Showing 60001 words to 63000 words out of 75493 words

Chapter 21 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt

GALILUL HARAS.

Mashin na jingine a cikin dakin tsafin Boka Muzaffar amma an rasa wanda zai sami nasarar daukar mashin a tsakaninsu su ukun domin sun wanzu a cikin kai wa junansu sara da suka cikin bakin zafin nama, juriya da jarumtaka ta gaban kwatance kuma kowannensu yana amfani ne da dukkan karfin dantsensa da karfin tsafinsa.

Duk sa'adda takubbansu suka hadu sai dai ka ji tartsatsin wuta na tashi gami da hayaki.
Duk wanda aka sari jikinsa kuwa sai ka ji kamar karfe aka sara, makamin bay a tasiri haka uma babu wanda yake da alamar gajiyawa a cikin yakin alhalin kwanansu goma sha hudu ke nan suna wannan masifaffen yaki a waje ďaya har ta kai cewa sun rugurguza gaba dayan ginin gidan na Boka Muzaffar tamkar ginin bai taɓa wanzuwa ba Komai dake cikin gidan ya kone ya zama toka, Mashin Galilul Haras ne kadai ko kwarzanewa bai yi ba.

Sadauki Najwar ya ci gaba da bincike domin ya gano wanda zai sami nasarar daukar mashin na Galilul Haras a tsakanin matsafan uku, amma sai abu ya gagara.

Ya sake yin bincike akan sa'adda yakin nasu zai zo karshe amma abu dai ya gagara. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin sadauki Najwar ke nan ainun fiye da ko yaushe ya fusata har ya maka madubin tsafin nasa a kas ya tarwatse.

Nan fa ya zauna ya yi tagumi yana tunanin abin da ya kamata ya yi. Sai da ya daɗe a zaune cikin wannan hali sannan ya yanke shawarar cewa duk yadda zai yi dole ne a cikin wannan dare ya mallaki Gimbiya Ramlatul Siyam kuma ya mallaki karagar mulkin Sarki Nashmir.

Ko a yau din ne kadai ya sadu da Gimbiya Ramlatul Siyam kuma ya zauna akan karagar mulki ai ya gama cika burinsa na duniya bai ki ba ma Ajalinsa ya riske shi tun da ya yi abin da babu wani mahaluki da ya isa ya yi shi a doron kasa. Ko ba komai ba zai yi mutuwar banza ba wacce za a manta da shi.

Dole ne a rinka tunawa da shi a cikin tarihin MAZAN JIYA wadanda suka yi gagarumar bajintar da ba za a taɓa mantawa ba.

Koda sadauki Najwar ya gama aiyana hakan sai ya mike zumbur! ya fita daga cikin gidansa, bai zame a ko ina ba sai inda Aljani Barukul Masnur yake a cikin gidan sarautar.

Irin su Aljani Barukul Masnur sun kai su miliyan daya da rabi a cikin Dakarun da ke tsaron fadar Sarki Nashmir kuma dukkaninsu sun fito ne da ga wata zuri'a ta aljanu a Birnin Hindu.

Tunda zuri'ar tasu ta wanzu a doron kasa, suka kasance bayi, ba su taɓa samun 'yancin kansu ba a wajen 'yan uwansu ajlanu da manyan Bokayen duniya na jinsin Bil'adama.

Wani babban abin takaici a gare su shi ne, sun kasance 'yan tsiraru a cikin al'ummar aljanu na Birnin Hindu, kuma an kafa musu karan-tsana, shi ya sa ake karar da dukkan rayuwarsu a cikin bauta.

Iyaye da Kakanninsu da wannan bakin ciki suka tsufa suka mutu, domin sun san cewa har abada ba za su iya yin tawaye ba don su kwaci 'yancin kansu. Lokacin da sadauki Najwar ya riski Aljani Barukul Masnur sai ya ja shi izuwa cikin wani daki suka kadaita a inda babu wanda zai ji abin da za su tattauna.

Najwar ya dubi Barukul Masnur ya ce, "Na ji dadi da ka rufa mini asiri ba ka gayawa kowa sirrina ba, bisa wannan dalili yanzu zan yi wa zuri'arku gabadayanta gatan da ba a taɓa yi muku ba. Ka sani cewa a cikin shekara guda sau daya jal ake ba ku hutun aikin bauta.

To ni yanzu na ba ku hutu na tsawon wata uku, kuma a yau na shirya muku walima ta musamman a cikin fadar maigirma sarki Nashmir".

Koda jin wannan batu sai idanun Barukul Masnur suka zazzaro ya cika da tsananin tsoro ya ce, "Haba ya shugabana, ai idan ka yi haka Sarki ya dawo sai ya sa a hallaka mu gaba dayanmu. Kai kanka ba za ka tsira ba daga sharrinsa".

Koda jin wannan batu sai Najwar ya bushe da dariya ya ce, "Ka san dai idan Sarki ba ya nan babu mai ba da umarni a gidan nan sai ni ko ba haka ba ne?"

Barukul Masnur ya ce, Haka yake". Najwar ya ce, Maza ka je ka sami ragowar yan uwanka su duka ka gaya musu cewa ina nemansu yanzu-yanzu a fada. Koda gama fadin hakan sai Najwar ya 6ace fat. Bai baiyana a ko ina ba sai a fadar Sarki Nashmir inda karagar mulki take.

Baiyanarsa ke da wuya ya bai wa Barori da Kuyangi umarnin su je su kawo abinci da abin sha iri-iri wanda za a yi walima da shi.
Nan take kuwa Barorin da kuyangin suka cika
wannan umarni cikin 'yan dakiku kadan. Faruwar hakan ke da wuya sai ga gabadayan zuri'ar su Aljani Barukul Masnur sun baiyan a fadar.

Al'amarin da ya matuka bai wa gabadayan Dakarun tsaro na gidan maraki ke nan, domin hakan ba ta taɓa faruwa ba tunda Sarki Nashmir ya hau karagar mulki.

Bayan zuri'ar su Aljani Barukul Masnur sun gama hallara gaba dayansu kimanin su miliyan daya da rabi sai sadauki Najwar ya daka tsawa ga sauran Dakaru, barori da bayi da ke cikin fadar ya ce kowa ya fita ya bar su da zuri'ar su Barukul Masnur. Nan take kuwa aka bi wannan umarni.

Bayan kowa ya gama fita ne sai Najwar ya sa aka kulle dukkan kofofi da tagogin fadar don kada ma wani ma ya ji abin da za su tattauna.

Ba tare da 6ata wani lokaci ba Najwar ya bai wa su Aljani Barukul Masnur umarni suka fara walima.

Saboda tsananin fari ciki da mamaki ba su san sa'adda suka kama bushasha ba har ma wasu suka rinka kade-kade da raye-raye, wasu ma suka yi ta shan ruwan barasa kai ka ce a cikin gidajensu suke ba a fadar mai girma Sarki Nashmir ba. Shi kansa Najwar sai ya shagala ya yi ta rawa a cikinsu yana nishadi.

Bayan kowa ya ci ya gyatse sai sadauki Najwar ya tafi kai tsaye izuwa kan karagar Sarki Nashmir ya zauna akanta ya harde kafafuwansa. Koda ganin haka sai gaba dayan aljanun suka firgice suka kama kuka suna rokon Najwar da ya ba su umarnin su fice daga fadar don kada Sarki Nashmir ya dawo a yanzu ya ga abin da ke faruwa ya sa a hallaka su su duka.

Koda jin wannan batu sai Najwar ya bushe da dariya, lokaci guda kuma ya murtuke fuska ya ce, 'Ya ku wannan zuri'a ta aljanu da ba su da gata a wannan kasa tamu, shin kun yi imani cewa ni ne Wazirin Sarki Nashmir?"

Su duka suka amsa da "Na'am". Najwar ya cigaba da bayani yana cewa. "Fiye da shekaru dubu arba'in ba ku taɓa samun 'yancin kanku ba, Iyayenku da Kakanninku duk a cikin kangin bauta suka mutu. Yau ni Najwar zan kwato muku 'yancinku. Koda jin haka sai gabadayan aljanun suka rude da shewa cikin tsananin murna har sai da Najwar ya daga hannunsa sama sannan suka yi tsit tamar mutuwa ta gifta.

Najwar ya ci gaba da cewa, "Ku sani cewa da kadan Sarki Nashmir ya fi ni jarumtaka da karfin shirin tsafi. To ni ma na gaji da yi masa bauta babu ci gaba. Yau ne ranar da na sami damar da zan yi masa tawaye, amma sai idan kun ba ni hadin kai sannan ni da ku za mu samu 'yancinmu.

Ina tabbatar muku da cewa Sarki Nashmir ya tafi wani gagarumin yaki shi kadai yakin da ba zai taba tsira da rayuwarsa ba. Yanzu zan nuna muku zahiri ku gani da idanunku".

Koda gama fadin hakan sai ya yi nuni da hannunsa izuwa ga jikin bangon fadar. Nan take suka ga taswirar hoton gumurzun da ake yi tsakanin Sarki Nashmir da su Boka Muzaffar. Al'amarin da ya matukar ba su mamaki ke nan.

Najwar ya sake nuna bangon da hannunsa hoton komai ya dauke sannan ya ce, na yi bincike a cikin tsafina na gano cewa za a kashe Sarki a wannan yaki, saboda haka a daren yau ina son ku ba ni hadin kai mu yi juyin mulki cikin shammace domin idan muka bari har dakakarun gidan nan suka san cewa Sarki mutuwa zai yi, to kuwa za su dora 'yarsa ne akan karagarsa. Idan kuwa hakan ta faru 'yancinku da nake son na karɓo muku ya suбuce ke nan har abada, domin da zarar Ramlatul Siyam ta zauna akan karagar mulki za ta sami dukkan karfin sihirin tsafi irin na mahaifinta, kun ga kenan ba zan taɓa iya yi mata juyin mulki ba.

Lallai da zafi-zafi akan bugi karfe, idan kuwa aka bari ya huce shi ke nan ba zai lankwasu ba. Sa'adda Najwar ya zo na nan a jawabinsa sai gaba dayan aljanun suka rude da shewa suna masu cewa sun ba shi hadin kai dari bisa dari.

Nan take farin ciki ya lulluɓe Najwar ya sallame su akan cewa, da zarar dare ya raba su dawo nan fadar yana nemansu. Nan take aljanun gaba daya suka tafi suka bar shi shi kadai tare da Aljani Barakul Masnur.

Aljani Barakul Masnur ya dubi Najwar cikin murmushi ya ce, "Tabbas yanzu na gamsu cewa duk abin da ka tsara zai tabbata. Amma muna da matsala guda daya. Yaya za mu yi da su Aljani Maruful Dauwaz wadanda su ma sun zo ne domin su mallaki Gimbiya, kuma ta yaya za ka iya fito da Gimbiya daga cikin gidanta alhalin kasan cewa ba za mu iya kawar da Dakarun da ke tsaronta ba?

KAKA-KARA-KAKA!

Lokacin da sadauki Najwar ya ji wannan batu
sai ya bushe da dariya har da faɗowa kasa daga kan karagar mulkin, ya yi ta dariyar kamar ba zai daina ba. Daga can sai ya tsagaita da dariyar tare da nutsuwa ya dubi Aljani Barakul Masnur ya ce, Ai ni ba na yin Kwaina sai da Zakara.

Tuni na yi bincike akan yadda zan sami wannan nasara, kuma na ga mafita don haka ka zuba ido za ka sha mamaki. Nan da cikar sa'a daya jal zan zo maka da Gimbiya Ramlatul Siyam kuma a cikin gidanka za mu ɓoye ta har sai mun sami nasarar juyin mulki sannan za a fito da ita a daura aurena da ita."

Gama fadin hakan ke da wuya sai Najwar ya 6ace ɓat. Koda ganin haka sai shi ma Aljani Barukul Masnur yai sauri ya bar cikin fadar.

Al'amarin sauran Dakaru, Bayi da Barori da Kuyangin da ke hidima a cikin gidan sarautar Sarki da Nashmir kuwa, lokacin da suka ga Najwar ya zo da Sababbin al'amura a gidan sarautar sai suka cika da tsananin mamaki, amma da yake sun san cewa yana matukar shakkar Sarki kuma yana matukar biyayya a gare shi sai suka za ta cewa abin da yake da sanin Sarki yake yi.

A can kurkuku kuwa, hankali Rahila da na Sarki Laffaru ya dugunzuma ainun sun kasa zaune sun kasa tsaye, sai kai kawo suke yi a cikin kurkukun domin gani suke kamar shi ke nan sun shiga inda ba za su taɓa fita ba, sai dai a fitar da gawarsu.

Shi kuwa Aljani Maruful Dauwaz ko a jikinsa wai an mintsini kakkausa. Da ma ya ga su Rahila sun damu ainun sai kawai ya kishingida ya kama rara wata waka. Koda yai nisa a cikin wakar sai ya fashe da kuka saboda ya tuno da masoyiyarsa marigayiya Rashmin.

Koda Rahila da Laffaru suka ga Aljani Maruful Dauwaz ya kama kuka sai su ma suka fara kukan domin a zatonsu zuciyarsa ce ta karaya bisa samun kuбutarsu.

Suna cikin wannan hali ne wani Badakkare ya durfafo dakin da suke ciki dauke da abincin su Rahila. An kawo musu abincin ne saboda sanin cewa su mutane ne idan ba a ba su abinci ba za su iya shiga mugun hali ko ma su rasa rayuwarsu gabaki daya.

Da isowar Badakkaren sai ya buɗe wata 'yar karamar taga ya zuro kwanon abincin. Kafin ya janye hannunsa tuni Aljani Maruful Dauwaz ya rike shi. Nan take Badakkaren ya zama dan minini ya shige cikin kurkukun.

Faruwar hakan ke da wuya sai Maruful Dauwaz ya rikide siffarsa gabadaya ta koma irin ta wannan Badakkare. Yana dafa Rahila da Laffaru sai suka zama 'yan mini-mini. Nan take ya dauke su ya dora su akan kafadarsa sannan ya fice daga cikin kurkukun kamar yadda danshi ke ratsa kasa suka bar wannan Badakkare kulle a cikin kurkukun yana kwance ya kasa koda motsawa.

Maruful Dauwaz ya ci gaba da tafiya a cikin kurkukun a siffar wannan Badakkare duk inda ya je sai ka ga an bude masa kofa ya wuce.

Rahila da Laffaru kuwa sai tsalle-tsalle suke akan kafadarsa suna tsananin murna bisa ganin sun fito daga cikin wannan kurkuku.

Saboda kankantar Rahila da Laffaru girmansu bai wuce na tsayin babban dan yatsa ba babu wanda ya gan su akan kafadar Maruful Dauwaz har suka fice gabadaya daga cikin kurkukun, sannan suka isa wani sako inda babu kowa.

A sannan ne Maruful Dauwaz ya ďaga tafin hannunsa dai kafadarsa, Rahila da Laffaru suka dirgo kan tafin hannunsa, sannan ya sauko da su Kasa daidai fuskarsa ya ce da su, "Kun gasgata maganata cewar zan iya kubutar da mu?".

Rahila da Laffaru suka gyada kai a tare cikin murmushi. Rahila ta ce, "Tabbas mun gamsu, Yanzu kuma mene ne abin yi na gaba?" Maruful Dauwaz ya ce, "Na ji a jikina cewar Najwar yaudararmu zai yi ba zai yarda mu mallaki Gimbiya Ramlatul Siyam ba. Dole ne yanzu mu nemi inda gidan Gimbiya Ramlatul Siyam yake domin mu je mu sace ta mu gudu gabadaya, da jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Rahila da Laffaru suka ce, "Kawai a tafi".

Har Aljani Maruful Dauwaz ya yunkura zai fita daga cikin sakon da suka бuya sai ya dawo da baya ya tsaya. Al'amarin da ya bai wa su Rahila mamaki ke nan. Rahila ta dubevshi cikin firgici ta ce m, ya kai Sarkin sadaukan aljanu, mene ne dalilin da ya sa ka dawo da baya?" Cikin alamun tsananin damuwa Aljani Maruful Dauwaz ya dubi Rahila kamar zai yi kuka ya ce, "Ya ke wannan 'yar Sarki ki yi sani cewa yanzu ne zamu tunkari masifar da tafi duk wacce ta same mu a baya don haka zan iya rasa rayuwata ku ma za ku iya rasa taku. Kafin mu je zan yi miki tambaya ta karshe ina so ki fada mini iyakar gaskiyarki, Shin idan na gama biya muku bukatarku za ku cika alkawarinki a gare ni? Shin da gaske ne za ki kai ni inda kika boye wasikar masoyiyata?"

Lokacin da Rahila ta ji wadannan tambayoyi sai idanunta suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo mata sannan ta ce, "Na rantse da darajar gemun mahaifina zan zamo mai cika alkawari a gare ka kuma lallai zan kai ka inda wasiyyar masoyiyarka Rashmin take."

Da jin haka sai farin ciki ya lulluɓe Aljani Maruful Dauwaz ya mayar da su Rahila izuwa kan kafadarsa sannan ya fito daga cikin sakon da suka buya ya ci gaba da tafiya yana neman ɓangaren da gidan Gimbiya Ramlatul Siyam yake.

Duk inda yake wucewa Dakaru ne tsibi-tsibi, da zarar ya ga ana kallonsa sai hankalinsa ya tashi don gudun kada a gano cewa shi ba Hadimin gidan ba ne.

*****

Al'amarin sadauki Najwar kuwa, lokacin da ya bace daga fadar Sarki Nashmir bai bayyana a ko ina ba sai kofar gidan Gimbiya Ramlatul Siyam.

Koda masu gadin gidan suka gan shi sai suka bude masa kofar gidan da sauri ya kunna kai ciki. Najwar bai isa inda turakar Gimbiya take ba sai bayan ya yi tafiyar rabin sa'a. Ya so ace ya isa turakar da wuri ta hanyar amfani da karfin sihirinsa amma da yake sihirin tsafi ba ya tasiri a gidan Gimbiya Ramlatul Siyam dole ya hakura ya yi wannan doguwar tafiya.

Shi kansa ya san cewa bai isa ya je ya dauko Gimbiya ba da karfin sihiri ko da karfin dantse, sai dai idan Gimbiyar ce da kanta ta amince ta biyo shi.

Ko ina a cikin gidan Dakaru ne na tsaro, manya-manyan sadaukan aljanu da bil'dama masu yawan gaske, yadda komai jarumtakar mutum ko aljan idan suka yi masa rubdugu dole ne suami nasara a kansa.

Lokacin da Najwar ya iso tsakiyar turakar Gimbiya Ramlatul Siyam sai aka tsayar da shi anan domin anan ne iyakarsa bai isa ya matsa gaba ba.

Babu wanda yake wuce wannan wuri ya isa har cikin turakar Gimbiya face Sarki Nashmir da kansa.

Koda aka tsaida Najwar sai kuwa ya tsaya cak batare da wata gardama ba sannan ya ce, aje a gaya wa Gimbiya cewa Sárki ne ya ba shi sako ya kawo mata.

Nan da nan aka je aka sanar da ita. Sai ta ce a komo a gaya masa cewar ya bayar da sakon a kai mata. Ya yin da Najwar ya ji haka sai ya ce aje a gaya mata cewa sako ne na sirri kuma Sarki ya ce lallai kada kowa ya ji wannan sako.

Koda Gimbiya ta ji haka sai ta mike zumbur!
Cikin tashin hankali ta taho izuwa inda Najwar yake. Tana isowa kuwa ta iske Najwar a tsaye yana tsumayenta.

A wannan lokaci Gimbiya ta tsala ado na gaban kwatance har kyawunta ya ninka na kullum. Koda Najwar ya ga Gimbiya a cikin wannan ado ai ya rude ya dimauce, bai san sa'adda ya kama dalalar da yawu daga bakinsa ba (Ka ji maye). Ita kanta Gimbiya sai da ta gane halin da ya shiga har ta kyalkyale da dariya.

Daga can sai ta hade fuska ta dubi gaba dayan Dakarun da hadiman da ke falon ta ce su kauce su ba su wuri. Nan take kuwa aka watse aka bar su su biyu rak.

A sannan ne ta yi masa nuni da wata kujera ya zauna, ita ma sai ta zauna bisa wata luntsumemiyar kujera da ke fuskantar tasa.

Ta dube shi cikin wani irin murmushi mai taushi wanda ya sake dimauta shi sannan ta ce, Ya kai Sarkin yaki ina mai sanar da kai cewa fiye da hekaru goma baya na sani cewa kana matukar so na kuma kana begena dare da rana. Kai kuwa kan wanne dalili ka dorawa kanka jarabar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login