Showing 66001 words to 69000 words out of 75493 words

Chapter 23 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt

ce, "Wannan shi ne sakamakon maci amana irinka!"

A dai-dai waunan lokacie Rahila da Aljani
Maruful Dauwaz suka furtado suna numfashi sama-sama kuma suna gani dishi-dishi. Koda ganin haka sai shugaban Dakarun gidan ya yunkura zai karasa kashe su Maruful Dauwaz amma sai Ramlatul Siyam ta daka masa tswa ya dakata.

Shugaban Dakarun ya dubi Ramlatul Siyam cikin tsananin mamaki ya ce, "Haba ya shugabata, saboda me za ki hana ni hallaka su alhalin sun kasance manyan abokan gaba waɗanda suka zo domin su sace ki su raba ki da mahaifinki kuma su raba ki da wannan daula da kike ciki wacce babu inda za ki sami irinta a wannan duniya?"

Sa'adda shugaban Dakarun ya zo nan a zancensa sai ya ga Gimbiya Ramlatul Siyam ta sunkui da kanta kas ta yi shiru. Nan take idanunta suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo mata sannan ta dago da kanta ta ce, "Ai tuni na rabu da mahaifina domin ba zai taɓa dawowa ba, tun ranar da ya bar gida na san cewa mun yi bankwanan karshe ba za mu sake saduwa ba har abada.

Hakika lokaci ya yi da zan bar ku domin na je na fuskanci rayuwata ta gaba domin ita ce kaddarata, tabbataccen al'amarin da ba zai shafu ba.

Daga yau gabadayan Hadiman da ke cikin Wannan gida kun sami 'yancin kanku, kowannenku yana da damar tafiya inda yake so a cikin wannan duniya domin ya fara sabuwar rayuwa. tabbas wannan masarauta sai dai a tuna da ita a tarihi amma ta ruguje ke nan. Idan kun so za ku iya nada sabon Sarki daga cikinku wanda zai ci gaba da jagorantarku".

Koda gama fadin haka sai Ramlatul Siyam ta sa aka shiga yi wa Rahila da Aljani Maruful Dauwaz magani domin a ceto rayuwarsu.

A daidai wannan lokaci ne Sarki Laffaru ya fito daga cikin kunnen Aljani Maruful Dauwaz. Koda yai arba da miliyoyin gawarwakin da ke cikin falon kuma ya ga Gimbiya Ramlatul Siyam tsaye a gabansa ga su Maruful Dauwaz a kwance ikin mugun yanayi mai kama da suma ko Imutuwa sai ya firgita ainun ya yunkura zai koma cikin kunnen Aljani Maruful Dauwaz.

Caraf! Sai Gimbiya Ramlatul Siyam ta cafo hannunsa tana mai yi masa murmushi ta ce, "Haba ya kai mijina na gobe tsoron me kuma za ka ji alhalin komai ya zo karshe, burinka na daf da cika".

Koda jin wannan batu sai Sarki Laffaru ya yanke jiki ya gangaro daga kan Aljani Maruful Dauwaz a sume saboda tsananin mamaki da farin ciki. Bai farfado ba sai bayan sa'a uku. 🤣🤣🤣 ( yasin Laffaru ya cika ďan sa'a)

Yana farfaɗowa ya ga Aljani Maruful Dauwaz zaune daf da shi yana ta faman shara kuka.Ba komai ne ya sa Maruful Dauwaz yin wannan kuka ba face ganin Rahila a cikin mugun yanayi saboda Likitoci sun taru a kanta suna iya yinsu amma har a sannan tana numfashi sama- sama. Su kansu Likitocin guiwoyinsu sun yi sanyi sun sallama cewar abu ne mawuyaci ta yi nisan kwana ko kuwa ta rayu.

Maruful Dauwaz ya ci gaba da rusa kuka kamar ba zai daina ba saboda ya san cewa idan Rahila ta mutu shi ke nan ba zai ga wasiyyar masoyiyarsa ba marigayiya Gimbiya Rashmin. Babban abin bakin cikin ma shi ne, Rahila ba ta iya koda bude bakinta ma bare ta yi magana ta gaya masa inda ta ɓoye wannan wasiyya ta masoyiyarsa

Bayan Maruful Dauwaz ya dade yana kuka, sai Gimbiya Ramlatul Siyam da Sarki Laffaru suka kamu da tsananin tausayinsa suka shiga rarrashinsa har Ramlatul Siyam ta kwantar masa da hankali. tana cewa, ya yi hakuri babu mamaki nan da wani lokaci ta iya bude bakinta har ta yi magana".

Cikin alamun karayar zuci Aljani Maruful Dauwaz ya share hawayen idanunsa ya dubi Gimbiya Ramlatul Siyam ya ce, "Ya ke wannan yar Sarki, ki yi sani cewa ni kam na cire rai da rayuwar Rahila, don haka rayuwata ba ta da wani sauran amfani a doron kasa.Ki sani cewa na yi matukar mamaki da kika hana a kashe mu.

Shin za ki iya gaya mana dalilin da yasa kika hana a kashe mu har kika sa aka ceto rayuwarmu? Wannan ita ce kadai alfarmar da nake nema a wajenki kafin na yi sallama da wannan duniya".

Lokacin da Gimbiya Ramlatul Siyam ta ji wannan tambaya daga bakin Aljani Maruful Dauwaz sai hawaye ya zubo ma ta ta ce, "Ya kai Sarkin sadaukan aljanu, ka yi sani cewa ni a rayuwata tun ina yarinya karama duk abin da zai same ni sai an nuna min shi a mafarkina.

Kuma duk mafarkin da na yi sai ya tabbata a gaske. Fiye da shekaru biyar baya da suka shude na gani a cikin mafarkina cewar Daular Mulkin Mahaifina za ta rushe kuma zai bar gida don tafiya neman wani mashi da ake kira Galilu Harus.

Idan ya tafi neman wannan mashi ba zai dawo ba, a can zai mutu wajen fafatawa da wanda ke rike da mashin.

Ba wani ba ne ke rike da wannan mashi ba face abokin tafiyarku wanda ya yaudare ku ya jefa rayuwarku a cikin TSAKA MAI WUYA, Kunci da bakin ciki mara tukewa, wato Boka Muzuffar.

Ku yi duba izuwa jikin wancan bango yanzu zan nuna muku abin da ya wakana."Koda gama fadin haka sai Ramlatul Siyam ta yi nuni da hannunta izuwa ga jikin bangon Falon wanda ke Kudu. Nan take suka ga Boka Muzaffar a cikin dakin Halwar tsafinsa ya dukufa yana ta nazari.

Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai suka ga Sarki Nashmir ya diro cikin dakin daga sama
kamar haske. Kai tsaye Nashmir ya durfafi inda Boka Muzaffar ya jingine mashin GALILUL HARAS da nufin ya dauka. Har ya kai hannunsa i zuwa kan mashin zai dauka ke nan sai ya ji an doki fuskarsa. Yai tsalle sama ya gwaru da bangon dakin ya fado kasa.

Cikin hanzari ya mike tsaye zumbur! Yana mai zare takobinsa sai yai arba da Boka Muzaffar tsaye a gabansa shi ma ya zare tasa takobin.

Muzaffar ya dubi Nashmir a fusace sannan ya daka masa tsawa ya ce, Kai tsohon azzalumi ka yi sani cewa yau shekara talatin da biyar ke nan ina gwagwarmaya akan na mallaki wannan mashin ban same shi ba sai yanzu. Kai ma kuma ka dade kana nemansa kuma ka kasa zuwa kogon Darul Iksina ka dauko shi. Yanzu da na gama shan wahalata shi ne kai kuma kake son ka same shi a banza? To ka sani cewa Karyarka ta sha karya ya kai Nashmir. Ina tabbatar maka da cewa, ka kawo kanka GIDAN AJALI, sai dai gawarka ta fita daga nan".

Sa'adda Muzaffar ya zo nan a zanensa sai Sarki Nashmir ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan ya murtuke fuskarsa kamar an aiko masa da sakon mutuwa ya ce, "Ai kuwa idan har ban sami nasarar raba ka da wannan mashi ba sai dai a dauki gawa guda biyu, ni da kai babu wanda zai fita daga cikin wannan daki a raye."

Kafin Nashmir ya gama rufe bakinsa tuni Boka Muzaffar ya afka masa sun kacame da azababben yaki, suka wanzu suna masu kai wa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta.

Sai da Muzaffar da Nashmir suka shafe kwana uku suna wannan masifaffen yaki, ya zamana cewa kowannensu ya yi amfani da dukkan karfin sihirinsa da karfin damtsensa amma aka rasa wanda zai samu nasarar kashe wani.

A karshe suka yiwa juna fata-fata, har ya zamana cewa ko ina a jikinsu raunika n. Lokaci guda suka yanke jiki suka fadi kasa matattu, dayansu bai sake shurawa ba.

Faruwar hakan ke dawuya sai ga wani haske ya baiyana a cikin dakin. Nan take hasken ya rikiďe ya zama Sharlis.

Sharlis ta je inda aka jingine Mashin Galilul Haras ta dauki mashin ta daga shi sama sai ta kyalkyale da dariyar farin ciki ta ce, "Na tsinci dami akala! Tabbas yanzu na zama Sarauniyar sadaukai ta duniya.

Da sannu zan dauki gagarumar fansa akan babban makiyina Sarki Laffaru sannan na mallaki wannan duniya gaba dayanta.

Da wannan mashi a hannuna, babu wani sadauki ko matsafi da zai gagare ni. Babu wani wuri da zai yi mini wuyar zuwa. Komai yawan rundunar mayaka sai na tarwatsa su, komai nisan tafiya sai na ketata. Gama fadin hakan ke da wuya sai ta shafi wani ɓangare na jikin mashin na Galilul Haras.

Nan take ita da mashin suka zama wani irin gagarumin haske suka cilla sama ta cikin rufin dakin. Kafin kiftawar ido sun kule a cikin gajimare sun ɓace ɓat.

Koda gama ganin wannan al'amari sai Gimbiya Ramlatul Siyam ta fashe da matsanaicin kuka, tana mai duban su Aljani Maruful Dauwaz ta ce, "Kun ga yadda karshen mahaifina ya kasance, shi ya sa na gaya muku cewa ba zan sake saduwa da shi ba.

Lokacin da Sarki Laffaru ya ga wannanal'amari sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya dubi Ramlatul Siyam cikin tsananin tsoro ya ce "Yanzu ta yaya zan tsira daga sharrin Sharlis tunda ga shi ta mallaki mashin Galilul Haras, wannan yana nufin ke nan za mu iya fadawa hannunta a ko yaushe ta ci gaba da tsarona har izuwa lokacin da za ta cika burinta a kaina, koda kuwa na aure ki mun haifi 'yar da za ta kare ni?

Koda jin wannan batu sai Ramlatul Siyam ta yi murmushi ta ce, "Ba haka ba ne, akwai inda za mu je mu yi rayuwa babu abin da zai same mu daga yanzu har izuwa tsawon shekara goma sha takwas, a sannan ne Shaddadu dan Sharlis ya cika shekara ashirin da daya a duniya, kuma mahaifiyarsa ta mallaka masa mashin Galilul Haras a sannan ne zai bazama farautata cikin duniya.

A sannan ne kuma 'yarmu za ta cika shekara goma sha takwas a duniya ta zama gagarumar BASADAUKIYA kuma MAYAKIYA, wacce za ta kare ka daga sharrin Shaddadu.

Amma fa ka sani cewa duk ranar da Shaddadu ya yi arba da kai babu 'yarmu a kusa taka ta kare, don sai Shaddadu ya kama ka ya tafi da kai izuwa ga mahaifiyarsa. Ma'ana sai ya kai ka har can Birnin Kufa ya wulakanta ka sannan ya yi maka kisan gilla.

Ya yin da Ramlatul Siyam ta zo nan a zancenta sai hankalin Sarki laffaru ya kara dugunzuma ainun fiye da ko yaushe, ya dubi Gimbiya cikin tsananin damuwa ya ce, "Ashe dai tashin hankali da rashin kwanciyar hankali bai kare mini ba? Yanzu ta yaya zan magance wannan fargaba?"

Koda jin wannan tambaya sai Ramlatul Siyam ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Hanya daya ce maganin wannan fargaba, sai dai ita ma 'yar tamu ta fita farautar Shaddadu kamar yadda shi ma zai fito farautarka, ta raba shi da mashin Galilul Haras ta hanyar yaudara ba ta hanyar karfi ba.

Da zarar ta raba shi da wannan mashi shi ke nan ta karya lagonsa ba zai taba samun damar kama ka ba bare ya iya hallaka ka."

Lokacin da Ramlatul Siyam ta zo daidai nan a zancenta sai suka ji Rahila ta turnuke da tari har tana aman jini.

Al'amarin da ya kara dugunzuma hankalin Aljani Maruful Dauwaz ke nan, ya zo kanta ya ciccibe ta ya tashe ta zaune yana mai zub da hawaye, bai san sa'adda ya kama sambatu ba yana cewa, "Ya ke Rahila shin kin manta da alkawarın da ke tsakaninmu ne?Ga shi na taimake ki na biya miki bukatarki, idan kika mutu yanzu ba ki yi mini adalci ba. Ki gaya mini inda kika boye wasiyyar masoyiyata kafin ki tafi!"

Gama fadin hakan ke da wuya sai suka ga Rahila ta bude idanunta da kyar a hankali sannan ta bude bakinta yana karkarwa domin ta yi magana, amma sai ta kasa.

Koda ganin haka sai Ramlatul Siyam ta kwalawa wani Likitanta kira ya rugo ya zo ya bai wa Rahila wani magani.

Tana gama hadiye ruwan maganin sai barci ya dauke ta. A sannan ne Likitan yai ajiyar zuciya ya mikawa Ramlatul Siyam kwalbar maganin ya ce, "Dole ne a rinka bai wa Rahila wannan magani bayan kowacce sa'a uku idan ba haka ba kuwa za ta ci gaba da aman jini wanda zai iya zama sanadin ajalinta, kuma digo daya na maganin za a dinga disawa a cikin bakinta. Idan aka bata sama da digo daya shi ma zai iya yi mata illah."

Nan take Ramlatul Siyam ta dubi Sarki Laffaru da Maruful Dauwaz ta ce, "Yanzu sai ku tashi mu yi shiri mu bar wannan Birni na Hindu domin idan muka ci gaba da zama a nan, nan da tsawon kwana daya rak Sharlis za ta gano inda muke ta zo a cikin dakiku kadan ta hallaka mu ta kama Laffaru ta tafi da shi.

Koda gama fadin hakan sai Maruful Dauwaz ya ce, "To yanzu ina ne inda za mu je mu yi jinyar Rahila har ta warke ta cika mini alkawarina kuma ke da Laffaru ku yi aurenku".

Ramlatul Siyam ta ce, "Babu inda za mu je mu tsira face wani daji da ake kira Rauful Mausur.

Shi dai wannan daji na Rauful Mausur yana tsakanin Birnin Kisra da Birnin Istanbul.
In dai akwai sihirin tsafi a jikin mutum bai isa ya shiga cikin dajin Rauful Masnur ba face ya zama gawa saboda haka a nan ne kadai za mu iya zama mu yi rayuwarmu a cikin kwanciyar hankali.

Fatana shi ne Rahila ta sami lafiyar da za ta iya budar baki ta gaya mini inda wasiyyar masoyiyarka take kafin rai ya yi halinsa".

Koda gama fadin hakan sai Ramlatul Siyam ta mike tsaye ta sa aka debo musu kayayyaki da guzuri ana dorawa akan Aljani Maruful Dauwaz.

A wannan lokaci ne Maruful Dauwaz ya fada cikin kogon tunani yana mai cewa a ransa, "Inda ina da tabbacin cewa Rahila ba za ta sami lafiyar da za ta iya yi min magana ba da tabbas yanzu zan kashe kaina na huta da bakin cikin rayuwar duniya domin ban ga amfanin rayuwar tawa ba. Yana cikin wannan tunani ne aka gama shirye-shiryen tafiya.

Koda Ramlatul Siyam ta zo yin bankwana da jama'arta sai ta fashe da kuka, suma suka fashe da kukan saboda shakuwa.

A lokacin ne Ramlatul Siyam ta tuno da mahaifinta Sarki Nashmir kuma ta tuno da irin tsananin kaunar da ya nuna mata gami da gata, sai ta je gaban wani gunkinsa da aka sassaka mai matukar kama da shi wanda ke tsaye a tsakiyar falonta ta rungume gunkin ta sake fashewa da matsanaicin kuka.

Da kyar da sidin goshi Sarki Laffaru ya ɓanɓare Ramlatul Siyam daga jikin gunkin sannan ya ja ta suka je suka hau kan Maruful Dauwaz suka zauna.

Dama an shimfide Rahila a kan Maruful Dauwaz a gefe daya kuma an lulluɓe jikinta duka da mayafi fuskarta ce kadai a bude. Nan take Aljani Maruful Dauwaz ya bude fuka-fukansa ya tashi sama a hankali. Ramlatul Siyam tana dagawa jama'arta hannu, su ma suna daga mata kowa na zub da hawaye har Maruful Dauwaz ya kule a cikin sararin samaniya.....


Aljani Maruful Dauwaz ya wanzu yana mai tsala gudu a cikin sararin samaniya babu sassauci har sai da ya shafe tafiyar sa'a biyu da rabi cif sannan ya iso dajin Rauful Masnur ya sauka a tsakiyar dajin.

Daji ne mai dauke da ni'ima sosai akwai kyawawan bishiyoyi, duwatsu da dabbobin daji iri-iri, babu kalar da babu masu hadari da marasa hadari.

Koda saukar Maruful Dauwaz a cikin wannan daji sai shi da Ramlatul Siyam suka kamu da tsananin sha'awar dajin shi kuwa Sarki Laffaru sai ya ji ya kamu da tsananin tsoro musamman da ya jiyo kukan manyan namun daji daga nesa suna gurnani. Koda Ramlatul Siyam ta fahimci halin da Sarki Laffaru ke ciki sai ta bushe da dariya, al'amarin da ya bai wa Maruful Dauwaz da Laffaru mamaki ke nan.

Maruful Dauwaz ya dube ta ya ce, "Ya ke wannan Sarauniyar kyawawan matan duniya ina dalilin wannan dariya taki?".

Ramlatul Siyam ta yi shiru ga barin dariya sannan ta ce, "Gani na yi mijin da zan aura rago ne kuma matsoraci ga shi ba zan taba yarda ya kusance ni ba face ya kawo mini kan rikakken Zaki a matsayin sadakina".

Koda jin wannan batu sai hankalin Laffaru ya dugunzuma ainun ya ce, "Haba dai! yaya ni da na rasa dukkan karfin dantsena za ki ce sai na je na kashe zaki na yanko kansa?"

Da jin haka sai Ramlatul Siyam ta murtuke fuska ta ce, "Ai kuwa ashe ba za ka taɓa zama mijina ba. Ai mu a kasarmu wannan ita ce al'adarmu ta aure. Kafin namiji ya kusanci matarsa sai ta zabi irin jarumtakar da take son ya yi, ya yi ta.

Inda za mu tsufa a haka a matsayinka na mijina ba zan taɓa yarda da kai ba sai ka zo mini da kan zakin da ka kashe da hannunka saboda haka, ka shirya daga gobe da safe za ka fara shiga cikin wannan daji domin farautar rikakken Zaki.

Ka sani cewa idan ka kawo mini kan yaron Zaki ka yi wahalar banza."

Koda gama fadar hakan sai Ramlatul Siyam ta dauki tanti daga kan Aljani Maruful Dauwaz ta fara kokarin kafa shi.

Shi kuwa Sarki Laffaru sai ya koma gefe daya ya yi tagumi yana tunanin wannan sabon al'amarin da Ramlatul Siyam ta zo masa da shi.

Nan take ya ji ya tsani kansa kuma nadama ta zo masa ya ce a zuciyarsa, "In da ya san cewa zai shiga cikin wannan tsananin tashin hankali da tun farko bai yarda ya baro kasarsa ba ya sha wannan bakar wahala da fuskantar tashin hankali, da gwara ma ya kashe kansa ya huta da takaici da bakin ciki.

Har Ramlatul Siyam ta gama kafa tantin ta dauko Rahila ta shigar da ita cikin tantin ta kwantar da ita, sannan ta debi kayayyakinta ta kai ciki ta zube, Laffaru bai daina tunani ba.

Yana cikin tunanin ne Ramlatul Siyam ta fito daga cikin tantinta ta dube shi ta ce, "Ai sai ka tashi ka yi kokarin kafa naka tantin domin ba zai yiyu ba na kwanta a waje daya tare da kai ba face ka kawo mini sadakina".

Tana gama fadin hake ta juya ta koma cikin tantinta. Shi kuwa Sarki Laffaru sai hankalinsa ya kara dugunzuma ainun ya rasa abin da ke masa dadi a duniya.

Kawai sai ya ji Maruful Dauwaz ya bushe da dariya. Al'amarin da ya fusata shi ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login