Showing 63001 words to 66000 words out of 71576 words

Chapter 22 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt

na asa wasiyyar masoyiyata.
Nan take shima Aljani Maruful Dauwaz ya murdewa kansa wuya ya fadi kasa matacce.
A dai dai wannan lokaci ne Sharlis ta zqre Takobinta ta yunkura zata afkawa Sarki Laffaru sai ya dakatar da ita da hannunsa ya dubeta yace,
To yanzu idan ma kin kasheni meye ribarki?
Ni kaina yanzu duniyar ta fita daga raina. Ki duba kigani na rasa yata, kuma na rasa matata, kin rabani da mulkina, kin rabani da kasata, me zan zauna nayi a duniya , wanne dadi ko farin ciki ne yai mini saura? Zan tafi na bar miki duniyar in yaso keki ci gaba da jin dadinta idan harbtana da dadin idan babu masoyi.
Kafin Sharlis ta ce wani abu tuni Sarki laffaru ya zaro wuka a jikinsa ya kiba a cikinsa.
Nan take shima ya sulale kasa matacce.
A dai dai wannan lokaci ne Yaldisa tarugo wajen da gudu tana kuka bisa hango gawar jarumi Shaddadu.
Ai kuwa itama Sharlisa sai ta yunkura zata cakawa kanta Takobi a ciki, ammavsaibYaldisa tadaka tsalle sama ta buge Takobin ta fadi kasa ta dakawa Sharlis tsawa tace, Idan kuma kika kashe kanki waye zaici gab da mulkin Birnin kufa?
Idan babu ke wa zamu kalla mu tuna da masoyinmu?
Na sami labarinki kaf a wajen masoyina Shaddadu.
Tabbas Sarki laffaru yaci zarafinki dana danginki amma kin wahalar da kanki akn daukar fansa gashi ta janyo miki asarar da tafi wacce kika yi a baya.
Sau tari hakuri shine ya fi komai a wannan rayuwa.
Koda jin haka sai Sharlis ta sake fashewa da matsanaicin kuka, ta zunguri cikin tsuntsun tsafinta ya sauko kasa ta dira.
Ita kuwa Yaldisa sai taje ta sare kan Sarauniya Zubaina ta dagashi sama a dai dai lokacin da ragowarbDakarun gidan suka rugo wajen.
Duk wadanda suka karaso suka ga kan Sarauniya Zubaina a hannun Yaldisa kuma sukaga layu da gurayenta na tsafi sai su zube kasa suyi mata sujjada.
Nan take aka dira Yaldisa akan karagar mulku, sannan aka shiga binne gawarwakin su jarumi Shaddadu.
Sai da aka kwana bakwai ana bikin binne sun amma dare da rana Sharlis bata da abin yi sai kuka
Abincima sai Sarauniya Yaldisa ta dura mata abaki sannan take ci.
Bayan an gama bikin binne su ne Sharlis ta yiwa Yaldisa sallama ta hau kan tsuntsun tsafinta ya tashi da ita sama tanabeaigen kabarurrukan su Shaddadu tana zubar da hawaye har ta luluka a cikin gajimare.
Cikin sa'o'i kadan ta isa Birnin kufa, inda ta zauna taci gaba da rayuwarta a cikin mulki, amma bata gushe ba tana yin kuka a kullum saboda tunani da begen danta Shaddadu har ma tayi aure ta haifi yayaye ta tsufa ainun.
Kai har a ranar da ajalinta yazo da hawaye na begen Shaddadu ta mutu.
Har yau har gobe idan mutum yaje birnin Sarauniya Yaldisa zai ga inda aka gina kabarurruka guda hudu, na Shaddadu, Ziya'ul Hak, Sarki Laffaru da matarsa Ramlatul Siyam.
Lokacin da Sarki Dujalu yazo nan a cikin labarinsa sai tari ya turnuke shi gami da aman jini, take Hursiyya ta kankameshi tana mai fashewa da kuka ta ce ya kai dan uwana kayi sani cewa kaima kayi rashin dabara irin ta Sharlis tunda gashi kaima zaka mutu burinka bai cika ba, duk wahalar da kasha a baya tsawon shekara da shekaru ta zama ta banza, inda ka karbi wannan addini na gaskiya da tabbas sai zuciyarka ta yi sanyi ka rungumi kaddara, kayi sani cewa wannan hawaye nawa dake zuba ba wai na bakin cikin rabuwa da kai bane kadai? A'a ina bakin ciki ne saboda tausayinka gami da rashin samun babban rabo, kaga kenan kayi biyu babu duniya bata samu ba kuma daya can gidan ma bai samu ba.
Koda jin wannan batu sai Sarki Dujalu ya dubi Gimbiya Hursiyya yayi mata murmushin karfin hali yace hakika yanzu naga gaskiya kuru-kuru da idona amman a lokacin da bazan iya karbarta ba, ina tayaki murna da kika dace har kika karbi wannan gaskiyar, kuma nima ina murna zan mutu akan abinda na gada iyaye da kakanni, albarkacin iyayenmu bazan mutu yanzu ba har sai na kammala maki hikayar sadauki Hulkas na birnin Romaniya domin itama hikaya ce mai dauke da dunbin darasi wadda zata amfaneki a rayuwarki ana gaba.
Koda ya zo nan a zancensa sai ya sake yin tari gami da aman jini har numfashinsa ya dauke dif.
Hursiyya ta fada saman girjinsa tana mai fashewa da matsanancin kuka.
Ba zato kuma ba tsammani sai kawai ta ji sarki Dujalu ya kawo gauron numfashi yana mai bude idanunsa da kyar, nan take ya budi baki da nufin ya cigaba da basu labari, kawai sai sukaga wata guguwa mai tsananin karfin gaske ta zo ta sure wadannan kayan yaki na mazan jiya tayi sama da su, a take kum guguwar ta rikide ta zama aljani Raugatul Agwanu yana mai kyalkkyala mahaukaciyar dariyar mugunta gami da farin ciki, yana mai cewa "Shikenan na tsinci dami a kala, gabadayanku kun sha wahalar banza ni kuma na zo naci gajiyar wahalar taku, na samu tsuntsu daga sama gasasse. Nan take aljani Raugatul Agwanu ya luluka izuwa can kololuwar sama yana mai cigaba da cewa shikenan duniya ta zama tawa dukkan mutane da aljanu sun dawo karkashina, kafin kiftawar ido ya bace bat a sararin samaniyar, har ma dariyar tasa daga baya ta gushe aka daina jinta.
A dai-dai wannan lokacin ne boka Sadusa, Halyal da Gimbiya shalbirat ma suka fito daga inda suke boye tare da rugowa inda su Sarki Dujalu suke, nan take suka gabatar da kansu kuma suka bayar da labarin abinda duk ya faru a tsakaninsu da aljani Raugatul Agwanu. Boka Sadusa ne yayi wannan bayani kuma bai boye wa Sarki Dujalu komai ba dangane da dukkanin shirinsu shida fadawansa na yi masa juyin mulki wanda har takai cewa an turo shi wannan tsibiri na Bahar sufiya domin ganin halin da ake ciki akan yakin da sarki Dujalu ke yi.
Lokacin da boka Sadusa ya zo nan a cikin jawabinsa sai Sarki Dujalu ya kyalkkyale da dariyar mugunta cikin karfin hali, sannan ya dubi jarumi Hasnalu yace da shi ya kai wannan saurayi ma'abocin kyau da jarumtaka kuma jagoran kawo haske mai kore duhu a wannan nahiya tamu ina mai rokonka da ka roki Ubangijinka daya lalata sihirin wadancan kayan yaki na mazan jiya wanda aljani Raugatul Agwanu ya dauka, ya zamana cewa babu wani mahaluki da zai kara amfanarsu, bawai dan na kasa mallakarsu bane nake so a lalatasu ba, sai domin na gane cewa duk abinda muka yi imani da su dangane da makaman tsafine kawai, kuma tsafi karya ne addinin musulunci shine kadai tafarki na gaskiya.
Dalili na biyu da nake son a lalata sihirin wadannan makamai shine na gane cewa zalunci bashi da wani amfani a doron kasa, tunda gashi na gani da idanuna, karshen ko wanne azzalumi baya kyau, sannan yakanyi mutuwar wulakanci, kaskanci gami da gagarumar asara. Daga can sai sarki Dujalu ya kamo hannun yar uwarsa gimbiya Hursiyya ya damke a lokacin da hawaye ya zubo masa ya ce ya ke yar uwata kiyi sani cewa ko a cikin tarihin rayuwata akwai babban darasi wanda ke nuni da cewa hadama da dogon buri basa kai mutum ko ina face asara gami da nadama, ki duba ki gani ina da mulki irin wanda babu wani sarki mai irinsa a wannan nahiya, haka kuma ina da dukiya wacce babu wani attajiri ko mai mulkin daya tara kamarta, hatta Sarki Maharaz kuwa. Amman duk wannan ni'ima dana samu ban godeWa Allah ba, gashi garin kwadayi da dogon buri na rasa komai nawa, a karshe kuma gashi rayuwar tawa ma zan rasata gaba daya, wannan shine babban darasi a cikin labarina.
Sarki Dujalu ya dubi boka Sadusa ya ce kaima sai wannan jawabi da nayi ya zama darasi a gareka, domin na tabbatar da cewa a cikin zuciyarka har yanzu kana da burin son mallakar wadancan kayan yakin na mazan jiya wadanda aljani Raugatul Agwanu ya sace ya gudu da su, abubuwan da suka faru yanzu ya isheka ishara tunda da idanunka kaga yadda tsafi ya kasa dauko kayan yaki, sai Ubangijin musulunci ne ya bada iko aka dauko su.
Lokacin da sarki Dujalu ya zo nan a zancensa sai Sarki Maharaz ya tsugunna daf da shi tare da kama hannayensa ya rike ya ce ya kai abokin gaba kayi sani cewa a halin yanzu na cire dukkan wata gaba dake cikin zuciyata dangane da kai, kuma na yafe maka dukkan wani bakin ciki da ka cusa mani, kaunarka ta shiga cikin zuciyata tamkar bata taba kinka ba, ina yi maka kwadayin samun wannan babban rabo wanda na samu yanzu na karbar addinin gaskiya, kaga shikenan ka samu dadi da daula anan gidan duniya, acan daya duniyar ma sai ka samu.
Koda sarki Maharaz ya zo nan a zancensa sai sarki Dujalu ya dubeshi cikin murmushin karfin hali, sannan ya daga hannunsa ya dora a saman kafadarsa da kyar ya ce hakika nima a halin yanzu naji ina kaunarka tamkar dan uwana na jini, kuma na yafe maka dukkan wani laifi da kayi mani, amman k sani cewa bakin alkalami ya riga ya bushe, kuma zuciyata ta bushe ga barin sauya manufarta. Hakika bazan iya karbar addinin Musulunci ba, saboda zan kasance a cikin tsananin kunya a ranar da aka tashemu ni da iyayena da kuma kakanninmu, suna kallona ina kallonsu za a yi masu azaba ni kuma a sannan a sakani a cikin Rahama.
Koda jarumi Hasnalu ya ji wannan batu daga bakin sarki Dujalu sai ya cika da tsananin mamaki ya ce ya kai wannan sarki yanzu ashe daman kasan cewa akwai wata rayuwa bayan wannan? Kuma ka sani cewa wadanda suka bijirewa Allah za a yi masu azaba, yayin da wadanda suka bishi za a yi masu sakayya da aljanna mafificiya?
Sarki Dujalu ya kada kai yayin da hawaye ya sake zubo masa ya ce tabbas nasan duk wannan al'amari, tun ban fi shekara bakwai a duniya, kuma mahaifina ne ya sanar da ni, shima mahaifinsa ne ya sanar da shi, amman da yake duk an cusa mana kiyayyar addinin Musulunci tun muna yara, sannan baiyi tasiri a cikin zukatanmu ba. Ya kai wannan jarumi kayi sani cewa na taba ji daga bakin mahaifina cewa kimanin shekaru ashirin baya da suka gabata akwai wani ma'abocin addinin Musulunci da yazo nahiyarmu yayi gwagwarmaya da iyayenmu sai dai mahaifina ya samu nasarar kasheshi, yanzu haka suturarsa gami da kayan yakinsa suna nan acikin dakin tarihi dake cikin gidan sarauta ta, kuma akwai bayanin inda aka binne gawarsa a cikin wani littafi dake cikin wani akwati da aka ajiye tufafinsa. Ga yadda aka yi bayanin wannan mutum kuwa da siffofin jikinka, a yanzu da kake tsaye a gabana kai da shi tamkar an tsaga kara ne, babu mamaki ma kana da nasaba da shi.
Koda sarki Dujalu ya zo nan a zancensa sai hawayen farin ciki ya zubowa jarumi Hasnalu ya ce hakika ka gajarce mani wahala, ka sanar da ni abinda nazo nema wannan nahiya taku, kuma gashi na jefi tsuntsu biyu da hoge daya, tunda gashi na samu abinda na zo nema kuma na samu nasarar korar duhun da kuke ciki na kawo maku haske.
Da jin haka sai Sarki Dujalu yayi murmushi cikin karfin hali a lokacin da tari ya sake turnukeshi ya zubar da yawun jini, Hursiyya ta sake kankameshi tana mai sake fashewa da kuka, da kyar sarki Dujalu ya sake bude baki ya dubi jarumi Hasnalu ya ce ya kai gwarzon jarumi ina mai rokonka daka gaggauta rokon ubangijinka akan ya lalata tasirin wadannan makamai na mazan jiya tungabanin aljani Raugatul Agwanu ya fara amfani da su.
Abu na karshe da nake son na rokeka shine tunda yar uwata Hursiyya ta karbi addininka kuma kuna son juna kai da ita, to ka aureta kuma ka dauketa ka tafi da ita can nahiyarku domin ina son ta manta da ni, kuma ta manta da kasarta ta haihuwa har abada.
Koda jin haka sai Hursiyya ta sake fashewa da matsanancin kuka tana mai cewa ya kai dan uwana kayi sani har abada fan uwa ba zai tana mancewa da danuwansa ba, har na mutu da begenka zan kasance gami da zubar da hawaye dan takaicin rashin karbar addinin gaskiya.
Koda jin wannan batu sai kowa dake wajen ya kama zubar da kwalla, a sannan ne boka Sadusa ya durkusa bisa gwiyawunsa gaban jarumi Hasnalu idanunsa cike da kwalla ya ce tabbas addininka shime addinin gaskiya, maza ka shigar da ni wannan addini mai girma da daraja.
Nan take kuwa jarumi Hasnalu ya budi baki dan ya biya masa kalmar shahada sai yaro Halyal da gimbiya shalbirat ma suka zo suka durkusa a gaban jarumi Hasnalu cikin hadin baki suka ce muma munyi imani da addinin Musulunci.
Cikin matukar farin ciki arumi Hasnalu ya biya masu kalmar shahada, suka maimaita. Sarki Maharaz da jarumi Imnal da ke tsaye gefe daya da gimbiya Mulaifa gami da Hursiyya duk sai suma suka mu da matukar farin ciki.
Bayan su boka Sadusa sun karbi addinin Musulunci ne, sai jikin sarki Dujalu ya kara tsanani, take numfashinsa ya fara sarkewa kuma idanunsa suk kama rufewa da budewa, da kyar ya samu ya sake bude bakinsa ya dubi jarumi Hasnalu ya ce ya kai wannan sadaukin sadaukai kuma sirikina, kalmata ta karshe a garek ita ce ina mai rokonka da ka mayar da gimbiya shalbirat kasarsu domin ta sadu da mahaifiyarta, kuma ka mayar d su sarki Maharaz zuwa birninsu tunda dai yanzu babu sauran aljani anan wanda xai iya mayar da su can garuruwan nasu har ya karesu daga sharrin mugayen abubuwan dake kn hanya.
Koda jin wannan batu sai jarumi Hasnalu ya numfasa ya ce kada ka damu ya kai wannan sarki, da izinin ubangijina kowannenmu anan zai isa gida lafiya, kuma daga nan babu inda zamu fara zuwa ba face dajin darul hishushul maut inda aljani Raugatul Agwanu yake domin naje na yakeshi na nuna masa cewa kayan yakin da ya makllaka na maxan jiya shirme ne tunda na dogara da ubangijin da yayi wadanda suka kirkiri kayan yakin mazan jiya. Da izinin Ubangijina zamu isa dajin darul hushushul maut acikin kankanin lokaci. Ya kai wannan sarki ina mai sake rokonka a karo na karshe daka janye wannan mugun ra'ayi akan addininka na gado ka karbi addinin gaskiya kodan saboda yar uwarka ta kasance a cikin farin ciki na kamutu cikin babban rabo.
Koda jin haka sai sarki Dujalu yayi dariyar karfin hali sannan ya ce kayi hakuri samari a rayuwata ban taba yin magana biyu ba, kuma ban taba sa abu a gabana ba ya gagareni ko kuma naja da baya sai a wannan karon da na kasa dauko makaman mazan jiya a karkashin wannan teku bayan nayi iyakar abinda zanyi amman na kasa, lallai ba zan juya wa iyayena da kakannin baya ba, burina shine na sadu da su a cikin irin halin da zasu kasance.
Gama fadar hakan keda wuya sai sarki Dujalu ya kama kakarin mutuwa, nan fa Hursiyya ta dada kankameshi a kirjinta tana mai kara fashewa da kuka.
Su kuwa su jarumi Hasnalu sai tausayin wannan yan uwa ya turnukesu suka kama zubar da hawaye, haka dai sarki Dujalu ya cigaba da kakarin mutuwa gami da shure-shure harda iface-iface har izuwa wani lokaci kafin daga karshhe aka zare masa ruhin numfashi, nan fa jikinsa ya sandare idanunsa suka kafe. Kaico! Kaji muguwar mutuwa irin ta marasa rabo, hakika wanda Allah Ya batar bazai taba zama mai shiriya ba, gashi dai babu yadda su Hursiyya basu yi da sarki Dujalu ba akan yya karbi addinin gaskiya domin ya rabauta, amman da yake tuni Allah Ya hukunta bashi da rabo sai ya kasa karbar gaskiyar.
Bayan sarki Dujalu ya mutu akan cinyar Hursiyya sai ta dada kankameshi a kirjinta tana mai dada fashewa da matsanancin kuka fiye da koyaushe, da kyar da shidin goshi gimbiya Mulaifa ta bambareta daga jikin gawar sannan ka tona rami aka gefen tekun bahar sufiya aka binne sarki Dujalu a ciki. Jarumi Hasnalu da jarumi Imnal suka je suka kinkimo wani katon dutse suka ajiyeshi a gaban kabarin sarki Dujalu, nan take suka zare takubbansu suka rinka kartar dutsen har sai da suka rubuta sunan sarki Dujalu a jikin dutsen sannan kuma suka dinga dora duwatsun wuta a bisa kabarin har saida suka rufeshi ruf domin kada kabarin ya baje, komai daran dadewa ya zama abin tarihi. Aikuwa har yau har gobe idan mutum ya je bakin kogin bahar sufiya zai ga wannan kabari na namijin duniya sadaukin sadaukai sarki Dujalu gami dana marigayi Sarkin yaki Hibru mahaifin jarumi Imnal, kuma tsakanin kaburburan bai wuce taku biyu ba.
Bayan su jarumi Hasnalu sun gama gina kabarin sarki Dujalu sai Imnal da sarki Maharaz suka je suka durkusa a gaban kabarin Hibru suka kura wa kabarin idanu sun masu zubar da hawaye, daga can kuma sai Imnal ya fashe da kuka.
Jarumi Hasnalu ya dafa kafadar Imnal cikin alamar matukar tausayawa ya ce ya kai abokina ina dalilin wannan matsanancin kuka naka? Kayi sani cewa dukkan mai rai mamacine, su da suka tafi basu yi gaggawa ba, haka mu da muke nan bamu yi jinkiri ba.
Imnal ya juyo ya dubi jarumi Hasnalu idanunsa sharkaf da hawaye ya ce ya kai abokina ba wani bane yasa ni zubar da hawaye ba face tunowa da cewa mahaifina ya mutu bai karbi addinin Musulunci ba alhalin kuma a bakinsa na fara jin labarin wannan addini, kuma a yadda yake yi mani bayani har a zuciyarsa yayi imani da addinin kuma yana takaicin akan rashin samun damar karbar addinin, domin shi bai samu damar hakan ba.
Lokacin da jarumi Hasnalu yaji wannan batu, sai yayi murmushi mai taushi ga jarumi Imnal ya ce ya kai abokina kayi sani cewa Ubangijina mai hikima ne akan komai, kuma mai Rahama ne ga bayinsa a duk sa'ad da ya so, tunda har mahaifinka ya kadaita Allah a cikin zuciyarsa duk da cewa bai sanshi ba kuma bai samu damar da zai sanshi ba, to Allah subhanahu wata'ala zai iya masa Rahama ya sa shi a gidan aljanna.
Koda jin wannan batu sai mamaki da farin ciki ya lullube su Imnal, sarki Maharaz yayi ajiyar numfashi ya ce hakika Ubangijin musulunci shine

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login