Showing 15001 words to 18000 words out of 75493 words

Chapter 6 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt

sai yai ajiyar zuciya ya kira sunan aljani Marhabul Zaurus ya ce, babu abin da zan iya cewa akan wannan tambaya da ka yi mini, abin da na sani kawai shi ne muna sa rai da samun nasara. Gama fadin haka sai boka Muzaffar ya tsuke bakinsa yai shiru bai kara cewa uffan ba.

Haka dai aka ci gaba da tafiyar amma duk wanda ka duba sai ka ga akwai alamun tsoro a yanayin fuskarsa. Hakika gaba dayan wadannan matafiya a gigice suke da shiga wannan daji na uku inda za a yi karo da wadannan masifaffun tsuntsaye .

Babban abin da ya fara karya musu zuciya shi ne, ganin yadda jaruma Shadira ta rasa dan uwanta a daji na biyu don haka kowa ya san cewa komai zai iya faruwa gare shi a cikin wannan tafiya babu mai tabbacin zai gama lafiya. Bayan shudewar sa'a biyu cif, Sai suka iso wannan daji na uku.

Tun daga baya-baya aljani Marhabul Zaurus ya saki fuka-fukansa ya sauko lasa ba tare da ya karbi izinin saukowa ba.

Al'amarin da ya fusata boka Muzaffar ke nan ya dube shi ya ce, Waye ya ba ka izinin ka sauko da mu kasa tun gabannin mu iso farkon daji na ukun?

Koda jin wannan tambaya sai aljani Marhabul Zaurus ya risina cikin biyayya ya ce, "Ya shugabana ka yafe ni kuma ka sani cewa, na yi haka ne domin mu sake yin cikakken shiri na shiga wannan daji na uku, saboda idan muka shige shi kai tsaye, wadannan mugayen tsuntsaye za su iya yi mana rubdugu a lokaci guda su gama da mu.

Ina tabbatar muku da cewa karfinmu da makaman mu ba za su cece mu ba daga harin tsuntsayen sai dai sa'a da jajircewa!

Lokacin da aljani Marhabul Zaurus ya zo nan a jawabinsa sai jikin kowa yai sanyi, kuma hankalin kowa ya kara dugunzuma, ban da na Shadira, domin ko kadan babu alamar tsoro a tare da ita, mutuwar ma nemanta take. Kai in ba don son Imran da ke yawo a zuciyarta ba da tuni ta kashe kanta ma, domin ba ta ga amfanin rayuwarta ba a doron kasa.

Nan take kowa ya sauko kasa daga kan aljani Marhabul Zaurus. Shaharan da dokinsa ne suka sauka daga karshe.

Shaharan ya ja dokinsa a hankali izuwa cikin wadansu ciyayi, ya sake shi ya kama kiwo abinsa a lokacin da ya kurawa dokin idanu yana kallon mugayen raunikan da ke jikin dokin, ga shi dama ba shi da lafiya, ko tafiya baya yi.

Nan take kwallah ta zovwa Shaharan domin a duniya babu abin da yake so sama da wannan doki, ko kuda ba ya son ya taɓacshi, amma yanzu gacshi duk ďinki ne kaca-kaca a jikinsa.

Bayan kowa ya zauna an dan huta, sai aka shiga tattaunawa bisa irin shirin da ya kamata a yi, don shiga cikin wannan daji.

Boka Muzaffar ya ce, "Abu na farko dai, kun ga su wadannan tsuntsaye ba sa jin sara da suka, kuma komai nauyin abu suna iya surarsa da 'yan yatsun kafafunsu su yi sama da shi, kuma duk abin da suka sura bai isa ya iya kubcewa daga hannunsu ba, saboda haka duk yadda za mu yi ka da mu kuskura mu bar tsuntsayen nan su dauki daya daga cikinmu ta kowane hali".Sa'adda boka Muzaffar yaczo nan a jawabinsa sai kowa yai shiru yana tunani. Daga can sai jarumi Haiman yai gyaran murya ya ce, "To shin su wadannan tsuntsaye a gaba dayan jikinsu babu inda KAIFI DA TSINI zai yi tasiri?"

Da jin wannan tambaya sai boka Muzaffar ya yi shiru yana tunani, daga can sai ya ce, "Fiye da shekaru dari bakwai baya ba a taɓa samun mahalukin da ya ratsa ta cikin wadannan dazuzzuka biyar ba, ya koma gida a raye bare aji daga bakinsa cewa wadannan tsuntsaye suna da lago.

A duniya babu abun da za a ce ba zai yiwu ba, saboda haka babu mamaki mu ne waɗanda za su gano lagon wadannan tsuntsaye. Ni dai a yanzu shawarar da zan bayar ita ce, mu rufe jikinmu da kayan yaki na karfe yadda koda tsuntsayen sun kawo mana sara da suka da faratan kafafunsu sai dai su sami karafunan ba dai jikinmu ba".

Koda jin wannan batu sai sarki Lafaru ya dubi boka Muzaffar a fusace ya ce, "Me ya sa tun kafin mu baro garuruwanmu ba ka sanar damu wannan al'amari mun yi tanadi ba?
Yanzu a ina za mu sami kayan yaki na karfe wadanda za mu rufe jikinmu da su?'

Koda jin wannan batu sai boka Muzaffarya ya bushe da dariya, lokaci guda kuma ya murtuke fuska sannan ya ce, "To ai in ban da abinka mene ne amfanin sihirin tsafin da muka mallaka?"

Kafin wani daga cikinsu ya kara cewa wani abu tuni boka Muzaffar ya rintse idanunsa ya fara karanta dalasiman tsafi. Sai da ya shafe dakiku dari biyu da ashirin yana karanta dalasiman tsafin a fili, yana gamawa kuwa sai kowa ya tsinci kansa a cikin kayan yaki na karfe. Hatta mahaifiyar Imran, Sarkin Farisa, Lumaira da dokin Shaharan kuwa. Sai ya zamana gaba dayan jikinsa a rufe yake da sulken karfe.

Kai bama dokin Shaharan ba, hatta aljani Marhabul Zaurus jikinsa ya lullube da kayan yaki, hatta katon kansa kuwa, idanunsa, bakinsa da kunnuwansa ne kadai a waje.

Koda kowa ya tsinci kansa a cikin wannan kayan yaki sai suka cika da murna saboda a tunaninsu sun tsira daga sharrin wadannan mugayen tsuntsayce. Abin da bacsu sani ba shi ne, wannan kariya ba zavta hana tsuntsayen cutar da su ba.

A wannan lokaci jaruma Shadira na zaune ita kadai a gefe daya bisa kan wani dutse ta daga kanta sama tana tunani. Ba komai take tunani ba face irin abubuwan da suka faru a baya tsakaninta da dan uwanta marigayi yaro Masnur. Musamman a irin lokutan da suke wasan 'yar birin-birin, da sa'adda suke cin abinci tare da kuma lokacin da take yi masa wanka ta yi masa ado. Kai hatta kwanciyar barci kullum akan kirjinta Masnur ke bacci, ba ya yarda ya gusa daga kusa da ita.

Sa'adda Shadira ta zo dai-dai nan a tunaninta sai zuciyarta ta karye, ta fashe da kuka. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin kowa ke nan. Cikin sauri jarumi Imran ya je gare ta ya zauna daf da ita, sannan ya sa hannunsa ya share hawayen da ke zuba a fuskarta ya ce, "Ya ke abar kaunata, na sani cewa kin yi babban rashi wanda har abada ba za ki taba mantawa da shi ba, amma saboda me ni ba zan maye miki gurbin dan uwanki ba?

Daga yau ina son ki daukeni a matsayin dan uwa, uwa, uba, uwa, kuma babban masoyi wanda babu kamarsa. Na rantse da darajar kaunar da nake yi wa mahaifiyata zan soki kamar yadda kowacce uwa ke son danta, kuma kamar yadda dan uwa ke son dan uwansa na jini. Sannan zan sallama rayuwata don kare taki".

Koda jaruma Shadiara ta ji wannan batu sai ta rungume Imran tana mai cewa, "Ina yi maka fatan cika wannan alkawari.Tabbas idan alkawarinka ya cika za ka maye mini gurbin dan uwana da na rasa".

A can gefe daya kuwa, Shaharan na satar kallon gimbiya Zarina, amma bai san cewa tana kallonsa ba da wutsiyar idonta, kuma dan uwanta ma Sarkin Farisa yana lura da abin da ke faruwa a tsakanin nasu. Nan take Sarkin Farisa yai murmushi a lokacin da ya dubi 'yar uwar tasa ya ce, "Ya ke 'yar uwata, ni kuwa ina son na nemi wata alfarma guda daya rak a wajenki".

Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Zarina ta ce, "Yanzu dama ashe akwai wata bukata da kake da ita amma tuntuni baka furta mini ita ba? Sarkin Farisa ya numfasa, "A'a a yanzu ne bukatar ta zo mini".

Zarina ta ce, "Ina sauraronka, in dai abu ne mai yiwuwa a duniyar nan, kuma ina da ikon yi sai na yi maka shi. Sarkin Farisa yai shiru kamar ba zai ce komai ba, daga can kuma sai ya dubi Zarina ya ce, "A duniya babu mutumin da nake tausayawa face wanda ya jarabtu da son wani, amma wanda yake so din ya ki karɓar soyayyar tasa.

Me zai hana ki yi wa sadauki Shaharan murmushi koda sau daya ne rak domin ya sau nutsuwa da saukin radadi da zogi na begenki a cikin zuciyarsa? Tabbas ya kamu da tsananin sonki, kuma so ba na wasa ba. Koda jin wannan batu sai Zarina ta haɗa fuska ta ce, "Haba ya kai dan uwana, ka sani cewa na yi alkawarin cewar bá zan yi aure ko soyayya ba face na ga kai ma ka warke, kuma ka sami masoyiya wadda za ka aura.

Lallai ina nan a kan wnanan alkawari nawa, babu abin da zai sa na karya shi face mutuwa. Ka yi hakuri ya kai dan uwana, ba zan iya yin wannan abu da ka umarce ni da yi ba".

Boka Muzaffar da Sarki Laffaru kuwa, a wannan lokaci suna zaune a can gefe daya kusa da gimbiya Rahila suma suna tasu hirar dabam. Duk sa'adda Rahila ta dago kai sai ta ga Sarki Laffaru ya kura ma ta idanu ko kiftawa baya yi. Abin da ya ba ta haushi ke nan, kuma ya ba ta mamaki.

Ta ce a cikin zuciyarta, "Wai shin me Sarki Laffaru yake ci ne na baka na zuba? Kuma mene ne ya burge shi a tare da ni, shi da yake kan tafarkin auren gimbiya Ramlatul Siyam 'yar Sarkin birnin Hindu wacce ban fi ta kyau ba, kuma mahaifinta yafi mahaifina arziki da daukaka a duniya?

Koda yake, ai shi mutum ne mai son mata da yawa. Ni kam babu ruwana da duk matsalarsa, burina kawai shi ne na biya tawa bukatar".Rahila na cikin wannan tunanin ne ta ji boka Muzaffar ya ce, "A tashi a ci gaba da tafiya".

Nan take kuwa aka mike aka durfafi cikin daji na uku. Imran ne akan gaba goye da mahaifiyarsa, Shadira na biye da shi daf da daf, sannan jarumi Haiman goye da matarsa Lumaira, sai Zarina goye da Sarkin Farisa, sai Raliila, sannan boka Muzaffar da Sarki Laffaru. Al'ajani Marhabul Zaurus ne na karshe.

Al'amarin da ya ke fusata boka Muzaffar ke nan, saboda yana mamakin yadda aljani Marhabul Zaurus yafi dukkan sauran abokan tafiyar tsoro, a matsayinsa na ljani mai shirgegiyar halitta, amma duk ta zama ta banza.

Koda shigar su Imran cikin wannan daji na uku sai suka fara daga kawunansu sama suna kalle-kalle don su ga ta inda wadannan mugayen tsuntsaye za su kawo musu farmaki, da ma kowa ya zare makaminsa yana dube-dube da waige-waige gami da kallon sama ta kowanne ɓangare.

Sai da suka yi doguwar tafiya a cikin dajin, amma ko motsin Tsuntsayen ba su ji ba. Al'amarin da ya matukar basu mamaki ke nan, har sarki Laffaru ya dubi boka Muzaffar ya ce, "Anya kuwa mun shigo cikin dajin da mugayen Tsuntsayen nan suke?"

Kafin boka Muzaffar ya budi baki ya ce wani abu sai kwatsam! Suka ji kasar dajin gaba daya ta kama girgirza tana darewa. Al'amarin da ya firgita su ke nan. Nan take ramuka suka rinka budewa, sai ga wadannan mugayen Tsuntsayen suna bullutsowa sama daga cikin ramukan tamkar an tashi matattu a makabarta.

Kafin su Imran su yi wani yunkuri sama da Tsuntsaye dubu dari sun yi musu kawanya babu ta inda za su iya ratsawa su wuce.

Daga can kololuwar sama kuma sai ga wata runduna guda ta wadannan tsuntsaye suna tsala gudu sun durfafo su.

Nan fa cikin kowa ya duri ruwa, hankalin kowa ya dugunzuma ainun, domin sun san cewa suna cikin bakin hadari. Tabbas rayuwarsu tana a tsakanin MUTUWA DA RAYUWA.

(Zuwa ga makaranta. Ina so mu sani cewa, salon da Madakin Gini ya bi wajen wahalar da jaruman yana da alaka da kwarjinin kogon DARUL IKSINA ne. Ana so a tabbatar mana da cewa, hakika waďannan dazuka sun cika gagarabadau ababan misali)

Kafin tsuntsayen saman su iso sai na kasan suka fara marmatsowa domin su afka musu. Koda ganin abin da ke shirin afkuwa sai Imran ya buɗe muryarsa da karfin tsiya ya ce, Ku biyo ni a baya, duk inda ku ka ga na yi ku bi ni.

Ai kuwa yana gama fadin haka sai ya falfala da azababben gudu ya tunkari tsuntsayen da ke gabansa ya ratsa ta cikinsu da karfin tsiya ya rufe su da duka da sandarsa, sai ga shi ya tarwatsa su da karfin tsiya ya sama musu hanya, suka ci gaba da gudu. Amma sai Tsuntsayen suka biyo su a guje aka ruguntsume da masifaffen yaki. Su Imran suna gudu suna juyowa suna kare harin tsuntsayen da makamansu. Duk sa'adda makamansu suka hadu da kafafun Tsuntsayen sai dai ka ga tartsatsin wuta ya tashi kamar karfe da karfe ne suka haďu.

A daidai wannan lokacin ne wadancan Tsuntsayen da ke tahowa daga sama suka iso suka lullube saman su Imran, yakin ya kara tsamari ainun. Duk da cewa su Imran suna tsala gudu suna ketawa ta cikin bishiyoyi amma Tsuntsayen ba su fasa bin su ta sama da kasa ba. Ko bishiya Tsuntsayen suka yi karo da ita, komai kaurin bishiyar sai dai ka ga ta karye ta fadi kasa sun wuce abinsu. Duk sa'adda tsuntsayen suka karci kayan karfen da ke jikin su Imran kuwa, sai dai ka ga kayan na darcwa tamkar takarda aka yanka da zabira.

Wani lokacin ma faratan Tsuntsayen na kartar jikin jaruman bayan sun keta kayan jikin nasu. Sai dai ka ji suna ihu, jini na tsartuwa a jikinsu.

Imran ne kawai Tsuntsayen ba su yiwa rauni ba, sai kuma gimbiya Rahila. Lokacin da jarumi Imran ya lura da halin da sauran abokan tafiyarsa ke ciki, wato waďannan tsuntsayen sun yi musu rauni, kuma suna kokarin surarsu, in ba don ma sun kasance jarumai ba masu juriya da naci da tuni tsuntsayen sun yi sama da su. Abin da ya fi dugunzuma hankalin su Imran shi ne, ganin yadda KAIFI DA TSINI ba ya tasiri a jikin tsuntsayen, har ta kai cewa ma takubbansu sun fara dakushewa.

Nan take Imran ya fusata ainun, ya ci gaba da dukan tsuntsayen da sandarsa kuma a kai ya fi dukansu, sai dai ka ga sun fado kasa, amma kuma sai su sake mikewa zumbur! Su yi sama su ci gaba da kawo hari.

Imran sai ya sauya salon yaki, ya rinka dawowa da baya yana kade tsuntsayen da sandarsa, don kubutar da sauran abokan tafiyarsa. Wato sai yai gaba kuma yai baya, amma duk da haka dai bai hana tsuntsayen ci gaba da kawo mugayen hare-hare ba. Duk wannan gumurzu da ake yi a cikin gudu ake yinsa.

Sau tari idan Tsuntsayen suka kawo farmaki sai ka ga jaruman na faduwa kasa saboda karfin iskar fuka-fukan Tsuntsayen da kuma karfin harin nasu. Amma kuma sai ka ga jaruman sun yi wuf sun mike sun ci gaba da gudu kafin Tsuntsayen su cafke su duk da cewa kuwa sun yi musu rauni. Haka dai aka ci gaba da wannan dauki ba dadi har tsawon sa'a daya da rabi, a sannan ne suka iso tsakiyar dajin.

Koda Tsuntsayen suka ga su Imran na neman tsira daga sharrinsu, sai suka taru gaba dayansu suka yi musu kawanya kuma suka yi musu rubdugu aka ruguntsume da sabon azababben yaki mai tsananin firgitarwa da tashin hankali, domin kuwa, su tsuntsayen suna yakin ne da dukkan karfinsu don ayi ta, ta kare, su ma su Imran sun jajirce iyakar iyawarsu don kare kansu.

Koda aka dan jima ana wannan bakin artabu sai al'amura suka sauya, saboda jaruman sun fara gajiya. Hatta gimbiya Rahila ma ta gaji ainun har wani tsuntsu ya cafi kugunta da 'yan yatsunsa biyu ya yunkura zai yi sama da ita ke nan sai sadauki Imran ya do ki tsakiyar kansa da sanda. Tsuntsun ya rikirkice, kuma ya yi wani uban ruri sakamakon tsananin zafi da zogin da ya ji, babu shiri ya saki Rahila ta fado kasa a matukar galabaice, saboda kugun na ta ma da ya danka da yatsun kafarsa ya yi ma ta rauni har ta kasa mikewa ta ci gaba da gudu. Koda ganin halin da Rahila ta shiga sai boka Muzaffar yai wuf ya sure ta ya goya ta a bayansa ya ci gaba da gudu, kuma aka ci gaba da gumurzun a haka.

Kaico! Tsautsayi ba a sa masa rana. Ita kuwa masifa, idan ta zo babu makawa sai ta afku, sai dai a dauki dakon hakuri dole.

Lokacin da aka sake dan jimawa a cikin wannan hali sai ya zamana cewa kayan karfen da ke jikin kowa wanda ke dan ba su kariya duka ya kekkece babu mai sauran amfani, kowa sai ya fara gajiya, ya Zamana cewa mugayen tsuntsayen sun rutsa jaruman a waje daya sun kasa ci gaba da gudu, don haka sai suka ci gaba da kai musu mugayen hare-hare. Tun suna karewa da mai da martani har ya zamana cewa sun kasa mai da martanin, sai dai kare kai. Tafiya gaba-gaba dai sai kare kai din ma ya gagara.

Wayyo! A wannan lokaci ne fa Tsuntsayen suka fara yiwa jaruman mugayen rauni. Sarki Laffaru ne ya fara kifewa kasa yana mai kwarara uban ihu sa'adda wadansu tsuntsaye biyu suka yi masa rubdugun sara da faratan kafafunsu a lokaci guda.

Saran farko a kirjinsa aka lafta masa har jini yai feshi, sara na biyu kuwa a gadon bayansa ne lafcece. Jarumi Shaharan da ke ta guje-guje da zulle- zulle a tsakankanin Tsuntsayen sai shi ma wani tsuntsu ya fake shi ya make shi a fuska. Saboda karfin makuwar sai da yai katantanwa a sama sau uku sannan ya baje a kasa sumamme.

Gimbiya Rahila da Zarina kuwa, wani tsuntsu ne yai musu kwaf daya da fuka-fukansa, su ma dai suka yi ďaiďai a kasa ko kyakkyawan motsi ba su kara yi ba. Haiman, Shadira da boka Muzaffar kuwa, a kafafunsu aka laf-lafta musu sara, suka yi tsugunnon dole suna kwarara ihu sakamakon tsananin zogi da radadin da suka ji.

Nan take jini ya rinka zuba a jikinsu, kuma jiri ya debe su suka kwanta a kas bisa dole suka rungumi Raddara kawai suna jiran su ji mutuwarsu domin babu abinda za su iya tsinanawa don kare kansu.

Lumaira mahaifiyar Imran da Sarkin Farisa kuwa, tuni duk sun suma,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login