Showing 6001 words to 9000 words out of 71576 words

Chapter 3 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt

kamar ba
za a daina ba:
babu wanda zai fi baka tausayi ma sama da
sarki Maharaz domin har birgima ya kama ya a
kasa sai da aka rirrikrshi aka shiga bashi baki
sbda jiya yiya tsani kansa gwara ma ace shima
ya mutu ya huta da bakin ciki:
Lokacin da aka sanya Hibru a cikin kabarinsa
aka rufeshi sai inmal da sarki maharaz suka
kwana akan kabarin suja cigaba da kuka ba
sassauci:
akan kabarin suka kwna suna kukan har sai da
alfirjir ya keto sannan aka zo aka kwashesi
sumammu aka kaisu cikin tanti aka kwantar:
da kyar da sindin goshi gimbiya Mulaifa ta ceto
rayuwarsu:
bayan sun dawo hayyancisu ne aka kawo
musu abin kalaci dama a jiya da daddare ma
basu ci komai ba:
nan fa gardama ta karke a tsakaninsu da
mulaifa suka ce ba zasu ciba:
Gimbiya Mulaifa ta zare wata karaar wuka mai
tsananin kaifi da tsini ta saita cikintana kuka
tace idan har baza ku cin abinci ba lallai zata
kashe kanta:
nan fa suka kama cin abinci bisa dole har sai
da suka koshi:
gama cin abinci nasu ke da wuya sai ga wani
badakare Mai suna GAIYABU ya shigo cikin
tanti rike da wasika a hannunsa:
Gaiyabu ya zube kasa gaban sarki maharaz ya
kwashe gaisuwa sannan ya mika masa
wasikar:
nan take sarki maharaz ya warware wasikar ya
karanta a fili kamar haka;

SAKO DAGA SARKI DUJALU:
ZUWA GA SARKI MAHARAZ BABBAN ABOKIN
GABATA:
YAKAI WANNAN SARKI KAYI SANI CEWA
ABINDA YA FARU TSAKANINMU DA KU BA
KOMAI BANE FACE SHARAR FAGE: NA
SANCEWA NA KUNSA MUKU GAGARUMIN
BAKIN CIKI BISA NASARAR DA NA SAMU TA
KASHE SARKI YAKINKA; KUMA BABBAN
MASOYINKA HIBRU TO AMMA NIMA HIBRU YA
TAFI YA BARNI DA TABON BAKIN CIKI DA HAR
ABADA BA ZAN MANTA DASHI BA TUNDA
YARABANI DA HANNUNA GUDA DAYA:
TABBAS NAYI JINJINA GA MAMACI HIBRU
DOMIN SHI NE JARUMI NA FARKO WANDA YA
TABA SAMUN DAMAR YI MIN RAUNI A FILIN
DAGA KUMA NA YI ALKWARI KODA BAYAN
WANNA YAKI NE ZAN ZIRYACI KABARIN
HIBRU NA YI MASA JINJINA:
INA MAI SANAR DAKAI CEWA BISA
GUMURZUN DA AKA YI A JIYA MU DAKU
BABU WANI SAKAMAKO FACE RAGAS
SABODA HAKA ZAMU CI GABA DA WANNAN
YAKI NAN DA CIKAR KWANA UKU SBDA NAFI
SON NAYI YAKIN DA KU A LOKACIN DA KUKE
DA NATSUWA BA YANZU BA DA KUKE CIKIN
DAMUWA DA ALHINI:
INA FATAN ZA KU KARBI WANNAN SHAWARA
TAWA HANNU BIYU::

Koda sarki maharaz ya zo nan a karatun
wasikar sai yamike tsaye zumbur a fusace ya
yayyaga wasikar sannan ya yunkura da nufin
yafita waje ya sa a fara shirye shiryen yaki::::
cikin hanzari inmal ya sha gabansa yace ya
shugabana ka tausasa zuciyarka ka dau hkr
sau tari yanke hukunci a lokacin da rai ya
fusata baya haifar da komai face nadama da
asara:
muyi amfani da shawarar wanan abokin ga
namu mujira izuw tsawon kwna ukun:
koda jin wanna batu sai sarki maharaz ya duci
inmal cikin alamun tsananin damuwa yace
yakai magajin sarkin yaki shin baka da tunanin
cewa sarki dujalu so yake ya yaudaremu ya yi
amfani dawann dama ya kawi mana harin
sumamea cikin kwana ukun nan yadda zai iya
murkusheu a cikin kankanin lokaci?
Inmal ya numfasa yace haba ya shugabana ai
babu wani motsi wanda sarki da dakarunsa za
suyi ba tare da mun gani ba tunda daga nan
sasaninmu muna hangensu suna hangenmu, dare da ranan masu gadi suna lura:
ka kara hakuri ya shugabana har ixuwa lokacin
da wadannan kwanki zasu ciki::
ni ina ji a jikina cewar mune zamu sami nasarar
dauko takobin Saiful Lujara a cikin wannan
kogi:
koda inmal yazo nan a zancensa sai Gimbiya
mulaifa mata dubeshi tace kayi amfani da
shwarar inmla ya kai abbana domin ina gainin
cewa itace zata fiye mana alheri:
koda gama fadin hakan mulaifa ta kama
hannun inmal taja shi suka fice daga cikin
tantin suka bar sarki maharaz a tsaye cikin
tsananin da muwada takaici::::
WANNAN SHINE ABINDA YAFARU A CAN
BAKIN KOGIN BAHAR SUFIYA BAYAN ANCI
GABADA FAFATA YAKKI TSAKANIN RUDUNAR
SARKI MAHARAZ DA RUNDUNAR SARKI
DUJALU A KARO NA BIYU 2::::::::::::
* * * * *
AL:AMARIN Gimbiya Hursiya Kuwa; lokacin da
aljani burzaru ya nufi can birnin da ira ta
tabbatar da cewa an rabata Da sarki kenan sai
ta fashe da matsaininci kukana bakin ciki:
Bata gushe ba tana kukan hat aljni Barzaru ya
sauketa a tsakiyar gidan sarautar tasu::
Koda bayi kunyangi barori da dakarun tsaro na
gidan suka ganta sai duk suka zube kasa a
gabnta suna kwasar gaisuwa ko kallomsu ba
tayi ba sai ta juya a fusace tashige izuwaa can
cikin gidan sarautar da sauri:
duk sa adda ta waigo bayanta sai ta ga aljani
Barzaru nabiye da ita:
Al'amarin da yai matukar ba ta mamaki da
tsoro kenan.
nan take ta gane cewa lallai sarki ne ya umarci
barzaru da ya sa ido akanta don kada ta sulale
ta koma can sansani yaki:
Nan fa Hursiya taji hankalinta ya dugunzuma
ainun kuma ta kudurce a ranta cewar
takowanne hali sai ta san yadda tayi ta
subecewa barzaru takoma can sansanin yaki
sbda gwara itama ta mutu a can da dai azo
mata da labarin mutuwar sarki tunda bata da
kowa a duniya sai shi.
kai tsaye Gimbiya Hursiyya ta wuce izuwa cikin
turakarta.
tana shiga ciki ta mai da kofa tarufe bam da
karfi cikin fishi sannan ta fada kam gadonta ta
kwanta ruf da ciki ta fashe da sabon kuka:
Shi kuwa aljani barzaru a kofar turakar yaja ya
tsaya kuma ya kame kamar gunki yana muzurai
ko yaushe idanunsa na kallon gabas da yamma
kudu da arewa don hada gimbiya Hursiya ta
Shamaceshi ta fice ba tare da sani ba:
su kuwa fadawan sarki dujalu wadanda aka
barwa jiran gari koda suka ji cewar gimbiya
Hursiya ta dawo daga sansanin yaki ita kadai?
Sai suka cika da tsananin mamaki suka
dugungumo gaba daynasu syka zo ganin
gimbiya.
koda suka aika da manzo a gareta bisa
zuwansu sai ta aiko a gay musu cewa baza ta
gana dakowa ba sai gobe da safe a fada:
Al:amarin da yai matukar dugunzuma hakalinsu
kenan suka rasa abinda ke musu dadi sabo sa
su kawai so suke suji matsayin da ake ciki a
can sansanin yaki:
Shin sarki Dujalu yana nan a raye ko kuwa ya
mutu?
MASU IYA MAGANA SUN CE IDAN KAGA KARE
YANA SHINSHINA TAKALMI TO SO YAKE ZAI
DAUKA.
tunda gimbiya Hursiyya taji cewa yan majalisar
sarki sun kagu da su yi magana da ita sai
jikinta ya bata cewar so suke suci amanar sarki,
ma'ana idan suka ji sarki ya mutu sai su yi
sauri su nada wanda suke son ya gajeshi
acikinsu batare da sun bata sarautar bakamar
yadda yake aka ida:
Koda aiyana hakan sai hankalin Hursiya ya sake
dugunzuma ainun domin ta fahimci cewar lallai
tana ciki hadari domin idan ta fadawa yan
majalisar gaskiya al amari cewar bata san
abinda ya faru a filin yakin ba tunda bata gani
da idanunta zasu zata karya take su dauka
cewa lallai itama da kyar ta tsira kuma an kashe
sarki da mukarrabansa:
ama da Hursiya ta tuna cewa ai tana tare da
aljani Barzaru babban jarumi kuma sadauki mai
watsa maza babbn hadimi sarki dujalu mai
amana sai hankalinta ya dan kwanta sbda ta
san cewa zai kareta daga dukkan wani mugun
abu amma kuma sai ta fara tunasnin hanyar da
zata bita koma can sansanin yakin domin
zamanta a can zai fiye mata kwnciyar
hankali.
Kashe gari da safe bayan Gimbiya Hursiya ta
gama kintsawa tayi kalaci sai ta caba ado
sanna ta nufi fada fuskarta cike da annuri tana
takawa dai dai tamkar taron dawisu ta rinka
tafiya cikin izza da jin kamshi:
da shigarta cikin fadar sai ta iske gaba dayan
yan majalisar a zaune sun yi tsuru tsuru suna
jira isowarta:
koda suka ga gimbiya a cikin fara ada nishadi
sai hankalinsu ya dugunzuma ainun suka fara
tunanin cewa lallai sarki dujalu ne yake samun
nasara acan filin yakin:
Dama bayan tafiyar sarki dujalu da rundunarsa
ta yaki sai yan majalisar suja yi taro na sirri a
tsakaninsu inda suka gaiyato wani amintaccen
bokansu mai suna IRMAS BINI KAIBUR suka
umarceshi daya yi musu bincike akan abinda
zai faru a can bakin kogin Bahar sufiya:
Koda boka Irmas ya dauko madubin tsafinsa
ya shafeshi da hannun hagu domin yaga
abinsa zai faru sai nan take madubin tsafin yayi
bindiga ya farfashe:
Al:amarin da yai matukar razana boka irmas da
yan majalisar kenan suka firgita ainun:
Har yan majalisar sun yunkura zasu mike tsaye
su fice da gudu dga cikin dakin tsaro sai boka
irmas ya daka musu tsawa yace kowa ya zauna
a inda yake in bahaka ba kuwa babu wanda zai
koma gidansa a raye:
Koda jin hakan sai kowa ya koa inda yake ya
zauna:
boka irmas yai gyaran murya sannan ya dubi
gaba dayan yan majalisar yace yaku
shuganbanina kuyi sani cewa babu wani
matsafi a wannan nahiya mai karfin sihiri
dayakai na sarki dujalu sbda haka ya boye duk
abinda ke faruwa a cam bakin tekun bahar
sufiya ga dukkan wani mahaluki dake cikin
wannan nahiya:
bisa wannan dalili ne kuka ga madubin tsafina
yai bindiga;
yanzu hanya daya ce zamu bi my iya ganewa
idan sarki dujalu yana samun nasara a filin yaki
ko baya samu:
Nan gaba a lokacin da yakin ya fara tsauri lallai
akwai mutumin da zai dawo daga can filin yakin
wandas ya kasance makusanci na sarki ya hau
kan karagar sarki ya zauna: to tabbas
rudunarmu basu da saa kuma baza su dawo ba
a raye,
idan kuwa yaki zama akan karagr sarki to
tabbas sarki dujalu zai dawo gida a raye:
Kofa gimbiya Hursiya taga yan majalissar sun
kura mata idanu sai hankalinta ya dugunzuma
ta dada tabbatar da cewa lalai akwai wani
mugun abu da ke ransu.
Awannan Lokaci aljani barzaru na biye da ita
yana take mata bayan don tabbatar da tsaro
amma babu mai ganinsa face gimbiy Harsiya
kadai, har Gimbiya hursiya ta nufi inda karagar sarki
take da nufin ta zauna sai aljani barzaru yi sauri
ta sha gabanta yayi mata nuni da jada taje ta
zauna akan karagar.
Batare da gardamar komai ba kuwa ta sauya
wuri taje ta zauna akan kujerar da ta saba zama
ko da yaushe a fadar kamar kullum:
koda ganin haka sai jikin yan majalisar ya yi
sanyi gaba dayansu sai murna takoma ciki
kuma hankain su ya dugunzuma sabo da burin
da suke son cikawa tsawon shekara da
shekaru ya rushe alhalin wannan ce kadai
damar da suke da ita da zasu kawr da bakin
zalunci da aka dade ana yi musu a nahiyar:
a wanna lok Icin fadar tacika makil da
mutanen gari da duk inda mutum ya duba sai
dai yaga kawunnan bil adama rututu ako ina
babu masakar sinke.
ba komai ne ya janyo wannan cikowa ba face
mutane sun ji cewar gimbiya hursiya ce kadai ta
dawo daga can baki kogin bahar safiya don
haka kowa yana son yaji halin da yan uwansa
ke ciki wadanda suka tafi yaki.
Bayan Gimbiya Hursiya ta zauna akan wannan
kujera wadda ta saba zama akai sai aka buga
mata tamburan sarauta gami da bushin algaita
don girmamawa a gareta bisa matsayinta na
kanwar sarki.
Ana gama buga tamburan ne gimbiya hursiya ta
mike ta fuskacin jamaar gari tace ua ku
jamaata ina mai sanar da ku cewar wannan yaki
da muka fita mun fita akan saa da nasara
domin kuwa na baro jamaarmu suna
ragargazar jama ar sarki maharaz doin haka
akwai cikakakiyar alama tacewar mune zamu ci
wannan yaki.
Koda gimbiya Hursiya tazo nan a zncenta sai
fadar ta rude da shewar mutane jama a su cika
da dumbin farin ciki kuma suka sami kwanciyar
hankali ba komai ne ke damub mutne ba facw
tunanin yan uwansu wadanda aka tafi da su
yakin suna ga nin cewa ba lallai bane su dawo
ba amma jin cewar sune kesamu nasara a
yakin sai suka sami nutsuwa sun san cewa da
yawan jama'arsu za su dawo a raye.
haka gimbiya Hursiya ta cigaba da kwantar
musu da hakalin jama a cikin kalami na kara
kwarin guiwar har suka sami cikakkiyar
nutuswa da fahimta:
a sannan ne ta sallami kowa a fadar ta watse
kowa ya kama gabansa.
* * * *
lokacin da yan majalisar suka fice daga cikin
fadar sai suka kewaye daya bayan daya a
sirrince suka hadu acan gidan waziri sarki
dujalu wanda ake kira MAZARUB IBINI
HALSHAM kuma basu taru ba sai da dare ya
raba saada gari yayi tsit ba a jin sauti komai
face kukan tsuntsaye da nakarnuka.


Zan ci gaba.

Da fatan an tashi lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp.
MAZAN JIYA
Littafi na Hudu 4
Part E
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey

A cin wani babban falo na waxiri mazarub suka hadu, hatta barori da bayi na gidan a wannna rana tsaresu aka yi a wani daki dabam don kada su gazuwan yan majalisar ko su ji abinda zasu tatauna, dakarun dake tsaron gidan ne kawai suke kai kawo wadanda suka kasance aminatattun waziri mazarub:::
Bayan kowa ya gama hallara a cikin wannan
falo sai aka janyo kofofi da tagogin falon aka
rufee sannan wziri maharab yai gyaran murya
ya kalli yan majalisar mutu tara shine cikon na
goman wadanda gaba dayansu sun kasance
dattijai babu dan kasa da shekara hamsin da
biyar a cikinsu:
waziri marzub yace yaku yan majalisa kun sani
cewa shekara da shekaru tun zamanin
mahaifin sarki dujalu muke fama da kunci bakin
ciki gami da takaici bisa irin mulkin zalunci da
ake yi mana ::
babu sasauci ga basarke attajiri ko talakan gari:
Gaba daya kasashen dake wannan nahiya a
karkashin ikon sarki dujalu suke sai abinda
yace shi akeyi:
Yafi kowa dukiya karfi tsafi da karfin dantse
amma dik da haka ya raina wanan baiwa daya
samu kuma so yake ya mallaki duniya nan
gaba danyata;;
Shin haka za mu cigaba da zuba ido muyi ta
zama a matsayin bayinsa yayanmu da
jikokinmu ma su cigaba da yi masa bauta har
abadan abidina, kuyi sani cewa mune makasantansa amma
bai san darajarmu da kimanmuba, to ko mutuwa yayi haka yar uwarsa gimbiya Hursiya zata ci gaba da azabtar damu.
Tunda yanzu sarki dujalu yana can sassann
yakin da yafi kowanne yaki hadari a
rayuwarsa mun sami dsmar da zamu kawo
karshen bakin cikinmu::
Yanzu gashi yar uwarsa ta dawo tace wai
mune muke samun nasara a wanna yaki ta
yaya zamu iya tabbatar da cewa abin data
fadi gaskiya ne:
kumas ta ya ya zamu iya cimma burinmu mu
yar da kwallon mangwaro mu huta da
kuda?
Sa adda waziri mazarub yazo nan a
zancensa sai falon yayi tsit Tamkar mutuwa
ce ta gifta gaba dayan suka kama muzurai
suna kallon junansu aka rasa wanda zai ce
kala
daga can sai wani tsohon mafi shekaru a
cikinsu wanda ya kasancve dan wada
wanda tsawonsa bai wucce kamu shida ba
mai suna SADUSA ya mike tsaye yana mai
gyaran murya:
Nan fa kowa ya Uba masa idanu:
sadusa yai murmushi sannan ya shafi dogon
gemunsa wanda ya sauko har kasan cikinsa
yace yaku yan uwana yan majalisa ku yi sani
cewa ga dade ina jiran zuwan wannan rana
har mana fidda tsammanin zuwanta ama sai
gashi tazo::
ina so ku sani cewa a duk fadin kasar nan
da nahiyar nan bani da wani makiyi wanda
yafi sarki dujalu::
domin a sanadinsa ne na rasa iyayena
iyalina da dukkan dangina:
A yanzu haka ni kadai ne na rage daga
cikoin zuri armu hakam ya samo asali ne
akan wani laifi da zuri armu tayi masa yasa
aka rinka kamosu daya bayan daya ana yi
musu yankan rago:::
A wannan lokaci ni bana wannan nahiyar na
bazama cikin duniya neman ilmin tsafi:
Ban dawo ba sai bayan sarki dujalu ya gama
kashe gaba dayan zuri ar tamu gidamu
mana iskeshi a kone kurmus ko tsinke guda
daya ban samu ba, a bakin wani makofcinmu na sami lbrin
abinda ya faru ga zuri ata gaba daya:
Nan take zuciyata ta kama tafarfasa kamar
zata kone sbda fishi::
Nan fa wannan makoci nawa ya shiga
rarrashina yana mai bani shawarar na
hanzarta na bar garin nan domin idan sarki
dujalu ya sami lbr cewa ina dsga cikin zuri
ar da suka yi masa wannan laifi tabbas
kashe ni zai yi.
A wannan lokaci ina ta faman rusa kukane
na bakin ciki amma ko danaji wananan
makofci nawa yace wai sarki zai sa a
kasheni:
Sai na bushe da dariyar takama na ce ai na
wuce wannan matsayi: Kai dai kawai ka
zuba ido ka sha kallo:
Ba komai ne yasana yarda da kaina ba sai
bisa tarin dumbin ilimin da na samo na tsafi
don haka ina ganin cewa zan iya kare kaina
daga dukkan masifa:
Nan take na mike tsaye na yiwa makobcin
nawa sallama sannan na bude jakata na
debo dukkan gurayena da layu na tsafi na
daddaurasu a jikina:
Bayan na kammala shiri sai na durfafi fadae
sarki dujalu kai tsaye ba tare da fargabar
komai ba:
Lokacin da na isa fadar sarki dujalu sai na
isketa a cike makil da fadawansa da
;mutanen gari ana tafiyar da harkokin
mulki, duk da cewar fadar cike take da dajaru a ko
ina masu kwarjini da banTsoro amma ni dai
ko gezau banyi ba na cigaba da tunkarar
inda karagar sarki take:;
Su kansu dakaru da zarar sun ganni sai ka
ga suna buda mini hanya ina wucewa:
koda sarki dujalu ya hangoni na durfafo
inda yake zaune sai ya kura mini ido kawai
yana sauraron isowata:
kafin mutum ya isa inda aka ajiye karagar
mulkin sarki dujalu akwai wadansu
dardumai guda uku da aka shimfida kala
uku:
fara baka da ja:
tunda sarki dujalu ya hau kan mulki aka
shimfida wadannan dardumai amma ba a
taba ganin ranar da wani mahaluki ya taba
isa inda dardumai farko take ba wato
wannan farar darduma ya take ba bare har
ya taka ta biyu da ta ukun komai matsayin
mutum komai jarumtakarsa da karfin
sihirinsa ma baya iya zuwa ya taka wannan
darduma ta farko::
Kawai sai na cigaba da tafiya ina durfafar
sarki dujalu:
A lokacin ne gaba dayan mutane dake fadar
suka cika da mamakina kuma suka zubo
mana idanu nida sarki dujalu domin su ga
abinda zai faru:
Saboda ba a taba ganin wanda yashigo fada
ba a haka babu iso kuma babu sallama
sannan kuma gashi ya durfafi inda sarki ke
zaune an rasa badakare daya da zai tsayar
dani::::
Haka dai na cigaba da tafiya har na sami
nasarar taka durduna ta farko:
Al:amarin da yai matukar baiwa kowa
mamki kenan:
Shi kansa sarki Dujalu sai da Gyara zama
Yana mai Al ajabina:
Na ci gaba da tafiya sai gashi na taka
darduma na biyu::
Kawai sai aka ga sarki dujalu ya mike tsaye
ya zare takobinsa jikinsa ya kama tsuma har
fuskarsa yana yi gatsine:
Nima Sai na zare waya adda wacce ta fini
tsawo tana sheki gami da wani irin walwali
na tsafi::
Na cigaba da tafiya da nufin na taka
darduma ta uku wacce ta kasance ja:
Koda na iso karshen darduma ta biyu sai na
kasa daga kafata na cigaba da tafiya:
Nan fa na shiga karanta wadansu dalasimai
na tsafi domin na wuce gaba amma sai
nakasa;
koda ganin abinda ya faru sai sarki dujalu ya
bushe da dariyar farin ciki; lokacin guda
kumkuma ya turbune fuska ya dubeni yace
lale
marhaban da sadusa ibn zaiyar T@bbas ban
ga laifinka ba da kake kokarin kasheni
tunda nine na kashe iyalinka danginka da
duk zuri arka:
A rayuwarta ban taba zaton cewa akwai
mahalukin da ya sami sihirin tsafin dake daf
da nawa ba tabbas na san cewa kasha
bakar wahala kafin ka sami sihirin tsafin da
kake da shi a yanzu samun kmarka a doron
kasa a yanzu sai an sha wuya:
Bisa wannan dalilin ba zan kashe kaba duk
da cewar ya kamata na kasheka din sbda na
san cewa ka tsaneni fiye da yadda ka tsani
mutuwarka: zan kyaleka kuma daga yau ka
zama dan majalisata amma busa sharadi
guda daya;
Sharadin kuwa shine idan har kayi wani
yunkuri na cutar dani zan yi maka daurin rai
da rai a kurkuku inda zaka karasa sauran
rayuwarka ta duniya.
Sa'adda tsoho Sadusa yazo nan a lbrinsa
kowa yayi ajiyar zuciya a cikin falon sannan
sadusa ya cigaba da bayani yace yanzu
abinda ya kamata mu fara yi shine mu
tabbatar da gaskiyar lbrin da gimbiya
Hursiya tazo mana da shi:
SHIN gaskiya ne mu muke samun nasara?
Babu wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login