Showing 12001 words to 15000 words out of 124668 words
Chapter 5 - So Da Buri Book 1 Hausa Novels by Humaira Bulama.txt
kira har ya zo ya daina shima.
Abba yana zaune Sudais yanata zuba masa surutu ya ji k’arar wayarshi,zaro ta yayi daga aljihun gaban rigarshi ya kalla screen d’in, k’ara kalla yayi ya d’ab bud’e idonshi…ganin da gaske ne yasa yayi saurin d’auka had’e da toshe wa Sudais baki
“Assa...”
Kafin ya k’arasa sallamar ya ji ance
“Ina falona,ka sameni yanzu”
Kit!! Ya ji an kashe wayar.
Mik’ewa yayi a take sai dai da kyar k’afafuwansa suka iya d’aukar sa saboda sanyi da rawar da suke yi dama kuma ga yanayin rashin lafiyar da yake ciki.
Ajiyar zuciya ya sauk’e,ya tattaro dukkanin kuzarinsa sannan ya fara tafiya a hankali domin amsa kiran mahaifin nashi.
Gaban Ummi ne ya fara dukan uku uku gashi Mom bata kusa…dukda sunada mafitar abinda za su fad’a amman hakan bai hanata jin tsoro ba,da kyar ta samu ta saisaita kanta gudun kar granpa ya fahimci wani abu,dukda ta san shi ba mutum ba ne mai zurfafa bincike iyakar abinda akai akan idanunsa da shi yake aiki sannan bashi da time d’in bibiyar abinda bai shafeshi sosai ba above all ya yarda da Ummi yana ji da ita sosai ba ya son abinda zai b’ata mata rai ita kad’ai ce in abu ya shafeta yake sawa ya sauk’o daga dokin zuciya…….tana cikin wannan tunanin suka ji sallamar Abba.
Granpa ne ya amsa sannan yace”k’araso ciki.”
Shigowa ya yi, sannan ya k’araso inda ya ga Ummi a zaune ya nemi guri ya shima ya zauna a d’an gefenta kad’an. “Barka da yamma”
shine abinda Abba yace da granpa, kanshi na kallon k’asa.
Juyowa granpa ya yi ya kalleshi sannan yace
“Ai ban yi tunanin har yanzu Ina da darajar da zaka gaidani ba.”
Bai jira jin abinda zai ce masa ba ya d’aura
“Bara in baka wani gajeran labari,dukda na san ka sani amman bara in sake maimaita maka.”
Mik’ewa ya yi yana dogara sandarsa ya koma wajen da su Ummin suka shigo suka sameshi d’azu ya tsaya yana kallon waje,a hankali ya fara magana...........
…….
“Asalina d’an k’asar Chad ne, mahaifin mahaifiyarmu ma haka,saidai mahaifiyarta ce ta fito daga yankin Niger,Agadaz.
Mu biyu iyayen mu suka haifa a duniyar nan,da ni da d’an uwana…gudun hijira ya sanya muka baro k’asarmu ta haihuwa,domin a lokacin har kakanninmu sai da aka kashe da kyar muka tsira,kasancewar Fulani bamu da yawa a yankin ya sanya aka yi galaba akanmu.
A lokacin inada shekaru tara a duniya d’an uwana kuma yanada 11,tun a hanya na lura mahaifin mu bashi da lafiya,da na tambaye shi sai yace mini gajiyar tafiya ne..
Yanayin gudun hijira ba abu bane mai sauk’i don ko ruwan da mutum zai sha ma aikine.
Mahaifin mu ya zab’a mu bi ta Agadaz domin mu duba ko zamu had’u da dangin mahaifiyar mamana ko zasu taimaka mana akan mu tafi garin da bamu san kowa ba. Mahaifiyarmu ta so yin tirjiya akan gara mu bi ragowar mutanen rugarmu waenda suka yi saura, saboda ta san a wannan lokacin danginta kowa yayi nashi wurin sannan y’an uwanta idan ma za ta samu yanzu mutun d’aya ce, wadda take aure a chan, don mahaifiyar tata su uku aka haifa a gidansu kuma itace auta,Babbar yayyarsu a ghana take aure.
K’in yarda da zancenta da mahaifinmu ya yi ne ya sanya
muka nufi Agadaz
Amma sai muka yi rashin sa’a muna zuwa aka tabbatar mana ciwon k’afa ya kamata an kaita Yemen neman magani.
Da kyar wani makwafcinsu ya bamu gurin kwana da abinci mukai wanka da safe muka nufi marad’i,don Yemen akwai nisa sannan babu ko sisi a wajenmu, dayake mahaifinmu ya tab’a zuwa daura ya sanya shi cewa mu zo daura ko marad’i inyaso idan ya d’an samu aiki yayi ya tara kud’i daga baya sai mu tafi Yemen d’in mu dubota.
kasancewar hanyar Sahara ce ko ina,yasanya muka wahala babu ruwa babu abinci kowannenmu idan ka kalla
a wahale yake
Shiyasa da zaran mahaifinmu ya nemo d’an abinci ko abun sha sai ya bamu mu ci yace mana shi ya ci a hanya saboda yana gudun kar wani abun ya samemu dan a ganinsa laifinshi ne saboda babu yadda mahaifiyar mu batayi da shi ba akan mu bi tawagar y’an hijira mu gudu tare amman ya k’i.
A lokacin naga amfanin ilimi domin da muka k’arasa marad’i babu wanda yake jin yarenmu, sannan muma bama jin nasu, sannan bama jin turanci ballantana mu yi communicating da su.
Hakanan muka kwana a y’ar kasuwarsu da kyar mai k’osai ta bamu sadaka mukaci,da safe muka samu wanda zaije daura ya tausayamana muka bishi a motar katakon shi (kiya kiya ).
Ga wahala ga yunwa ga kuma yin tafiya mai nisa a kiya kiya a wannan lokacin ba dadi .
Tun kafin mu k’arasa mahaifinmu ya fara jijjiga idanunsa suka k’akk’afe, muna isa garin aka taimaka mana muka yi asibiti da shi, ba a jimaba Allah ya karb’i ransa ta sanadin rashin abinci likitoci suka tabbatar mana da cewa ya shiga hypoglycemia ne, sannan bai samu taimakon gaggawa akan lokaci ba.
A lokacin bamu san kowa ba, ganin haka yasa Likitan ya nemo mutane aka sallaci mahaifin mu aka kaishi gidanshi na gaskiya, bayan ya tabbatar da mu Musulmai ne.
Bayan an dawo daga mak’abarta lokacin tafiyar sa gida yayi still ya ga bamu da niyyar tashi, dan haka ya zo ya sami Mamanmu yace mata idan ba damuwa mu bishi gidanshi, kafin a san ya za a yi.
Muna isa gidan kuwa matar sa tace ba za ta rik’e mutum uku ba sai dai a kaimu gidan marayu da ni da d’an uwana In yaso ita mamanmu ta dinga mata wanke wanke da shara.
A lokacin rigima ce ta b’arke tsakanin Likitan nan da matarshi, domin ita tace ‘ba za ta rik’e tsintacciyar mage ba ai ya ma yi sa’a da ta yarda za ra d’auki Maman namu aiki’
Shi kuma ya dage akan sai mun zauna ai daman ba yau ta saba yi mishi irin haka ba!
Taya yana miji amman ita ace ita za ta dinga zartar da hukunci.
Rigima suka hau yi sosai,har ta kai ya fara ik’irarin rabuwa da ita.
Ganin hakan ya sanya Maman mu tace”Ta yarda a kaimu gidan marayun In yaso idan ta yi aikin ko na wata hud’u ne ta d’an tara kud’i sai ta fara sana ‘a taje ta d’auko mu ta kama haya.’
Hakan kuwa aka yi muna kuka muna komai aka kaimu gidan marayu….
Maman mu mace ce da baka iya gane tak’memen abun da yake cikin zuciyar ta amman zan iya cewa a wannan lokacin na ga tsananin tashin hankali da k’unci a fuskarta domin kuwa itama harda kukanta.
Every weekend take zuwa ta dubo mu
A lokacin ne kuma yayana duk da k’arancin shekarun shi ya dage wajen koyan sana‘a, dan zan iya cewa duk wata sana ar da ake koyarwa a gidan marayun nan babu wadda bai iya ba,ba ya isheshen bacci kullum cikin aiki,idan nace mishi ya huta yakan ce mini ‘ba dan kanshi yakeyi ba,saboda ni da mama yakeso ya yi sana’a ya tara kud’i ni da shi mu koma makaranta sannan ya siya mana gida.’
A kullum maganarshi kenan.
Tun muna Yara mun kasance masu tsananin k’aunar juna,soyayyar da yayana yake yi mini ba kad’an bace ba,ba ya son ya ga rai na a b’ace duk da kuwa ni d’in na kasance Miskili ne amman in dai ina tare da shi sai ya san yadda yasa na ware sosai saboda baya bari na ma har sai ya ga Ina dariya.
Kamar yadda mahaifinmu ya dinga sacrifice yana bamu abincin da ya samu(lokacin gudun hijira)haka shima ya dinga yi mini a gidan marayu,gashi ya hanani aikin komai,shi yake had’awa nawa da nashi ya yi,zan iya cewa ni kam ban san wahalar gidan marayu ba kwata kwata.
Mun shafe wata uku a gidan Marayu muna neman shiga na hud’u.
Ranar wata lahadi muka tashi mukai wanka da sassafe muna jiran mahaifiyarmu,kasancewar ranar zuwanta kenan amman har yamma bata iso ba,sai da daddare wannan Likita ya xo ya tura aka kiramu. Muna fitowa da ya had’a idanu da mu kawai sai naga ya fashe da kuka,da sauri muka k’araso gabanshi muka hau tambayarshi amman sai bai amsa mana ba kawai ya cewa shugaban wajen yayi checking namu out zai tafi da mu.
Sai da muka je gidan nasa muka gane dalilin kukanshi…ciwon zuciya mahaifiyarmu take fama da shi tun watanni uku da suka shud’e tanata nuk’u nuk’u babu wanda ta fad’awa yau kuma da safe ta yanke jiki ta fad’i jininta yai high sosai,babu irin taimakon da basu bata ba amman rai yayi halinshi.
A ranar kam mun sha kuka iya kuka hatta wannan matar Likita sai da ta tausaya mana.
A ranar sadakar uku ne kuma ta tada balli tace ‘sai dai mijin ta ya nemi wani wajen ko ya kama mana haya mu koma
dan ba zai barta da Yara maza a gida ba bayan ita mata ne nata kuma k’anana, ai mu maza ne ko aikin k’arfi ne za mu iya mu samu mu rik’e kanmu.’
Hakan kuwa akayi
Sai dai kud’in da mahaifiyarmu ta tara bai isa kama haya ba balle a had’a da Sana’a. Shawara Likita suka yi da yayana aka kama haya shima sai da ya cika mana.
Gefen gidan wata tsohuwa da y’ar jikarta aka kama mana haya, sannan Likitan ya bata amanar mu.
Kasancewar Yayana ya iya sana a kala kala ya sanya yake fita sana a,Allah kuwa ya sanya mishi albarka domin duk abinda yayi ko ya tab’a sai ka ga bud’u da karb’uwa ta koina dukda kuwa k’arancin shekarunshi..hakan ya sanya masu shago suka rik’esa kowa yanaso ya yi aiki da shi.
Acikin shekaru biyar yaya ya bud’e shagon d’inkin sa,da wajen had’a hula da takalma, da turarurruka,sannan ya koma makaranta nima yasaka ni a makaranta,kuma cikin ikon Allah har gidan wannan y’ar tsohuwa shi yake ciyarwa,domin ta zame mana kamar uwa jikarta kuma y’ar uwa Likita kuma ya kan zo duk wata ya duba mu,haka nan muka zama kamar family.
A lokacin da shekaru na suka ja,naje na samu yayana da batun inaso inyi aure don a lokacin ina matuk’ar k’aunar mahaifiyarku, kuma babanta har ya fara shirin maganar zai bata wani d’an uwanta za ai musu aure, to a wannan lokacin shima d’an uwana Ashe yanada tashi budurwa harya gama hada kudin lefe da na siyan gida da komai amman ganin yadda hankali na ya tashi yasanya ya bani kudin lefen muka je ya siya mini gida da duk wani abun da za a buk’ata, sannan ya bani wajen had’a turarenshi a matsayin kyauta yace in kula da Iyalina da shi.
Both mahaifiyar ku da budurwar da yayana yake nema, y’ay’an masu kud’i ne neman auren su ba abu ne mai sauk’i ba hakan ya sanya da yayana ya nemi da a k’ara mishi lokaci ya sake shiryawa, mahaifin ta ya k’i amincewa barema da ya ji k’aninsa zai
yi aure sai ya yi tunanin raina musu hankali yake son yi…
haka nan yanaji yana gani aka aurar da ita kuma ya b’oye mini don ya san ba zan bari ba shi kuma ya fi son ya fi son farin cikina akan nashi.
Shi ya wuce mini gaba ya tabbatar na auri Maijiddah , Likita ya yi mini wakili.
Bayan nan muka ci gaba da karatu da business gadan gadan,Yaya iyakacinshi masters amman ni har PHD sai da ya tabbatar nayi, ya rik’e gaba d’aya companies d’in harda na turare na daya bani wanda a lokacin ya bunk’asa , yace zai iya inje inyi karatun nawa.
Yaya bai yi aure ba,sai bayan shekaru goma mutane sunata gulmace gulmace amman ya toshe kunnuwanshi,saboda shi tunda aka aurar da wacce yake so aure ya fice mishi akai.
Sai da na saka baki ni da Likita tukun ya yarda ya yi auren
a lokacin har kai an Haifa.
Matar Likita wadda ta dinga m korarmu a gidanta itace ta kawo d’aya a cikin y’ay’anta tace ‘ta bashi ya aura’.
Don a lokacin Yaya yayi kud’i na ban mamaki,sai kuma akayi dace ya yarda don yana ganin ta ta kwanta mishi,sannan
kuma ko da ace bayaso yaci ace ya karb’i y’ar Likita a matsayin mata ko dan halaccin ubanta.
Tunda na yi aure nake burin in haifi y’a mace, sannan ina son in saka mata sunan Mahaifiyarmu, amman Allah bai bani ba, da kai da Yusuf da Yahaya Allah ya bani.
Bayan auren Yaya kuwa da shekara d’aya aka haifi Zainab(Ummi)
Da ni da Yaya ban san wa ya fi wani sonta ba gashi sunan mahaifiyarmu gareta.
A lokacin ne kuma Yaya suka yi wani accident wanda akai mishi aiki aka tabbatar mana magudanar kwayayan haihuwanshi sun sami matsala,ba zai sake haihuwa ba! Mun girgiza sosai amman kasancewar mu masu tawakkali ne sai muka mik’awa Ubangiji lamuranmu muka rungumi k’addara.
Abu d’aya muka sa a gaba shine faranta ran Ummi,Yaya ya tab’a gaya mini yana neman kud’ine saboda faranta raina da na mahaifiyarmu amman hakan bata faruba a b’angaren mahaifiyarmu domin mun rasa ta tun kafin ta ji dad’in da muka so bata,shiyasa yayi alk’awarin d’aura dukkan wani gata na duniyar nan akan tilon y’ar sa tunda takwarar ta ce,ya kance idan ya ga Ummi tana dariya gani yake yi kamar mahaifiyarmu ya sanya farinciki, domin kusan halinsu d’aya dan itama Ummi tun tana da shekaru biyu da y’an watanni muka fahimci tanada nuk’u nuk’u da b’oye abu a rai.
Shiyasa ya zama har y’ar rige rige muke ni da Yaya wajen cika mata burinta,muddin ta furta.
Shekararta biyar a duniya Yaya da Likita suka tafi Abuja,a hanyar su ta dawowa suka yi wani mummunan hatsari!! Likita tun a lokacin ya cika sai da aka kawoshi emergency yanata cewa yana son ganina… a lokacin Ina office aka sanar mini ana san ganina a asibiti tun a lokacin gabana ya fara fad’uwa,Ina zuwa kuwa a reception aka ce
mini ai y’an uwanane suka yi hatsari d’ayan ya rasu d’ayan kuma yana wanchan d’akin aka min nuni da d’akin da Yayana yake ciki…
A gigice na shiga inda yake,ina ganinshi cikin jini nai kanshi da gudu na rik’esa ina kuka.
Dukda halin da yake ciki bai hanashi lallashi ba,sai da ya ga na yi shiru tukunnan ya kamo hannuna duka biyu yana d’an tari da nishi da kyar...
Kalmarshi ta k’arshe itace
Dan Allah dan Annabi ka kula mini da Zainab ka bata duk wani farin cikin da kake da iko ga amanarta nan na bar maka
sannan ya yi kalmar shahada daganan na ji jikinshi ya sake idanunsa suna kallon sama.
A lokacin na yi kuka mai yawa dan na rasa rabin jiki na sannan bani da kowa bani da wani bani da elder mai kula da ni.
Maraicin sai ya dawo mini sabo fil.”
……
Hawaye granpa ya share ya gyara tsayuwar shi yace
“Ko mutuwar iyayena ban ji ta ba kamar yadda na ji ta Yaya..na yi alk’awarin faranta mishi ko bayan ranshi ko da kuwa ace hakan zai sanya in karya tawa k’aidar.
Ga matarka nan,ko ka san tana d’auke da ciwon zuciya???”
Ya yi maganar tare da juyowa yana kallon Abba wanda ya juya a razane yana kallon Ummi da kamar mamaki a fuskar shi.
Juyawa granpa ya yi ya ci gaba da cewa
“U won Yakubu, ka yi amfani da weakness d’ina and ka ci nasara a kaina! This time around,zan iya yafe maka laifin da ka yi mini tunda na ga alamar so kake ka dawo da baya yanzu.
Komai ya wuce!!sannan ka rushe maganar tashinka daga estate d’innan babu ita.
Abu d’aya zuwa biyu zan baka umarni shine
“Ka maida matarka yanzunnan, sannan ka kaita asibiti ga katin nan,Dr yana chan yana jiranku.
And
Kamar yadda na fad’a maka a baya,babu kai ba Maryam,amma in dai har ka shiryawa tsinuwa ta to bismillah
Ka je ka bibiyi rayuwarta....
SHARE PLS.
BULAMA✍️
So da Buri
Free Book
06
Shiru Abba ya yi yana so ya gano inda kalmar ‘ka maida ita!’ Ta nufa,dan bai gane ba.
Fusata granpa ya yi jin yadda yayi masa shiru
Dan haka ya daka mishi tsawa ta hanyar cewa
“Ko baka ji na ne Abba!!!”
Tuni Abba ya hau cewa “to granpa in shaa Allah..yanzu yanzu….”
Duk ya bi ya rikice.
Ganin hakan ya sanya Ummi share fuskarta da ta jik’e da hawaye ta faki idon granpa ganin ba su yake kallo ba ya sanya ta d’an tab’a Abba tace
“Ka taso mu tafi,yake nufi.”
Kallon ta Abba ya yi sannan ya mik’e ya ce “taso mu tafi.”
Dan ba ya so ya fara zazzage mata ta cikinsa a gaban granpa. Har ya juya sai kuma ya dawo ya zo ta gaban granpa ya tsugunna yace
“Dan Allah ka yi hak’uri na san na yi maka laifi, ka yafe mini, in shaa Allah duk abinda kace inyi zan yi daga yau ba zan sake k’etare umarnin ka ba.”
Kusan 1 minute tukunna granpa ya juyo ya kalleshi sannan yace “Yafe maka da na yi ba wai yana nufin na manta da abunda ka yi bane,na yafe maka ne saboda ni kaina in samu peace of mind na zama a same environment da kai tunda ka zame mini dole,
it’s all for Ummi’s sake, so idan kanada hankali do your best to keep her happy hakan ne zai sa ka gujewa b’acin rai na, ka samu mu rabu lfy.
Yana gama fad’in haka ya juya ya fara dogara sandarshi
har ya kai k’ofar d’akin shi ya juyo yace mata idan bai yi abunda nace ba, ko kuma ya yi trying anything stupid ki zo ki sameni.”
Daga nan ya shige ya barsu a palon.
Kallon ta kawai Abba yake yi, ji yake kamar ya shak’e ta ya huta, gashi ya yiwa granpa alk’awari…idan ya fahimci kalmar granpa ta ‘ka maida ita’
Tabbas Yaji Ummi ta yo
Ta karkad’e zani ta kawo k’arar sa kenan. Sannan
for her sake ne ma aka hak’ura zai ci gaba da zama a estate d’in….
Muryarta ce ta katse masa tunani
“Doctor is waiting”
Kawai tace ta