Showing 33001 words to 36000 words out of 124668 words

Chapter 12 - So Da Buri Book 1 Hausa Novels by Humaira Bulama.txt

25 Sep 2025

2316

babban mutum ne. Amman na san garin a yake ba zai wuce Abuja ba.”

Shuwa ce tace “ai ba lalle Abujan ba, kawai dai yanzu
muyi ta saka shi a addu’o’in mu muna yi mishi fatan alkhairi, inda rabo wata rana za a had’u ai.”

“Haka ne kam!”
Cewar, wadda ta k’i tafiya ita da Sadiya sai da sukaji kwakwaf.

Haka dai kowa yayi ta tofa albarkacin bakinsa…sannan aka ci gaba da murnar dawowar su, daga baya Madu da Shuwa suka tafi gida, aka bar Bilkisu da Maryam a gidan Baaba Bashir saboda gidan yayi k’ura sosai, aka bari akan washegari idan an gyara sa dawo.
A ranar Ya Jamilu ya koma saboda daman saboda case d’in ya dawo kuma akwai abubuwa da dama a kanshi.

Da daddare wajajen 8 Ya Usman ya aiki Bilkisu yace ‘ta kira mishi Maryam’.
Tana zaune tana tunanin Abba Bilkisu ta shigo ta fad’a mata sak’on Yayan nasu ta juya ta fita wajen Baaba Talatu…
Da farko kamar ba zata je ba, sai kuma kawai ta mik’e ta fita.
A can waje babban tsakar gida ta iskeshi zaune a kan tabarma, gefen sa ta nema ta zauna ta gaidashi sama sama
tunda ga nan daga ‘um’ sai ‘um um’.
Ko ba a gayawa Usman ba ya san cewa Maryam ta chanza mishi, dan gaba d’aya hankalinta baya gareshi, shi gani yayi ma kamar haushinsa take ji, dan tunda ta fito bata yi mishi dariya ba.
Da kyar! Ya samu ya kawar da tunanin da zuciyar shi take k’ok’arin dasa wa kwakwalshi, dan shi dai ya san makarantar mata take yi, babu maza ballanta tayi saurayi! Da wannan tunanin ya sallameta ya sanyawa ranshi maybe ko bacci take ji yau d’in.
Amman ga mamakinshi washegari ma haka ta yi mishi
wata washegarin ma haka, sai da aka shafe kwana biyar suna a haka.
Da yaga abun yayi yawa yau sai ya chanja lokaci, around 4 na yamma ya aika aka kirata a zatonsa ko yana hanata bacci ne amman yau sai yaga ma b’acin ran da take ciki ya fi na kullum, dan tun daga nesa ta had’e rai!
Ita kuma Maryam a nata b’angaren takaici ne ya rufeta…shi wannan Ya Usman d’in baya tashi kiranta sai ya daidai ci daidai lokacin da take tsakiyan tunanin Abba..

Kasa jurewa Usman yayi, hakan yasa ya ce mata
“Maryam anya har yanzu kina sona kuwa?”
D’agowa tayi ta kalle shi, kafin ta yi k’asa da kanta ta fara tunanin...
‘Gara fa ta fad’a mishi gaskiya, ita daman chan ba sonshi take yi ba! Kar taje su yi aure tana tunanin wani ta yi ta kwasowa kanta zunubi!’
Wata zuciyar ce tace mata ‘to ke Abban aka ce miki sonki yake yi? ko ya tab’a gaya miki ne?’
Da sauri ta rumtse idanunta dan she can’t begin to think of the fact that wai Abba baya sonta! Sai yanzu ta kuma tabbatar wa kanta ta kamu da sonshi ba kad’an ba, dan da basa had’uwar nan ta yi kewarshi ba k’adan ba!’……

“Maryam kin yi shiru@
Muryar Ya Usman ta katse mata tunani..
Bud’e idanuwanta ta yi waenda har sun chanja kala!
Zuwa yanzu kam tabbas Ya Usman ya fara kaita bango…domin kuwa ita a gaskiya bata son naci babu abunda ta tsana kamar takurawa, bata son yawan magana! kuma ya sani.
Shiyasa a makaranta ake mata kallon mai girman kai..mutane
ma dayawa tsoron mata magana suke yi karta yarfa su,
a cewarsu masu kyau daman ance girman kai ne dasu.
Itakam basu san kawai yawan maganar ce bata so….

“Hmmm, tou inaga dai kin d’auko kuramen aljanu a boarding d’in taku.”
Ya Usman ya sake fad’in haka.

A yanzu kam ta gama yanke shawarar…
‘Ko Abba baya sonta, za ta fad’awa Ya Usman gaskiya dan indai ta aureshi a haka tabbas ba zata iya yi mishi biyayya ba, hakan yasa a hankali ta sago ta kalleshi!
Ya kuwa kafe ta da ido ko kyaftawa bayayi, nauyinshi taji shiyasa ta maida kanta k’asa ta fara magana a hankali….
“Ya Usman ka daina cewa bana sonka, Ina sonka a matsayinka na d’an uwana mana, ai kai Yayana ne.”
Shiruuuu!! Ne ya wanzu a wajen, dan ya kai kusan mintuna biyar bai ce mata uffan ba, ita tama yi tunanin ya bar wajen ne dan haka a hankali ta d’ago tana juyowa kuwa suka had’a ido! gabanta ne yayi mugun fad’uwa sakamokon idanuwansa da taga sun koma tamkar garwashi, bata gama fassara yana yin da fuskarshi take ciki ba taji yace “A matsayin saurayin ki fa? mijin da zaki aura uban Ya’yanki??”
Ya yi mata tambayar yana mai kallon cikin kwayar idanuwanta.
K’arya ba halin Maryam bace ba, zuwa yanzu ta so ta d’an b’oye masa ko dan halin da taga yana shirin shiga a cikin y’an mintunan da basu gaza goma ba, amma sai ta tsinci kanta da girgiza mishi kai.

Wannan karon ta tsorata dan hawaye ta gani ya sauk’o ta idonsa d’aya, bata ankara ba taga d’ayan ma ya sake sauk’owa. Dasauri ya mik’e ya bar wajen yayi cikin gida ba tare da yace mata uffan ba.
A hankali itama ta tashi ta bi bayanshi tana mai jin wani nauyi yana sauk’a daga kan m k’irjinta....

Sai da tayi kwana biyar bata sake saka Ya Usman a idonta ba, a lokacin kuma sauransu kwana d’aya su koma makaranta, mutumin da tun tasowarta
in dai yana gari to sai yazo gidansu sau hud’u a rana.
Tana zaune tana had’a kayanta a jaka Shuwa tace “ta je ta kira mata Zainab, Abba Madu yace a tambayeta idan akwai abinda take buk’ata bayan provision d’insu.”
Tana shiga gate d’in gidan gabanta ya fara fad’uwa, ba kowa sai motar Baba Bashir a parke a chan gefe, a hankali ta k’araso ta tura k’ofar k’aramin tsakar gidan ta shiga, nan d’in ma ba kowa. Har ta wuce zata isa k’ofar d’akin Zainab, ta ganshi yana fitowa daga corridor d’in kitchen da plate a hannunshi, bata san dalili ba kawai taji jikinta ya fara rawa kamar wadda ta yi laifi, sosai take mamakin ramar da yayi…tana tafe tana waigen shi dan a tunanin ta zai yi mata magana, bata yi auni ba kawai taji ta yi tuntub’e ta kusa fad’uwa, da sauri ta saita kanta ta tura k’ofar d’akin Zainab ta shige….
Wani abu da ya bata mamaki shine tabbas ta san Ya Usman ya ganta to amman kuma mai yasa bai ce mata komai ba?! Har fa kusan fad’uwa tayi amman bai kulata ba! Mutumin da ada idan ana hirar tsakar gida ko sauro baya so ya hau jikinta, ya dinga yi mata fifita kenan har a tashi.
Yo ai ko babu soyayya shi Yayanta ne so ya kamata ace ya kulata, lallai indai hakane kuwa to hakan yana nufin Ya Usman yayi zuciya kuma da alama ya hak’ura da ita kenan, a cikin zuciyarta tace “barka na”.

“Malama lafiya? Za ki shigo babu sallama?”
Muryar Zainab ta katse mata tunaninta.
Sak’on Shuwa ta fad’a mata, bata jira amsar da zata bata ba ta juya kawai ta fito gudun rikici dan yanzu kam itama bata ragawa Zainab.

Har ta kai k’ofa, sai kuma ta kalli y’ar barandar da zata kaita d’akin Baaba Talatu, tunani ta yi akan bari ta shiga su d’an gaisa dan haka ta nufi k’ofar d’akin nata! Tana isa bakin k’ofar ta saka hannu kenan zata tura taji muryar Ya Usman yana cewa “Baabaa to ai ni a tunanina sharetan da zan dinga yi kamar zai janyo mini in sake fita a ranta ne, yanzu fa har kusan fad’uwa tayi ban kula ta ba, ku.....”
Cikin fad’a fad’a taji Baabaa Talatu tana cewa “Yanzu Usman Ina uwar ka amman ba zaka bi abinda nake gaya maka ba? Yo ai maganar fita a rai kuma ta faru ta k’are! Sai dai bayan auran ku ka nuna mata so ta yadda zata dawo kamar da, ka ji ai da kunnenka Zainab tace ‘Yaron balarabe ne!’
Shi ne ya rud’eta….kawai abunda nake so da kai shine ka nuna mata kamar ka hak’ura ta yadda za ta sakankance, ni iya in sha Allah da kaina zan je in samu Madu…ba zata k’are makarantar nan ba sai da auranka a kanta bi izinillahi.
Ka kwantar da hankalinka, dan k’ank’aninka da kai ka bi ka d’aga hankalinka! Ai kana ji dai
abinda Likita yace ranar ‘jininka ya yi mugun hawa, Allah kad’ai ya taimaka baka samu stroke ba, lokacin da ka fad’i ka suma wallahi na d’auka mutuwa ka yi, nayi mugun tsorata.

Zancen banza ma kenan!!! Ita daa chan ta san bata sonka amma shine ta bari aka kawo har i yanzu?? Ko da yake na san ba yin kanta bane ba, wannan Yaron ne yake neman juya mata tunani.
Amma ba komai na san abunda zan yi kai dai kawai
ka kwantar da hankalinka kaji ko??”

A hankali yace “tou Baaba.”

Jin kamar zai fito yasa Maryam ta yi saurin barin wajen ta fice tana tafiya tana share hawayenta, da kyar ta kai gida dan har wani duhu duhu take gani ga jirin da yake k’ok’arin zubar da ita, tana shiga ta wuce d’akin su ta kwanta a kan gado ko bi ta kan kayanta da take had’awa bata yi ba.
Banda tashin hankalin da yake a ciki sosai mamakin Baaba Talatu ya turnik’e ta yake juya mata Kai! Tabbas tsakanin ‘da da uwa sai Allah, Baaba Talatu da take nuna mata tsananin so
har fa dukan Zainab take yi saboda ita amma wai yau itace take shirin k’ulla mata auren dole kawai dan taga d’anta ya suma, wata zuciyar ce tace mata ai itama tana da tata uwar, taje ta fad’awa Shuwa tun kan ayi mata auren dole.
Da sauri ta shiga girgiza kai ita kad’ai dan ta san yadda gidansu da nasu Baba Bashir yake,
Irin tsananin shak’uwa da zumuncin da yake tsakani ba na wasa baneba, ita kanta bama ta san ba brothers bane iyayen nasu sai kwanaki da suka je Maiduguri karkarsu take fad’a mata.

Tabbas kuwa ta san Shuwa ba zata d’auki wannan shirmen nata ba.
Sai a lokacin ta fahimci kuskurenta, ta kuma gane ta d’aukowa kanta hanyar da ba zata b’ulle ba dan ta san iyayenta ko giyar wake suka sha ba zasu tab’a hana Usman itaba. Kamar ma Shuwa da Madu sun fi son Usman a kaf cikin y’ay’an Baba Bashir, don gashi Madu ya biya mishi hajji sun tafi tare ko Baba Bashir d’in bai biya ma ba.

A take ta yanke shawarar rabuwa da Abba duk da ta san za ta sha wahala, dan da wuya in wannan ba shine ajalinta ba, amman ya ta iya?
a haka bacci ya kwasheta sai la’asar ta farka.

Toilet ta fad’a ta yi alwala ta fito ta yi sallah, sannan ta mik’e ta yi waje, a hanyar kitchen suka had’u da shuwa tana tsugunne kan kujera a bakin kitchen d’in tana gyaran alaiyyahu.
Gaidata Maryam tayi sannan ta zauna a kan takalmanta tasa hannu ta fara tayata.
Lokaci zuwa lokaci Shuwa tana lura da ita…sai da suka gama har za ta mik’e ta kai kitchen ta ji Shuwa tace
“Zauna Ina so za mu yi magana”

Da sauri ta kalleta sai kuma ta koma ta zauna a kan takalmanta da tayi kujera da su.
Cikin nutsuwa Shuwa tace
“Mai yake damunki?
D’azu naga kin shigo kina kuka!
Ga idon ki duk sun kumbura
Da alamun kukan kika yi ta yi ko?
A zuwa yanzu ba san kin daina yiwa Zainab kuka dan haka ba matsalarta baceba, ko?”

A hankali ta d’aga mata kai
Alamar ‘eh’.

“Fad’a min to? menene?”
Inji Shuwa.

Shirun da Maryam ta yi ne yasa ta sake tambayar ta tare da cewa “Ko kinada wadda ta fini da za ki gayawa?
Kin manta tun lokacin da Zainab ta daina k’awance da ke na yi miki alk’awarin na zama babbar k’awar ki?”

Cikin murmushi Maryam ta share kwallar da ta zubo mata tace “a’a”
A hankali Shuwa ta kamo hannayenta duka biyu sannan tace “fad’a min to, menene?”

Tun daga ranar da ta had’u da Abba ta hau gayawa Shuwa har yau d’innan bata b’oye komai ba…

A hankali Shuwa ta sauk’e ajiyar zuciya, bayan Maryam d’in ta gama, sannan cikin nutsuwa tace “Maryam na san menene so, kuma zan so ki auri wanda kikace kina so a yanzu, amman idan muka da ni dake da babanku za ayi mana kallon butulu.
Abu na biyu kuma ki yarda dani idan nace miki, har yanzu k’iba son Usman, tunda ai da kina son shi, kyale kyale na wanchan Yaron shi ya rufe miki ido har kike nema ki guji Usman wanda na san in sha Allah bayan auranku komai zai daidai ta.
Sannan abu na uku, wanchan
Yaron daga yana yin labarinki na fahimcei d’an masu kud’i ne, na gaske! Maryam ke Yarinya ce har yanzu, Yaran masu kud’in nan b’atawa mutum lokaci kawai suka iya.
Tabbas idan kika bincika already akwai Yarinyar da zasu aura wadda aka riga aka had’a su dan basa tab’a yarda su auri y’ay’an talakawa.
Shawara ta anan shine
ki auri Usman, ki zauna a cikin y’an uwan ki, ki manta da batun Abba kar ki bi zuciya ki zama butulu, daa chan baki ji rashin son auranshi ba sai yanzu? Usman zai kula da ke, tun kina k’ank’anuwar ki yake d’awainiya da ke dan zan iya ce miki laulayi da nak’udarki ne kawai Usman bai yi ba amma har Goya ki yake yi, kashi da fitsari babu kalar wanda baki yi masa ba.
Kiyi ta Addu’a zaki ji zuciyarki tana yin sanyi, kinji ko?
Allah ya yi miki albarka.”

A hankali tace “Ameen.”
Ta yadda kuma ta gamsu dukkanin abunda Shuwa ta fad’a gaskiya ne, sai dai kuma tanata so tace mata itafa tun farko daman murnar da taga sunayi ita da Baabaa Talatu ne ya sanya ta yarda da soyayyar ya Usman, amma sanin ko ta fad’a hakan ba lalle a fahimceta ba tunda da chan bata fadaba sai yanzu da take son rabuwa da shi saboda Abba, hakan ya san kawai ta yi shiru ta mik’e ta koma d’aki.
Tana shiga ta nemi bakin gado ta zauna a hankali ta sauk’e ajiyar zuciya, sannan tace “Abban ma da nake ta abu a kanshi maybe ma shi bai san m inayi ba.”

Ahaka dai sukuku ta k’arashe wannan ranar washegari da sassafe Ya Usman da Ya Jamilu wanda ya dawo jiya da daddare suka maida su makaranta, har suka juyo Kano Usman ko kallon inda take bai yi ba, Ya Jamilu ne dai dukda ya kasance Soja baya yawan dariya amman hakan yayi ta janta da hira ganin kamar tanata tunani.

Ana gama checking d’in kayanta ta fara k’ok’arin kaiwa hostel.
Isowarta bakin Unity gate kenan kamar ance ta d’aga kanta gabanta ya yi mugun fad’uwa sakamokon had’a ido da suka yi da Abba, ya kafeta da ido da alamun ya dad’e da ganin tahowarta, yana zaune gefen house mistress d’insu wadda ta mayar da second checking d’abiarta dan duk dawowa hutu bayan an gama duba maka kaya a main gate to itama sai ta sake nata a bakin Unity gate.
Da alamun checking d’in yake tayata, amman sai magana take yi mishi hankalinshi baya wajenta har sai da ta d’an zungureshi tukunna ya mik’a mata abun hannunshi ya taso ya taho inda Maryam d’in take, tana k’ok’arin k’arasowa wajen tana k’ok’arin kaucewa ya sha gabanta…had’a ido sukayi tana mamakin ramar da taga yayi, taji yace “Maryam I could hug u right now! Kin san yadda na dinga nemanki kuwa? You said za mu had’u 11 tun 10 nake Admin Ina jiran ki har kowa ya tafe, and now kin ganni k’ok’ari ma kike yi ki wuce kawai ki tafi, bakiyi missing d’ina ba??”
Ya yi mata tambayar yana kallon ta da yanayin sa kamar na mai shirin yin kuka.

Ahankali tace “sir, i want to pass, u are blocking my way.”

Shek’ek’e!! haka ya tsaya yana kallonta, anya kuwa Maryam ce? to ko dai wani abun yayi mata ana I gobe hutun, maybe ma shiyasa ta tafi ba ta jirashi ba…
Yana cikin wannan tunanin yaga tana k’ok’arin zagaye shi ta wuce.
Shan gabanta ya kuma yi, sannan yace “Wai me yake damunki ne? Kin san halin da na shiga kuwa? Ina ta Allah Allah a dawo makaranta don in sake ganinki, wallahi kinji na rantse har a asibiti na kwanta, all because of u and yanzu shine za ki zo mini da wannan sabon attitude d’in?
To wallahi baki isa ba! Idan ma wani misunderstanding ne u better talk mu yi clearing d’inshi right away cos u can’t turn your back on me like this, ba zan iya jurewa ba, not now, not ever!!!”
Ya fad’a da d’an k’arfi da alamun ranshi ya soma b’aci.

A hankali Maryam cikin sanyin ta, tace “Y? Meye had’ina da kai?”

Ga mamakinta sai taga ya fara murmushi, kafin yace “do I really have to say it?”
Yayi mata tambayar yana kafeta da idanuwanshi data kasa jurewa kalla ta yi k’asa da kanta.

Y’an tsirarrun students ne a wajen, most of them ma y’an ajin su ne, kasancewar sai yamma sosai ake cikowar dawowa, sai house mistress d’in da take checking…
Tafa hannunwanshi Abba ya fara yi yana cewa “attention everyone.”
Cikin k’ank’anin lokaci ya had’a kan y’an mutanen wajen da basu da wani yawa, sai da ya tabbatar attention ya dawo kansu sannan ya durk’usa a gaban Maryam, ya sago yana kallonta ya fara magana.
“Maryam i Found the reason for my smile, the day i found you! In you, my life becomes whole, with you my days become bright.
In your hands i would love to lay, for the rest of my life, you’ve got everything i’ve been searching for in life, i would love for you to grow old with me! The best is yet to be and it begins from the moment you say yes!
I love you, so much Maryam, will you please be my soulmate?, will u marry me?, will u stay with me till death do us apart??”.

Ai kuwa nan students suka hau tafi, suna “Say yes, Maryam say yes!!”
Ihun su ne yasa house mistress d’in ta k’araso wajen.

“Stand up!”
tace mishi.

A hankali ya mik’e, tukunna tace “you know all this is not allowed right?”

Cikin sanyi jiki yace “yes”

Murmushi yaga tayi sannan tace “but I’m willing to sopport

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login