Showing 57001 words to 60000 words out of 75493 words

Chapter 20 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt

Nan dai yai shiru ya faɗa kogin tunani mai zurfi har dabara ta faɗo mas.

Dabarar kuwa ita ce, kawai ya yi shiri ya je ya tunkari Boka Muzaffar ta kowanne hali ya hallaka shi ya dauko mashin Galilul Haras tunda da can ya yi iyakar kokarinsa a kan ya dauko mashin a kogon Darul Iksina ya kasa tunda yanzu ga mashin ya samu a banza kawai sai ya je ya karba.

Ko shakka Sarki Nashmir ba ya yi cewar akwai wani mahaluki da ya isa ya shigo har cikin fadarsa ya sace yarsa Gimbiya Ramlatul Siyamu saboda sanin irin tsananin yawan Dakarun, tsaron da ya tanada masu tsananin karfin dantse da karfin sihiri.

Cikin gaggawa Sarki Nashmir ya katse halwar tsafinsa ya tafi izuwa turakarsa ya yi gagarumar shigar yaki, ya debi dukkan makamansa na yaki gami da guraye da layu na tsafi sannan ya hau kan wani tsuntsun tsafinsa wanda ba rai ne da shi ba Ma'ana ba tsuntsun gaske ba ne.

Take tsuntsun ya tashi da shi sama ya durfafi, Birmin Sarki Laffaru inda gidan Boka Muzaffar yake a tsakiyar wani daji da ke bayan Birnin.

Kash! In ba don mantuwa ba da Nashmir, ya gama samun nasara!

Ba komai ne ya manta ba face bincika alamarin Sarkin yakinsa sadauki Najwar

A yanzu sarki Nashmir bai san cewa sadauki Najwar ya hada kai da su Aljani Maruful Dauwaz domin a zo a rushe mulkinsa kuma a sace Gimbiya Ramlatul Siyam. In da ya san da wannan al'amari da ba zai tafi neman mashin Galilul Haras ba.

A can Birnin Kufa kuwa, Sarki SHADDADU na tafiyar da mulki cikin tsari kamar yadda ya kamata bisa umarnin mahaifiyarsa Sharlis kuma mutanen gari suna jin dadin mulkin sosai.

Wata rana da safe Sharlis da Shaddad na zaune a fada, ana tafiyar da harkokin mulki kawai sai tunanin Sarki Laffaru ya fadowa Sharlisa a rai, man take hankalinta ya dugunzuma ainun, ta yi zumbur! Ta mike tsaye ta fice daga fadar cikin sauri. Al'amarin da ya matukar bai wa kowa mamaki ke nan domin tun da ta dora Shaddad akan karagar mulki ba ta taɓa fita ba ta bar shi shi kadai zaune a fadar sai yau.

Kai tsaye Sharlis ta wuce izuwa cikin ɗakin halwar tsafinta tana tafe tana mamakin yadda aka yi ma ta yi sakaki ba ta yi bincike ba bisa matsayin da su Sarki Laffaru ke ciki ba tun daga ranar da ta neme shi ta rasa, sai dai ta yi binciken ta gano inda suka tafi shi da Boka Muzaffar.

Lokacin da Sharlis ta isa cikin dakin tsafin sai ta turo kofar ta rufe sannan ta zauna ta dukufa tana bincike. Nan take ta ga duk abin da ya faru gà su Sarki Laffaru a cikin wadannan ragowar dazuzzuka na masifa da suka ratsa har suka isa cikin kogon Darul Iksina suka sadu da Aljani Maruful Dauwaz kawo izuwa yakinsu na karshe da su sadauki Najwar har shi Najwar din ya hada kai da su bisa cewar zai taimaka musu su je su yaki maigidansa Sarki Nashmir domin a sato Gimbiya Ramlatul siyam.

Koda gama ganin wannan al'amari sai Sharlis ta kwarara uban ihu cikin tsananin bakin ciki a lokacin da hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abin da ke ma ta dadi. daga nan kuma sai ta sake yin bincike ta ga halin da Sarki Nashmir ke ciki cewar ya taho izuwa nan Birnin Kufa domin ya riski Boka Muzaffar a gidansa don ya karbi mashin Galilul Haras.

Koda ganin wannan sabon al'amari sai Sharlis ta sake dimaucewa ta rasa abin da ya kamata ta fara yi. Shin za ta tafi can Birnin Hindu ne ko kuwa za ta soma zuwa gidan Boka Muzaffar ne da ke kusa da ita ta yake shi ta karɓe mashin Galilul Haras tun kafn Sarki Nashmir ya iso?

Ai idan ta mallaki mashin Galilul Haras tafi karfin kowa, cikin kankanin lokaci za ta iya hallaka gaba dayan makiyanta har ma ta mallaki duniyar gabadaya.

Sa'adda Sharlis ta gama aiyana hakan a zuciyarta sai ta bushe da dariya sannan ta ce, "Hakika Boka Muzaffar ba shi da wayo. Maimakon ya shiga halwar tsafi ta kwana arba'in don ya yi sihirin da zai hana kowa samun damar raba shi da mashin, kamata ya yi ya fara zuwa ya kashe duk mutanen da ya san za su yi yunkurin raba shi da mashin tukunna.

Nan take Sharlis ta yanke shawarra ta fara zuwa gidan Boka Muzaffar ta raba shi da wannan mashi sannan ta je ta hallaka su Aljani Maruful Dauwaz ta kamo Sarki Laffaru da karfin tsiya ta zo ta kulle shi a kurkuku har sai danta Shaddad ya girma ya dauki fansa a kansa.

Koda gama aiyana hakan sai ta fita daga cikin ɗakin tsafin ta ruga izuwa turakarta.

Cikin kankanin lokaci tayi gagarumar shigar yaki ta hau doki ta tafi izuwa dajin da gidan Boka Muzaffar yake tana mai falfala azababben gudu akan doki.


AL'AMARIN su sadauki Najwar kuwa, sai da suka taya su Aljani Maruful Dauwaz zaman jinya a cikin wannan tsauni har tsawon kwana goma sha hudu sannan su Aljani Maruful Dauwaz suka warke suka sami kwarin jikinsu. Nan take suka fara shirin tashi domin su tafi izuwa can fadar Sarki Nashmir.

Bayan kowa ya gama kimtsawa sai sadauki Najwar ya dubi Aljani Barukul Masnur ya ce, "Ina mai gargadinka da kada ka kuskura ka kaucewa umarnina ko kuma ka ce za ka tona mini asiri saboda ka ga yanzu za mu koma fada kana shakkar Sarki, Idan har kunne ya ji to gangar jiki ta tsira".

Koda gama fadin haka sai Najwar ya dubi Aljani Maruful Dauwaz ya ce, "Idan muna son mu sami nasarar rushe mulkin maigidana mu kawar da shi, dole ne mu yi abu uku. Abu na farko yanzu zan kama ku na daure ku na kai ku wajensa a matsayin fursunoni. Na san ba zai yi gaggawar hallaka ku ba sai dai ya sa a kulle ku a kurkuku. Mataki na biyu na shi ne, zan shiga tunanin dabarar da zan yi na sace Gimbiya Ramlatul Siyam daga turakarta a sirrance ko a dabarance sannan na shirya matakan hallaka Dakarun tsaro na fadar, yadda idan aka fara yakin za mu sami nasarar kawar da su duka a cikin kankanin lokaci.

Shi kuwa Sarki Nashmir ni ne zan tare shi mu fafata in ya so muna cikin gumuzun sai ku kawo mini dauki mu hada KARFI DA KARFE mu hallaka shi. Da zarar sauran Dakarun nasa sun ga mun ballaka shi dole ne su yi mubaya'a a gare mu su dawo karkashin ikonmu."

Sa'adda sadauki Najwar ya zo nan a zancensa sai Aljani Maruful Dauwaz ya dube shi ya ce, "Ya kai wannan sadaukin sadaukai, mun ji duk bayaninka kuma mun gamsu da shi, amma muna son mu gana a tsakaninmu idan akwai wani korafi sai mu sanar da kai".

Koda jin haka sai sadauki Najwar yai murmushi ya ce, 'Ai babu komai ina sauraronku."

Nan take Maruful Dauwaz, Rahila da Sarki Laffaru suka koma gefe daya suka fara tattaunawa Inda Aljani Maruful Dauwaz ya dubes u ya ce, "To kun ji abin da wannan sadaukin jarumi ya zo mana da shi, anya kuwa ba kwa tunanin cewa akwai. yaudara a cikin al'amarin?

Ku tuna fa cewa shi ne Sarkin yakin Sarki Nashmir tsawon shekaru, ta yaya kuke tsammanin cewa zai bijire wa Sarkinsa a yanzu?"

Koda jin wannan batu sai Rahila da Sarki Laffaru suka yi shiru kamar ba za su ce komai ba, kuma hankalinsu ya kara dugunzuma.

Daga can sai Rahila ta yi ajiyar zuciya sannan ta dubi Maruful Dauwaz ta ce, "Ai yanzu ba mu da wata huija da za mu ce ba za mu yard jarumi Najwar ba tunda inda ya so hallaka mu da tuni ya kawar da mu.

Tunda har ya kyale mu lallai akwai kamshin gaskiya a cikin zantukansa, sai dai ina shakku akan batun Gimbiya Ramlatul Siyam da ya ce shi zai san hikimar da zai yi ya sace ta. Ina ji a jikina cewar yana da wani shiri na musamman akan Gimbiya Ramlatul Siyam don haka dole ne mu sa ido a kansa.

Tabbas yanzu ba mu da wani zaбi wanda fi ya mu bi umarninsa tunda ya fi mu sanin dukkan sirrin fadar Sarki Nashmir kuma masu iya magana sun ce, 'Da dan gari akan ci gari', ko kuwa a cikinku akwai mai wata sharar daba?"

Da jin haka sai Rahila da Laffaru suka dubi juna sannan suka yi shiru. Rahila ta ce, "Ba mu da wata shawara wacce ta fi kawai mu yi kundunbala mu bi umarnin sadauki Najwar tunda al'amarin ya zama lalube a çikin duhu, ba a san inda za a dace ba."

Nan take Maruful Dauwaz ya matsa gaban sadauki Najwar ya ce, "Mun amince da dukkan umarninka sai mu tafi kawai".

Koda jin haka sai Najwar ya bushe da dariyar farin ciki. Nan take yai nuni da hannunsa izuwa ga Maruful Dauwaz, Rahila da Sarki Laffaru sai wata murtukekiyar sarkar tsafi ta kanannaɗe su su duka ta ɗaure su tamau amma wannan karon babu wuta a jikin sarkar.

Sadauki Najwar ya dubi Aljani Barukul Masnur ya ce, "Maza ka dauki su Maruful Dauwaz ka dora su a gadon bayanka sannan mu juya mu koma izuwa Birnin Hindu".

Nan take kuwa Barukul Masnur ya cika wannan umarni. Shi ma Najwar sai ya hau kan Barukul Masnur ya zauna. Nan take Barukul Masnur ya bude fuka-fukansa ya tashi sama ya kama tsala azababben gudu yana mai tunkarar Birnin Hindu.

Hakika inda ace mutum na nan a lokacin da Aljani Barukul Masnur ya dauki su Aljani Maruful Dauwaz ya tashi da su sama dole ne ya cika da tsananin mamaki ya sallamawa Ubangiji bisa wannan iko nasa, saboda shi kansa Maruful Dauwaz girman halittar jikinsa ta isa abin al'ajabi domin in daga nesa mutum ya hange shi zai yi zaton ko tsauni ne amma sai ga shi Aljani Barukul Masnur ya ninka shi girma sau uku.

Tabbas! Babu wanda ya san iyakar balittun ke wannan duniya face Allah. Hakika shi ne abin tsoro, wanda ya zamo mafi cancanta a bauta masa tunda shi ne Ya halicci kowa da komai.

Tafiyar rabin sa'a kacal Aljani Barukul Masnur ya yı ya iso fadar Sarki Nashmir. Koda isowarsa bakin kofar shiga gidan sarautar sai ya tsaya cak sakamakon ganin masu gadin kofar sun ki bude musu kofar su shiga.

Koda ganin haka sai sadauki Najwar ya dubi masu gadin ya daka musu tsawa ya ce, "Me kuke jira ne ba ku bude mana kofar mun shiga ba ko kuwa ba ku shaida mu ba ne?"

Da jin wannan tambaya sai shugaban masu gadin kofar ya dubi sadauki Najwar cikin girmamawa ya risina ya ce, 'Ya shugabana ka yi hakuri muna kan umarnin Sarki ne domin da zai fita bai gaya mana cewa za ku dawo tare da fursunoni ba kuma ka san dokar gidan nan babu wani bako da aka yarjewa shiga face da izinin Sarki".

Sa'adda sadauki Najwar ya ji cewar Sarki baya nan ya fita sai ya cika da tsananin mamaki gami da tsananin farin ciki saboda sanin cewa ya sami babbar dama da zai iya cika burinsa a saukake, amma duk da haka dole ne ya bi al'amarin a sannu.

Najwar ya dubi shugaban masu gadin kofar ya sake daka masa tsawa a karo na biyu ya ce, "Shin zan aikata wani abu ne daban ba tare da izinin Sarki ba? Maza ka sa a bude mana kofa kada fishin Sarki ya tabbata akanku idan ya dawo".

Koda jin haka sai shugaban masu gadin ya sunkui da kansa kas yai shiru kuma ya ki ya bayar da umarnin a bude kofar saboda ya fada cikin wasi-wasi da fargaba.

Koda ganin haka sai sadauki Najwar ya fusata ainun ya zare takobinsa ya dubi shugaban masu gadin kofar ya ce, "Maza ka bayar da umarnin a bude mana kofa ko yanzun nan na zare maka ruhin numfashinka da dukkan jama'ar taka".

Koda jin haka sai jikin shugaban masu gadin ya kama kyarma, ba shiri ya dubi yaran nasa ya daka musu tsawa ya ce su yi maza su bude kofar! Nan take kuwa masu gadin suka fara kokarin bude kofar.

Ita dai wannan kofa ta shiga fadar Sarki Nashmir tsawonta ya kai kamu dubu uku, haka ma fadinta. Idan aka fara bude ta sai an shafe sa'a uku ana janye ta daga sama tana shigewa cikin karkashin kasa. Wata murtukekiyar sarkar karfe ce guda biyu a jikin kofar a dama da hagunta.

Kowacce sarka guda akwai aljanu dubu goma wadanda ke rike da ita. Idan za a bude kofar aljanun da ke dama ne suke jan wannan sarka har sai sun shafe sa'a uku suna janta sannan za ta gama budewa ta kule a cikin kasa.

Haka kuma idan za a rufe kofar aljanu dubu goma da ke hagu ne za su yi ta jan sarkar har tsawon sa'a ukun sannan kofar take rufewa ta tokare da saman ginin fadar.

Kaurin wannan kofa ya kai kamu dari uku, huma an yi ta ne da zallan karfen lu'u-lu'u, babu wani makami da zai iya yiwa kofar lahani komai kkarfinsa, tsininsa da nauyinsa.

Sai da su Najwar suka yi jira har tsawon sa'a uku sannan kofar ta gama budewa suka kunna kai izuwa cikin gidan sarautar.

Da shigarsu sai Aljani Maruful Dauwaz da Rahila da Sarki Laffaru suka cika da tsananin mamaki sakamakon ganin tsananin girman gidan da kuma irin gine-ginen da ke cikinsa da kayan kawar da aka shirya tamkar aljannar duniya.

Babu abin ma da ya fi ba su mamaki face ganin yadda Aljani Baruk! Masnur ya yi ta tafiya a cikin gidan sarautar, bai iso inda aka gina kurkukun gidan ba sai da ya shafe tafiya mai nisan gaske Wacce suka yi a baya tun daga dajin Hizurul Aswad.

Nan take Aljani Barukul Masnur ya sauko kasa ta dira a bakin kofar kurkukun.
Dirarsa ke da wuya sai sadauki Najwar
Ya dubi masu gadin kurkukun ya ce, "Ga fursunonin Sarki ku shigar da su ciki a kulle su har sai na dawo karbarsu"

Nan take Wadansu jibga-jibgan aljanu wadanda sun ninka Aljani Barukul Masnur sau biyu a girma da Kwarjini suka kama su Maruful Dauwaz tamkar Shaho ya kama Dan tsako suka shige da su izuwa cikin kurkukun aka yi ta tafiya da su har sai da aka yi doguwar tafiya ana wuce mugayen matakan tsaro, sannan aka jefa su a cikin wani daki aka kulle su.

Babu abin da ya firgit su Aljani Maruful Dauwa face ganin tsananin tsaron kurkukun da kuma irin yanayin ginin da aka yi shi, komai jarumtakar mahaluki da Karfin sihirinsa bai isa ya iya guduwa daga cikin wannan kurkukun ba.

Koda suka garkame su Aljani Maruful Dauwaz a cikin wani kuntataccen ďaki sai hankalinsu ya dugunzuma domin ji suka yi kamar an jefa su a cikin rijiya gaba dubu an rufe muffin rijiyar.

Cikin tsananin takaici da nadama Rahila ta dubi Aljani Maruful Dauwaz ta ce, hakika mun yi babban kuskure da muka yarda da sadauki Najwar. Abin da na fahimta yanzu shi ne, Sadauki Najwar ba ya son ya kashe mu so yake a kawo mu gare shi a raye, wata kila don ya ďanďana mana muguwar azaba ne kafin ya hallaka mu.

ya Koda jin wannan batu sai cikin Sarki Laffaru duri ruwa ba, ya firgita ainun bai san sa'adda ya saki fitsari a wando ba. Al'amarin da ya sa Aljani Maruful Dauwaz ya tuntsure da dariya ke nan, sannan ya daka wa Laffaru tsawa ya ce, "Kai tsohon azzalumin Sarki, shin ka manta ne da irin bakin mulkin da ka yi wa mutane a baya?

Ai bai kamata a ce ka zamo matsoraci mai gudun azaba tunda babu irin kalar azabar da ba ka sa an yi wa mutane ba.

Hakika a da can kai Kura ne, amma yanzu wannan Kurar ta zama Akuya. Abin da nake so da kai shi ne ka kwantar da hankali ka. Ka sani cewa mai rai ba ya kasa motsi. Na yi muku alkawari ba za mu tozarta ba a cikin wannan kurkuku, ta kowanne hali sai na ceci rayuwarmu na fitar da mu".

Sa'adda Rahila da Sarki Laffaru suka ji wannan batu sai suka cika da tsananin mamaki. Rahila ta dubi Maruful Dauwaz ta ce, Kai kuwa ta yaya za ka iya fitar da mu daga cikin wannan mugun kurkuku mai tsananin tsaro haka?"

Da jin wannan tambaya sai Maruful Dauwaz yai murmushi ya ce, Ku zuba ido kawai ku sha kallo, nii ne fa jarumi mai sa'a da rabo wanda komai RINTSI DA TSANANI sai ya fita daga cikin kowanne bala'i.

Idan kuka yi la'akari da abubuwan da suka faru a gare mu a baya za ku gane cewa sa'ata ita ce ta kai mu ga kawowa i yanzu.

Wannan shi ne abin da ya faru ga su Aljani Maruful Dauwaz bayan an kawo su fadar Sarki Nashmir a matsayin fursunoni.

Al'amarin su sadauki Najwar kuwa, lokacin da ya ga an shigar da su Aljani Maruful Dauwaz cikin kurkuku an je an kulle su sai ya tafi cikin tsananin farin ciki bisa ganin cewa duk abubuwan da ya tsara don cika burin rayuwarsa suna tafiya daidai.

Babu abin ma da ya kara karfafa masa guiwa face da ya zo ya tarar da cewa Sarki Nashmir ba ya nan. Abin da ya fado masa a rai shi ne, dole ne yanzu ya je ya yi bincike domin ya gano inda sakri Nashmir ya tafi da kuma lokacin da zai dawo domin ya yi sauri ya gama kammala dukkan shirye- shiryensa kafin Sarki Nashmir ya dawo.

Kai tsaye sadauki Najwar ya wuce izuwa gidansa wanda ke can ɓangare daya a cikin gidan sarautar. Cikin tsananin farin ciki ya shiga gidan ya wuce izuwa dakin halwar tsafinsa ya dukufa. Nan take ya ga abin da ya matukar girgiza masa hankali ya ga cewa ashe ma idan ya cika burinsa a yau din ma tsugune ba ta kare ba, akwai gagarumar masifa a gabansa.

Ba wani abu sadauki Najwar ya gani ba a cikin madubin tsafinsa face rincaɓewar masifaffen yaki tsakanin Boka Muzaffar, Sarki Nashmir da Sharlis a can gidan Boka Muzaffar da ke Birnin Kufa a dokar daji.

Su ukun suna yakar juna ne akan abu daya. Ba wani abu bane face MASHIN

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login