Showing 3001 words to 6000 words out of 71576 words
Chapter 2 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt
da
mahaifinsa tazo.
Bayan sarki dujalu ya gama kururwar murna
gami da dariyar faran ciki sai ya dubi Rijiju
sannan ya dubi inmal yace, ku kadai ne kuka
rage baku dauki tsakuwoyin kuba don haka
dole dai baku da sauyin abkin gwami don
haka ba sai kun sa hannun a cikin wannan
kuttaba.
Yanzu mu bi ka idar wanan fafatawa domin
a fara.
Gama fadin hakan ke da wuya sai sarki
dujalu Matinu da Ratinu suka hada baki suka
yi rantsuwa da Girman Gunki da suke
bautawa cewar baza suyi amfani da karfin
tsafi ba ko yaudara a cikin wannan gumurzu
da za ayi face tsagwaron karfin dantsen su
da kwarewarsu ta yaki.
Koda gama fadin hakan sai suma su inmal
su ka hada baki suka yi irin rantsuwar da su
dujalu sukayi suna kammalawa ne Matinu da
Barde Kurshm na zare takubbansu suka
buda suna masu kallon juna cikin nazari
sannan kuma sai suka fara zagaya gama da
dan uwansa cikin kankanin lokaci.
Lokaci guda gaba dayansu suka yi kururuwa
uku ruga kan juna suka kacame da
azababben yki suna masu kaiwa junansu
sara da suka cikin tsananin zafin nama
juriya da jarumtaka kowannensu na kokarin
yiwa dayan farat daya.
Bisa mamaki sai aka ga duk suna amfani da
da salon fada iri daya kuma sai gashi sun
kasa cutar da juna.
Haka dai suka ci gaba da fafatawa har izuwa
tsawon dakika dari uku da tamanin amma
babu yanda ya sami nasarar koda
kwarzanar jikin dan uwansa.
Hatta kaifin takubbansu sai da ya fara
dusashewa sbda yawan goguwa da juna da kansu suka ja da baya suka yi cirko cirko
suna haki kamar zakaru sbda gajiya gami da
mamakin yadda aka yi salon fadan
Nasu yazo iri daya.
A bangare sauran dakarun yaki kuwa
kowannen bangare sun zuba idanu ne suna
kallo cikin fargaba gami da zakuwar sin
ganin nasu ne ya sami nasara.
Bayan Matinu da barde Kursham sun samu
hutu na tsawon yan dakiku sai kowanensu
ya yar da takobin hannunsa.
Matinu ya zare wadansu gajerun adduna
guda biyu dake kuibin cinyoyinsa a cikin
kufe shi kuma Barde Kursham sai ya zare
wata sharbebiyar wuka wacce tsawonta bai
wuce kamu biyu ba amma tana da fadi gami
da tsananin kaifi sannan ya kuya ya dubi
jama,ar runfunarsa dake baya yana mai
daga hannu.
Nan take wani badakare ya rugo ya kawo
masa garkuwa ya riketa da hannun hagu.
.
Yana karba garkuwar sai ya fuskanci matinu
suka rugo da gudu izuwa kan juna.
Ya yin da yarage saura baifi taku hudu ba
sai kowannensu ya daka tsalle sama suka
kaiwa juna mugun hari.
Cikin sa.a Matinu ya dankarawa barde
kursham sara a kan kafada.
Shim kuma kursham ya sokeshi da wannan
wuka a tsakiyar kirjinsa har sai da wukar ta
bullo ta gadon bayansa.
Duk su biyun suka tsanfara uban ihu a
lokacin da jijiyar kafadar barde Kursgam ta
tsinke jini ya kama tsartuwa a sama.
Shi kuwa matinu jini ne ya kama bulbulowa
ta cikin ramin da wukar ta yi a kirjinsa
wanda inda za a tara yar kwatarniya sai ta
cika fal da jini.
Nan take du su biyun suka kama mata gun
gun a tsaye har sai dasuka sulale kasa suka
kama shure shure.
Idan suka yunkura kamar zasu iya mikewa
sai kaga sun sake bajewa.
A haka dai duk su biyun suka zama gawa.
Koda ganin wanan al mari sai kowane
bangare sukakamu da tsananin bakin ciki
sakamakon RAGAS da akayi.
Har sarki yaji ya yunkura zai tari sarki dujalu
sai shi sarki dujalu ya nole yace ai ni da kai
manyan giwaye ne mu bari mu ga yadda
fadan kananun giwaye zai kasance sannan
muyi namu a karshe...
Manyan giwaye ne mu bari mu ga yadda
fadan kananun giwaye zai kasance sannan
muyi namu a karshe...
Ba tare da gardamar komai ba Hibru ya ja da
baya ya dubi inmal.
Kawai sai inmal ya tunkari abkin gwaminsa
Ratiju ba tare da ya zare takobinsa ba.
Koda Ratiju ya ga inmal ya durfafoshi babu
makami sai ya cika da tsananin farin ciki
sbda tunanin cewa ya sami babbar da mar
da zai yi masa kwaf daya.
Cikin hanzari Ratiju ya zare takobinsa ya
falfala da azababben gudu izuwa kan inmal
yana kwarara ihu mai tsananin firgitarwa
wanda ka iya tarwatsa gungu dakaru a filin
fama.
Zan ci gaba.
Da fatan an tashi lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp.
MAZAN JIYA
Littafi na hudu (4)
Part C
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
Ko gezau inmal bai yiba yaci gaba da
tunkarasa batare da yazare takobinsa ba
daga cikin kufeta.
Ai kuwa suna haduwa sai ratiju ya kawowa
inmal wani irin mugun wawan sara a wuya
da dukkan karfinsa cikin bakin zafin nama
inamal ya sunkuya domin ya kauce saran
amma dukk da haka sai da kaifin takobin
ratiju ya shaftare saman kunne inmal ya
yanke rabin gashin kansa sai ga jini na diga
daga kunnen inmla a yayin da aka sami yar
taraza a tsakaninsu.
Kofa inmal ya shafa kunnensa ya ji jini kuma
ya ga rabin gashin kansa a kas sai ya fusata
ainun zuciyarsa ta kama tarfafasa kamar
zata kone.
Shi kuwa ratiju sai ya kama dariyar keta da
murna yna ganin cewa idan aka sake
gamuwa fara daya zai gama fa inmal.
Batare da inmal ya zare takobin tasa ba sai
ya sake durfafar ratiju al.amarin da yai
matukar dugunzuma hankalin sarki Maharaz
ke nan.
Har Hibru ya fara kwalawa inma kira yana yi
masa tsawa akan ya zare takobinsa kafin su
hadu da ratiju.
Inmal yayi kamar bai ji umarunin Hibru ba ya
ci gaba da tunkarar ratiju a hakan.
Ita kuwa Gimbiya mulaifa wacce ke tsaye
acan gefe daya tana kallon abin da faruwa
tuni ta fara kuka tun sa,adda ta ga an
rutsure rabbin gashin kan inmal kuma anyi
masa rauni a kunne.
Sarki dujalu kuwa dariya yake ta kyalkyalawa
yana yiwa ratiju kirari gami da kara masa
kwarin guiwa.
Dama sadaiki ratiju ya fi Matinu karfin
dantse da zafin nama shi kansa sarki dujalu
idan suna yar gwajin jarumtaka shi da ratiju
sai yayi da gaske yake samun nasara akansa
don haka a yanzu yana kyautata zato cewa
ratiju zai iya hallaka inmal duk da cewa yayi
yaki da inmal ya ga irin tsananin tasa
jarumtakar.
Koda ratiju da inmal suka sake haduwa a
kari na biyu, sai ratiju ya kawowa inmak
muguwar suka a ciki.
Kawai sai inmal ya tare tsinin takobin da
tafin hannayensa biyu.
Nan fa ratiju ya fara danno takobin da
dukkan karfinsa domin ya huda cikin inmal.
Wohoho! Mai karfi sai allah ya isa! Nan fa
tsagwaron karfin dantse ya fara amfani sai
gashi duk su biyun kwanjin jikinsu ya
kumbura jijiyoyinsu suka tashi suka yi
burdin burdin.
A lokacin guda duk su biyun sai ga gumi na
karyi musu. Shi dai Ratiju ya kasa dannan
tsinin takobin ta shige izuwa cikin inmal.
Shi kuma inmal ya kasa kautar
da takobin daga saitin cikinsa.
Tsawon komanin dakika dari da sittin suna
tsaye kikam a hakan kowannensu yana jin
jiki har kaifin takobin ta Ratiju ya fara
yankar tafin hannun inmal jimi ya fara diga.
Kwatsam! Sai inmal ya kwarara uban ihu ya
daga takobin da shi kansa ratiju sama yai
wurgi da su.
Tamkar an cilla hoge sama hakan ratiju da
takobin suka luluka sama suka watse a
saman.
Kafin ratiju ya fado kasa inmal ya daka tsalle
sama ya taresahi kawai sai ya kama kansa
da hannu biyu ya murde masa wuya.
Sai gashi inmal ya duro kasa bisa kan turba
rungume da gawar tatiju.
Nan take yi jifa da gawar tamkar tsummam,
ya mike tsaye yana mai karkade jurar jikinsa.
Ai kuwa su sarki Maharaz basu san saadda
suka kaure da shewar farinciki ba suka
kama yiwa inmal kirari gami da jinjina bisa
wannan gagarumar jarumtaka da yayi.
Shi kuwa sarki dujalu da jama.arsa kamewa
suka yi kamar gumaka sbda mamaki da
bakin ciki. Nan take hawaye takaici ya
zuvowa sarki dujalu sbda ya san cewa yayi
asarar babban mayakinsa wanda bashi da
kamarsa.
Bayan sarki dujalu ya gama alhinin mutuwar
ratuju izuwa tsawon yan dakiku sai ya tako
kafafunsa yazo tsakiyar filin dagar ya tsaya
sannan ya xare wadansu manyan takubba
guda biyu dake soke a gadon bayansa ya
fuskanci sarki yaki Hibru.
Adaidai wannan lokacin ne hankalin inmal
da na Sarki Maharaz ya dugunzuma ainun
suka ji kamar su rike Hibru su hanashi tarar
sarki dujalu.
Kawai sai suka ga shima Hibru ya zare nasa
takubban guda biyu ya yunkura zai tunkari
sarki dujalu.
A guje inmal yasha gaban Hibru ya dubeshi
cikin tsananin damuwa yace yakai abbana
ka bani dama na karbeka a wannan
gumurzu ni na fafata da sarki dujalu.
Koda jin wnan batu sai Hibru ya yi
murmushi yace yakai dana kayi sani cewa ai
bakin alkalami ya riga ta bushe.
Tun da har muka yi rantsuwa da girman
ubangikinmu Darbuza babu gudu kuma
babu ja da baya.
Kamar yadda na zuba ido ka yina ka
gumurzu har kasami nasara hakan kaima
zaka zuba ido ka kalli nawa.
YAU ne ranar da zan san iyakar jarumtakata
kuma ka sani cewa ko kashe ni aka yi zan mutu
ne a cikin alfharin kare kasata gami da
martabar sarautar abkna aminina:
alfarma daya nake nema a wajenka; duk wuya
duk rintsi karka bari gimbiya Mulaifa ta rasa
rayuwarta kuma in dai kayi tsawon rai ka aureta
ku koma birninmu ku karasa rayuwarku ta
duniya:
koda gama fadin hakan sai Hibru ya juya ya
kalli abkinsa sarki Maharaz wani kallo yayi
masa mai kama dana bankwana a cikin
murmushi mai dugunzua hankali:
Nan take sarki Maharaz ya ji hawaye ya zubo
asa kua ya ji kamar ya ruga da gudu ya rike
Hibru ya hanashi karo da sarki dujalu:
Nan take Hibru ya durfafi Sarki Dujalu shima
sarki dujalu sai ya tunkaroshi kiwannensu ya
taho a fusace acikin mugun nufi amma a
hankali suke tahowa cikin nutsuwa ba tare da
sauri ba;
sai da yarege saura baifi taku goa a tsakninsu
ba sannan suka ruga da gudu izuwa kan juna
suka ruguntsue da azababben yaki:
Wohoho! Maza maganin maza.
Hakika idan jarumtaka ta hadu da
sadaukantaka gami da naci da tsantsar juriya
dole ne gumurzun ya yi dadin kallo kuma ya
zama abin tsaro:
anfara wannan bakin artabu tsakanin sarki
dujalu da Hibru sai labri ya zaa sabo:
gaba dayan mutanen dake fili babu wanda
hankalinsa bai dugunzuma ba fiye da ko
yaushe sbo da ganin yadda jaruman biyu suke
kaiwa junansu mugayen hare hare na
musamman wanda babu mai iya yin irinsa face
tshon hannu bangaren yaki:
duk dace wa sarki dujalu yafi Hibru tsauntsar
karfin dantse amma sai gashi Hibru na iya kare
hare harensa har ma yana mai da martanin shi
kansa sarki dujalu yayi matukar mamkin yadda
hakan ta kasance domin yayi zaton cewa suna
fara gumurzu zai iya kuntatashi da karfin
dantsensa cikin kankanin lokaci amma sai
gashi labari ya sha bamban:
Nan ta suka tashi hankalin kasa kura ta turnuke
filin yakin dudufniyar kafafuwansu dakarar
haduwar makamansu suka cika dodon kunne
kaai cw mutum dubu ne suka gwamuse suke
yakin:
Sai da suka shafe sa:a uku cur! Suna wannan
dauki ba dadi tamkar jikinsu bana kashi da
tsoka bane face na karfe zallah sannan suka
gaji:
bisa dole kowannensu ya ha da baya suja yi
cirko cirko kmar zakaru suna haki gami da
kallon juna kuma kowannensu ya jike sharkaf
da zufa kamar daga cikin kogin aka tsamosu;
Abin da ya daurewa kowannensu kai kuma ya
basu haushi shine ganin yadda suka dade
suna wannan gumurzu amma dayansu bai
sami nasar koda kwarzanar jikin daya ba:
Su kansu taron rudunonin biyu dake kallon
wannan gumurzu ji suka yi kamar da can ruwan
masifa ake zubowa daga sama amma da
jaruman sua daina yakin sai suka ji an dauke
ruwan masifar:
Sai da sarki dujalu da Hibru suka shefe tsawon
dakika dari biyar da arba:in suna haki da
hararar juna kuma kowannensu na tunanin irin
salon da ya kaata ya sauya domin ya sai
nasara:
kamar hadin baki sai aka Ga duk su biyun sun
taso da gudu a lokaci guda sun durfafi juna:
gudu ne na bala i tamkar zasu tashi sama
kuma kowannensu da dukkan karfinsa ya taho
cikin mugun nufi:
maimakon su daka tsalle sama su yi mugun
gamo a kasan kowanensu ya kaiwa dan
uwansa mumunnan hari:
sai ga shi kowannensu ya wuce dan uwansa
amma sai duk suka sulale kasa bisa
guiwoyinsu suka kame kamar gumaka:
Al:amarin da ya razana kowa kenan a wajen
gashi dai dukkanninsu sun rankwafar da
kawunansu kas ama basa motsi tamka babu
mai rai acikinsu, daga can sai aka ga jini na malalowa kasa daga
jikin hannun daman sarki dujalu kuma yana rike
da hannun:
shi kuwa Hibru sai aka ga jini na malalowa ta
kuibin cikinsa:
jim kadan sai hannun daan na sarki dujalu ya
gutsure ya fado kasa shima ya sulale kasa
sumame:
shi kuwa Hibru sai ya bingire kasa ya kaa shure
shuren mutuwa;
cikin tsananin dimauta sarki maharaz da inmal
suka ruga izuwa kan Hibru:
tun daga nesa suka fara rasu ihu suka fashe
da kuka:
a bangare sarki dujalu kuwa dakarunsa ne suka
rugo da gudu suka daukeshi yana cikin halin
suman suka ruga dashi izuwa can cikin
sansaninsu:
lokacin da inmal da sarki Maharaz suka iso kan
Hibru yana takakarin mutuwa sai suka durkusa
a gabansa suka sake fashewa da matsanaicin
kuka sbda sun lura da raunin dake kuibin cikin
nasa sun ga yayi rami zururu babu yadda za ayi
ya rayu:
hannun Hibru na karkarwa ya kamo hannun
sarki Maharaz ya dora bisa kirjinsa suka
kurawa juna idanu, cikin matukar karfin hali Hibru ya dudi baki da
kyar yace yakai abkna yau fa ranar rabuwarmu
ta zo:
Tabbas mutuwa zan yi yanzu ba zan tashi ba:
ina alfahari da wannan mutuwa tawa domin na
mutu ne a filin daga bisa kare kasata da
mutuncika:
sannan ina alfahari da cewar na sarewa sarki
dujalu hannun daya har ya bar duniya ba zai
taba mantawa da niba na cusa masa bakin
cikin da zai tafi da shi har kabarinsa:
koda Hibru yazo nan a znacesa sai sarki
Maharaz ya tasoshi zauna ya rungumeshi yana
mai fashewa da sabon kuku yace yakai
masoyina babban amina saboda me zaka tafi
kabarni a cikin wannan duniya wacce baya da
dadin zama idan babu masoyi?
Ka sani cewa in banda yata ba mulaifa bani da
kowa sai kai gashi zaka mutu a dai dai lokacin
da zan samu duniya na yi aka sakayya bisa
bautar da kayi mini a baya gai da nuna tsantsar
so da kauna:
ai kuwa tun da har tafiya zaka yi nia ina mai
rokin darbuza da ya gaggauta dauke....
Kafin sarki Maharaz ya gama rufe bakinsa sai
HIBRU yarufe asa baki da tafin hannunsa yace
idan kaima ka tafi waye zai ga auren yayanmu
kenan? Ya kai masoyina komai RINTSI DA
TSANANI Lallai ka rayu a wannan yaki koda
kuwa bamu samu nasara mallakar Takobin
Saiful Lujara ba:
burina kawai shine kai da inmal da gimbiya
mulaifa ku koma gida a raye:
Saadda Hibru yazo nan a zncensa sai sarki
maharaz yasake fashewa da kuka yace yakai
masoyina kayi sani cewa bakin alkalami ya
bushe domin kafin mu baro gida mai girma
Darbuza ya tabbatar Mini dacewa mutum hudu
ne kacal zasu tsira a wannan filin yaki kuma
mutum biyu daga cikinmu:
kaga kenan a tsakanin ni inmal da mulaifa dole
ne dayanmu ya mutu:
koda jin wannan batu Sai Hibru ta ci gaba da
kakarin mutuwa da zafi;
Al amarin da ya dimauta su inmal kenan:
inmal yai sauri ya karbi Hibru daha hannu sarki
maharaz ya rungumeshi a kirjinsa yana mai
tsala ihun bakin ciki sa;adda hawaye ke ta
kwararowa daga cikin idanunsa:
a sannan ne Hibru ya dan dawo cikin
hakanlinsa ka dan ya dubi inmal yayi masa
murmushi karfin hali yace yakai dana ka zamo
mai juriya bisa rashina:
ina mai fari ciki kasancewar zan mutu akan
tafin hannunka kamar yadda mahaifin ya mutu
akan tafin hannuna kuma a filin yaki:
kaima ina maka fatan mutuwa irin ta manya
mazaje a karshen rayuwarka:
ina fatan baza ka manta da wasiyyata ba akan
masoyiyarka mulaifa:
a wannan lokaci mulaifa na can nesa da su
kadan tana faman rusa kuka ta kasa karosowa
inda suke:::
Zan ci gaba.
Da fatan an tashi lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp.
MAZAN JIYA
Littafi na hudu (4)
Part D
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
hibru ya juyar da kansa ya dubi inda mulaifa
take tsaye a lokacin da idanunsa ke ganinta
dishi dishi sannan ya waigo ya dubi inmal yayi
masa kallon karshe:
a hakan idanunsa suka kafe yana yiwa inmal
murmushi; kuma gaba dayan jikinsa ya
sandare:
inmal bais san cewa Hibru ya mutu ba sai daya
lura da cewa idanunsa sun daina kiftawa:
koda ya fahimci hakan sai ya tsandara uban
ihu wanda ya firgita komai da kowa ke cikin
dajin:
nan take shi da sarki maharaz suka kankame
gawar hibru a jinsu suna masu fashewa da
matsainincin kuka:
a sanna ne itaama gimbiya ta rugo sa gudu ta
fada kan gawar Hibru ta tayasu kukan:
* * *
Al amarin sarki dujalu kuwa lokacin da darunsa
suka daukeshi da gudu suka tafi dashi izuwa
cikin sansaninsu sai aka wuce da shi izuwa
cikin tintinsa aka kwantar da shi akan
shimfidarsa:
nan fa likitansa ya shiga aiki:
bayan ya tsaida jinin dake zuba a gundulmin
hannunsa sai ya samasa magani sannan ya
lulluceshi iya kirji da mayafi kowa ya fice daga
cikin tanti aka bar sarki dujalu shi kadai har a
sanna bai farfado daga dogon suman da yayi
ba amma akwai alamar fitar numfashinsa
kadan kadan:
sarki dujalu bai farfado ba sai bayan saa biyu
sa rabi :
koda ya bude idanunsa ya tsinci kansa a cikin
tantinsa a kwance sai ya cika da tsananin
mamaki domin shi a zatonsa ya mutu a filin
yaki:
sarki dujalu ya yunkura domin ya yaye
mayafinsa da aka lullbeshi da hannunsa na
dama kawai sai yaji kamar bashi da hannun
gaba daya:
cikin tsananin firgici ya sa daya hannun nasa
na hagu ya yaye mayafin take yayi arba da
hannunsa na dama ya ga yazama gungulmi:
sarki dujalu ya takarkare ya kwarara mugun ihu
mai tsananin karfi gami da amsa kuwwa izuwa
cikin dajin gaba daya: kai hataa dabbobi da
aljanun dake rayuwa a cikin karkashin teku
bahar Sufuya sai da wannan ihu na sarki dujalu
ya eazansu:
bayan yayi ihu kuma sai ya fashe dd matsanaici
kukan vakin ciki domin wanan shine karo na
farko da Taba yi masa rauni a filin yaki a iya
tsawon rayuwarsa duk da cewar ya halarci
yakukuwa sama da guda dari a
rayuwarsa:::::::::::::::::::
kuma tunda uwarsa ta haifeshi bai taba zubar
da hawayen takaici ba sai yau:
cikin wannan hali ne shugaban Dakarunsa na
jinsin Aljanu wanda ake kira BARUZUL
MADWAN yashigo cikin tantin ya zube kasa ya
kwashi gaisuwa yace Ya shugabana yanzu
mene ne abin yi tsakaninmu da su waye zai
sami damar shiga cikin wannan kogi na Bahar
Sufiya don dauko Takobin saiful Lujara
tsakanin mu da su; tunda anyi yarjejeniya bisa
cewar wadanda suka yi nasara a yakin mutum
uku uku sune zasu dauko takobin kuma gashi
yanzu kamar RAGAS akayi tunda kai suma kayi
a filin yakin shi kuma Hibru mutuwa yayi:
Page 33
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lulube
sarki dujalu bisa jin cewar yasamin nasarar
kashe Hibru amma kuma da ya dubi gundulmi
hannunsa sai ya sake kamuwa da tsananin
bakin ciki:
Tsawon tan dakiku sarki dujalu yana tunani bai
baiwa aljani barzul madwan amsar tambayarsa
ba sai daga can ya dago kai ya dubeshi yace ya
kai shugaban dakarun aljanu kayi sani cewa a
halin yanzu yarjejeniyar da ke tsakaninmu da su
sarki maharaz ta rushe wannan yaki ya zama
danye don haka za ayi hutu na tsawon kwna
uku domin na baiwa avkan gabamu damar da
zasu sami saukin dacin rashin da suka yina
babban masoyinsu:
dalilina anan shine abin kunya ne a gareni na
yakesu a lokacin da zukatansu ke cike da rauni:
lallai na fi son na yakesu a lokacin da suke
cikin nutsuwarsu sbda haka yanzu kaje ka sa a
rubuta takarda a kaiwa abkan gaba bisa
wannan hukuci da nayanke.
Aljani barzul madwan ya risina yace angama ya
shugabana:
kawwai sai ya bace bat! Daga cikin tanti tamkar
bai taba wanzuwa ba a ciki::
* * * *
bayan su sarki Maharaz sun kwashe
gawarwakin dakarunsu mutum biyu da aka
kashe; wato gawar sarki yaki Hibru data Barde
Kursham sun koma cikin sansaninsu sai aka
shiga gidimar binne gawar:
nan fa kowa da kowa ya kama kuka