Showing 27001 words to 30000 words out of 124668 words

Chapter 10 - So Da Buri Book 1 Hausa Novels by Humaira Bulama.txt

25 Sep 2025

2306

mata kud’in makaranta bai tab’a nuna gajiyawa ba shine take yiwa y’ar sa haka??.
A lokacin suna aji biyu a js amman babu shiri aka siya mata form ta yi junior waec , aka fara shirin tura ta boarding. Madu yana dawowa Bashir ya rok’esa yace “yanaso zai had’a da Maryam ya kaisu makarantar kwana, anfi karatu dan kwata kwata Zainab bata karatu”.
Sam Madu bai so hakaba don baya son yayi nesa da Maryam amman kawai sai yayi kawaici ya amince, Bashir a tunanin sa Zainab da Maryam za su shirya ne idan an kaisu boarding tare tunda daman chan k’awaye ne, kuma yana kyautata zaton Sadiya ce ta had’asu fad’a. Sai dai kuma ko da akaje boarding d’inma, farin jinin da Maryam take da shi a wajen Malamai da d’alibai sai ya sake jawo mata bak’in jini a wajen Zainab, sannan Yayanta Usman sai ya zo makarantar sau da yawa wajen Maryam amman ita sai dai ya bada sak’o yace a bata, kuma sai ya cukowa Maryam leda da kayan kwad’ayi amman ita sai ya bada kad’an yace a bata..
Abunda ba ta sani ba a ko da yaushe sai Maryam d’in ta k’ara mata a kan wanda Ya Usman d’in ya bayar yace bata.

Haka kurum sai ta daina kulata ko ta hau yada magana idan ta ganta, shirin da akeso dai su yi bai yiwu ba domin kuwa alamarin k’ara tab’arb’arewa ma yayi don kwata kwata Zainab da Maryam basa shiri,duk mates d’insu sun sani.
Har sai da Zainab ta kai Maryam bango duk kuwa hak’urinta sai da ta tanka mata sukayi wani damben da suka jiwa kansu ciwuka har aka kai ga kiran iyayen su, sai a nan ne Madu ya ji abinda ya faru har Bashir ya kaisu boarding duk dan ya samu daidaita tsakaninsu.
Ganin k’ok’arin Bashir na ganin zaman lafiya ya wanzu ya kuma tabbata a tsakanin Yaran nasu ne ya sanya kawai shima Madu ya barsu sukaci gaba da boarding d’in.

Wanda bayan sun dawo hutun gama ss1 ne Ya Usman ya zo da zungureriyar wasik’ar shi ya bawa Maryam ta inda ya ke bayyyana mata cewa shi fa sonta yakeyi tun tana y’ar k’aramar ta….
Ita dai Maryam ba zata ce bata son Ya Usman ba saboda Yayanta ne kuma ya kula da ita sosai, amman a gaskiya so na soyayya sam bata yi masa kwata kwata. Ko da ta gayawa Umma Talatu da Hajiya Shuwa..kalar murnar da ta gani a kan fuskokinsu ne ya sanya kawai ta amince suka fara soyayyarsu ita da Usman gwanin ban sha’awa.

Zainab kuwa (duk da kaita boarding school d’in da akayi hakan bai saka sun rabu da Sadiya ba, don indai aka aike Zainab to sai ta biya wajen Sadiya a b’oye).
Ai kuwa tanajin labarin soyayyar Maryam da Usman,
Sadiya ce kawai ta fad’o mata a rai, dan ba zata iya irga adadin wasik’un da Sadiya ta bata ta bawa Ya Usman ba..tun tana y’ar shekara sha d’aya take son Ya Usman,
shi kuma Ya Usman idan akwai wadda ya tsana a duniyar nan to Sadiya ce! Idan ka kalli Sadiya sam ba zaka tab’a ce mata mummuna ba, ba doguwa baceba amman tanada manyan idanuwa da matsakaicin hanci bakinta dai dai misali ga dimples a fuskarta sai dai bak’a ce amman tanada dirin jiki mai kyau sannan tanada gashi wanda ya sauk’o har kan kafad’arta, sai dai sam waennan qualities na Sadiya basu d’ad’a Usman da k’asa ba hasalima shi ya tsane ta kwata kwata bata kwanta mishi ba..
A cewarshi Yarinyar bata da kamun kai, ga munafurci irin na Ubanta dan sarai ya san ita ta shiga tsakanin Maryam da Zainab, shiyasa daya ga nacin nata yana neman yi mishi yawa ya had’asu ita da Zainab d’in ya ci ubansu, tun daga ranar ya samu sa’ida.
Sai dai fa dukda hakan da yayi sam soyyarshi a zuciyar Sadiya ba abinda ya ragu sai ma k’aruwa da tayi….

Da wannan tunanin Zainab wadda ta saci hanya ta isa gidansu sadiya, bayan sun gaisa da Baba Laraba ta tambaye ta Ina Sadiya tace mata “Tana d’aki”.
Tana shiga ta sameta a kwance tana bacci, jijjigata Zainab ta shiga yi har sai da ta farka sannan ta shiga koro mata halinda ake ciki

A ranar Zainab ta sake gasgata soyayyar Usman a zuciyar Sadiya domin kuwa kuka ta dinga yi harda ihu kamar wata y’ar k’aramar Yarinya da kyar suka lallasheta ita da Baba Laraba bayan ta shigo Zainab ta gaya mata halin da ake ciki.

kafin ta bar gidan kuwa zazzab’i ne mai zafi ya rufe Sadiya dan ko idanunta bata iya bud’ewa.

Satin Sadiya uku tana rashin lafiya, idan ka ganta sai ka tausaya mata, duk ta rame ta fita a haiyyacinta, har shagon d’inkin Usman taje tai sallama da shi daya fito tayita masa kuka, ganin da yayi abun nata na gaske ne yasa ya lallasheta ya rakata gida, wannan itace rana 1 daya mata magana mai dad’i shiyasa tana dawowa gida har mamakinta Laraba ta dinga yi saboda yadda ta ware kamar ba ita ba.

Hutun makaranta ya k’are!
su Maryam an fara shirin komawa, wannan karan Baba Bashir ne ya yi musu provision da kyar Madu ya bari kuwa.
Ranar Lahadi Usman da Madu suka maidasu makaranta.

BULAMA ✍️





So da Buri
Free Book
10


Ranar Monday aka yi chanjen aji, sannan da yamma aka nad’a shadow prefects wanda a ciki har da Maryam, Maryam ta so an bawa Zainab itama domin zuwa yanzu Maryam ta lura a duk lokacin da ta samu abu Zainab d’in bata samuba ne suke samun matsala da ita.

Duk da k’ok’arin ganin an zauna lafiya da Maryam d’in take yi hakan bai hana Zainab kyarar ta ba kasancewar hostel d’aya suke room d’aya aji d’aya kuma seat d’aya.

washegari Tuesday, suna zaune suna jiran first period na English, English theacher d’in ya shigo tare da wani kyakkyawan saurayi sanye cikin khakin sa na nysc,
kusan duk matan ajin ido suka zuba mishi….
Har suka k’araso bakin board suka tsaya da shi da English teacher d’in idanunsu na a kanshi, shi kam bai ma san suna yi ba don idanunsa suna a k’asa yana kallon k’asa yayinda su kuma ko fahimtar bayanin English teacher wanda yake cewa “ga sabon copper shi zai dinga yi musu English a yanzu for 10 months, daganan idan ya gama service d’inshi ya tafi aiki zai dawo hannunshi kamar farko” basa yi, har sai da yace “Are u guys with me??”
Da d’an k’arfi, tukunna hankulansu ya dawo jikinsu, suka ce “Yes sir.”
Banda Zainab wadda tayi mutuwar zaune, dan a lokaci d’aya ta ji bawan Allah n ya tafi da imanin ta.
Kasancewar Madu da Bashir sun gayawa Malaman su su dinga zaunar da su sit d’aya ita da Maryam ya sanya akoda yaushe suna tare, hakanan wani lokacin zainab sai ta kawo jaka ta saka a tsakiyar su wai kar jikin Maryam ya goge ta ta kwashi bak’in jini,
Amman yau kam zainab bata san lokacin da ta kamo hannun Maryam da k’arfi ba!
Ita maryam d’inma tsorata ta yi dan kwata kwata hankalinta baya ajin, ya tafi ga takardar da take hannun ta tanata bitar debate d’in da za suyi da safen nan, kawai ta ji an damk’o hannunta kamar za a karya ta.
Kallonta ta yi amman sai ta ga hankalinta gaba d’aya baya tare da ita, wani wajen ma daban take kalla.
Da sauri ta kalli inda zainab take kallo ta ga englishi teacher yana ta zuba bayani a gaban board da wani balarabe a gefen sa da koren kaya a jikin sa….dan haka ta juyo gareta cikin kulawa tace
“Zainab menene?”
Kallon ta zainab d’in ta yi sannan tace
“Maryam kinga wannan kyakkyawa ko?.
Dama haka ake ji a lokacin da ka ga wanda kake so? kinji yadda k’irjina yake bugawa kuwa? haka kike ji idan kika kalli ya Usman?”
Ta yi mata tambayar tana mai sake kallon saitin da copper d’in yake.

Wani farin ciki ne ya lullub’e Maryam dan rabon da zainab ta yi mata magana mai tsaho haka har ta manta…dan haka ta saki wani k’ayataccen murmushin da ya sake fito da ainihin kyawun fuskarta sannan ta d’ago kanta domin ta kalla wanda y’ar uwarta ta haukace a kai haka cikin lokaci k’ank’ani. Tana d’ago kan nata dai dai shikuma English teacher ya mik’a masa chalk yana cewa “introduce yourself to them.”
Karb’a yayi sannan ya d’ago
daidai ita kuma Maryam ta juyo tana murmushi a take idanunsu suka sark’e a cikin na juna! Bai san ya aka yi ba kawai ya ji chalk d’in dake hannunsa ya fad’i k’asa! Lokaci d’aya zuciyarsa ta hau bugawa da sauri da sauri….
Itama Maryam kusan hakan ne a nata b’angaren, jin yadda zuciyarta ke bugawa gashi ya tsareta da manyan idanuwanshi farare k’al masu kama dana mai jin bacci, hakan ya sanya ta saurin sunkuyar da kanta k’asa.
Maganar Mr Solomon ce ta dawo da shi daga duniyar daya tsinci kanshi a ciki dak’ik’un k’alilan da suka wuce.
Chalk d’in da ya yar yaga yana mik’a mishi sannan ya sake cewa “introduce yourself to your students.”

A hankali ya saka hannunshi ya karb’a sannan ya sake juyawa ya kalli inda Maryam take a ranshi yana adduar Allah yasa ta sake d’agowa ya kalli fuskarta, domin kuwa baya jin akwai abinda ba zai tab’a gundurar sa a duniyarnan kamar kallon fuskar wannan extraordinary beautiful young lady d’in ba.

Ganin tak’i d’agowa ne yasa shi juyawa…a hankali ya k’arasa jikin black board d’in ya rubutu sunan shi kamar haka
‘YAKUBU UMAR FAROUK M.T’
Sannan ya juyo ya kalli students d’in yace “that’s my name, but u can all call me ‘ABBA’
I’m your new English Teacher....”
Cikin nutsuwa ya karanto musu tsarinshi kamar ‘baya son surutu a aji sannan yana son in ya bada assighment a dinga maida hankali ana yi......’
Sai da ya gama tukunna Solomon yace “akwai debate d’in da ya basu as an assignment group A B and C”.
sannan ya mik’a mishi textbooks d’in da suke hannunshi ya juya ya fita….

Cikin kwarewa da nutsuwa Abba yake koyar da su, sun nutsu kuwa suna fahimta sosai don duk hankalin su yana a kanshi, sai da ya gama yace “Ina masu debate?”
Maryam ita take representing group A, dan haka ta mik’e tsaye. A hankali cikin sauk’e ajiyar zuciya yake kallon ta, kafin ya janye idanunsa ya mayar kan group leaders d’in B and C da suka mik’e sannan yace “su fito gaban board”.

Topic d’in yana magana ne a kan who is more responsible a karatun Yara
A, parents
B, teachers
C kuma both.
Maryam itace mai parents.
Haka suka dunga mahawarar a tsakanin su har kowa ya kawo gaba d’aya points d’inshi.

Points d’in da Maryam ta kawo ko kai shed’an ne dole ka san itace winner! Danhaka ya bawa group d’inta 10/15
ragowar groups biyun kuma ya basu 6.
Bayan sun koma seats d’insu sun zauna ya tambayesu ko “akwai mai question”,
sukace “a’a”hakan yasa ya tattare books d’inshi, ya duba time table yaga sai Friday shida ya sake shigowa ajin. Daga haka ya yi musu sallama ya fita.

Ai kuwa kamar jira sukeyi yana fita kowacce ta hau tofa albarkacin bakinta, wasu su ce balarabe ne wasu suce d’an India wasu kuma pakistan, gashi daga ganin sa ka san d’an masu kud’i ne! Nan ajin ya haukace da zancen sa har sai da malamar next period ta shigo tukunna aka samu ajin ya nutsu da zancenshi.

Kafin kwana biyu, gaba d’aya makarantar ta d’au zancen copper Abba balarabe (sunan da suka saka mishi kenan)
Hatta junior section ba’a barsu a baya ba, masu love letters suma yi suke yi su je su zira ta saman glass d’in motasa
Inda yake d’an bari kad’an a
zuge saboda iska ya d’an dinga shiga.

Zainab tun ranar da ta fara ganinsa ta haukace bata da labari sai na Abba, hannuta kuwa kullum da kalar design d’in da za ayi da biro a cikin heart d’in a rubuta ‘Abba’
duk inda kuwa akace Fridays Mondays ko Tuesdays ( ranakun da suke da English kenan) hakanan za ta rambad’a kwalliya ta yi skipping assembly kuma, dan kar a goge mata.

Kamar yadda y’an makaranta suka haukace da ganinsa hakanan shima zuciyarsa ta haukace tunda ya ga Maryam.
Yau satin sa biyu da fara koyar da su kuma zuwa wannan lokaci kam ya gama fahimtar son Maryam yake yi domin kuwa tun ranar farko daya ganta ya rasa nutsuwarshi gaba d’aya bashi da burin da ya wuce yayi ta ganinta, har Allah Allah yake ranar da zai shiga ajinsu ta yi ya samu ya sake sakata a idanunsa.

Through out this week ko me yake yi kawai tunanin ta yake yi. Ganin da yayi yana b’atawa kanshi lokaci yasa kawai ya yanke shawarar gaya mata in his next period, dukda kuwa yana fargabar mai amsarta za ta kasance, duba da yanayin k’arancin shekarunta amma kuma ya san ‘a bari ya huce shi ke kawo rabon wani.’

Yau Monday!! kasancewar Abba ba’a staff quarters yake da zama ba..gida ne guda mahaifin shi ya siya mishi saboda service d’in da aka turo shi…ya sanya ya tashi da sassafe dan baya son ya makara, kuma akwai d’an tazara tsakaninsu da makarantar.
Har yayi wanka yayi breakfast yana murmushi jifa jifa shi kad’ai, kawai idan ya tuna zai ganta yau sai yaji wani farin ciki ya lulllub’eshi .

Duk saurin shi kuwa sai da aka gama assembly tukunna ya samu ya zo. Zainab yau sneaking ta yi bataje assembly ba saboda ta shafa jambaki da powder ga kwalli ta saka kuma ta san indai aka ganta to punishment ne bayan an sakata ta goge.

Y’an aji suna fara shigowa suka ganta a zaune, wata classmate d’insu ce tace “wato yau sneaking kika kuma yi ko?Hmm bai ma fa san kina yi ba! Dan ko kallonki baya yi.”
Dariya tayi kafin ta sake cewa “tou shadow sai ki rubuta sunan y’ar uwarki, a cikin masu sneaking in dai ba son kai bane abun”
Ta yi maganar referring to Maryam.

Ko gama zama ba su yi ba Abba ya shigo ajin hakan yasa zainab ta had’iye masifar da ta taso mata take shirin juyewa classmate d’in tasu tahau murmushi tana kallonsa.

Cikin dabara ya kalli wajen zaman Maryam yaga tana goge wajen zaman ta da duster kafin a hankali cikin nutsuwarta ta zauna sannan ta fara yiwa Zainab magana a hankali…
Ajiyar zuciya ya sauk’e a hankali sannan ya amsa gaisuwar da suka shiga yi masa.

Bayan ya kammala duk abunda ya kamata yace dasu “su ciro takarda zai yi test”.

Hakan kuwa aka yi….
Lokaci yana cika ba tare da ya b’atawa kanshi lokaci ba ya kalli Maryam yace “ta tattare gaba d’aya papers d’in ta kai mishi office.”
Sai da ya ga fitarta tukunna ya bi ta a baya.
Jin kamar mutum a bayan ta yasa ta juyo, ganin shine ya sanya ta d’an tsaya sai da yayi gaba tukunna ta bishi a baya saboda daman ko taje Admin d’in sai tayi tambaya tunda ba sanin office d’insa tayi ba.

Office d’inshi kusan shine na k’arshe a jerin k’ananun offices d’in da suke wajen…suna zuwa ya saka hannu cikin aljihun wandonshi ya zaro key ya bud’e ya tura ya shiga sannan a hankali yace mata “Bismillah”.
Sallama tayi ta shiga…office d’in d’an k’arami ne, sai dai ya had’u sosai, sai
k’amshi yake fitarwa, ga wata k’ofa a gefe wanda tanada tabbacin toilet ne….
Maganar sa ce ta dawo da ita daga duniyar k’arewa office d’in nasa kallo data tafi, jin yana cewa
“Zauna mana, ga seat.”
A hankali ta ajjiye takardun a kan tebur sannan ta girgiza kai ta juya za ta fita taji yace
“I order u to sit.”
Sai da tayi kusan 1 minute sannan ta zo ta zauna kan kujerar da take facing tashi benci ne kawai a tsakaninsu.

Sai da ya d’an sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “from which state are you ?”

“Kano”
ta bashi amsa.

“Which area??”

“Gandun albasa”
Ta fad’a a tak’aice.

“Are u sure?”
Yai mata tambayar kafin yace
“cos banga alama ba, at all”

Da mamaki ta kalleshi, kafin tace “U too”
Sannan ta mik’e tace
“Please sir zan tafi muna da test.”

Mik’ewa shima yayi yana murmushi kafin yace “sai yaushe? Ba kiyi mini kwatancen gidanku ba balle in kawo miki ziyara idan an yi hutu, ko bakya so in zo???“

Da sauri ta d’aga mishi kai
alamar ‘eh’.

With surprise yace
“Y”

“Nothing”
Kawai ta iya ce mishi sannan ta sunkuyar da kanta k’asa, tana adduar Allah yasa ya bata izinin tafiya, dan bata san daliliba in dai suna waje d’aya ji take tamkar zuciyarta za ta
faso k’irjinta ne ta fito waje, tsabar bugawa.

Abba fahimtar da yayi kamar yana yin komai cikin sauri..kar kuma yaje ta k’i shi idan taga zalamarshi…hakan ya sanya ba dan ya gamsu da shawarar da zuciyarshi ta bashi ba kawai ya bata izinin tafiya.

Ai kuwa da sauri ta juya ta fita a office d’in.

Zama yayi a kan kujerar sa, sannan ya bud’a hannunshi kafin ya kaisu duka biyu bayan k’eyarsa kamar zai yi filo da su…
Lumshe idanuwanshi yayi sannan ya fara tunanin duk wani possible hanya da zai b yayi getting close to her, dan ya lura he needs her attention first.

A bakin Admin block d’in taci karo da Zainab tana ta faman kai kawo, tana hango ta kuwa ta iso tana tambayarta inda office d’in nashi yake..kwatance Maryam d’in tayi mata daga haka tayi gaba, bata san ya sukayi ba....


A b’angaren Abba kuwa, a da
k’arfe 2 yake tashi ya tafi gidanshi, amman yanzu voluntarily yayi exceeding time d’inshi har 10 pm (Time d’in tashi daga night prep) ko tsoron hanya baya yi, hakanan
yacewa mai principal kawai zai dinga supervising evening and night prep, Friday kuma zai samu aji ya dinga k’ari a sms. Da murna kuwa principal d’in ta yarda, dan yace ba sai an bashi ko sisi ba.

Kasancewar Maryam shadow ce ya sanya ba a ajin su take night prep ba, a jss2 take zama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login