Showing 12001 words to 15000 words out of 71576 words

Chapter 5 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt

su afkawa abkan
gaba.
Sarki maharaz ma sai gashi akan gaba kusa da
inmal rike da takobi da garkuwa:
Al amarin da yai matukar baiwa inmal mamaki
ke nan kuma ya firgitashi ya dubi sarki
maharaz cikin tsananin damuwa yace Ya
Shugabana mene ne ya kawoka nan gaba
alhalinka san cewa kai ba gawurtaccen ma yaki
bane kuma gashi ba za ayi amfani da karfin
sihiri ba a wannan yaki face tsagwaron karfin
dantse kwarewa da sanin makama:
Sa adda sarki maharaz ya ji wannan tambaya ta
inmal sai yayi guntun murmushi cikin yake yace
ya kai dana kayi sani cewa ni yanzu komai na
duniya yafita daga raina koda mun sami
nasarar wannan yaki kuma mun sami nasarar
dauko Takobin SAIFUL LUJARA bani da sauran
bukatar na mulki duniyar tunda abkan jin dadin
mulkin nawa bbu shi a lokacin da burin nawa
ya cika na mallaki kayan yakin maxan jiya a
sannan ne zan biya abkina Hibru wahalar
bautar daya yi mini da kua hkrin da yayi dani na
tsawon shekaru ina wulakantashi da rashin
jansa a jikina::
ina so kasani cewa yau ne ranar farki da zanyi
yaki a cikin fishin da ban taba yi ba sbda haka
lallao zan baka mamaki a wannan yaki ::
Zan yi gagarumar jarumtaka irin wacce ban
taba yi ba kuma zan ragargaji abkan gaba da
yawan gaske.
Sa'adda sarki maharaz ke wannan jawabi sai ya
hango gimbiya mulaifa a can bayan mayakansa
a tsaye bisa kan wani dutse mai tudu tana
hango abin da ke faruwa:
koda ganinta sai idanun sarki maharaz suka
ciko da kwallah ya dubi innal yace yakai dana
kayi sani cewa a bayan wannan yaki ne uwa da
uba a waken mulaifa sbda haka na damka
amanarta agareka:
Ina mai farin ciki daya zamana cewa yata ta
kamu da tsaananin kaunarka ko ba komai na
san cewa ba zan mutu na barta a matsayin
marainiya ba mara kowa ko masoyi ba na san
tana da kai.

Zan ci gaba.

Da fatan an tashi lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp.

* * *
A dai dai wannan lokaci ne sarki dujalu ya zare
takobinsa da hannunsa na hagu daya
dungulmin nasa na dama kuwa na boye acikin
rigar da ke jikinsa::
yana zare takobin tasa kuwa sai yadubi inmal
ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa
mai amsa kuwwa hari sai da kasa takama
girgiza kamar zata tsage komai ya rufta cikinta
sannan yace ya kai da mai kamar ubansa kayi
sani cewa yakin da zamu yi yau ba irin wanda
muka yi bane a karon farko kuma ba irin na
karo na biyu bane:
Yanzu zamu kaure ne da yaki kwanmu da
kwaekatarmu:
Ma ana mu cakude mutanenmu da aljaninmu
kuma ba yaro ba babba babu tsoho ko
tsohuwa bare mace ko namiki:
babu sani kuma bbu sabo Zamu yi ta yi har sai
mai nisan kwana a cikinmu ya tsira da
rayuwarsa:
Amma bisa sharadin nan dai na farko wato
babu batun amfani da karfin sihiri sai
tsagwaron karfin dantse:
Kafin inmal ko sarki maharaz daya daga cikinsu
ya budi baki yace wani abu tuni sarki dujalu
yayi nuni da takobinsa izuwa ga rundunar su
sarki Maharaz.
Wohoho! Ai kuwa nan take gaba dayan
dakarunsa mutane da aljanu suka kama zare
makaman:
Karar zare makaman ta cika dodon kunne da
dajin gaba daya tamkar ana aiki da dukkan
makerun duniya:
Ai kuwa suma rundunar tasu sarki maharaz sai
suka zazzarenasu makaman:
A lokacin guda kowannen bangare suka rugo
da gudu suna ihu da kururuwa domin a
gwamutse:
Wohoho Inda ace mutum na tsaye a gefe daya
yana kallon wannan sansanin yaki daga nesa
kadan to da nan take zai tsure da gudawa sbda
tsananin tsoro da fargabar abinda zai faru, kai hatta kasa sai mutum ya tausaya mata sbda
girgiza ta kama yi kamar zata rufta da duk
abinda ke samanra sbda tsabar dudufniyar
kafafuwan bil adama dana aljanu sararin
samaniya kuwa sai yauo bakikkinri sbda ha
yakin bala in dake fita daga cikin bakunan
aljanu gami da sautin ihunsu mai haddasa
tsawa da walkiya ai kuwa rundunonin biyu na
haduwa aka ruguntsu me da masifaffen bala in
yaki wanda yafi gaban bayani mai bayani:
fasaltawar mai basira ko labarin mai labari
kawai sai dai abinda ido ya iya tantancewa:
tartsatsin wuta ya tinka fallatsi a sararin sama
yana zuvowa kasa yana haddasa gobara.
KAICO! WANDA BAI SAN YAKI DA MASIFA BA
SHINE YAKE FATAN SU:
A wannan rana duniyar gaba dayanta sai da ta
yi girgiza tamkar zata nutse i zuwa cikin
karkashin kasa:
Duk wani abudaya kasance mai rai walau
mutum aljan dabba tsuntsu ko kwaro sai daya
firgice yayi nadamar zuwn wannnan rana:
Nan fa filin yakin ya ruguntsume gami da
hautsinewa da dumulmulewa aka shiga cin
kasuwar daukar rayuka:
jini kuwa daya soma fallatsi da malala gami da
tsartuwa a sama da kasa sai da kalar bishiyoyi
mutane da aljanu suka koma jajaye suka rine
da jini babu kyan gani:
Sai da takai ta kawo cewa aljanu nasa shaida
yan uwansu aljanu mutane basa gane yan
uwansu mutane; banda sara da suka babu
abinda ake ji:
Sassan jikin bil ada;a kuwa suka rinka shawagi
a sararin sama suna zubowa kasa tamkar
ruwan samansu akeyi::
* * *
Wohoho! JARUMTAKA KYAUTA DAGA ALLAH:
WANDA DUK ALLAH YABASHI
SADAUKANTAKA GAMI DA JURIYA DA NACI
TO FA SAI DAI AZUBA MASA NA MUJIYA KO
KUA AYI MASA ALLAH YA ISA!
DOMIN YAZAMA ALAKAKAI KO KUMA ACE
KADANGAREN BAKIN TULUA KARSHI A KAR
TULU A BARSHI YAYI BARNA.
Duk inda sarki dujalu da jarui inmal suka sa
gabansu sai dai kaga mazaje na zubowa kasa
tamkar ana sassabe a gona:
Sai da aka shafe sa a bakwai ana asarar
miliyoyin rayuka amma duk bala in da ake yi
inmal da sarki dujalu suna ta laluben juna
amma sun kasa haduwa sbda bala in yaki gami
da cakudewarsa::::::
Al amarin sarki maharaz Kuwa a wannan rana
yayi shammace kuma yayi matukar bada
mamaki domin shima sai yazamo gagarumin
FASA TARO mai TARWATSA MAZA:
domin duk inda ya durfafa sai dai kaga ana
zubewa tamkar ana karkada bishiyar busassun
ganyaye:
Takobinsa ma gaba daya rinewa tayi tazama
jajawur kamar yadda dukkkanin jikinsa yayi: Kai
a wannan rana zufar jini ceta lullube fuskokin
mutane aljanu har sai sun goge jinin dake
fuskokinsu sanan suke iya gani:
kai sbda tsananin bala i da masifar wannan
yaki sai gaba dayan nahiyar da ake wannan
mugun yaki sai da tayi bakikkirin tayi duhi
dundum Tartsatsin wutar da ke tashi
sakamakon haduwar makaan yaki kawai ya
rinka haskawa har ake iya gane juna:
Ana cikin wannan bakin gumurzu ne sarki
maharaz ya ga wani bakon jarumi a cikin jama
arsa yana ta ragargaza abkan gaba:
Jarumin ya rufe fuskarsa da jakinsa gaba daya
yaddda an kasa shida namiji ne ma ko mace:
Yana rike da takubba guda biyu kuma shima
duk inda sarki maharaz ya dauke kafarsa anan
yake sa tasa.
Duk sa adda aka kai wa sarki maharaz wani
mummunan hari sai kaga wannan bakom
jarumi ya kareshi:
Babu abinda ya daurewa sarki maharaz kai
face tsananin zafin naman jarumin jarui da
tsananin jarumtakarsa tamkar ta inmal:
Burin sarki maharaz shi ne yaga fuskar wannan
bakon jarumi amma abu ya gagara:
Ai kuwa shima inmal sai ya hango wannan
bakon jarumi koda yaga irin gagarumin aikin da
yake yi gami da kare rayuwar sarki maharaz sai
ya cika da dumbin farin ciki:
ya sami dadin kwarin guiwa da kuzari ya ci
gaba da tagargazar maza:
KAICO MUTUWA RIGAR KOW:
BALA I BA A SA MAKA RANA:
MUGUN JI DA MUGUN GANI BA SHI DA DADI:
TSAUTSAYI DA ASARA BASA JIN BIRKI IN
SUKA TAHO TAMKAR KUMALLO SUKE BABU
MAI IYA TSAIDA SU::::
KAICO MUTUWA RIGAR KOWA, BALA I BA A SA MAKA RANA:
MUGUN JI DA MUGUN GANI BA SHI DA DADI:
TSAUTSAYI DA ASARA BASA JIN BIRKI IN
SUKA
TAHO TAMKAR KUMALLO SUKE BABU MAI IYA
TSAIDA SU::::
* * *
Haka dai aka cigaba da wannan yaki wanda
tun daga farko kafuwar duniya kawo i
yanzu ba a taba yin makamancinsa ba
domin sai da aka kwana tara gami da sa a
tara ana zubar da mazaje da aljanu da
mutane a kas a sannan ne tsananin gajiya
da nadama ta sa kowane bangare yayi
janyewar dole aka ja da baya domin
makogwaron kowa ya bushe sbda tsananin
kishirwa:
Hanji cikin kuwa ya kananade ya daure sbda
yunwa:
Shin kasan ruwan Kogin BAHAR SUFIYA
wanda ya rine ya zama jini tafarfasa yake
sbda masifar tartsatsin wutar dake zbowa
cikinsa.
Da Zarar mutum ya tsoma hannunsa a ciki
domin ya debo ruwan jinin ya sha ya kawar
da kishirwa sai kaga nan take hannun nasa
ya kone tamkar a cikin wuta ya tsomashi::
** *
Lokacin da kowanen bangare ya ja da baya
aka dai na sara da suka sai gaba dayan
duhun da ya mamaye sama da kasa yayaye
tamkar da can a cikin bakin dare ake gari ya
waye:
A sannan ne idanun kowa suka bude sosai
aka ga irin mummunar asaran rayukan da
akayi:
Da zazar mutum ko aljan ya dubi kas sai
yaga ashe kowa akan gawarwaki yake
tamkar da gawar aka yi kasar wajen duka
sai dai kaga gawa kan gawa; lodi ajan lodi
har tana tsiri tana ruguzowa kasa:
A sannan ne mazaje suka kama mugun haki
kamar ransu zai fita daga cikin gangar
jikinsu aka fara kallon kallo aka fara iya
shaida juna:
sai gashi sarki dujalu da jarumi inmal sun yi
arba da junansu ashe ma tazarar da ke
gsakaninsu bata wuce taku goma ba amma
wani iko na allah duk tsawon kwanakin da
suka shude ana wannan bakim artabu ko
sau daya basu hadu ba sun yi gaba da gaba:
A dai dai wannan lokaci ne bakon jarumin
cikin rundunar su sarki maharaz ma ya cire
hular karfen da ke kansa sai ga dogon gashi
na mace mai tsananin baki da sheki ya zubo
kasa, BA WATA BACE FACE GIMBIYA MULAIFA!
Al amarin da yai matukar girgiza kowa
kenan a filin yakin aka cika da dumbin
mamaki:
Sarki maharaz dake tsaye a can gefe daya
yana ta faman haki baisan saadda ya saki
takobinsa ba ta fadi kasa ba sbda tsananin
mamakin ganin cewa ashe yarsa ce gimbiya
mulaifa bakuwar jarumar da tayi ta
ragargazar abkn gaba::
Abinda yai matukar daure masa kai shine
yaushe mulaifa ta koyi yaki haka har ta
kuma tasami wannan gagarumar
jarumtakar amma bai sani ba?
Koda sarki dujalu ya hango sarki maharaz
sai ya yunkura da nufin ya ruga izuwa
gareshi domin ya gagauta hallakashi ya
kunsawa jarumi inmal bakin ciki a karo na
biyu:
KwatsaM! Ba zato b tsammani sai aka ji an
busa kahon tsai da yaki daga kowannen
bangare::
Cikin tsaninin bakin ciki sarki dujalu ya mai
da takobinsa cikin kufe sannan yadubi a
dadin gawarwakin jama arsa na mutane da
aljanu ya kwantantasu da nasu sarki
maharaz sai ya ga kusan kunnen doki ne
amma kuma a kaso goma na kowannen
bangare An karaar da kaso bakwai bakwai:
Al amarin da yai matukar dugunzuma
hankalinsa keanan ya tabbatar da cewa lallai
RAGAS aka dada yi a cikin wannan yaki.
Kawai sai sarki dujalu ya durfafi inda sarki
maharaz ke tsaye:
Har inmal ya yunkura zai tareshi sbda
tunanin ko cutar da maharaz zai yi:
sai sarki maharaz ya dagawa inmal hannu
yana mai yi masa nuni da ya dakata:
inmal ya vi umarni ya tsaya a inda yake har
sai da sarki dujalu ya iso daf da inda sarki
maharaz yake tsaye yadda har suna iya jin
numfashi juna sannan yace yakai babban
abkin gabata kayi sani ce wa hakika ka
shammaceni ainun domin ban taba zaton
cewa kai da yarka kuna da gagarumae
jarumtaka haka ba:
To amma ka sani cewa idan aka dawo filin
daga zamuyi karo ne na karshe:
Na rantse da darajar abin bautata ba zaku
tsallake masifataba:::
Da wannan hannunawa guda daya sai na
dada kunsa muku bkin cikin da bazai taba
shafewa ba a cikin kundin tarihin
rayuwarku::
Lokacin da sarki dujalu ya yazo nan
azancesa sai sarki maharaz ya bushe da
dariya lokaci guda kuma
ta turbune fuska ya dakawa sarki dujalu
tsawo ya ce yakai babban abkin gabata kayi
sani cewa mulki da daukaka ba banza bane:
Duk dan sarki dole ya gaji jarumtaka domin
ba a yin mulki a banza:
na dade ina boye jarumtakata kuma ina
tandinta sbda zuwan irin wannan rana: ina
mai tabbatar maka dacewa koda zaka cusa
mana wanna bakin cikin a karo na biyu kaar
yadda ka kunsa mana na farko ka rabau da
babban masoyinmu sarki yaki Hibru to kai a
kwa sai mun kunsa maka bakin cikin da zai
bibiyeka har izuwa karshen rayuwarka.
Koda gama fadin hakan sai sarki maharaz ya
juya ya nufin sansannsu gaba dayan sauran
jama arsa wadanda suka yi saura mutane da
aljanu sai suka bi bayansa sai jarumi inmal
da mulaifa suka tsaya ana kallon kallo
tsakaninsu da sarki dujalu a lokacin da suma
jama ar sarki dujalu suka juya suka nufi
sansaninsu:
tsirarun dakaru na kowannen bangare ne
suka tsaya suna tatara gawarwakin yan
uwansu suna tarasu a waje guda domin
akonesu sbda yawnsu yafi karfin ace za a
binne::
Sai da ka shafe kusan dakika dari da ashirin
ana kallon kallo gami da harara tsakanin
sarki dujalu da su inmal sannan mulaifa ta
zo ta kama hannun inmal ta janyeshi suka
tafi izuwa nasu sansannin suna waigen
sarki dujalu:
Har sai da su inamal suka bacewa dujalu
dagani sannan shima ya juya a fusace ya
nufi nasu sansanin
* * =
bayan kowa ya huta hankalo ya dawo jiki:
wato kawar da yunwa da kishirwa:
MULAIFA da inmal na zaune a cikin tanti
suna hutawa har izuwa tsawon lokaci
daynsu bai ce uffan ba sai inmal yayi gyaran
murya yana mai dubeta yace yake abar
kaunata;
kiyi sani cewa a yau ya da uba sun yi
matukar shammatata kuma sun bani
mamaki:
ashe keda sarki kuna da gagarumar
jarumtaka haka amma ban taba sani ba? To
wau shin dama kuna karbar horon yaki ne a
boye batare da kowa yasani ba???
Koda jin wannan tamb&ya sai gimbiya mulaifa
tayi dariya sannan tace ni kaina ban taba sani
cewa mahaifina yana da irin wannan
gagarumar jarumtakar ba:
Amma tawa jarumtakar na sameta ne daga
wajen wanda ya ko ya maka::
Koda jin wannan batu sai inmal ya sake
mamaki ya dubi mulaifa cikin alamun rashin
yarsa da batunta yace haba masoyiyata ya ya
zaki min da wani zance na rainin hankali?
Yaushe mahaifina ya kooya miki yaki amma ko
sau daya ba taba gani ba alhalin ke boyeki ma
ake yi a cikin gidan sarauta babu wanda ya isa
ya je kusa dake?
Sa adda mulaifa taji wannan batu sai ta bushe
da dariya sanan tace yakai abin kauna kayi sani
cewa mahaifinka bashi da iyaka a cikin
gidanmu face daki guda daya wato dakin da
maigirma darbuza yake:
Ba zan taba mancewa da ranar da mahaifika ya
fara koya mini yaki na:
Abun ya faru ne a wani yammaci ina zaune a
cikin farfajiyar turakata a cikin lambu ina
shakatawa cikin nishadi ina kallom furaanni da
kananan tsutsaye wadanda aka killace acikin
kanannan kejina suna ta dan tsattsage
tsattsagesu a ciki abin gwanin ban sha awa
kasancewar su kyawawan tsutsaye masu
launin jiki kala kala.
Kwatsam Ina cikin wannan hali sai na hango
marigayi shi kadai ya durfafo cikin lambun::
Nan take na mike tsaye da sauri na ruga
gareshi ina mai risinawa cikin biyayya da nufin
na duka na gaishe shi amma sai yai sauri ya
kama kafaduna ya tasheni tsaye yace haba
ranki yadade a ina kika taba ganin ubangida ya
dukawa bawansa?
Koda naji wannan tambaya sai na dubeshi a
cikin mamaki nace ya kai abkin abbana hakika
kabani mamaki domin ban taba zaton cewa
wannan kalma zatafito ba daga bakimka duk
da cewae nasan a halin yanzu mahaifina baya
girmamaka kuma baya janka a jikinsa na san
cewa kana da babban matsayi a wajensa
wanda yakasance boyayyen al amarin:
Dajin wannan batu sai shima marigayi ya cika
da tsananin mamaki ya dubeni yace dani
mahaifinki ya taba baki balarin matsauina ne
wajensa???
Da jin haka sai na girgiza kaina nace ko kadan
bai taba gayamin ba amma naga tarihin duk
alakar da ke tsakaninku ne acikin kundin tarihin
rayuwarsa wanda ya boyeshi acikin wata
akwattu da ke karkashin gadonsa na barci::
Duk duniya babu wnda ya isa ya iya bude
wannan akwati sbda an kulleta ne da karfin
wadansu dalasimai na tsafi guda saba in da
daya:
Dole sai mutm ya hadasu sannan zata budu::
Tun ina da shekara shida a duniya nake jin
sarki yana karanta wadannan dalasimai na tsafi
kullum da tsakiyar dare a cikin turakarsa kuma
baya daga murya a duk sa adda zai karantasu
sai dai na jiyoshi kamar yana yiwa wani rada::
Tun a sannan na ke labewa na kara kunnenaa
ina sauraron abin da yake fada amma ban sami
ikon haddace kalmoin ba sai a ranar nan da
kayi laifi aka bankareka a saa aka yi maka
wannan mummunana hukunci::
A ranar ne na bude akwatin sarki naga tarihirin
A ranar ne na bude akwatin sarki naga tarihin
alakarsa da mahafinka kuma naga wani babban
sirri wanda bazan iya gaya makashi yanzuba
saidai a bayan wannan yaki idan muna raye::
lokacin da Gimbiya mulaifa tazo nan a zancenta
sai jarumi inmal ya cika da tsananin mamaki yai
shuru yana mai kallonta cikin mamaki:::
kada ganin haka sai tayi masa murmushi
sannan ta kwanta yana mai dora kanra akan
cinyanta domin ta dada huta gajiyar yaki::
WANNAN SHINE ABIN DA YA FARU A
SANSANIN YAKI NA BAKIN TEKUN BAHAR
SUFIYA BAYAN AN FAFATA KAZAMIN
MASIFAFFEN YAKI A KARO NA UKU::
* * ¥
A CaN Birnin sarki dujalu kuwa karshe gari da
sassafe tun kafin alfirjir ya keto boka sadusa
yayi shirin tafiya wata nahiyar dabam domin
neman aljanin da zai aika can bakin kogin
bahar sufiya a matsayin dan leken a sirin
wanda zai gano musu halin da ake ciki:::
boka sadusa yanada matar aure guda daya
wata kyakkyawar mace wadda ake kiraa
Hunaisa sai kuma da Guda daya wani karamin
yaro dan kimanin shekara bakwai 7 wanda ya
kasance kyakkyawa kuma allah ya hore masa
basira hikima da sauran fahimtar al amari har
da hasashen abin da ka iya faruwa a gaba.
Allah ya jarrabi boka sadusa da matukar son
wannan da nasu mai suna HALYAL kuma sun
shaku matuka yadda ko kadan basa son
rabuwa da juna dai dai da kwana daya:
Wani abin mamaki shi ne babu yadda boka
sadusa bai yi ba akan ya koyawa halyal ilimin
tsafi amma ko kadan shi Halyal bashi da ra
ayin ya gaji ubansa a wannan bangare::
Shi dai Halyal bashi da wani buri a rayuwarsa
wanda yafi ya halarci yaki koda sau daya ne a
rayuwarsa amma sadusa ya hanashi:
babu irin rokin da Halyal bai yiwa Sadusa ba
akan ya kyaleshi ya tafi izuwa bakin kogon
bahar sufiya domin ya gawannan gagarumin
yaki wanda yayi Hasashen akana cewar yaki ne
wanda ba a taba yin kamarsa ba a duniya kuma
ba a zaton za ayi anan babban burin Halyal
shine ya ga jarumtaka a fili yadda maza ke
dakawa maza gumba a hannu kuma shima
yana son anan gaba ya zama gawurtaccen
jarumi wanda zai shahara a duniy ammma da
yake ra ayinsa ya sha bamban da na mahafinsa
bai taba samun damar koyon yaki ba sannan
kuma ko kadan bashi da wata jarumtaka ko
sadaukantaka a jikinsa al aarin da yasan asa
bakin ciki da takaici kenan a cikin zuciyarsa.
bayan sadusa ya gama shiri tsaf Ya sanya
tufafinsa kua ya dauko jakar guzurinsa sai ya
shiga cikin turakar matarsa Hunaisa domin ya
yi musu sallaa:
ita kadau a zuane tana kalaci::
Cikin mamaki ya dubeta yace ina Halyal yake?
Koda jin wannan tamabaya sai itaa ta dubeshi
cikin mamaki tace ai yau halya ya rigani tashi
ma:
Tun dazu yai wanka ya kitsa har ya dauki
jakarsa ta tafiya don ya shaida mini cewa
xakuyi wannan tambaya:
Koda jin haka sai boka sadusa ya murtuke
fuska ya ce aa ni bamuyi haka da shi ba kuma
ba zan yarda nayi wannan tafiyar mai hadari ba
da shi:
wai shin ma yanzu ina Halyal din yake??
Hunaisa ta ce yana can kofar gida ya jiranka:
Ni dai ina rokinka da girman tsofafinka ka
amince masa kuyi wannan tafiya .....
Ni dai ina rokinka da girman tsofafinka ka
amince masa kuyi wannan tafiya:::
Tare domin kuwa ya kwallafa ransa gaba daya
akanta sbda yana gani cewa wannan ce kadai
damar da yake da ita da zaije sansanin yaki
yaga yadda ake zubar da jarumtaka tunda ka
gaya mana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login