Showing 9001 words to 12000 words out of 124668 words

Chapter 4 - So Da Buri Book 1 Hausa Novels by Humaira Bulama.txt

25 Sep 2025

2318

ne.
Can u imagine in 2 weeks time fa granpa yace “mu bar gidan nan amman Abba a jiya da sassafe ya kira masu penti aka fara pentin gidanshi na kundila yanzu kinga yau da safe yace mufara parking, na tabbatar ko kammala pentin ba a yi ba. Atleast ai ya jira ya dawo daga asibiti ko?
Ya samu ya d’an warware maybe b4 then ma granpa ya saukkk’o.”

Murmushi Mom ta yi kafin tace
“Haba Zainab,ke har yanzu ba ki san waye uncle d’inki ba ne?
If there’s one thing that I’m sure of shine granpa ba zai goge decision d’inshi ba sai dai in ya sassauta,yanzu mafita itace abar nema ba wai wannan dogon labarin ba
Dan ba ke kad’ai ba hatta ni da Mammy sai mun raina kanmu idan zance ya fito….
Na san granpa Hates Maryam with passion
But what we did is something da bai kamata ace mu bari a kamamu da laifinshi ba!.”

Ajiyar zuciya Zainab ta sauk’e kafin ta juyo ta kalli Adama sannan ta kama hannuwanta biyu tace” ki taimakeni…
at any cost kar mu bar gidan nan,you always come out with the perfect solution, do something. Har yau ban samu soyyayyar Abba ba,I’ve been trying my best wajen ganin na yi winning nashi kuma na san I’m almost there but in dai
matarnan ta dawo cikin rayuwarsa komai lalacewa zai yi.”

Shiru Mom ta yi tana d’an tunani ta kusan 5minutes sannan ta yi murmushi tace mata “kawo kunnenki kiji wata magana”
Matsowa ta yi sannan ta fara rad’a mata maganar…..
Da farko juyowa ta yi ta kalleta da alamun mamaki mamaki sai kuma ta juya ta ci gaba da sauraronta ahankali ta fara murmushi....


“Ummi!Ummi!!Ummi!!!”
Suka ji murya ana kwala kira a parlour.
Da sauri Zainab ta juyo tace inaga ga su shuraim sun dawo d’azu suka tafi asibiti.”
Har ta kai bakin k’ofa ta murza key d’in za ta fita sai kuma ta juyo ta kalla Mom tace mata
“Kin tabbata babu matsala?”
Murmushi mom ta yi sannan ta d’aga mata kai,alamar’eh.’
Juyawa tayi ta fita itama ta biyo bayanta suka fice a d’akin.

Wani Yarone yake shigowa cikin parlourn fari tass da shi kyakkyawa,suna had’a ido da Zainab ya kalli sama yana kallon d’ayan Yaron da ba zai wuce 10 years ba yanata hawa Bene yana kwala kiran “Ummi!!” ,
da d’an k’arfi ya ce “Sudais!”
Da sauri wanda aka kira da sudais d’in ya juyo yana kallon d’an uwanasa wanda juyowar da ya yi ne zai sanya ka fahimci ashe twins ne dan komai nasu iri d’aya ne.

Nuna masa Zainab ya yi sannan yace “ga Ummin nan.”
Da saurin sa kuwa ya sauk’o ya zo ya rungumeta kafin ya d’ago kai yacee mata “Ummi Abba ya dawo,Dr yace ya warke!suna waje shi da ya Arshaad yanzu zai shigo da shi.”

bai gama rufe bakinsa ba kuwa Arshaad ya shigo
Shi da wani mutumi kyakkyawan gaske,dogo d’an kakkaura amman bashi da k’iba kwata kwata,fari tas da shi, kyakkyawar fuskarshi cike da tsananin kyau haiba da kwarjini ‘ABBA’ ya rik’e hannun Arshaad d’in na dama shikuma Arshaad d’in ya ruk’o kafad’arshi da dayan hannun for support suna tafiya a hankali,kana ganin mutumin ka san bashi da lafiya.
A hankali suka k’arasa Arshaad ya kaisa har kan d’aya daga cikin kujerun parlourn ya zaunar da shi tukunna ya juyo ya kalli su Ummi ya gaida su.
Sai da suka gama gaisawa sannan Ummi ta k’araso kusa da su tace “Abba ya jiki?
Yaushe aka sallameka?
Mai yasa baka kirani ba?”

D’an gyaran murya Arshaad yayi, saida ta d’ago ta kalle sa sannan a hankali yace
“Ummi Dr yace kar a dameshi fa,and yana buk’atar Hutu,sosai!.”

Juyawa ta yi ta kalla gefe ta d’ayan staircase d’in yadda aketa sak’k’owa da kaya ana shige da fice kafin tayi murmushi tace “To Arshaad yanzu daka kowoshi ka ga alamun rashin hayaniya anan d’in?
Kalla fa parking aka hau yi yau d’innan gadan gadan,nima Ina dawowa daga asibitin na tarar da su suna jirana a gate da na
tambaya sukace wai Abban ne yace su zo su fara kwashe kaya suna kaiwa sabon gida,
yanzu saboda Allah idan bai ji da lafiyarsa dan kanshi ko ni ba,ai ya duba Yaran nan”ta yi maganar tana nuna su Sudais tare da share kwallar da ta zubo mata.

A hankali Abban ya yi d’an tari sannan ya gyara zamanshi tukunna yace
“Arshaad.”

“Na’am Abba.”
Arshaad d’in ya fad’a cikin girmamawa ya d’an rankwafo ta saitin shi.
Sai da ya kuma yin
tari sannan yace “Ka duba moving van d’in dake a waje akwai boxes da Ghana most go a ciki ka d’auko empty ones d’in dayawa,ka shiga parlourna da d’akina duk wani abu ka had’a su ka tattare,sannan ka rubuta sunan items d’in da suke ciki a jikin kowanne box da makar saboda kar ya bada wahalar tantancewa idan anje chan.
Ka yi sauri idan ka gama za su shiga yanzu su kwashe furnitures, naga har sun kusan gama chan side d’in.”
Ya k’arashe maganar yana d’an tari.


“To Abba”
shine abinda Arshaad yace,daga haka ya nufi waje domin d’auko boxes d’in.


Juyawa Abba yayi ya kalla su Sudais sannan yace “kuma ku je ku d’auko ku had’a naku kayan.”

Har ya gyara zaman ya d’an jingina ya lumshe idanunsa, sai kuma ya d’ago ya kalli Ummi sannan a hankali yace mata
“Za ki bimu ko a nan za mu barki!”
Yunk’urawa ta yi za ta yi magana ranta na sake b’aci,
Da sauri Mom wadda ke a bayanta ta rik’o hannunta ta d’an matse alamar ta yi shiru.
Shurun kuwa ta yi sannan Mom ta yi gaba tace
“Abba sannu da jiki, Allah ya sa kaffara ne.
Bara muje saman in taya ta had’a kayanta. Idan kana buk’atar wani abu muna sama sai ka kiramu a waya....”

D’aga kanshi ya yi alamar ‘to’
sannan ya mayar da idanunsa ya lumshe ya koma ya jingina a jikin kujerar.
SHARE PLS.
BULAMA✍️





So da Buri
Free Book
05


Jan hannunta Mom ta yi sannan suka yi sama,suna shiga d’akinta tace
“Adama ba fa inda zanje sannan suma babu inda za su je.”

“Na sani”
Shine abinda Mom tace sannan ta fara dube dube kamar tana neman wani abu.
Drowern gaban mudubi ta kai hannunta ta bud’e,aikuwa ta ci karo da abinda take nema..da sauri ta d’auko littafin da ta gani da biro sannan tace “oya d’auko mini takardar gidanki wanda ya baki in kalla signature da wani note haka da ya tab’a rubutawa.”

D’an tsayawa Ummi ta yi tana kallon ta da alamar tsoro a fuskarta.

Ganin haka ya sa Mom ta kawo gabanta ta tsaya sannan tace
“I’m just trying to help,ba mu da ishesshen lokaci,ki daina
dogon nazari.
Besides har yanzu ukune akan ki so don’t worry about one ballantana ma bashi da masaniya,so babushi a lissafi.
Kowa ya sani a estate d’innan kece weakness d’in granpa,ki
duba ki ga abubuwan da yake yi just to make sure u stay happy..I can assure u ba zai bari Abba ya tafi ko Ina ba idan ya ga wannan.”
tayi maganr tana nuna mata takardar da ta yaga daga jikin book d’in.

Shiru Ummi ta yi kafin tace
“Adama I love my husband, banaso in shiga tsakaninshi da mahaifinsa..”
Wannan karon tsaki Mom ta yi sannan tace”Zainab kin fara bani haushi wallahi zan yi tafiyata, shiga tsakani kuma na nawa??
Waye ummulaba’isin fad’an nasu?sai da abu ya zo gangara za ki fara tunanin tsame hannunki?
To bari kiji! ta inda akabi aka hau ta nan ake sauk’a sannan
na san Dr Abba farin sani If things get out of control zan yi paying nashi ya maka masa case na memory loss, a ce yayi for a day ne,
a time din kuma yayi ta misbehaving,sai mu ce a lokacin ne yayi shi kansha kenan bai san yayi ba. Dan mutumin da ya kwana ya wuni bai san inda kansa yake ba ai zai yi morethan this,kuma babu wanda ya isa ya musa.”

Da sauri Ummi tace”ok ok”sannan ta nufi wardrobe d’inta ta d’auko key a k’asan tulin kayanta sannan ta saka key d’in a jikin wani d’an k’aramin locker wanda yake nan ata k’asan kayannata ta murza mukullin ya bud’u. Wani suitcase ta d’auko ta yo kan gadon da shi,a tare suka hau bincikawa har sai da suka d’auko wani file da wata envelope.
File d’in takardun gida ne, envelope d’in kuwa da suka bud’e ta wani had’add’en rubutu ne ya baiyana a cikin da alama wasik’a ce .
Zama Mom ta yi a kan gadon sannan ta saka wannan wasik’ar a gaba ta yi shiruu…ta kai kusan 2 minutes tana k’are mata kallo kafin ta ajjiye ta a gabanta tukunna ta hau rubutu akan wannan blank papern data yago….exactly handwriting d’in irin na wannan wasik’ar takeyi.
Ta d’auki y’an mintuna tana rubutawa kafin ta d’auki dayan file din ta bud’o dai dai wajen signature ta kalla da kyau sannan ta ajiye ta yi irinta a k’asan takardaar da ta gama rubutu a kai.
Tashi tayi daga kan gadon sannan ta juyo ta kalli Ummi tace mata
“Done!!”

Mik’a hannu Ummin ta yi ta karb’a ta karanta sannan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace
“Yanzu ta Ina zan wuce??
kin san fa yana falo.”

“D’auko mayafinki”
inji Mom.
Cikin wardrobe d’inta ta bud’e wajen mayafai, sannan ta jawo abinda hannunta ya kai kai .
Warewa ta yi tana shirin saka hijabin Mom tace a’a bani nan zan saka a cikin nawa maya fin in fita in yaso sai ki sak’k’o daga baya ki yi kamar kin shiga kitchen,ni kuma zan jiraki a k’aramin compound ta baya,sai ki fito mu wuce.”
Har ta juya za ta fita,sai kuma ta dawo ta k’ara rad’a mata wata magana sannan ta fice.

Yadda Mom d’in ta tsara hakan kuwa akayi…

Bayan sun fita daga gate d’in gidan suka nufi na granpa.
Suna zuwa daniel ya gaidasu suka shige suka isa k’ofar main parlor.
Suna shiga kamar kullum sukaga ba kowa,shiruu sai k’arar ac
Ganin hakane ya sa suka nufi kitchen a tunanin su ko za su ga granma ta yi musu iso,amman nan d’in ma ba su sameta ba,sai masu aiki.
Ganin suna b’atawa kansu lokacine yasa Mom ta d’auko wayarta, ta kira gramma,bugu biyu ana ukun ta d’auka.
“Assalamu alaiki, Adama.”
Aka fad’a daga d’ayan b’angaren.
Cikin girmamawa mom tace
“Ameen wa alaiki assalam,Ina wuni gramma”

“Alhamdulillah”
Shine abinda gramma tace.

Cikin ladabi Mom tace”daman yanzu Zainab ta zo ta sameni akan wata magana,shine muke son ganin granpa,ban sani ba ko yana nan?.”

“Yana nan.”Ta ce,daga haka
ta katse kiran.

Kusan mintuna talatin suka yi a kitchen d’in, har sun fara gajiya sukaji k’arar bud’e k’ofa.
Da sauri suka fito a kitchen d’in dai dai k’ofar da take kallon kitchen d’in aka bud’e sosai wata farar tsohuwa ta fito,bata da tsayi sosai amman tanada k’iba,idanunta sanye cikin medicated eye glasses, tana sanye cikin wata royal blue d’in atamfar super xclusive
ta yi d’aurinta irin na tsoffi. A hankali take tafiya tana tunkaro k’ofar kitchen d’in tana yin mitsi misti da idanu alamun so take ta fahimci su d’inne a wajen domin kuwa dudda glass d’in ba kasafai take iya hango abu idan yayi nesa sosai ba.
Gane hakan da suka yi ne ya sanya suka yi saurin k’arasawa inda take sannan suka d’an rissina suna sake gaida ita. Cikin kulawa ta amsa sannan tace “ina fata dai abu mai muhimmanci ke tafe da ku ba shirme ba,dan kar ku je ku yi ta shiririta,kun san ba yawan son surutu yake ba,yanzu hakan ma da kyar ya yarda zai ganku..”
Takardar hannunta kawai Ummi ta mik’a mata.
Kallonta gramma ta yi sannan ta sa hannun ta karb’a takardar ta fara dubawa….gyara glases d’in idanunta ta yi da kyau cikin zaro ido kafin ta d’ago ta kallesu sannan tace
“Shi Yakubun ya baki wannan???yaushe!??”

K’asa Ummi ta yi da kanta sannan a hankali tace
“Shekaran jiya”
Cikin fad’a gramma tace”kuma to me kika tsaya yi tun shekaran jiya baki zo nan ba?
Ai cewa yayi ki tafi wajen iyayenki,ko kina da iyayen da suka fi mu ne?”.
Da sauri Ummi ta girgiza kai tana share hawaye.
Cikin tausayawa,gramma ta kamo hannunta ta rungumeta tana bubbuga bayanta,sai da ta yi shiru sannan tace su je wajen granpa d’in.

Ta cikin parlourn da gramma ta fito suka shiga,suka bi ta wani had’add’en staircase suka isa wani tafkeken parlour sannan suka sake bin bene kafin su iso wani had’add’en parlour.


A tsaye suka hangosa gaban wani k’atoton glass wanda gaba d’aya bangon wajen glass d’in ne ya cinye…ya
juya baya yana kallon glass d’in wanda ta cikin k’atoton glass d’in kana iya hango har compound d’in estate d’in.

Waje gramma ta nuna musu sannan ta k’arasa gabansa ta mik’a mishi takardar,kafin ahankali tace”ga abinda yake tafe da su”.
Ya kusan 2 minutes tukunna ya ce “Read it loud”

Cikin nutsuwa grmma ta fara karantowa.
“Ni Yakubu Umar Farouk mai turare, na saki matata Zainab Umar Farouk mai turare,saki d’aya…dalilin kuwa Ina gudun shiga hakkin aure domin na kasa bata kulawar da ta kamata da waje a zuciyata
ta koma gidan iyayenta ta ci gaba da zama,nima zan tafi nawa gidan, idan ta samu miji ta yi aure.”


Shiru kakeji d’ip! Kamar ba halitta a parlourn.
Da farko tari Ummi ta fara a hankali,chan kuma sai ta farayi da k’arfi har da kamar kakarin amai kafin a hankali ta sulale daga zaunen da take akan kafet ta kwanta a wajen.

“Ya subahanallah jini!!!”
shine abinda suka ji Mom ta fad’a….da sauri gramma ta yo kansu,itama tana zxuwa ganin alamun jini jini a cikin bakinta yasa a rud’e ta ce
“Adama mai ya faru?innalillahi wa inna ilaihirrajiun, maza d’auko ruwa ga firij chan ki zo ki yayyafa mata…”

Ruwa aka d’auko aka fara yayyafa mata amman a banza sai ma jinin da yake ta biyo yawu yana dalala a k’asa….da sauri gramma tace maza kira wani a cikin samarin nan ya zo a taimaka a kaita asibiti,da sauri mom ta mik’e sai kuma ta tsaya tace “gramma duk basa nan na manta,amma d’azu naga Dr ya zo duba Abba,in kirashi??”

Da sauri gramma tace
“Eh kirawoshi,Allah ya kawo sauk’i ma ai.”

Nan ta fita gramma kuma ta cigaba da jijjiga Zainab tana tofa mata addu‘o’i.
Cikin mintunan da basu gaza ashirin ba Mom ta dawo Dr na biye da ita,suna zuwa aka gyara wa Ummi kwanciya anan kan kafet din Dr ya shiga duba ta da kayan aikin da ya shigo da su.
D’agowa ya yi ya kalli Mom sannan yace”tun yaushe ta fara?”

“Bata tab’a suma irin wannan ba gaskiya,sai dai tarin jini kuma ba ya zuwa sosai kamar na yau.”

“Tun yaushe ta fara?”
Doctor ya sake jeho mata tambayar ba tare da ya kalleta ba dan ya duk’ufa ya tarkata hankalinshi duk a kan Ummi burinsa kawai ya ga ta farfad’o.

Kwanaki ta yi a gaba na har sau biyu,na yi mata magana tace “wai ta je absibi ance ba komai.Yau kuma sau uku kenan har da wannan,shima da naga ta yi ta sakeyi na tamabayeta tace mini ba komai fa.”

“Unhm“
Shine abunda Dr yace yana zuk’o wani ruwan allura sannan ya saita jijiyan hannun Zainab d’in ya juye mata shi a ciki ya ci gaba da bata taimakon da ya kamata.

Bayan wasu y’an mintuna…
A hankali take bud’e idanuwanta waenda suka yi jazir…da sauri gramma ta k’araso gabanta ta fara k’ok’arin mik’ar da ita tanata faman jera mata sannu,Allah sarki gramma duk ta rud’e.

“Doctor mai ka fahimta yana damunta???”
Granpa ya yi mishi tambayar yana dogara sandarshi yana mai k’arasowa wajen.

Mik’ewa tsaye ya yi sannan ya zare farin glasses d’in idonsa ya d’an mutsitsika idon ya maida glass d’in kafin yace
“Heart d’inta ke da matsala, and da alamar ya yi serious gaskiya tunda har ga jini,ban san dalilin da ya sanya ta b’oye ba ta gayawa kowa ba,but this is very serious,idan ba damuwa yanzu zan tafi da ita mu yi ECO, saboda mu san matakin d’auka,dan ba a d’aukar issue na heart irin wannan likely.”

“A wanne asibiti za a sameka?”
Granpa ya sake mishi tamabayar.

Card d’insa ya mik’awa granpa mai d’auke da suna da address na diagnostic center d’inshi sannan yace “nan waje nane it’s a private place.
I’m a consultant a AkTH,idan hankalinku ya fi kwanciya da chan sai ayi mata a chan d’in, dai nasu zai d’auki time kafin a gama.

“Za a sameka a chan (nakan)nan da 1 hour,get every thing ready”

“Ok sir,”shine abinda Doctor yace sannan ya juya ya fita.

“Let me show him the door” Mom tace sannan ta bi bayanshi.

A hankali ya k’arasa takowa inda suke kafin ya kalli gramma yace mata
“Leave us”
A hankali gramma ta mik’e ta juya ta fita.

K’arasowa yayi ya zauna a kan kujerar da take zaune a gefenta kadan a kan kafet sannan yace
“Since when kika yi realizing baki da lafiya??”

“2 years ago”tace.

“Wa kika fad’awa?”

“Ba kowa.”

“Mai ya yi causing abun?”

Shiruu ta yi wannan karon.

Zan b’ata miki rai Ummi,kin san ba na son kame kame da kyaliya.

Hawaye ta share kafin tace
“Abba ne”cikin sheshshek’ar kuka.
Tari ta fara yi sai da ya d’ab tsagaita sannan ta ci gaba da magana
“Ba ya bani time d’inshi,kullum cikin zancen Maryam yake,i tried very well inga na daidaita relationship d’inmu amman na kasa,yak’i ya bani had’in kai
at the end ma gashi ya zo ya rabu da ni gaba d’aya.
Inaji yana waya da Abokinsa wai ya san idan ya had’amu ni da Maryam ranar lahira da shanyayyen b’arin jiki zai tashi…..tunda yanzu ya samu chance d’in da zai iya maida ita…..kuma wai yana jin tausayina,gara ya sauwak’e mini inyi aure nima In samu wanda zai iya bani kulawa tun kafin lokaci ya k’ure.

Granpa it’s like har yanzu suna tare a yanayin maganarsa.”

Tana kaiwa nan ta fara tari irin na marasa lfy,abun tausayi.

A hankali ta ji granpa ya dafa ta sannan yace “ki huta,ya isa haka.”

Waya ya d’auka ya fara lalube sannan da kyar ya nemo numbershi,yayi mamaki da ya samu number dan ya jima basa waya…ko abu zai fad’a mishi sai dai ya gayawa Dad ya fad’a mishi, ko Abban ya kirashi domin ya gaidashi baya amsawa.
Sometimes kuma yayi rejecting
shiyasa tun yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login