Showing 12001 words to 15000 words out of 75493 words

Chapter 5 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt

tsammani sai wannan Biri ya ji an dankara masa naushi a tsakiyar kansa. Take kwanyarsa ta ɓare, sai ga kwakwalwa ta yi ɓullutso ta tarwatse a sama, ya baje a kasa matacce.

Cikin matukar zafin nama Shaharan ya suri Zarina da dan uwanta ya goya su a bayansa ya manta da batun dokinsa, wanda ke goye a bayan aljani Marhabul Zaurus ya falfala da azababben gudu irin wanda bai taɓa yi ba a rayuwarsa. Sai ga shi wannan karon ya tserewa Birirrikan duk da cewa a sama suke binsa, amma ya ba su muguwar rata.

Al'amarin aljani Marhabul Zaurus kuwa, shi ma a wannan lokaci ya sami raunika sama da guda arba'in a jikinsa, da kyar yake iya gudu goye da dokin Shaharan, har ma yana faduwa yana tashi saboda juriya da na ci.

Shi kansa dokin na Shaharan an sassare shi ya pmfi sau goma, kamar ma ba zai rayu ba, domin ko motsin kirki ba ya iya yi akan aljani Marhabul Zaurus, sai numfashi sama-sama.

Hakika wannan rana dai babu wanda bai ga mutuwa ba muraran a cikin wannan abokan tafiya. Kuma babu wanda bai sami raunika sama da guda goma ba a jikinsa ba. Har 'yan uwan jaruman wadanda bavsu iya kare kansu bare su kare wani.

Sarki Laffaru kuwa, rauni tara ne a gadon bayansa, kuma ya daɗe da suma a bayan boka Muzaffar, amma saboda bala'i ya kai bala'i, shi kansa boka Muzaffar din yana cikin mugun hali bai san abinda ya faru ga Sarki Laffaru ba.

Ita ma gimbiya Rahila wacce ake ganin cewa tafi kowa jarumtaka, juriya da na ci, sai da ta sami manyan raunika guda uku a jikinta, ya zamana cewa da kyar take iya gumurzu kuma tuni ta karaya, ta san cewa dayansu ba zai tsira ba daga sharrin wadannan Birirrika.

Sai da aka shafe sa'a hudu cur! Ana wannan bakin gumurzu tsakanin wadannan Birirrika da su sadauki Shaharan, amma ba a sake kashe wani biri koda guda daya ba.

Lokacin da jaruma Shadira ta dawo cikin haiyacinta sa'adda ta baje a kasa da rub da ciki, tana bude idanunta ta ga jini na malala akan fuskarta, kuma ta taɓa dan uwanta Masnur wanda ke goye a bayanta ta ji ya langwaɓe kamar ba shi da rai, sai ta takarkare ta kwarara uban ihu cikin tsananin fusata.

Kamar sifirin haka ta do ki kasa da hannayenta biyu, sai gani aka yi ta yi sama kamar an janye ta da majajjawa. Tana saman ta janyo kibiyoyi a kuttun bakanta ta dana akan bakanta ta taɓe ta sakarwa Birirrikan harbi. Nan fa kibiyoyin guda ashirin suka cake a cikin idanun Birirrika guda ashirin. Take suka zube kasa matattu.

Koda ta ga ta sami wannan nasara sai ta ki yarda ta duro kasa kawai sai ta rinka dira akan bishiyoyi tana dada yin tsalle sama kamar tsuntsuwa mai fuka-fuki. A saman ta ci gaba da zaro kibiyoyi tana dada ďanawa akan kwarin ta yi ta harbin Birirrikan cikin bakin zafin nama wanda ita kanta tavyi mamakin yadda aka yi ta iya wannan jarumtaka.

A wannan lokaci tuni sauran abokan tafiyarta duk sun sare suna zubewa kasa cikin tsananin galabaita, wasu ma a sume suke, Shadira ce kadai take gumurzu da Birirrikan.

Ganin irin muguwar ɓarnar da Shadira ke yiwa Birirrikan ne yasa Birirrikan suka rabu da sauran abokan tafiyar suka mai da hankalinsu akanta suna daka tsalle sama domin su cafke ta amma sai ta zame musu alakakai ta rinka zulle musu ta zama kamar shaidaniya a tsakiyarsu, tana dada ci gaba da ragargazar su.

Haka dai aka ci gaba da wannan azababben yaki tsakanin jaruma Shadira ita kaɗai da waɗannan mugayen Birirrikan ba ji ba gani, kuma ba sassauci domin tana yin yaki ne da dukkan karfinta cikin kunar rai da dakewar zuciya ko ita ko su. Su ma Birirrikan sai suka haukace suna ta yin wannan ruri mai dimauta bil'Adama suna ta kai wa Shadira mugayen hare-hare. Duk sa'adda ta ga za a kaiwa Masnur hari sai ta wurkila bayanta ta goce, ta gwammate a sami jikinta. Da zarar an sari jikinta ko an soketa sai ta kurma uban ihu ta yi kamar za ta rikito kasa, amma saboda na ci sai ka ga ta daure ta ci gaba da gumurzu. Sai da aka shafe sa'a biyu da rabi ana wannan masifaffen artabu sannan Shadira ta sami nasarar kashe gabadayan Birirrikan, itama ta rikito kasa, ji kake bam! fuskarta ta gwaru da kasa ta baje a kasa sumammiya.

A wannan lokaci sadauki Haiman ne kadai a zaune cikin haiyacinsa, amma kowa ya suma. Sadauki Haiman yai sauri ya kwance matarsa Lumaira daga bayansa ya kwantar da ita a kasa. Koda ya ga bata wani motsi kuma ga raunika har guda uku a jikinta sai ya rude ya kidime yai zumbur ya samo ruwa ya yayyafa ma ta a fuskarta. Faruwar hakan ke da wuya sai ta farfado tana mai jan dogon numfashi. Koda ta bude idanunta ta ga mijinta zaune a gabanta a raye sai ta rungume shi, duk su biyun suka kamu da tsananin farin ciki. Jim kadan kuma sai sauran abokan tafiya suka fara farfadowa suna dawowa cikin haiyacinsu, duk wanda ya bude idonsa ya ga masoyinsa a raye sai ya rungume shi yana murna.

Sai da kowa ya nutsu sannan aka ga cewa har yanzu jaruma Shadira bata farfado ba, shi ma dan uwanta yaro Masnur wanda ke goye a bayanta bai farfadoba kamar maya zama gawa, domin babu ko alamar numfashi a jikinsa. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin kowa ke nan. Cikin hanzari aka kwance Masnur daga bayan Shadira aka shiga yi musu magani ana ta yayyafa musu ruwa domin su farfado. Da kyar da sidin goshi aka sami nasara Shadira ta fara numfashi sama-sama, shi kuwa yaro Masnur babu labari. Nan take hankalin kowa ya kara dugunzuma aka shiga shawarar abin da ya kamata a yi. Boka Muzaffar ya mike tsaye da kyar ya zo kan yaro Masnur ya daga hannunsa guda sannan ya kara hancinsa a dai-dai nasa ya ji babu alamar numfashi, ya dora kunnensa a kirjin Masnur, nan ma ya ji babu alamar numfashi, sai ya dago kai ya dubi abokan tafiya daya bayan daya cikin yanayin karayar zuciya yana mai musu nuni da yaro Masnur ya mutu. Nan take kowa ya fara kuka, masu kwalla na yi, masu zubar da hawaye na zubarwa..

Ana cikin wannan hali ne jaruma Shadira ta farfado sosai, ai kuwa sai ta mike zaune zumbur! ta shafa bayanta, koda ta ji babu yaro Masnur sai ta mike tsaye zumbur! tana waige-waige tana neman dan uwanta Masnur ta fara kwala masa kira.

A wannan lokaci MAsnur na kwance a bayan boka Muzaffar ba ta ganshi ba. Ganin zubar hawaye ne akan fuskokin abokan tafiyar ta ta yasa jikinta yai sanyi. Kawai sai ta dubi boka Muzaffar ta ce, "Ina dan uwana?" Muzaffar ya kasa ba ta amsa, kawai sai ya share hawayen idanunsa ya koma gefe daya, Shadira ta yi arba da gawar Masnur a kwance idanunsa a bude kamar zai yi ma ta magana, har a sannan jini na kwarara daga kan tsakiyar kansa.

Shadira ta tunkaro inda gawar ke kwance çikin tsananin tsoro, har jikinta na makyarkyata. Koda ta iso daf da gawar ta dubi tsakiyar kan Masnur sai ta ga ashe kan ya kusan darewa ma gida biyu har tana ganin kwakwalwarsa. Nan take Shadira ta kwarara uban ihu sannan ta durkushe-kasa bisa guiwoyinta ta ciccibi gawar Masnur ta rungume ta a kirjinta ta fashe da matsanancin kuka tana mai kurma ihu. Al'amarin da ya jefa kowa cikin tsananin tausayi da bakin ciki kenan aka ci gaba da kuka kamar ba za a daina ba.

Komai rashin imanin mutum idan ya ga yadda Shadira ke wannan uban kuka da bakin ciki bisa rashin dan uwanta dole ne ya kamu da tsananin tausayinta.

Bayan Shadira ta dade a kankame da gawar dan uwanta yaro Masnur tana kuka sai kuma ta shiga sambatu cikin rera waka mai dauke da kalmomin ban tausayi masu karya zuciya tana mai cewa:

"Ina amfanin rayuwa idan babu masoyi? Duniya ki rike jin dadinki Kuma ki rike kayan kawar da ke cikinki.

"Domin ba ki da abin da zai kawar mini da bakin cikin zuciyata"

"Ke mutuwa ashe ke matsoraciya ce? Ki fito fili ki tare ni idan kin isa, yau sai na ga bayanki!"

Lokacin da su sadauki Haiman suka ji irin wannan sambatu da Shadira ke yi sai suka daďa kamuwa da tsananin tausayinta. Nan take Lumaira ta saki Haiman ta je wajen Shadira ta rungume ta ta baya ta shiga rarrashinta, amma a banza, kamar ma daďa zuga ta ta yi, sai Shadira ta sake fashewa da matsanaicin kuka tana mai dada kankame gawar ďan'uwanta Masnur, kuma ta ci gaba da sambatu.

Har aka gama sa wa kowa magani a rauninsa Shadira ba ta saki gawar Masnur ba, kuma ba ta daina kuka da sambatu ba.

Al'amarin da ya dugunzuma hankalin kowa ke nan a wajen. Koda ganin haka sai boka Muzaffar ya kira dukkanin jaruman, wato Haiman, Imran, Zarina da Shaharan suka koma gefe daya domin su tattauna akan al'amarin jaruma Shadira

Boka Muzaffar ya dubi jaruman a nutse, ya ce, "Ya ku abokan tafiya, ku yi sani cewa na kira ku ne izuwa nan domin mu yi shawara bisa halin da abokiyar tafiyarmu ta shiga. Idan muka kyale ta ba mu raba ta da gawar dan uwanta ba ta ci gaba da wannan sambatu za ta iya haukacewa. Ma'ana ta rasa hankalinta gabadaya, idan kuma muka ce za mu rabu da ita anan tabbas za ta iya kashe kanta tunda ba ta da sauran buri da farin ciki a rayuwarta. Haka kuma ba za ta yarda ta bi mu ba mu ci gaba da wannan tafiya tare da ita tunda burinta ya yanke. Yanzu mene ne shawararku bisa abin da ya kamata mu yi a kanta?" Sa'adda boka Muzaffar ya zo nan a zancensa sai hankalin kowa ya kara dugunzuma aka rasa wanda zai ce kala, kuma suka kara kamuwa da tsananin tausayin Shadira.

Bayan shudewar 'yan dakiku masu tsawo, sai sarki Laffaru yai gyaran murya ya ce, "Ni ina ganin cewa ba mu da wani zabi wanda ya fi kawai mu tafi mu bar ta a nan ita da gawar dan uwanta, domin idan ma muka tafi da ita matsala za ta zame mana, ba za ta iya taɓuka komai a cikin tafiyar ba, sai dai ma ta daďa karya mana zuciya".

Koda jin wannan batu sai gimbiya Zarina ta fusata, ta daka wa Sarki Laffaru tsawa ta ce, "Ai dama kai tsohon azzalumi ne, ba ka san irin ciwon da masoyi yake ji ba yayin da ya rasa masoyinsa, shi ya sa ka raba Sharlis da iyayenta, ka lalata rayuwarta, gavshi kuma kaicma yanzu rayuwarka ta shiga mugun hadarin da ba ka da tabbacin kubuta. Wato yanzu mun gama cin moriyar ganga kenan kana son mu yar da kwauranta? Sai da Shadira ta gama sallama rayuwarta ta ceto tamu sannan kake son mu yi mata butulci mu tafi mu bar ta a lokacin da bacta da kowa, ba ta da sauran buri."

Zarina ta dubi boka Muzaffar ta ce, "Ba za mu bar Shadira a nan ba. Yanzu sai mu lallaɓa ta mu karbe gawar daga hannunta mu binne shi sannan mu ci gaba da wannan tafiya bayan mun yi jinyar jikku nan mu ta a kallah kwanaki bakwai.

Koda jin wannan batu sai kowa ya aminta. Nan take Zarina da Lumaira suka je wajen Shadira suka shiga rarrashinta a kan ta ba su gawar yaro Masnur domin a binne shi amma sai taki.

Koda ta ga sun matsa ma ta sai tacyi wuf ta goya gawar a bayanta ta daure ta tamau sannan ta dana kibiyoyi akan bakanta ta tsira su ta ce, "Duk wanda ya ce, "Zai raba ni da dan uwana a cikinku sai na kashe shi!"

Cikin alamun tsoro Zarina da Lumaira suka bar wajenta suka koma can inda su boka Muzaffar ke zaune. Nan fa aka rasa wanda zai je ya karbi gawar a hannunta. Da ma tunda aka fara wannan rikici sadauki Imran bai ce uffan ba.

Kawai sai ya dubi mahaifiyarsa ya ce, "Zan je na karbi gawar wannan yaro daga hannun 'yar uwarsa na binne shi".

Koda jin haka, sai mahaifiyar Imran ta firgita ainun ta rike hannayensa ta ce, "Kada ka je gare ta ta kashe ka a banza". Imran ya yi murmushi ya ce, "Koda ta rasa hankalinta ba za ta kashe ni ba. Ki zuba ido kawai ki ga abin da zai faru".

Yana gama fadin hakan sai ya mike tsaye ya nufi inda Shadira ke tsaye goye da gawar yaro Masnur ya durfafe ta kai tsaye ba tare da shakkar komai ba, amma ya kura mata idanu cikin alamun tausayawa, har kwalla ta ciko a idanunsa.

Lokacin da Shadira ta ga Imran ya durfafo ta kuma ta tabbatar da cewa so yake ya karɓe gawar Masnur daga gare ta sai ta ritsa shi da bakanta ta saita shi, kuma ta tabe bakan, amma sai hannunta ya kama karkarwa ta kasa harbinsa, ita ma ta kura masa idanu kawai ba tare da ta sauke bakan nata kasa ba. Imran ya ci gaba da tunkararta ba tare da jin tsoron komai ba. Al'amarin da ya bai wa kowa mamaki kenan aka ci gaba da kallonsu kawai domin a ga abin da zai faru.

Yayin da ya rage saura bai fi taku uku ba kacal tsakanin jaruma Shadira da Imran sai ta dan sauke bakanta ta saki harbi daf da kafarsa ta daka masa tsawa ta ce, "Kada ka kara kusanto ni. Wannan shi ne kashedin karshe a gare ka!" Imran ya yi murmushi kawai ya ci gaba da tunkaro ta, ita kuma ta dada daga kwarinta ta saita shi kuma ta taɓe kwarin iya karfinta. A wannan lokaci ne mahaifiyar Imran ta fashe da kuka saboda ganin za a kashe danta a banza.

Har Imran ya zo daf da Shadira yadda baka ce kawai a tsakaninsu amma ta kasa harbinsa kawai sai ya sa hannunsa ya ture Bakan nata sannan ya buďe hannayensa a lokacin da hawayen tausayi ya zubo masa. Nan take Shadira ta yi jifa da bakanta ta rungume shi tana mai sake fashewa da kuka, ta kankameshi a jikinta.

Imran ya janye jikinsa daga cikin nata suka fuskanci juna sosai ya ce, "Ya ke abar bege da tunanina tun farkon haduwarmu, ki yi sani cewa tsananin tausayinki bisa wannan babban rashi da kika yi yanzu ya sa na karya alkawarin da na yi wa mahaifiyata a baya cewar ba zan yi soyayya ba sai bayan ta sami lafiya. Hakika na kamu da tsananin tausayinki da na ga kin rasa dan uwanki wanda kike so fiye da komai a duniya, sannan sai na kwatanta rashin a kaina na ce inda ni ne na rasa mahaifiyata lallai zan ďimauce fiye da yadda kika ďimauce. Daga yau na yi alkawarin zan ba ki soyayya ta gaskiya gami da kulawa irin wacce kika bai wa dan uwanki Masnur domin na debe miki kewar rashinsa. Ina son ki rungumi kaddara. Ki sani cewa gabadayanmu nan babu wanda ya fi karfin ya tsinci kansa a cikin irin halin da kika shiga. Yanzu sai ki bani gawar Masnur domin mu binneshi".

Sa'adda Imran ya zo nan a zancensa sai Shadira ta sake rungume shi ta fashe da sabon kuka na murna da bakin ciki.

Lokacin da mahaifiyar Imran ta ji abin da danta Imran ya fada wa Shadira sai farin ciki ya lulluɓe ta ta ji kamar an ba ta kyautar mulkin duniya, domin ďanta ya samu soyayyar gaskiya. Haka dai suka taru suka haka kabari suka sanya yaro Masnur a ciki suka bizne koda Shadira lallai da gaske ta rasa ďan uwanta har abada sai ta kara fashewa da kuka ta rungume Imran. Haka dai Imran ya cigaba da rarrashinta har gari ya waye ba tare da sun runtsa ba. Bayan cikar kwanaki bakwai sai kowa ya kimtsa ya yi shiri domin a cigaba da tafiya. Lokacin da jaruma Shadira ta ga za ta bar kabarin dan uwanta Masnur kuma abu ne mawuyaci ta sake ganin kabarin sai ta fashe da kuka ta fada kan kabarin tana sumbatarsa.

Al'amarin da ya karya zuciyar gabaďayan abokan tafiyar kenan, saboda kowa ya san cewa shi ma zai iya rasa masoyinsa nan gaba a cikin tafiyar. Su duka sai suka kama kuka. Hatta gimbiya Rahila, boka Muzaffar da Sarki Laffaru wadanda ba su da 'yan uwa ko masoya a cikin wannan tafiya, ba su san sa'adda suka fara kuka ba. Da kyar Imran ya samu ya bambare Shadira daga kan kabarin dan uwanta Masnur, ya ja ta suka je suka hau kan aljani Marhabul Zaurus suka zauna.

Cikin gaggawa sauran abokan tafiyar ma suka hawo suka zazzauna sannan Marhabul Zaurus ya bude fuka-fukansa ya tashi sama ya luluka izuwa cikin gajimare yana mai tsala gudu suka durfafi dajin na uku

Bayan an sami kamar sa'a uku ana tafiya a sama ba tare da kowa ya ce kala ba, sakamakon alhinin mutuwar da aka yi, sai aljani Marhabul Zaurus yai gyaran murya sannan ya juyo da kansa ya dubi boka Muzaffar cikin alamun tsoro ya ce, "Ya shugabana ka yi sani cewa tun yanzu zuciyata ta fara bugawa da karfi saboda tsoro, domin nan da cikar sa'a biyu rak za mu riski wannan daji na uku mai dauke da miyagun manya-manyan tsuntsaye.

Ka sani cewa aljanu ma komai girmansu da karfinsu suna shakkar waďannan tsuntsaye saboda karfin sihiri ba ya tasiri a kansu, kuma suna da gagarumin karfi na gaban kwatance domin da yatsu biyu kacal suke surar giwa su yi sama da ita komai girmanta. Kuma duk abin da suka karta da faratan kafafunsu to fa ko dutse ne sai ya farfashe.

Daya daga cikinsu yana iya cinye rabin giwa ya baiwa 'ya'yansa rabin su cinye Suna da tsananin yawan gaske yadda ko a birni guda suka yiwa rubdugu za su iya hallaka komai da kowa a cikin kankanin lokaci. Anya kuwa za mu iya tsallake sharrin wadannan tsuntsaye?"

Koda jin wannan tambaya sai boka Muzaffar ya sunkui da kansa kas yai shiru bai ce komai ba, saboda ba shi da wani bayani mai gamasarwa. Daga can

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login