Showing 69001 words to 71576 words out of 71576 words

Chapter 24 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt

cika alkawarina na kai kowannenku zuwa kasarsa.
Cikin matukar farin ciki kowa ya bude jakar guzurinsa ya dauko abinci ya kamaci, shiko jarumi Hasnalu sai ya dauko tasbaha ya kama lazimi.
Jarumi imnal, sarkk Maharaz da gimbiya Mulaifa suka ware waje guda suna cin abincinsu tare, Sadusa tare da dansa Halyal da gimbiya Shalbirat suma suka taru akan abinci guda. Ita kuwa Hursiyya sai ta kasa cin nata abincin, sakamakon cewa jarumi Hasnalu yaki yaci abincin kuma ya kama lazimi, kawai sai ta dauki nata abincin taje ta zauna gefen jarumi Hasnalu ba tare da ya lura da ita ba.
Koda Hursiyya ta danyi motsi sai Hasnalu ya juyo ya dubeta, da dai yaga ta ajiye abincin taki ci sai ya cika da mamaki ya dubeta ya ce me yasa baki ci naki abincin ba?
Da jin wannan tambaya sai gimbiya Hursiyya tayi murmushi tace ta yaya masoyi zai ji yunwa alhalin masoyinsa baya ji, ina mai tabbatar maka da cewa jina da ganina duk sun zama naka, koda kaya ce idan ta sokeka a halin yanzu nima sai naji zafin sukar a jikina, idan kaga naci wani abu yanzu to sai dai idan yare da kai ne.
Sa'ad da jarumi Hasnalu yaji wannan bato sai nan take yaji kaunar Hursiyya ta baibaye ilahirin zuciyarsa kai da ransa ma gabadaya har bai san sa'ad da ya maida mata da martanin murmushi ba, kawai sai ya juyo ya fusknaceta sosai tare da tsoma hannunsa cikin abincin dake gabanta ya fara ci ya ce sa hannu muci tare, domin dai dana barki da yunwa gwara na kawar da kunya na saka hannu muci tare tunda a gaban mutane ne, inda dai mun kadaita ne ba zan yadda na kusanceki haka ba.
Cikin tsananin murna gami da farin ciki Hursiyya ta sanya hannunta a cikin abincin ssuka fara ci tare suna masu yi wa junansu murmushi mai nuna tsantsar so da kauna.
Bayan kowa ya gama kimtsawa ne sai jarumi Hasnalu ya dubi gabadaya abokan tafiyyar ya ce yanzu ina so kuyi mani affuwa mu fara zuwa birnin su gimbiya shalbirat, domin ita ce wacce aka raba da mahaifarta da iyayenta tun tana da shekara bakwai, kuma ita ce take da burin sake saduwa da mahaifiyarta idan har tana raye.
Koda jin haka sai kowa yayi kabbara aka kuma aminci da wannan magana ta jarumi Hasnalu, nan take kowa ya mike tsaye aka hau kimtsawa, bayan kowa ya gama ne jarumi Hasnalu ya shige gaba tare da falfalawa da gudu yana mai karanta wasu Addu'o'i na musamman a cikin zuciyarsa.
Hakika Allah shine mai yin yadda ya so, kuma shine mai kunfa yakun, da yace kasance sai kawai abu ya kasance take. A cikin rabin sa'a su jarumi Hasnalu suka shafe tafiyar watanni tara, sai gasu a kofar gidan sarautar gimbiya shalbirat, duk da cewa an sauya tsarin fasalin gidan kama daga katanga, da sauransu, kuma an kawata gidan ainun ba kamar yadda yake a da ba tsawon shekaru shekaru goma sha tara baya, sai da gimbiya Shalbirat ta shaida gidan sarautar, ta tabbatar da cewa nan gidansu ne.
Koda masu tsaron kofar gidan sarautar suka ga su jarumi Hasnalu tsulum a gabansu kamar aljanu, kuma basu ga ta inda suka taho ba, sannan basuga durarsu daga sama ba, sai suka kamu da tsananin tsoro jikinsu ya kama tsuma, kafin su jarumi Hasnalu suyi magana an bude masu kofa sun kunna kai ciki.
Shalbirat ce ta yi masu jagora wato ta wuce gaba su kuma suna biye da ita a baya haka suka nufi fada kai tsaye. Duk inda suk wuce sai dai kaga dakaru,bayi, barori da kuyangin gidan sarautar suna ratsawa gami da basu hanya, a haka har suka isa cikin fadar inda suka iske Sarauniya Juzairat bisa karagar mulki, koda Shalbirat ta kura mata idanu sai ta shaidata, domin ita ce ta ci amanar mahaifinta ta kawar dashi daga kan mulki, ta sa masa cutar ajali, kuma itace tasa aljani Raugatul Agwanu ya saceta ya kaita can dajin darul hushushul maut.
A wannan lokaci fadar ta cika makil da fadawa da mutanen gari, amman koda aka hango su jarumi Hasnalu sun durfafi karagar mulki, sai fadawa da dakaru suka kama mikewa tsaye suna masu ja da baya cikin matukar tsoro da razana, ya zamana cewa wannan sarauniya dake kan kujerar mulki idanunta sun zazzaro, kuma ita jikinta na tsuma kamar ace kyet ta fida da gudu.
Gimbiya shalbirat ta cigaba da tunkarar sarauniya, su jarumi Hasnalu na take mata baya, a haka har sai da suka iso daf da ita, yadda ita da Shalbirat suna iya jin numfashin junansu. Shalbirat ta dubeta ta ce nice gimbiya shalbirat yar danuwanki, sarkin da kika kashe kika hau kargar mulkinsa, sannan kika sa aljani Raugatul Agwanu ya sace ni ya tafi dank can dajin darul hushushul maut, ka rabani da uwata da ubana tsawon shekara goma sha tara.
Koda jin wannan batu sai sarauniya Juzairat ta dada cika da tsananin mamaki ta kura wa shalbirat idanu, alokacin da ta dada kamuwa da tsoro jikinta da baikinta suka hau rawa ta kasa cewa komai.
Shalbirat ta sake dubanta a karo na biyu ta ce ni yanzu nazo maki da addinin gaskiya wato addinin Musulunci, kuma na baki zafi ki karbi addinin Allah ki tsira da rayuwarki, sannan ki sauka daga kan matsayin da kike a yanzu ki dawo talaka kamar kowa ko kuma yanzu ki rasa rayuwarki?
Koda jin Wannan batu sai sarauniya Juzairat ta bushe da dariyar keta ta ce tsakanina da addinin musulunci sai gaba..
Kafin ta gama rufe bakinta gimbiya Shalbirat ta juyo cikin tsananin zafin nama ta zare takobin jarumi Hasnalu ta kuma juyawa ta fille kan Sarauniya Juzairat, nan take jini yayi tsiri sama yayin da kan nata ya gangaro daga kan karagar mulki.
Nan take Shalbirat ta kwala kabbara kuma ta karanta kalmar shahada ta na mai umartar gabadaya mutanen dake fadar da su biya kalmar.
Ba tare da wata gardama ba gabadaya mutanen fadar suka maimaita kalmar shahada, cikin tsananin farin ciki gimbiya Shalbirat ta hau kan karagar mulki ta zauna alokacin da su jarumi Hasnalu suka cika da tsananin mamakin wannan gagarumar jarumtaka da ta yi.
Zaman Shalbirat akan karagar mulki sai idanunta suka ciko da kwalla, har hawaye ya zubo mata a lokacin data gama kare wa karagar mulki da kuma fadar kallo. A sannan ne ta dubi wani dattijo a fadar ta ce ya kai waziri Lamsanu mene ne labarin mahaifiyata?
Cikin tsananin mamaki waziri Lamsanu ya dubi gimbiya Shalbirat ya ce rankiya dade qshe ba zaki manta da kamannina ba, kiyi sani cewa mahaifiyarki ta samu tabin hankali, kuma tana can a tsare a kurkuku.
Koda jin haka sai bakin ciki ya turnuke Shalbirat har hawaye ya sake zubo mata ta mike ta ce muje ka kaini inda take.
Nan take Waziri Lamsanu ya wuce gaba Shalbirat dasu jarumi Hasnalu na take mashi baya, haka suka yita tafiya a gidan sarautar suna masu shiga lungu da sako na gidan sarautar har sai da suka iso inda kurkukun yake, aka kai su kofar dakin da mahaifiyar Shalbirat take. Da zuwa sai suka isketa a kwance tana bacci, gashin kanta yayi buzu-buzu ba kyan gani, ga kuma furfura duk ta rufeshi Hakazalika rigar jikinta ta yi dauda sosai har tana wari.
Su duka dai da suka zibar da hawaye saboda tausayi, Shalbirat ta kira sunan mahaifiyar tata har sau uku sannan ta taso zaune tana mai kura wa Shalbirat idanu, kawai sai ta bushe da dariya ta kama surutu irn na masu tabin hankali tana mai kawo wa Shalbirat duka.
Koda ganin haka sai jarumi Hasnalu ya yi sauri ya matsar da Shalbirat baya sannan ya shiga karanta wata addu'a yana tofawa mahaifiyar Shalbirat, aiko nan take wani nannauyan bacci ya dauketa, jim kadan ta farko tana mai tashi tsaye da kafafunta tana mai binsu da idanu daya bayan daya, koda idanunta suka yi arba da yarta Shalbirat sai ta kura mata idanu har hawaye ya zubo mata, ta nuna Shalbirat da hannu kuma ta kira sunanta tana mai cewa Yata ashe kina raye a wannan duniya, ashe zamu sake saduwa?
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama su Jarumi Hasnalu suka yi kabbara a tare, nan take Shalbirat tasa aka bude kofar dakin da mahaifiyarta ke ciki ta ruga da gudu suka rungume juna ita da mahaifiyarta tata suka fashe da sabon kukan farin ciki.
Suma su Imnal basu san sa'ad da kukan ya kwace masu ba, saboda tausayi gami da murna, a wannan rana aka kaddamar da addinin musulunci a Birnin, gimbiya Shalbirat kuma ta hau kan karagar mulki.
Lokacin dasu jarumi Hasnalu suka je yi mata bankwana sai ta fashe da kuka, ta dubi Sadusa da dansa Halyal ta ce kune farkon sanadin tsirata daga hannun azzalumi aljani Raugatul Agwanu, bani da bakin yi maku godiya face addu'ar Allah ya saka maku da mafificin alheri.
Ba tare da bata lokaci ba su Hasnalu suka yi mata sallama suka tafi, ana isa birnin sarki Dujalu nan ma aka kaddamar da addinin musulunci amman gimbiya Hursiyya bata karbi sarauta b sai aka ba Sadusa. Waziri da jama'arsa kuwa suka bashi hadin kai.
A sannan ne aka shiga dakin tarihi na gidan sarautar inda aka gano wannan littafin mai dauke da tarihin kamannin mahaifin Hasnalu da kuma inda kabarinsa yake, nan take aka dunguma aka tafi wajen, koda aka tona saman kabarin sai aka yi arba da fuskar mahaifin Hasnalu lafiyarta sumul ko kwarzanewa bata yi ba, kamar ma asannan ne aka binne shi, kuma kamanninsu iri daya ne sak da jarumi Hasnalu tamkar an tsaga kara, bambancinsu kawai na shekaru ne.
Koda jama'a sukaga wannan gawa cikin koshin lafiya alhalin ta kusa shekaru talatin a binne sai suka cika da al'ajabi aka kama hailala da kabbara, aka kuma sallama Wa Allah bisa ikonSa.
Hasnalu ya kura wa mahaifinsa idanu yana mai zubda hawaye ya ce ya kai abbana ban taba ganinka ba sai labarinka da mahaifiyata ta bani, rayuwarka gaba daya ta gushe a cikin yada Addinin Allah, yau gashi Allah ya cika mani burina naga fuskarka da idanuna kafin mutuwata. Burina ya cika, fatana nima Allah ya dau raina a irin wannan tafarki naka, nan take ya mayar da kasar kabarin ya rufe sannan yayi masa addu'a.
Kamar yadda aka kaddamar da addinin musulunci a birnin Sarauniya Shalbirat da birnin sarki Dujalu haka akaje birnin sarki Maharaz aka kaddamar da shi, kuma duk d cewa jarumi Imnal da gimbiya Mulaifa sun kasance yara a sannan aka daura masu aure, akayi gagarumin shagalin biki a gaban jarumi Hasnalu da gimbiya Hursiyya.
Lokacin da Hasnalu da gimbiya Hursiyya suka zo zasu yi wa su Imnal da sarki Maharaz bankwana domin su tafi izuwa can nahiyar su jarumi Hasnalu inda acan ne Hursiyya zata karasa sauran rayuwarta ta duniya sai su duka suka kama kuka saboda bakin cikin rabuwa da juna, sarki Maharaz ya rungume jarumi Hasnalu yana mai cewa ya kai jarumin jarumai, kaine ka tsamoni daga cikin duhun jahilci ka haskake mana wannan nahiya gaba daya da hasken musulunci, hasken ilimi kuma haske na gaskiya, tabbas har abada ba zamu taba mantawa da kai ba, kuma har mu mutu zamu rinka tunawa da kai muna alfahari da kai, idan ka amince ina so tun gabanin ku barmu a daura aurenka da gimbiya Hursiyya a gaban idanunmu domin mu zama sheda kuma ku tsira daga dukkanin wani tsautsayi na sharrin shedan dana zuciya, tunda zaku kadaita a cikin wannan doguwar tafiya da zaku yi izuwa nahiyarku.
Koda sarki Maharaz yazo nan a zancensa sai jarumi Hasnalu yaji matukar farin ciki, kuma ya kama yin godiya ga sarki Maharaz bisa hango masu abinda zai fiye masu alheri.
Nan take aka daura auren jarumi Hasnalu da gimbiya Hursiyya bisa ka'idar addinin Musulunci, bayan nan sai suka yi bankwana su sarki Maharaz suna zubar da hawaye suma suna zubarwa, har jarumi Hasnalu da Hursiyya sun juya zasu tafi sai kawai sarki Maharaz ya kira sunan Hursiyya ta juyo ta dubeshi ya ce da ita ya ke yata in da tambaya a gareki?
Tambaya ta farko ita ce wane irin darasi kika samu a cikin hikayar jarumi shaddadu, kuma wane ilimi kika gani a cikin tamu rayuwar ni da fan uwanki sarki Dujalu?
Koda jin wadannan tambayoyi sai hawaye ya zubo daga cikin idanun Hursiyya domin babu wanda ya taba mata irin wannan tambaya face sarki Dujalu.
Hursiyya ta yi ajiyar numfashi sannan ta ce ya kai abbana ka sani cewa a cikin hikayar jarumi shaddadu na fahimci cewar zalunci da son zuciya basa haifar da komai face nadama da kaskanci gami da dunbin wahala kamar yadda karshen rayuwar sarki Laffaru ta kasance, tunda a farkon rayuwarsa karfin mulki, dana jarumtarsa hadi da na sihiri sun sa masa isgilanci har yana cin zalin al'umma, ganin cewa babu wani da ya isa ya taka masa birki, amma sai gashi ya mace ta rabashi da mulkinsa, karfinsa da duk daukakarsa, kuma ta jefashi a cikin tsananin wuya da rashin kwanciyar hankali har izuwa karshen rayuwarsa.
Darasi na biyu a cikin wannan labari shine abu ne mara kyau mutum ya tsananta gaba a tsakaninsa da wani, kamar yadda Sharlis da Laffaru suka tsananta gaba a tsakaninsu har ga yayansu, wanda sai ga shi a karshe yayan nasu sun kamu da son juna kuma suka zabi su mutu tare dan kawo karshen gabar iyayen nasu, abinda ya cusa wa iyayen bakin ciki kenan suka kashe kansu, suka rasa komai ba tare da burin dayansu ya cika ba.
Dangane da ilimin dana samu game da rayuwar dan uwana Dujalu da taka rayuwar shine na fahimci cewar wanda duk bai gode Wa Allah ba bisa baiwar da yayi masa ta arziki da daukaka, har yake harin ya samu wadda tafi wannan to karshensa nadama gami da hasara, tunda gashi kai da shi duk kunyi mummunar asara ta dukiya da rayukan jama'a kuma burinku bai cika ba, haka kuma na samu babban ilimi na kadaita Allah, ikonsa da isarSa akan komai da kowa, tunda gashi matsafa da aljanu sun kasa dauko kayan yakin mazan jiya a cikin tekun bahar Suffiya, amman sai gashi wanda yayi imani da Allah ya kadaitashi ya dauko su salim alin, kamar yadda ake cire silin gashi daga cikin tandun mai, hakika ubangijin musulunci shine buwayi gagara misali, wanda duk yayi imani da shi ya kubuta kuma ya tsira daga dukkanin sharri, wanda kuma ya bujire masa ya hadu da masifa da halaka.
Koda Hursiyya ta zo nan a jawabinta sai sarki Maharaz ya cika da tsananin murna gami da farin ciki, yace AlhamduLillahi tabbas kin samu duk irin darasin daya kamata ki samu a cikin wadannan labarai, albishir din da zanyi maki shine kije ki nemi wani littafi mai suna Tsatsuba tabbas zakiji labarin Sadauki Hulkas na birnin Romaniya a cikinsa tunda dai dan uwanki sarki dujalu bai samu damar baki labarin ba ajali ya riskeshi.
Koda jin haka sai farin ciki ya lullube gimbiya Hursiyya ta ce aiko in sha Allah duk inda Littafin Tsatsuba yake zan nemeshi domin na karanta tarihin Sadauki Hulkas mai hular lamsara n birnin Romaniya.
Nan take Jarumi Hasnalu da gimbiya Hursiyya suka sake yi wa sarki Maharaz sallama suka tafi suna masu waigensa har suka fice daga fadar tasa, gabadaya suka nausa izuwa cikin daji suna masu falfalawa da azababben gudu, cikin yarda da huwacewa ta Allah suka nufi nahiyar su jarumi Hasnalu inda zasu cigaba da rayuwa bisa tafarkin addinin Muslunci.
AlhamduLillahi nanne karshen wannan littafi na mazan jiya da fatan kunji dadin wannan littafi wanda Abdulaziz Sani madakin gini ya rubuta ni kuma Abubakar Saleh Alquyraemey na jagoranci typing insa nake cewa mu hadu da ku a wani littafin.




Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login