Showing 39001 words to 42000 words out of 71576 words
Chapter 14 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt
kallonsu, koda suka ji tsit alamar cewa suma su Boka Sadusa sunyi bacci, sai suka fito daga cikin kunnen aljani Raugatul Agwan uka fara kokarin sakkowa kasa, wanda a kokarin haka ne Hursiyya bata lura ba ta tsikari idon aljani Raugatul Agwanu da kafarta, ai kuwa sai Raugatul Agwanu ya kai duka da hannunsa izuwa kan idon. In ba don aljani Radiyan ya sureta sun rikito kasa tare ba da tuni ta ragargaje. Kawai sai sukaga aljani Raugatul Agwanu ya muskuta ya gyara kwanciya kuma ya cigaba da baccinsa tamkar ace mutum ne yake bacci kuda ya dameshi ya kureshi.
Nan dai Boka Radiyan da Gimbiya Hursiyya suka mike tsaye suka kama tafiya cikin sanda dan kada su boka Sadusa suji motsinsu, a haka suka nausa cikin daji.
Lokacin da suka yi nisa daga inda su aljani Raugatul Agwanu suke, ya zamana cewa basa iya hangosu, sai suma suka tsaya tare da zama a karkashin wata bishiya domin su huta. Gimbiya Hursiyya ta bude jakar guzurinta ta dauko abinci ta kama ci, sai da ta koshi sannan ta daga battar ruwa ta sha, kawai sai aljani Radiyan ya dubeta ya bushe da dariya. Al'amarin da yayi matukar bata mamaki kenan, ta dubeshi a fusace ta ce mene ne abin dariya anan?
Aljani Radiyan ya ce gani nayi kudai bil'adama abu abinda yake wahalar da ku sama da cikinku, n fuskanci cewa da yawanku idan baku ci abinci ba sau uku a rana bakwa samun kwanciyar hankali, sabanin mu aljanu da idan ta kama sai muyi shekara da shekaru babu ci da sha kuma mu rayu. Kamar yadda aljani markahussabus ya rayu shekaru dari uku da wani abu a cikin akwati, sa'ad da wani mashahurin matsafin sarki ya tsare shi a cikin wani kurkuku na karkashin kasa.
Koda jin wannan batu sai gimbiya Hursiyya ta gyara zama tana mai tattara hankalinta gabadaya akan aljani Radiyan tana mai cewa wane ne kuma Aljani Markahussabus?
Koda jin Wannan tambaya sai aljani Radiyan ya sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan ya ce To sarkin jin labari, ai sai dai kije ki nemi wani littafi mai suna KUNDIN TSATSUBA a cikinsa ne zaki samu labarin sarkin jaruman aljanu na duniya, wato Markahussabus wanda yayi gadon jarumtaka a wajen ubansa Larkul.
Koda jin haka sai Hursiyya ta murtuke fuska ta yi shiru bata ce komai ba, a lokacin da ta dan kishingida tana tunani. Daga can kuma sai ta dubi aljani Radiyan ta ce wai shin yanzu da ka janyomu nan muka yi nisa da su aljani Raugatul Agwanu idan kuma suka tashi suka tafi bamu sani ba, ta yaya zamu karasa can bakin kogin bahar sufiya?
Da jin wannan tambaya sai aljani Radiyan ya ce ashe ma ke duk hirar da su aljani Raugatul Agwanu suke yi dazu baki saurara ba, ai Raugatul Agwanu ya ce daga wannan daji zuwa bakin kogin bahar sufiya bai wuce tafiyar sa'a daya da rabi ba, kinga kenan zamu iya karsawa da kanmu, kuma idan bamu rabu da su anan ba asirinmu zai iya tonuwa har su ganmu. Idan kuwa suka ganmu to tabbas tamu ta kare dan nasan cewa kashemu z su yi, yanzu dai abinda nake so dake shine ki tashi mu cigaba da tafiya tunda kin huta domin mu rigasu zuwa sansanin yakin, tunda naji sunce su sai nan da sa'a bakwai sannan zasu cigaba da tafiya.
Ba tare da gardamar komai ba Hursiyya ta mike tsaye ta fara harhada kayanta cikin murna domin bata da wani buri d ya wuce ta isa bakin kogin Bahar Suffiya ta sake saduwa da danuwanta sarki dujalu kafin mai rabawa ta rabasu. Nan da nan kuwa ta nade shimfidarta, aljani Radiyan ya shige gaba tana biye da shi suka cigba da tafiya, haka dai suka cigaba da ratsa wannan kyakkyawan daji mai dauke da ni'imar kyawawan bishiyu, duwatsu da koramai, babu abinda da yake baiwa Gimbiya Hursiyya haushi face idan ta kalli aljani Radiyan ta ganshi dan mitsitsi a gabanta bai fi ta sa kafa ta shureshi ba, sai wasu siraran kahuhuna a kansa, sannan ga shi bakikkirin hade da jajayen kwalakwalan idanu, yana tafiya shafal-shafal kamar iska zata daukeshi, babu damar ya goyata bayanshi su tashi sama suyi wannan tafiyar cikin kankanin lokaci saboda kankantarsa da rashin karfinsa.
Haka dai suk cigaba da tafiya har tsawon rabin sa'a a cikin wannan daji b tare da sun hadu da wani mugun abu ba face face tsuntsaye da suketa shawagi a sama, sai kuma kananun dabbobin daji da kwari da ke kai kawo.
Kwatsam! Sai suka hango wani mutum daga can gabansu a zaune bisa buzu ya fuskanci gabas yana wani irin aiki mai kama da bauta, Mutumin yana sanye da fararen tufafi wadanda suka rufe jikinsa gabadaya, a gefe daya kuwa takobinsa ce a ajiye da jakar guzurinsa, da yake ya juya masu baya ne basa iya hangonsa balle su gane cewa tsohone ko yaro ne. Koda su Hursiyya suka hango wannan mutumin acan nesa da su sai suka firgita ainun, aljani Radiyan yayi maza ya kama hannu Hursiyya ya jata zuwa bayan wani dutse suka buya suna leken wannan mutum.
A lokacin ne Hursiyya ta dubi aljani Radiyan cikin tsananin mamaki tace haba ya kai Radiyan yaya kana matsayin aljani amman ka dinga shakkar biladama, duk ina hatsabibancinka?
Sa'ad da aljani Radiyan ya ji wannan tambaya sai yayi ajiyar zuciya sannan ya dubi Hursiyya cikin alamun karayar zuciya ya ce ai duk mahalukin da kika gani a cikin wannan daji to babu shakka hatsabibancinsa yafi gaban tunani, dan abubuwan hatsarin daya wuce sunfi gaban tunani, ke yadda aka yi ma yazo har nan dinma shine babban abin al'ajabi, saboda fiye da shekaru dubu arba'in ba'a taba samun wani mahaluki daya keta dazuzzukan wannan nahiya ba har ya isa bakin tekun Bahar sufiya ba sai a wannan shekara da aka zo neman kayan yakin mazan jiya, ni abinda nake so ki gane shine ban yarda da cewar wancan mutum ne ba, babu mamaki day daga cikin aljanun da suka zo wannan yaki ne ya zo nan dan yayi leken asirin abokan gaba dan kada a karo gudunmawar dakarun yaki.
Koda jin wannan btu sai gimbiya Hursiyya ta yi tsaki sannan ta ce ai wannan zancen banza nema kake yi, ta yaya wani aljani zai baro can sansanin wannan azababben yaki har ya zo nan alhali nasan ana can ana cikin bala'i da masifar da mutum bai isa ya gudu ba, tunda kai tsoro kake ji ni bari inje inga ko waye.
Kafin aljani Radiyan ya kara cewa wani abu tuni gimbiya tabfito daga bayan dutsen da suke boye ta durfafi inda wannan mutumin ke zaune, nan fa tsoro ya sake baibaye aljani Radiyan ya kasa biyota bare ya dawo da ita, dan haka sai ya cigaba da buya a bayan wannan dutse yana mai.leken abinda zai faru.
Hursiyya ta cigaba da tunkarar inda wannan mutum yake har yya zamana cewa tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku goma ba, kuma gashi takun sawun Hursiyya ya cika dajin gabadaya, saboda kasancewar tana taka busassun ganyayyakin da suka zubo kasa, amman abin mamaki shine ko motsawa wannan mutumi bai yi ba bare ma ya waigo yaga mai ke tahowa.
Kawai sai ya tsaida hankalinsa akan bautar da yake yi yana mai cigaba da fuskantar alkibla, al'amarin da yayi matukar baiwa Gimbiya Hursiyya mamaki kenan har ziciyarta ta buga da karfi, a lokacin da tsoro ya baibayeta ta fara tunanin to ko abinda aljani Radiyan ya fada mata gaskiya ne, na cewar wannan ba mutum bane aljani ne, kawai sai ta yi kundunbala ta cigaba da tafiyar har sai da ta isa daf da mutumin ta kuibin damansa, take tayi arba da fuskarsa, aiko nan take gimbiya ta dimauce ta kuma cika da dimbin mamaki, har bata san sa'adda ta durkushe kasa ba bisa gwiywoyinta tana mai kura ma wannan mutumi idanu ko kiftawa bata yi, ba wani abune ya ja dimauta gimbiya Hursiyya ba har ta kamu da tsananin mamaki ba face tsananin kyawun wannan mutum, domin ya kasance kyakkyawan saurayi wanda shekarunsa baza su wuce ashirin da biyar ba, duk irin tsananin kyawun gimbiya Hursiyya kuma duk da kasancewarta ya mace da tayi arba da wannan saurayi sai nan take ta ji ta raina kanta domin gani tayi ta zama mummuna akan wannnan saurayi.
Sai da saurayin ya gama ibadarsa ya juyo da nufin ya mike tsaye sannan ne yayi arba da Hursiyya. Cikin mamaki y ce mutum ko aljan?
Koda jin wannan tambaya sai ta kamu da tsananin mamaki da wani irin kallo mai dauke da alamar tambaya ta ce ai nice ya kamata nayi mkaa wannan tambaya, tunda babu wani mahaluki da ya isa ya kawo kansa nan face ya cika hatsabibi.
Koda jin haka sai saurayin yayi guntun murmushi wanda hakan yasa kyawunsa ya karu ainun, nan fa Hursiyya ta dada rudewa taji kamar ta rungumeshi, amman sai ta dake ta cigaba da kura masa idanu.
A lokacin ya cigaba da magana d cewa ni ba hatsabibi bane, kuma ban dogara da komai ba face Ubangijina, sunana Hasnalu Ibn Bashriyya ni ma'abocin addinin Musulunci kuma ba wani abu ya kawo nan ba face neman mahaifina wnada ya baro can nahiyarmu kimanin shekaru ashirin da suka wuce tun ban fi shekara biyar ba a duniya domin ya zo y yada Addininmu na Musulunci a nahiyoyin dake wannan bangare, tunda mahaifin nawa ya baro gida awancan lokacin kawo izuwa yanzu bai koma ba kuma ba a sake jin duriyarsa ba, ni burina kawai sjine na sani ko yana raye ko kuma ya mutu, idan ma ya mutu zan so ace koda kabarinsa ne na gani. Na sami labari cewa gaba daya mutanen dake wannan nahiyoyi sun tsani addinin Musulunci kuma sunyi imani da tsafi gami da bautar gumaka, dan haka ana sa ran lallai sune zasu kashe mahaifina.
Tun da na taso na fara wayo mahaifiyata take bani wannan labari, ni kuma tun a sannan n kudiri aniyar sai na zo wannan nahiya na sauya wa mutane addininsu da ma rayuwarasu akan tafarkin gaskiya domin duk addinin da suke yi addini ne na karya, tsafin da suke yarda da shi shirka ce kuma bata ne mabayyani, domin Ubangijine wanda yafi cancanta da a bauta ma wa, shine wanda ya halicci sammai da kassai kuma shine ya halicci mutum da aljan badan komai ba face su bauta masa a doron kasa, amman sai wasunsu suka bijire masa suka bautar waninsa suna aikata kafirci da alfasha a bayan kasa.
Lokacin da Jarumi Hasnalu Ibn Bashriyya ya zo nan a zancensa sai gimbiya Hursiyya ta cika da tsananin mamaki fiye da koyaushe ta dubeshi ta ce yanzu kai ta yaya zaka iya aiwatar da abinda ya gagari mahaifinka?
Koda jin wannan tambaya sai Hasnalu yayi murmushi ttare da cewa ai daman na fada maki tun farko ni da ubangijina na dogara, tunda kika ga mahaifina ya kasa jaddada addinin Allah a wannan nahiyoyi naku to Allah ne bai nufeshi da dacewa ba, amman ni ina sa ron dacewar.
Hursiyya ta yi shiru tana tunani gami da nazari al'amari a cikin zuciyarta, daga can kuma ta dago kai ta dubeshi ta ce yanzu yaya za a yi na gamsu cewar wannan addini naka shine na gaskiya akan namu, kuma ya za a yi nasan cewa Ubangijinka shine mafifici akan dukkanin wani Ubangiji?
Hasnalu ya sake yin murmushi a karo na uku sannan ya ce ai ni indai muna tare d ke, to da sannu zaki gaskata hakan.
Hursiyya tace ni kuwa idan har na fahimci addininka shine na gaskiya, to zan kaika inda zaka sa gaba daya mutanen dake wannan nahiya su karbi addininka kuma nayi maka alkawarin zan sa a bincika labarin mahaifinka, idan ma yana raye zan sa a nemoshi a duk inda yake.
Koda jin wannan batu sai Hasnalu ya cika da mamaki gami fa murna ya dubi Hursiyya ya ce ke kuma wace ce awannan nahiya da har kike tunanin zaki iya yi mani wannan taimako?
Hursiyya ta kalleshi sannan ta yi murmushi kana daga bisnai ta ce da shi suna na gimbiya Hursiyya, kuma na kasance kanwa ga sarki Dujalu, sarkin da gabadaya nahiyoyin nan babu kamarsa a karfin tsafi, mulki, jarumtaka gami da arziki face wani sarki d ake kira Maharaz. A yanzu haka dakarun sarki Dujalu dana Maharaz suna can a bakin wani teku da ake kira bahar sufiya suna ta gabza yaki a tsakaninsu... Nan dai Hursiyya ta zayyane wa jarumi Hasnalu dukkanin abinda ke faruwa har da makasudin wannan yaki, wato akan dauko kayan yakin mazan jiya saboda kowanne sarki yana da burin mallakar kayan yakin dan kawai ya samu damar mulkar mutanen duniya gaba daya.
Yayin da Hursiyya ta gama baiwa Jarumi Hasnalu wannan labari, sai ya cika da tsananin mamaki bis yadda mutane suka yi imani da karya da tsafi, sannan kuma sai ya kamu da farin ciki dan yana ganin cewa ya samu hanyar da zai jaddada addinin Allah a wannan nahiyoyi.
Hursiyya ta dubi Hasnalu cikin nutsuwa ta kare masa kallo sai taga bai kasance wani katon mutum ba mai kirar Sadaukai kuma gashi ya ce shi baya tsafi, dan haka sai fara tunani a ranta cewar ta yaya zai iya nuna wani abin jarumtaka wanda har zai sa mutane su amince da shi su karbi addininsa, tabbas indai zai je bakin tekun bahar sufiya ya dauko takobin Saiful Lujara a karkashin takun kowa ya gani to da ya tsaida yakin gabadaya kuma dole ne a gaskata ubangijin nasa.
Tana cikin wannan tunani ne suka hango aljani Radiyan ya taho da gudu dugul-dugul kamar zai kife kasa saboda gajarta, har jarumi Hasnalu ya zare takobinsa zai afka masa, sai Hursiyya ta sha gabansa ta dube shi cikin murmushi tace mayar da takobinka ai wannan abokin tafiyata ne, in ba don shi ba da ban zo nan ba, har ma na sadu da kai, nan take aljani Radiyan ya ja Hursiyya gefe suka kama kuskus, ya dubeta cikin alamun tsoro kamat ace ket ya fita da gudu, jikinsa na tsuma yace shin kin tabbatar da mutum ne wannan ba aljani ba?
Hursiyya ta kyalkkyale da dariya sannan ta ce na tabbar mutum ne. Nan take ta kwashe labarin dukkan abinda ya faru tsakaninta da jarumi Hasnalu ta zayyane masa.
Koda jin haka sai boka Radiyan ya murtuke fuska ya dubeta cikin fushi ya ce saboda me zaki gaskata zancen ma'abota addinin Musulunci, mutanen da suka kasance abokan gabarmu tun iyaye da kakanni, to ki sani cewa bamu da makiya sama da wadannan mutane, kuma duk abinda ya fada maki zancen banza ne babu gaskiya a cikinsa, kada kyawun wannan saurayi ya rudeki kizo ki aikata abinda zaki jefamu a cikin danasani.
Sa'ad da gimbiya Hursiyya ta ji wannan batu sai ta yi ajiyar zuciya kuma ta yi shiru tana tunani har izuwa tsawon yan dakiku, sannan ta dubi ljani Radiyan tace dole ne na jaraba wannan saurayi domin na tabbatar da gaskiyarsa ko rashinta kafin na ki bashi yarda ta, ai masu iya magama sunce ranar wanka ba a boyon cibi, kuma sunce sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a je ba, kawai mu cigaba da wannan tafiya tare da shi har mu kure karyarsa.
Koda ta zo nan a zancenta sai Hursiyya ta rabu da aljani Radiyan taje gun Hasnalu ta dubeshi cikin murmushi ta ce ni da abokin tafiyata mun amince mu tafi tare da kai har ixuwa filin daga inda ake fafata yaki, amman bisa sharadi guda, sharadin kuwa shine dole ne kayi abubuwan al'ajabi guda uku wadanda zasu nuna mana cewa ka cika jarumi, kuma ubangijinka shine ubangijin gaskiya.
Sa'ad da jarumi Hasnalu ya ji wannan batu sai yayi murmushi shima y ce nayi imani da ubangijina dari bisa dari, dan haka nasan cewa zai bani ikon hayewa wannna sharadi da kuka gindaya mani, nima kuma bisa sharadin muddin na yi wadannan abubuwa da kika shardanta mani to zaki karbi addini na.
Hursiyya ta yi murmushi sannan t ce na amince zan karbi addininka matukar kayi abubuwan dana sharadanta maka, muje zuwa mahaukaci ya hau kura.
Koda ta zo nan a zancenta sai jarumi Hasnalu ya mayar da takobinsa a cikin kubenta, kuma ya nannade buzunsa ya sabashi a bayansa ya daure sannan ya dubi aljani Radiyan ya ce wace hanya zamu bi ta kaimu zuwa bakin kogin na bahar sufiya inda ake yakin?
Aljani Radiyan yayi nuni da hannunsa izuwa yamma yana mai cewa nan zamu bi.
Nan take Hasnalu ya wuce gaba yan mai karanta wasu Addu'o'i na musamman a zuciyarsa, Hursiyya na biye fa shi daf da daf, sannan sai aljani Radiyan a bayansu.
Nan fa suk cigaba da kutsawa cikin sarkakiya, duhuwoyi, koramu d kwazazzabai, haka suka cigaba da tafiya tamkar ba zasu daina ba, wani lokacin sukan jiyo kukan manyan dabbobin daji acn nesa da su, wani lokacin ma sai suji tamkar a gabansu dabbobin suke kuka, amman wani iko na Allah har sai da suka shafe rabin sa'a sun tafiyar basu yi arba da muguwar dabba ko guda daya ba, banda kukan dabbobima sukan jiyo gurnani irin na dodanni da aljanu wanda hakan yasa aljani Radiyan da Hursiyya suka tsorata ainun jikinsu ya kama tsuma, amman sai suk ga shi jarumi Hasnalu ko gezau beyi ba, kawai sai cigaba yake ma da tafiyarsa tamkar a cikin gari yake ba a daji ba.
Kwatsam sai kawai suka ga sun shigo cikin wani wuri mai wani irin yanayi na ban tsoro, wajen yana dauke da wasu irin dogayen bishiyu masu tarin dogayen jijiyoyi da suka zubo kasa tun daga sama, sannan akwai ruwan wata korama a wajen da ke kwararowa daga kan duwatsu, bugu da kari kuma sai suka ga bishiyoyin ayaba da yawa a wajen kuma g shi an tsittsinki ayabar, anci wata an kuma zubar da wata a kasa gata nan a ko'ina birjit.
Koda suka yi arba da wannan wuri sai jarumi Hasnalu ya tsaya cak, kum ya juyo yayi w su Hursiyya da suma su tsaya kuma suyi shiru.
Nan take kuwa suka bi umarninsa, Hasnalu ya zaro takobinsa daga cikin kubenta a hankali dan kada aji sautin zaretan, sannan ya fara kallon gabas da yamma, kudu da arewa yana nazarin hanyar da ya kamata