Showing 3001 words to 6000 words out of 124668 words

Chapter 2 - So Da Buri Book 1 Hausa Novels by Humaira Bulama.txt

25 Sep 2025

2319

tsayuwarta tare da nad’e hannuwanta akan k’irjinta irin ina jinki d’innan.
Kallon ta Mama ta yi sannan tace”yanzu Jalila saboda Allah dukan da kike sakawa yayanku Ja’afar yana yiwa y’ar uwarki ba tare da hakkinta ba kina ganin ya dace kenan? Ke kenan kullum ba za ki ja k’anwarki a jiki ku zauna lafiya ba?
Ki duba fa
saboda Atule d’in fa da kike sakawa Yara suna yi mata kullum hakan ya sanya dole Babanku ya chanza mata islamiyya aka maida ita ta dare da asabar da lahadi na safe.
Yarinyar da ta taso da k’aunarki acikin ranta kina k’ok’arin maida mata rayuwa kurkuku?Meyasa kike hakane Jalila?mai ya faru kika chanja?”

Umma ce ta hankad’o labule ta fito daga dakinta cikin masifa tace
“Kawai kinga munafuka ki fito fili b’aro b’aro kice tunda na dawo gidan nan na chanjata,akan wanne dalilin za ki tasa mini y’a a gaba kina wani cewa ta chanza hali? To bari kiji in gaya miki Allah ne ya tsameta a cikin munafukai ya dawo da ita cikin masu gaskiya,kuna abu simi sumi da ke da y’arki nankuwa kunfi kowa iya munafurci da cin dunduniyar mutum!.”
Juyawa Mama ta yi ta kalli Jalila wadda ta ga ta yi shiru tana kallon gefe kamar bata wajen,a tunanin Mama nutsuwa ce ta zowa Jalilan,
Juyawa tayi ta kalli Umma wadda har yanzu take fad’a baki da kumfa tace mata
“kinga Sadiya ba dake nake ba, ya Ina shirin shirya tsakanin Yara ke kuma kina k’ok’arin kiga kin b’ata?ki daina shiga fad’an y’an uwa fa dan wataran za ki ji kuny.....”

“In sha Allah ke ce za ki ji kunya ba dai Ummana ba!”

maganar Jalila ta katse ta,

“kuma da kike ta cewa wani wai y’an uwa da ni da Huda shin wai Ubanta ne d’an uwan Baba? ko kuwa ke uwarta ce y’ar uwar Umma???”

Shiru Mama ta yi tana kallon Yarinyar da ta rena ta goya a bayanta ta ci kashinta taci fitsarinta tana rera mata rashin kunya.
Cikin son fahimtar da ita Maman tace
“Jalila ai ko babu y’an uwantaka ke kin san Hudan k’anwarki ce.”

“Chan ki je ki nemo y’an uwanta wallahi ba dai ni ba.”
Jalila ta fad’a cikin d’aga mata Hannu kafin ta d’aura da cewa”kiganni nan kaf y’an uwana na dangin Ummana da Babana suna da nasabarsu kuma suna amsa sunan iyayen su!…da za ki ce wani Ummana za ta ji kunya dan kawai ke kinji kunya shine za ki so kowa ma ya ji?kinje kin Haifo shegiya kin kawo ta cikin gidanmu still za ki yi ta lak’aba mini ita kina wani y’ar uwartace ita?
Idan ba tsoroba ki nuna ubanta mana ki kaita wajenshi Yarinyar da ko sunanta Babanta ba ya so yaj.....”

Jalila bataga k’arasowar Mama daff da ita ba sai kawai wani haske da ta gani sakamokon marin da Mama ta d’auke ta da shi,ai kuwa batai wata wata ba itama ta d’aga hannunta za ta mari Mama.

Ji ta yi an rik’e hannun hakan
ya sanya da sauri ta juyo,nan suka had’a ido da Junaidu ya had’e rai. Matse hannun nata yai da k’arfi sai da tayi k’ara sannan yace mata
“baki da hankali Mama za ki mara?”
Nan Umma daga bakin d’akinta toyo wata super tayi kan Junaidu ta rufe shi da duka tana cewa”saketa ta rama ka saketa nace!!”
duk irin dukan da Umma take yiwa Junaidu hakan bai saka ya saki hannun Jalila da taketa tsalle tana k’ok’arin fizge hannunta ba tana kallon Mama tana”Ya Junaidu ka cika mini hannu in rama Allah yau Mama kin tab’o tsuliyar dodo,idan sama da k’asa za ta had’e sai na rama!!”
duk ta birkice ta tada k’ura tana k’ok’arin fizge hannunta a cikin na Junaidun.
Junaidu da ya ga dambe ma take shirin yi da shi ne yasa ya fizgo ta ya juyo da ita ya d’auke ta da wani irin gigitaccen mari
yace
“ke ki nutsu!”
ya daka mata tsawa,ganin haka yasa Umma tayi kan Mama ta d’aga hannu zata mareta Mama tai saurin rik’e hannun ai kuwa gida ya kacame Umma kawai k’ok’arin ta ta mari Mama ta yi dambe da ita ita kuwa ta k’i bata daman yin hakan ta dai rik’e mata hannu shi kuma Junaidu yana gefe yana fama da Jalila.

“kai!kaii!!kaiii!!!!,lafiyarku kuwa?”
sukaji muryar Baba wanda ya gama parking machine d’in sa a soro yana k’arasowa cikin gidan da d’an sauri ga leda a hannunshi da alama yanzu dawowarsa kenan.
Umma ce ta saki hannun Mama cikin fushi tace”Alhaji gara da Allah ya dawo da kai yanzu,dan yau za ayita ta k’are a cikin gidan nan,matar nan ta kwashi k’afa ta kai k’arar mu gurin kaka,kaka ya goya mata baya an hanamu ni da Jalila ko kallon banza mu yiwa Huda,shine yanzu ni ta d’aga hannu ta zabgawa Jalila mari saboda Allah duba fuskar Yarinyar nan.”
Ta finciko Jalila daga gaban Junaidu da ya sake mata hannu ta hankad’ata wajen da Baba yake tsaye,aikuwa kamar jira take ta fashe mishi da kuka,lallashinta Baba ya shiga yi cikin rawar jiki kafin a fusace ya d’ago ya hau Mama da fad’a,Umma ce ta katseshi ta hanyar cewa
“Ai matar nan ta raina ka,tun ranar da ka hanamu shiga harkar Huda a cikin gidan nan muka daina bi takanta,amman ita da ka ce in an hukunta Hudan kar ta yi magana
shine saboda tsananin raini yau tun safe bata barmu mun sha ruwa ba a cikin gidan nan,saboda an tab’a y’ar gwal kalla yadda ta mari Jalila saboda Allah.”
Junaidu ne ya kalli Baba sannan ya juyo yana kallonta yace “Umma ba fa hakane ya faru ba,yau tun safe Ina cikin gidan nan babu inda naje,a idona aka yi komai, ita Jalila ce bat...”
Tsawar da Umma ta daka masa ne ta sanya shi yin shiru
“Junaidu!! Bar nan”ta nuna mishi hanyar fita da yatsarta manuniya,baki ya bud’e zai yi magana ta sake daka mishi tsawa tace
“bar nan nace!!”
sum sum haka ya juya ya fita ba yadda ya iya.

Juyowa ta yi ta kalli Baba tace “Alhaji a bi mana hakkinmu.”

Shiru ya yi yana kallon Mama wadda ta yi k’asa da kanta,
...Harga Allah yana son Mama, babu abinda ya chanza daga soyayyar da yake yi mata tun suna Yara amman idan ya tuna da yadda ta yi fatali da soyayyarshi saboda waninshi sai yaji wani haushin ta yana shiga masa rai yadunga jin babu abinda yakeda Buri sama da ya cusguna mata itama ta d’and’ana ta ji ya zafin cusgunawan yake...
Umma ce ta katse masa nazari ta hanyar cewa
“Alhaji muna sauraronka.”

Takawa yayi inda Mama take ya tsaya,yai mata nuni da yatsunshi guda biyu sannan ya fara magana
“Maryama a cikin zab’i guda biyu da zan baki yanzu ki d’auki d’aya….
na farko ko ki tsaya Yarinyar nan ta rama marin da ki ka yi mata na biyu ko kuma ki bata hakuri tare da alk’awarin ba za ki k’ara ba, kuma muddin kika k’ara to tabbas a bakin zaman Huda a cikin gidan nan!.”
a razane Mama ta d’ago kai tana kallon shi da idanuwanta da suka kawo kwalla…tausayinta ne ya kama shi tashi d’aya yaji zuciyarsa tana neman yi mishi gardama
dan haka cikin sauri ya juya ya daina kallonta yana me cewa “zab’i ya rage naki.”
Jalila da Umma kuwa zuciyoyinsu sun yi fess sai faman murmushi sukeyi,Jalila har da tattare hijabinta ta yi gaba d’aya ta jefa shi baya ta wajen wuyanta tana hurawa hannun damanta iska ta matso daff da Mama…
ganin da Mama tayi Jalila na neman kifa mata mari, ne ,ya sanya ta yi saurin runtse idanunta tace
“Jalila na mareki tsautsayi ne ki yi hak’uri na yi alk’awarin ba zan sake ba!.”
Da sauri kafin su Jalila su ce wani abun Baba yai saurin cewa “barka to!! kin shafama kanki lafiya,wuce ki tafi d’akinki.”
Jalila kuwa ta b’ata rai za tai magana Umma ta yi saurin rik’o hannunta tai mata alamun ta yi shiru kafin ta juya ta kalli Baba tace
“Alhaji mun gode da adalci”
Daga haka ta ja hannun Jalila suka yi d’aki.
Suna k’arasa shiga d’akin Jalila ta wafce hannunta a cikin na Umma sannan tace
“haba Umma!!mai yasa kika hanani yin magana?”gashi yanzu ban rama marina ba,harfa Ya Junaidu sai da shima ya mareni,kuma abun haushin ni Baba ya hanani dukan Hudan da a kanta zan huce,ni dai gaskiya da kawai kin barni nace ban hak’ura ba na rama marina! yanzu Ina kikeso in kai wannan d’acin da zuciyata take yi mini??”
Ta yi maganar tana mai zama da dukkan k’arfinta a kan y’ar kujerar su two seater da take ita d’aya a d’akin duk ta yayyage.

Murmushi Umma ta yi kafin ta zo ta gabanta a hankali ta d’aura dukka hannayenta akan kafad’arta sannan ta durk’usa a gabanta tare da sauk’e ajiyar zuciya kafin tace
“ta Yaro kyau takeyi bata kwari, ai Jalila ko da ace ta zab’i ki rama marin nan da ta yi miki to fa da ni da kaina ba zan bariba,saboda zab’i na biyun nan da Alhaji ya fad’o shi ji na yi kamar an tsunduma ni a cikin aljanna”
Shiru Jalilan ta yi tana kallon Umma sak’ak’e alamun tana buk’atar k’arin bayani, fahimtar hakan da Umma tayine yasata sauk’e numfashi sannan tace “menene babban burinmu a yanzu??”
Shiru ta yi na y’an sakanni sannan tace
“in auri mai kud’i kuma mu ga bayan Mama da Huda”
Murmushi Umman ta yi kafin tace “yanzu idan Hudan ta bar gidan nan tanada wajen zuwa? Girgizama Umman nata kai tayi kafin Umman ta sake cewa
“wane hali kike tunanin Maryam za ta shiga?”Babu b’ata lokaci Jalila tace”tashin hankali”sannan ta kyalkyale da dariya sai da tayi mai isarta tukunna tace
“Umma idan na fahimceki so kike in sake yi mata abunda zai b’ata mata rai har ta kai ga sake mari ko dukana”
“Abinda nakeso kenan”
Umma ta fad’a tana murmushin jin dad’i mai had’i da dariya kafin ta mike tsaye tana kallon k’ofa kamar mai tunanin wani abun tace
“Jalila ki tuna ata dalilin matarnan na bar gidan nan na rabu dake naje nai rayuwar wahala, itakuma ta dinga gallaza miki azaba
ki tuna da cewa bakiji dad’in tashi a gaban uwa ba kamar ko wacce y’a
ki tuna yadda ta ci amanata ta aure mini miji,
ki tuna! ki tuna!! ki tuna!! dayawan abubuwan da ta yiyyi mana.”

Murmushi Jalila ta yi sannan tace”Ummana kar ki damu, zan tattaro gaba d’ayan abunda na san bataso in yi ta zuba mata har sai ta kai ga tab’a ni,kuma na riga na gano abinda yafi b’ata mata rai
shegiyar y’artan nan ce bataso akira da shegiya ni kuwa yanzu na fara….”
Zuciyar Umma fess ta dawo ta zauna kusa da Jalila sukaci gaba da k’ulla yadda za su k’untatawa Mama…..


A chan d’akin Mama kuwa tana shiga ta saki kukan da take ta k’ok’arin rik’ewa,da sauri Hudan ta taso ta zo ta rungumeta itama kawai sai ta fashe da kuka kowa ya kasa lallashin d’an uwanshi,sai da sukayi mai isarsu tukunna Mama ta d’ago da fuskar Hudan tace mata “mai
ya saki kuka?”
Shiru tayi kafin tace “Mama gani nai kina kuka kuma naji abinda ya faru a tsakar gida”
Sharemata ragowan hawayen nata tayi kafin tace “bakomai ki kwantar da hankalinki”sannan ta mik’e tayi kan gado ta kwanta ta lumshe idanunta….ganin hakan ne yasa itama Hudan ta mik’e taje ta kwanta a kusa da ita tana sauk’e ajiyar zuciya kafin bacci ya yi awon gaba da ita….
SHARE PLS.

BULAMA ✍️




So da Buri
Free Book
03

A hankali Mama ta bud’e idanunta da suka d’an kumbura ta juyo tana kallon fuskar Hudan kafin ta kai hannun a hankali ta shafa kumatunta tausayinta yana sake shigar mata zuciya.

Nasarawa GRA, Kano.

Wani dogon dattijo ne ke tsallako titin da sauri had’e da d’an gudunshi,hannunsa na dama rik’e da agwaluma guda uku a cikin farar leda,na hagun kuma yana amfani da shi wajen mayar da y’an chanjin sa cikin aljihun gabar rigarsa,da alama agwalumar ya tsallaka siyowa.
K’ara saurin gudun nasa yayi sakamokon ganin har motocin da ya hango sun iso bakin mahaukacin gate d’in makeken estate d’in.
Da saurinsa ya zaro wani d’an k’aramin makulli a cikin aljihun gefen wandonsa ya isa gaban wata had’add’iyar k’ofa wadda ke a ta gefen makeken gate d’in wadda colour d’inta da design d’in exactly irin na gate d’in ne, cikin sauri ya zura mukullin a ramin mukulli sannan ya murza k’ofar ta bud’u ya tura da sauri ya shiga har yana tuntub’e, shigarsa ke da wuya waennan motocin da ke jiransa a ta wajen gate d’in suka fara danna masa horn babu k’akk’autawa…tashi d’aya duk ya bi ya rikice hakan yasa ya yi sauri ya fad’a d’akinsa na mai gadi ya d’aga k’asan pillow ya d’auko mukullin babban gate d’in ya fito yanata sauri ya k’araso jikin gate d’in ta baya ya bud’e padlock d’in sannan ya bud’e wani lock kafin ya durk’usa k’asa ya zare wata makekiyar sakata tukunna ya mik’e ya fara k’ok’arin tura gate d’in jikinsa duk yana rawa kana ganinsa ka san a rikice yake gashi an k’ara rikita shi da uban horn d’in da ake ta maka masa babu k’akk’autawa… ,
Bai kai ga k’arasa tura gate d’in ya bud’u duka ba motar farko k’irar benz G wagon Bak’a wuluk! ta danno kai da mugun gudu ta biyun na binta a baya, ba don ya yi hanzarin barin wajen ba da babu abunda zai hana gilashin motar tafiya da y’ar sharar jikinsa.
Ganin motocin sun shige ne yasanya shi K’arasowa bakin gate d’in ya fara turawa domin rufewa, da kyar yake iya turawa saboda tsabar girma da nauyi.

Wani gate d’in motocin suka nufa a cikin jerin gidajen estate d’in da a kalla sun kai 15 kuma gaba d’aya ginin gidajen yanayin tsarin 3D ne masu hawa biyu,tsayuwa fad’an haduwar ginin gidajen b’ata lokaci ne.
Wani kakkauran mutumi ne zaune a bakin gate d’in da suka nufa,sanye cikin uniform d’in sojoji,da alama shi ke gadin wannan particular gate d’in, mik’ewa ya yi sakamokon hango motocin sannan ya shiga ta k’aramar k’ofa ya bud’e musu gate d’in wanda hakan ya bawa farfajiyar gidan damar baiyyana..mahaukacin makeken mansion ne yanayin tsarin ginin 3D shima…
Ma sha Allah aljannar duniya kenan domin kuwa ya had’u har ya gaji da had’uwa da tsaruwa ga kyau ga girma duk ya had’a.
Wajen da aka tanada domin ajijiye motoci suka nufa sannan suka yi parking.

Wani mutum ne ya bud’e motar farko,ta wajen mazaunin driver ya fito ya zagayo ta wajen owners corner da d’an saurin shi ya bud’e murfin motar ya koma gefe ya tsaya .


....K’afarshi ta dama wadda ke sanye cikin had’add’en black d’in covershoe mai tsananin tsada ya fara zurowa waje, kafin ya sauk’o da d’ayar sannan ya mik’o ya fito gaba d’ayansa, ba matashi bane ba ko magidanci ko kuma dattijon Alhaji, tsohon mutum ne ,tukuf da shi!!
Sanye yake cikin wasu zazzafan suit,ash colour, kai kana ganin yanayin kayan ka san ya kai kud’in jarin mai k’aramin k’arfi,idanunsa sanye cikin wani farin glasses wanda kana gani ka san na k’arin k’arfin gani ne,walking stick d’in dake rik’e a hannunsa for sopport ma kanta abar kalloce!! Ka na gani ka san an zuba mak’udan kud’ad’e wajen siyar ta,ga wani had’add’en Rolex watch a hannunsa,
Tsohone amman skin d’insa glowing yake yi wanda kana gani ka san tsabar hutune..to cut it short dai,every part of him is screaming ‘I’M RICH!!’.

Sandar hannunsa ya d’aga domin yin tafiya har ya d’an tura k’afarsa gaba sai kuma ya yi amfani da ita ya juyo ya tsaya yana kallon motar da suka shigo tare.

Wani kyakkyawan saurayi ne ya fito daga mazaunin driver da alama shi ya tuk’o motar da kansa, yana d’an fizgen kama da tsohon sannan kalar fatar su iri d’aya ce.
Ganin da Auwal ya yi kakan nasa ya kafeshi da idanune ya sanya shi K’arasowa wajensa da d’an sauri, tukunna ya d’an rissinar da kansa yana mai kallon k’asa kafin yace”Garanpa,u need something??.”
Ya yi masa tambayar ba tare da ya kallesaba .
Juyawa Grandpa d’in ya yi ba tare da ya sake kallonsa ba,har zuwa lokacin da drivern d’insa ya d’auko suitcase d’inshi ya gama rufe motar yana taka mishi baya….
yana tafiyar ba tare da ya tsayaba cikin muryarsa ta tsofaffi yace”Go and give iliyasu 50k,ask him to leave this house foreva,he is fired!!
Sannan ka cewa Daniel ya nemo sojan da ya san zamu shirya ni da shi,ya fara gadin main gate,within 3 hours.”
Yana magana yana tafiya ko sake waigowa bai yi ba balle ya amsa Auwal wanda yake cewa”Ok Granpa consider it done”.
Ya shige.

Wani shu’umin murmushin jin dad’i Auwal d’in yayi, daman shi ya tsani Malan iliya, domin kuwa kamar gadin sa shi kad’ai yakeyi a gidan,ya saka masa ido dayawa, kullum idan ya dawo dukda kuwa motarshi tinted glass gareta sai Malan iliya ya san yadda yayi ya d’an lek’a ta gaban dukdan ya ga shi kad’ai ya dawo ko kuwa tare da wata yake,sannan bai isa yayi dare ba,yana wuce 12 zai fara ganin kiran Daddyn sa ko da kuwa Daddyn nasa baya gari,ko me yayi in dai malan iliya ya gani to a kunnen Daddynsa, kuma sai an hukuntashi hukunci mai tsanani, ya zame masa kamar wani cctv camera sam ya hanasa sakat duk dan kawai idan ya kai wa Daddyn nasa rahoto yana bashi kud’i da kaya, and the most annoying part of it Daddyn nasa ya hanashi ko da hararar mallan iliya ne,balle wata banzar magana.

Yana wannan nazarin da murmushi akan fuskarsa ya k’arasa bakin gate d’in granpa ya fad’awa Daniel sak’on granpa sannan ya nufi main gate wajen mallan iliya. Daniel kasa b’oye zumud’in sa yayi , a take ya d’au waya ya kira wani abokinsa solomon wanda ya san irin halinsu d’aya, nan da nan kuwa Abokin nasa ya amince bayan Daniel ya fad’a masa nawa ake biyan malan iliya, yace masa ya jira zuwanshi nan da 2 hours yanzunnan zai sallami mamanshi da sistern shi ya taho.

Shikuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login