Showing 6001 words to 9000 words out of 124668 words

Chapter 3 - So Da Buri Book 1 Hausa Novels by Humaira Bulama.txt

25 Sep 2025

2325

Auwal yana isa maingate ya sanar da malan iliya sak’on granpa,tsabar mugunta dubu hamsin akace ya bashi amman yabashi dubu ashirin,kayansa kuwa kala uku ya bari ya d’iba waenda ya zo gidan da su,ragowar kuwa yace “ba zai d’auka ba ai ta wajen Daddynsa ya samu ta hanyar kai gulmarsa.” Sai da ya tabbatar ya bar gidan tukunna ya k’ulle kayayyakin da ya hanashi tafiya da su ya jefar a babban garbage bin na Estate d’in, ya koma ciki abinsa.

Cike da annashuwa ya nufi wani Triplex a cikin jerin gidajen estate d’in, kamar yadda kowanne yake gate d’inshi daban da compound haka shima wannan, knocking ya yi sannan ya d’an ja ya tsaya, cikin y’an seconds wani tsohon mutumi ya bud’e y’ar k’aramar k’ofar gefen gate d’in gidan ya d’an lek’o, ganin waye a tsaye ya sanya tsohon saurin bud’e k’ofar sannan ya d’an rissina yace
“Barka da yamma.”

“Lafiya”
kawai Auwal d’in yace dashi daga haka ya kutsa kai ya nufi cikin gidan wanda yake zagaye da flowers kala kala,an shafe k’asan compound d’in gidan da interlock, ta tsakiyan compound d’in kuwa wani k’aramin roundabout ne,ta left side na roundabount d’in wani k’awataccen garden ne wanda yake d’auke da su porch swing,hammock chairs da k’ananun kujeru domin hutawa sannan ga shuke shuke kala kala, ta right side kuma parking space ne, sai ta gaba hanyar shigowa,gate kenan,
sannan ta bayan roundabout d’in kuma anan ne k’ofar shiga gidan ta main parlour take.
Kasancewar gidan a zagaye yake..idan ka wuce main door d’in ka yi hanyar baya akwai k’aramar k’ofar kitchen ta shiga kitchen da wajen wanke wanke da d’an k’aramin fili.

Yadda ginin gidan nan yake haka gaba d’ayan gidajen estate d’in suke apart from gidan granpa ,wanda ya fi kowanne girma da tsaruwa.


Karasawa yayi ya shiga y’ar k’aramar varander da aka dan zagayeta da k’arafuna da flowers,sannan ya isa bakin k’ofar parlourn ya danna doorbell.
Wata farar budurwa wadda ba zata wuce shekaru goma sha biyar bace ta bud’e k’ofar,hannunta rik’e da waya kirar iPhone tana daddanawa tana murmushi,da alama chatting d’in da takeyi ya tafi da hankalinta, dan bata ma lura da waye ta bud’ema k’ofar ba,kawai ta juya ta nufi k’aton parlourn nasu mai d’auke da set d’in kujeru uku da katon dining area ,sai staircase biyu.
Juyawa Auwal yayi ya rufe k’ofar sannan da d’an sauri ya biyota ta baya yasaka hannu ya warce wayar,
da sauri ta juyo suna had’a ido da shi ta saki wani sassanyan murmushi.

B’ata rai ya yi sannan yace “da wa kike chattn haka??”
Ya yi mata tambayar yana maida idanunsa kan wayar domin ganin da waye take chattn d’in. Zaro ido ta yi sannan da sauri ta kai hannunta kan wayar da niyyar warcewa amman sai ya yi saurin kama hannun ya rik’e da d’an k’arfi har sai da ta yi k’ara,ganin k’ok’arinsa na ya karanta mata chat ne ya sanya a karo na biyu ta sake yunk’urin karb’ar wayar tata cikin shagwabarta tace
“Ya Auwal dan Allah ka bani waya ta.”

Murmushi ya yi ganin chat d’in nata ita da wata friend d’inta ne, tana bata labarinsa, expressing how much she loves him, har tana ce mata ta fi son smile d’insa saboda hakan yana fitar da dimples dinsa,sake fad’ad’a murmushin nasa yayi sannan yace
“D’ago kanki mana ,ungo wayarki.”
Shiru ta yi,sai hannunta d’ayan da bai rik’e ba da ta d’ago da niyyar karb’ar wayar amma sai ta ji ya had’a da nashi hannun da wayar ya rik’e, da sauri ta d’ago kanta ta yi kalar tausayi tace
“Da zafi fa,ka bani wayata mana.”

Yanayin kallon da yake yi mata babu ko kyaftawa had’e da murmushi ne ,yasanya ta yi saurin mayar da kanta k’asa.

Taku d’aya ya yi ya matso daf da ita,sannan ya yi k’asa da murya a hankali yace
“Da gaske kina son dimples d’ina?”
D’aga masa kai ta yi alamar ‘eh’. Sannan ta d’an yi taku d’aya ta yi baya
Sake takowa ya yi kamar d’azun ya matso da gefen fuskar sa kusa da tata yace “Tou bara in goga miki,kema ki zama mai dimple, kinga sai mu Haifa Yara masu dimples hud’u.”
Yayi maganar yana matso da gefen fuskarshi har yana gogar kumatunta,ba ta san ya akayi ba kawai ta ji ya sakar mata light peck a gefen fuskartata,
tana k’ok’arin matsawa taji ya yi saurin ruk’ota ta hanyar rik’e mata gefen cikinta.

“AAIMA!!!”
Suka ji an fad’a cikin tsawa,
Da sauri ta juyo,a tsorace.

Karkarwa jikinta ya fara yi sakamokon had’a ido da tayi da yayaynta ransa a mugun b’ace.
Sak’k’owa ya fara yi daga benen cikin sauri mai had’e da d’an gudu,yana tafe yana k’ok’arin kwance belt d’in jikin wandonsa, kafin ya k’arasa sak’k’owa kuwa har ya k’arasa zaro belt d’in ya rik’e ta a hannunsa,gadan gadan ya yi kansu.
A take Aiima ta fashe
da kuka tun kan a daketa,ta fara kiran “Mammy!!” da k’arfi.

Mammy da anty Adama da suke kitchen ba su ji shigowar Auwal ba amman tun lokacin da ARSHAAD ya kwala kiran Aiima sukaji suka fito da saurin su.
Ganin Arshaad ya yi kan Aiima da belt ne ya sanya Mammyn k’arasowa da sauri ta shiga gabanta ta tsaya tace”Arshaad meye haka?lafiyarka kuwa?”

Anty Adama kuwa ganin Auwal a tsaye yasa ta kafeshi da idanu kafin ta ce”mai ya faru?”
Sai a lokacin ma shi Arshaad ya lura da Anty Adama a wajen dan gaba d’aya idanunsa sun rufe ransa ya yi mugun b’aci!! Ya so ace yau ya damk’i Yarinyar nan wallahi da sai yayi mata mugun dukan da sai ta yi jinya tunda ya lura kunnen k’ashi gareta kuma ta raina shi, ba sau d’aya ba ya sha ja mata kunne ya hanata shiga harkar Auwal amman ta k’i yarda inda ace Aslam ne ya yi mata magana ya san da tuni ta bari……
Maganar Anty Adama ce ta katse masa tunani,jin ta sake cewa “Wai kai Auwal ba da kai nakeba?mai ya faru wai?me kuka yi mata take kuka??”
Saurin katse ta Auwal yayi yace”Nooo,Mom bani baneba!!”ya yi maganar cikin d’aga tafukan hannayensa biyu kamar za a yi arresting nashi yana tab’e baki,alamun shi fa ba ruwanshi,kafin
ya ci gaba da cewa “ta yaya zan sakata kuka? Zance na zo
fa.
D’azu da muka yi waya da ke kika ce mini kun dawo,shine nace bara inzo in ganta kuma in gaida Mammy,kin ganni daga office wallahi ko wanka banje na yi ba na zo nan mu gaisa,shine fa yana hango mu tare ya zaro belt ya yo kanmu zai dakemu!”

Kallon mamaki Arshaad ya tsaya yana yi mishi ganin yadda ya d’aure sa da jijiyoyin jikinsa,dukda kuwa yadda ya san halin Auwal sarai na iya juya al’amari….haka yake tun suna Yara kamar mace wajen iya makirci,kaf cikin mazan estate d’in sai da ya san yadda yayi kutun kutun ya kawar da kowa ya zama na right hand d’in granpa,yanzu haka shine MD , granpa ya d’aurasa a kan komai saboda shi sai end of the month yake shiga office , ko kuma in akwai Manyan Bak’in da suka zo ya kanje ya gansu, ko kuma wani important meeting,shima still Auwal d’in yana nan manne da shi baya barin kowa ya je jikinshi sosai, idan ma ya ga kuna shiri da granpa d’in to sai ya san yadda yayi ya had’a maka gurmi an maka fata fata.

“Wai Arshaad sai yaushe za ka bar wannan mugun abu daka d’aukarwa kanka ne?”
Ya ji muryan Mammy cikin fad’a, da alamun maganar Auwal ta yi tasiri akanta har ta kai ga b’ata mata rai.
Anty Adama ce ta kalli Arshaad da duk kunyarta ta rufesa,gashi shi mutum ne mai kawaici ba zai iya fad’i a gabanta abinda ya ga Auwal d’in yayi ba .
Takowa ta yi ta zo gaban sa ta tsaya sannan ta sa hannunta ta kamo nashi, cikin yin k’asa da murya tace
“Son, please ku zauna lafiya kai da d’an uwanka mana,kowa yana son had’in nan nasu shi da Aiima ko dan zumunci ya k’ara k’ulluwa, but if there’s anything da kake gani ya sanya baka san Auwal d’in a tare da sistern ka just name it,I promise zanyi putting into consideration and if kanada gaskiya I’ll support u 100%.”

“Bafa shi da wani reason da zai baki,kawai ke kin san halinsa ai tun suna Yara ba shiri sukeyi ba,abu kad’an sai fad’a,shine har yanzun basu san sun girma ba!!!ki barni da shi na san maganin sa”
inji Mammy.


Ganin bashi da niyyar yin magana ne yasanya Anty Adama ta cika hannunsa ta kalli Auwal tace masa “lets go””Mammy za mu k’arasa tattaunawa a waya.”

“Ok” kawai Mammy tace mata…bayan sun fita ne ta maida hankalinta ga Aaima wadda ke durk’ushe a k’asa har yanzun tana gunjin kuka,
Kamo ta tayi ta mik’ar sannan tace mata “goge hawayenki,daina kuka kinji auta wuce ki tafi d’akin ki.”

Da saurinta ta zo ta wuce ta gaban Arshaad dan gani takeyi kamar zai kamota.

Juyowa Mammy tayi ta kallesa sannan tace “Ko ba komai ni na haifeka atleast idan ka so abunda nakeso zan ji dad’i,ko dan Adama da zumuncinmu ya kamata ace ka yi hak’uri ka zauna lafiya da d’anta.
Dukda na san taurin kanka da kuma yadda ka raina ni ba lalle ya bari ka yi abinda nakeso ba
amman ni dai ba zan gaji da fad’a maka gaskiya ba.”

tana gama fad’in haka ta wuceshi…har ta d’an tsaya kamar za ta sake yin magana sai kuma ta juya ta nufi hanyar kitchen,suka barshi a tsaye a wajen.....




Su Auwal suna shiga main parlour ya yi hanyar staircases d’in da yake a hannun dama,da alama ata nan side d’insa yake.
“We’re not finished.”
Ya ji muryan Mom d’insa.

Juyowa ya yi ya kalle ta sannan yace “Let me freshen up first,Ina zuwa .
Ya fara hawa stairs d’in da d’an sauri.

“What did u do??”
Ya ji ta sake tambayar shi.

“A peck.”
kawai yace mata, da ga haka ya ci gaba ta tafiyar sa ba tare da ya juyo ba.


BULAMA✍️




So da Buri
Free Book
04

A nan ya tafi ya barta a tsaye kamar wata statue, kana ganin fuskarta ka san ranta a b’ace yake, ita sam! ta kasa gane kan Auwal kwata kwata,bata son halayyar nan tashi, kalli yanzu k’iri k’iri ya had’a uwa da d’anta fad’a, shikuma Arshaad ta tabbata kunyar ta ce ta sanya ya k’i cewa komai,gashi
Daddy ya rok’eta akan dan Allah su taru ita da shi su dinga rufama d’ansu asiri…shi kad’ai Allah ya basu su daina yayata wasu halayyarshi da kansu a cikin family, domin kuwa duk ranar da aka yi rashin sa’a granpa ya ji to tabbas kashin Auwal ya bushe….
Tana cikin wannan tunanin ta ji an dafa ta…tana juyowa suka had’a ido da Mijinta Alhaji Yusuf MT
murmushi ta yi kafin tace
“Daddy yaushe ka dawo?”

Sai da ya d’an k’ura mata ido kafin yace “Auwal ne ko?”

Murmushin ta sake yi sannan tace”amsa tambaya da tambaya, are we??”

Sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya ya yi kafin ya fara magana”Ta windown kitchen na hangoku Ina waya da doctorn ABBA, shine na fita ta k’aramar k’ofa na rufe na tsaya a k’aramin compound saboda bana son Auwal ya ji ni.
Kin san yadda suke shi da granpa,ba k’aramin aikin sa bane ya kwashe komai ya fad’a mishi
Tunda ya san in dai da granpa a case babu abinda zan iya yi masa.”
Shiru yayi da alamun damuwa a kan fuskarsa kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yace
“Adama akwai matsala fa, don sun sake yin wani fad’an da granpa har ya ma fi na last time, sannan shi kuma ya sakawa kanshi damuwa over gashi yanzu har ya kusan shiga next stage.”

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”shine abinda Mom tace idanunta suna kawo kwallah kafin ta kalle sa sosai tace
“To ai ni da ka bari Auwal d’in ya ji ya fad’a ma granpa d’in watak’ila hakan ya sanya shi ya d’an sauk’o daga fushin.
Na ga kwana biyun nan ma ai kamar yad’an yi sanyi ai ba kamar da ba,ko?”

D’an murmushi Daddy ya yi tukunna yace”babu fa abinda ya chanja daga halin granpa,kawai dai kwana biyun ba a samu wanda ya tab’o sa bane ba shiyasa kika ji shiru…d’azun fa malan iliya ya kirani ya ke ce mini Auwal ya fatattake sa,da na tambayi drivern granpa d’in yace mini shi granpa d’in ne yace a kori mallan iliyan d’azu daga dawowarsu daga meeting,wai dan ya bar bakin main gate ya tafi siyan agwaluma.”

“Allah ya kyauta”
Shine abinda Mom tace, sannan ahankali tace “wai menene ma to abunda ya taso da fad’an nasu shi da Abban??
daa fa har muna murnar almost 2 years lafiya k’alau tsakaninsu,shima kuma Abban ciwon nasa ko tari babu.”

Sai da Daddy ya d’an furzar da numfashi tukunna yace”Wai mafarkai yakeyi da Maryam! da jariri a hannunta,tana kuka tana cewa ya zo ya taimaketa, abun ya kai 3 months yace kullum in ya kwanta sai yayi shinefa ya d’aga hankalinsa…
Da farko,Dad ya samu ya fad’a mishi. Shikuma Dad yace mishi ya yi ta addua kawai…
shine fa tsabar ganganci kawai ya je ya tunkari granpa da maganar..
akan wai yana so yaje ya ganta,ya tabbatar babu Yaro a tsakaninsu,saboda mafarkan da yake ta yi.”

Ba shiri Mom ta zaro ido waje sosai kafin ta yi k’asa da murya tukunna tace”me granpa d’in ya ce??”

“Cewa za ki yi me ya yi masa,ba me yace ba!
In banda abun Abba kai da ka san mutumin nan yanata fushi da kai for morethan 24 years ko ga miciji ba kwa yi da shi, amma shine zaka kwashi k’afa ka je ka tunkare sa da irin wannan zancen?
Ni wallahi Adama nima na fara tunanin ko dai asiri ne matar nan ta yi masa,saboda ki duba kiga yadda he’s willing to risk everything just to talk to her again. Dukda irin bak’ak’en maganganun da ta dinga rubuto masa har da fa threatening nashi da kotu fa ta yi…
Daga k’arshe fa idan ta aiko da sak’o ba ya nuna mana! daina nuna mana yayi ni da Dad
Allah kad’ai ya san irin maganganun da suke a ciki
Shikuma a wannan lokacin kullum cikin bata hak’uri yakeyi yana aikawa.
Da kyar granpa ya samu ya rabasu, shine yanzu yake son tada zaune tsaye, shi ko ta jikinsa da lafiyarsa ma bayayi, gashi yanzu granpa ya yi masa horo mai tsanani…..
..Kinga da farko ya sallame shi a duk wani company da kika sani namu a yanzu babu Abba a ciki,sannan ya hanashi share d’inshi. Kuma ya bashi notice akan ya bar masa estate d’inshi kar ya k’ara ganin shi ko y’ay’ansa.
Yace kuma duk wanda ya bashi hak’uri sai ya had’u da tsananin b’acin ranshi,hatta gramma.”

“Ya subahanallah”
shine abunda Mom ta fad’a
sannan a hankali tace “bara inje wajen Zainab.”

“To” kawai yace mata ya juya ya nufi dining area ya nemi guri ya zauna ya fara zuba abinci,
kana ganin fuskarsa ka san yana cikin matsananciyar damuwa.


Fitowa ta yi tana zancen zuci ta k’arasa bakin gate sannan ta fita ta k’aramar k’ofa,ta nufi d’aya daga cikin gidajen tana d’an sauri,tana isa tayi knocking,kamar kowanne gida nan ma mai gadi ne ya zo ya bud’e mata,ya gaidata ta amsa sannan ta shiga.
Tana shiga ta hango wata k’atuwar moving van ga jakankuna a ajiye a waje da boxes, sannan ana ci gaba da fitowa da wasu.
K’ara saurin tafiyar tata ta yi ta nufi hanyar k’ofar shiga main parlourn wadda ke nan a wangale anata shige da ficen kwashe kaya.
Da sallama a bakinta ta shiga,
tana shiga ta hango wata farar mata zaune a kan 2sitter na d’aya daga cikin jerin kujerun falon,matar ta zabga uban tagumi,kana ganin ta ka san tana cikin damuwa sannan tayi nisa a tunani.
K’arasawa Mom tayi kusa da ita sannan ta dafa ta,ganin kamar ma ba ta san ta dafa tan bane ya sanya ta kira sunanta”Zainab!“
Firgigit!! Ta yi ta juyo,suna had’a idanu da Mom kuwa kamar jira takeyi ta fashe da kuka,sannan ta kamo hannayenta duka biyun kafin ta fara jujjuya kai ahankali tana kallonta tace “Adama inata kiranku yau kwana biyar wayanki baya tafiya,komai ya zo mini k’arshe
kashina ya bushe!! I never saw this coming!!
Shikenan na san yanzu zai yi finding out kum......”

Mom bata bari ta k’arasa ba ta yi saurin zare hannunta wanda ta rik’e ta yi amfani da shi
wajen toshe mata baki sannan ta juya tana kallon falon tana rarraba ido cikin fargabar kar wani ya jiyoso.
Ganin da ta yi ba kowa a falon masu kwasar kayan ma duk sun gama na k’asa sunyi sama ne ya sanya ta kamo d’ayan hannaunta da har yanzu yake cikin nata ta mik’ar da ita sannan ta jata suka nufi d’aya daga cikin d’akunan parlour.

Sai da Mom ta tabbata ta saka key,tukunna ta juyo tace
“Yanzu menene abun yi?”
Share kwallarta Zainab ta yi sannan tace “Granpa ya koremu shiyasa kikaga anata kwash..”
“Na sani“ Mom ta katse ta
sannan tace “Daddy ya fad’a mini komai.”
Shiru Zainab tayi, sannan ta jingina da bango ta d’aga kanta sama ta rufe idanunta a hankali tace “In dai muka bar gidan nan,kin san cewa babu abunda zai hana Abba bibiyar Maryam ko?
Saboda ya kasa yarda da takarda har yau,kin san
cewa ko a kwanakin baya dama na gaya miki Ina ganin kokwanto a fuskarsa….ita kuma mayyar gashi yanzu har a mafarki zuwar masa takeyi.”

Bud’e idanunta ta yi ta kalli Mom sannan ta ci gaba da cewa “4 days ago fa yana tashi yace shi wajenta zai je, ya gaji da wannan mafarke mafarken,da ya je wajen granpa suka yi fad’an nasu da suka saba,dan bai samu an goya masa baya ba shine tun a chan ya zube,sai kwasar shi aka yi ,akai asibiti da shi.
Kwanan mu d’aya da wuni bai san inda kanshi yake ba ana fama.”
Shiru ta yi kafin ta ci gaba da cewa “Adama granpa shi kad’ai yake iya takawa Abba burki akan Matar nan yanzu ya bashi freedom!!Saboda wannan abun fa da akayi da
granpa da mutane ne suke ganinshi as punishment amman a wajen Abba freedom

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login