Showing 21001 words to 24000 words out of 124668 words

Chapter 8 - So Da Buri Book 1 Hausa Novels by Humaira Bulama.txt

25 Sep 2025

2313

ya fad’o k’asa!
Karaf! kuwa a kan idon Jalila, da sauri ta k’araso inda ta ga handkarcheif d’in ya fad’i,har tana gurd’ewa.
Duk sai suka zubawa inda ta nufa ido, cikin sauri ta durk’usa ta d’auka,sai a lokacin Hudan ta lura aikuwa ta fara rarraba ido gabanta na mugun fad’uwa kana ganin ta ka ga mara gaskiya.

K’arasowa Jalilan ta yi kusa da Mama, dai dai fuskarta ta d’ago handkerchief d’in ta yi mata fifita da shi a dai dai setin fuskarta kafin tace “kowa dai ya ga lokacinda ya fad’o daga hannun Huda ko?
Tambayata a nan itace ‘shin a ina kamila nitsatstsiya Huda ta samu handkerchief mai kyau haka da k’amshin turare wanda na tabbata na maza ne?’.”

Ya Junaidu wanda kishi ya turnuk’e sa a take ne, yace “Kawo in gani!”

Mik’a masa ta yi ya k’arasa warewa…Farine tas! Hanky d’in, kana gani ka ga had’add’en personalize handkerchief, ta chan k’asa an rubuta ‘AY’ da wani had’add’en glitter gold, ga uban k’amshin da yake ta zubawa na had’add’en designer perfume.

Da kyar ya samu ya d’an yi controlling temper d’inshi tukunna ya kalli Huda yace “na waye???“
Ya yi mata tambayar yana tsareta da manyan idanuwanshi da suka fara chanja kala.

Shiru Huda tayi ta fara goge hawayenta da suke zuba a yanzun babu k’akk’autawa.

Mama ma da gabanta yake ta fad’uwa tana kiran sunan Allah da k’ok’arin kawar da mugun tunani akan y’artata tace
“Huda tambayar ki fa akeyi, kin yi shiru ki bamu amsa!”

Baba wanda ya shigo yanzu ne yace “Ku barta ai ba zata tab’a cewa komai ba! Gani nan, ni ne zan baku amsa!.”

BULAMA ✍️



So da Buri
Free Book
08.


Duk juyowa suka yi suna kallonshi da mamaki a kan fuskokinsu.
K’arasowa yayi ya kalli Mama yace “Nace miki Yarinyar nan yawonta ta tafi irin wanda kika yi amma kin k’aryata ni ko??
To mai adaidaita sahun da ya kawota shi na bi na tsare na tambaya ya kuma tabbatar mini da cewa ‘Ita da wani saurayi dogo fari tass suka tsaida shi a wajen kwandila, bayan ta shiga har yana ce mata ta gaida su Mama har ya bada dubu d’aya a kawota, da mai napep d’in ya bata chanji tace ta bar masa.’ Haka akayi ko ba haka ba?”
Ya k’arashe tambayar yana kallon Huda wadda jikinta a yanzu yake mugun karkarwa ga hawaye sai zuba sukeyi ta gagara controlling d’insu.

Mama ce ta k’arasa ta kamo hannunta ta share mata hawaye sannan a hankali tace
“Huda da gaske ne abinda mai napep ya fad’awa Baban ku? Dan Allah kar kiyi mini k’arya.”
Addua Mama take yi a ranta Hudan tace mata ‘A’a’
amman sai taga tana d’aga mata kai alamar ‘Eh’.

Wata uwar gud’a Umma ta rangad’a sannan tace
“Huda Allah dai ya yi miki albarka, gwara da kika fara fitowa fili kina fad’in gaskiya, yanzu sai a daina janta d’aki a na b’oyewa..
Don kowa yanzu ya san hali!
har shi Junaidu mai goya mata baya yau kam ya ji kuma ya gani. A bi dai a hankali kar a kwaso k’anjamau.”

A fusace Mama tace
“Bana son mugun alkaba’i, dan an ganta da wani sai kuma akace wani abun ke tsakaninsu??
Ki fad’i alkhairi ko ki yi shiru mana! Mai ya kawo maganar k’anjamau a nan?”

Baba ne yace “Wallahi Maryam zan yi mugun sab’a miki!!!
Ya da girman mu kina raina mana hankali? Uban mai ya had’ata da shi to da har ya sako ta a adaidaita sahu?
To bari kiji in gaya miki!!
Malam Iro mai kayan Miya da kika rainawa arzik’i kika hana shi auranta, yanzu zan je ince ya turo!! Dan ba zan zauna Yarinya ta lalata mini gida ba.
Amman kafin nan sai na sauya mata kamanni ta yadda shi kansa d’an iskan saurayin nata ba zai iya ganeta ba, kuma gobe ko ance ta je ba za ta je ba.”

Junaidu ne ya sha gaban sa ganin ya yo kan Hudan, kafin
yace “Baba a yi bincike dan Allah, kar a yi saurin yanke hukunci.”

Cikin fushi Umma tace “tou shanyayye!!
binciken me kuma bayan wanda akayi?”

Da sauri yace
“Umma mu tambaye ta mana mu ji, kina gani fa bata b’oyewa kowa ba ta fad’i gaskiya bata k’aryata mai adaidaita sahun ba, ko?”

Yanzu wannan munafukar Yarinyar za ka tambaya???
Kuma kana zaton za ta fad’i gaskiya? Tou Bismillah bari mu ji.”
Umman tace tana mai gyara tsayuwarta da d’aurin d’ankwalinta.

Ahankali cikin nutsuwa Junaidu ya tambaye ta “hanky d’in na waye? sannan waye wannan mutumin da aka gansu tare,a ina ta sanshi?”

Amsa d’aya ta iya bashi,
“hanky d’in na mutumin ne amman ita wallahi ba ta sanshi ba.”
Ta kuma bashi labarin tun daga yadda kare ya biyo ta har lokacin da ya sakota a adaidaita…..

Dariya Umma da Jalila suka saka kafin Jalila tace
“Lalle Huda kin cika tantiriyar mak’aryaciya!”

Junaidu kuwa ganin raina masa hankali ma zata yi yasa ya jefar da hanky d’in kawai ya juya ya fita ranshi a mugun b’ace…..A hanyar fita suka had’u da Ya Jaafar yana shirin shigowa shi kuma, yana tafe yana tangad’i.

Yana shigowa ya hango Mama a gaban Huda ta na k’ok’arin kare ta daga dukan da Baba yake shirin yi mata tana kuka tana bashi hak’uri..saboda ita har ga Allah ta yarda da labarin da Hudan ta basu.

Da saurinshi ya k’araso yace
“Ke dan ubanki Ina zob’o na???tun jiya na k’i shan ruwa ke nake jira, Jalila tace mini tun jiya da yamma muka aikeki, a gidan ubanwa kika kwana?”

Ita Hudan sai yanzu ma ta tuna da kud’in aiken kuma indai za ta iya tuna a inda ta zubar to a wajen gudun kare ne….
Hak’uri ta shiga bashi tana cewa “Bata ga gidan mai tuwo tuwo ba, ta duba duk wani lungu da sak’o na Gabdun Albasa. Sannan kud’in sun fad’i, ya yi hak’uri dan Allah.”

Zancenta na kud’in sun zube kawai ya iya fahimta, dan haka ya yo kanta zai daketa
nan ma Mama ta kuma karewa, ta hau rok’on Baba tana cewa “Dan Allah ka bawa Jaafar hak’uri, ka ga a yanayin da yake ciki, baya cikin hankalinshi kar ya je ya ji mata ciwo.”

Umma ganin kamar Mama za ta yi nasara a kan Baba ne yasa ta sanya gaba d’ayan k’arfin ta ta ja Mama ta cilla ta gefe har saida ta fad’i k’asa.
Ya Jaafar kamar jira yake yi ya hango wani tsohon katako a gefe kawai ya nufe shi ya d’akko.
Mama na ganin haka ta fara k’ok’arin mik’ewa da sauri ta nufi inda suke amma kafin ta k’araso har ya bugawa Hudan a cikinta da dukkan rogowan k’arfinsa.

Aikuwa dukan ya shige ta ba kad’an ba, k’usoshin da suke jikin katakon suka chaketa wanda hakan ya sanya jini ya fara zuba, a take ta fad’i a wajen ta sume.

Sai da numfashin Mama ya d’auke da jinta da ganinta na y’an sakanni tukunna a hankali ta taka ta k’araso ta durk’usa ta fashe da kuka, tana dudduba ta tana neman pulse…..
Da sauri ta mik’e ta nufi d’aki ta
bud’e jakarta ta zaro waya ta hau kiran Ummu.…
Shi kuwa Ya Ja’afar yana ganin ta sume, shi ya d’aukama ko ta mutu ne, dan haka ya kwasa a guje ya yi waje.
Umma da Jalila kuwa d’akinsu suka nufa, haka shima Baba….babu wanda yace uffan a cikinsu.

Ummu,
an ci sa’a har yanzu suna gidan Hajiya Shuwa, dan ya fi
kusa da asibitin, shiyasa suka zauna a nan gudun kar su koma gida ciwon Sumayyan ya sake tasowa. Suna cikin hira ta ji k’arar wayarta,
ganin sunan Mama wanda tayi saving da sister a kan screen d’in ya sanya ta yin murmushi kafin ta d’auka tana mai cewa “Mama jikin nata fa da sauk’i, ki kwantar da hankalinki bacci ma takeyi yanz....”
Jin sheshshek’ar kuka yasa tace “Me ya faru? Ya naji kamar kina kuka??”.
Salati ta fara lokacin da Mama ta fara gaya mata halin da Hudan take ciki… ba ta tsaya
jin ba’asi ba ta zaro mayafinta ta yi waje, ganin hakan ya sanya Sakina biyo ta.
A bakin gate suka ci karo da Madu, ganin yanayinta ya sanya shi tambayarta “mai ya fati?” shi a tunaninsa ma ko jikin Sumayyan ne…nan ta hau
gaya mishi abunda ya samu Hudan….Shiruuu! yayi ba tare da yace komai ba, chan kuma a hankali ya rab’a ta gefenta ya wuce cikin gida.
Wani siririn kuka Mama ta sake fashewa da shi sarai Ummu ta san ta ji yadda sukayi da Madu yanzu da yadda Madun ya nuna halin ko’in kula da lamarin….
Shiru kawai ta yi ta cigaba da tafiya da sauri domin ta je ta iske su ita da Hudan akan lokaci tunda yanzu shine priority.

Sauri takeyi still da wayar kare a kunnanta dan ta cewa Maman “kar ta kashe har ta k’araso.”
A bakin layin suka ci karo da Junaidu, ganin ta da yayi a hargitse yasa ya shiga tambayar ta “mai ya faru??”
Ce masa kawai ta yi “Ya nemo mai adaidata ya kawo k’ofar gidan Baba yanzun nan.”

Da farko kamar ba zai yi ba, domin kuwa shi Yaji! ma yake shirin yiwa gidan gaba d’aya
saboda kwata kwata baya son ya had’u da Huda don idan yana ganin ta kishi zai iya sakawa ya bubbugeta, shi kuma baya son hakan ta faru.
Dan haka ya yanke shawarar barin gidan for some time.

Ji yayi zuciyar shi tana bashi shawarar ya yi abinda Ummun tace dan haka kawai ya nufi titi....

Ummu
sai da ta zo shiga gidan tukunna ta lura da Sakina, dan haka a tare suka kutsa kai suka shige.
Suna isa tsakar gidan kuwa suka hango Hudan a kwance malale cikin jini, ga wani makeken katako a kwance a kan cikinta ragowanshi kuma yana jan k’asa, kanta a kan cinyar Mama wadda taketa kuka tana rik’e da waya a kunnenta dayan hannun kuma tana ta shafa kan Hudan.
Kukan da Sakina ta fashe da shi ne ya janyo hankalin ta garesu, aikuwa ganin y’ar uwarta yasa ta fashe da wani sabon kuka abun tausayi.

Ummu ma bata san lokacin da ta fara kukan ba, Sakina kam da gudu ta k’arasa inda suke ta hau kiran sunan “Huda!”
Jin kamar k’arar adaidaita sahu ne yasa Ummu juyawa tana addua Allah yasa Junaidu ne, aikuwa a soro suka had’u da shi yace mata “mai napep d’in yana waje” sannan ya juya zai fita, da sauri tace “dan Allah Junaidu zo ka taya mu d’aukar Huda.“

Da mamaki yake kallonta sai kuma kawai ya bita suka shiga ciki…gabanshi ne yayi mugun fad’uwa da ganin halin da Hudan take ciki, da gudu shima ya k’arasa yana kiran sunan ta yana tambayar Mama “mai ya faru?” Duk a lokaci d’aya.

Da kyar Mama ta iya ce mishi “Ja’afar ne.”

A zabure ya mik’e ransa a b’ace zai yi waje Ummu ta taro shi, tace “Yanzu ba lokacin wannan bane ba, mu ji da lafiyarta tukunna.”
“Sakina, d’auko zanin gado ko wani babban hijabi mu samu mu raba ta da wannan mugun katakon, mu danne jinin sai mu kaita asibiti.”

Hakan kuwa aka yi…
Daga nan suka kinkimeta da taimakon Junaidu aka sakata a napep aka nufi asibitin kusa da su dan emergency ne….



Sai da Umma da Jalila suka ji fitarsu tukunna suka sauk’e ajiyar zuciya a tare
Jalila ta saka dariya kafin tace”Ai ko banza ta wahala!. Da farko fa amma tsorata nayi Umma dan wallahi na d’auka ta mutu ne, sai da na ga Mama ta duba hannunta da wuyan ta tace ‘Alhamdulillah’ tukunnan hankalina ya d’an kwanta, amman da har na fara shirin guduwa wallahi.”

Umma ce tace “ke dalla chan rufe min baki!!! Banza kawai!! kina nan zaune gashi ita har ta yo saurayi mai kud’i!, ke kina fama da malamin maths wanda sai dai yayi ta lissafa uban kud’ad’e amma ba zai iya baki ko sisi ba.
Wannan kuwa kina gani kin san mai kudi ne, kalli kyallen da ya bata, k’amshin turaren jiki duk ya cika gidan nan.
Tunda na dawo kike ta ce mini kin had’a bomb in jira yau burinmu zai cika ashe ke shirme kika had’a ban sanib..”

Cikin katseta Jalila tace
“Wallahi Umma da gaske ni plan d’ina shine Ya Ja’afar ya zaneta sannan ta yi dare sosai tunda kinga ai ba lalle ta gane gidan ba tunda ta dad’e bata je ba, sannan ita kuma Mama idan ta ji mun aiketa gidan ai kinga ranta zai b’aci
Daganan ni kuma inyi ta fad’an maganganu a kanta yadda Mama zata ji haushi ta fusata.
Ni sam ban yi tunanin za ta yo saurayi b...”

“Aikuwa gashi ta yo kuma mai kud’i, kina jin kan zanjen nata kin san Yaron sonta yake yi.”
Cewar Umma.

Shiru Jalila ta yi kamar mai tunani chan kuma tace “Umma kema kin yarda da labarin da ta bayar kenan?”

“To ai shine gaskiya.”
Inji Umma, kafin ta d’aura da “idan ba hakan ba ta Ina wachchar gab’uwar Yarinyar ta san wani zuwa wajen saurayi??? Ni yanzu babban tashin hankalina kar ya zo ya zubewa Babanku kud’i kin san halinshi in dai yaga kud’i, mu je ya yarda ya bashi ita!
Gashi ita kuma wawiya ta yi kwatancen gidan nan kuma nasan ya ji, zai zo….”

Shiru duk sukayi Umma in banda huci ba abunda take yi kana ganinta ka san hankalinta a mugun tashe yake
sannan tayi zurfi cikin tunani.
Me ta tuna? Allah kad’ai ya sani, haka nan ta fara murmushi kafin tace “Allah ya kawoshi lafiya.”
Kawai, ta fad’i hakan still da murmushi a fusakarta.

Jalila dai ba fahimtarta ta yi ba, hakan yasa ta hau gado ta kwanta tana sinsinar k’amshin jikin handkerchief d’in a haka bacci ya yi awon gaba da ita, ta bar Umma tanata faman tufka da warwara.


A chan asibiti kuwa, suna zuwa aka yi emergency da Huda. Likitoci suka rufu a kanta, Allah sarki Junaidu har da kukan sa shima Ummu da Sakina suma suna taya Mama..Har sai da
wata nurse ta zo ta fara musu fad’a tana cewa
“Addua za ku yi mata ba kuka ba, sanna kai kana Namiji kana kuka wa zai basu hak’uri??”
Tukunnan a hankali Junaidu ya mik’e ya fice ya nufi masallaci
Su Mama suma suka shiga k’ok’arin tsayar da kukan su, suna masu addu’ar Allah ya bata lfy ya kawo mata sassauci, dukda hawayen ba daina zuba yayi ba.


Sai da aka yi! aka yi!! Tukunna suka tsayar da jinin, da kyar suka fito wajen awan su 4, dan numfashinta k’in daidaituwa ya yi da farko.
Likitan ne yace “su godewa Allah k’usoshin basu tab’a komai ba. An yi mata tetanus da duk wani abunda ya kamata, an kaita d’akin hutawa za su iya zuwa.”
Daga haka ya mik’a musu takardar bill.
Cikin mutuwar jiki Mama ta fara k’ok’arin mik’a hannu za ta karb’a, Ummu ta yi saurin amsa tana dubawa, kafin ta cewa Sakina “ta hau Napep ya kaita gidan Hajiya Shuwa ta fad’a musu halin da ake ciki ita da su Baabaa Talatu sannan ta d’auko mata jakarta da atm d’inta.” A take Sakina ta wuce.

Wasu zafafan hawayene suka zubowa Mama, a hankali tasa hannuta ta goge sannan ta mik’e ta nufi d’akin da aka yi musu kwatance, inda Hudan take.

Ummu kawai binta ta yi a baya dan ta san abinda ya zo mata rai yanzun har yasa ta kasa yi mata magana.

Kusan a tare suka shiga d’akin,
Ummu ta zauna wajen k’afarta ita kuma Mama ta zauna a kan kujerar dake kusa da kanta a gefen gadon.
A hankali ta shiga gayawa Ummu abinda ya faru har Ja’afar yayi mata wannan aika aikar…

Share kwalla Ummu ta yi sannan tace “Gaskiya Mama ni kam zan d’auki Huda mu tafi gidana da ita, koda kuwa Hajiya Shuwa zata yi fushi. Dan naga alamar burinsu Sadiya su kashe ta ne, wannan wanne irin abu ne??
Ana sallamrta za mu tafi tare ba za su sake ganin ta ba.”

Da sauri Mama tace “a’a Bilkisu, kar kiyi haka, dan Allah. Fushin Hajiya Shuwa bashi da dad’i ni zan fad’a miki wannan, ba zan so saboda ni ki samu matsala da ita ba.
Kawai ki barmu a yadda muke, Allah yana sane da mu...

Wani irin tausayin su ne ya rufe Ummu, ganin tana shirin fashewa da kuka yasa ta yi saurin mik’ewa tana cewa
“Bara inje inda Sakina ta barmu in jirata, kar tazo tayi ta nemanmu bata ganmu ba.”
Tana gama fad’in haka da sauri ta fita tana sakar kukan daya taho mata babu shiri.

Murmushi Mama tayi dan sarai ta gano k’anwar tata.

A hankali ta fara shafa kan Huda wasu zafafan hawaye suna tsiyaya daga idanunta sakamokon kwakwalwarta da ta fara tariyo mata wasu shud’ad’d’un al’amura da suka wakana shekaru ashirin da shida baya.........

………………..
Alhaji Muhammad Madu shine asalin sunan Mahaifin Mama, Mahaifin sa Babarbarene gaba da baya, Mahaifiyarsa kuma y’ar jahar Yobe ce, Fune, Jajere .
Ya fi kama da Mahaifiyarsa domin idan ka kalle sa yanayin farar fatar sa da siririn jikinsa komai nasa irin na fulani ne.
Iyayaensa shi kad’ai suka haifa, sannan sun rasu ne tun yana Yaro.
Mahaifin Anum (Hajiya Shuwa ) shine ya d’auke sa ya rik’e shi kamar d’an sa.
Bashi da d’a Namiji, Shuwa da yayunta mata biyu Allah ya bashi, shiyasa ya rik’e Madu a matsayin d’ansa, sannan an yi zaman mutumci a lokacin da iyayenshi kafin su rasu.

Mahaifin Hajiya Shuwa da Mahaifiyarta gaba d’aya dangin su Shuwa Arab ne.

Mahaifin ta ya kasance Malami Babba a Maiduguri, domin babu inda zaka tsaya a lokacin ka ambaci sunanshi ace ba a sanshi ba.

Shekarun Madu suna d’an ja suka fara zazzafar soyayya shi da Anum. Mahaifin ta yana fahimtar hakan kuwa, ya tsaida wata biyu aka d’aura musu aure, dukda Mahaifiyarta ba wani so take yi ba, dan Anum d’in a wannan lokacin shekarunta 13 kuma tafiso y’ay’anta duk su yi aure a k’abilarsu, gashi Anum d’in tana da masoya sosai a cikin y’an uwa, dan duk Yara masu shekarunta a wannan lokacin babu mai kyau da gashinta, shiyasa ma sunanta ya b’uya daga Anum kowa yake kiranta da Shuwa.

Shikuma Mahaifin Anum, hazak’a da k’ok’ari irin na Madu ya gani dan kaff cikin d’alibansa babu wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login