Showing 54001 words to 57000 words out of 75493 words
Chapter 19 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt
su gwada 'yar kashi.
Sadauki Najwar ya yi murmushi ya yafito da hannu. Nan take Rahila ta afka wa Najwar ta hau bugunsa da naushinsa da hannu da kafa. Wannan karon ma Najwar bai kaucewa harin nata ba. Duk sa'adda Rahila ta naushi jikin Najwar sai ta ji kamar karfe ta nausa, ba shiri ta ja da baya tana yarfe hanhayenta domin ji ta yi kamar yatsunta sun kakkarye. Kafin ta sake yin wani yunkuri sai ta ga Najwar tsulum a gabanta ya gabza ma ta naushi a fuska.
Nan take ta sulale kasa sumammiya. Koda Laffaru ya ga abin da ya faru ga Rahila sai ya razana ainun gaba daya jikinsa ya kama karkarwa bai san sa'adda ya sakin guntun fitsari ba a wando saboda tsananin razana. Har izuwa wannan lokaci Aljani Maruful Dauwaz ya kasa kwatar kansa daga hannun Aljani Barukul Masnur sai wutsil-wutsil yake kamar Bera a bakin Mage.
Sadauki Najwar ya sake tuntsurewa da dariya a karo na uku sannan ya dubi Barukul Masnur ya ce, Saki Maruful Dauwaz na fafata da shi domin ina son na ga iyakar jarumtakarsa".
Da jin wannan umarni sai Barukul Masnur ya yi jifa da Maruful Dauwaz a kas tamkar an yar da jikakken tsumma. Cikin taurin rai Maruful Dauwaz ya mike tsaye zumbur! Ya zare sihirtacciyar takobinsa ya ce, "Tabbas zan nuna maka cewa ni jarumi ne wanda ba ya gudu kuma ba ya shakkar abokin gaba komai jarumtakarsa da karfin sihirinsa."
Najwar ya yi murmushi ya ce, "Da kyau, haka nake son na ji kalamin yarda da kai daga bakin jarumin kwarai".
Gama fadin hakan ke da wuya sai shi ma Najwar ya zare tasa sihirtacciyar takobin ya fuskanci Maruful Dauwaz suka tsaya suna kallon kallo, a lokacin da takobin Maruful Dauwaz ke fitar da wani irin farin haske ita kuma takobin Najwar tana fitar da jan haske.
Kwatsam! Sai suka ruguntsume da azababben yaki, Aljani Barukul Masnur da Sarki Laffaru suka zama 'yan kallo, ita kuwa Rahila har a sa'anan ba ta farfado ba. Najwar da Maruful Dauwaz suka rinka kai wa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta Duk sa'adda takubban nasu suka hadu sai ka jí an tsala tsawa mai firgitarwa kuma tartsatsin wuta da hayaki na tashi. Ai kuwa suna fara gumurzu Maruful Dauwaz ya raina kansa domin da kyar yake iya kare harin Najwar saboda ji yake kamar dutse mai nauyi ake maka masa akan takobinsa.
Da suka kara nutsawa a cikin gumurzun sai ya zamana cewa sun tashi hankalin tsaunin gaba daya domin duk wanda aka kai wa hari ya goce da zarar an sari dutsen kogon sai ka ga dutsen ya zabtare yana rugujewa.
Babban abin da ya fi dugunzuma hankali Aljani Maruful Dauwaz shi ne, KAIFI DA TSINI ba sa tasiri a jikin sadauki Najwar amma tuni Najwar ya yi ma Maruful Dauwaz kyawawan yanka guda biyu, ďaya a kirjinsa, daya kuma a kan kaurin kafarsa ta hagu. Raunin kafar ya yi zurfi jini na ta zuba har ta kai cewa yana ďingishi da jan Kafar amma saboda naci da juriya bai fasa ci gaba da yakin ba a haka.
Lokacin da Aljani Marufu! Dauwaz ya fahimci cewa idan har suka ci gaba da yakin a haka tabbas Najwar zai sami nasarar hallaka shi a cikin kankanin lokaci, sai ya fara turanin dabarar da ya kamata ya yi. Nan take kuwa dabara ta fado masa ya sauya yanayin fadan ya fara guje-guje.
Nan fa suka kasa tsere suna ratswa ta cikin ramukan da ke kan tsaunin da azababben gudu. Al'amarin da ya matukar bai wa Aljani Maruful Dauwaz mamaki ke nan bisa ganin yadda bil'adama ke da tsananin karfin gudu kamar yadda shi ma yake da azababben gudu a matsayinsa na Aljani, Aljanin ma wanda babu mai karfin gudunsa a cikin dukkanin al'ummar aljanun duniya. Amma da ya tuna cewa aikin sihiri ne sai hankalinsa ya dawo jikinsa ya kara zage dantse a cikin tseren gudun da suke yi. Wani lokacin idan ya ɓace wa Najwar sai kuma ya dawo masa cikin shammace yana mai kai masa wawan sara amma duk da hakan ya kasa samun nasarar koda lakutar jikinsa.
Haka dai suka ci gaba da yakin бuya har izuwa tsawon lokaci ba su kara yin gaba da gaba ba. Koda sadauki Najwar ya ga Aljani Maruful Dauwaz ya fara wahalar da shi har ma yana haki sai ya fusata ya tsaya cak! a waje daya kuma ya mayar da takobinsa cikin kufe ya zauna a kasa dirshan ya harde kafafunsa yana mai runtse idanunsa.
Ashe Maruful Dauwaz ya makale a saman jikin rufin tsaunin yana ganin duk abin da yake yi.
Cikin shammace Maruful Dauwaz ya baiyana tsulum a gaban sadauki Najwar ya kai masa wawan sara da nufin ya raba kansa gida biyu.
Caraf! Sai sadauki Najwar ya rike takobin Maruful Dauwaz da hannu daya amma sai takobin ta sari hannun nasa jini yai tsartuwa yana mai kwarara uban ihu sakamakon mugun zafi da ya ji amma duk da hakan bai saki takobin ba sai yai wuf ya shaki wuyan Aljani Maruful Dauwaz ya jijjiga shi a sama sannan ya fyada shi da kasa ya kuma take wuyansa da kafa daya sai ga shi Aljani Maruful Dauwaz ya soma kakarin mutuwa.
Sa'adda sadauki Najwar ya ga Maruful Dauwaz ya kusan mutuwa sai ya dauke kafarsa daga kan wuyansa sannan ya nuna shi da hannun hagu, take wata irin sarkar tsafi mai dauke da wuta ta kanannade Maruful Dauwaz tana kona shi yana rusa ihu kamar ransa zai fita.
A lokacin ne Aljani Barukul Masnur ya fashe da dariyar mugunta saboda jin dadin ganin azabar da ake yi wa Maruful Dauwaz.
Ba zato ba tsammani sai Najwar ya sake nuna Maruful Dauwaz da hannu sarkar sihirin da take kona shi ta ɓace ɓat. Koda ganin haka sai Aljani Barukul Masnur ya dubi sadauki Najwar cikin mamaki da fishi ya ce, "Saboda me za ka ki karasa kashe shi alhalin abin da yakawo mu ke nan?"
Ya yin da sadauki Najwar ya ji wannan tambaya sai ya bushe da dariya lokaci guda kuma ya murtuke fuska ya ce, "Ba zan kashe shi ba saboda zai yi mini gagarumin amfani".
Koda jin haka sai Barukul Masnur ya fusata ainun ya ce, "Idan ba za ka kashe shi ba ni ka ba ni wuri na kashe shi don kada ka sa fishin Sarki ya tabbata a kanmu".
Kafin Barukul Masnur ya gama rufe bakinsa tuni Najwar ya daka masa tsawa sanan ya ce, "Ya kai Barukul Masnur ka yi sani cewa daga yanzu ka daina bin umarnin Sarki Nashmir sai dai ka bi umarnina a matsayina na wanda zai hau karagar Sarki Nashmir nan da cikar kankanin lokaci". Ya yin da Aljani Barukul Masnur yaji wannan batu sai ya cika da tsananin mamaki ya sake buɗar baki zai ce wani abu sai Najwar ya tari numfashinsa ya ce, "Ka bi umarnina ko kuma kai ma yanzun nan na kashe ka. Ka sani cewa yau shekara talatin da biyar ke nan ina jiran zuwan wannan rana ga shi kuma ta zo don haka, babu wani mahaluki da ya isa ya hana ni amfanarta.
A dai-dai wannan lokaci ne Rahila ta farfadodaga dogon suman da ta yi. Koda ta bude idanu ta ga Aljani Maruful Dauwaz kwance magashiyan a gefe daya duk jikinsa ya cika da kunar wuta sai zuciyarta ta karaya da tabbatar da cewa dukkan burinsu ya yanke, kawai sai ta kurawa sadauki Najwar idanu tana jira kawai ya zo ya karasa kashe ta.
Ba zato ba tsammani sai ta ga sadauki Najwar ya dube ta ya yi murmushi sannan ya dubi Aljani Maruful Dauwaz wanda ke numfashi sama-sama ya ce da shi, "Ya kai jarumin jarumai, ka yi sani cewa akan hanyata ta zuwa nan inda kuke na yi bincike na gano cewa kana da sa'a kuma duk bala'in da za a yi ba za ka mutu ba kuma kai kadai ne za ka iya samun nasarar sace Gimbiya Ramlatul Siyam daga cikin fadar maigidana Sarki Nashmir.
Bisa wannan dalili ne na yanke shawarar ba zan kashe ka ba. Ina so ku sani cewa a duniya ba ni da wani buri wanda ya fi na mallaki karagar Sarki Nashmir saboda haka yanzu ina son ni da ku mu hada KARFI DA KARFE mu yaki Sarki Nashmir mu kawar da shi kun ga ni zan sami karagata ku kuma za ku sami Ramlatul Siyam.
Batun yawun barcin Sarki Nashmir kuwa, tuntuni na dade da mallakarsa bari na nuna muku zahiri".
Nan take sadauki Najwar ya zura hannu a cikin aljihun wandonsa ya dauko wata 'yar mitsitsiyar kwalba ya nunawa Maruful Dauwaz da Rahila.
Koda ganin wannan kwalba sai Aljani Maruful Dauwaz ya ce, "Ya za a yi mu tabbatar da cewa abin da ke cikin wannan kwalba yawun barcin maigidanka ne?"
Najwar ya bushe da dariya ya ce, "Babu yadda za a yi ku iya tabbatar da hakan face kun je da kwalbar izuwa gidan tarihi na Birnin Kisra kun tona kasa kun binne ta kuna yin hakan za ku ga mashin Galilul Haras ya baiyana a cikin gidan tarihin. Idan kun amince da bukatata sai mu zauna anan cikin wannan tsauni har ku gama jinyar jikinku tsawon kwanakin da ya dace sannan mu yi shiri mu je a yi yakin karshe tsakaninmu da Sarki Nashmir domin burina da naku ya cika."
Lokacin da sadauki Najwar ya zo nan a zancensa sai Maruful Dauwaz, Rahila da Sarki Laffaru suka hau kallon junansu suka kasa cewa komai. Daga can sai Maruful Dauwaz ya yafito Rahila da Laffaru suka zo wajensa suka yi kus-kus sannan Laffaru ya dubi sadauki Najwar ya ce, "Mun amince za mu hada kai domin bukatarmu da taka ta biya."
Da jin haka sai sadauki Najwar ya bushe da dariyar farin ciki ya ce, "Tabbas kun yi dabara mai kyau domin sai da dan gari akan ci gari.
Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin sadauki Najwar da su Aljani Maruful Dauwaz bayan sun kece raini kowa ya san matsayinsa a fagen jarumtaka da karfin sihiri.
***
A can kogon Darul Iksina kuwa, lokacin da iskar bakin wannan karamin yaro ta sumar da Imran ya baje a kas wanwar kamar ya zama gawa sai yaron ya cika da tsananin farin ciki. Nan take shi ma ya rikide izuwa ainahin siffarsa ta aljanu mai matukar muni da ban tsoro. Kawai sai ya durfafi kan su Haiman da ke kwance da nufin ya dasa musu wawa ya cinye su.
A daidai wannan lokaci ne Lumaira da mahaifiyar Imran suka farfado daga suman da suka yi. Ai kuwa mahaifiyar Imran tana yin arba da wannan mummunan Aljani sai ta dimauce suka kama kwallah ihu. Saura bai fi taku biyu ba tsakaninsu da Aljanin suka ga an doki Aljanin yai sama ya maku da jikin bango ya fado kasa. Suna ďaga kawunansu sama, sai suka ga ashe Shaharan, Zarina da Shadira ne suka kawo musu dauki. Mummunan Aljanin na ganin su Shabaran sai ya mike tsaye ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa ya afka musu aka guntsume da azababben yaki mai tsanani a tsakaninsa su.
Sai da aka shafe sa'a tara ana bakin gumurzu tsakanin mummunan Aljanin da su Shaharan ya Zamana cewa duk su ukun Aljanin yai fata-fata da jikinsu sun sami raunika da yawa har jiri na dibarsu suna faduwa. Da kyar da sidin goshi daya daga a cikinsu ya sami nasarar saran Aljanin a tsakiyar kansa, bisa tsautsayi.
Nan take Aljanin ya yanke jiki ya fadi kasa matacce. Faduwarsa ke da wuya sai suma su Shaharan suka yanke jiki suka baje a kasa ciki mugun hali kamar ba za su yi rai ba. A sannan ne Lumaira makauniya ta fara rarrafe tana shasshafa mutanen da ke kwance a kas tana neman mijinta Haiman.
Ita kuwa mahaifiyar Imran da ta kasance gurguwa sai ita ma ta tafi izuwa inda Imran ke kwance cikin rarrafe tana kuka. Koda ta iso gare shi ta dube shi ta ga ko motsi ba ya yi sai hankalinta ya dugunzuma ta rinka jijjiga shi tana mai cewa, Tashi zaune ya kai dana, ai ba ka gaya mini cewa za ka mutu ba. Ya za a yi ka tafi ka bar ni a cikin wannan duniya?"
Haka dai ta yi ta sambatu irin na wadanda suka sami matsala a cikin kwakwalwarsu.
A wannan lokaci ne Lumaira ta iso kan mijinta Haiman, ai kuwa tana shafa fuskarsa ta shaida shi don haka sai ta dago shi zaune ta rungume shi ta fashe da kuka, ita ma ta kama sambatu.
Haka dai Lumaira da mahaifiyar Imran suka kasance a cikin halin kuka da bakin ciki har tsawon rabin sa'a amma su Shaharan ba su farfado ba.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai mahaifiyar Imran ta ji danta ya ja dogon numfashi. Nan take ta cika da tsananin farin ciki ta daďa kankame shi a kirjinta ta fara sabon kuka na murna.
Ita kuwa Lumaira da ta tabbatar da cewa mijinta Haiman ya mutu sai ta saki gawarsa ta lalubi wuka a jikinsa ta daga sama za ta caka a cikinta sai ta ji wuf an rike hannunta.
Ba wani ba þne ya rike hannunta face Gimbiya Zarina. Zarina da Lumaira suka sake fashewa da kuka tare, Zarina na cewa, "Idan babu ke babu mijinki wane ne zai bayar da labarin wannan bakar wuya da muka sha a kasarku?"
Nan dai kowa ya farfado daga suman da ya yi aka shiga dinke raunika da sa magani.
Ita kuwa Lumaira sai ta sake rungume gawar mijinta Haiman ta ci gaba da kuka. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin kowa ke nan aka kamu da tsananin tausayin Lumaira.
Lokacin da Imran ya dawo cikin haiyacinsa sosai ya yi arba da mahaifiyarsa zaune a gabansa ta kura masa idanu tana zubar da hawayen farin ciki sai ya rungume ta ya bushe da dariyar murna yana mai cewa, "Ya ke Ummina ki yi sani cewa babu wani bala'i ko wata masifa da ta isa ta raba ďa da mahaifiyarsa.
Tun a baya na gaya miki cewa na ji a jikina ba zan mutu ba kuma ke ma ba za ki mutu ba.
Komai daɗewa sai mun koma gida a raye sai dai mun yi tafiyar banza mun sha wahalar banza tun da babu biyan bukata".
Koda Imran yazo nan a zancensa sai ya fashe da kukan bakin ciki, gabadayan sauran abokan tafiyar ma sai suka fashe da matsanaicin kuka aka rasa wanda zai rarrashi wani.
Sai da suka jima a cikin wannan gida suna kuka da bakin ciki sannan suka fita daga cikinsa. Anan aka bar gawar jarumi Haiman kuma da kyar aka banɓare Lumaira daga kan gawar tana ta ihu da kuka. Komai rashin imanin mutum idan ya ga yadda Lumaira ta rinka wannan kuka bisa rabuwa a mijinta dole ne tausayinta ya kama shi, shi ma ya yi kuka.
Bayan su Shaharan sun fito daga cikin wannan gida sai suka zazzauna a gaban gidajen bakwai kowa yai shiru da tagumi har izuwa tsawon rabin sa'a dayansu bai ce uffan ba.
Daga can sai Shaharan ya dubi Shadira, Zarina, Lumaira da mahaiflyar Imran ya ce, "Ya ku abokan tafiya ku tuna cewa da can mu goma sha daya ne a cikin wannan tafiya, dokina shi ne cikon na sha biyu, amma yanzu ga shi saura mu shida kacal a cikin wannan kogo na Darul Iksina. Ban taɓa zaton zan rayu ba na kawo i yanzu.
Ni kadai ne namijin da ya rage mai sauran kuzari tunda ga Imran ma ya sami manyan raunika a jikinsa wadanda sai ya daɗe yana jinyarsu kafin ya warke ya samu karfin da zai iya ci gaba da gwagwarmaya.
Yanzu mece ce shawararku? Shin za mu ci gaba da neman ruwan albarka ne a cikin wannan kogo ko kuwa za mu zauna nan mu ci gaba da rayuwa har izuwa sa'adda wata masifar za ta afko mana ta hallakamu?"
Lokacin da Shaharan ya zo nan a zancensa sai Shadira ta dago kai ta dube shi ta ce, "Yanzu mene ne amfanin ruwan albarka a wajena da wajeu Lumaira?
Na rasa dan uwana Masnur wanda ruwan albarka zai yi wa magani. Lumaira ta rasa mijinta wanda take da burin ta ga kalar fuskarsa bayan ta warke daga cutar makanta. Yanzu ma idan ta warke ďin ai babu wanda idonta za su gani ta ji dadi sama masoyinta Haiman."
Koda jin wannan batu sai tausayi ya sake turnuke kowa aka ci gaba da zubar da hawaye, kowa ya sake yin shiru har izuwa lokaci mai dan tsawo sannan Imran ya ce, "Ni ina ganin cewa mu ci gaba da zama a nan wajen kawai har izuwa sa'adda za mu gama jinyar jikinmu domin akwai alamun cewa babu abin da zai same mu anan din face mun shiga daya daga cikin wadannan gidaje bakwai."
Nan take kowa ya nuna amincewarsa akan Wannan shawara da Imran ya kawo suka fara kokarin neman abincin da za su ci tunda ga komai han na dangin abinci da abin sha iri-iri a kogon Darul Iksina kuma wani abin mamaki shi ne babu abun da yake lalacewa daga cikin irin kayan.
Wannan shi ne abin da ya faru ga su jarumi Imran a cikin kogon Darul Iksina bayan sun rage saura su shida kacal a cikin abokan tafiyarsu su goma sha daya.
***
A CAN Birnin Hindu kuwa, lokacin da Sarki Nashmir ya shiga dakin halwar tsafinsa sai ya shiga bincike akan mashin Galilul Haras nan take ya gano abin da ya yi matukar girgiza masa hankali.
Ba komai ya gani ba face Boka Muzaffar rike da mashin Galilul Haras zaune a cikin dakin tsafinsa yana gabatar da wani aiki na tsawon kwana arba'in wanda da zarar ya sami nasarar kammala aikin to fa babu yadda za a yi a iya raba shi da mashin Galilul Haras har abada, koda kuwa an je Birnin Kisra an binne yawun barcin Sarki Nashmir din.
Koda ganin wannan al'amari sai Sarki Nashmir ya dimauce ya rasa abin da ya kamata ya yi. Shin zai yi shirin yaki ne ya tafi can inda Boka Muzaffar yake ya yake shi ya raba shi da mashin Galilul Haras ko kuwa zai tsaya ne ya ga dawowar su sadauki Najwar don ya tabbatar da cewa sun hallaka su Aljani Maruful Dauwaz?"
Nan fa Nashmir ya rasa hukuncin da ya kamata ya yanke.