Showing 24001 words to 27000 words out of 71576 words
Chapter 9 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt
CAN
SANSANIN YAKI DOMIN TA SADUWA DA DAN
UWANTA SARKI DUJALU
:
* * *
ACAN sansanin yaki kuwa ba a sake fitowa filin
daga ba sai bayan cikar kwanaki uku:
Da sassafe kowane bangare suka fito alaui
sahu sahu ana fuskantar huna aka baiwa tekun
bahar sufiya baya:::
NIMA SULEIMAN ZIDANE SAI NABAWA TEKUN
BAHAR SUFIYA BAYA:
DOMIN SAMUN LITTAFAN YAKI NA SOYAYYA
E:BOOK KAI HAR DAMA AUDIO MP3 ZAKA IYA
MANA MAGANA TA WATSAPP TA WANNAN
NUMBER KAMAN HAKA 09064179602:
TURAMAKA KUMA MUSAKA A GROUP DINMU
NA WHATSAPP:
NAKU HAR KULLU SULEIMAN ZIDANE KD
NAKE CEWA ALLAH YANUNA MANA GOBE
LAPIYA ::::
MAZAN JIYA 4
Littafe Na Hudu
Part 23
Na abdul aziz Sani:
Typing: Suleiman Zidane Kd:
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Da sassafe kowane bangare suka fito alaui
sahu sahu ana fuskantar huna aka baiwa tekun
bahar sufiya baya:::
wannan karon sai gashi su magaba daya
dakarun aljanu ma sun sauko kasa bisa turba
fuskanci junansu:
Rundunar sarki maharaz na kallon gabas su
kuma rudunar sarki dujalu sun bawa yamma
baya kowa sai muzurai yake:
Gurnani da hucin dakarun aljanu kadai ya isa ya
firgita mutu ya tsure da gudawa bare kuma
idan yaga tsananin yawansu da kwarjininsu:
Abangare bil adama kuwa dakarun kowane
bangaren sun yi sabuwar shiga Yaki fiye da
wadda suka yi a karon farko da karu na biyu a
Yakin kuma kowacce runduna ta fito ne a
fusace da nufin ayi ta ta kare a yau wadanfa ke
da sa a su sami nasara:Page: 131
Batare da shakkar komai ba Jarumi Inmal ya
fuskacin wani babban jarumi mayaki na sarki
dujalu wanda yafi kowa kokari a wancan karo
na biyu da aka fafata:
Sarki ya dubi inmal a wulakance cikin raini
sannan ya dubi sarki Maharaz ya bushe da
mahaukaciyar dariya yace yau zan kashe da a
gaban ubansa:
Sannan nayiwa uban mugun kisan gilla irin
wanda ba a taba yiwa wani mahaluki ba:
Kafin sarki dujalu ya gama rufe bakinsa tuni
jarumi inmal yatari numfashinsa cikin daga
murya ya daka masa tsawa yace kai tsohon
azzalumi karyarka ta sha karya:
Na rantse da kaunar da nake yiwa mahaifina
marigayi yau sai na kasheka da Hannuna kamar
yadda ka kashe min mahaifina domin na rushe
mugun nufinka na son ka mallaki kayan yakin
MAZAN JIYA domin ka cigaba da mulki zalunci
a doron kasa:
koda jin haka sai dujalu ya sake tuntsurewa da
dariyar mugunta a karo nabiyu sannan yace ai
shi kenan inda babu kasa anan ake gardamar
kokawa kuma ga filo ga mai doki sai akasa
tseren mugani:
Yau fa ba gudu ba ja da baya:
Ba za a busa kahon tsaida yaki ba har sai dole
bangare guda ya sami nasarar murkushe daya
bangare a yau babu batun mutum da mutu ko
aljani da aljan babu batun da tsafi ko babu
tsafi: Duk abin mutu yake takama dashi to yayi
amfani da shi tunda yau ne karo na karshe:
Page 132
Suleiman zidane kd:
whatsapp 09064179602:
Dajin wannan wajabi sai sarki maharaz ya yi
murmushi murna yace abin nema yasamu
tunda matar falke ta haifi jaki: Tunda ka zaba
hakan nima na amince muje zuwa mahaukaci
ya hau kura:
Nan take wani Shirgegen aljani mai siffan
batoyi daga bangaren dakarun Sarki Dujalu ya
daga wani narkeken kaho ya busa karar
bushin kahon ta cika dajin gaba daya amsa
kuwa har ruwan tekun yakaa tamba tambal
kamar zai yi ambaliya ya cinye duk abinda ke
wajen:;
KAI HATTA NI ZIDANE SAI DA NA TOSHEN
KUNNUWA NA SABDA TSABAGEN KARAR DA
YA ADDA BINI::
koda mayaka suka ji sautin wannan kaho sai
aka zabura aka ruga dagu daga kowawane
bangare::
Wahoho ! Karar sawayen Mutane da aljanu cika
kunnuwa sbda dudufniya kuma ya haddasa
karamar girgizar kasa:
Ihun mazaje kuwa da karajin aljanu ya haifar
da rudewar duk wata hallita dake dajin gaba
daya rudewar duk wata hallitar dake dajin gaba
daya har da wacce take cikin karkashin tekun
bahar sufiya:
Page 133
lokacin da rundunoni biyu suka gwamutse
kuwa sai aka ruguntsume da azababben yaki
na gaban tashin hankali; domin nan take
kasuwar diban rayuka ta kama ci:
sai dai kaga aljani ya daga kafa ya talitse bil
adama hamsin a lokacin guda:
WANNAN WANA KALAR BALA KI NE ZIDANE
KD:
Koda sarki maharaz da sarki dujalu suka ga
anfara asarar rayunka bil ada;a daga kowane
bangare sai kowannensu ya fara amfani da
karfin sihirinsa na kone aljanun abokan gaba:
Waiyo! Nan fa gaba dayan aljanun da ke
sansanin suka raina jarumtakarsu gami da
karfin sihirinsu domin duk ya tashi a banza sai
dai kaga aljani ya kama da wuta yana ihu yana
gudu domin ya fada cikin tekun bahar sufiya
amma kafin ya kai bakin tekun tuni ya kone
kurmus Hatta kasusuwan jakinsa sai sun
ruburbushe sun zama toka:
Babu abinda zai baiwa mutum tausayi face
yanayin mutuwar da suke yi domin da farko dai
sai sun fara kumbura sun yi suntum Ya yin da
wutar ta fara cin jikinsu sannan sai kaga
idanunwansu suna bullutsowa su fado kasa
daga nan kua sai cikin ya fashe kayan cikinsu
su zubo:
da sun fara kokarin gudu kuwa sai kaga
sassan jikinsu na guntulewa yana faduwa kasa
a haka har sai sun narke gaba dayan su zama
toka::
Page 134
zidane kd:
Sai da aka shafe sa a bakwai ana wannan bakin
gumurzu suma mutane suna nasu yakin:
kuma kowanen bangare suna asarar rayuka:
Duk inda jarumi inmal ya kutsa a cikin rudunar
sarki dujalu ta bil adama sai dai kaga mazaje na
zubewa kasa ramkar ana sassabe a gona
sbda inmal ya fito da wanannan yaki ne a
fusace da takobi biyu yake amfani don haka
nan da nan jikinsa gaba daya ya rune da jini:
Koda sa a bakwai ta cika sai ya zamana cewa
gaba dayan dakarun aljanun sun kare babu ko
guda daya a wajen:
Don haka sai aka daiana jin karajinsu: hakan
cetasa kowanne bangare suka janye aka ja da
baya akayi cirko cirko ana haki da kallon juna:
A sannan ne kowane bangare ya gano irin
mummunar barnar da akayi masa:
Su kansu dakarun bil adama na kowane
banagare an kashe kimanin kaso saba in daga
ciki dari::
Tarin gawarwakin da ke zube a kasa kuwa
wasu kan wasu har suna tisra a sama gar ya
ninka na wancan karon:
koda sarki dujalu ya dubi gaba day gawarwakin
dake zube a kasa kuwa wasu kan wasu har
suna tsira a sama har ya ninka na wancan karo;
koda sarki dujalu ya dubi gaba dayan
gawarwakin da ke kwance a kas kuma ya dubi
ragowar dakarun bil adaman da suka rage a
tsaye ya fahimce cewar RAGAS ake yi a
wannan yaki: sai rabsa ya baci zuciyarsa taka
ma tafarfasa kaan zata kone:
Page 135:
zidane kd:
kawai sai ya takarkare ya kwarara uban ihu
sannan ya wangame bakinsa wata irin
gagarumar guguwa ta rinka fitowa daga cikin
bakinsa ta durfafo inda abkan gaba suke zata
hallakasu gaba daya:
koda sarki maharaz yaga wannan guguwa ta
durfafo rundunarsa sai shia ya wangame
bakinsa irin wannan guguwa ta rinka fita da
gudu taje ta tare guguwar dujalu:
Ai kuwa suna haduwa sai suka haifar da tsawa
tartsatsin wuta gai da walkiDa kumma girgizar
kasa:
tsawon yan dakiku ana cikin wannan masifa
gami da tashin hankalo amma an rasa wanda
zai iya cutar da wani:
Al amarin daya fusata sarki maharaz da sarki
dujalu kenan suka ci gaba da jarraba sirrinkan
tsafin su kenan har sai da kowannen yayi
amfani da sihiri guda dari da tara da casa in da
tara; a Lokacin be duk su biyun suka jigata
ainun kuma suka jike sharkaf da gumi suka
zube kasa a cikin matukar galabaice suna
numfashi sama sama:
kamar ransu zai fita:
A wannan lokaci jama ar kowannensu sun yi
cirko cirko suna kallon abin al ajabi: baan sarki
dujalu da sark maharaz sun dawo cikin
hayyacinsu sai suka mike tsaye a tare kamar
hadin baki suka tako kafafuwansu suka durfafi
juna:
Page 137
Cikin Alamun tsoro inmal ya yunkura zai kaiwa
sarki maharaz dauki don gudun kada dujalu ya
cutar da shi kawai yaji anrukoshi ta baya yana
waigawa ya ga ashe Gimbiya mulaifa ce kawai
sai ta dubeshi tace kwantar da hankalinka ya
masoyina sarki dujalu ba zai iya cutar da
mahaifina ba sbda karfinsu yazo daya kuma
kasani cewa babu yaudara ko ha inci a wannan
yaki bisa alkawarin da aka dauka da farko sai
gaskiya da gaskiya:
kai ga ke nan ko yar kashi zasu gwada kafin ya
cutar da shi zamu iya kai masa dauki a sake
ruguntsumewa da yakin gaba daya: kuma ni
ina ganin cewa tunda yanzu sarki dujalu yasami
nakasa hannu daya gareshi sarki zai iya saun
galaba akansa:
inmal ya girguza kansa yace bahaka bane duk
yadda kike zato sarki dujalu ya wucce nan
wannan rashin hannun dayan da yayi ba zai
rage masa komai ba face a yakara masa
tsananin kafin zuciya da taurin domin ya gaya
dauki fansa:
Ni yanzu kawai abinda nake tsoro shi ne rashin
sanin mutane hudun da aka ce sune kadai zasu
rayu a wannan Yaki; ni kaina bana sa kaina a
cikin wadanda zasu tsiran:
Page
137
koda jin haka sai mulaifa ta girgiza ka tace idan
har kayi imani da cewa akawi wani addini
wanda yafi dukkan addininmu gaskiya to bai
kamata yanzu karinka amfani da abinda
tsafinmu ko tsafin sarki dujalu ya fadi ba:
Ka yi sani cewa tun da ka bani labarin ma
abota addinin MUSULUNCI sai tunanina ya
sauya akan komai kuma naji cewar na gamsu
da addini don haka kaia yanzu ina sonka sauya
tunaninka daga kan komai ya koma ya izuwa
ga yarda da wannan sabon addini na
Musulunci:
Sa adda jarumi inmal yaji wannan batu sai yayi
ajiyar zuciyar sannan yace hakika kin yi Gaskiya
ya masoyiyyata tabbas yanzu bani da tabbacin
abin da zai faru a karshen wannan yaki:
Yanzu dai bari muzuba ido muga abinda zai
faru a tsakanin manya Giwayen biyu:
Gama fadin hakan ke da wuya sarki maharaz da
sarki dujalu suka hada yazamana cewa tazarar
da ke tsakaninsu bata wucce ta ku uku ba:
sarki dujalu ya dubi maharaz ya kyalkyale da
dariya ai kuwa shima sarki maharaz ya bushe
da dariyar suka zama kamar wadanda suka
sami tabin hankali:
lokacin guda kuma suka tsuke bakunansu
koda ya murtuke fuska sannan dujalu ya
dubeshi yace Hakika nayi maka jinjina yakai
abkin gaba:
domin haka akeson namijin kwarai ya zamo mai
taurin rai da rashin Karayar zuciya:
gashi dai fiye da rabin dakarunmu na yaki sun
shude amma baka sare ba kuma gashi na
kashe babban amininka abokinka kuma
masoyinka na kwaria wanda ya kasance dirka
birninka amma ba ka razana ba:
to fa ka sani cewa yanzy ne zan a rufe babin
wannan yaki tunda ni da kai duk mun yi amfani
da karfin sihirinmu har guda daru tara da casa
in da tara saura guda dai dai yarage mana
kuma kasani idan mukayi amfani da cikon na
dubun dayan mu bai sami nasara ba shi ne har
abada tsafinmu ya daina tasiri::::
ANAN ZANDAKATA SAI KUMA GOBE IN
ALLAH YAKAIMU :SULEIMAN ZIDANE KD:
DOMIN SAMUN LITTAFAN YAKI NA SOYAYYA
E:BOOK KAI HAR DAMA AUDIO MP3 ZAKA IYA
MANA MAGANA TA WATSAPP TA WANNAN
NUMBER KAMAN HAKA 09064179602:
TURAMAKA KUMA MUSAKA A GROUP DINMU
NA WHATSAPP:
NAKU HAR KULLU SULEIMAN ZIDANE KD
NAKE CEWA ALLAH YANUNA MANA GOBE
LAPIYA ::::
Pls kuringa comment inbakwayi zan dana post
gaskiya nafara gajiya
MAZAN JIYA 4
Littafe Na Hudu
Part 24
Na abdul aziz Sani:
Typing: Suleiman Zidane Kd:
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
sihirinmu har guda daru tara da casa in da tara
saura guda dai dai yarage mana kuma kasani
idan mukayi amfani da cikon na dubun dayan
mu bai sami nasara ba shi ne har abada
tsafinmu ya daina tasiri::::
Sa adda sarki maharaz yaji wannan batu sai ya
bushe dariya al amarin da yai matukar baiwa
sarki dujalu mamaki kenan:
Maharaz ya dubi dujalu a fusace yace ai ni ban
ga amfanin sihirin tsafi ba a wajenmu yanzu
tunda gashi yanzu dayanu bai cinye wannan
Yaki ba sbd haka in ka shirya ga cikon sihirin
tsafi nan na dubu gareka:
Kafin sarki dujalu ya budi baki yace wani abu
tuni sarki maharaz yayi nuni da Hannunsa
izuwa kan dujalu:
Nan take wata irin farar wuta ta tafi izuwa
kansa zata koneshi:
bisa dole ba don a son ransa ba yana kuka da
ihu gami da takaici sarki dujalu ya tare wannan
farar wuta da nasa tafin hannun sai gashi
shima tasa farar wuta ta taho da gudu ta tari ta
Sarki maharaz:
Wutar biyu na haduwa sai suka yi bindiga
tamkar dutsen wuta ne ya fashe har sai da
dajin gaba daya ya yi girgiza:
Sarki dujalu da Sarki maharaz kuwa sai gani
aka yi sun sulale kasa sumammu:
A guje kowane bangare suka je suka dauko
sarkinsu Sai da aka yayyafawa su sarki
maharaz ruwa sannan suka farfado:
Koda kowannensu ya bude idanu sai suka mike
tsaye zumbur a fusace: Nan take kowannensu
ya zare takobinsa ya daga ta sama:
Page 139:
cikin hadin baki kowanensy ta kwarara uban
ihu yana mai ba da umarnin a afkawa abkan
gaba:
Nan take kuwa kowacce runduna ta zare
makamanta aka ruga da azababben gudu cikin
mugun nufi ana ihu da kururuwa:
Ana haduwa a tsakiya sai aka gwamutse kuma
aka ruguntume da masifaffen yaki:
karar karafa ta cika dodon kunne aka shiga
gididdibar sassan jiki jii ya rinka fallatsi da
fauntsama asama yana yiwa mutane da kasa
ado:
Ihun mazaje ya yawaita bisa sa kuwa sai sarki
dujalu da inmal suka yi karo da juna:
Sarki maharaz da babban sadaukin nan na
dakarun dujalu ma suka yi karo;
NIKUMA ZIDANE SAI NAYI KARO DA
WADANDA BASU SAN YI MANA COMMMENT:
PAGE 139
Nan fa aka kacame da azababben yaki ya
zamana cewa jaruman hudu suna kaiwa
junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama
juriya da bajinta :
CAIKO HAKIKA MASU KARIN MAGANA SUYI
GASKIYA DA SUKA CE TASHIN HANKALI BA A
SAMASA RANA KUMA WANDA BAI SAN YAKI
BA SHI NE YAKE CEWA ALLAH YA KAWOSHI
DOMIN MASIFARSA TA WACCE TUNANIN MAI
TUNANI:
IN BA YAKI BA MENENE YAKE KAWO FATARA
DA TALAUCI FARAT DAYA?
YAKI NE YAKE HADDASA YUNWA DA
KISHIRWA KUMA SHI NE YAKE HADDASA
CUTUTTAKA MARASA ADADI:
YAKI NE YAKE KONE ALBARKATUN KASA
KUMA YA GURBATAR DA RUWAN SHA:
Kai jama;a wanan rana ita kanta masifa sai da
tasan cewa ta jangwalo masifa domin sai da
maza suka raina kansu domin sun san cewa
suna karo da maza yan uwansu:
anfara wannan yaki Gumurzu tsakanin sarki
dujalu da jarumi inmal duk su biyun suka gano
cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba
domin karfin yazo daya duk da cewa kuwa
Sarki dujalu da hannun daya yake yakin amma
sai gashi yazamewa inmal alakakai:
Shi dai sarki dujalu yana amfani da kwarewarsa
gami da sanin makama kuma da tsohon kashi:
Page 141
zidane kd:
Shi kuwa inmal yana amfani ne da tsananin
juriyarsa da nacinsa inbadon hakan ba datuni
ssarki dujalu ya gama da shi::
Gashi dai karfin dantsensu yazo daua gami da
zafin namansu domin kowanensu yana iya kare
harin kowa kuma yamai da martani to amma
dai kowanensu hankalinsa a tashe yake, domin
sun san cewa idan aka jima anan wannan
gumurzu a haaka komai zai iya faruwa:
Irin wannan matsala da Sarki dujalu da inmal
suka fuskanta ce ta sami sarki maharaz da
sadauki Himalu na bangare sarki dujalu, don
haka tsanani yakai tsanani, tura takai tura kowa
ya kuntata mafita kawai ake nema ta kowanen
hali.
WANNAN SHINE ABINDA YAFARU A BAKIN
TEKUN BAHAR SUFIYA A LOKACIN DA YAKIN
KARSHE YA KACAME TSAKANIN RUDUNAR
SARKI DUJALU DA RUNDUNAR SARKI
MAHARAZ, DUK SABODA KAYAN YAKIN
MAZAN JIYA WADANDA SUKE KARKASHIN
KOGIN BAHAR SUFIYA KUMA BABU WANDA
YA SAN A INDA KAYAN YAKIN SUKE FACE
WADANSU MUGAYEN AZZALUMAN ALJANU
MASU TSANANIN KARFIN DANTSE MAZAUNA
KARKASHIN TEKUN WA DANDA SUNE MASU
GADINSU.
ADADIN ALJANUN YA NINKA ADADIN
DAKARUN DA SUKA YI YAKIN A BAKIN TEKUN
SAU ARBAlN, DON HAKA SUN ZUBA IDO SUGA
WANNAN ZAI IYA SHIGOWA CIKIN
KARKASHIN TEKUN YA HALLAKASU GABA
DAYANSU YA IYA DAUKAR TAKOBIN SAIFUL
LUJARA:
Page 141
zidane kd:
page 142
ANAN ZANDAKATA SAIKUMA IN ALLAH YA
NUNA MANA GOBE KUYI HKR BAYAWA YAU
DAN ALLAH COMMENT:::::
DOMIN SAMUN LITTAFAN YAKI NA SOYAYYA
E:BOOK KAI HAR DAMA AUDIO MP3 ZAKA IYA
MANA MAGANA TA WATSAPP TA WANNAN
NUMBER KAMAN HAKA 09064179602:
TURAMAKA KUMA MUSAKA A GROUP DINMU
NA WHATSAPP:
NAKU HAR KULLU SULEIMAN ZIDANE KD
NAKE CEWA ALLAH YANUNA MANA GOBE
LAPIYA ::::
MAzAN JIYa 4
Littafe na hudu
Part ::25
Typing:: Suleiman zidane kd:
whatsapp 09064179602:
::::::::::::::
DON HAKA SUN ZUBA IDO SUGA WANNAN
ZAI IYA SHIGOWA CIKIN KARKASHIN TEKUN
YA HALLAKASU GABA DAYANSU YA IYA
DAUKAR TAKOBIN SAIFUL LUJARA:
Page 141
zidane kd:
page 142
::::::::::::::::::::::::::::::::
Acan dajin darul Hushushul maut kuwa aljani
Raugatul Aguwanu Ya shafe sama da sa a tara
yana bincike a cikin madubin tsafinsa domin ya
tabbatar da gaskiyar al amarin da su boka
sadusa suka zo masa da shi amma sai ya kasa
ganin komai.
A karshe ma daya matsa bincike sai madubin
tsafin nasa yayi bindiga ya tarwatse. Al amarin
da matukar firgitashi ke nan ya sake sallamawa
boka sadusa.
Da sassafe su boka sadusa suka farka daga
barci a cikin wannan kogo na aljani Raugatul
Aguwanu, suna bude idanuwansu suka ga aljani Raugatul Aguwanu a zaune yagama shirin tafiya yana
sanye da bakin sulke na yaki irin nasu na aljanu
sannan yana rike da wani dogon mashi gami da
garkuwa.
A wannan lokaci idan mutum ya kalli ajani
Raugatul Aguwanu sai yayi zaton cewa shi
kadai zai iya yakar duniyar gaba dayanta sbda
tsananin girmansa da kwarjinsa:
Nan take Raugatul Aguwanu ya dubi boka
sadusa yace na gama dukkan binciken da zan
yi kuma na gamsu da duk abinda kazo mini da
shi sbda haka yanzu ni nagama shirin wannan
tafiya ku kawai nake jira.
Page 144:
Tabbas da na zauna yaki yazo yacini har gida
gwara naje na tari yakin. Koda jin wannan batu sai boka sadusa ya kyalkyale da dariya mugunta sannan yace ai
kuwa kayi wa kanka riga kafi domin da cin dare
daya kumburin ciki gwara dayawa tunda a dade
anayi sai gaskiya. Batare da bata wani lokaci ba su boka sadusa
suka shiga harhada kayayyakinsu:
Suna cikwannan hali ne aljani Raugatul
Aguwanu ya kyalara ido ya kalli Gimbiya
Shalbirat ya ganta a cikin ainahin siffarta ta
mutum nan take yaji ya kamu da tsananin
sonta fiye da ko yaushe, sannan sai takaici ya
rufeshi ya fara tunani zuci, yana mai aiyanawa
aransa cewa idan fa yayyi wasa wannan karon
shi kenan an rabashi da shalbirat.
Nan take ya dubi boka sadusa a fusace ya ce
yakai wannan takadarin boka shin mun yi
yarjejeniyane da kai akan cewa zaka fiddo
Gimbiya shalbirat daga cikin kejin dana sata
har ka dawo mata da ainahin siffarta?
Sadusa yadakawa Raugatul Aguwanu tsawa
yace tsakanin ni da kai wanene yafi sanin
abinda yadace?
Kada kasake yi mini shisshigi a cikin aikina, ' domin
duk abin da kaga nayi shi ne daidai kuma
kauce masa zai janyo rugujewar dukka
shirinmu.
Page 145
zidane kd:
koda jin wannan batu sai jikin aljani Raugatul
Aguwanu yai sanyi ya sunkui da kansa kas
sanna yace toni zan fita waje dommin na sami
damar bude fuka fukaina gaba daya zan
kwanta a kasa na rankwafa da zarar kunfito sai
ku hau kaina ku zauna ni kuma na tashi daku
sama mu kama tafiya. Ina mai tabbatar muku dacewa zan kaimu bakin
tekun bahar sufiya a cikin abinda bai wuce sa a
hudu ba amma fa bisa sharadi guda :
Cikin mamaki boka sadusa yace wannen irin sharadi kenan?
Raugatul Aguwanu yace ai dama tunda farko baku yi dani cewa cikin sansanin yaki zan kai
ku ba: lallai zan sauka ne a can bayan sansanin
nesa da shi inda ba za a hangomu ba sai dai
mu hangosu.
Koda jin wannan batu sai boka sadusa ya bushe da dariya yace haba ya kai Raugatul Aguwanu yaya kana matsayin sarkin sadaukai na aljanun duniya amma ka dinga jin tsoro?
Raugatul Aguwanu yace ai komai isar aljani a wannan zamani dole ne yaji tsoron sarki dujalu.da sarki maharaz sbd sun kure sun kai kololuwa a matakin karfe na sihirin tsafi.
Sadusa yace to shi kenan naji mazza kaje wajen ka jirau gamu nan fitowa.
page 146
Nan take Raugatul Aguwanu ya fice daga cikin
kogo dutsen yana ai waigen gibiya shalbirat
cikin wani irin kallo mai nuna tsantsar kaunarsa
a gareta ita kuwa sai ta galla masa harara tana
ai da masa martanin kallon na tsananin kiyayya yadda inda za a danne mata shi zata iya sa wuka ta yankashi, musamman idan ta tuno da yankan kaunar da yai mata ya rabata da kasarsu da iyayenta ya ajiyeta acikin keji kamar tuntsuwar tsawon shekaru goma sha tara.
Da fitowar aljani Raugatul