Showing 66001 words to 69000 words out of 71576 words

Chapter 23 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt

mafi rahama da jin kai akan bayinsa, lallai muna roko akan yasa mu kasance cikin bayinsa masu rabo da dacewa, gaba dayansu suka amsa da Amin.
Nan take Jarumi Imnal ya tashi ya rungume Hasnalu ya ce hakika a yau kazo mani da batu mafi dadi dana taba ji a rayuwata wanda ya jefani acikin farin cikin da bantaba ji ba a rayuwata.
Nan dai suka dunguma gaba dayansu tare da barin bakin takun Bahar sufiya suka nausa izuwa cikin daji. Jarumi Hasnalu nayi masu jagora, Imnal, sarki Maharaz, da gimbiya Hursiyya suna tafiya suna kuma waigen kabarin masoyansu suna zubar da hawaye har ya zamana cewa sun yi nisa da bakin tekun.
A daidai wannan lokacin ne jarumi Hasnalu ya fara sauri-sauri, gudu-gudu kuma yana mai karanta wasu Addu'o'i na musamman a cikin zuciyarsa, daga can sai ya waigo ya dubi su jarumi Imnal da su gimbiya Hursiyya yace kuyi koyi dani bisa dukkanin abinda kukaga na yi. Ai kuwa sun fara yin gudun da yake yi suka ga abin al'ajabi irin wanda basu taba ganiba a rayuwarsu, domin gani suke tamkar iska ce ke daukarsu sama tana tafiya da su, aikuwa nan da nan suka dinga keta dazuzzuka suna yin azababben gudu tamkar gudun tauraruwa mai wutsiya, gashi dai gudu suke amman ko kadan babu mai alamar gajiyawa a cikinsu, sannan a kiyasce suna shafe tafiyar sa'a uku cikin dakika goma kacal. Kai hakika tsananin gudun da suke yi ya wuce misali kawai Allah ne kadai ya barwa kansa sanin mizaninsa.
Wannan shine abinda ya faru da su jarumi Imnal acan bakin kogin bahar sufiya bayan an fafata yakin karshe a kokarin dauko makaman mazan jiya.

***************** *****************

Al'amarin aljani Raugatul Agwanu kuwa lokacin da ya sace wadannan kayan yaki na mazan jiya guda uku wato; Takobin Saiful Lujara, mashin galilur haras da kuma hular lamsara sai yayi sama ya luluka a cikin gajimare, kawai sai ya rataya wannan takobi ta Saiful Lujara a bayansa ya sanya hular a kansa kuma ya rike mashin a hannunsa na hagu, nan take yaji wani irin gagarumin karfi ya shige shi mara misaltuwa tamkar zai iya dakon duniyar gabadaya, kai hatta karfin gudunsa a sararin samaniya sai da ya ninka na da sau dubu.
Cikin abinda bai fi dakika biyu ba rak yaga har ya iso dajinsa na darul hushushul maut, dan haka cikin tsananin farin cikk ya sakko kasa ya kunna kai izuwa cikin wannan kogon dutsen nasa, koda ya shiga cikin kogon kawai sai ya kama kyalkkyala dariya jar da faduwa kasa kamar wanda ya zautu, haka dai aljani Raugatul Agwanu ya cigaba da wannan dariyar tamkar ba zai daina ba, haka dai ya rude kuma ya kidime yama rasa abinda zai yi daga can wata zuciyar ta ce da shi; kaje ka fara yakar manyan kasashen duniya da babu kamarsu, ka cisu da yaki su dawo karkashin mulkinka. Wata zuciyar kuma sai ta ce da shi A'a kamata yayi ka tara aljanun duniya kaf su durkusa a gabanka suyi maka sujjada domin ka zama ubanjinsu sannan kasa a gina maka masarauta irin wadda ba a taba gina kamarta ba tun daga wanzuwar duniya kawo iyanzu. A cikinta kasa a gina maka aljannar duniya a kuma kawata ta kyawawan mata na jinsin mutane da aljanu guda miliyan dubu ɗay-ɗay kuma a zuba kayan kawa na dangin su dinare, lu'u lu'u, jauhar, zubar daji da dai sauransu irin wanda ba a taba tara mai yawansu ba.
Haka dai aljani Raugatul Agwanu ya cigaba da sake-sake iri-iri a cikin zuciyarsa yana mai cike da mamakin yadda aka yi yayi wannan babbar tsuntuwar a sama alhalin shekara da shekaru manyan sarakunan aljanu da Sadauku, Bokaye na aljan dana mutane sunyi iya yinsu su mallaki kayan yakin mazan jiya amman sun kasa.
Sai da aljani Raugatul Agwanu ya shafe sama sa'a guda yana tunani gami da sakar zuciya sannan ya yanke shawarar ya fara ziyartar kaaashen aljanu ya tara sarakunansu kaf sannan ya basu umarnin bisa bukatarsa ta fara gina masa fada wacce babu kamarta.
Nan take aljani Raugatul Agwanu ya juya da nufin ya fice daga cikin wannan kogo nasa, amman bisa mamaki sai ya ji yana jin yunwa, al'amarin da ya fusata shi kenan ya ce a cikin zuciyarsa ai ya kamata ace yanzu na daina jin yunwa da kishin ruwa a rayuwata tunda na mallaki wadannan kayan yakin na mazan jiya wadanda ke dauke da sihirin da babu kamarsu a duniya. Kawai sai ya kama cin yayan itatuwa dake cikin kogon nasa har sai da yaji ya koshi gami da yin gyatsa. Sai a sannan ne ya sake juyawa a karo na biyu ya fice daga cikin kogon da nufin ya bude fuka-fukansa ya tashi sama, amman sai yayi arba da abinda ya bashi mamaki fiye da tunnainsa gami da hankalinsa, ba wani abu bane aljani Raugatul Agwanu yayi arba da shi ba face jarumi Hasnalu, su duka tsaye a bakin kogon dutsenasa tamakar dama sun dade a wajen.
Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin jarumi Hasnalu da aljani Raugatul Agwanu, alokacin da su Imnal suka rakube gefe daya sakamakon ganin kayana yakin mazan jiya fa suka yi a jikin aljani Raugatul Agwanu.
A wannan lokaci girman aljani Raugatul Agwanu da kwarjinsa ya kinka nada sau goma tamkar hurashi akayi ya kumbura, tsananin karfin sihirin kayan yakin mazan jiya ne yasa suffar tasa ta sauya gaba daya, shi kansa jarumi Hasnalu in banda yana da dakakkiyar zuciya irin ta manyan jarumai kuma yayai imani da Allah da ja zai yi da baya, domin sai fa xuciyrsa ta darsu ya tabbatar da cewa karo da wannan aljani ba karamin aiki bane, domin karfi ko kwarewar yaki ba zata ceci mutum ba.
Aljani Raugatul Agwanu ya dubi su jarumi Hasnalu ya daka masu tsawa yana mai cewa, yaku wadannan kananun kwarin maza kuyi sujjada a gareni kafin gushina ya tabbata a gareku, kuyi sani cewa ni yanzu na zama ubangijin mutane da aljanu,wanda duk bai bauta mani ba to zai zama gawa, ko kuma ya gamu da azabata mara yankewa...
Kafin aljani Raugatul Agwanu ya gama rufe bakinsa jarumi Hasnalu ya tari numfashinsa yana mai daka mashi tsawa ya ce kai tsohon mushriki kuma batacce ka sani cewa babu abun bautawa da gaskiya face ubangijin musulunci, ina mai kira a gareka daka zubar da wannan kayan yakin dake jikinka na mazan jiya, kuma ka tuba ga Allah ka karbi addinin gaskiya runda kaga yadda gaskiyar ta rinjayi karya a bakin tekun bahar suffiya, kuma kaga wannan al'amari kuru-kuru da idanunka, idan kuwa ka bujere wa wannan umarni nawa zan yankeka da taimakon ubangijina na halakaka take yanzu.
Koda jarumi Hasnalu yqzo nan a zancensa sai aljani Raugatul Agwanu ya bushe da wata mahaukaciyar dariya, wacce ta haifar da wata irin guguwa mai karfin gaske, wadda tasa bishiyoyi suka kama kakkaryewa suna zubewa kasa, ruwan korama ya kama fanjam-fanjam, iskar ta tashi su jarumi Imnal kamar zata tashi da su sama, har saida aljani Raugatul Agwanu ya tsuke bakinsa sannan komai ya lafa.
Cikin tsananin fushi aljani Raugatul Agwanu ya zare takobin Saiful Lujara tana mai yin wani irin haske gami da walwali na sihiri mai ban tsoro ya dubi jarumi Hasnalu yace yaro maza bisa kanka, sai ubangijin naka ya kareka na gani.
Kafin Jarumi Hasnalu ya zare tasa takobin tuni aljani Raugatul Agwanu ya kawo masa wawan sara fa nufin ya tsargeshi gida biyu, cikin zafin nama ya goce wa takobin Saiful Lujara, takobin ta dira akan wani katon dutse na wuta, take dutsen ya ragargaje kuma ya nike ya zama gari, fallutsuwar da ruburbushin da dutsen yayi ne gami da tsananin zafin ruburbushin da karfin karar bindigar dutsen ya zubo akan su jarumi Imnal take gaba dayansu suka zube sumammu.
Alokacin ne fa aka fara azababben yaki tsakanin aljani Raugatul Agwanu ya jarumi Hasnalu ya zama cewa sun himmatu suna kaiwa junansu sara cikin bakin zafin nama juriya da bajinta, a duk sa'ad da aljani Raugatul Agwanu ya kawo wa jarumi Hasnalu sara ko suka ya kauce tofa duk abinda ya samu walau dutse, bishiya ko kasa take abin yake narkewa kuma ya kamada wuta, babban abinda ya daure wa Raugatul Agwanu kai shine ganin yadda takobin Hasnalu bata karyeba sakamakon haduwar da tayi da takobin Saiful Lujara, alhalin dutse d bishiya ma narkewa suke yi idan takobin ta shafesu bama ta saresu ba, abinda aljani Raugatul Agwanu bai sani ba shine karfin addu'a ne yasa takobin jarumi Hasnalu ta tsira.
Shi kuwa jarumi Hasnalu duk sa'ar da takobinsa ta sari jikin aljani Agwanu sai dai yaga tartsatsin wuta yana tashi tamkar karfe ya sara, idan kuwa takobin ta sari hular lamsara sai dai kaga tsawa fa walkiya na tashi gami da wani irin mugun hayaki da yake turnuke dajin gabadaya.
Sai da suk shafe tsawon sa'a guda suna wannan bakin artabun amman babu wanda ya samu wata nasara a tsakaninsu, al'amarin daya fusata aljani Raugatul Agwanu kenan kuma yayi matukar bashi mamaki, dan haka sai ya ja da baya ya sakar wa Hasnalu mashin galilur haras, aikuwa sai mashin ya tafi da tsananin gudu yana shirin cake idonsa na hagu, koda Hasnalu ya goce sai mashin ya wuce ta saman fuskarsa ya je ya shige ta vikin wani katon dutse ya fice fit, kuma ya dawo da baya da gudu ya yo kan Hasnalu.
Nan fa Hasnalu ya cigaba da yaki da wannan mashi na galilur haras, shi kuwa aljani Raugatul Agwanu sai ya tsaya cak yana kallon bakin gumurzun da ake yi tsakanin mashin galilur haras da kuma karumi Hasnalu ma'ana ya zama dan kallo babu abinda Aljani Raugatul Agwanu yake face kyalkkyala dariyar mugunta musamman da yaga cewa mashin ya kuntata Hasnalu.
A daidai wannan lokaci ne su Imnal suka farfado daga dogon suman da suka yi, koda sukaga irin azababben yakin da ake yi tsakanin mashin galilur haras da jarumi Hasnalu sai suka cika da tsananin mamaki gami da tsoro, domin basu taba ganin makami kamar galilur haras wanda yake muguwar barna kamar haka, barnar data ragargaza dajin gabadaya, ta haddasa famtsamuwar narkakken dutse, b shiri su jarumi Imnal suka mike suka ruga da gudu izuwa can nesa kadan suka tsaya suna kallon ikon Allah, domin idan suka tsaya inda ake gumurzun narkakken ruwan dutsen ne zai dafar da su.
Sai da aka kara shafe wata sa'a guda ana gumurzu tsakanin mashin galilur haras d jarumi Hasnalu har takai cewa Hasnalu ya fara gajiya, a lokacin ne kuma mashin ya kawo wa Hasnalu mugun suka a ciki ya goce cikin matukar zafin nama, amman duk da haka sai da mashin ya huda rigarsa ya fice fit, take kuwa rigar ta kama da wuta, cikin hanzari Hasnalu ya yaga rigar tasa ya jefar fa ita, a lokacin ne kuma mashin ya kara dawowa da baya ya saito kirjinsa zai tsireshi, kawai sai su Imnal suka ga Hasnalu ya mayar da takobinsa cikin kufe kuma ya runtse idanunsa yana mai karanta wata addu'a. Al'amarin da ya firgitasu kenan, gimbiya Hursiyya ta kama kwala wa Hasnalu kira daga inda suke labe cikin dimauta tana mai ce mashi ya kauce kada mashin ya soke shi.
Ko juyowa ya dubeta Hasnalu baiyi ba, kuma sam babu alamar tsoron wannan mashin a tare da shi.
Shiko aljani Raugatul Agwanu sai ya kama kyalkyala dariyar mugunta saboda yana ganin cewa tabbas wannan karon ajalin Hasnalu ya zo, koda ya rage saura baifi kamu daya ba jal tsakanin kirjin Hasnalu da mashin galilur haras sai akaga mashin ya tsaya cak a sama, shi bai gado kasa ba kum shi bai wuce ba, a sannan ne jarumi Hasnalu ya bude idanunsa kawai sai ya dafa mashin da hannunsa na dama take mashin ya dagargaje kuma ya tarwatse yayi gutsu-gutsun kamar kwayar zarra.
Koda ganin abinda ya faru sai aljani Raugatul Agwanu ya kwarara uban ihu cikin tsananin bakin ciki har kwallar takaici ta zubo daga cikin idanunsa.
Su kuwa su sarki Maharaz koda ganin wannan nasara da Hasnalu ya samu akan mashin galilur haras sai suka kama kabbara gami da yiwa Allah godiya.
Nan fa aljani Raugatul Agwanu ya sake kwarara uban ihu a karo na biyu, sannan cikin tsananin fushi ya zare takobin Saiful Lujara ya afka wa jarumi Hasnalu da dukkan karfinsa suka sake kacamewa da azababben yaki.
Wohoho! Hakika wuya ba a sa mata rana, maza sune maganin maza, kuma tabbas karfi yana da ranarsa, haka ma kwarewa da sanin makama a yaki tana da rana. Tabbas inba dan jarumi Hasnalu ya kasance gwarzon mayaki ba wnda ya saba gwagwarmaya tare da fafatawa a cikin maza ba, kuma yana hadawa da neman tsari a wajen Allah da tuni aljani Raugatul Agwanu yayi masa kwab daya a wannan fafatawar da suka fara, amman duk da haka sai da kai cewa aljani Raugatul Agwanu ya zame masa alakakai, ya rasa ta inda zai bullo masa, shima kuma Aljani Raugatul Agwanu ya rasa hanyar da zai bi ya samu nasara a kansa, sai gashi takobin tasa ta Saiful Lujara da hular lamsara sun kasa tsinana masa komai, a haka sai da suka shafe sa'a guda suna wannan gumurzu.
Kaico! Ance gobara daga kogi maganinta sai Allah, ba shiri aljani Raugatul Agwanu ya ja da baya ya tsaya yana haki yana kum kallln jarumi Hasnalu cikin tsananin al'ajabi, domin shi a rayuwarsa ma bai taba gajiya a filin yaki ba dan yana iya kwana arba'in yana yaki a filin daga cikin tsakiyar miliyoyin abokan gaba, amman yau gashi mutum daya jal ya gagareshi kuma ya gajiyar da shi a cikin sa'a daya da rabi. Bayan anyi kallon kallo tsakanin jarumi Hasnalu da aljani Raugatul Agwanu na taawon dakika dari uku da sittin, sai nan take hadari ya gangamo aka fara wata Irin iska mai karfi amman hakan bata sa su Imnal sun bar wanen da suke labe ba, saima suka nemi mafaka suka labe, babban burinsu kawai shine suga yadda karshen wannan fada zai kasance.
Nan take kuwa aka fara yayyafi kadan-kadan yana mai sakkowa kasa, kawai sai ljani Raugatul Agwanu ya cire hular lamsara ya ajiyeta gefe guda, sannan kuma ya ajiye takobin Saiful Lujara a kusa da hular, ya tada kwanjinsa yayin da jijiyoyin jikinsa suka tashi suka yi burdin-burdin nan fa kirarsa ta sadaukantaka ta fito ainun, aiko sai ya takarkare ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa, duk da irin jarumtaka tasu Imnal sai da suka ji kamar su arce da gudu, domin babu wanda bai motsa ba harma da jan baya ba a cikinsu, duk da cewa suna can baya nesa a matsayin yan kallo.
Shikuwa Jarumi Hasnalu ko gezau bai yi ba, kawai shima sai ya gyara tsayuwa yana mai dunkule hannunsa.
Su zukatan su Imnal kuwa cike suke da mamaki har suna tambayar zukatansu cewa wai shin wacce irin dakakkiyar zuciya jarumi Hasnalu ke da ita ne, ta yaya zai tari wannan gansamemen sadaukin aljani yana matsayin biladama.
Aljani Raugatul Agwanu ya dubi jarumi Hasnalu yace na ajiye dukkan ababan dogaron nawa da dukkan tsafina, zan yakeka da tsagwaron karfin damtsena, idan ka sa kaima ka yakeni da tsagwaron karfin damtsenka, kada kayi amfani da karfin sihirinka.
Sa'ad da jarumi Hasnalu yaji wannan batu sai yayi murmushi sannan ya ce na yarda xan yakeka da tsagwaron karfin damtsen da ubangijin ya bani, kuma ina ka sani cewa ni bani da wani sihiri face karfin ubangijina da yake bani kariya daga dukkan sharrinku na aljanu...
Kafin jarumi Hasnalu ya gama rufe bakinsa tuni aljani Raugatul Agwanu ya shammaceshi ya daka tsalle sama yayi masa rotse fa gwiywar hannunsa a ka, nan take Hasnalu ya sulale kasa magashiyan mugun yananyi mai kama da suma ko gushewar tunani.
Nan fa hankalin su Imnal ya dugunzuma ainun, kuma suka kamu da tsananin tsoro, abinda ya basu mamaki shine kamata yayi ace kan jarumi Hasnalu ya dgargaje domin ko dutse aljani Raugatul Agwanu ya doka da wannan gwiywar hannuntasa sai dutsen ya farfashe, amman sai gashi babu abinda ya samu Hasnalu, sai dai jini da yayi fitar burgu daga cikin hancinsa gami da bakinsa.
Nan take Imnal ya yunkura zai falfala da gudu domin ya kaiwa jarumi Hasnalu dauki, amman sai sarki Maharaz yai caraf ya rikeshi tare da cewa ai kada mage ba yanka bane tsaya dai muga abinda zai faru. A wannan lokaci aljani Raugatul Agwanu sai faman ihu yake gami da kuri da cika baki, bisa ganin yayi wa jarumi Hasnalu kaf daya ya baje a kasa yana neman shekawa barzahu, koda yaga cewa Hasnalu ba zai iya tashi ba, sai ya juya ya dauko takobin Saiful Lujara da nufin ya dawo ya daddatsa Hasnalu yayi gutsu-gutsun da sassan jikinsa. Aiko yana daukar takobin kafin ma ya juyo tuni jarumi Hasnalu ya mike tsaye zumbur tamkar an ja zaren baka, kawai sai ya dako tsalle sama daga inda yake ya daki bayan aljani Raugatul Agwanu, kamar daga cikin baka aka harba aljani Raugatul Agwanu aka yayi tsalle sama yaje ya gwaru da wani katon dutse, karar haduwar kirjinsa da dutsen ta cika dajin gabadaya, dutsen ya farfashe kuma ya fado kasa a matukar galabaice yana mai yin aman jini ta baki da hanci kai harma ta kunnesa ma jini ne ke bulbulowa, anan ya kama shure-shuren mutuwa sakamakon cakudewar jini da ƙwaƙwalwarsa.
Cikin tsananin mamaki da farin ciki su Imnal suka rugo da gudu izuwa ga jarumi Hasnalu suka rungumeshi sun masu yi masa jinjina bisa Wannan gagarumar jarumtaka da ya nuna, shi kuwa Aljani Raugatul Agwanu bai shafe dakika talatin ba yana wannan shure-shuren ya zama gawa.
Farin ciki a wajen gimbiya Hursiyya da su sarki Maharaz ba sai an fada ba,nan dai suka zauna gabadayansu jarumi Hasnalu ya shiga koyar da su yadda ake yin ibada kamar su; tsarki, wanka, alwala da sallah, koma ya fara koya masu karatun Alkur'ani mai girma, ya biya masu suratul fatiha da falaki da nasi, bayan nan ne yayi masu limanci suka gabatar da sallar la'asar, da aka idar da sallar akayi addu'a sai jarumi Hasnalu ya dubesu gabadayansu tare da cewa to yanzu duk wanda yake jin yunwa sai yaje ya ci, wanda kuma duk yke da bukata ya kawar da ita, domin zamu cigaba da tafiya ne, da izinin Allah zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login