Showing 39001 words to 42000 words out of 124668 words

Chapter 14 - So Da Buri Book 1 Hausa Novels by Humaira Bulama.txt

25 Sep 2025

2307

tace “ba damuwa.” Ta juya ta fice.
Ko kayanta su Shuwa basu bari ta koma hostel ta d’auko ba, cewa suka yi ‘Zainab ta taho mata da shi’. Hakanan tana kuka tana komai suka shiga mota aka ja aka yi gida da ita.

Zainab kuwa yau farin ciki a wajenta ba a cewa komai, murna takeyi ai tunda Maryam ta tafi to fa duk wata hanya da zata bi sai ta bi ta cusa soyayyar ta a zuciyar Abba, kasancewar yau suna da period d’inshi daman yasa tun kafin su k’arasa class ta tsaya ta wanke fuskarta a tap, akayi y’an shafe shafe, k’awayen ta suka duba suka tabbatar mata tayi kyau tukunna aka nufi class ana tunanin hanyoyin da za a bi a karkato da zuciyar Abba gareta!
Sai dai kuma har period d’inshi ya shiga ya fita bai shigo ajin ba, washegari ma haka….ahaka suka shafe kusan sati babu Abba babu alamar shi.
Zainab har office d’inshi taje ta tarar a rufe….haka ta dawo jiki duk ba kwari zuciyarta ta a cunkushe, haka take rayuwa a makarantar gaba d’aya komai baya mata dad’i, sauk’inta d’aya ma ba Maryam.

A b’angaren Maryam kuwa tun da suka shiga mota take kuka har suka isa gida, a tunanin ta za a yi mata fad’a ko duka amman ba wanda yace mata komai, amma fa ko gaisheda Shuwa ko Madu tayi a cikinsu babu mai amsa mata, ko suna zaune idan ta zo ta zauna to zasu tashine su bar mata wajen, hatta Bilkisu da suka shak’u sosai a duk lokacin da Shuwa ta gansu tare sai tazo ta d’auketa ta kuma hau yi mata fad’a, tun Bilkisu tana kulata a b’oye har ta daina saboda a d’aki Shuwa take sakata ta kunna mata kallo, ko girki an daina girkawa da Maryam a gidan! A wajen mutum d’aya kawai take samun sauk’i itace Baabaa Talatu dan a gidan ta ma take cin abinci sai kuma Ya Usman wanda yake wani sabon shige mata kwana biyun nan ta kasa gane mishi kwata kwata, itafa ko ba Abba ba zata auri Ya Usman ba! She is not suppose to be feeling this towards Ya Usman amman she can’t help it, kawai ita all she knows bata sonshi kwata kwata bata sonshi ba zata iya zaman aure da shi ba.

Yau satinta d’aya da kwana d’aya da dawowa daga boarding, gaba d’aya duniyar ta yi mata zafi, zuwa yanzu rashin kulata da iyayenta sukeyi ya fara bata tsoro dan har ta rame ba kad’an ba.
In ba wajen Baaba Talatu taje ba tou kullum tana d’aki ita d’aya.
Yau ma ganin shiru zai haddasa mata wata damuwar bayan wadda take ciki ya sanya ta yanke shawarar fita dan shan iska ko ta samu ta d’an ji sauk’i.

Hijabinta ta d’auka ta nufi wajen Baaba Talatu, tana shiga a babban tsakar gidan ta had’u da Ya Usman tare da wani Abokin sa suna hira yana ta dariya, ta dad’e bata ga dariyar sa irin haka ba, tun kafin ta k’araso taji yana cewa
“To kai ba ka tsaya wasa ba?! Kawai ka jira zan baka y’ata ta farko”
Magana Abokin yake mishi amman bata ji sosai sai dai taji kamar yace “Ranar juma’ar nan ne wai da gaske?”.

Ita dai bata gane me suke nufi ba ta zo ta gaishesu.

Sai a lokacin ma Ya Usman ya lura da ita, Abokin ne ya amsa yana cewa “uwar gida ya gida?” Da kyar tace “Lafiya” Dan in Abokanan Ya Usman suka ce mata uwar gida duk sai taji wani iri, shiyasa bata tsaya biyewa tsokanarta d’in daya shiga yi ba tayi wucewarta cikin gida.


Ta isa k’ofar Baaba Talatu kenan har zata tura taji suna magana, sai da ta kara kunnenta tukunna ta gano ita da Ya Jamilu ne…mamaki da murna takeyi a ranata tace “yaushe ya dawo?”.
Har ta fara k’ok’arin shiga sai kuma taji maganar da yake yi daga ji ran shi a b’ace yake dan yana maganane cikin d’aga murya…
“Habaa Baaba! Yanzu abunda za a yi an kyauta kenan??? Shi fa Usman d’in da kansa yake ce mini tace ‘bata sonshi’!
Garin son sake k’ulla zumunci sai kunje kun yi abinda zai tarwatsa komai!!
Ku kanku fa kun san halin Maryam tun tana Yarinya tanada mugun taurin kai!! Ya kamata ku fahimci tunda har tace muku a yanzu wanchan Yaron take so to shi d’in take so a yanzun!
Amma baku tsaya kun yi nazari ba, tashi d’aya kun rabota da shi sannan kuma kawai rana tsaka kun zo kun ce zaku d’aura mata aure wannan juma’ar ita da Usman?? Idan wanchan Yaron ne bakwa so kwata kwata ai at least dai kwa bari idan ma auren ne ita da Usman d’in ya kamata a bari su sake fahimtar juna, dan wallahi idan aka yi auren nan bata sonshi a haka a wannan yanayin da take ciki to ba zata tab’a son shi ba.”

Baba Talatun ce itama ta rufeshi da fad’a tana cewa
“To ubana!!! wanda ya san salon so! Yaushe aka haife ka ne Jamilu??
Bari kaji….rud’u ne yake damun Maryam amman ba wani Abba da takeso ni na san Usman take so, kuma bari kaji, ko da ace bata auri Usman ranar Juma’ar nan ba to tabbas Abban ta zai aurar da ita a sadaka ranar dan yayi wannan alk’awarin, furucin nasa ne ma ya sa Babanku yace ‘ga Usman’ to kaga ai taimakon tama zai yi! Wai dan ma ban ce d’a na ba zai auri ragowar wani ba!?”

“Haba! haba!! Baaba, bai kamata ku yarda da zancen su Zainab akan Yarinyar nan ba fa, idan y’an layi suna yamid’id’i kema sai ki biye su? Maryam fa kamar y’a take a wajen ki, kuma kin san basa shiri da Zainab dama.”

Da sauri Baaba ta karb’e tana cewa “Ai Maryam bata d’aukeni uwa ba tunda gashi k’iri k’iri tana so ta guji Usman. Kuma kana nufin dan basa shiri da Zainab d’in za ta k’ulla mata sharrine??”

Ji tayi Ya Jamilu yaci gaba da magana “Ni dai in za ‘a j....”

Maryam kasa tsayawa ta cigaba da jin maganar tasu tayi. Zuwa yanzu ta fahimci komai, tuni fuskarta ta jik’e sharkaf da hawaye da uban gumi…nan da nan ta fara ganin dishi dishi! Da gudu ta fita a gidan ko bi ta kan Ya Usman da yake kiran ta bataiba!
Taya mahaifinta wanda yake masifar sonta zai yi sadaka da ita??? lalle kuwa zata kashe kanta, wato sun yarda da maganar mutane akan ta kenan?….
Da wannan tunanin ta isa gida tana shiga falon sukai kicib’us da Madu wanda yake shirin fita ..
Goge hawayenta tayi sannan ta durk’usa a gaban shi ta hau magiya “Abba dan Allah ka yi hak’uri, na rantse da Allah sharri aka yi mini, wallahi Abba bana son Ya Usman, kar ka aura mini shi dan Allah…”

Zagayeta Madu yayi ya wuce ya fita ba tare da yace mata komai ba. Mik’ewa ta yi ta nufi Shuwa wadda ta fito daga kitchen yanzu itama ta fara yi magiya tana “Hajiya dan Allah ki kulani yau, ki yarda dani wallahi sharri aka yi mini, baba son Ya Usman kar ku yi mini auren dole, wallahi k’arya su Zainab aka yi mini! Yanzu kin yarda da abinda suka ce??”

Da sauri Shuwa tace
“Na yarda!!! Duk wani abu da aka fad’a na yarda, ko da ace zuciya ta tana son k’aryatawa, to zan tirsasa mata in tilastawa kaina in gasgata hakan ne.
Tunda har zaki iya k’etare umarnina! Maryam a nan”
Ta yi maganar tana nuna k’ofar kitchen, sannan ta ci gaba “A nan na zaunar dake nace miki ki rabu da wannan Yaron, kika nuna mini kin amince, amman saboda kin raina ni, ban isa in baki shawara ki d’aukaba, kuma ki nuna ban isa dake ba shine kika ci gaba da kulashi!!
Jiya principal d’inku duk sai da ta fad’a mana komai har yadda yace “yana son ki a gaban kowa da yake shi bashi da kunya ke kuma kika biye masa bayan kin san da zancen Usman!!
Daman na riga na gama yanke shawarar ko ba a kore ki ba to baza ki ci gaba da zama a makarantar ba!
Maryam kin bani mamaki matuk’a wallahi, banyi tunanin haka daga gareki ba sam,
kuma nima zan baki mamaki, dan wallahi idan baki tsaya kin auri Usman ba to ki saka a ranki babuni babu ke!
Idan taurin kai kike tak’ama dashi ina so ki san cewa a wajena kika gada!
Da ni dake aga wanda zai janye.”

Kuka Maryam ta sake fashewa dashi, ita kuwa Shuwa ta wuce tayi hanyar d’akinta ta barta a wajen…Bilkisu ce ta zo tayi ta lallashinta har aka samu ta d’an yi shiru ta tashi suka tafi dakinta.

Haka ta wuni har dare sukuku, tana d’akin taji Baaba Talatu ta shigo tana tambayarta, wai “Usman yace mata d’azu taje ta lab’e mata ita da Jamilu”
Shuwa ce tace
“Ai yanzu Maryam komai ma akace tayi ba zan musa ba, kiji fa har da lab’e ta koya, tabbas ta yi kam dan nan ta shigo tana ta faman yi mana haukan k’arya….”
Nan dai Shuwa ta hau labarta mata yadda sukayi d’azu…

“Allah ya kyauta”
Baaba Talatu tace.
Daga nan suka hau shirye shirye.

Bayan sun gama ne taji Baaba
Talatu tana cewa “bari ta lek’ata kafin ta tafi, da mugun sauri ta shige bargo ta hau barcin k’arya, tana jinta ta lek’a har fuskarta tana cewa “Ashe ma tayi barci”
Ita dai bata kula taba har ta juya ta fita, dan ita yanzu Baaba Talatu ta fara bata mamaki, k’iri k’iiri take nuna son y’ay’anta, sab’anin su Shuwa.

Da daddare tana daki ta idar da sallah abun duniya ya mata yawa, ita ta rasa ta gudu ne ko ta tsaya bama ta san ta Ina za ta fara ba amma idan akawai abunda yake da yak’ini akai
shine ‘ko sama da k’asa zasu had’e ba zata tab’a yarda da auren Ya Usman ba!!’ Idan ta yarda kenan tama karb’i laifin sharrin da aka k’ala mata ta yarda ta yi d’in kenan!!!Shigowar Shuwa ne ya katse mata tunani.
Da sauri ta mik’e ta hau gaisheta, bata amsa mata ba kawai ta juya tace “kije parlourn Abban ku yana son ganinki.”
Daganan ta sa kai ta fita.

Ninke sallayar Maryam tayi ta bi bayanta ta nufi parlourn Abban nasu.

Tana shiga ta sameshi yana shan shayi, da Al’Qurani a hannunshi…sai da ta jira ya kai aya ya rufe sannan ta gaida shi…cikin kulawa ya amsa mata kafin ya ce “Maryama.”
A hankali ta amsa kanta a k’asa.
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya fara magana cikin nutsuwa…
“Ki sani ko da ace duk duniya zasu yarda da abinda akace a kanki ni ba zan tab’a yarda ba.”

Da sauri ta d’ago kanta ta kalleshi wasu hawayen farinciki suna gangaro mata, bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba.
Gyad’a mata kai yayi sannan yaci gaba “na san halinki na san tarbiyyar ki, fiye da kowa.
Amman Maryam ya zama dole a d’aura miki aure ranar juma’ar nan!!”.

“Innalillahi wainna ilaihir rajiun.”
Shine abunda Maryam ta fara maimaitawa, tana hawaye sannan tace
“Abba yanzun fa kace ka yarda da ni.”

Jinjina kai yayi alamar ‘eh’, kafin yace “Tabbas Maryam na yarda dake amman kuma auren shine mafi alkhairi a tattare dake, makarantar nan da kika yi sananniyar makaranta ce, yanzu sun baki expel!! Ko kin san cewa babu makarantar da zata d’auke ki da saninsu? Sannan mahaifiyarki tace ‘ba zaki k’ara komawa makaranta ba!’ Zaman me to za ki zauna yi??
Sannan abu na biyu, ban san ya akayi zancen nan ya zagaye gari ba, amman jiya har meeting aka had’a da dattijawan unguwa, saboda ke!! Abun takaicin anan shine ba zan iya kare ki ba saboda all
evidences are against u, abunda nake tsayawa tsayin daka dan ganin al’umma basu fad’a ciki ba, yau nine ake zargin y’ata da shi...

Maryam da ace kin yi abunda ya kaiki makarantar kawai baki tsaya kula Yaron nan ba da duk haka bata taso ba, yanzu idan shekaru suka yi gaba, ba lalle ki auru ba domin kusan kaf layin nan maganarki akeyi, kuma kin san idan miji ya fitowa mace a wajen y’an unguwar su da makarantar da tayi ake bincika halayenta wanda inada tabbacin ba zasu bada shaida mai kyau a kanki ba!
Maryam hakan zai fi yi mini ciwo fiye da aurar dake da zanyi a yanzu, ko ba komai hankalina a kwance yake da Usman, na san zai kula dake matuk’a.

Ki yi hak’uri, wanda ya riga ka zama dole zai riga ka tashi, ki rungumi k’addararki, baki da wayo shiyasa aka yi saurin k’ulla miki sharrin da ba zaki iya fitar da kanki ba….”

Kukan da Maryam take yi ne ya sanya shi sak’k’owa daga kan kujerar da yake, ya shiga lallashinta da fad’a mata kalamai masu kwantar da hankali har sai da yaga tayi shiru tukunna ya sallameta, jikinta a mace haka ta tashi ta fita.

A hankali ya saka yatsarshi ya d’auke kwallar data taru a idonshi, sannan ya koma ya zauna ya jingina da jikin kujerar had’e da lumshe idanuwanshi…….

BULAMA ✍️




So da Buri
Free Book
13


Maryam tana shiga d’aki ta fad’a kan gado ta fashe da wani mugun kuka…ta kusa awa d’aya tana abu d’aya, idanuwanta duk sun kumbura fuskarta tayi jajawur!!! Sai da tayi mai isarta tukunna ta hak’ura ta shiga sauk’e ajiyar zuciya akai akai….
Kamar wadda ta tuna da wani abun ta mike zumburr!! ta nufi wajen kayanta, k’asan ta d’aga ta zaro wata farar takarda..tun ranar da Abba ya bata takardar bata duba ba, warewa ta shiga yi a hankali,
tana gama bud’ewa idanuwanta suka sauk’a kan wasu y’an nambobi a jere waenda ko ba a fad’a mata ba ta san number landline d’inshi ce.
“Lalle ma Abba!! wato ma nice zan kirashi!! despite the fact that na yi mishi kwatancen gidanmu!! he didn’t even bother to come. Sannan kuma all this time already yanada wadda zai aura ya tsaya b’ata mini lokaci……Allah ya isanaa!!”
Ta fad’i hakan a cikin zuciyarta cikin d’aci da zafin zuciya.
Jin zuciyarta tana shirin fashewa ne yasanya ta duk’unk’une takardar ta jefar da ita ta koma ta zauna a kan gado ranta yana sake b’aci.
Gaskiya Shuwa ta fad’a da tace mata “b’ata mata lokaci kawai zai yi amma yanada wadda zai aura.’ Dan kuwa gashi ashe Abba yaudarar ta yake yi ita bata sani ba, dan inda ace son gaskiya yake mata ai da zai lek’o ta.
Ganin zuciyarta tana shirin fashewa tsabar takaicin abinda take tunanin yayi mata gashi zaai mata auren dole kuma duk shi ya ja amman bai ma damu da ya san halin da take ciki ba, kuma duk yadda ta k’ok’arta ta kasa rabashi da zuciyarta! Hakan ya sanya kawai ta yanke shawarar ta d’auki number ta kirashi, ta fad’a mishi ta fa san yaudararta yayi, at least zata rage wani b’angaren na damuwa takaici da tashin hankalin da take a ciki!! kwana biyun nan.
Sai dai kuma Allah yasa yana gidan, dan ta san maybe a time d’innan yana school yanzu….
Da wannan tunanin ta mik’e ta isa inda ta yar da duk’unk’unanniyar takardar….da kyar ta iya bud’ewa dan har sai da ta d’an yage tsabar yadda ta d’unkuleta ta jefar d’azun…Haddace nambobin tayi a kanta sannan ta nufi falo. Kamar ko da yaushe landline d’insu yana kan tebur kusa da tv, kamar munafuka haka ta lek’a kitchen ta tabbatar Shuwa bata nan maybe ko ta fita ne Itada Bilkisu dan gidan shiruu, a hankali ta isa ta murza nambobin ta d’aga ta kara a kunnen ta…ba‘a wani dad’e ba aka d’aga.

“Hello who is there?”
Taji ance mata
A hankali tace “please i want to speak with Abba.”
“Ok! hold on, let me tell him.”
Mutumin yace sannan taji yana magana “Sir, someone wants to talk to you.”
Daga chan nesa taji muryar Abba yana cewa “Who’s it?”kamar bashi da lafiya
Jin muryar tasa kuwa da tayi , sai taji kamar rabin damuwarta ya kau, dukda haushin sa da take ji.
Mutumin ne ya sake tambayar ta “Ma’am pls what’s your name?”
“Maryam”
Ta bashi amsa.
Tanaji mutumin yace mishi “Maryam.”
Kafin kace kwabo muryar Abba har ta iso cikin dodon kunnen ta, da alamun har ya k’araso ya amshi wayar, muryarshi har wani rawa take yi
taji yana cewa
“Maryam! da gaske kece?
Ya kike? how is everything?
Zan zo soon, in shaa Allah…i missed you a lot!”
Ya fad’a kamar zai yi kuka wanda hakan yasa Maryam ta ji tausayinshi a d’ayan b’angaren zuciyarta kuwa tana ganin rainin hankali irin na Abba wai ‘he missed her!’ amman kuma shine ya kasa zuwa ya ganta?.

Murmushin takaici tayi sannan tace “Ai ba zaka damu ka zo ka ganni ba tunda kana da wadda zaka aura, Abba I just call saboda Ina so in tambayeka dalilin da yasa ka tsaya b’ata mini lokaci, bayan ka san an yi maka mata??”
Tayi mishi tambayar ranta yana sake b’aci.

Murmushi taji yana yi, kafin yace “Even your anger sounds sweet to me Maryam, i‘m just happy Ina jin muryar ki yanzu..”

Maryam zuwa yanzu ranta ya b’aci sosai kamar ta fashe da kuka haka take ji…
Jin tayi shiru yasa yace
“Maryam kema idan kin san kina da wanda zaki aura mai yasa kika tsaya kulani??”
Jin tayi shiru yasa shi sake maimaita mata tambayar.
A hankali tace
“Ni bana sonshi, tun farko”
Da sauri yace “nima haka wallahi
&
Inaso ki san cewa ‘ni Abba na yi miki alk’awarin ke! Zan aura duk runtsi, ko menene zai faru after that I don’t care, i‘ll choose our happiness akan koma.......”
Kukan da ta fara yi ne ya saka shi kasa k’arasawa.. nan ya fara tambayarta “mai ya faru??”
Cikin sheshshek’ar kuka tace “Abba duk wannan ba shi da amfani yanzu, da ace ka zo ka lallab’a Abban mu da duk hakan bata faru ba, amman ya....”
Cikin tare numfashin ta yace
“Maryam Yayana ne yayi grounding d’ina for 2 weeks!! Ya ma k’i ya tsaya ya saurareni kwata kwata, gaba d’aya baya kulani…

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login