumaira da dokin Shahara sun dade da suma sakamakon mummunar buguwar suka yi a kas.
Koda ya rage bai fi saura taku goma ba tsakanin Kunamar da su Imran, Shaharan ya ga mutuwa muraran ta taho gare su sai ya kwarara uban ihu, duk da cewa akwai Raton rauni a kafarsa wanda naman wajen ya zabtare yana reto har ana ganin kashin Kafar sai ya daka wawan tsalle sama kamar kibiya aka harba ya dira akan tsakiyar Kunamar yana rike da takobi da hannu daya. Daya dungulmin hannun nasa kuwa ya naushi idon kunamar da shi. Saboda karfin naushin sai da dungulmin hannun nasa ya nutse a cikin idon Kunamar. Yana zaro hannun nasa sai ga jini yana feshi.
Duk da haka Kunamar ba ta daina kawo masa sara da suka ba da dukkan sauran hannayenta, shi kuwa ya wanzu yana mai kade hannayen na ta da takobinsa cikin bakin zafin nama wanda ko a mafarki bai taɓa zaton zai iya yin hakan ba. A hakan Kunamar ta ci gaba da matsawa tana kokarin isa inda su Haiman ke kwance sun kasa tashi domin ta turmushe su.
Koda Shaharan ya gane nufin Kunamar sai ya sake dankara ma ta wawan naushi a daya idon nata. Take shi ma idon ya burme, jini ya kama ɓulbulowa ta zama makauniya.
Wohoho! Nan fa Kunamar ta haukace ta yi wata uwar girgiza ta jeho Shaharan kasa daga kanta. Dai-dai inda ya fadin ta kai wawan suka da dukkan hannayenta, cikin matsanancin bakin zafin nama ya goce, kafafuwan na ta suka cake a cikin kasa suka lume can kasa. Kafin ta zaro kafafun na ta Shaharan ya mike zumbur ya falfala da masifaffen gudu. Duk da cewar Kunamar ta makance, sai ta yi amfani da sautin takun sawayensa ta bi shi a guje, suka kasa uban tsere.
Tabbas in ba don Shaharan ya yi wannan dabara ba ya dauke hankalin Kunamar daga wajen abokan tafiyar tasa da sai ta hallaka dukkan abokantafiyar a lokaci guda.
Sai da aka shafe rabin sa'a ana wannan tseren gudu tsakanin Shaharan da wannan Kunama, duk sa'adda ya waiga bayansa sai ya ga tazarar da ke tsakaninsa da ita bai wuce kamu biyar ba, don haka a ko yaushe za ta iya luma masa faratanta.
Da zarar ya yi yunkurin sauya wurin da ya nufa sai ya ga itama Kunamar ta sauya ta bi shi. Al'amarin da ya kara dugunzuma hankalinsa ke nan musamman da ya ga cewar har a sannan ba su iso kogin tudun tsira ba.
Baya ga wannan tashin hankali da yake ciki abin da yai ta fado masa a rai shi ne, rashin sanin halin da su Zarina ke ciki a yanzu. Shi dai ya san cewa gabadayansu suna cikin mugun hali, babu mamaki ma wasunsu sun mutu bai sani ba, don haka, kokarinsa shi ne yai sauri ya kai kunamar cikin wannan kogi domin ta hallaka sannan ya dawo baya a guje domin ya kaiwa su Zarina agajin gaggawa. Haka dai Shaharan ya ci gaba da gudu iyakar karfinsa.
Hakika idan masifa ta kai masifa mutum na iya mantawa da wani bala'in. Saboda tsananin tsoron wannan Kunama wacce ke biye da Shaharan, ya manta da lafcecen raunin da ke kafarsa har ma gudan tsokar da ya zabtaro a jikin kafar ya gutsure da kansa ya fadı kasa amma bai sani ba.
Da kyar da siďin goshi Shaharan ya riga wannan Kunama isa cikin wannan kogi na tudun na tsira, amma kafin ya faɗa cikin kogin sai da ta sare shi da kaifin faratanta sau uku a gadon bayansa. Duk sa'adda ta sare shi sai ya tsandara ihu ya gantsare kamar zai fadi kuma sai jini ya yi feshi daga jikinsa.
Yana fadawa cikin kogin ne ita ma Kunamar kafafunta suka tsunduma a cikin ruwan kogin. Nan take jikin Kunamar ya kama narkewa, kafin cikar dakika sittin gaba dayan jikin nata ya narke ya zama ruwa. A sanann ne jarumi Shaharan ya fito daga cikin ruwan da kyar yana dingishi da mai da numfashi kamar zai mutu.
A dai-dai wannan lokaci ne ya ji raunin kafarsa ya dame shi da tsananin zogi. Koda ya dubi raunin ya ga yadda tsokar naman kafarsa ya zabtare sai ya kwarara uban ihu ya fadi kas. Yana faduwa ya tuno da halin da ya baro abokan tafiyarsa, sai ya sake mikewa zumbur! Ya falfala da irin wannan azababben gudun nasa ya koma da baya tamkar babu wannan rauni a jikinsa.
Da isar Shaharan inda ya baro su Haiman sai ya iskesu a cikin wani irin mugun hali. Duk wuraren da wannan Kunama ta sara a jikinsu har ya rube ya fara tsutsa kuma wajen dada girma yake yana dada zabtarewa, su duka suna ihu.
Ya Koda ganin wannan bala'i sai hankalinsa ya dugunzuma ainun kuma ya cika da tsananin mamaki bisa yadda aka yi shi nasa raunin bai rube ba ya kama tsutsa.
Abinda ya fara fado masa a rai shi ne, watakila saboda ya shiga cikin wannan kogi ne na tudun tsira shi ya sa nasa raunikan ba su yi tsutsar ba.
Cikin firgici da hanzari ya cicciɓi Zarina da Shadira ya saɓa su a kafadunsa ya sake falfalawa da gudu ya nufi inda kogin tudun tsira yake. Wannan karo shi kansa ya yi matukar mamaki bisa ganin irin masifaffen gudun da yake yi don ya ninka wanda ya yi da farko.
Kafin rabin-rabin sa'a ya iso bakin kogin. Da zuwa sai ya jefa Zarina da Shadira a ciki, suna fadawa cikin kogin sai raunikan nasu suka daina tsutsa kuma suka dawo kamar yadda suke da farko. Koda ganin haka sai farin ciki ya lullube Shaharan ya juya da sauri ya sake falfalawa da gudu ya koma can wajen sauran abokan tafiya.
Haka ya rinka dauko su da bibbiyu akan kafadunsa yana gudu yana kawo su cikin kogin tudun tsira yana watsa su ciki har ya gama debo su gabadaya ya zamana cewa saura dokinsa da Aljani Marhabul Zaurus kadai.
wannan lokaci shi ma dokin Kunamar ta sare shi a waje biyu kuma raunin ya zama tsutsa har ya cinye rabin jikinsa, dokin ya baje a kas har ya fara kokarin mutuwa.
Koda Shaharan ya ga halin da dokinsa ke ciki kuma ya ga shi ma Aljani Marhabul Zaurus yana cikin irin wannan hali sai hankalinsa ya dugunzuma ainun tunda shi ma Marhabul Zaurus din ba zai iya koda mikewa zaune ba bare ya dauki dokin ya kai shi can bakin kogin tudun tsira.
Shaharan ya sunkuya ya cicciɓi dokinsa da dukkan karfinsa amma sai ya kasa koda raba dokin da kasa ne saboda nauyinsa. Sai da Shaharan ya jarraba daukar dokin nasa har sau uku amma yana kasawa, kawai sai ya zauna a gefe daya yana kallon dokin yana kuka, sa'adda dokin ya fara kakarin mutuwa.
Yana ji, kuma yana gani tsutsa ta baibaye gabadaya jikin dokin, wannan tsutsar ta zamo sanadin ajalinsa. Nan fa Shaharan ya kurma uban ihu sannan ya sake fashewa da matsancin kuka.
Shi kuwa Aljani Marhabul Zaurus lokacin da azabar tsutsar jikinsa ta addabe shi sai ya fara ihu yana kuka yana mai cewa, "Ya kai wannan jarumi ka sani cewa ni ma mutuwa zan yi yanzu, ina mai yi maka gargadi da ka yi hankali da Boka Muzaffar domin gaba dayanku yaudararku yake yi, so yake da zarar kun isa kogon Darul Iksina ya hallaka ku, ku duka saboda shi kadai yake son ya mallaki wannan ruwan sihiri da kuma Aljani Maruful Dauwaz.
Tabbas idan ya mallaki wadannan abubuwa biyu babu abin da zai gagare shi a cikin wannan duniya. Ni kaina sai yanzu ne na gane cewa ya yaudare ni ya cutar da ni.
Tabbas wannan duniya makaranta ce kullum ana samun kima a cikinta. Ka yi hattara ya kai Shaharan, lallai ka yi iya kokarinka wajen ceton rayuwar sauran abokan tafiya. Ni kam tawa ta kare, sai dai nan gaba ku bayar da labarina idan kun tsira da rayuwarku!".
Gama fadin hakan ke da wuya sai Aljani Marhabul Zaurus ya ɓingire kasa ya zama gawa. Shi kuwa jarumi Shaharan sai ya ci gaba da matsanaicin kuka sakamakon mutuwar dokinsa.
Bai gushe ba yana wannan kuka har izuwa tsawon sa'a guda sannan ya mike tsaye ya juya ya nufi hanyar da za ta kai shi can bakin kogin tudun tsira. Yana tafe yana waigen dokinsa yana zub da hawaye har ya daina hango dokin nasa.
Lokacin da Shaharan ya iso bakin kogin tudun tsira sai ya iske kowa ya dawo cikin haiyacinsa, ana ta yi wa juna magani a jikin raunika.Tun daga nesa Zarina ta hango shi sai ta mike tsaye ta ruga gare shi, suna haduwa suka rungume juna cikin tsananin farin ciki.
A wannan lokaci Haiman da matarsa Lumaira na zaune a gefe daya suna ta duba lafiyar junansu kuma suna murna da ganin junansu a raye.
Shadira Imran da mahaifiyarsa ma suna gefe a tare. Boka Muzaffar, Sarki Laffaru da Gimbiya Rahila na zaune a tare su ma suna ta murna da ganin kansu a raye
Lokacin da Boka Muzaffar ya ga jarumi Shaharan ya dawo shi kadai babu dokinsa kuma babu Aljani Marhabul Zaurus sai ya ji a jikinsa cewa lallai Aljani Marhabul Zaurus da dokin Shaharan rai ya yi halinsa.
Cikin hanzari Zarina ta janye jikinta daga cikin na Shaharan ta shiga duba lafiyarsa. Koda tayi arba da wannan katon rauni da ke kafarsa sai ta dimauce kuma ta fashe da kuka. Nan take ta zaunar da shi ta shiga sa masa magani akan raunin sannan ta je ta nemo tsumma mai tsafta ta nannade raunin duka ta ɗaure shi.
Gama hakan ke da wuya sai ta kwantar da Shaharan a kas tana mai dora kansa akan cinyarta ta shiga tunani mai zurfi. Daga can sai ta fara rera waka cikin sanyaya kalamai masu dimauta maza alokacin da hawayenta ke diga bisa kan fuskar Shaharan. A cikin wakar tana bayani kamar haka;
"Mazaje sun fadi a yayin da gumu ya kai gumu"
"Ranar wuya ita ce ranar da daci ke yanke zaki"
"Ranar masoya ke rasa masoyansu"
"Daji biyar na masifa yau mazan Kwarai sun ratsaka mma basu sha da dadi ba"
"Ga ďa da uwa a cikin bala'i, amma ba su iya tseratar da juna ba"
"Miji da mata sun ga gararin da ba su taɓa" gani ba.
"Jini da jini na hade amma bakin takobi ya raba su"
"Yau fa ga ranar cika buri amma amfaninta ya gushe tunda babu masoyi"
"In ban da akwai sauran masoya a doron kasa da mazaje sun zabi mutuwa akan rayuwa!"
Lokacin da Shadira ta fara rera waďannan baitoci sai jikin kowa ya yi sanyi aka yi ta kuka kamar ba za a daina ba. Kuma aka yi tsit ana saurarenta har izuwa dogon lokaci.
Ita kanta sai da ta ji ta gaji da yin wakar sannan ta yi shiru ta kifa kanta akan kirjin Shaharan har barci ya sace su su biyun ba su sani ba.
Gaba dayan abokan tafiyar sai da suka yi baccin wuya, baccin dole saboda tsananin gajiyar da ke jikinsu. Dayansu bai farfado ba sai bayan sa'a biyu da rabi.
Mahaifiyar Imran ce ta fara farfadowa tana bude idonta ta hangi danta Imran da Shadira kwance a waje daya sai ta ji ta cika da tsananin farin ciki da ta rayu ta kawo izuwa wannan lokaci da take daf da warkewa daga cutar da ta addabi rayuwarta tsawon shekara da shekaru kuma take daf da ganin auren danta.
Bayan ta jima tana kallon Imran da Shadira tana ta murmushi sai kuma ta juya ta kalli inda Haiman da matarsa Lumaira ke kwance, nan take taji suma ta tayasu farin ciki ainun tunda suna daf da cika burinsu na warkewar. Lumaira daga cutar makanta.
Koda ta tuno da yaro Masnur dan uwan Shadira, Sarki Farisa dan uwan Zarina da kuma dokin Shaharan ai ta fashe da matsanaicin kuka saboda ko ba komai ta shaku da su a cikin wannan doguwar tafiya da aka yi kuma ta tausayawa masoyansu matuka bisa rashin su da suka yi.
Sautin kukan mahaifiyar Imran ne ya sa kowa ya farka daga barci.Koda Imran ya ga mahaifiyarsa na kuka sai ya mike tsaye zumbur daga jikin Shadira ya ruga "Ya ke izuwa wajen mahaifiyar tasa ya durkusa a gabanta suka rungume juna yana mai cewa, Ummina ina dalilin wannan kuka naki?"
Ki yi sani cewa yanzu lokaci ne na farin ciki ba na kuka ba tunda muna daf da cika burin zuciya. Koda jin wannan batu sai mahaifiyar tasa ta janye jikinta daga cikin nasa suk fuskanci juna sosai sannan ta ce, "Ya kai dana ka yi sani cewa ba komai ne ya sani wannan kuka ba face tsananin tausayinmu gaba daya nan. Tabbas ko nan gaba idan ana bayar da labarinmu sai an yi kuka a duniya kuma labari ne irin wanda baya shafewa kuma ba za a taɓa mantawa da shi ba. Ko a iya nan labarinmu ya tsaya mun aje tarihin abin al'ajabi kuma abin alfahari".
Sa'adda mahaifiyar Imran ta zo nan a jawabinta sai Imran ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ya ke Ummina ki yi sani cewa a cikin matafiyan nan gaba daya ba masu sa'a sama da mu ni da ke. Duk tsananin masifun da muka hadu da su a baya ni da ke babu wanda ya rasa wani bangare na jikinsa, amma sauran abokan tafiya kuwa daga wanda ya sami manyan raunika a jikinsa sai wanda ya rasa masoyi da wanda ya rasa wani бangare na jikinsa.Ina ji a jikina cewa har mu shiga cikin kogon Darul Iksina babu abin da zai same mu kuma sai bukatarmu ta biya."
Koda jin wannan batu sai mahaifiyar tasa ta dube shi cikin firgici ta ce, "Haba ya kai dana kai kuwa mene ne tabbacinka cewa za mu sami wannan nasara alhalin har yanzu akwai sauran tashin hankali a gabanmu na shiga cikin kogon Darul Iksina?"
Ya yin da Imran yaji wannan batu sai ya yi murmushi ya ce, "Ba komai ne ya sa nake da wannan yakinin ba face na san cewa a duniya babu wata soyayya mai karfi sama da soyayyar da ke tsakanin da da mahaifi. Ya ke Umkina ki tuna cewa tun ina cikin cikinki kike dawainiya da ni kike shan wuya har kika haife ni sannan kika shiga rainona. Sa'adda na fara zama mutum kuwa sai ya zamana cewa soyayyarki a gare ni kullum tana karuwa kuma ya zamana cewa ko kuda ba kya son ya taɓa dafiyar jikina. Ba zan taɓa mantawa ba da irin dawainiya da wahalar da muka sha ta rayuwar talauci, rashin makwanci da tsananin yunwa gami da yawo kwararo-kwararo har ta kai mu ga zaman dole a cikin daji. Na yi imani a zuciyata cewa wannan wahala da muka sha ba za ta zamo a banza ba, lallai sai mun ji dadi kafin cikar ajalinmu".
Ya yin da Imran ya zo nan a zancensa sai mahaifiyarsa ta cika da dumbin farin ciki ta sake rungume shi a kirjinta tana mai bushewa da dariyar murna shi ma ya tayata dariyar.
A dai-dai wannan lokaci ne Boka Muzaffar ya mike tsaye ya dubi gaba dayan abokan tafiyar daya bayan daya ya ce, "Ya ku 'yan uwana ku yi sani cewa yau ne muka kawo karshen wuya a cikin wannan tafiya tamu kuma daga nan zuwa kogon Darul Iksina tafiya ce ta kwana uku kacal. Ina mai tabbatar muku da cewa babu wani mugun abu da za mu sake haduwa da shi akan hanya har mu isa kogon Darul Iksina amma ku sani cewa a cikin kogon Darul Iksina akwai masifu iri-iri har kala dari tara da casa'in da tara. Gaba dayanku nan babu wanda ya san yadda za a iya tsallake masifun da ke cikin wannan kogo face ni saboda haka da zarar mun shiga cikin kogon ku kasance masu biyayya a gare ni da bin umarnina. Duk abinda na ce ku yi kawai ku yi shi cikin gaggawa kada ku yi mini gardama ko jayayya. Idan kunne ya ji, gangar jiki ta tsira. Yanzu zamu zauna anan har tsawon kwana uku domin mu yi jinyar raunikan jikinmu sannan mu ci gaba da tafiya".
Koda gama wannan jawabi sai Boka Muzaffar ya koma inda yake ya zauna. Zamansa ke da wuya sai jarumi Shaharan ya dube shi ya ce, "Ya kai jagoran wannan tafiya ina da tambaya guda daya a gare ka. Wai shin me ya sa tun da muka fara wannan tafiya ba ka ceci rayuwar mutum daya ba daga cikinmu da karfin sihirinka? Ka tuna fa cewa ka shafe shekaru masu yawa kana bincike da hidima akan wannan tafiya tamu, ai ya ci ace ka san duk irin bala'in da za mu fuskanta a cikinta ka tanadar mana riga-kafinta."
Koda jin wannan batu sai Boka Muzaffar ya kyalkyale da dariya sannan ya hade fuska kamar an aiko masa da sakon mutuwa ya ce, "Ya kai Shaharan ka yi sani cewa babu wani sihirin tsafi da ya isa ya yi tasiri a cikin wadannan dazuzzuka biyar da muka ratsa fiye da shekaru dubu da suka gabata haka wannan al'amari yake amma idan muka shiga cikin kogon Darul Iksina kowannenmu sihirin tsafinsa zai iya tasiri".
Koda Boka Muzaffar ya zo nan a zancensa sai Shaharan ya mike