Showing 48001 words to 51000 words out of 75493 words

Chapter 17 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt

guda kuma ya murtuke fuska ya ce, "Sunana Sharkamuza ibini Zarlala na kasance daya daga cikin manyan hadiman Serki Nashmir na Birnin Hindu. Waďannan jaruman da ke tare da ni kuwa Sharmal, Zarhuf da Hazwan kenan, manyan Dakarun yaki na Sarki Nashmir. Sarkinmu ya aiko mu ne a gare ku domin mu ragargaza ku mu yi filla-filla da sassan jikinku domin kun kasance manyan abokan gabarsa masu son raba shi da 'yarsa da kuma wani sirrin tsafinsa. Idan kuna da wasiyya ta karshe ga iyalanku sai ku furtata yanzu kafin mu zare muku ruhin numfashi. Lallai za mu isar da wasiyarku. Wannan shi ne iyakar alfarmar da za mu iya yi muku."

Kafin Aljani Sharkamuza ya gama rufe bakinsa sai Aljani Maruful Dauwaz ya tari numfashinsa yana mai kara daka masa tsawa a karo na biyu ya ce, "Ya kai tsohon azzalumi ka yi sani cewa karyarku ta sha karya ba ku isa ku ida nufinku ba akanmu. Ina tabbatar maka da cewa da cewa sai mun yi fata-fata da ku mun maishe ku gawa sannan mun dangana da fadar Sarkin naku mun kawar da shi kuma mu dauke 'yar tasa gami da sihirin tsafin nasa."

Koda jin wannan batu sai Aljani Sharkamuza da su jarumi Sharmal suka fusata ainun jikinsu ya kama tsuma. Cikin bakin zafin anma Sharkamuza yai sama ya kawowa Maruful Dauwaz wawan naushi da zabgegen hannunsa. Maruful Dauwaz yai wuf ya sunkuya hannun Sharkamuza ya naushi iska amma sai iskar hannun nasa ta yi fatali da Maruful Dauwaz ta dauke shi ta makashi a jikin wani tsauni ya sulale kasa a matukar galabaice.

A zaton Sharkamuza kasusuwan bayan Maruful Dauwaz sun kakkarye amma bisa mamaki sai ya ga ya mike tsaye zumbur kamar babu abin da ya same shi sannan ya zare takobinsa yana mai gyara tsayuwa.

Duk wannan abu da ke faruwa Rahila da Sarki Laffaru na rike da gashin wuyan aljanu Maruful Dauwaz suna reto ba su yarda sun fado kasa ba.

Koda ganin abin da ya faru sai Aljani Sharkamuza da su jarumi Sharmal su ma suka zare takubbansu suka sake rugawa izuwa kansa aka ruguntsume da sabon azababben yaki ya zamana cewa suna kai wa junansu sara da suka cikin zafin nama, juriya da bajinta.

Shi kuwa Sarki Laffaru wanda ya fara kokarin kai harbi da kibiya sai Sharmal ya daka wawan tsalle sama daga kan Sharkamuza ya doki kirjinsa da kafa daya. Kamar ya daki tamaula haka Laffaru ya lula can baya ya gwara kai a jikin wani dutse. Nan take kan nasa ya dare jini tsa jini yai tsartuwa ya fado kasa sumamme ko motsin kirki bai yi ba. Nan fa gumurzu ya dawo tsakanin rai biyu da rai hudu.

Wohoho! Hakika idan mutum ya ga mutuwa muraran a sannan ne yake iya yin abin da shi kansa bai taɓa tsammanin zai iya ba. Nan take Rahila da Maruful Dauwaz suka fusata ainun sakamakon ganin abin da ya faru ga Laffaru ya zamana cewa sun kara ZAGE DANTSE iya karfinsu aka cigaba da bakin artabu.

Duk sa'adda takubba suka haɗu sai dai ka ga tartsatsin wuta da hayaki na tashi.

Da yake su Sharmal sun kasance sadaukai masu karfin Allah Ya isa, nan da nan suka fara jigita Rahila da Maruful Dauwaz har ta kai cewa ba sa iya mai da martani sai dai kokarin kare kai.

Koda aka sake dan jimawa a haka sai su Sharmal suka sami nasarar buge takobin Rahila ta fadi can gefe daya kafin ta yi wani yunkuri tuni Sharmal, Zarhuf da Hazwan sun kai ma ta hari a lokaci guda.

Sharmal ya dankara ma ta sara a gadon bayanta, Zarhuf ya sare ta a cinyarta, shi kuma Hazwan ya soke ta a gefen kirjinta 6angaren hagu Take Rahila ta kwarara uban ihu a lokacin da jini yai feshi da tsartuwa daga jikinta sannan ta subuto daga kan Maruful Dauwaz ta baje a kas wanwar babu alamar rai a jikinta.

Koda Maruful Dauwaz ya ga abin da ya faru da Rahila sai ya fusata ainun irin fusatar da bai taɓa yi ba a rayuwarsa, kawai sai ya kurma wawan ihu ya sake afkawa su Aljani Sharkamuza su duka hudun ya hau su da SARA DA SUKA ba ji ba gaji.

Duk da cewa su hudun suka tarar masa sai ga shi ya zame musu alakakai domin sun kasa koda kwarzanar jikinsa.

Abin da ya tayar wa da Mauruful Dauwaz hankali shi ne shi ma ya kasa yivwa koda dayansu rauni. In ba don ma yana da matukar naci da juriya ba da tuni sun hallaka shi.

Ana cikin wannan gumurzu ne Aljani Sharkamuza ya shammaci Maruful Dauwaz ya durma masa wawan dundu a gadon baya. Saboda tsananin zafi da zogin da Maruful Dauwaz ya ji bai san sa'adda ya saki takobinsa ba ta fadi kasa kuma ya durkushe bisa guiwoyinsa ya kama amai da gudan jini.

Har Sharmal, Zarhu da Hazwan sun daga takubbansu na sihiri sama za su gididdiba Aljani Maruful Dauwaz sai Sharkamuza ya yi musu nuni da su tsaya, sai suka saurara. Sharkamuza ya dubi su Sharmal ya ce, "Haba! ai abin kunya ne a ce mun kashe wannan Aljanin da makami, da karfin dantsena zan kashe shi. Gama fadin hakan ke da wuya sai aljani Sharkamuza ya cafi makoshin Maruful Dauwaz da hannun hagu sannan ya shiga gabza masa naushi da hannunsa na dama a fuska. Karar naushin ta cika dajin gaba daya tamkar ana dukan dutse da katuwar guduma. Nan da nan cikin kankanin lokaci ya kumbura fuskara Maruful Dauwaz ko ina ya duri jini, tun Maruful Dauwaz na iya ihu har sai da muryarsa ta dashe, jikinsa gaba daya ya saki kamar an jika tsumma a ruwa ya zamana ccwa ko motsa dan yatsan hannunsa ba ya iya yi a lokacin da jini ke ta kwarara daga fuskar tasa. Sai da Aljani Sharkamuza ya ga ko kadan babu alamar numfashi a tare da Maruful Dauwaz sannan ya daina naushinsa, sannan ya bushe da mahaukaciyar dariyar mugunta, kuma ya shiga yi wa kansa kirari yana koda kansa.

A daidai wannan lokaci ne Sarki Laffaru ya farfado daga dogon suman da ya yi, kawai sai ya ji kansa ya yi masa nauyi ainun har ma ya fi sauran gangan jikin nasa don haka sai ya kasa mikewa.

Koda ya bude idanunsa a hankali sai ya hango Aljani Maruful Dauwaz a hannun Aljani Sharkamuza ya shake wuyansa, kafafun Mauful Dauwaz na reto babu alamar rai a tare da shi. Nan take hawaye ya zubowa Sarki Laffaru domin ya sa cewa yau dai karshen rayuwarsa ce ta zo.

Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai Aljani Sharkamuza ya ji Maruful Dauwaz ya gabza masa wawan naushi a ido. Saboda karfin naushin sai da hannun Maruful Dauwaz ya shige cikin kwarmin idonsa ya fito ta keyarsa. Maruful Dauwaz na zare hannunsa daga cikin kokon kan sai Sharkamuza ya yanke jiki ya fadi kasa matacce.

Koda Shamral, Zarhuf da Hazwan suka ga wannan gagarumar jarumtaka da Maruful Dauwaz ya yi alhalin a zaton su ma ya mutu ba shi da rai sai suka firgaita ainun, jikinsu ya kama karkarwa suka kasa sake afkawa Maruful Dauwaz.

Maruful Dauwaz ya dube su a fusace sannan ya takarkare ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa. Ai kuwa sai su Shamral suka dada dimaucewa suka falfala da gudu izuwa cikin dajin Hizurul Aswad ba tare da sanin inda suka dosa ba.

Maruful Dauwaz ya ruga inda Gimbiya Rahila ke kwance ya rungume ta a jikinsa ya fashe da kukan bakin ciki. Ba zato ba tsammani sai ya ji ta kawo gwauron numfashi. Nan take Maruful Dauwaz ya cika da tsananin farin ciki da ya ga ba ta mutu ba dama tuni ya ga Sarki Laffaru yana numfashi ya san cewa yana raye.

Cikin gaggawa Maruful Dauwaz ya shiga dinke raunika ukun da ke jikin Rahila. Bayan ya gama dinke mata raunikan sai ya shafa mata magani jini ya daina zuba sannan ya sa mata battar ruwa a bakinta ta sha. Daga nan sai ya koma kan Sarki Laffaru shi ma ya dinke masa wannan rauni da ke kansa ya sa masa magani.

Lokacin da Rahila ta farfaɗo sosai ta dawo cikin haiyacinta ta ga yadda fuskar Maruful Dauwaz ta kumbura kuma ta yi kaca-kaca da jini har ya zamana cewa ba a shaida kamanninsa sai ta fashe da kuka kuma ta dube shi cikin matukar alamun tausayawa ta ce, "Ya kai jarumin jarumai, ka gafarce ni, hakika ni ce na janyo maka wannan masifa kuma yanzu ne na gane irin wahalar da ka hango mana za mu shiga bayan ka yi halwar nan ta kwana uku".

Koda jin wannan batu sai Aljani Maruful Dauwaz ya budi baki da kyar a lokacin da yake numfashi sama-sama kamar ba zai rayu ba ya ce, "Ya ke wannan 'yar Sarki ki yi sani cewa wannan wahalar da muka sha yanzu ba komai bace fac somin taɓi daga cikin irin wahalar da za mu sha nan gaba. Bai kamata ki ba ni hakuri ba ko ki nemi gafarata ba tunda ban fito wannan gwagwarmaya don ke ba sai domin na cika burin masoyiyata marigayiya Rashmin. Abin da nake so da ke kawai shi ne idan har mun sami nasara bisa abin da muka fito nema ki kasance mai cika alkawari a gare ni". Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa Gimbiya Rahila ta yi shiru ba ta ce komai ba.

A wannan lokaci ne Sarki Laffaru ya mike da kyar daga inda yake kwance ya dawo wajen su Maruful Dauwaz ya zauna sannan ya dubi Maruful Dauwaz cikin alamun karayar zuciya ya ce, "Zai fi kyau mu hakura da wannan bukata da ke gabanmu domin babu yadda za a yi mu kai ga samun nasara.

Ku duba fa ku gani, wadannan Dakarun Sarki Nashmir ne su hudu kacal suka jefa mu a cikin wannan hali, idan kuma muka isa fadarsa ya za mu yi da miliyoyin Dakarun nasa?"

Kafin Sarki Laffaru ya gama rufe bakinsa tuni Maruful Dauwaz ya tari numfashinsa yana mai cewa, "A kul! Ka kara yi mana irin wannan furuci. A iya rayuwata duk abin da na sa a gabana sai na yi nasara.

Duk wuya duk rintsi ba na gudu kuma ba na ja da baya. Babu abin da zai sa mu janye akan wannan al'amari face ba na numfashi a doron kasa.

Lallai yanzu za mu zauna anan mu yi jinyar raunikan jikinmu har izuwa tswon kwana goma sha hudu sannan mu ci gaba da tafiya, saboda kasusuwan fuskata guda bakwai ne suka karye.

Hakika a iya rayuwata ban taɓa yin karo da sadauki mai tsananin karfin naushi ba kamar Aljani Sharkamuza. Tabbas na jinjina masa domin ya cika gwarzo, ba zan taɓa mantawa da shi ba.

Koda jin haka sai Rahila ta yi ajiyar numfashi ta çe, ai komai gwarzontakarsa da karfin naushinsa bai kai naka ba, tunda kai ka iya shanye naushinsa da yawa amma da ka yi masa naka guda daya sai ga shi ka burma masa kai ya zama gawa".

Cikin mamaki Maruful Dauwz ya dubi Rahila ya ce, "Yaya aka yi kika san da faruwar hakan alhalin sa'adda abin ya faru kina kwance a sume?"

Rahila ta yi murmushi cikin karfin hali ta ce, "ban gan sa'ad da abin ya faru ba amma lokacin da na farfado na ga gawar Sharkamuza kuma na ga kansa a 6ule alamar shatar hannu ce ta bula shi, shi ne na aiyana faruwar al'amarin a cikin zuciyata".

Koda jin haka wannan batu sai Maruful Dauwaz ya kwanta a kas ya baje sosai don ya huta yana mai cewa, "tabbas kina da hikima da basira Idan kun huta ke da Laffaru za ku taru ku gyare karayar kasusuwan fuskata.

Wannan shi ne abin da ya faru ga su Aljani Maruful Dauwaz bayan sun yi MUGUN GAMO da su Aljani Sharkamuza sun fafata kazamin yaki.

*****

A can Birnin Hindu kuwa cikin fadar Sarki Nashmir, duk abin da ya faru tsakanin su jaruma Rahila da su Aljani Sharkamuza a dajin Hizurul Aswad Sarki Nashmir da dukkan fadawansa sun gani a cikin madubin tsafinsa.

Koda gama ganin wannan al'amari sai Sarki Nashmir ya kamu da tsananin bakin ciki. Cikin tsananin fishi ya mike tsaye ya kwarara uban ihu wanda ya zamo sanadiyyar girgizar fadar gaba daya, duk mutanen da ke cikin fadar suka dimauce sannan kuma sai ya naushi katon madubin tsafin nasa wanda ke manne a jikin bango.

Nan take mdubin ya rugurguje ya tarwatse yai gutsun-gutsun. Sarki Nashmir ya sake dakawa fadawansa tsawa ya ce, "Kowa ya bar su su biyu rak daga shi sai Sarkin yakinsa sadauki Najwar.

Nan da nan kuwa kowa ya fice ya bar su fadar tayi tsit tamkar babu wani mahaluki mai numfashi a cikinta. Tsawon 'yan dakiku Sarki Nashmir da Najwar na kallon juna dayansu bai ce uffan ba. Daga can sai Sarki Nashmir ya kyalkyale da dariya, lokaci guda kuma ya murtuke fuska ya dubi Najwar ya ce. "Ya kai Sarkin yakina abin alfahari a gare ni, ina son ka yi shiri yanzu ka tafi izuwa dajin Hizurul Aswad ka hallaka Aljani Maruful Dauwaz da abokan tafiyarsa tunda su Aljani Sharkamuza sun kasa kawar da su."

Sa'adda sadauki Najwar ya ji wannan umami sai ya dubi Sarki Nashmir cikin alamun tsoro da matukar damuwa ya ce, "Ya shugabana ka yi sani cewa Aljani Maruful Dauwaz ba karamin hatsabibi ba ne don haka ina matukar shakkar tararsa da yaki duk da cewa kuwa na san na fi karfinsa. Ina mai baka shawarar ka yi shiri da kanka ka je ka gama da shi tun gabannin ya iso nan ya yi maka muguwar ɓarna".

Koda sadauki Najwar yazo nan a zancensa sai Sarki Nashmir ya sake bushewa da dariya a karo na biyu daga bisani kuma sai ya murtuke fuskarsa kamar an aiko masa da sakon mutuwa ya nuna Najwar da yatsa cikin fishi ya ce, "Ya kai Najwar ka yi sani cewa duk wani motsi da za ka yi akan tafin hannuna kake. Na san sirrin zuciyarka fiye da yadda kake tsammani. Karya kake yi ka ce da ni kana shakkar yin karo da Aljani Maruful Dauwaz domin ka fi karfinsa nesa ba kusa ba. Na sani cewa ka daɗe kana da burin ka ga na mutu ka haye kan karagata sannan ka auri 'yata Gimbiya Ramlatul Siyam da karfin tsiya, amma baka sami damar hakan ba. In da za ka iya hallaka ni da tuntuni ka kawar da ni. Bisa dole ne ka hakura ka ci gaba da jira.

Yanzu zan ba ka zabi guda biyu. Ko dai mu yi yakı yanzu take anan cikin fadata idan ka kashe ni ka sami karagata da 'yata. Idan kuma ni ne na kashe ka shi ke nan sai na je na tari su Aljani Maruful Dauwaz. Idan. kuwa ba za ka iya yakata ba sai ka shirya ka tafi izuwa dajin Hizurul Aswad. Maza ka yankewa kanka shawara yanzu-yanzu"

Sa'adda Najwar ya ji wannan zaɓi da Sarki Nashmir ya ba shi sai hankalinsa ya dugunzuma ainun yai shiru yana tunanin abin da ya kamata ya yi. Kawai sai Sarki Nashmir ya mike tsaye ya zare takobinsa ya ce, "Tunda ka kasa bai wa kanka zabi sai mu yi yakin.

Da jin haka sai sadauki Najwar ya yi murmushi sannan ya risina cikin biyayya ya ce, "Haba ya shugabana, wane ni na ce zan yi yaki da kai alhalin tuntuni na jarraba na gani cewa kana gaba da ni. Na amince zan tafi na tari su Aljani Maruful Dauwaz kuma na rantse da darajar karagarka ba zan dawo nan gare ka ba sai da kan Maruful Dauwaz da na abokan tafiyarsa".

Koda gama fadin hakan sai sadauki Najwar ya juya ya fice daga cikin fadar da sauri. Cikin kankanin lokaci ya isa gidansa ya shiga kimtsawa. Cikin hanzari ya yi gagarumar shigar yaki, ya debo dukkan gurayensa da layunsa na tsafi ya daurasu a jikinsa sannan ya fito ya hau kan wani basamuden Aljani wai shi BARUKUL MASNUR wanda ya ninka Sharkamuza sau uku a girma da karfin dantse da na sihiri.

Nan take Barukul Masnur ya bude fuka- fukansa ya tashi sama dauke da sadauki Najwar suka luluka a cikin gajimare.

Lokacin da Sarki Nashmir ya fito daga cikin fadarsa bayan ya gama ganawa da sadauki Najwar sai ya wuce kai tsaye izuwa cikin gidan sarautar ya nufi bangaren da turakar Gimbiya Ramlatul Siyam. Duk inda Sarki Nashmir ya ratsa sai ka ga wadannan Dakaru na aljanu da na bil'adama suna sujjada a gare shi kuma suna buɗa masa hanya yana wucewa.

Koda Sarki Nashmir ya dubi miliyoyin Dakarun aljanun da ke shawagi a kan saman rufin turakar Gimbiya don tabbatar da tsaro sannan ya dubi miliyoyin Dakarun bil'adama da suka kewaye harabar turakar gaba daya sai ya cika da farin ciki ya kama zancen zuci yana mai cewa a ransa, ya ma su Aljani Maruful Dauwaz za su iya shigowa har cikin wannan fada su kashe gabadayan wadannan Dakaru sannan su sace Gimbiya Ramlatul Siyam? To wai shin ma shi yana ina har hakan za ta faru?

Abu na biyu kuma, ta yaya su Maruful Dauwaz za su sami yawun barcin bakinsa alhalin shi ba ya barci sai sau daya a cikin kwanakin mako?"

Koda Sarki Nashmir ya zo nan a zancen zucinsa sai ya kyalkyale da dariya a fili bai sani ba har Dakaru, barori da kuyangin gida sarautar suka bi shi da kallo suna mamakin dalilin dariyar tasa.

A daidai wannan lokaci ne ya iso daf da kofar turakar Gimbiya Ramlatul Siyam, Dakarun da ke tsaron kofar turakar suka bude masa ya kunna kai ciki. Sai da ya yi doguwar tafiya a cikin turakar sannan ya iso cikin dakin barcin Gimbiya Ramlatul Siyam, ko ina ya duba sai dai ya ga kuyangin na ta hidima iri-iri.

Da shigar Sarki Nashmir cikin dakin barcin sai ya iske Gimbiya Ramlatul Siyam ita kadai kwacen akan gado ta yi rub da ciki tana ta faman rusa kuka.

Cikin tsananin mamaki da tashin hankali Sarki Nashmir ya karasa gare ta ya zauna a gefen gadon ya tashe ta zaune a lokacin da idanunta suka cika sharkaf da hawaye ya dube ta a cikin matukar damuwa ya ce, "Ya ke 'yata, mene ne ya faru gare ki wanda har ya sa ki zubar da hawaye? Kin sani cewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login