Showing 60001 words to 63000 words out of 71576 words
Chapter 21 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt
ne ya yi arba da Ziya'ul Hak su bambance a wannan rana tunda kowannensu sai dai karfin dantsensa ya kwace shi ba dai karfin sihiri ba saboda kowannensu sihirin tsafinsa ya daina aiki.
****
A can Turakar Sarauniya Zubaina kuwa, tana cikin yin barcinta mai dadi har da munshari sai ta ji hayaniya kamar a mafarki.
A firgice ta farka ta mike zaune. Ai kuwa sai ta ji mafarki ya zama gaskiya domin gabadaya gidan Sarautar ya cika da sautin ihun Dakaru da guje-gujensu.
A daidai wannan lokaci ne ta ji Shugaban Dakarun tsaron na gidan Sarautar yana kwalla mata kira kuma yana buga kofa.
Cikin hanzari ta sauko kasa daga kan gadon tana sanye da rigar barci, kawai sai ta zaro Takobinta wacce ke tataye a sama jikin bango sannan ta je ta bude kofar, tana budowa ta yi arba da Shugaban Dakarun a tsaye jikinsa na tsuma.
Shugaban Dakarun ya dube ta cikin tsananin kaduwa ya ce, ya Shugabata yau dai wadansu zakwakuran Jarumai ne guda biyu suka kawo mana harin sumame gidan nan, duk yawan nan namu ya zama na banza sai tarwatsa mu suke, ga shi suna sanye da kayan Karle ko mun saresu bama iya cutar da su kuma ga dukkan alamu so suke su Karaso nan Turakarki.
Koda jin haka sai Zubaina ta yi murmushi ta ce, tabbas babu wadanda za su vi wannan aiki face Jarumi Shaddadu da Yaldisa.
Abin da nake so da kai shi ne, ka ruga can masaukin baki ka dauke Jaruma Ziya'ul Hak da sauri ka boye ta a wani wurin kada ka bar ta ta ce za ta tari su Shaddadu ta yake su face na yi arba da su, yanzun nan ni ma zan kimtsa na fito. Shugaban Dakarun ya risina ya ce, an gama ya Shugabata.
Kawai sai ya ruga da gudu ita kuma Sarauniya Zubaina sai ta shiga sanya kayanta na Yaki da sauri, ta kawo damara ta bakin karfe da bakin sulke ta sanya kuma ta zuba layu da gurayenta na tsafi duka sannan ita ma ta fito da gudu daga cikın Turakarta tana neman inda su Shaddadu suke.
Babban kuskuren da Sarauniya Zubaina ta yi shi ne, ba ta dauko madubin tsafinta ba ta duba ta ga a daidai inda Shaddadu yake bare ta je ta tare shi.
Al'amarin Jaruma Ziya'ul kuwa tun da ta kwanta a masaukin nata a wannan dare sai idanunta suka kekashe ta kasa yin barci saboda tunani da zullumin halin da ta tsinci kanta a ciki.
Hakika zuciyarta ba ta gamsu da cewar Sarauniya Zubaina za ta iya taimakonta ba akan su kawar da Jarumi Shaddadu kuma hankalinta bai kwanta da ita ba tunda ta fuskanci cewar babu wani abu da ya damı Sarauniya Zubaina face son ta mallaki Mashin Galilul Haras.
Nan take Ziya'ul Ilak ta ji babu abin da take so sama da ta yi gaba da gaba da Shaddadu domin su kawo Karshen wannan muguwar kiyayya tasu. Tana cikin tsakivar wannan tunani ne kawai ta ji gıdan Sarautar ya rude da hayaniya.
Nan take jikinta ya ba ta cewa lallai su Jarumi Shaddadu ne suka kawo harin sumame, kawai sai ta ji farın cıkı ya lullube ta. Cikin hanzari ta mike tsaye ta dauki makamanta na Yaki ta bude kofar dakin nata ta ruga waje da gudu tana neman su Shaddadu
Duk inda ta fi jiyo ihun mazaje nan take yi amma duk inda ta je sai dai ta yi arba da gawarwakin Dakaru ko kuma ta ga wadansu Dakarun sun taho da gudu sun wucewa ta suna neman su Shaddadu.
Al'amarin da ya fusata taa ke nan ta cigaba da falfala gudu tana shiga sako-sako, lungu-lungu.
Kwatsam! Tana shigowa cikin wata babhar haraba sai ta yi kicibus da Jarumi Shaddadu ya sheko da gudu. Wani akasi kuma da aka samu shi ne, babu kowa a wajen sai su biyu kacal, sai kuma daidaikun Dakarun gidan da ke gilmawa a guje ba su ma lura da su ba.
Lokaci guda duk su biyun suka yi tirjiya aka fara kallon-kallo, kuma kowannensu jikinsa ya kama tsuma, har tsawon 'yan dakiku
Daga can sai kowannensu ya fara kokarin zare makami, kuma a yanzu ne duk su biyun suka sami damar karewa juna kallo kamar yadda ya kamata
Koda kowannensu ya ga irin tsananın kyawun da Allah Ya bai wa dan uwansa sai zuciyoyinsu suka buga da karfi suka ji kamar su fasa yakar juna amma kuma da kowannensu ya tuno da irın labarin da aka ba shi akan irin kiyayyar da ke tsakanın iyayensu da kuma yadda aka cusa musu gabar juna ķtun suna yara sai dukkaninsu suka rugo da gudu izuwa kan juna suna masu daga makamansu sama suna kurma uban ihu
Ai kuwa suna haduwa suka kacame da azababben Yaki suka rinka kai wa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta tamkar jikinsu ba na jini da tsoka ba ne, na karfe ne.
Sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna bakin artabu amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin daya ba. Al'amarin da ya nuna cewar karfi ya zo dava ke nan. Da kansu suka ja da baya suka tsaya suna dan haki amma ko alamar gajiya babu a tare da su. kawai sun tsaya ne domin su yi tunanin irin salon fadan da ya kamata su sauya.
Ai kuwa sai suka sake rugowa da gudu a káro na biyu suka sake kacamewa da sabon masifaffen fada, Wannan karon dai sai suka sauya salo suka hada da yin alkafira a sama da kasa kuma suna kai naushi hannu da kafa.
Nan take kuwa fadan ya sauya yanayi domin sun fara samun nasarar yi wa juna illa sai dai wani abin mamaki shi ne, da zarar Shaddadu ya samu nasarar naushin Ziya'ul Hak a fuska sai ka ga ita ma ta samu nasarar ramawa.
Nan da nan cikin Kankanin lokaci suka hadawa juna jini da majina. A sannan ne fa suka fara jigata har kowannensu ya sami nasarar yankar kowa sau uku.
Ita dai Ziya'ul Hak ta yanki Shaddadu ne a cinyarsa ta hugu da ta dama, sai kuma a gefen kafadarsa ta hagu. Shi kuwa ya yanketa ne a dantsen hannayenta biyu da kuma bayan cinyarta ta hagu.
Kowannensu jini na diga a jikinsa har suna layi amma saboda na ci gami da taurin rai ba su daina ci gaba da kai wa juna hari ba.
***
A can wani bangare dabam na gidan Sarautar kuwa Sarauniya Zubaina ce da Yaldisa aka yi mugun gamo a lokacin da tazarar da ke tsakaninsu ba ta wuce taku goma ba.
Bayan kowacce ta yi turus! Sai Yaldisa ta yi sauri ta yar da Bakan da ke hannunta kuma ta cire jakar Kibiyoyin da ke goye a bayanta ta yar da ita sannan ta fuskanci Sarauniya Zubaina ta ce, abin kunya ne Jarumar Sarauniya kamar ki ta Yaki baiwarta da karfin sihiri ko makami, idan har kin yarda cewar ke Sarauniya ce kuma Jarumar da ta gaji jarumta da mulki ki ajiye tsafinki da makaminki ki yake ni da tsagwaron karfin dantsenki.
Ki yi sani cewa na dade ina jiran zuwan wannan rana da zan dauki fansa a kanki da iyayenki domin ku ne sanadin mutuwar iyayena, kuma ke ce sanadin lalacewar rayuwata na taso a cikin rashin tarbiyya na zama karuwa!
Koda Yaldisa ta zo nan a zancenta sai Sarauniya Zubaina ta bushe da dariyar mugunta, lokaci guda kuma ta turbune fuska ta ce, Ke yarinya tabbas yau zan nuna miki cewa na gaba yai gaba, na baya sai labari. Na rantse da darajar iyayena ba zan yake ki da karfin sihiri ba ko makami ba, zan yake ki da tsagwaron karfin dantsena.
Sai na yi miki dukan kawo wuka sanann zan murde miki wuya ko kuma na shake ki har sai numfashinki ya dauke kin zama gawa.
Yaldisa ta ce, ai inda babu kasa a nan ake gardamar kokawa, ga fili ga mai doki sai a zuba a gani.
Gama fadin hakan da wuya sai Yaldisa ta kwabe kayan karfen da ke jikinta ta zubar a gefe daya.
Ita ma Sarauniya Zubaina sai ta cire sulkenta da dukkan kayan Yakinta ta watsar sannan ta cire layu da gurayenta na tsafi ta dora su a kan wani gini mai tudu.
Nan fa kowacce a cikinsu ta dunkule hannayenta suka gyara tsayuwa suka kama tsuma, kawai sai suka tugo da gudu suka ruguntsume da azababben fada, Ko dakika goma ba a yi ba ido ya raina fata, domin nan take Yaldisa ta gane kuskurenta ta san cewa ruwa ba sa'an kwando ba ne, domin Zubaina ce ta rinka hada mata naushi ba kakkautawa, cikin bakin zafin nama. Tun Yaldisa na iya karewa har ta kasa, nan da nan Zubaina ta rinka gabzarta, kafin a jima ta fasa ma ta hanci da baki kuma ta kumbura ma ta idanuwa.
Tun Yaldisa na tsaye sai da ta fara ja da baya tana layi amma saboda juriya gami da taruin rai ba ta fasa kokarin kai hari ba. Cikin fusata Zubaina ta kutufi Yaldisa a ciki. Take cikin Yaldisa ya kulle ta rankwafa kasa, ai kuwa sai Zubaina ta dage iya karfinta ta yi mata wawan dundu a gadon baya.
Kawai sai Yaldisa ta kife kasa da rub da ciki ta kama amana jini a cikin wani irin mugun yanayi har ta kasa mikewa.
Koda ganin haka sai Sarauniya Zubaina ta kama kyalkyala dariyar mugunta ta zo kan Yaldisa ta raba kafafunta sannan ta kama gashin kanta ta fisgo baya.
Yaldisa ta kwarara ihu sakamakon tsananin zafi da zugin da ta ji tamkar wuyanta zai karya.
Zubaina ta tofa Yaldisa yawu a fuska ta ce, Karyarki ta sha karya ya ke 'yar talakawa. Hakika kin yi babban kuskure da kika bijire mini kuma zuciyarki ta yaudare ki da cewar za ki iya daukar fansa a kaina.
Yarinya tun kafin ki zo duniya na sami gadon jarumtaka domin a nono na sha ta, ba taka haye na yi ba, gado ne.
Kafin Zubaina ta gama rufe bakinta sai kawai ta ji Yaldisa ta doko bayanta da kafarta guda. Saboda karfin dukan sai da Sarauniya Zubaina ta yi tsalle can gaba ta fado kasa bakinta ya gurzu da kasa ya fashe.
Kafin ta yunkura ta mike tsaye tuni Yaldisa ta riga ta mikewa ta daka tsalle izuwa kan wannan tudun gini inda Zubaina ta ajiye gurayenta da layunta na tsafi. Cikin tsananin zafin nama da hanzari Yaldisa ta suri layun ta daurasu a wuyanta da hannayenta kuma ta daura gurayen a kugunta. Faruwar hakan ke da wuya Yaldisa ta ji wani irin gagarumin karfi ya shige ta.
Koda ganin abin da ya faru sai Sarauniya Zubaina ta durkusa kasa bisa guiwoyinta ta shiga rokon Yaldisa tana cewa, ya ke Yaldisa ki gaggauta cire waďannan layu da guraye daga jıkınki in ba haka ba kuwa komai da kowa da ke cikin gidan nan zai narke yanzu take ya zama ruwa.
Koda jin haka sai Yaldisa ta sa hannu ta share jinin da ke bakinta sannan ta bushe da dariyar farin ciki ta ce, ya ke wannan tsohuwar azzaluma, ke ma kin sani cewa babu abin da za ki gaya mini na yarda da shi. kuma ke ma kin san na san cewa kin fi ni Karfin dantse da jarumtaka nesa ba kusa ba. kawai na yi ganganci ne na tare ki domin na yaudare ki na sami nasarar raba ki da layun sihirinki, sai ga shi kuma gangancin da na yi ya yi min rana na sami dacewa. Yanzun nan zan hallaka ki domin na dauki fansa ta tsawon shekara da shekaru.
Kafin Yaldisa ta gama rufe bakinta sai Zubaina ta yunkura cikin shammace da zafin nama ta juya da baya guje domin ta gudu, ai kuwa sai Yaldisa ta yi nuni da hannunta izuwa kanta, take wata irin iska mai karfi ta daga ta sama ta rinka gwarata a jikin gini. Kafin a jima duk gabobin jıkınta sun kakkarye kuma jikinta ya farfashe ko ina jini ne ke zuba.
Sai da Yaldisa ta ga Zubaina ta daina motsi ko kadan babu alamar rai a jikinta sannan ta sauke hannunta ta zo kan gawar ta dube ta da kyau ta tabbatar da gawar ce sannan ta ruga da gudu izuwa cikin gidan Sarautar tana neman Jarumi Shaddadu tana kwalla masa kira.
********** **********
A can bangaren jarumi Shaddadu da jaruma Ziya'ul Hak kuwa, fadansu yayi tsamari ainun ya zama abin tsoro domin ta kai cewa kowannensu bai san sa'adda makaminsa ya subuce daga hannunsa ba don haka sai suka ci gaba da gabzawq juna naushi da bugu hannu da kafa.
Wani lokacin har gwara fuskokinsu suke sai dai kaga sun zube kasa magashiyan kamar sumammu.
Daga can kuma sai kaga sun mike sunyi gaba da kwarmazuwa da kokawa. Su fada nan su wulkila can. A haka ne suka ringa hawa kan wata matattakala wacce ta kai su har can saman wani gini mai tsawo gaske suka ci gaba da bugun juna
Suna cikin haka ne kafar Ziya'ul Hak ta gurde ta subuto daga kan wannan gini mai tsawon gaske zata fado kasa, har ta kwalla ihu saboda tsananin razana sai kawai taji an cafo hannunta tana reto a kasa koda tadago kai ta ga wanda ya cafo hannun nata sai ta cika da tsananin mamaki. Ba wani bane face abokin fadanta jarumi Shadaddu .
Kawai sai taga ya kura mata idanu hawaye na zubo masa ya kasa sakin hannunta ta fado kasa ta mutu.
Cikin tsananin mamaki ta dubeshi tace, ya kai abokin gaba meyasa ka ceci rayuwata yanzu alhalin tun dazu kake neman damar dazaka hallakani baka samu ba?
Sa,adda jarumi shaddadu yaji wannan tambaya sai hawayensa ya digo akan kumatun Ziya,ul Hak yace, yake ma,abociyar kyawu da kwarjini, kiyi sani cewa tun a lokacin da wannan fada namu yai tsamari naga muna neman muyi RAGAS naji nadama ta shigeni ba don komai ba sai don da na tuna cewa nifa yanzu a duniya banda uwata bani da sauran dan uwa ko dangi a doron kasa face ke tunda kin kasance ya a wajen mahaifi na.
Take a lokacin naji sonki ya mamaye zuciyata amma sai na kudurce a raina cewar da dai na kasheki gwara muyi MUTUWAR KASKO.
Wato mu mutu tare na huta da takaici ko bakin cikin tunanin na kashe yar uwata da hannuna.
Yanzu kuma dana ga ke ki mutu ki barni sai naga ba zan iya hakura ba shi ya sa na ceci rayuwar taki na dagoki sama izuwa kan wannan gini dana ke kwance a kai ko kuma nima na biyoki kasa mu mutu tare kinga shike nan mun kawo karshen gabar iyayenmu.
Lokacin da jarumi Shaddadu yazo nan a zancensa nan take itama taji ta cika da tsananin mamaki nan take itama taji ta kamu da tsananin kaunarsa a matsayin dan uwanta na jini.
Ba ta san sa'adda hawaye ya zubo mata ba.
A dai dai wannan lokacine Sharlis ta iso daf da su bisa Tsuntsuwan tsafi sannan kuma sai ga sarki laffaru da matarsa Ramlatul Siyam bisa Aljani Maruful Dauwaz sun bayyana an sa Shaddadu a tsakiya ana kallon kallo.
Gaba dayan jikin Sharlis sai ya kama tsuma tana kallon danta wanda ke rike da Ziya'ul Hak tana daka masa harara kuma tana hararar Sarki Laffaru.
Shima sarki laffaru yana hararar Ziya'ul hak kuma yana hararar Sharlis jikinsa na tsuma.
Daga can sai sharlis ta dakawa Shadaddu tsawa tace, Saboda me zaka ceci rayuwar yar babban makiyina a duniya.
Maza ka saki hannunta ta fado kasan wannan gini mai tsawo ta hallaka.
Kafin ta gama rufe bakinta tuni shima sarki Laffaru ya dakawa Ziya'ul hak tsawa yace da ita.
Me kike jira da dan babbar abokiyar gabata? Ga wuka nan a kugunki na hagu maza ki zareta ki caka masa a kirji.
Bisa mamaki sai Sharlis da Laffaru suka ga yayan nasu sun yi buris da umarninsu kawai suna kallon junansu suna murmushi.
Duk tsawon wannan lokaci Shaddadu bai gaji da rike hannun Ziya'ul Hak ba tana reto a sama.
Shaddadu ya dubi mahaifiyarsa yace, Yake Ummina kiyi sani cewa ni yanzu bazan iya kashe Ziya'ul Hak ba domin ina kallonta a matsayin yar uwata ta jini guda jal a duniya.
Tabbas bai kamata ace gabarku ta shafemu ba.
Yau dai gaki kuma ga abokin gabarku saiku rabawa kanku gardama. Idan har ya zama dole sai mun tayaku yin wannan gaba to ni na zabi na mutu tare da yar uwata inyaso ku mu barku a duniyar kuci gaba da gabarku.
Kafin Shaddadu ya gama rufe bakinsa sai itama Ziya,ul Hak ta dago kai ta dubi Sarki laffaru da mahaifiyarta Ramlatul Siyam a lokacin da hawaye ke zubo mata tace, Yaku iyayena kuyi sani cewa nima yanzu na gane kuskurena da kuka cusq mini gabar dan uwana a zuciyata tsawon shekara da shekaru kuma a halin yanzu babu abinda nake kauna sama da shi a zuciyata don haka nima nazabi na mutu tare da shi.
Tana gama fadin hakan sai ta dubi Shaddadu tayi masa wani irin murmushi mai nuna tsantsar so da kauna tace , Ya kai dan uwana idan har son da kake yi mini na gaskiyane to kazo mu hallaka kanmu yanzu take domin mutuwar mu ce kadai zata kawo karshen wannan tsohuwar gabar tw iyayenmu.
Nan take Shaddadu ya dago kaivya dubi mahaifiyarsa Sharlis a lokacin da hawaye ya zubo masa yace, ki gafarceni yake mahaitiyata wannan shi ne kallon karshe da zan yi miki a duniya. Tabbas ba zan bi zancenki ba sai dai nabi zancen yar'uwata.
Yana gama fadin hakan sai ya fado kasa dagga kan ginin ea yake kwance, shi da Ziya,ul Hak suka sallamo izuwa can kasan wannan gini mai tsawon gaske.
Akan wadansu cako cakon karafuna suka fado suka tsire, ko shurawa dayansu bai yi ba.
Koda ganin abin da ya faru sai Sarki laffaru da Sharlis suka kwarara uban ihu a lokaci guda kuma suka fashe da matsanaicin kuka na bakin ciki.
Ita kuwa Ramlatul Siyam saboda tsananin bakun cikin ganin mutuwar yarta a gaban idanunta nan take ta hadiyi zuciya ta bingire kaea matacciya.
Aljani Maruful Dauwaz kuwa, kasa ya sauko yai watsi da su Sarki Laffaru ya kama birgimq da ihu yana matsanaicin kuka saboda ganin mutuwarnZiya,ul Hak.
Bai san sa,adda yabkama sambatu ba yana mai cewa, Rayuwata bata da sauran amfani a doron kasa tunda na rasa mai kama da masoyiyata , kuma