Showing 9001 words to 12000 words out of 71576 words

Chapter 4 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt

hanya da zamu iya sanin hakan
face mu tashi aljni mai tsananin karfin
gudun da zai iya zuwa bakin kogin Bahar
Sufiya koda a cikin kwana bakwai ne yaje ya
gano mana zahiri Al;amarin:
Idan har su sarki maharaz ne ke samun
nasara to tabbas akwai tuggun da zan iya
shiryawa mu yiwa sarki dujalu juyin mulki
yadda ba zai taba iya karba karagarsa bA:
Amma fa idan mune muke samun nasara a
filin yakin sai dai mu rungume kaddara mu
cigaba da zaman hkri har ixuwa sa;adda
ajali sarki dujalu zaizo: yanzu babbar
matsalar ita ce gaba dayan aljanun dake
wannan nahiryar tamu sarki dujalu ya tafi
da su wannan yaki saura matansu tsofaffi
da yaransu wadanda baza su iya wanan Aki
ba:
Sarauyin aljani mai tashen samartaka da
kafin gudu data be ya rage a yanxu kua ba
wani bane face aljani barzuri wanda
yadawo da Gimbiya Hursiya daga CAN bakin
Tekun Bahar sufiya:
Barzaru ya kasance amintaccen sarki dujalu
na gani kasheni don haka bazai taba yarda
yayi mana wannan aiki ba sai dai maya tona
mana asiri:
Ya zama wajibi nayi shiti da kaina na bar
wannan nahiya tamu na tafi nean aljanin
dazai yi ana wannan aiki a cikin gaggawa.
Sa'ad da sadusa yazo nan a zancensa sai
hankalin kowa ya kara dugunzuma domin
suna ganin cewa ai babu isasshen lokacin
da za ayi wannan aiki:
Cikin alamun tsananin damuwa waziri ya
dubi sadusa yace yanzu a cikin kwana nawa
kake ganin za ka iya zuwa kasamo aljanin
da zai yi mana wannan aiki?
Sadusa yai murmushi yace ku bani kwana
uku rak Ai Al mari ne na tsafi:
Koda jin haka sai farin ciki ya lullbe waziri da
sauran yan majalisar:
Nan take suka salami sadusa akan cewa za
su jira dawowarsa nan da cikar kwana uku:
Nan dai taro ya watse kowa ya sulale ya tafi
gidabsa cikin wannan dare:
* * *
AL AMARIN Gimbiya Hursiya kuwa; tun
sa;adda fada ta watse ta shige cikin gidan
sarautar sai ta wuce izuwa cikin turakarta ta
zauna a gefe gadonta ta shiga tunani mai
zurfi.
A dai dai wanan lokaco ne wata kuyagarta
mai suna laziramat ta shigo cikin turakar
dauke da farantin shayi:
shi dai wannan shayi na ka:ida domin
kullum sai lazimat ta dauko butar shayin ta
tsiyaya a cikin wani dan karamin kofi na lu u
lu u ta kaiwa Gimbiya Hursiya:
Koda ta mikawa Gimbiya kofin shayin sai ga
ashe Gimbiya kuka take yi hawaye na ta
sartu kan kumatuwanta:
Al amarin da yai matukar dugunzuma
hankalin lazimat ke nan dubeta cikin
tsananin damuwa ba mai ajiye kofin shayin
akan faranti ta ce ya shugabata ki yafeni
idan nayi miki wani abu wanda ya bata miki
rai:
koda jin wannan batu saI Gimbiya Hursiya ta
sa hannu ta share hawayenta sannan tace
ya lazimat kiyi sanicewa a iya zamana dake
Tsawon shekaru baki taba yi mini wani abu
ba wanda ya bata min rai::
Wannan hawaye nawa dakika gayana zuba
bana komai bane face na tsananin bakin ciki
bisa karyar dana yiwa mutanen garin nan a
yau a fada:
Maganar gaskiya ban san abinda ya faru ba
a filin yaki domin ana daf da fara yakin ne
sarki shammaceni yasa aljani barzaru ya
sureni yai sama da ni kafin na ankara ya
luluka dani izuwa cikin gajimare:
Cikin abinda bai wucce kwanaki tara ba
muka iso nan gida, ni yanzu babban abin bakin cikina shi ne
idan sarki ya mutu bana son na gajesgi
kuma yazama duniya babu wani mutum
dana shaku da shi sai shi;
Mene ne amfanin naci gaba da rayuwa a
duniya bani da masoyi?
Mulki daula da arziki duk shire ne a wannan
duniya idan babu masoyi:
Soyayya itace abar da take kawar da dukkan
takaici da bakin cikin rayuwa:
koda Gimmbiya Hursiya tazo nan a zanceta
sai kunyaga lazimat takamu datsananin
tausayinta har itama kwalla ya cika mata
idanu ta dubeta tace ya shugabata to yanzu
ke wanne irin hukunci kika yankewa
rayuwarki?
Hursiya ta ajiyar zuciya sannan tace ni yanzu
bana bukatar koai face na koma can bakin
kogin Bahar Sufiya domin naga yadda
karshen wannan yaki zai kasance idan har
sarki mutuwa zai yi to zanso na mutu tare
da shi amma bana son ace sarki ya mutu ni
nacigaba da sarauta anan sbda basan cewa
kamar yadda mutne ke kin sarki haka nima
zasukini:
Nasani cewa dan uwana Azzalumi ne
tsawon shekara da shekaru mutanen dake
nahiryar nan basa jin dadi mulkinmu tun
iyaye da kakani, kin sani cewa nima bana son irin wannan
mulki da sarki ke yiwa jamaa amma ban isa
na hanashe ba don haka ciwon ido sai hkri:
Ni ina ganin cewa zai fi kyau ni da sarki duk
mu mutu a wajen wannan yaki domin a
sami sabo shugabanci a wannan nahiya
mutane su huta da mulkin zalunci a sami na
sauyin rayuwa mai dadi:
Koda Hursiya tazo nan azancenta sai ta
fashe da kuka Al amarin da ya kara jefa
kunyaga lazimat cikin tsananin tsananin
tausayinta kenan ta rungumeta ta
na mai rarrashinta har tadaina kukan
sannan ta ja jikunta daga cikin na tata
debeta tace;
Ya shugabata kiyi sani cewa a iyarayuwata
ta duniya ban taba zama da basarake mai
tunani da sani yakamata ba kamarki wanda
yake da jin kai gama son talakawansa tunda
gashi kin zabi ki mutu don kawai takawa su
sami rayuwa mai dadi:Ya shugabata kiyi
sani cewa rashinki a doron kasa ba karamar
asara ba ce domin samun mace mai kyau da
kyan hali irin naki sai an tona:
Ya kamata a ce kin sami saurayi kyakkyawa
kuma mai kyawun hali irin na ki domin
yazma abkin rayuwarki ku haifawa baya
abinda zasu amfanesu;
yayin da Gimbiya Hursiya taji wannan sai
murmushi ya subuce mata tace ai niban
yaba yin soyayya ba kiuma ban zaton zanyi
ta anan gaba har izuwa karshen rayuwata
ban san maye SO ba:
Tun ban taba kamani ba:
KAUNA kawai na sani irin wacce ke
tsakanina da dan uwana sarki dujalu da
kuma mutane ire irenku wadanda nayi sabo
da su sanadiyar zamantakewa;lokacin da
Gimbiya hursiya tazo nan a zanceta sai itaa
kuyanga lazimat
Tayi murmushi tace ya shugabata kada kiyi
kuri ko cika baki akan SOYAYYYA Domin
kuwa shI SO abu ne wanda baya sallama
bare ayi masa iso a duk yayin da yaga zuciya
yake nean shiga cikinta::
Karfin gudunsa ya wuce na iska ko guguwa
haka kuma DAFIN SO yafi na kibiya:
A duk sa:adda ya soki mutum to fa babu
wani magani da zai warka dashi face
kasancewa tare da masoyinsa::
Dajin wannan batu sai Hursiya ta bushe da
dariya sannan ta dauki wannan kofin shayi ta
kurba sau uku tace daga yau mun kulla gasa
nidake na ga wanda zai lashe gasar:
Ni Hursiya na cika miki baki cewar KIBIYAR SO
ba ta isa ta huda jikina ba bare ta samini dafin
da zan rasa maganinsa::
Duk ranar da kika lashe wnnan gasa in dai ina
raye nayi alkawari zan yantaki kuma zan baki
dukiya mai yanwa gaske:
Koda jin wannan batu sai kuyanga lazimat ta
kamu da tsananin farin ciki tace tabbas zamu
bambance tsakanin aya da tsakuwa kuma
lokacin ne zai raba wannan gardaa dake
tsakaninmu Hursiya ta yi ajiyar dogon numfashi
a lokacin data ajiye wannan kofin shayi sannan
ta kurawa lazimat idanu tace yanzu wacce
hanya kike ganin zan bina sami damar komawa
sansanin yakin nan a cikin yan kwanaki kadan
kafin yakin yakare?


Zan ci gaba.

Da fatan an tashi lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp.

MAZAN JIYA
Littafi na Hudu 4
Part G
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey


Yayin da lazimat taji wannan tambaya sai
hankalinta ya dugunzuma tayi shiru tana
tunanun har izuwa tsawon wadansu yan dakiku
kamar ba zatace komai ba.
Daga can sai ta kawo gwauron numfashi ta aje
sannan tace ya Shuganta akan bukatarki ta
biya zan iya sallaa raina da jikina sbda kauna
da aminci dake tsakaninmu don haka ki bani
kwana biyu rak zan je na biwata hanya wucce
nake gani cewa zata kaimu ga nasara::
Koda jin haka sai gimbiya Hursiya takamu da
tsananin farin ciki nan take ta bude wata farar
akwati ta debo dinare da yawa batare da sanin
adadinsa ba cikin tafin hannunta ta mikawa
lazimat tace ungo wannan ki tafi da shi sbda
nasan cewa yanzu aiki wannan zamani babu
wani wani aiki da yake tafiya ba tare da kudi ba:
Lazimat tacce haba ya shugabata ai wannan
kudn yayi yawa:
Hursiya ta kada kai tace ai girman wannan aiki
da nabaki yafi wannan dinare cikin turakar nan
tawa duka:
Hadarinsa kuwa dai dai yake da mutum ya sayi
ajalinsa inda zan baki dukiya cikin gidan
sarautar nan gaba daya ban biyaki ladan
wannan aiki ba:
Ki tashi ki tafi na sallameki sai nan da kwana
biyu ki dawo mini da jawabi mai dadi sai ki
wakilta wata daga cikin sauran kuyangina ta
cigaba da yin irin aikin da kika saba yimini::
Amma lallai ki sami mai amana wacce zata iya
rike sirrina:
kunyanga lazimat ta risina cikin biyayya tace
angama ya shugabata:::
WANNAN SHINE ABIN DA YAFARU A BIRNIN
SARKI DUJALU BAYAN ALJANI BARZARU YA
DAWO DA GIMBIYA HURSIYA DAGA BAKIN
TEKUN BAHAR SUFIYA INDA AKE SHIRIN
FAFATA YAKI TSAKANIN RUNDUNARSU DATA
SARKI MAHARAZ:::
* * *
ACAN Sansanin yaki kuwa awana na ukun da
akayi ana hutun yaki kullum inmal da sarki
mahazar suna zaune a gaban kabarin sarki yaki
Hibru suna kuka dare da rana:
Abinci a da kyar suke cin kadan idan Gimbiya
Mulaifa ta matsa musu tana mai yi musu tuni
da cewar idan fa basu ci abinci ba to fa bazasu
sami damar cigaba da yakin ba tunda bazasu
samu kuzari ba ajikinsu::
Wannan batu ne yasa suke daurewa su ci
abinci kadan bayadda zasu koshi ba:
A ranar dare na biyu ne sarki maharaaz inmal
da sauran manyan daraunsu na Yaki suka
zauna domin su tattauna akan yadda zasu
bullowa wannan yaki a wannan karo na uku
domin su sami nasara akan abokan gaba cikin
kankanin lokaci:
Wani barde da ake kira shamal shine ya fara
magana yana mai duban sarki maharaz yace ya
shugabana shawara ta ta farko dazna bayar ita
ce kamata yayi ana fara wannan yaki inmal tare
da manyan jarimanmu masu jarumtakar gaske
su yiwa sarki dujalu rubdugu domin a kashe shi
da wurin tabbas idan muka sami nasarar kashe
sarki dujalu mun karya logon abkan gabarmu
tunda a bangaren dakarunu na aljanu karfinsu
yazo daidai da na dakarun aljanun su:
koda jin wannan batu sai sarki maharaz ya
dubi kowa yace ya ku dirkokin birnina kun ji
shawarar da shamal ya kawo:
Shin kun amince da ita ko kuwa akwai mai korafi akanta?
Gaba dayansu sai suka yi shiru aka rasa wannan da zaice kala, sai inmal ne yai gyaran
murya sannan ya ce ai ko kadan wannan
shawarar da shamal ya kawo ba zata yi tasiri
ba:
dalilina na fadin haka shine masu iya magana
sunce MASO ABINKA YAFI KA DABARA:
kada ku manta cewa shi kansa srki dujalu zai yi
irin wannan tunanin da shamal yayi don haka
dole ne ya san dabarar da zaiyi yarufe wannan
kofa: abu na biyu da nakeso da nake so ku
gane shine:
Dakarun yakinsa suna da bakin naci fiye da
namu dakaru:
Idan muka tattara hankalinu akan sarki dujalu
kawai zasu sai damar daza suyiwa namu
dakarun mumunar barna, kafin inmal ya gama rufe bakinsa tuni shamal
ya tarin numfashinsa yace to wai shin kaanta
ne cewar sarki dujalu ya zama masaki mai
hannu daya:
wannan lalura da ta same shi zata rage masa
karfin da zafin nama:
inmal ya girgiza kai ya ce ba haka bane ai kada
mage ba yanka bane kuma ina so ka sancewa
mazanjen kwarai suna yaki ne da zuciyarsu
kafin jikinsu:
Ma ana taurin zuciyarsu da karfinta yafi na
hannayensu sbda haka wannan rashin hannu
daya na sarki dujalu ba zai rage shi da komai
ba face ma ya kara masa kuzari da mugun nufi
akanmu:
Sa adda inmal yazo nan a jawabinsa sai jikin
kowa yayi sanyi aka yi shiru ana tunani :
Jim kadan sai wani bardw shi KIMARU ya
numfasa yana mai duban sarki maharazz yace
ya Shugabana wai shi mezai hana goben da
dazar an busa kohon ci gaba da yakin nan ka
shammaci abkan gaba ka hallakasu da karfin
sihirinka?
Kafin kimaru yagama rufe bakinsa tuni sarki
maharaz ya shara masa mari sbda karfin marin
sai da kimaru ya tuntsure kasa ya mike zaune
wuf, cikin firgici yana mai sunkui da kansa kas::
sauran dakarun kuwa duk sai suka firgita suka
sunkuui da kawunansu kas don kada laifin
wani ya shafesu.
Sarki Maharaz ya dubi kimaru a fusace yace
shin kai kurma ne a lokacin da nayi rantsuwa
da sunan mai girma darbuza cewar ba zan yi
amfani da karfin sihiri ba tun a farkon wannan
yaki bisa yarjejiniyar da ke tsakaninmu da sarki
dujalu?
To ka sani cewa ni da sarki dujalu babu
wandazai yi amfani da karfin sihiri har a gama
wanna yaki tunda shima yayi rantsuwa da
ubangijinu kamar yadda nayi:
yanzu dai na fuskaci cewa gaba daynku babu,
Wanda yake da wata dabara ko sabuwar
hikima wacce zamu yi amfani da ita don ganin
mun saminasara r wannan yaki.
Abin da nakeso da ku kawa shine kowa yaje
yayi shirin tunkarar wanannan yaki gobe idan
aka fara yakin kowa yayi iya kokirinsa lallai sa a
tana ga mai rabo walau garemu kukuma
garesu.
Koda gama wannan jawabi sai sarki maharaz
ya mike tsaye ya tafi izuwa cikin tantinsa:
a sannan ne su bardw kimaru a suka tashi
suka tafi izuwa nasu tantunan aka bar sadauki
inmal a zaune shi kadai a lokacin da yada cikin
kogin tunani:
A wannan lokaci wata irin iska mai sanyi ke
kadawa:
inmal na cikin wannan tunanin ne yaji an taba
kafadarsa ta baya.
Cikin dan alamun razana inmal ya waiga da
sauri don a zatonsa aljanu ne keson tabashi, koda ya yi arba da wanda ke tsaye abayansa sai ya cika da mamaki ba wani bane face Gimbiya Mulaifa:
Mulaifa da inmal suka yiwa juna murmushi sannan ta zauna a kusa da shi suka dubi gabas
ba tare dayansu yace kala ba har izuwa tsawo
yan dakiku.
Inmal ne ya katse shirun yace menene ya
hanaki yin barci har izuwa tsawon wannan
dare?
Mulaifa ta sake yin murmushi a karo n biyu
sannan tace abinda ya hanaku yin barci kai da
abbana shi ne ya hanani:
Ya kai abin kaunata kayi sani cewa bamu taba
tsintar kanmu a cikin halin bakin ciki irin na
wannan lokaci ba sakamakon mutuwar
mahafinka::
Sannan kuma bamu san yadda karshen
wannan yaki zai kasance ba:
Ni babban abin ma daya dugunxuma hankalina
shine naga mahaifina jikinsa yayi sanyi gaba
daya akwai alamar cewa bashi da sauran
kuzari da sa ran samun nasara a wannan yaki:
Koda jin wannan batu sai inmal yayi ajiyar
zuciya ya ce ni kaina jikina yayi sanyi ba don
komai ba sai sbda ina ginincewa karshen
wannan yaki ba zai yi kyau ba:
Za a yi asarar miliyoyin rayuka ko dai ayi ragas
ko kuma ayi kare jini biri jini:
Ni babban abinda yake damuna guda biyu ne:
Abu na farki shine na tsaya nayi tunani na gano
cewa damu da su sarki dujalu duk muna yin
wannan yaki ne sbda son zuciya kawai
kowanne bangare suna son su mallaki kayan
yakin MAZAN JIYA don kawai su mulki duniya:
Wannan duk al:amarin ne na zalunci:
Ni ka zan fi son su mallaki kayan Yakin MAZAN
JIYA don kawai su mulki duniya, wannan duk al amarin ne na zalunci:
Ni ka zan fison na mallaki wadannan kayan yaki
na MAZAN JIYA don kawai na bar abin tarihi
na jarumtaka wanda baza ataba mantawa dani
ba:
Abu na biyu da yake damuna shi ne zuciyata
tana rawa akan allolin da ake bautawa a
wadannan nahiyoyo namu sbda na fuskanci
cewar suna yin karya:
Sau tari sukan fadi wani abun suce zai faru
amma kuma sai aga sabanin haka:
An ya kuwa ba kya ganin cewa akwai wani
ubangijin wanda yafi dukkanninsu wanda shine
ne mafi karfi da daukaka?
Koda jin wannan tamabaya sai mulaifa tayi
ajiyar zuciya sannan tace hakika duk abinda ka
fada gaskiya ne kuma duk mai hankali dole ne
yayi tunani akan hakan:
To amma abinda nake so naki daga gareka shi
ne shin kana da wata hujja ne mai karfi wacce
tasa ka fadin hakan?
Inmal yayi shiru yana mai daga kansa sama
cikin alamun tunani sannan yace akwai wani
lokaci a baya da marigayi mahaifina ya gaya
mini cewa akwai wani ADDINI da ake kira
ADDININ MUSULUNCI: YA tabbatar mini da
cewa bai taba ganin mai karfinsa ba kuma yaji
ajikinsa cewar shine addinin gaskiya sbda
abinda ma abotansa suka sa a gaban koda jin
wannan batu saijikin Gimbiya mulaifa yai sanyi
tayi shiru har izuwa tsawon yan dakiku sannan
tadubi inmal
Inmal tace ni kaina yanzu naji a a cikin raina na
gamsu da wannan addini domin ka karbi
addininin mu sami taimakon ubangijinsa bisa
wannan gagarumin yaki dake gabanmu:
Inmal ya ja dogon numfashi yace hakika
maganarki dutse ce amma tunda babu damar
hakan sai mu rungumi kaddara:
Ta shi muje mu kwana domin kuwa dare ya
raba sosai:
Yana da kyau mu sami barci a wannan dare
sbda gagarumin aikin dake gabanmu a gobe::
mulaifa ta mike tsaye tace zanje dai na kwanta
amma tun nayi barci ba zan iya ba tunda ina
cikin fargaba da zullumi bisa abinda ka iya
faruwa gobe:
Hatta kai da sarki duk nasan cewa baza ku iya
rintsawa ba a wannan dare::
inmal yayi murmushi karfin hali yace hakika
maganarki gaskiyace.
Koda gama fadin haka sai ya kama gannun
mulaifa yaja ta izuwa ga tantin sarki:::
Koda suka iso kafar tanti sai ta dubeshi tace
inason na karar da wannan dare tare dakai
gaba dayansa tund babu mamaki daga yau ba
zamu sake samun damar jin muryar juna ba da
ganin fuskokinmu.
Koda jin haka sai inmal ya girgiza kai ya ce ai
duk wuya duk dadi komai RINTSI DA TSANANI
ina san ran cewa bazamu rabu ba kumma
muna tare.
Ki sani cewa mahafinki ya gaya mini cewa bisa
binciken da yayi a hallarar tsafinsa lallai mutum
hudu zasu tsira da rayuwarsu a wannan
sansanin yaki:
Kuma mutum biyu daga bangare abkan
gabarmu ne ragowar mutum biyu kuma daga
namu ban garen:
Ina ji a jikina cewar kina daya daga cikin
mutane biyun :
koda inmal yazo nan a zancensa sai idnsa suka
ciko da kwallah har hawaye yazubo masa :
Al amarin da ya dugunzuma hankali mulaifa
kenan ta rungume inmal tana mai cewa yakai
abin kaunata ina dalilin zubar wannan hawaye
naka?
Inmal yace ba komai ne yasani wannan kuka
ba face tunanin cewa zan iya rasa babban
masoyina na biyu a wannan yaki wanda na
tabbatar da cewa yana sona kamar yadda
mahafina marigayi yake sona.
Dajin wannan batu sai hawauye yazuvowa wa
mulaifat tace Tabbas na san ba
wani kake nufi ba face mahaifina::
Koda jin haka sai inmal ya dada kankame
mulaifa a kirjinta yana mai sake fashewa da
sabon kuka: itama ta tayashi da kukan::::
A haka dai suka karasa cikin tantin na ta
suka zauna suka cigaba da hira maimakon
su kwnta su yi barci basu gushe ba suna
hira har sai da Alfijir ya keto a sannan ne
mai sacewa ya sacesu basu sani ba suka
kama gyangyandi:::
Sai da gari ya waye sosai har rana ta hudo
bayan kowanne bangare na mayanka sun
kimtsa sannan aka yiyo gayya aka taho filin
daga:: azuvowa wa mulaifat tace Tabbas na
san ba wani kake nufi ba face mahaifina::
Koda jin haka sai inmal ya dada kankame
mulaifa a kirjinta yana mai sake fashewa da
sabon kuka: itama ta tayashi da kukan::::
A haka dai suka karasa cikin tantin na ta suka
zauna suka cigaba da hira maimakon su kwnta
su yi barci basu gushe ba suna hira har sai da
Alfijir ya keto a sannan ne mai sacewa ya
sacesu basu sani ba suka kama gyangyandi:::
Sai da gari ya waye sosai har rana ta hudo
bayan kowanne bangare na mayanka sun
kimtsa sannan aka yiyo gayya aka taho filin
daga.

* * *

Sarki Dujalu akan gaba tare da zakwakuran
dakarunsa cikin gagarumar shigar yaki mai
tsananin kwarjini fiye da wadda suka yi a yakin
daya gabata:
* * *
A bangaren su sarki maharaz kuwa inmal ne
akan gaba shima tare da nasu zakwakuran
mayakan ababan dogaro:
A kowanne bangaree kuma a sararin samaniya
aljanu ne ke shawagi rike da muggan makai na
KARE DANGI::
Kawai jira suke a basu umarni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login