Showing 21001 words to 24000 words out of 75493 words
Chapter 8 - MAZAN JIYA Littafi Na 3 True Adventure Books By MADAKIN GINI.txt
Muzaffar ya ce, "Ya kai abin dogaronmu wai shin yanzu idan muka ratsa ta cikin wadannan dazuzzuka biyu muka wuce lafiya, ya ya batun shiga cikin kogon Darul Iksina ya ke? Shin babu wata matsala da za mu fuskanta a cikinsa?" Koda boka Muzaffar ya ji wannan tambaya sai yai ajiyar zuciya sannan ya ce, "Ni kam dukkan ilimina ya tsaya iya nan ban san ma yadda za mu iya shiga cikin kogon Darul lksina ba kuma ban san irin matakan tsaron da ke cikinsa ba".
Koda jin wannan batu sai ran sarki Laffaru ya
ya dubi boka Muzaffar a fusace ya ce, "Ashe kai wawa ne ba ka san ciwon kanka ba! Yanzu kai da ba ka ma san yadda za mu shiga cikin kogon Darul Iksina ba amma ka debo mu muka sha wannan bakar wahala?"
Kafin sarki Laffaru ya gama rufe bakinsa boka Muzaffar ya daka masa tsawa wacce ta firgita shi ainun ya ji kamar an kaɗa hantar cikinsa. Boka Muzaffar ya ce, "Ai kaine babban wawa wanda rashin hangen nesansa ya jefa shi a cikin bala'i.
Ai wanda yake cikin ruwa ko bakin takobi masa kamawa zai yi. Shin ka manta da bala'in da kake ciki ne na abokiyar gabarka Sharlis? Ai da ka zauna ka jira ranar da ɗanta zai girma ya yi maka gisan gilla ya haye kan mulkinka da dukiyarka gwara ka taho neman maganin wannan barna koda kuwa ba za ka samu ba. Ka tuna cewa rai ba a bakin komai yake ba muddin akwai biyan bukata. Sai da Sharlisa ta sai da rayuwarta ta sha bakar wahala tun tana yarinya karama har ta girma sannan ta sami nasarar hawa kan tafarkin daukar fansa a kanka. Saboda me kai yanzu ba za ka sallama rayuwarka ba don ganin ka kubuta daga sharrinta?
Gabadayan abokan tafiyar nan tamu sun sallama rayuwarsu ne don cika burin zuciyoyinsu, ga shi har daya daga cikinsu ta rasa dan uwanta, dukkan burinta ya rushe, amma duk da haka ba ta fasa ci gaba da yin wannan tafiya ba. Ai ko ba komai mun ajiye abin tarihi wanda babu wani mahaluki da ya
taba yinsa, koda kuwa a iya nan tafiyarmu ta yanke. Lokacin da boka Muzaffar ya zo nan a jawabinsa sai sarki Laffaru ya shiga taitayinsa har ya bai wa Laffaru hakuri. Al'amarin da ya janyo jikin kowa ya yi sanyi ke nan.
Boka Laffaru ya ce, "Ya zama wajibi mu zauna anan har tsawon mako biyu domin mu yi jinyar jikinmu sosai kafin mu shiga daji na biyar saboda idan muka yi gangancin ci gaba da tafiya a haka, cikin kankanin lokaci mu duka zamu hallaka". Nan take kowa ya aminta da wannan shawara ta boka Muzaffar. Ba tare da ɓata lokaci ba suka kafa tantuna sannan aka ci abinci.
Bayan kowa ya huta sai suka shiga janye gawarwakin wadannan tsuntsaye suna jefa su a cikin ramin nan mai zurfi don kada su dame su da doyi, kuma kananan tsuntsaye masu cin mushe su adabbe su a wajen.
Suna gama watsa tsuntsayen a cikin ramin sai suka kunna wuta suka jefa a cikin ramin. Nan take gaba dayan gawar tsuntsayen ta kama ci da wuta.
Haka dai su Imran suka ci gaba da zama a cikin wannan daji suna jinyar kansu har tsawon mako biyu amam kullum a tsorace suke domin gani suke kamar ko yaushe ragowar wadannan tsuntsayen za su iya
kawo musu MAMAYAR BAZATO.
Ai kuwa tsuntsayen sun sha zuwa su yi shawagi a samansu amma wani Iko na Allah ko sau daya tsuntsayen ba su yi yunkurin kai musu hari ba. Daga karshe ma sai tsuntsayen suka ɓace ɓat tamkar ba su taɓa wanzuwa ba a dajin.
A ranar da kwanaki goma sha hudu suka cika ne kowa ya ji ya sami karfin jikinsa sai dai tabon raunika kawai a jikinsu. Nan fa suka yi shiri kowa ya kimtsa sannan aljani Marhabul Zaurus su duka ya tashi da su sama aka ci gaba da taifya suka durfafi daji na hudu wanda ke dauke da muggan dabbobin daji iri-iri masu matukar hadari
Da isowarsu farkon dajin sai aljani Marhabul Zaurus ya saki fuka-fukansa ya sauko kas ya tsaya cak bai motsa ba. Kowa sai ya noke ya ki saukowa daga kan aljani Marabul Zaurus aka kama kallon- kallo.
Al'amarin da ya sa boka Muzaffar ya bushe da dariya ke nan ya ce, "Me kuke tsoro kowa ya kasa sauka kasa? Ba a sami wanda ya iya amsa masa wannan tambaya ba. Koda ganin haka sai boka Muzaffar ya sauka kas sannan ya dubi gimbiya zarina ya ce, "Gaishe ki ya mai ilimin daji ki yi sani cewa yau ne ranarki domin muna bakin daji na huďu da ke dauke da mugayen dabbobi. Ke kaɗai ce za ki iya kuбutar damu a cikin wannan daji don haka sai ki sauko ki yi mana jagora har mu isa karshen dajin".
Koda jin wannan batu sai Zarina ta yunkura za ta sauko kas. Cikin hanzari sarkin Farisa ya ruko ta dube ta cikin alamun firgici da tashin hankali a lokacin da idanunsa suka ciko da kwallah ya ce, "Ya ke 'yar uwata ki yi sani cewa a halin yanzu zuciyata tana bugawa da karfi kuma ina ji a jikina cewa in dai muka shiga cikin wannan daji karshen zamanmu tare ya zo. Ni kam na hakura da wannan buri da ke gabanmu saboda haka mu yanke wannan tafiya tamu daga nan mu zauna anan mu jira mu ga abin da hali zai yi ko abokan tafiya za su isa can kogon Darul Iksina su dawo lafiya. Idan kuma ba su dawo ba sai mu juya da baya mu koma kasarmu. Gwara mu koma gida mu ci gaba da rayuwarmu a cikin mulkinmu muna ganin juna ba tare da mun cika burinmu ba".
Sa'adda sarkin Farisa ya zo nan a zancensa sai Zarina ta kamu da tsananin tausayinsa har hawaye ya zubo ma ta. Nan take ta rungume shi tana mai cewa, "Ya kai dan uwana ka kwantar da hankalinka ka sani cewa babu abin da zai same ka muddin ina tare da kai, duk tsautsayin da zai taɓa ka sai dai bayan ya taba ni. Ka tuna cewa yanzu fa saura daji daya jal a gabanmu mu isa kogon Darul Iksina bayan mun gama da wannan wanda ke gabanmu. Bai kamata a ce wannan wahala da muka sha ba a baya ta zama ta banza ba dama masu magana sun ce 'Idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi' Amma kuma ai bayan wuya sai dadi."
Ya yin da Zarina ta zo nan a zancenta sai jikin sarkin Farisa ya yi sanyi. Haka dai ya sauko daga kan aljani Marhabul Zaurus ba a son ransa ba. Yana sauka sai Zarina ta goya shi a bayanta ta ɗaure shi tamau sannan ta matsa gaba tayi taku bakwai sai ta waigo ta dubi su Imran ta ce, "A nan za ku tsaya ne ko kuwa za ku biyo ni?"
Da jin haka sai gaba dayansu suka sauko da sauri daga kan aljani Marhabul Zaurus sannan gimbiya Lahira, boka Muzaffar da sarki Laffaru suka bi su a baya aka nausa cikin wannan daji na biyar. Zarina na kan gaba tana dube-dube da waige-waige har suka shafe dan dogon lokaci ba su gamu da komai ba, kuma ba su ji sautin komai ba a cikin dajian tamkar babu wani abu mai rai a cikinsa.
Kwatsam! Sai suka iso wata mararraba wacce ke dauke da alamar hanyoyi guda bakwai. Da zuwansu wannan wuri sai Zarina ta tsaya cak ta zaro takobinta.
Koda ganin haka sai kowa ma ya gyara makaminsa. Zarina ta dubi kowacce hanya daga cikin guda bakwan ta yi nazarinsu sosai amma ba ta ga sawun wata dabba ba a cikinsu. Ta tsugunna ta dora kunnenta a kan kasa, nan ma sai ta ji shiru. Kawai sai ta mike tsaye ta dubi abokan tafiya cikin alamun karayar zuciya ta ce, "Ya ku abokan tafiya ku yi sani cewa na kasa gano ainihin halin da wannan daji ke ciki a yanzu domin babu wata alama ta wata dabba a cikinsa. Tabbas idan ma akwai dabbobi a cikin wannan daji sun kasance masu wayon gaske, kuma ba mamaki sun kasance masu yawo a sama, wato fuka-fukai ne da su domin babu alamar sawun kafafunsu akan kasa. Saboda haka yanzu ba mu da wani zabi wanda yafi mu yi kundunbala mu afka cikin dajin ta cikin daya daga cikin wadannan hanyoyi bakwai, in yaso idan ma mun haɗu da wata dabbar a gaba sai mu yake ta".
Koda gama fadin haka sai Zarina ta kunna kai izuwa cikin dajin ta bi hanyar farko daga cikin bakwan, suma suka rufa ma ta baya.
Nan fa suka yi ta tafiya Zarina ta raba hankalinta biyu ya zamana cewa tana kallon kasa ko za ta ga sawun wata dabba, kuma tana kallon saman bishiyoyi ko za ta ji wani motsi, amma shiru kamar an aiki bawa garinsu.
Wani babban abin tashin hankali shi ne, suna fara nisa a cikin dajin suka tsinci kansu a cikin wadansu irin dogayen bishiyoyi masu yawa har gaba daya dajin ya yi dan duhu. Tabbas wata muguwar dabbar za ta iya ɓuya a cikin wadannan duhuwoyi na saman bishiyoyin.
Haka dai suka ci gaba da tafiya har tsawon rabin sa'a amma ba su hadu da komai ba. Kwatsam Sai Zarina ta ga wani katon sawu na Gwaggon Biri. Saboda girman sawun har wajen rami ya yi wanda su duka suka shige cikin ramin suka tsaitsaya. Kowa ya rika kallon sawun cikin tsananin mamaki.
Cikin firgici boka Muzaffar ya dubi Zarina ya ce, "Ya ke masaniyar daji, wannan sawun wacce irin dabba ce haka?".
Zarina ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ba sawun komai ba ne face na gwaggon biri".
Koda jin haka sai kowa ya firgita aka zazzaro idanu ana mamaki. Muzaffar ya ce, "Yanzu dama akwai biri mai tsananin girma kamar haka?"
Zarina ta ce, "Ai a duniya gaba daya kaf irin wadannan birirrika guda uku ne kacal. Daya yana wannan nahiya. Na biyun yana can nahiyar Bimin Sin. Shi kuma na ukun yana can nahiyar Birnin Hindu.
Su ne birirrika guda uku wadanda babu kamarsu a duniya. tabbas idan muka yi gaba da gaba da wannan biri dayanmu ba zai tsira da rayuwarsa ba kuma daga yanzu zuwa koda yaushe za mu iya yin arba da shi. Ni dai a tawa shawarar zai fi kyau mu koma da baya mu sauya wata hanyar".
Sa'adda sauran abokan tafiya suka ji wannan batu sai hankalin kowa ya dugunzuma aka yi shiru ana tunani. Daga can sai boka Muzaffar ya ce, "Ya ku abokan tafiya kun sani cewa a cikinmu nan gaba daya babu wanda ya san sirrin daji da sirrin mugayen dabbobin dake cikinsa sama da jaruma Zarina, saboda haka dole ne mu yi amfani da dukkan shawarar da ta ba mu. Ina ganin cewa zai fi kyau mu koma da baya mu sauya hanya kamar yadda ta shawarce mu". Da jin haka sai kowa ya aminta, ba a sami wanda ya yi gardama ba. Nan take suka dunguma suka juya da baya suka koma izuwa farkon hanyar inda ta rarraba izuwa kaso bakwai.
Da zuwa sai suka tsaya suna shawarar hanyar da ya kamata su bi daga cikin bakwan, aka rasa wanda zai zaɓi hanyar. Kawai sai boka Muzaffar ya dubi Zarina ya ce, "Ya ke wannan jaruma ki yi sani ccwa ke ce shugabarmu a cikin wannan tafiya don haka ke ce za ki zaɓar mana hanyar da ya kamata mu bi". Sa'adda Zarina ta ji haka sai ta yi ajiyar zuciya sannan ta cc, "Zan zaɓi hanya daya daga cikin ragowar guda shidan da suka rage mana. Amma fa ku sani cewa duk hanyar da muka bi babu komawa da baya komai bala'in da muka gani a cikinta".
Koda jin wannan batu sai kowa yai shiru aka rasa wanda zai zo da jayayya. Kawai sai sadauki Haiman ya ce, Mun yarda da wannan sharadi naki. Koda jin haka sai gimbiya Zarina ta nufi wata hanya da ke tsakiyar hanyoyi shidan da suka rage ta durfafi cikinta kai tsaye ko waige ba ta yi.
Sadauki Haiman wanda ke goye da matarsa Lumaira shi ne ya fara bin bayanta sannan Imran goye da mahaifiyarsa, sai Shaharan sannan gimbiya Rahila, boka Muzaffar, sarki Laffaru. Aljani Marhabul Zaurus ne a karshe dauke da dokin Shabaran wanda ko yaushe a durkushe yake bisa kafafunsa ko mikewa baya iya yi sakamakon rashin lafiyarsa.
Haka dai waɗannan jarumai suka wanzu suna tafiya a cikin wannan daji har tsawon sa'a guda ba su ga koami ba kuma ba su ji motsin komai ba.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai suka ji wani irin gagarumin gurnani wanda ba su taɓa jin irinsa ba a rayuwarsu. Gurnanin ya cika dajin gaba daya kuma suka rasa ta inda gurnanin ya fito. Lokaci guda su duka suka dimauce babu wanda jikinsa bai kama kyarma ba, hatta Zarina kuwa wacce ke kan gaba tana yi musu jagora.
Nan fa suka ji kamar su juya da baya su ranta ana kare. Har sarki Laffaru da boka Muzaffar sun yunkura za su juya da baya sai Zarina ta daka masu tsawa ta ce, "Duk wanda yake son ya juya da baya sai ya yake ni ya kawar da ni tukunna. Ai mun yi sharadi da ku kafin mu shigo wannan dajin, saboda haka babu gudu kuma babu ja da baya, ko mutuwa ce sai dai mu tunkare ta".
Gama fadin hakan ke da wuya sai Zarina ta daga takobinta sama ta ci gaba da tafiya izuwa gaba. Babu shiri kowa ya bi bayanta cikin alamun tsananin tsoro.
Lokacin da Zarina tayi taku bakwai kacal sai tsulum! Suka ga wani murjejen Zaki ya dako tsalle daga can nesa bisa wani tsauni ya duro kasa daf da su. Saboda nauyin Zakin yana dira sai kasa ta yi girgiza, gaba daya dajin ya yi tambal-tambal kamar zai rufta kasa.
Ko a tarihi ko a labarai su boka Muzaffar ba su taɓa jin zaki mai girma ba kamar wannan, domin sai an cure manyan giwaye guda uku a waje guda sannan za su kai girman wannan Zaki.
Da ni Maiboko da ku makaranta, bari mu jira zuwa gobe domin mu ga wane ne zai rasa rayuwarsa a cikin wannan dajin domin kuwa tabbas! Kwarjinin wannan dajin ya ci a ce an rasa rayuka a cikinsa.
Zakin ya wangame bakinsa mai kama da bakin rijiya ya yi wani sabon gurnani Karfin gurnanin ya sa bishiyoyi suka dinga kakkaryewa suna zubewa kasa. Duwatsu suka kama mirginowa suna karo da junansu suna farfashewa. Ba shiri kowa ya tsugunna ya toshe kunnuwansa biyu don gudun kada su kurmance.
Sai da gurnanin ya lafa sannan su Zarina suka ďago da kawunansu. Bisa mamaki, sai suka nemi wannan Zaki sama ko kasa suka rasa kamar an yi ruwan sama an dauke dif.
Al'amarin da ya matukar dugunzuma hankalinsu kenan, suka rasa abin da ke musu dadi duniya, don sun tabbatar da cewa Zakin buya ya yi domin ya kawo musu MAMAYAR BAZATO. Cikin hanzari gabadayansu suka taru a waje daya kowannensu ya daga makaminsa sama yana kalle-kalle da waige-waige kawai jira suke yi su ga ta inda Zakin zai 6ullo musu.
A wannan lokaci ne Zarina ta ga cewa ashe Lumaira mahaifiyar Imran da sarkin Farisa wanda ke goye a bayanta tuni sun suma saboda tsananin firgitar da suka yi bisa ganin wannan katon Zaki. Suna cikin wannan hali ne Zakin ya yi fitar burgu daga cikin karkashin kasa ya dako tsalle a sama izuwa kansu kai ka ce cillo shi aka yi daga cikin baka. Cikin bakin zafin nama gabadaya jaruman suka daka tsalle sama domin su tare shi da nufin su sassara shi.
Kash! Rashin sani ya fi dare duhu. Inda wadannan jaurmai sun san abin da zai biyo baya da ba su yi wannan ganganci ba.
Koda Zakin ya hadu da su a sama sai ya kai wa dukkaninsu hari da kafafunsa na gaba da na baya, da kuma bakinsa a wangame. Cikin sa'a kauwa ya cisge hannun Haiman na dama da hannun Shaharan na Thagu. Jarumi Imran kuwa akan cinyarsa ya lafta masa wawan sara sai ga naman cinyar ya bude yana lage- lage kamar an farke cikin dabba.
Sarki Laffaru kuwa a gadon bayansa ya tsira masa farcen, wajen ya yi rami. Boka Muzaffar kuwa a gefen cikinsa ya soke shi, jini yai tsartuwa. Shadira kuwa kanta ne yai karo da kan Zakin jini yai tsartuwa daga cikin hancinta da bakinta, tun a saman ta suma. Zarina ce kadai Zakin bai yiwa rauni ba amma takobinta ta rabe gida buyu sa'adda ta dankarawa Zakin sara a kuiɓin cikinsa. Lokaci guda jaruman duka suka rikito kasa suka baje a kas sumammu.
Zarina ce kadai a tsaye bisa kafafunta jikinta na kyarma saboda tsananin razana bisa ganin abin da ya faru ga sauran abokan tafiyarta. Ita kuwa gimbiya Rahila Zakin ya mangare ta ta je ta buga kanta akan wani dutse, kan nata ya dare jini na kwarara ko motsi ba ta yi ba babu alamar akwai rai a jikinta.
Nan fa Zarina da ke goye da dan uwanta Sarkin Farisa ta fara ja da baya-baya a lokacin da Zakin ya tsaya a gabanta suna kallon-kallo.
Shi dai Zakin tsananin mamaki ne ya sa shi ya kasa afka mata, domin a iya tsawon wanzuwarsa a cikin wannan daji komai yawan rudnunar mayaka in dai ya dako wannan tsalle ya dira akansu to fa babu wanda zai tsira da rayuwarsa. Amma yau ga shi wata hatsabibiyar bil'adama guda daya ta tsallake wannan mugun hari nasa.
Zarinata ci gaba da ja da baya yana tunanin dabarar da za ta yi ta tsira daga sharri wannan Zaki don tabbas kwaf daya zai yi mata ta mutu.
Abu na biyu kuma da ya kara dugunzuma hankalinta shi no, ta san ba za ta taɓa iya tsere masa ba da karfin gudu sai dai ta yi ta 'yan zille-zille da guje-guje. Kuma a hakan da zarar ta gaji zai banke ta kuma kasancewar tana dauke da goyon dan uwanta ta san cewa da wuri za ta gaji kuma ba za ta iya yin gudu mai yawa ba.
Kawai sai ta yanke shawarra ta fara guje-gujen. ta cikin bishiyoyi tana zulle-zulle wata kila ta shiga