Showing 39001 words to 42000 words out of 75493 words
Chapter 14 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt
Darul Iksina amma yanzu zan janye wannan alkawari albarkacin wannan wasiyya ta masoyiyata wacce ban san da ita ba sai yanzu.
Gargadina na karshe a gare ki shi ne, ina son ki sani cewa na san kalar rubutun masoyiyata, kuma gaba dayan matan aljanu na duniya babu mai irin rubutun Rashmin. Lallai idan na ga rubutun ba nata ba ne hukuncin kisa ya tabbata akanki. Ke ba ma rubutun ba, hatta tauwadar da aka yi rubutun da ita na san irin kalar ta gidan su masoyiyata Rashmin, idan ba da ita aka yi rubutun ba na san karya ne ba wasiyyarta ba ce.'
Sa'adda Rahila ta ji haka sai ta yi murmushi ta ce, "Duk na yarda da wannan sharadin naka."
Nan take Rahila ta kwashe labarin haduwarta da su Boka Muzaffar da kuma yadda aka yi suka je suka dauko sauran abokan tafiya a kasashe daban-daban, aka ratsa wadannan manyan dazuzzuka aka iso nan kogon Darul Iksina har da irin bakar wabalar da suka sha da kuma rayukan da aka rasa.
Koda Rahila ta gama bayar da wannan labari sai Aljani Maruful Dauwaz ya jamu da tsananin tausayi har ya fashe da kuka, sai ga shi Rahila da Laffaru suna rarrashinsa. Da kyar ya daina kukan sannan ya nutsu ya dubi Laffaru da Rahila ya ce, hakika Boka Muzaffar ya cuce ku kuma ya cika azzalumi. Tabbas kun yi babban kuskure da har kuka bar shi ya sami nasarar shiga wannan gida na farko da ke cikin wannan kogon na Darul Iksina, domin babu makawa sai ya mallaki Mashin Galilul Haras. Idan kuwa ya mallaki mashin Galilul Haras tamkar ya mallaki duniya ne.
Abu daya za mu iya yi mu tsayar da sihirin da ke jikin Mashin Galilul Haras. Ba komai bane face mu je mu nemo yawun barci na bakin SARKI NASHMIR BN HAYAT na Birnin HINDU, Sarkin da a halin yanzu babu wani matsafi da ya kai shi karfin sihirin tsafi a duniya, kuma shi ma babu yanda bai yi ba akan yazo nan kogon Darul Iksina don ya mallaki mashin Galilul Haras amma abu ya gagara. Idan har muka samo yawun barcin Sarki Nashmir muka kai shi can gidan tarihi na Sarautar Birnin KISRA, muka binne shi a cikin gidan to duk inda mashin Galilul Haras yake zai kai kansa can ya adana kansa babu wanda zai iya sake mallakarsa face wanda ya tono inda aka binne wannan yawu ya jika kasar ya sha."
Sa'adda aljani Maruful Dauwaz ya zo nan a jawabinsa sai Rahila da Sarki Laffaru suka dubi junansu cikin alamun tsananin mamaki.
Rahila ta dubi Aljani Maruful Dauwaz ta ce, "Ashe faduwa tazo daidai da zama, ai bukatar da muke so ka biya mana ba komai bace face ka je har fadar Sarki Nashmir ka sato mana 'yarsa Gimbiya Ramlatul Siyam domin Laffaru ya aure ta sannan ni ma na aure shi, saboda haka me zai hana a jefi tsuntsu biyu da hoge daya Ma'ana, idan ka je sato Gimbiya Ramlatul Siyam sai kuma ka samo yawun barcin mahaifin nata?"
Koda Aljani Maruful Dauwaz yaji wannan batu sai ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa wanda ya sa gaba daya kogon ya kama girgiza har sai da ya tsuke bakinsa sannan komai ya dawo daidai.
Cikin tsananin fushi Aljani Maruful Dauwaz ya dubi Rahila da Laffaru ya ce, "Hakika kun cika wawaye masu tarar aradu da ka. Idan da kun san irin tsananin tsaron da ke cikin fadar Sarki Nashmir ba za ku ce na je na sato 'yarsa ba bare kuma har na samo yawun barcinsa ba. Ina tabbatar muku da cewa komai jarumtakar Aljani ko mutum muddin ya kuskura ya yi gaba da gaba da Sarki Nashmir sai dai uwarsa ta haifi wani. Ta yaya kuke zaton cewa zan iya shiga fadar Sarki Nashmir har na iya yi muku wannan aiki guda biyu?"
Yayin da Rahila ta ji wannan batu sai ta kamo hannun Sarki Laffaru ta ja shi suka juya don su fita daga cikn gidan.
A dimauce Aljani Maruful Dauwaz ya kira sunanta ya ce, "Ya ke Rahila, yaya kuma za ki tafi ba mu gama magana ba?"
Rahila ta juyo ranta a ɓace ta ce, "Me kuma za mu tsaya mu yi maka tun da ba ka da wani amfani a gare mu, kuma ba ka bukatar wasiyyar masoyiyarka, shi kenan, sai ka ci gaba da zaman jiran ranar ajalinka a nan cikin kogon Darul Iksina. Amma ka sani cewa idan har ka mutu ba ka biya bukatar masoyiyarka Rashmin ba wacce ke rubuce a cikin wasiyyarta lallai ka ci amanar soyayyaku".
Gama fadin hakan ke da wuya sai Rahila da Laffaru suka sake juyawa da sauri suke, nufi bakin kofar gidan.
Tsulum! Sai suka ga Aljani Maruful Dauwaz ya baiyana a gabansu hawaye na zuba a idanunsa, Kawai sai ya dube su ya ce, "Raina fansa ne ga bukatar masoyiyata gimbiya RASHMIN. Na amince zan biya muku bukatarku koda kuwa zan hallaka. Ma za ku hau kaina mu bar wannan kogo yanzu-yanzu domin mu je mu fara shirye-shilyen zuwa fadar Sarki Nashmir da Birnin Hindu".
(Ni Maiboko na zabi aljani Maruful Dauwaz a matsayin madubina a cikin abin da ya shafi soyayya. Ina koyi da halayensa ďari bisa ďari)
Lokacin da Rahila da Laffaru suka ji wannan jawabi na Aljani Maruful Dauwaz sai suka cika da tsananin farin ciki. Nan take suka hau kansa suka zauna, shi kuma sai ya bude fuka-fukansa ya tashi da su sama ya keta ta cikin rufin saman kogon kamar yadda danshi ke tsattsafowa daga cikin kasa.
Nan da nan ya luluka a cikin gajimare ya fara tsala azababben gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya.
A daidai wannan lokci ne Rahila ta tuno da sauran abokan tafiyarsu wadanda suka baro a cikin kogon Darul Iksina. Nan take hankalinta ya dugunzuma ta dubi Aljani Maruful Dauwaz ta ce, "Kash! Na manta ban nemi alfarma a wajenka ka ceto rayuwar sauran abokan tafiyarmu da muka baro a cikin kogon Darul Iksina".
Koda jin haka sai Aljani Maruful Dauwaz ya gyada kai cikin alamun takaici da tausayi ya ce, "Ai kuwa kin yi babban kuskure domin yanzu bakin Alkalami ya bushe. Babu wani mahaluki da ya isa ya shiga cikin daya daga cikin gidajen da ke kogon Darul Iksina face ya zama gawa. Ni kaina na manta da batun abokan tatiyar taku kuma ya kamata ki yi mini uzuri saboda mu aljanu babu halittar da ta fi mu yawan mantuwa".
Koda jin haka sai hankalin Rahila ya sake dugunzuma ainun ta ce, "Yanzu kana ganin kuwa su Imran za su iya fitowa daga cikin kogon Darul Iksina?"
Koda jin wannan tambaya sai Aljani Maruful Dauwaz yai ajiyar zuciya sannan ya ce, "Tun kimanin shekaru dubu uku baya da wanzuwar kogon Darul Iksina babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da ya taɓa shiga cikinsa ya fito a raye sai ni din nan yanzu sai kuma ku biyun nan. Saboda haka ba ni da wata amsa da zan iya ba ki akan wannan tambaya. Amma dai na san cewa in ba wanda ya san dalasiman tsafin da ake karantawa ba kofar kogon ta bude babu wanda zai iya shiga cikinsa ko kuma ya fito daga cikinsa. Ina tabbatar miki da cewa duk duniya babu wanda ya san wadannan dalasiman tsafi face mutum daya da Aljani daya.
ba wasu ba ne face ni kaina da kuma wannan hatsabibin Boka naku, wato Boka Muzaffar wanda a halin yanzu na san tuni ya ďauki mashi galilul Haras ya tafi da shi izuwa can dakin halwar tsafinsa.
Ba zai fito ba daga cikin dakin tsafin nasa sai bayan cikar kwana arba'in. A ranar da ya fito ne zai mallaki kowa da ke cikin wannan duniya, kun ga ke nan, gagarumin aikin da ke gabanmu ba kadan ba ne. Ya zama dole mu yi iya kokarinmu mu tabbatar da cewa mun sami nasarar sato Gimbiya Ramlatul Siyam gami da yawun barcin mahaifinta kafin cikar kwana arba'in din har mu je mu binne yawun a can gidan tarihi na Birnin Kisra. Ku sani cewa samun nasarar wadannan abubuwa biyu dai-dai yake da tafiya neman Jaki mai kaho!
Lokacin da Aljani Maruful Dauwaz ya zo nan a jawabinsa sai jikin Rahila da na Sarki Laffaru ya yi sanyi matuka kuma hankalinsu ya dugunzuma ainun suka sami karayar zuciya bisa samun nasara akan wannan gagarumar bukata tasu don haka duk su biyun sai suka yi shiru suna tunani.
Sa'adda Aljani Maruful Dauwaz ya ji su Rahila sun yi shiru sai ya bushe da dariya sannan ya ce, "Ya ku abokan alkawarina, kada ku dakushe zuciyoyinku da tunanin rashin samun nasara. Ku sani cewa tsakanin RASHI DA SAMU taki ne dan mitsitsi. Tabbas matsoraci ba zai taba zama gwani ba, kuma sai an gwada akan san na Kwarai. Lallai za mu siyar da rayuwarmu ko don mu ceto mutanen duniya daga sharrin Boka Muzaffar domin idan ya fito daga wannan halwar tsafi ta kwana arba'in sai ya buwayi mutane da aljanu. Kai hatta dabbobi ma da ke cikin daji sai sun shiga uku. Yanzu sai ku fada mini inda za mu je mu keɓe kanmu domin ina son ni ma na shiga halwar tsafi ta kwana uku rak saboda na gano matsalolin da za mu fuskanta ya yin da muka tafi izuwa Birnin Hindu don sato Ramlatul Siyam da samo yawun barcin mahaifinta, na san yadda zan tare su kuma na gano yiwuwar samun nasararmu da rashinta".
Koda jin haka sai Rahila ta dubi Sarki Laffaru ta ce, "Ko Birninka za mu je ne? Laffaru ya zazzaro idanu ya ce, "Shin kin mantane da bala'in da nake ciki? Yanzu haka Sharlis tana nan a masarautata ta dora danta Shadaddu akan karagar mulkina.
Burinta shi ne yanzu ta kama ni ta tsare har sai danta ya girma sannan ya yi mini KISAN GILLA bayan ya yi mini mugun wulakanci ya tozarta ni a kasata gaban talakawana.
Ni a yanzu ma in ban da muna tare da Maruful Dauwaz da ba zan taba samun kwanciyar hankali ba. Abin da nake bukata yanzu shi ne, idan Maruful Dauwaz ya shiga halwar tsafinsa ya yi mini bincike shin gaskiya ne idan na auri Gimbiya Ramlatul Siyam zan haifi 'yar da za ta kare ni daga sharrin dana Shaddadu? Hakika na tsorata da maganganun Boka Muzaffar babu mamaki karya ya shirya mini".
Koda jin haka sai Aljani Maruful Dauwaz ya bushe da dariya sannan ya ce, "Ya kai wannan Sarki, ka kwantar da hankalinka ka sani cewa na yi maka alkawari muddin muna tare babu abin da zai same ka, amma fa sai idan ka tabbatar da cewa a zamanin da kana kan sarautarka ba ka yi mulkin Zalinci ba domin ni a rayuwata babu abin da na tsana sama da zalunci, cin amana da rashin gaskiya."
Koda Sarki Laffaru ya ji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma kuma cikinsa ya duri ruwa domin ya san cewa a lokacin mulkinsa ne ya zalunci Sharlis da zuri'arta kuma a dalilin haka ne mahaifinta ya yi gagarumin tanadi na daukar fansa akansa.
Nan take Laffaru ya aiyana a zuciyarsa cewar ba zai taɓa gaya wa Aljani Maruful Dauwaz gaskiyar labarinsa ba bisa irin mulkin zaluncin da ya yi a kasarsa da yadda ya cutar da Sharlis dadanginta.
Haka dai Aljani Maruful Dauwaz ya ci gaba da tsala gudu a sararin samaniya har izuwa tsawon sa'a biyar ya zamana cewa Rahila da Laffaru ba su kara cewa uffan ba har ma suka fara gyangyadi.
Koda Aljani Maruful Dauwaz ya fahimci halin da suke ciki sai ya dan kada jikinsa suka farka a firgice. Aljani Maruful Dauwaz ya ce da su, "Ku yi hakuri na tashe ku daga barci, hakan ta faru ne saboda har yanzu ba ku zaɓi inda ya kamata mu je ba. Muna bukatar inda za a karɓe mu hannu biyu kuma mu sami damar gudanar da harkokinmu cikin sirri".
Caraf! Sai Lahir ta ce, "Mu je kasarmu dornin a can ne nake da yakinin ba za mu fuskanci wata matsala ba, kuma ina son na sake saduwa da mahaifinatun gabannin burina ya gama cika saboda na san cewa na bar mahaifina a cikin kewata".
Koda jin wannan batu sai Aljani Maruful Dauwaz ya bushe da dariya ya ce, "Tabbas kin yi mana zaɓin wuri mafi dacewa kuma ina mai yi miki albishir da cewa kafin cikar rabin sa'a za mu isa Birninku na Shauful".
Kamar yadda Aljani Maruful Dauwaz ya fadi haka al'amura suka kasance, wato a cikin rabin sa'a cif suka iso kofar Birnin Shaufi.Nan take Aljani Maruful Dauwaz ya sauko kasa ya dira daf da Birnin ya zamana tazararsa da bakin kofar garin bai wuce taku ashirin ba.
Koda masu gadin kofar Birnin suka yi arba da Aljani Maruful Dauwaz sai suka firgice suka ruga izuwa cikin gari suna ihu, dayansu bai yi jarumtakar tsayawa ba duk da cewa yawansu ya kai dari uku. Saboda tsananin razanar da suka yi basu ma lura da cewa Aljani Maruful Dauwaz na dauke da 'yar Sarkinsu ba, wato GIMBIYA RAHILA.
Nan da nan labari ya riski Sarki cewar ga wani bakon Aljani wanda babu mai girmansa daga cikin aljanun duniya ya sauka a kofar gari. Koda jin wannan batu sai Sarki ya mike tsaye zumbur ya sa aka busa kahon fita yaki. Nan da nan Dakaru suka shiga shiri ka rifa debo makaman yaki. Shi ma Sarkin ya ruga izuwa cikin turakarsa ya yi damarar yaki ya debo dukkan gurayensa da layunsa na tsafi ya sanyasu a jikinsa sannan ya jagoranci Dakarun yakin nasa kimanin su dubu dari uku suka yi hawa bisa dawakai rike da muggan makamai suka sukwane su i zuwa can kofar gari.
Da isar wannan runduna bakin kofar gari sai gaba dayan dawakan nasu suka firgice suka kama tirjiya da haniniya, suna daga kafafunsu sama suna zubar da mahayansu, kuma suna komawa da baya a guje izuwa cikin gari.
Ba komai ne ya haddasa hakan ba face tsorata da dawakan suka yi sakamakon yin arba da Aljani Maruful Dauwaz saboda kwarininsa da cikar surarsa ta sadaukantaka da girman halittarsa.
Dokin Sarkin kadai ne bai juya da baya ba amma shi ma ya tsorata ainun da ganin Aljani Maruful Dauwaz. Shi kansa Sarkin taurin zuciya da kishin mulkinsa ne da jama'arsa ya sa ya dake ya ki ya gudu.
Koda ya dubi mutane biyu da ke kan Aljanin da kyau sai ya shaida 'yarsa Gimbiya Rahila. Cikin tsananin farin ciki ya duro daga kan dokin nasa ya ruga izuwa inda Aljani Maruful Dauwaz yake. Itama Rahila sai ta duro kasa daga kan Maruful Dauwaz ta ruga izuwa wajen Sarki.
Suna haduwa suka rungume junansu cikin farin cikin sake saduwa. Sarki ya yi ta sumbatar fuskarta da gashinta kamar ba zai daina ba. Bayan sun nutsu sai ya dube ta ya ce, "Ya ke 'yata ki gayawa abokin tafiyarki Sarki Laffaru cewa shin ya taba cika alkawari a rayuwarsa kuwa?"
Koda jin haka sai Laffaru ya bushe da dariya sannan ya sauko da sauri daga kan Aljani Maruful Dauwaz ya ruga izuwa wajen mahaifin Rahila ya mika masa hannu suka gaisa sannan ya ce, yau ne ranar farko a rayuwata da na taba cika alkawari dawo maka da 'yarka cikin koshin lafiya".
Sarki ya yi murmushi ya ce, "Ai dama ba kai ba ne ka dauki wannan alkawari ba, Boka Muzaffar ne, ina kuka baro shi?
Koda jin wannan tambaya sai Rahila da Laffaru suka yi sunkui da kansu kas sukai shiru ba su ce komai ba. Rahila ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Labari ne mai tsawo sai mun zauna. Yanzu dai mu shiga cikin gari domin jama'a su ganmu tare hankalinsu ya kwanta."
Sarki ya yi murmushi ya ce, "Kin yi gaskiya yake 'yata, amma ku gayawa wancan abokin tafiya taku ya tsaya anan kadanya biyo mu domin koda an ganshi tare da mu sai jama'a sun firgice. Wai shin ma wane ne shi?"
Rahila ta yi murmushi ta ce, "Wannan shi ne Sadaukin Sadaukan aljanun duniya, jarumi uban jarumai dodon maza kuma gwarzon mayaki ma'abocin gaskiya da amana, Aljani Maruful Dauwaz."
Koda jin wannan batu sai Sarki ya cika da tsananin farin ciki ya ruga izuwa wajen Aljan Maruful Dauwaz ya rungurne shi yana mai cewa "Lale marhaban da babban bako aminin Talmara ibni Saumur.
Koda jin wannan batu sai jikin Aljani Maruful Dauwaz ya kara yin sanyi, kuma ya ji ya kara aminta da Gimbiya Rahila dari bisa dari.
Nan dai Sarki, Rahila da Sarki Laffaru suka dunguma suka tafi izuwa cikin gari suka bar Aljani Maruful Dauwaz anan bayan gari yana mai warwasa kafarsa yana rangadi domin rabonsa ma da ya wasa kafafunsa bisa turba shekaru dubu biyu da dari biyu ke nan.
Da shigarsu cikin gari jama'a suka ga Sarki tare da 'yarsa Rahila sai suka cika da tsananin murna. Nan fa aka shiga taya shi murna.
Nan da nan gari ya gauraye da kade-kade da raye-raye. Sarki, Laffaru da Rahila suka shige izuwa cikin gidan sarauta suka zauna a cikin dakin cin abinci aka kawo musu nau'in abinci iri-iri sama da kala dari.
Nan fa Sarki Laffaru ya bude cikinsa ya yi ta zuri domin rabonsa da cin lafiyayyen abinci haka tun kafin ya baro Birninsa.
Tuni Sarki yasa aka gyara manyan raguna guda arba'in gami da ruwa cikin duro arba'in ya ce a kaiwa Aljani Maruful Dauwaz ya fara taɓawa kafin a kawo masa nau'in abinci.
Da kyar aka sami wadansu dakakkun Dakaru masu taurin zuciya suka daure suka mika wannan sako. Koda Maruful Dauwaz ya ga an kawo masa wannan abinci sai shi ma ya cika da tsananin farin ciki domin ya shafe dubunnan shekaru bai ci irinsa ba, sai ma wanda ya fishi dadi da ni'ima a cikin kogon Darul Iksina. A wannan rana dai sai da Rahila da Sarki suka raba dare suna hira inda ta kwashe labarin duk abin da ya faru a cikin wannan tafiya tasu ta zaiyane masa tun daga lokacin da su Boka Muzaffar suka zo suka dauke ta a gida kawo izuwa sa'adda suka sami nasarar keta wadannan dazuzzukan guda biyar har suka isa kogon Darul Iksina da yadda suka hadu da Aljani Maruful Dauwaz suka baro su jarumi Imran a can.
Koda mahaifin Rahila ya ji wannan labari sai ya kamu da tsananin tausayi, bai san sa'adda ya kama zubar da hawaye ba kuma ya cika