Showing 54001 words to 57000 words out of 71576 words

Chapter 19 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt

suka wuce har i zuwa cikin Turakarta suka Zauna. Zamansu ke da wuya Kuyangi suka kawo abinci da abin sha na alfarma suka kama ci da sha suna hira cikin nishadi da annashuwa tamkar sun kasance 'yan uwa ko kuma aminan juna

Bayan sun ci sun sha sai aka kawo musu giya. Koda Zubaina ta zuba giyar a cikin kofuna guda biyu ta mika wa Ziya'ul Hak domin ta sha, sai ta ki karba. Ta dubeta ta ce, ya ke wannan Sarauniya ki yi sani cewa ni a daji aka haife ni kuma a cikinsa na girma don haka ban saba da shan giya ba, amma kuma babu abin da iyayena ba su koya mini ba dangane da irin rayuwar da ake a cikin Birni.

Koda jin wannan batu sai Sarauniya Zubaina ta bushe da dariya sannan ta ce, na yarda da wannan labari naki amma na tausaya miki kuma na tausayawa iyayenki da suka yi rayuwar dole a daji sabo da tsoron sharrin mahaifiyar Shaddadu.

Lallai idan har kina son iyayenki su sami zaman lafiya da kwanciyar hankali dole ne ki yi iya kokarinki ki tabbatar da cewa kin samu nasarar kashe Jarumi Shaddadu.

Wai shin ma ke ba kya so ne ki ga mahaifnkı Sarki Laffaru ya koma birninsa na Kufa ya karbi karagarsa ta mulki?

Hakika a duniya babu mutumin da ya fi zama abin tausayi sama da wanda ya rasa dukiya ko mulki domin ya dandana dadi mara misaltuwa kuma dadin ya zo ya salwanta. A cikin wanne irin yanayi kike tsammanın zai tsıncı kansa?

Zıya'ul Hak ta dubi Sarauniya Zubaina ta ce, ina mai tabbatar miki da cewa ta kowanne hali sai na ga na tabbatar da na sami nasara akan Shaddadu da mahaifiyarsa. Yanzu ke ta yaya kike ganin cewa za mu iya kamo Shaddadu mu hallaka shi?

Koda jin wannan tambaya sai Sarauniya Zubaina ta yi murmushi sannan ta ce binciken da na yi a cikin hallarar tsafina na gano cewa, ba wani ba ne ya taimaki Jarumi Shaddadu cikin wannan gari nawa ya boye shi a sa'adda nake matukar nemansa face wata baiwata kum karuwa mai zaman kanta wacce ake kira Yaldisa. Akwai wani gidan sai da abinci nawa wanda Yaldisa ce ke kula da shi, a nan ne ta fara haduwa da Jarumi Shaddadu. Tun a wannan gida ne na shirya masa tuggun da za a kashe shi a dauko mini Mashinsa na Galilul Haras a kawo mini amma sai ya tsallake wannan tarko nawa bisa karfin dantsensa da kuma taimakon Yaldisa inda ta dauke shi ta kai shi can gidanta ta boye shi a cikin wani ďakı da ke karkashin kasa.

Ni da kaina tare da Dakaruna mun shiga har cikin gidan Yaldisa mun duba ko ina ba mu ga Jarumi Shaddadu. Duk ban gano wannan al'amari ba sai a yau da na tsananta bincike a cikin madubin tsafina. Tabbas ko shakka ba na yi a yanzu haka ma duk inda Jarumi Shaddadu yake yana tare da Yaldisa. Abin da ya daure mini kai shi ne, na yi iya bincikena na kasa gano a inda suke a yanzu.

To amma ai idan sun san wata ai ba su san wata ba. Tun da Jarumi Shaddadu ya yi mana wuyar gani da kamawa, ai ita Yaldisa ba za ta yi mana wuya ba. kamata ya yi mu kamo Yaldisa mu zo mu tsare ta anan fada kuma mu sa a yi cigiyar cewa idan Jarumi Shaddadu bai kawo kansa fada a cikin sa'a goma sha hudu ba za a kashe ta ta hanyar ratayewa.

Na tabbalar da cewa ba zai iya zuba idanu yana gani a kashe ta ba saboda halaccin da ta yi masa a zuwansa wannan gari nawa.

Lallai zai iya kokarinsa ya ga ya ceci rayuwarta duk da cewa ba sonta yake ba, asali ma shi bai san mene ne so ba kuma bai taba son wata 'ya mace ba ko ya yi sha'awarta

Kin ga, da zarar Jarumi Shaddadu ya zo fada in yana tare da Mashin Galilul Haras za mu sa shi ya miko shi gare mu ko mu kashe Yaldisa.

Idan kuma ba ya tare da Mashin sai mu hada karfinmu ni da ke mu yake shi, tabbas in muka hada jarumtakarmu ni da ke sai mun rinjayi tasa mun hallaka shi.

Lokacin da Ziya'ul Hak ta ji wannan jawabi na Sarauniya Yaldisa sai ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce, to ke mene ne ribarki idan muka kashe Shaddadu ba ki sami Mashin Galilul Haras ba?

Koda jin wannan tambaya sai Sarauniya Zubaina ta kama in-ina ta rasa me za ta ce, amma sai ta wayance ta ce, ai kashe Shaddadu abu ne mai muhimmanci a gare ni ko don saboda kwararan dalilai guda biyu.

Dalili na farko shi ne, Shaddadu ya shigo birnina ya karya mini doka, kuma ya nakasta mini dakaruna da yawa ya karva mini kofar gari.

Dalili na biyu kuma shi ne, koda ba ya tare da Mashin Galilul Haras ai Mashin yana nan a cikin Birnin nan nawa tunda a bincikena na gani cewa Mashin ya fada cikin wannan korama wacce kuka fada cikinta ke da shi tun farkon fara fadanku sa'adda Mashin Galilul Haras ya hadu da Takobinki.

Ina mai tabbatar miki da cewa ke ma yanzu gabadayan sihirin tsafinki ya daina tasiri kamar yadda na Jarumi Shaddadu ya daina, amma fa ki sani cewa da zarar Mashin Galilul Haras ya dawo hannunsa shi ke nan tsafinsa ya dawo. Don haka, dole ne mu yi iya kokarinmu mu tabbatar da cewa Mashin bai dawo hannunsa ba, ya zamana cewa hannunmu ya riga nasa kaiwa kan Mashin.

Lokacin da Sarauniya Zubaina ta zo nana zancenta sai hankalin Ziya'ul Hak ya dugunzuma ainun ta fara tunanin cewa hada kan da take kokarin yi da Sarauniya Zubaina ba shi da wani amfani domin idan Zubaina ta mallaki Mashin Galilul Haras tamkar ta mallaki komai da kowa ne na duniya, don haka mahaifinta ma da kasarsu ta Birnin Kufa za ta dawo karkashin Sarauniya Zubaina.

Nan take wani tunani ya fadowa Ziya'ul Hak ta ce a cikin ranta, Wai shin mene ne ya hana mahaifiyar Shaddadu kokarin mulkar duniya a lokacin da ta mallaki Mashin Galilul Haras?Maimakon haka, sai ta sallama Mashin ga Shaddadu saboda kawai ya zo ya neme ni ya halaka ni kuma ya hallaka mahaifina?

Tana cikin wannan tunani ne Sarauniya Zubaina ta katse mata tunanin ta dafa kafadarta ta ce, yanzu zan sa a kai ki masauki domin ki kwanta ki huta sai gobe za mu fita ni da ke mu aiwatar da wannan gagarumin aiki don cika burinmu.

Koda gama fadin hakan sai Zubaina ta kirawo wata kuyangarta ta hada ta da Ziya'ul Hak aka tafi da ita izuwa masaukinta.

Kas! Babban kuskuren da Ziya'ul Hak ta yi shi ne, da ta manta da batun abokin tafiyarta Aljanı Maruful Dauwaz. Kamata ya yi ta koma can daji in da suka rabu ta sanar da shi abın da ya faru tsakaninta da Sarauniya Zubaina amma sai ta manta da hakan gaba daya.

****

Al'amarin Yaldisa kuwa ashe lokacin da Ziya'ul Hak ta shigo fadar Sarauniya Zubaina ita ma tana nan a cikin fadar amma ta batar da kamanninta babu wanda ya isa ya shaida
ta.

Bayan ta gama gani da sauraren duk abın da ya faru tsakanin Ziya'ul Hak da Sarauniya Zubaina sai ta sulale ta bar fadar, ta kunna kai izuwa cikin daji. Idan ta yi 'yar doguwar tafiya sai ta sami bayan dutse ko bayan bishiya ta labe har izuwa tsawon lokaci domin ta tabbatar da cewa babu wani dan leken asiri da ya biyo sawunta.

A haka dai ta samu ta isa har cikin wannan Kogo wanda ta bar Jarumi Shaddadu a kwance yana jinyar raunin da ke kansa.

Da shigarta cikin Kogon sai ta ga wayam! Babu Shaddadu babu alamarsa a cikin Kogon.

Al'amarin da yai matukar dugunzuma hankalinta ke nan ta firgita kuma ta dimauce.
A razane ta juya ta fito daga cikin Kogon dutsen ta wangame baki da nufin ta kwalla masa kira, kawai sai ta gan shi tsulum! Ya duro a gabanta daga kan wata bishiya.

Cikin tsananin farin ciki ta rungume shi, shi kuwa sai ya kankameta a jikinsa yana mamakin kansa domin wannan ne karo na farko da ya ji ya aminta ya hada jikinsa da na 'ya mace.

Alamarin da yai matukar dugunzuma hankalinsa ke nan ya janye jikinsa daga cikin nata ya sunkui da kansa kas yana tunani.

Ita kanta Yaldisa ta yi tsananin mamakın yadda ta ga har ya tsaya ta rungume shi alhalin ya tsani ya ga mace ta kusance shi

Cikin sanyın jıkı Yaldisa ta dubi Shaddadu ta ce, Mene ne dalilın da ya sa ka fito daga cikin Kogon dutsen nan da na boye ka alhalin ka san cewa rayuwarka a cikin mummunan hadari take tunda makiya suna farautarka kamar yadda mai yunwa yake farautar abinci?

Koda jin wannan tambaya sai Jarumi Shaddadu ya yi ajiyar zuciya cikin alamun karayar zuciya sannan ya ce, ai dole ne na fito daga cikin wannan Kogo saboda hankalina ya yi mummunan tashi bisa rashin ganin Mashina. Ki sani cewa babu inda ban duba ba a cikin koramar nan amma ban ga Mashin ba.

A lokacin da nake neman Mashin ne ma na ga wannan mugun Aljani abokin tafiyar Ziya'ul Hak na buya. Shi ma babu irin neman da bai yi ba a cikin wannan korama don ya dauko Mashina. Tabbas inda ya gan ni da tuni ya hallaka ni tunda ni yanzu ba ni da sauran karfin sihirin da zan iya yakarsa.

Ki yi sani cewa ni yanzu ina cikin tsaka mai wuya tunda ga shi makiyana suna farautar rayuwata ni kuma ina farautar Mashina.
Kin ga ke nan, hankalina ya rabu gida biyu, dole ne na yi iya kokarina na zabi abin da ya kamata na fara durfafa tsakanin makiyana ko kuma neman Mashina.

Sa'adda Yaldisa taji wannan batu sai ita ma hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abin da ke ma ta dadi.

Nan take ta dubi Shaddadu cikin yanayin matukar damuwa ta ce, ya kai ma'abocin kyawu da kwarjini, ka yi sani cewa muddin ina numfashi a doron kasa babu abin da zan bari ya taba lafiyarka.

A halin yanzu Sarauniyarmu da abokiyar gabarka Ziya'ul Hak sun hada karfi da karfe domin su yake ka su hallaka ka, kuma ga dukkan alamu gobe da safe za su fito farautarka. Ni kaina yanzu rayuwata a cikin hadari take domin na san cewa tuni Sarauniya ta yi bincike ta gano cewa ni ce na ke boye ka

Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Jarumi Shaddadu ya yi shiru yana tunani. Daga can sai ya dago kai ya dubi Yaldisa ya ce, wai shin mene ne dalilin da ya sa kika siyar da rayuwarki domin ceton tawa?

Koda jin wannan tambaya sai Yaldisa ta sunkui da kanta kas ta yi shiru ta kasa ba shi amsa, daga can kuma sai ta dago kai ta dube shi a lokacin da idanunta suka ciko da kwallah ta ce, ya kai Jarumi abin kwatance ka yi sani cewa ban taba jin na yi nadamar karuwancin da nake yi ba sai bayan haduwa ta da kai.

Na yi hulda da mazaje da yawa amma ban taba haduwa da namijin da na ji ba na son rabuwa da shi ba face kai duk da cewar wani abu bai taba shiga tsakanina da kai ba kuma na girme ka da shekaru a kalla kusan goma.Tun da na hadu da kai na ji na tsani wannan muguwar sana'a tawa ta karuwanci kuma na gane sewa bautar da nake yi wa Sarauniya Zubaina ba ta da wani amfani tunda ta kasance azzaluma kuma duk dukiyar da na ke tara mata ba ta taba ba ni ladan dirhami daya ba

Ni nake rike da kaina ta hanuyar siyar da jikina a wajen maza. Hatta wannan gida nawa da na kai ka ka kwana haya nake yi a cikinsa. lyayena sun mutu tun ban fi shekara bakwai ba a duniya kuma sun kasance bayın Mahaifin Sarauniya Zubaina.

Tsananin wahalar aikin bauta ne ya zamo sanadın ajalinsu. Bayan sun mutu ne Sarauniya Zubaina ta ci gaba da rike ni a matsayin baiwarta, amma saboda sanın ina da kyau tun a sannan ta ajiye ni a wannan gidan abinci nata aka koya mini yadda ake dafa abinci da siyar da shi.

Ba zan taba mantawa ba sa'adda na cika shekara goma sha biyu, lokacın da dukkan surar jikina ta 'ya mace ta bayyana wasu Dakarun Sarauniya Zubaina su biyu suka yi mini fyade a wannan gidan abıncı.

Ko kadan Sarauniya ba ta hukunta wadannan Dakaru ba da suka yi mini fyaden duk da cewar sai da na kwana goma sha biyar a kwance ina jinyar jikina.

Bakin cikin nuna halin ko in kula da Sarauniya ta yi ne bisa abin da ya same ni ya zamo sanadın fara karuwancina. Har yau har gobe idan na tuna da wannan alamari sai na ji babu abin da na tsana a rayuwala sama da Sarauniya Zubaina domin ita ce ta salwantar da rayuwata.

Lokacin da Yaldisa ta zo nan a zancenta sai hawaye ya zubo mata sannan ta ci gaba da magana tana mai cewa, ya kai ma'abocin kyawu da kwarjini ka yi sani cewa ni ba na neman soyayyarka a gare ni saboda in na ce ka so ni ban yi maka adalci ba tunda ni ba tsararka ba ce a soyayya, kuma ni mace ce mara asali da mutunci ban dace da dan Sarauta ba kamarka a yadda ka ba ni tarihin rayuwarka amma ina da buri guda daya a rayuwata. Wannan buri nawa kuwa shi ne, na mutu akan tafarkın sonka kuma na ceci rayuwarka har izuwa lokacin da za ka sami nasara akan makiyanka. kuma ka ga Mashinka.

Lokacin da Yaldisa ta zo nan a jawabinta sai Jarumi Shaddadu ya ji ya kamu da tsananın tausayinta har hawaye ya zubo masa

Tsawon 'yan dakiku suna kallon junansu an rasa wanda zai ce Kala. Ita dai Yaldisa sai farın cıkı da mamaki suka kama ta a lokacin da ta ga hawaye na zuba daga cikin idanun Shaddadu. Abin da ta fara tambayar kanta shi ne, wai shin wannan hawayen na Shaddadu da ya zubo na tausayinta ne ko kuwa na kamuwa da sonta ne?

Nan ta kasa bai wa kanta amsa, amma sai ta Kudurce a ranta cewa har abada ba za ta taba mancewa da wannan hawaye ba na farin cıkı. ko iya shi ta samu a wajen Shaddadu ta san za ta tabu da shi a cikin farin cikın ya tausaya mata a rayuwa ko kuma ya so ta.

Bayan Jarumi Shaddadu ya yi dan dogon tunani da nazari a cıkın zuciyarsa sai ya dubi Yaldisa ya ce, ya ke wannan ma'abocıyar kyau da karamci ki yi sani cewa, kin yı mını taimako a rayuwa irin wanda ni ma har abada ba zan taba mantawa da shi ba kuma kin nuna mini Kauna kwatankwacin irin wadda babu wanda ya taba nuna mini face mahaifiya ta.

Ina fatan na saka miki da abın da ba za ki taba mantawa da shi ba. Tabbas na tausaya mikı matuka bisa yadda rayuwarki ta kasance kuma na gamsu cewar kaddara ce ta salwantar da rayuwarki.

Hakika ba ki da wani abokin gaba a doron Kasa wanda ya fi Sarauniya Zubaina. Ina so ki sani cewa, matsoraci ba zai taba zama gwani ba. Na fuskanci cewa ke ma kina da jarumtaka gami da taurin zuciya daidai gwargwadon irin ta ki, saboda haka, ina so ki zo mu hada karfi da karfe mu tunkari gıdan Sarauniya Zubaina yanzu mu yake ta ita da abokiyar gaba ta, a yi ta ta kare, ko mu ko su. Ni na san cewa zan ıya yakarsu da tsagwaron jarumtaka ta domin na samı cıkakken horon Yaki a Wajen maharfiyata.

Tabbas ba ni da burin da ya fi na daukı fansa a kan Ziya'ul Hak bisa abin da mahaifinta ya yi wa mahaifiyata, ya kashe dukkan zuri'arta kuma ya yi ma ta fyade aka samı cıkına.

Wani lokacın idan na tuna cewa ina farautar rayuwar mahaifina da kanwata ne sai na ji na kamu da tsananın bakin ciki. Amma kuma idan na tuna da irin wulakancin da aka yi wa mahaifiyata gami da bakin cikin da aka cusa mata sai na ji na tsani Mahaifin nawa da yar uwata Ziya'ul Hak. Koda Jarumi Shaddadu ya zo nan a zancensa sat ya fashe da kuka.

Alamarın da ya karya zuciyar Yaldisa ke nan ta kamu da tananın tausayinsa ba ta san sa'adda ta rungume shi ba ita ma ta fashe da kukan. Jim kadan sai ta janye jikinta daga cikin nasa suka fuskanci juna ta ce, yanzu idan muka yi kundunbala muka je muka tari su Sarauniya Zubaina da yaki to mene ne makomar Mashinka wanda ya fada cikin wannan korama? Shin ba ka zaton cewa zai iya fadawa hannun abokan gabarmu?

Sa'adda Jarumi Shaddadu ya ji waďannan tambayoyi guda biyu sai ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce, tabbas irin neman da na yiwa wannan Mashi nawa a cikin wannan korama inda yana cikinta da tuni na gan shi.

Haka kuma idan Mashin ya fada hannun abokan gabata da tuni sun gano inda nake sun zo sun hallaka ni.

A cikin biyu dole ne ya zamo daya, wato ko dai ruwa ya tafi da Mashin ya nutse a cikin Teku, ko kuma wadansu aljanun masu tsananin rabo sun tsince shi.

Ni a ganina abin kunya ne na koma gida wajen mahaifiyata na sanar da ita cewar wannan Mashi ya salwanta a hannuna bayan tun ina yaro karami take horar da ni Yaki da jarumta domin na kare kaina da wannan Mashi kuma na hallaka abokiyar gabata.

Masu iya magana sun ce, Sai an gwada akan san na kwarai. Yanzu ina neman alfarma ta karshe a wajenki da ki raka ni izuwa gidan Sarautar Sarauniyarku a yanzu domin na yake ta tun gabannin gari ya waye su fito yakata, saboda an ce, Ka kashe makiyinka kafin shi ya kasheka. Ba wai ina son ki raka ni ba ne domin ni kadai ba zan iya ba, a'a sai don saboda ke kin san sirrin gidan Sarautar kuma an ce, da dan gari akan ci gari.

Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Yaldisa ta ce, ai dama na gaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login