Showing 18001 words to 21000 words out of 124668 words

Chapter 7 - So Da Buri Book 1 Hausa Novels by Humaira Bulama.txt

25 Sep 2025

2353

kin gama kukan munafurcin ki yi sauri ki fito ki k’arasa tattare wajen wanke wanken nan, dan har k’udaje sun taru.”
Sannan ta juyo ta mik’awa Ya Ja’afar naira hamsin.
Karb’a ya yi ya jujjuya ta kamar yana neman wani abun a jikin hamsin d’in kafin yace
“Hamsin nake gani!”

“Eh,ai wai da d’ari nace zan baka, yanzu kuma sai na ga sauran ashirin da hamsin biyu shine zan baka naira hamsin sai a siyo mana zob’on saba’in a gidan mai tuwo tuwo..
Kaga kenan Naira d’ari da ashirin ma na baka.”

Shiru ya yi yana son ya had’a lissafin amma sam sai ya gagara…ganin hakan yasa tace
“To bani kud’ina na fasa, kawai yau daki kud’inka.”

Da sauri yace
“A’a, barshi kawo in je In siyo.”

Kallonshi ta yi kafin tace
“Wato har ka manta da bashin da take binka ko?
Ranar nan fa har gidan nan waenan k’artin mazan masu tuk’a mata tuwo suka biyoka za su dakeka, da kyar Baba ya basu hak’uri.”

Shiru yayi kafin yace
“Kuma fa hakane,to yanzu ke zaki je kenan?”

Da ido Jalila ta nuna masa Huda wadda ta fito yanzun nan tace
“Ai ga k’arama chan,sai ni za ka aika? tsoronta kakeji ko?”
Da sauri yace
“Haba deee!! a’a.”

Ganin ta fara cin nasara,ya sanya ta ci gaba da cewa
“To kirata mana ga kud’in ka bata, amman wannan Yarinyar ma na san k’arshenta tace ba za ta je ba saboda d’azun nan na ji Mamanta tana cewa indai ka sake aikenta kar ta je , kuma idan ka daketa ta rama!!”

Ai tun kafin ta k’arasa ya wafce kud’in ya hau kwalawa Huda kira yana hura hanci.

Da saurinta ta k’araso tana “Na’am” tace “gani”

Kud’in ya watsa mata yace ‘maza ta je ta siyo mishi zob’o a gidan mai tuwo tuwo’.

Zaro ido ta yi kafin tace
“Maama ta hanani zuwa gidan saboda akwai y’an shaye shaye da maza da yawa, kuma ni ban ma san hanya ba yanzu.”

Cikin zuga Jalila tace
“Ai dama na san za a yi haka, ka ji ko?”
Sai kuma ta kalle ta tace
“Tukunna ma shaye shaye me kenan??”
Ba ta jira ta bata amsa ba tace”Yaya irinfa d’an maganin ciwon kan nan da kake sha yake d’an saka ka jiri shine take zagi! Tab!! kaga kenan ta had’a har da kai ta zage tasss!!!.”


Ai kuwa Jalila ta yi nasara dan Ya Ja’afar cewa yayi “wallahi yau idan Huda za ta suma sai ta je kuma wallahi ta dawo gidan babu zob’on gidan mai tuwo tuwo sai na lahira ya fita jin dad’i.”

Hakanan tana kuka tana komai ta zo ta wuce, sai da ta kai k’ofa ta juyo tace
“Yaya Jalila dan Allah to ko kwatance ne ki yi min.”

Cike da son sake dilmiyar da ita Jalilan tace
“Idan kika fita ki mik’e, ki yi kwana sau bakwai sai ki yi tambaya.”
Haka kawai Jalilan tace da ita sannan ta juyo tai hanyar d’aki har ta tura k’ofar sai kuma ta juyo
Sanin cewa Huda bata da wayo kwata kwata, tunda ba shiga mutane take yi ba ya sa tace mata
“Kuma saura ki biya gidan shuwa ki kai k’ara, ranar da kunne na na ji tace ‘sai ta yanka ki a duk ranar da kika yi
gangancin zuwa mata gida’.”

Hawayenta ta share cike da fargaba da tsoro ta juya ta fita daga gidan.

Kamar yadda Jalilan ta yi mata kwatance haka ta yi amman sai aka ce mata ‘ai nan arean kwata kwata babu gidan mai tuwo tuwo’.

BULAMA✍️





So da Buri
Free Book
07

Tun 11 na safe take bulayin neman gidan mai tuwo tuwo
har 4 na yamma bata samu ba, kusan kaff Unguwar ta Gandun Albasa har kwargiji da wajejen Gada duk babu inda ba ta duba ba.
Ganin ta kusa shiga g r a d’in Sharad’a ne ya sanya ta koma da baya ta ci gaba ta kutsa kai tana nema.
An nuna mata gidan mai tuwo tuwo har biyu amman ba nan bane ba kuma su ba sa siyar da zob’o.

Idan ka ganta sai ka tausaya mata, duk ta yi wujiga wujiga ga yunwa ga gajiya sannan ga k’ishirwa.
Tana cikin tafiya ta ga ta fara hango kwandila a tsallaken titin side d’in da take, sanin da ta yi cewa gidan mai tuwo tuwo ba a kwandila yake ba ne ya sanya ta yanke shawarar komawa gida kawai! Ko da kuwa Ya Ja’afar zai kashe ta da duka ne.
Har za ta juya sai ta hango tuk’a tuk’a, k’ishin da take ji yasa ta yanke shawarar ta tsallaka ta sha ruwan inya so sai ta tsallako ta koma ta tafi gida.
Da kyar ta samu ta tsallaka, ta rok’i wani almajiri ya buga mata, ta samu ta sha.
Ta gama sha kenan!
D’agowar da zata yi sukayi ido biyu da wani mahaukacin kare, da alama shima k’ishin ruwan yake ji dan ya k’urawa ragowan ruwan da bai gama tsiyaya ta kan famfom tuk’a tuk’an ba ido.

Yunk’urawa ya yi ya tunkarota cikin sauri, ai kuwa babu shiri ta nannad’e zanin jikinta ta kwasa a guje, a tunanin ta ita ya biyo. Shikuwa Karen ganin ta hau gudu kamar jira yake yi kawai sai shima ya bita a guje…..


Tsere suke zubawa ita da Karen nan tana ihu tana neman Agaji, musamman ma da ta tuno da wata magana da Sakina ta tab’a gaya mata
“Indai kare ya kama saman dunduniyar k’afar mutum ta baya to cirewa yakeyi gaba d’aya.
Kai da tafiya har abada.”
Ai kuwa nan ta k’ara k’arfin gudun nata….
Wasu su yi mata dariya wasu su ji tausayinta wasu kuma ta basu mamaki….gatanan dai doguwa kyakyyawa y’ar budurwa da ita amman ta zage tana tik’ar gudun ceton rai a wajen Kare.

Ganin da tayi k’afafuwanta sun fara zafi sosai, gashi ta gaji!! Ya sa kawai ta yi kalmar shahada ta tsaya chak! sannan ta juyo ta durk’usa…dai dai Karen ya iso dab da ita, ta rufe idanunta da mugun gudu da k’arfi ta hau had’ashi da Allah tana cewa “Dan Allah dan Annabi ka yi hak’uri, kar ka cijeni, na gaji ka yi hak’uri…”
Ta kusan mintina 2 a haka..
Jin shiru yasa ta bud’e idanunta a hankali k’irjinta na dukan uku uku.
Cikin ikon Allah kuwa babu Kare babu alamar shi. Hamdala ta yi ta mik’e da niyyar tafiya gida…sai ta ganta a tsakiyar kwandila. Layin shiruu ba kowa sai maka makan Gidaje, mota d’aya ta hango a k’ofar wani had’add’en gida da alamar mamallakin motar yana jira ne mai gadi ya bud’e masa ya shige.
Bayan wannan motar babu komai kuma babu kowa a layin. Dubawa ta yi sosai ta ga ba ma ta san a ina take ba, sai a lokacin ta fashe da wani irin kuka ta zauna dab’ass!! A wajen ta cusa fuskarta cikin cinyoyinta.......

Bai dad’e da shigowa cikin Unguwar ba, akwai wasu takardu da Abba ya sanya shi zuwa ya d’auka dan yana son yin amfani da su kuma har an tarkato an kawo sabon Gida.
Yana shirin danna horn kenan ya ji kamar ihu!! Kasancewar bai rufe gaba d’aya glass d’in motar tasa ba.
Yana kallon direction d’in da ya jiyo ihun nata kuwa ya hango ta ita da Karenta. Da farko
abun dariya ya bashi, sai kuma ta fara bashi tausayi…da
har zai je wajenta sai kuma ya fasa ya dannawa sabon mai gadin da aka saka a Gidan horn ya bud’e masa ya shige.
Bai b’ata lokaci ba ya shiga, inda takardun suke ya je ya d’auko ya fito ya shiga motarsa ya sake yin horn aka bud’e mishi gate d’in ya nufi waje.
Kamar ance ya juya, yana juyawa ya ganta this time around ta cusa fuskarta tsakiyan cinyoyinta kuma babu Karen a wajen.

Kawai tsintar kansa yayi da son zuwa wajen ta, da farko kamar ba zai je ba sai kuma yayi tunanin inda Aaima ce a wajen ai da ba zai so a barta ita kad’ai haka ba.

D’an rivers ya yi sannan ya karkata hancin motar ya nufi inda take.

Yana isowa ya d’an tsaya, ya
kasa fitowa kawai yana kallonta, dan ji yakeyi kamar ya juya.

Ya d’an jima a haka sai kuma yayi tsaki ya bud’e motar ya fito ya zo ta gabanta ya tsaya.

“Hey!!”
Ya ji shiru…sake maimaitawa yayi tukunna a hankali jin kamar mutum a tsaye a kanta yasa ta d’ago fuskarta wadda ta jik’e da hawaye tana kallonsa.

Da k’arfi ya ji zuciyarsa ta wani irin bugawa sakamokon had’a idanun da suka yi, ita kuma ganin sa da tayi ya sanya da saurinta ta mik’e tana karkad’e zaninta d’ayan hannun kuma tana goge hawayen da ya k’i tsayawa da bayan hannun.

Tsayawa yayi yana k’are mata kallo a ransa yace”Who’s she??
How can someone be this beautiful??.....”

“Ina yini”
d’in da tace masa ne ya dawo da shi daga duniyar lissafi da k’are mata kallon da ya tafi.

Da kyar ya iya tattaro kalmar
“Alhamdulillah”
Dan zuciyarsa bugawa take yi ba kad’an ba.

“Dan Allah ka san hanyar gidanmu?”
Ya sake jin muryarta.

This time around sai da ya lumshe idanunsa ya bude tukunna ya iya ce mata
“A’a, why are you crying?”.

Ta fahimci tambayar da yayi mata, dukda cewa a iya primary ta tsaya.
Amman kuma sai ta tsinci kanta da kasa bashi amsa…ta ga yawan maganarsa turanci ne, kar taje ta bashi amsa da Hausa ya kasa ganewa kuma
tana tsoron yin turanci dan ba wani iyawa ta yi ba, kar taje yayi mata dariya kamar yadda su Ya Jalila suke mata a duk lokacin da ta yi turanci.

Ganin ta yi shiru yasa ya fara tunanin ko bata jin turancin ne domin kuwa yanayin duk’unk’unennen hijabinta da kod’add’en zanin jikinta kad’ai sun isa su fad’awa mutum ita d’in ba wata shahararriyar y’ar Boko bace ba. Dan haka ya yanke shawarar maimaita mata tambayar da Hausa.
“Me ya saka ki kuka??”

Da mamaki a fuskarta, ta ke kallon sa jin Hausar tasa tarr!! A ranta tace “To ko dai koya yayi??” Dan tabbas ita dai ta san wannan ba bahaushe bane ba, ko dai balarabe ko kuma d’an India ,
Saboda yanayin cikar gashin kansa, gashi a kwance sai kyalli yakeyi, shigen na larabawa, gashi fari sosai, dukda cewa itama bakinta pink ne amman ta san nashi ya fi nata zama pink sosai, ga hancinshi mai kyau d’an dogo, sannan idanunsa irin manyan nan kuma a kwance dogaye, kuma wani ikon Allah yanayin shape na gashin girarsu iri d’aya..ba irin cika d’innan ne da girarba, amman shape d’inta na medium arch ya fito sosai……

Shi kam Arshaad zuwa yanzu ya fara tunanin ko dai kurma ce Yarinyar nan?! To amman kuma ai d’azu har gaida shi ta yi.
A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya sake ce mata
“Umm?”
Yana mai tsare ta da idanuwa dan yaga kamar ba ta ji na farkon ba.

K’asa ta yi da kanta ta fara wasa da y’an yatsun hannunta kafin tace
“Ya Ja’afar ne yace in siyo mishi zob’o, na manta gidan, tun Ina Yarinya aka hanani zuwa, kuma yanzu na b’ata.“
Ta yi maganar tana share siririn hawayen da ya zubo mata da bayan hannunta.

Shi kam he don’t know Y amman yanayin maganarta burgesa yake yi, komai nata a nutse take yinsa, ya dad’e bai ga mace mai magana cikin nutsuwa da kamewa ba kamar ita.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ganin ta d’ago kai ta kalleshi a karo na biyu bayan gama yi masa maganar, sai kuma ta sake yin k’asa da kanta ta cigaba da goge hawayen.

Wani white handkerchief ya zaro daga cikin aljihunsa ya mik’a mata.
Da farko k’in karb’a ta yi sai da yace “Ungo ki goge fuskar ki,ya b’aci da yawa da hawaye, Yara za su yi miki dariya.”
Tukunna a hankali ta sanya hannu ta karb’a ta fara goge fuskarta tana lumshe idanu saboda wani fitinannan k’amshi da yake shigar mata hanci.

Sai da ta goge hawayen tass sannan yace “Zo,mu je ga mota sai in kaiki Gida.”

A hankali ta girgiza masa kai sannan tace “Ban san ka ba, ba zan shiga motar ka ba.”

Wani d’an cute smile ya yi, kafin yace “To in tarar miki napep za ki shiga??”

Da sauri ta d’aga mishi kai alamar ‘eh’.
Smiling ya yi har sai da hak’oransa suka d’an baiyyana, sannan yace “To shi a ina kika sanshi? me napep d’in!”
Rau rau ta yi da idanunta, har za ta yi magana sai kuma tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta, dan bata da amsar da za ta bashi.

Ganin hakan yasa yayi locking motanshi daga inda yake da key d’in, sannan ya fara tafiya yace “mu je In saka ki a napep d’in.”

Da saurinta ta bi bayanshi…a
hanyar yake tambayar ta sunan ta, tace masa “Huda.”

Basu wani dad’e suna tafiyar ba, tun kafin su fita a kwandila suka samu napep, ta fad’a mishi inda zai kaita ta shiga.

D’an sunkuyowa ya yi yana kallonta a cikin napep d’in…ji yake kamar kar su rabu amma
da ya tuna ya ji sunan layin Gidan nasu yanzun har ma da d’an guntun kwatancenta da ta yiwa mai napep d’in duk ya haddace. Sai kawai yace mata “ki gaida gida da su Mama.”
Daga haka ya zaro 1k a aljihunshi ya bawa mai napep d’in, kafin ya yi waving nata yana smiling suka yi gaba suka barshi a wajen.

Har ya isa inda motarshi take ya shiga ya ja yai gaba, yana smiling.
Ita kuwa Huda mamakin kyau da had’uwa da gayunshi take ta yi, dukda ta san su Ya Junaidu ma kyawawa ne sosai amman wannan kam ya fi su, gashi da kirki.

Ahaka suka shigo layin su, ta nuna k’ofar gidansu aka ajjiyeta.
K’irgo y’an chanji mai napep d’in ya yi(950), har ta d’an yi gaba ya kirata ta dawo ya mik’a mata.
Sai a lokacin ta ji gabanta ya fad’i domin kuwa ta san tabbas ba za ta b’oyewa Mama abunda ya faru ba, gashi kuma har da sakota a napep har k’ofar gida, ta ina za ta fara bayani, waye shi?? ya aka yi ma ta sake da shi haka bayan jan kunnen da Mama ta sha yi mata a kan maza!? Mai ya sa duk wannan tunanin ba su zo mata ba d’azu??.

Muryar mai napep d’in ce ta katse mata tunanin da take yi
“Ungo mana, ko bakya so?”
D’aga mishi kai ta yi a hankali tace “Ka rik’e na bar maka.”
Daga haka ta juya ta nufi gida da sauri.

Tana d’ago kanta gabanta ya fad’i da k’arfi sakamokon had’a ido da suka yi da Baba ya hard’e hannayenshi a k’irji ya jingina da jikin bangon gidan da tafin kafarshi kwaya d’aya da bayanshi, yana kallonta yana kallon mai napep d’in.
Da sauri ya d’ago daga jinginar da ya yi ya zira silifas d’insa guda d’ayan wanda ya cire ya jingina da k’afar, ya tunkari mai napep d’in da yake shirin buga mashin d’insa ko gaisuwarta bai amsa mata ba.

A hankali ta tura k’auren ta shiga…tun daga soro ta fara jiyo maganar Jalila da Umma, Umma tanata masifa Jalila na zugata, tana ida shiga tsakar gidan kuwa ta hango Mama a zaune a bakin k’ofar d’akinsu tana kuka, Ya Junaidu ya durk’usa a ta gefenta da alama hak’uri yake bata, Umma sai ce masa take yi “shanyayye!! ya tashi a wajen kafin ranshi ya b’aci!!”
Jalila kuma tana cewa “ai dama ya fi son Mama a kan Umman tasu.

Sallamarta ce ta sanya duk suka juyo suka zuba mata idanu.
Ganin Mamanta na kuka
yasa da sauri ta yi inda take ta durk’usa a gabanta ta saka hannu ta hau share mata hawaye.
D’an kama hannunta Mama ta yi sannan ta goge hawayen da d’ayan hannunta kafin tace
“Daga ina kike? ya aka yi kika dad’e? Jalila tace Ina fita kema kika fita.”
Mama ta jero mata tambayoyin tana kafeta da idanu.

Za a wani tsaya ana yi mana kukan munafurci kamar ba ki san Ina ta tafi ba!! Kawai ke dai kice baki san waye saurayin ba amman sarai kin san me ta je ta yi.”
Cewar Umma sannan ta d’aura da cewa “Yo Allah na tuba daman Yaran yanzu ka haifo su ta hanya mai kyau ma ya aka k’are, ballantana ta hanyar da ba ta dace ba!!”.

Da k’arfi Mama ta runtse idanunta wasu zafafan hawaye suka shiga tsiyayo mata…
Umma bata damu ba ta ci gaba da cewa
“Sannan sai ki dinga goya mata baya tana abubuwan da ta ga dama idan anyi magana ki ce sharri aka yi mata saboda bakin ku d’aya ko??
Kina samu tana kawo miki taro da sisi.”

Hudan ce ta mik’e ta k’arasa kusa da Umma tace “Umma dan Allah ki yi shiru kinga fa maganar ki yadda take saka Mama kuka.”

D’an zaro idanu Umma ta yi kafin tace “Eh lalle Yarinyar nan kin rik’a!!!! Ko da yake ba zan ga laifin ki ba, yanzu ai gani kike yi daidai kike da ni tunda duk abinda na sani kema kin sanshi, zafin ciwon nak’uda kawai ya rage.…..”

Da sauri Mama itama ta mik’e ta k’arasa daff da Umma ta ce “Dan Allah dan annabi Sadiya ya isa haka! Za kisa Yarinya ta san abunda shekarunta ma basu kai ba, tun d’azu kinata aibantata da bakinki kuma yanzu kin zo kina irin wannan maganar a gaban Yara saboda Allah.”

Mamaki ne ya cika Umma saboda ta dad’e ba ta ga b’acin ran Mama kamar haka ba, cikin matsowa kusa da sosai itama tace “Lalle Maryam!! na jinjina miki. Son y’arki ya rufe miki ido har kina gaya mini magana dan na fad’i gaskiya??”.

Mama bata bari ta k’arasa ba tace “Wallahi ba gaskiya kika fad’a ba!”
Sannan ta juya ta kamo hannun Huda wadda take ta kuka ganin ana fad’a a kanta, ta kawo ta gaban Umma tace “Zan iya dafa Al Qur’ani akan sharri kuke yi mata,
Allah ne shaida ta na san kalar tarbiyyar da na yi mata.
Idan kuma kina da shedar da zaki tabbatar da abinda kike cewa gaskiya ne to Bismillah Ina sauraron ki.”

Hudan garin k’ok’arin goge hawaye bata saniba handkarcheif d’in da Arshaad ya bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login