Showing 18001 words to 21000 words out of 71576 words

Chapter 7 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt

min
gaskiyane to yaya zan iya kubuta kena
n:
Ni dai kam da dai na zauna a karkashin wani
mulkeni gwara na kashe kaina domin ban ga
anfani wannan tsananin karfin dantsen nawa
gai da karfin sihirina wanda na shafe sama da
shekaru arba in ina yawon nemansa a cikin
duniya::
Sadusa ya gyada kai yace tabbas kayi gaskiya:
Amma ina mai tabbatar maka dacewa ni ina da
mafita a gareka amma sai bayan ka gama
bincikenka kaga gaskiyar wannan al amari
sannan zan gaya maka mafitar kuma bisa wani
sharadi::
Koda jin haka sai aljani Raugatul Aguwanu ya
kyalkyale da dariya sanna yace hakika yai na
gamu da sarkin wayo:
Ti amma fa kasani ramin karya kurarre ne idan
har duk abinda kazo mini dashi ba gaskiya
bane asirinka zai tonu::
idan kuwa asirinka ya tonu da kai da wancan
kyakkyawan dan naka sai nayi muku mugun
kisan gilla irin wanda ba taba yiwa wani
mahaluki ba a doron kasa:::
kafin Aljani Raugatul Aguwanu ya gaa rufe
bakinsa tuni boka sadusa ya dakamasa tsawa
yana mai cewa kai matsoracin aljani wanda
yakasa fita filin daga inda manya mazaje ke
fafatawaa:
ina mai horonka da ka iya bakinka ka saisaita
lafazinka a gareni in ba haka ba kuwa yanzu
nan zan fusata na koneka kua na kone gaba
dayan wannan daji dakake matukar kauna
kamar yadda uwa keson danta::
Dajin wannan jawabi sai Raugatul Aguwanu ya
dan tsorata don haka sao ya sunkui da kansa
kas cikin alamun girmamawa yace kayi mini
uzuri ya kai takadarin boka ka sani fa ni haka
halina yake bana son raini::

YANzu dai ni a koshe nake zan sha giya domin
na kwanta na yi barci sosai sai dare ya tsala
sannan zan tashi nayi bincike a Hallarar tsafina
bisa wannna sabon al amarin daka zo mini da
shi::
Abinda nake bukata da ku shine ya yin dana
fara barci bana bukatar naji matsin komai ko
yaya yakee domin idan har na farka bana iya
komawa barci::
Kai idan da hali ma ku fita daga waje kuje ku
yawata a cikin dajin nan har izuwa lokacin da
zan tashi daga barcina::
ina mai tabbatar muku da cewa akwai abbuwan
al ajabi da yawa a cikin daji nan wadanda zasu
debe muku kewa izuwa lokacin tashina daga
barci:
Koda jin wannan batu sai sadusa yayi
murmushi sannan yace ka san ance da dan gari
akan ci gari:
Me zai hana fito da wannan kyakyawar yarinya
daga cikin keji domin tayi mana jagora a cikin
wannan daji tunda ta fimu saninsa?
Sa adda aljani Raugatul Aguwanu yaji wannan
bukata ta sadusa sai yai shiru ya juya al amarin
a cikin zuciyarsa kuma ya kurawa sadusa
idanun cikin alamun Rashin Yarda daga can sai
yace Menene tabbacin cewa ba yaudarata za
kuyi ba ku gudu da Gimbiya SHALBIRAT?
Kai sani cewa da raina babu wani abu na biyu
da nakeso sama da ita:
Page 101
sadusa yai murmushi yace Ai inda don ita na
zo wannan daji da baza kazo ka riskemu ba a
cikin kogonka tunda ina da karfin sihirin da zan
iya saceta:
Raugatul Aguwanu ya gyada kai cikin alamun
nuna gamsuwa amma a can karkashin
zuciyarsa Dari dari yake yi:::
Kawai sai yayi kuru ya sa danyatsansa guda ya
bude kejin da gimbiya Shalbirat ke ciki:
Shabiyat ta taka dan yatsan Raugatul Aguwanu
cikin tsananin farin ciki mara misaltuwa sbd
tsawon shekaru goma sha bakwan da ta yi a
wannan daji na Darul Hushushul maut a cikin
kejin ta yisu bata taba fitowa ba waje:::
A sannan ne Raugatul Aguwanu ya sauke tafin
hannunsa kasa ta dir:
Sai gata yar motsitsiya a gaban sadusa tamkar
dan karamin bera::
Duk wannan abu dake faruwa Halyal na tsaye a
can gefe daya ya kurawa Shalbiyat idanu yana
mai matukar al Ajabi bisa ganin tsananin
kyawunta wanda yake ganin cewa ko Gimbiya
Hursiya kanwar sarki dujalu Albarka::
Lokacin da Shalbirat ta duro kasa daga kan
tafin hannun Raugatul Aguwanu sai ta kaa
raawa da tsalle doin murna kuma ta fasge da
kukan farin ciki:
Page 102
A sannan ne aljani Raugatul Aguwanu ya dubi
sadusa yace Ga masoyiyata Gimbiya Shalbirat
na fito da ita kua na damkata amana a
hannunka:
ka tafi da ita izuwa cikin daji ku yawata daga
nan har izuwa wayewar gari:
Koda gama fadin hakan sai aljanin Raugatul
Aguwanu ya nufi inda aka ajiye wani katon tulu
wanda sbd girmansa da nauyinsa kato arba in
bazasu iya rabashi da kasa ba ama shi da yan
yatsu biyu ya daga tulun:
Ashe tulun cike yake da ruwan gida kawai sa
i ya kafa bakin tulun a bakinsa ya kama sha
kwal kwal karar tafiyar ruwan giyar a cikin
cikinsa tamkar ruwan tekune ya balle yana
shatata izuwa cikin teku::
Raugatul Aguwanu bai sauke tulun giyar
kasaba sai da yaji babu sauran digo daya na
ruwan giya sannan ya ajiyeshi a kas ya tafi
izuwa kan wannan katon gado nasa na alfarma
yana layi yakife kasa:
ko dakika goma bayi ba ya kama wani irin
gagarumin Munshari:::
koda ganin faruwar hakan sai gimbiya shalbirat
ta yunkura a fusace ta zare wata wukar sihiri ta
aljani Raugatul Aguwanu dake kugunsa daga
sama da nufin ta caka masa ita a kirjinsa sai
boka sadusa yai wuf ya rike hannunta sanan ya
karbe wukar ya mai da ira cikin kufenta da ke
jikin Raugatul Aguwanu Sadusa yayiwa
Shalbirat da Halyal nuni da suyi shiru kuma
kada suyi wani kyakkyawar motsi:
Nan take yajasu suka fice daga cikin kogon
gaba daya:
Sai da suka yi nisa da inda kogon dutsen yake
inda basa iya hangoshi sannan suka zauna
domin su dan huta:
za;ansu ke da wuya sai Shalbirat ta fashe da
matsanincin kuka::
Al amarin da yai matukar dugunzuma hankalin
su Halyat kenan suka shiga rarrashinta suna
tamyarta dalilin kukan nata:
Da kyar suka shawo kanta ta daina kukan
sannan tace ba komai ne yasa kuka ga ina
wannan kuka ba face tsananin bakin cikin kun
hanani kashe aljani Raugatul Aguwanu domin
ya salwantar da rayuwata kuma ya kunsa min
bakin cikin da Har na mutu babu wata fansa da
za ta kankareshi:
Page 103
kuyi sani cewa ni ce ya guda daya a wajen
mahaina sarki sharyalu na Birnin taukib:
babu irin kalar gatan da ban gani ba a duniya
kuma a nahiyar damuke babu wani sarki mai
karfin mulki da tarin dukiya irin ta mahaifina:
Mahaifin nawa bashi da kowa a duniya face
wata kanwaesa mai suna JUZAIRAT ta ri ga
mahaifina yin aure da shekara shida amma
bata taba samun haihuwa ba har mahaifina
yazo ya yi auren ka haifeni:
Al amarin da yajefa juzairat cikin tsananin bakin
ciki kenan sbda bata da wani buri wanda ya fi
ta haifi dan da zai gaje sarauta::::Page 104
Suleiman zidane kd::
babu irin asirin da juzairat ba tayiwa
mahaifiyata ba akan kada tasamu ciki gami da
kulle kulle da makirce makirce na zahiri amma
duk butaka bata biya ba::
Kai sai da takai ta kawo juzairat tana nuna
kiyayyerta ga samun juna biyun mahaifiyata a
filin har maifina ya fahimta amma bai taba
nuna mata damuwarsa ba sbd tsananin son da
yake mata:
Lokacin da na isa shekara ba kwai a duniya
lavarin tsananin kyawuna ya bazi ko ina a
nahiyar ya zamana cewa tun a sannan ya yan
sarakai da yan mayan attajirai sun fara zuwa
neman aurena sai hankalin juzairat ya
dugunzuma ainun kuma ta tsaneni fiye da
komai:
A wannan lokaci tsufa ya fara riskar mahaifina
kuma gashi kullum yana cikin fama da lalura ta
rashin lafiya iri iri:
gaba daya likitocin mahaifina sun kasa gane
abinda ke damunsa don haka suka daina bashi
magani aka rinka kiran bokaye kowa yana yin
iya bakin kokarinsa amma babu sauki::
A wannan lokacin na shaku da mahaifina ainun
fiye da yadda na shaku da mahaiyata domin
dare Darana bana yarda na nisanra dashi sau
tari sai bayan nayi barci akan kirjinsa sannan
mahaifiyata take zuwa ta daukeni ta tafi dani
izuwa kan gadonta ta shimfideni::
Page 105
Wani dare wanda shine daren mummunan
bakin ciki a Tarihin rayuwata wato daren da ba
zan taba mancewa dashi ba:
Ina kwance akan gado MAHaifina muna ta
wasa dariya sai ciwo ya taso asa har ya mike
zaune da kyar ya zama tari har da aman jini::
Al amarin da ya dugunzuma hankalina kenan
na fara kuka kuma na yunkura da nufin naje na
kirawo mahaifiyata amma sai mahaifina ya yi
wuf ya riko hannuna a lokacin da shima ya
kama zubar da hawaye::
Cikin karfin hali yadubeni yace yake yata kiyi
sani cewa bakin alkalami ya riga ya bushe
mutuwa zanyi kuma yanzu nan ba dadewa ba:
Koda jin wanna batu sai na cika da tsananin
mamaki na kasa tambayarsa dalilin da yasa ya
fadi haka:
Mahaifi nawa ya kankameni a kirjinsa ya
fashe da matsananincin kuka har izuwa lokaci
mai tsawo::
Daga can sai ya janyeni daga jikinsa muka
fuskacin juna yace yake yata ki saurara da kyau
kiji abinda zan gaya miki::
Kinga wannan rashin lapiya da na dade a
kwance ina fama da ita ba wani bane yasa mini
ita ba face yar uwata juzairat::
koda jin wanna batu sai idanuna suka zazzaro
jikina ya kama tsuma sbd tsananin mamaki da
tsoro:::
Page 106
mahaifina yacigaba da cewa juzairat tayi mini
asiri ne ta hanyar amfani da wani azzaluin aljani
wai shi Raugatul Aguwanu::
Duk mutumin da wannan aljani ya shafa har
abada ba zai warke ba daga cuta sai dai ajali::
aljani Raugatul Aguwanu bai amince zai yi
wannan mummunan aiki ba sai bisa sharadin
cewa za a mallaka masa ke kyauta domin
kyawunki:
ina tabbatar miki da cewa nan da cikar sa a uku
zan mutum kuma junaizar da aljani Raugatul
Aguwanu suna nan suna jiran cikar wannan
lokaci domin juzairat ta sami damar hawa
karagata ta mulki shi kuma aljani Raugatul
Aguwanu ya sami damar daukeki ya tafi dake
izuwa can wani sihirtaccen daji wanda baya
shiguwa inda zai tsareki:
Na san zakiyi mamaki bisa yadda akayi nasan
duk wannan al amari to na sani ne ta hanyar
wanin shahararren bokon boka wanda yazo ya
dubani::
Hatta lokacin da juzairat ta gana da aljani
Raugatul Aguwanu sai da yanuna mini a cikin
madubin tsafinsa kuma ya tabbatar mini da
cewar bakin alkalami ya bushe babu wani
magani da zai iya bani na sha na warke daga
wannan ciwo::
Koda na ji haka sai na fashe da kuka na dubi
bokan nace yakai wannan boka kayi sani cewa
ina yin wannan kuka ne ba don zan mutum ba
ko don bakin cikin abinda yar uwata taui mini
kawai inayi ne sbda zan mutu na bar yata
gimbiya shalbirat::
Page 107
Ina mai rokanka da ka bani taimkon da zan iya
kunbutar da rayuwar yata da mahaifiyata a
bayan raina koda kuwa zasu gudu sukama
wata nahiyar su cigaba da sabuwar rayuwa::
koda nazo nan a zancena sai boka yakamu da
tsananin tausayina Har hawaye ya zubo masa
sannan ya dora hannunsa a cikin aljihu ya
dauko wani lailayayen dutse ya miko mini na
karba sannan yace ka boye wannan dutse sai
nan da Kwanaki casa in: a daren kwana na
casa in dinne zaka mutu a lokacin dare ya raba
tsakiya:
Lallai kafin cikar wannan lokaci ka damkawa
yarka wannan dutse dana baka yanzu sannan
ka umarceta da taje ta janye mahaifuarta a cikin
wannan dare su sulale daga cikin birnin nana:
idan har wannan dutse yana hannin yarka
shalbirat kuwa tana tare da mahairyarta babu
wani tsautsayi da zai samesu har sun fice daga
wannan nahiya:
koda bokan yazo nan a jawaabinsa sai na
kamu da tsananin farinciki:
duk da cewar a kwance nake cikin jin radadin
ciwo sai dana yunkura na mike zaune da kyar
na kama yi masa gdya:
kafin na kirawo hadimina nasa a baiwa bokan
lada tuni ya bace bat:
Ya nanemeshi sama da kasa ya rasa:
Nan take na boye wannan farin dutse a cikin
aljihun wandona bantaba yarda ani ya ganshi
ba duk dacewar ina cikin halim cuta::
Page 108
daga wannan rana kullum sai yar uwata
Juzairat tazo turakata ta zauna sai ta sani a
gaba ta na ta kuka tana nuna matukar bakin
cikina bisa lalura da nake ciki:::::::::::
daga wannan rana kullum sai yar uwata
Juzairat tazo turakata ta zauna sai ta sani a
gaba ta na ta kuka tana nuna matukar bakin
cikina bisa lalura da nake ciki:::::::::::
Dai dai rana daya ban taba nuna mata cewa
nasan kaidin data kulla mini ba:
Sai dai kawai idan na kalleta na zubar da
hawaye takaici:
ba komai ne yasa nake zubar da hawayen
takaici ba face nayi matukar mamaki bisa
yadda wacce nake kauna fiye da komai a
duniya ita ce take son ganin mutuwata:
Har izuwa wannan lokacin da nasan cewa ita
ce ta samini wannan ciwo ban ji na tsaneta
cikin zuciyata ba sbda tun muna yara kanana
na taso da tsananin sonta:
A dalilinta nayi yake yake ba adadi:
Na bata da abkaina sarakai wadanda suka
kasance aminena sbda sun nemi aurenta basu
samuba:
hakan ta faru ne sbda na bata damar tazabawa
kanta miji: Muna yara juzairat ta taba taka dan
aljani suka shafeta:
A kokarin samo mata magani sai dana bar gida
na shekara hudu a cikn daji har na kusan rasa
rayuwata domin da na dawo gida sai da na
shekara guda akwance ina jinya::
kuma an bata maganin da nakawo take ta
warke daga cutar mutuwarrabin jiki::
Yau gashi an wayi gari Juzairat suk ta manta
da wannan wahalar da na sha a dalilinta wai ita
ce ma take neman rayuwata sbda kawai
kwadayin mulki kuma har takeson ta sabauta
iyalina:
Page 109
yake yata yanzu zan baki wanan fari dutsen
wanda boka ya bani:
Da zarar kin karbeshi sai ki ruga izuwa dakin
mahaifiyarki ki labarta ma duk abinda na gaya
miki yanzu domin ku gudu:
Koda gama fadin hakan sai sarki ya zura
hannunsa acikin aljihun wando ya dauko
wannan farin dutsen ya miko mini:
HANNUNAna karkarwa kuma ina kuka na karbi
dutsen sannan na fada kan kirjinsa na
kankameshi ina mai sake fashe wa da
matsaicin kuka ina cewa ba zan iya rabuwa da
kai ba ya kai abbana gwara na tsaya aljani ya
kamani ya kaini inda bazan sake ganin komai
da kowa ba har izuwa ranar ajalina tunda dai
kaima mutuwa zakayi::
koda jin haka sai hankalina ya dungunzuma ya
shiga rarrashina yana bani baki:
sai da na shafe sa a biyu ina kankame da shi
ina kuka da kyar ya shawo kaina na amince na
sauka daga kan kadon rike da wannan farun
dutsen na sihiri a hannuna ina waugensa ina
zubar da hawaye shima yana daga mini hannun
hawaye na kwararowa daga cikin idanunsa:
INA ZIDANE RANAR SAI DANAYI HAWAYE
SOSAI::
Haka dai na daure na fice daga cikin turakar na
ruga izuwa turakar mahaifiyata a cikin wannan
dare:
Duk inda na gifta a cikin gidan sai naga
dakaru suna bina da kallo cikin mamaki::
Page 110
Haka dai na cigaba da gudu har na isa cikin
turkar mahaifiyata na kunnan kai izuwa cikin
turakarta:
Ina shiga sai na iske mahaifiyar tawa zaune a
gefen gado idanunta cike da hawaye kuma ko
kadan babu alamar tayi barci a kwayar
idanunta:
Al amarin da yai matukar bani mamaki kenan
na karasa gareta jikina a sanyaye:
HAR NA BUDI baki zan yi mata bayanin abinda
ke tafe dani sai ta rigani tace duk abin da ya
faru yanzu tsakaninki da m Amahaiki naji kua
na ganin domin ina labe a kofar dakin ina
kallonku baku sani ba::
Yake yata kiyi sani cewa zuciyarta ta karaya
domin nasan cewa abi ne mawuyaci mu tsira
daga sharrin Juzairat:
Ni kam na zabi na mutu tare da mijina yau a
cikin wannan dare nan da cikar sa a guda
inyaso ke ki tserar da kanki::
koda jin wannan batu sai na fada kan kirjin
mahaifiyata na fashe da sabon kuka ina mai
cewa ai kuwa sai dai nima na tsaya na mutu
tare da ku din da dai na tafi wata nahiyar daban
na zauna inda ban ssan kowa ba ba a sannani
ba inda babu uwa kuma babu uba:
Hakika rayuwar da babu masoyi ai ba ta da
wani amfani a doron kasa::::::::
Page 110
koda mahaifiyata taji wannan batu sai ta mike
tsaye zumbur cikin firgici ta sureni da gudu
muka fito daga cikin turkarta:
Nan fa ta direni kasa ta kamo hannuna ta jani
muka cigaba da gudu muka nudi kofar fita
daga cikin gidan sarautar gaba daya:
Har a sannan ina rike da wannan farin
mulmullen dutse na sihiri wanda mahaifina ya
bani:
muka cikin gudun ne muka jiyo alamar wata
irin gagarumar iska ta biyomu a baya tana
kokarin cafkomu amma ta kasa:
Sai da ya rage saura bai fi taku biyar ba
tsakaninmu da bakin kofar wacce tuni masu
gadi sun firgice sun budeta suma sun cika
wandunansu da iska sun yi waje:
Kawai sai muka ji wani irin gurnani mai
tsananin ban tsoro a bayanmu:
page 111
Cikin tsananin firgita ni da mahaifiyata muka
waiga baya ai kuwa sai muka yi arba da aljani
Raugatul Aguwanu:
Nan takemuka razana ainun:
Faruwar hakan ce tasa nayi tuntube na fadu
kasa:
ina faduwa sai wannan dutse dake tafin
hannuna ya subuce ya gangare kasa can
gabana:
kafin na mike ba ruga inda dutsen yake sai
kawai naji an figeni anyi sama dani ana ta
kyalkyala wata dariya mugunta:
Abinda idanuna kawai suka iya hangowa sa
adda na kallo kasa shine: Haukacewar
mahaifiyata tana ihu tana cisge gashin kanta
kuma tana sambatu:
Page112
Daga nan sai jinayi an lulaka dani izuwa can
kololuwar samaniya a sannan ne jiri ya debeni:
Lokacin fa na farka na bude idanuna sai na
tsinci kaina a cikin wannan dan karamin keji da
ke rataye a saman kogon aljani RAUGATUL
AGAWANU:
a firgice na mike tsaye na kama kai kawo cikin
kejin: a sanan ne na gane cewa an asirceni na
zama yar mitsitsiya:
Nan take na kwarara uban ihu kuma na fashe
da matsanaicin kuka:
lokacin da Gimbiya Shalbirat ta zonan a
Labarinta sai hawaye ya zubo mata ta dubi
sadusa Halyal tace wannan shine labarina don
haka ni na sancewa anan dajin zan gama
rayuwata tunda ba zaku iya kubutar dani ba
daga hannun wanan azzalumin aljani kuma ko
dama kin kubutar dani bani da sauran sha awar
cigaba da rayuwa tuda bani da sauran masoyi a
doron kasa:
Koda jin wannan batu sai tausayin shalbirat
takama boka sadusa da dansa halyal har
idanun su suka ciko da kwallah:
kawai sai halyal ya dube shalbiyat yace yake
wannan ma abociyar kyawu kayi sani cewa
baki databbacin cewa mahaifiyarki tana raye ko
ta mutu?
Saboda haka bai kamata ki cire sha awar ci
gaba da rayiwa b a doron kasa:
Page 11 3:
Suleiman zidane kd:
bayan haka ina mai tabbatar miki dacewa
mahaifina da muke tare da shi a yanzu zai iya
kubutar dake daga hannun wannan aljani kua
na yi miki alkwari komai dadewa sai na rakaki
har izuwa birninku kin sadu da mahaifiyarki
muddin tana raye:
Haka kuma indai juzairat na nan a raye sai kin
dauki fansa akanta:
Sa adda Gimbiya Shalbiraat taji wannan bau sai
ta girgiza kai tace wannan albishir naka daidai
yake da tatsuniya a cikin kunnena ko kumma
na kirashi da mafaarki da va zai taba zama
gaskiya ba:
Koda jin haka sai boka sadusa yayi dariya
sannan ya dubi shalbirat yace ke yarinya
abinda dana yafada miki gaskiyane amma bari
na fara nuna miki karfin aikina tun daga yanzu::
Gama fadin hakan ke da wuya sai sadusa ya
karanta wadansu dalasiman tsafi guda bakwai
ya tofa akan tafin hannunsa na hagu sannan ya
dafa kan shalbirat::
Nan take Shalbirat ta dawo cikakkiyar surarta ta
budurwa mai tsananin kyauwun diri da sura
maimakon yadda ta kasance a da yar mitsitsiya:
Shi kansa sadusa sai daya dimauce bisa ganin
tsananin kyawun nata:
Yayin da shalbirat taga ta dawo izuwa
chakkiyar surarta ta mutum sai ta cika da
tsananin farin ciki ta kama kyakyal dariya kamar
bazata daina ba::
Page 114:
sai daga can ta nutsu ta dubi boka sadusa ta
durkusa har kasa bisa guiwoyinta takama yi
masa gdya shi kuma sai ya kama kafadunta ya
yasheta tsaye suka fuskacin juna yana mai yi
mata murmushi yace wannan taimako dana yi
miki ba komai bane face taimakon kaina domin
kema akwai muhimmiyar rawa da zaki taka nan
gaba bisa bukatar da ta fito damu daga
birninmu::
A gobe ne zan rabaki da wannnan daji kuma
idan mun isa can bakin kogin bahar sufiya za ki
rabu da wannan azzalumin aljani har abada:
yanzu sai kuzo mu cigaba da yawatawa a cikin
wannan daji har izuwa lokacin da aljani
Raugatul Aguwanu ya bukata:
Koda gama fadin haka sai boka sadusa ya
kunna kai izuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login