Showing 36001 words to 39000 words out of 124668 words
Chapter 13 - So Da Buri Book 1 Hausa Novels by Humaira Bulama.txt
you a hundred percent, because I’ve never seen a perfect match like yours!
But don’t do too much of zance at school because it’s not allowed, don’t cause problems for her, you can visit her as much as u want whenever she gets back to her fathers house.”
“Ok.”
Ya cewa house mistress d’in yana d’an murmushi sannan yace “tnx”.
Kamo hannun Maryam tayi tace “ta wuce hostel tayi freshening up, kafin wannan oyinbo boyfriend d’in nata ya hanata.”
A hankali ta wuce…Abba k’ok’ari yake su had’a ido amman tak’i ta bashi damar hakan.
Sai da suka yi kwana biyu tukunna aka fara night prep, ta so ta yi dodging kawai tayi class d’insu amman sai ta kasa.
A hankali ta k’arasa js2, tun ta window ta hango shi zaune wajen zamanshi, yana hango ta ya kafeta da ido har ta k’araso.
Cikin nutsuwarta ta gaidashi ya amsa mata yana kallonta.
Bayan sun d’an gaggaisa sun d’an yi hira tana ta jin nauyin sa ita dai, yace mata ”ya baki fito da wankin ki ba?”.
Da mamaki ta kalleshi tace “ai yanzu na warke!”
Kicin kicin yayi da kyar da nacin da yayi ta zuba mata washegari ta kawo mishi wanki.
.……..
Duk wani gatan da ya dace Abba yana tabbatarwa ta samu, sai dai kamar yadda house mistresses d’insu ta fad’a mishi, baya takurata sosai gudun kar ya ja mata matsala, kuma itama house mistress d’in ta rufa musu asiri kar ya bata kunya, hatta prep d’inma yanzu sai ranar karb’ar wanki da dawowa da shi ne kawai yake zuwa, yana bada tazarar kwana bibbiyu dukda yana takura da hakan amma ya san hakan shine dai dai.
Soyayyarsu sukeyi gwanin burgewa, Maryam ta ma manta ta wani Ya Usman sannan tunda yanzu Abba yace yana son ta,za ta fad’ama Shuwa itafa daman chan ba son Ya Usman take yi ba, don haka a d’aga mata k’afa. Addu’ar ta d’aya Allah yasa su fahimceta su kuma yadda da Abba.
Kamar kullum yau ma suna zaune a night prep suna y’ar hirar su, yake bata labarin yayanshi da irin son da yake yi masa, har yake ce mata yace masa first born d’inshi in Namiji ne takwara zai yi masa.
Murmushi tayi tace
“D’an gatan Yaya.” Tana dubanshi ta k’asa k’asa, dan a yanzu kam kunyarshi takeji kwana biyun nan, kuma take ji bata bari ta kalleshi dan suna had’a ido zai ce mata I luv u.
Garin kallon ne ta kalli fingers d’inshi, sai taga sun d’an kumbura ba kamar ko yaushe ba, hakan yasa tace masa
“Mai ya samu hannunka?”
One thing about him
bai iya k’arya ba, dan haka
ya hau bata labarin tun ranar da ta fara bashi wanki, yadda yake wankewa da gogewa ya ce “maybe yawan tab’a ruwa ne ya sa hannun nasa ya yi haka” shi kam ya ma manta bai kamata ya gaya mata hakan ba.
Maryam haushin kanta ta fara ji, dan a yanzu kam yadda Abba ya damu da ita itama ta san sarai ta damu da shi.
Dan haka tayi fushi yayi yayi ta k’i kulashi, har aka zo tashi.
Ganin tana shirin mik’ewa yasa shi ya rik’e mata jaka, ya fara bata hak’uri, ganin ya k’i sakin jakar kuma Yara har sun fara kallonsu yasa ta koma ta zauna.
Sai da aka gama fita tace “zan hak’ura amman ba zan k’ara kawo maka wanki ba, ai hannun ya warke.”
Shi kuma yace “ba zai barta ta tafi ba har sai ta rantse zata kawo wankin, dan ba zai barta ta dinga shan wahala ba.”
Wasa wasa basu ankaraba, kawai alarm d’inshi na 11 wanda yasa dan lokacin exercise d’inshi kenan b4 going to bed kawai sukaji yana k’ara.
Maryam da taga time a firgice ta mik’e, ko sauraronsa ma bata yi ba ta suri jakarta tayi hostel tana adduar Allah yasa ba a rufe ba.
Shima Abba ganin yadda duk ta rud’e kuma yaga dare yayi yasa bai tsaida ta ba, ya tattare kayan shi ya tafi.
Adduar ta kuwa ta karb’u, dan ba a rufe unity gate d’inba sannan hostel d’insu ma ba a rufeba. Room d’inta nema aka rufe dan sai da tayi knocking tukunna Zainab ta bud’e mata.
Tana ganinta ta juya taje suka ci gaba da hira da ragowan mates d’insu ba tare da ta kalleta ba.
Fitsarin daya isheta tun a chan ga kuma tsoron daya sake ingizo shi yasa itama bata kalli Zainab d’inba kawai kan gadonta ta nufa ta ajjiye jakarta ta zari torch ta fice ta nufi toilet.
Bayan ta gama fitsarin ne taga ashema period d’inta ya d’auke, daman yau take expecting hakan ko gobe da safe, kasancewar ana tsula sanyi ga duwatsun garin na kusa da makarantar, ta san ba zata iya yin wanka da Asubah ba ga kuma isha hakan yasa kawai ta koma d’akin nasu
taje k’asan gadonta ta jawo bokiti mai ruwa. Towels d’inta guda biyu data sak’ale a jikin bunk ta kai hannu ta zari d’aya, ta wuce toilet ta je ta yi wankaan ta, ta dawo.
Hular kanta da ta yi sharkaf da ruwa ta cire, gashin ya zubo.
Ita dai ta san ta bar towel d’aya a jikin bunk amman da tazo da nufin d’auka domin tsane gashin kanta, sai ta neme shi ta rasa…dube dube ta fara yi har su k’asan gado, tana d’agowa suka kusan yin karo da Zainab tana mik’o mata towel d’in, sannan tace
“Sorry na wanke face d’ina ne kuma duk towels d’ina sun yi datti shine na ara na goge fuskana, ungo.”
Murmushi Maryam d’in tayi tasa hannu ta karb’a. Zainab d’in ce tace mata
“Me za kiyi ba ga wani a jikin ki ba?”
“Gashina zan tsane”
Ta bata amsar tana k’ok’arin fara goge kanta. Bata kawo komai a ranta ba, ta hau goge gashin da towel d’in, har ruwan ya d’an fallatsar wa Zainab.
Juyawa Zainab d’in tayi ta nufi Majalisar su.
Ita kuma Maryam sai da ta gama gogewa ta nad’e shi a kanta ta shiga corner d’inta ta shafa mai ta saka kaya, tayi addua abinta ta kwanta .
Har lokacin tana jin k’us k’us d’in maganar su Zainab dan ba suyi bacciba amman a hankali
suke maganar sunata k’us k’us, daga bayama tashi Zainab d’in tayi ta fita ita da wata k’awarta,ita dai Maryam bata san lokacin da suka dawo ba bacci ya kwasheta.
Kiran sallar farkon da aka maka a mosque d’in dake tsakiyar hostels d’in ne ya farkar da ita daga baccinta mai cike da mafarkin Abba…..
‘yana ta zuba mata murmushi ya rik’e hannunta yana janta ita kuma ta kasa zuwa garesa, kamar akwai wani abu da yake janta baya’,
haka ta ji a mafarkin.
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
12
Da ‘bell’ ta yi amfani wajen tashi y’an hostel d’in nata tukunna ta wuce ta yi alwala ta fice mosque.
Sai da gari ya d’an yi haske
tukunna y’an mosque d’in suka fara dawowa. A hanya ne wata roommate d’insu da suka fito daga mosque d’in tare take ce mata “gaskiya Maryam kin b’ata wayonki, ban yi expecting haka daga gareki ba, gashi yanzu kin janyowa kanki! Allah kad’ai ya san hukuncin da za’a yanke miki.”
Da mamaki Maryam take kallonta kafin tace “Ban gane ba Hafsa, mai nayi?!”.
Tsaki Hafsat d’in tayi kafin tace “Ai ga irinta nan, daman Zainab ta fad’a.. k’aryata mutane zaki yi!
Ni dai shawara ta idan an je wajen principal ki rungumi laifinki, dan wallahi kin san halin principal idan kika yi mata k’arya laifin ki k’aruwa zai yi.”
Zuwa yanzu kam gaban Maryam ya fara dukan uku uku gashi sun iso bakin gate d’in shiga hostel, hakan yasa tayi saurin rik’o hannun Hafsat tace “Hafsa dan Allah d’an tsaya, kin saka ni a duhu, kiyi mini bayani, sai magana kike ta yi a baibai.”
Har Hafsat ta bud’e bakinta zata yi magana, wasu y’an mata biyu suka fito da bokiti a hannunsu, suma duk y’an d’akinsu ne, kallonsu sukayi kafin d’ayar tace
“Ah lalle Hafsa, me ake koya miki? lalube ko shafa mai??.”
Hararar su Hafsat tayi sannan ta cire hannunta a na Maryam ta yi cikin hostel ba tare data waiwayi kowa ba.
Su kuwa dariya suka saka sannan suka nufi unity tap d’in dake tsakiyar hostels d’in domin d’ibar ruwa.
Ita dai Maryam har ta shirya…taje dining aka nufi assembly ground, duk tayi sukuku, k’ok’ari take yi ta fassara kalmar ‘lalube ko shafa mai’ amman ta kasa, saboda amsar da kalmar take bata ba abune mai ma’ana a tsarin rayuwar da take yi a makarantar ba.
Ana shirin roundin up assembly d’in Principal ta rambad’a kiran sunan ta a mic tace kar taje class ta sameta a office d’inta.
To fah!!
Dan yanzu kam Maryam ta gama rud’ewa.
Da kyar a daddafe ta k’arasa office din principal d’in, gaba d’aya jikinta in banda karkarwa ba abunda yake yi, gashi gabanta sai fad’uwa yake.
Knocking tayi,
ta ciki aka bata izinin shiga.
Tana shiga mamaki ya kamata sakamokon ganin Abba, metron da house mistress d’insu duk a zazzaune a cikin office d’in.
Da kyar ta iya k’arasawa ta zauna ta gaishesu, principal d’in ce kawai ta iya amsa ta Abba kuwa kanshi a k’asa yake tunda ta shigo, bai d’ago ba.
Gyaran murya principal d’in tayi sannan ta mik’o mata wata takarda, tace mata “ta karb’a tayi signing.”
A hankali ta mik’e taje ta amsa, tun kafin ta dawo wajen zaman ta ta fara dubawa….ai kuwa bata iya k’arasawa wajen zaman nata ba sakamokon rikicewar da ta sake yi tashi d’aya ta shiga matsanancin tashin hankali……
Karantawa take yi tana sake duba takardar ‘expell’ d’in da aka bata ga sunanta b’aro b’aro a jiki, hankalinta bai gama tashi ba sai da taga dalilin korar!
“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un” shine abinda ta fara maimaitawa idanunta na zubar da kwalla, a hankali ta k’araso ta durk’usa a gaban teburin principal d’in ta fara magana muryar ta na rawa
“Ma, wallahi this is not the truth, pls don’t expel me, i promise I won’t talk to Abba ever again!. I don’t want my parents to find out about this. I have been framed here I swear….”
Cikin rashin walwala principal d’in tace mata
“Don’t worry your parents already know about this since yesterday, they are on their way now as we speak.”
Rushewa Maryam tayi da kuka, ta fara magiya, tana cewa “sharri aka yi musu” …..tana alk’awarin rabuwa da Abba har abada, amman principal d’in bata saurareta ba kawai dai tace mata “Ita fa ta riga ta gama magana, so ta jira zuwan iyayenta kawai.”
Metron kuwa munafuka in banda zuga principal babu abunda take yi, hadda cewa “ai ranar tun a clinic ya fara rungumeta. Waye waye”
Sai faman zuba dai take yi,
ba ita tayi shiru ba sai da principal ta aiketa ta je ta kira Zainab da wasu class mates d’insu.
Su Zainab sun shigo bai fi da minti goma ba Madu da Shuwa da Ya Usman suka shigo.
Da gudu Maryam taje ta fad’a jikin Shuwa tana kuka tana cewa “wallahi k’arya ake mata.” Kama kafad’unta Shuwa tayi sannan ta ajjiyeta a kujerar gefe, ba tare da tace da ita komaiba! Ta k’arasa suka je suka zazzauna a kan kujerun suka gaisa da mutanen wajen.
Bayan an gama gaisawa ne principal d’in tayi gyaran murya ta nuna Zainab tace “
Yarinyar nan ta zo ta sameni last week akan maganar sister d’inta da wannan Yaron” ta yi maganar tana nuna Abba kafin ta d’aura da cewa “I was surprised because irin haka bai tab’a faruwa ba, dan it’s a very strict rule ‘ba a soyayya tsakanin malami da d’alibi’!
I don’t know why they choose to break the rule. I called their house mistress first, Ina so ince mata ta sakama Yarinyar ido but to my surprise sai take ce mini ‘ai ta riga ta sani already, amman kawai dai gaisawa suke yi, kuma basa zance. Dai ya fad’a mata yana sonta ne amma basa soyayya a makaranta because she warn them and sun yi biyayya da abunda ta fad’a’ She gave me good reasons, wanda reasons d’in da ta bani ne ya sa na yi deciding to just let it go,
dukda na san it’s not allowed but kamr yadda tace if basa soyayya a makaranta I see no reason da zanyi interfering.
After two days ina zagaye da daddare, wanda ba kowa ne ma ya san ina yin hakan ba, saboda Ina yi ne to make sure all is fine. A time d’in na bi ta jss2 block and I saw them together, I know Maryam very well tunda shadow prefect d’inmu ce and Abbas shima ba b’oyayye bane shiyasa nayi saurin ganesu….ban ji d’ad’in yadda na gansu ba! He was holding a book tana so ta karb’a ya hanata, and they are sitting too close to each other! Na so inyi musu magana but a yadda raina ya b’aci a time d’in sam bana zan ma iya kallon Yaran.
So na yanke shawarar fara yiwa house mistress d’insu magana first, i was very disappointed a ita da su.
So, na sameta nayi mata magana and ta gaya mini cewa ‘wallahi bata san suna zama guri d’aya ba, that was when I called their metron, and she told me ‘ai tun time d’in da Abba ya fara zama night prep tare suke zama kullum, and sometimes they even hug, kuma basa tafiya sai kowa ya watse, in sun gama abinda zasu yi’.”
Kukan Maryam ne ya k’aru kafin tace “wallahi k’arya ne, Hajiya Shuwa dan Allah ki tsaya kiji nawa kar ki yarda da maganar su…..”
Cikin tsananin b’acin rai Ya Usman yace “Wallahi Maryam idan bakiyi mana shiru ba sai na b’abb’allaki a nan!!”
Ganin yadda ya taso yayo kanta kuma taga alamar ranshi a mugun b’ace yake dan bata tab’a ganinshi a irin wannan yanayi ba, ya sanya ta yi shiru, ta hau k’ok’arin tsaida kwallarta ta…
Numfashi principal d’in taja sannan ta ci gaba “Na kira 2 to 3 children a js2 and sunce gaskiya su basu tab’a ganin komai ba, kawai dai basa tafiya tare da su kamar yadda metron tace.
So hankali na ya d’an kwanta but dukda haka sai na kira Zainab saboda Ina son sake jin bayaninta dan Insan ta Ina zan fara “A nan ne ma take sake tabbatar mini da cewa ‘ai Maryam d’in already tana da mijin da zata aura a gida!.’
Na kira Yayan Abba dan in fad’a mishi halin da ake ciki ince yayi wa Abban magana ko In d’auki mataki, amma wani abun mamaki kamar had’in baki sai shima yake gaya mini cewa ai shima Abba tun bai kai hakaba already Mahaifinsu ya zab’a mishi wadda zai aura cousin sister d’insu, kuma kowa ya san da maganar….
Shi Ya’yan nasa ma he was very surprise da yaji wai Abba yana soyayya da wata…..
So definitely kunga ba soyayyar gaskiya Maryam da Abba suke yiwa juna ba kenan, ko?.
A time d’in bana son yanke hukunci cikin sauri, shiyasa
na saka Zainab da those two” ta yi su maganar tana nuna k’awayen Zainab da suka shigo tare, tukunna tace “nace su saka musu ido sosai.!
Yesterday around 11 metron taje gidana, saboda nace musu ko k’arfe nawa ne idan abu ya faru su sameni a gidana na quaters in dai inanan….
Banji dad’in abinda metron ta gaya mini ba at all, although shine abunda nake suspecting
but Maryam is one of our best students sannan d’a na kowa ne.
Kasa bacci nayi da jin maganan metron that’s why
nima kawai immediately na nemi land line d’inku…..”
Shiruuuu!! kowa yayi kafin principal d’in tace “Zainab, ku maimata musu abinda kuka fad’a mana.”
Zainab ce tafara magana
“Daman kullum idan ya shigo aji sai yayi ta kulata, tun yana b’oyewa har ya daina, tou akwai k’anwar k’awar mu a jss 2 itace ta fad’a mana abunda sukeyi, itace ta zo ta samemu jiyama tun kafin a tashi tace wai gashi chan ya d’auketa sun fita ba a san ina suka je ba!.
Mun yi ta jiranta a hostel bata dawo ba, daga k’arshe dai sai after 11 tukunna suka dawo
kuma data shigo har wanka tayi dan sai da na tab’a gashinta na tabbatar!. Shiyasa naje na samu metron ita kuma tace yanzu zata je wajen ki ba sai gobe b..”
Sai a lokacin Abba ya d’ago kai ya kalli Zainab da idanuwanshi da suka chanja kala..wanda hakan ne ya sa ta kasa k’arasa maganar ta.
House mistress d’insu ce tace “amman ku, kun tabbatar fita sukayi kuwa? Because d’azu da sassafe naje wajen gateman yace min jiya Abba shi kad’ai ya fita kuma sai wajajen 11.”
Da sauri Zainab tace “Ai gidansu na coppers
na staff quaters suka je……”
Ita kam Maryam zuwa yanzu muryarta har ta dishe tsabar kuka!! Madu ne ya kirata yace “ta zo!” Tana zuwa yace “Da gaske ne???”
Da sauri ta fara girgiza kai tana kuka, abin tausayi….
Metron sarkin zuga tace “ki ji tsoron Allah har wanka fa sukace kin yi!”.
Cikin k’ok’arin son fahimtar da su Maryam tace “Eh nayi wankan amman wallahi ba wank.....”
Bataga k’arasowar Ya Usman ba sai sauk’ar marin da taji wanda yasa ta fad’uwa a wajen gefen bakinta ya fara zubda jini, tana k’ok’arin tashi taga ya sake yunk’urawa da nufin rufeta da duka…..
Ta gama sadak’arwa tana jira taji sauk’ar dukan!
Jin shiru yasa ta d’ago, Abba ta gani ya kare mata…a hankali ya sunkuyo kanta ya kamo hannunta ya mik’ar da ita cikin tafin hannun nata ta ji yana cusa mata takarda
karb’a tayi tana kallonshi
shima Itan yake kallo
da idanuwanshi da suka yi jazir!! A hankali yace “I luv u Maryam.”
Bai tsaya jin fad’an da su metron suke mishi ba
na ‘ya kama hannunta a gaban iyayenta!’ Kawai ya juya ya fita.
Madu ne ya cewa Shuwa su tashi su tafi, hakan yasa ta mik’e ta yiwa principal sallama
wadda take ta bawa Shuwa hak’uri tana cewa “She is just looking out for Maryam, ba dan hakanba da ta barta a makarantar, gara ta tafi gidan iyayenta su saka mata ido.”
Jinjina kai Shuwa tayi sannan