Showing 45001 words to 48000 words out of 71576 words
Chapter 16 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt
ya kama rawa, haka dai aljani Radiyan ya cigaba da kyalkkyala wannan dariya har izuwa tsawon yan dakiku, katsam kuma sai yayi girgiza ya zama guguwa, take guguwar tayi kan gimbiya Hursiyya zata sureta cikin zafin nama jarumi Hasnalu ya zare takobinsa ya kai wa wannan guguwa wawan sara ba tare da ya bude idon nasa ba, kawai sai suka ji aljani Radiyan ya rusa uban ihu daga can kuma sai suka ji karar faduwarshi kasa.
Hasnalu ya bude idanunsa yaga gawar aljani Radiyan a kasa gangar jikinsa ta rabu gida biyu.
Koda gimbiya Hursiyya tayi arba da gawar aljani Radiyan ya kwance sai ta rungume Hasnalu ta kuma fashe da kukan murna hadi da yi masa godiya bisa ceton rayuwarta da yayi daga sharrin aljani Radiyan.
Cikin sauri Hasnalu ya janye jikinsa daga nata ya ce ai ba ni bane abin godiya face ubangijina, wai shin kin manta ne cewa a baya kema kin ceci rayuwata, ai babu bukatar kiyi mani godiya.
Hursiyya ta yi murmushi sannan ta ce saboda me ba zanyi godiya ba ga abin kaunata ba, ya kai Hasnalu kayi sani cewa a rayuwata na fidda tsammanin cewa zan iya samun masoyi a duniya bbanda dan uwana sarki Dujalu, amman dana sadu da ki sai na gane ba haka bane, ina mai tabbatar maka da cewa a lokacin dana fara kyallara ido na ganka a take naji wani abu ya soki kahon zuciyata ban gane ko mene ne wannan abu daya soki zuciyar tawa ba sai bayan munci gaba da tafiya sannan na gane ashe so ne gami da haduwar jini, kaine namijin farko daya taba burgeni a rayuwata har naji na daina burin na bar duniya.
Koda jin wannan batu sai jarumi Hasnalu yayi murmushi sannan ya ce yake wannan yar sarki kiyi sani cewa tundaga lokacin da kika ceci rayuwata kika tsaida jinin dake zuba a cikina, kuma naga kina hawaye saboda damuwa bisa halin dana shiga, kuma kika gode wa Ubangijina sakamakon farfadowata, sai naji nan take nim sonki ya shigeni, tabbas nayi matukar mamaki da har na kamu da sonki saboda acan garinmu naki yarda na baiwa kowacce ya mace soyayyata saboda na kudira a raina cewa sai na cika burin da mahaifina ya kasa cikawa na jaddada addini musulunci a wannan nahiyoyi naku, sannan zanyi aure kuma har sai bayan naga inda kabarin mahaifin nawa yake, ko kuma na samu labarin yadda aka yi ya mutu, ina ji a jikina cewa a sanadiyyarki zan cika burin nawa, kuma da izinin ubangijina sai kin zama matar aure bisa ka'idar addinina.
Sa'ad da Hasnalu ya zo nan a zancensa sai gimbiya Hursiyya ta cika da tsananin farin ciki, ta dubeshi cikin murmushi ta ce ya kai abin kaunata ka yi sani cewa a halin yanzu ka cika sharadin dake tsakaninmu na ukun, tunda kayi gagarumin abin al'ajabi na kashe munafiki aljani Radiyan da taimakon ubangijinka, ni din nan ganauce na jiyau ba dan haka na bada gaskiya ga addinin musulunci, yanzu ba tare da wani bata lokaci ba in so ka shigar da ni cikin wannan addini naka na Musulunci.
Koda jin wannan batu sai shima jarumi Hasnalu ya cika da tsantsar farin ciki, ba tare da wani jinkiri ba kuwa Hasnalu ya karanta mata kalmar shahada ta maimaita. Faruwar hakan keda wuya sai Hasnalu ya mike tsaye yana mai mayar da takobinsa daya kashe aljani Radiyan cikin kufenta suka nausa izuwa cikin daji da sauri kuma gudu-gudu tare da barin gawar aljani Radiyan anan.
***********
Acan sansanin yaki kuwa lokacin da ttsanani yai tsanani sai labari ya sha bamban domin kowacce rundun dimaucewa ta yi, hankalinsu ya gushe banda kashe junansu babu abinda suke yi, kuma ragas ake yi a wannan aki dan ido bai isa ya tantance bangaren dake samun nasara ba.
Acan bngaren sarki Maharaz da sadauki Himalu kuwa abin abu kyan gani domin kowanne ya sari abokin gwaminsa sau akalla bakwai bakwai, kowannensu jini ne ke zuba daga jikinsa, tun suna iya kaiwa juna hari har sai da takai cewa sun kasa, dan haka da kansu suka zubar da makamansu tare da sulalewa kasa cikin wani irin mugun yanayi wanda babu tabbacin zasu kai labari.
A bangaren manyan zakuna kuwa wato sarki Dujalu da kuma jarumi Imnal abin ya kazanta fiye da na kowa saboda sai da suka shafe fiye da sa'a uku suna kaiwa juna sara da suka cikin matukar zafin nama juriya gami da bajinta ba tare da dayansu ya samu nasarar koda lakutar jikin daya ba, take a lokacin ajiya ta riskesu dan haka sai suka j da baya suna masu yin haki kamar zakaru, babban abin mamaki shine babu wanda yake iya kawo masu hari acikin mayan, kai ba wanda ma ya yarda ya rabi inda suke saboda kura ta san gidan mai babbar sanda.
Bayan sarki Dujalu da Imnal sunyi kallon-kallo a tsakaninsu cike da harar juna gami da mugun nufi a cikin zukatansu har izuwa tsawon yan dakiku, sai suka sake rugowa da gudu suka kacame da sabon azababben yaki cikin sabon salo, a wannan karon kowannensu yana kai sara da suka cikin tsalle-tsalle gami da kwance-kwance, kuma suka dinga hadawa da kai naushi hannu da kafa.
Faruwar hakan keda wuya sai rawa ta sauya tunda kidama ya sauya, nan take suka fara samun damar cuttar da junasu, a duk sa'ad da sarki Dujalu ya samu nasarar naushin Imnal a fuska, kafin ya sake kaima masa wani naushin shima imnal ya rama wannan naushi, nan da nan kuwa suka hada wa junansu jini da majina, suka fara luguiguita juna, ana cikin haka ne sarki Dujalu ya sammaci Imnal ya soka masa takobinsa a gefen saman kirjinsa, wanda har sai da takobin ta bullutso ta gadon bayansa.
Imnal ya kwarara uban ihu saboda tsananin zafi da yaji, Dujalu yasa kafarsa ya doki kirjin Imnal jini yayi tsartuwa kuma Imnal yayi sama tare da fadowa kasa cikin tsananin galabaita yana numfashi gami da shure-shure kamar wanda ranshi zai fita.
Cikin tsananin murna sarki Dujalu ya bushe da wata mahaukaciyar dariya ta mugunta ya taho izuwa kan Imnal tarw da raba kafafunsa biyu akan Imnal din yana mai daga takobinsa sama da nufin ya cakata a cikin Imnal.
Ba zato ba tsammani sai kawai yaga imnal ya tashi zaune, cikin zafin nama na gaban kwatance shima ya sokawa Dujalu tasa takobin a kirji a daidai inda shima ya sokeshi ya bullutso har gadon bayansa.
Nan fa Imnal ya daddage iya karfinsa tare da naushin sarki Dujalu da daya hannun nasa, a take dujalu yayi sama a lokacin da Imnal ya zare takoninsa daga cikin kirjin sarki Dujalu aikuwa sai jini ya kama bulbulowa daga cikin kirjin, Dujalu ya fadi kasa magashiyan yana kakarin mutuwa.
Imnal ya sake mikewa da nufin ya mike taaye amman sai jiri ya debeshi ya sake faduwa a kasa ya baje, nan fa aka rasa wanda zai iya sake tashi tsaye daga cikinsu, gashi dai suna cikin wani irin mugun hali na daf da mutuwa amman saboda naci gami da taurin rai kowanne a cikinsu burinshi shine ya tashi tsaye domin yaje ya kasara kashe abokin gabarsa amman sai gashi abu ya gagara. Ganin sun kasa mikewa tsaye ne yasa suka fara tafiya da jan ciki suna masu tunkarar junasu, sai da ya rage saura baifi taku uku ba a tsakaninsu sai duk su biyun suka sume a lokaci guda.
A wannan lokacin gaba-daya dakarun dake a wannan filin yakin sun mutu babu sauran mutum daya daga cikin rundunonin wanda ya tsira da rayuwarsa.
Adaidai wannan lokacin ne kuma jarumi Hasnalu da gimbiya Hursiyya suka karaso filin yakin a guje,tun daga nesa gimbiya Hursiyya ta ga babu mutum ko daya a filin yakin, duk inda ta hanga sai dai taga gawarwaki fululu dan haka sai ta ringa duba gawarwakin tana neman gawar dan uwanta sarki Dujalu kuma tana mai fashewa da kuka, shima jarumi Hasnalu sai ya shiga duba gawarwakin dake a filin yakin ko zai ga wanda yake da sauran rai, sai da suka shafe rabin sa'a suna dube-dube sannan a lokaci guda suka zo kan Dujalu da Imnal, cikin gaggawa suka shiga kokarin ceto rayukansu, inda d farko suka fara tsayar da jinin dake zuba a jikinsu, sannan suka shiga dinke raunikan dake jikinsu tare da sa masu magani, kafin daga nan suka yayyafa masu ruwa suka farfado suna masu dawowa cikin hayyacinsu. A sannan nan ne Dujalu da Imnal sukaga jarumi Hasnalu da Hursiyya tsaye a gabansu kawai sai suka cika da tsananin mamaki kuma suka kmaa kalle kalle da hange-hange sukaga gabadaya filin gawarwaki ne babu sauran wani mai rai a cikinsa.
Koda Hursiyya taga dan uwanta sarki Dujalu ya tsira da rayuwarsa sai ta rungumeshi ta fashe da kukan farin ciki, shi kuwa Jarumi Imnal a sannan ne hankalinsa ya dugunzuma ainun, ya fara kuka saboda ya hanga ko ina amman baiga gimbiya Mulaifa ba, kuma baiga sarki Maharaz ba, nan take ya takarkare ya kwarara uban ihu tare da fashewa da matsanancin kuka, haka yayita yin kukan yana mai dunkule kansa a kasa kamar ba zai daina ba. Kwatsam ba zato ba tsammani sai suka hango wani mutum daga can nesa ya mike cikin gawarwakin yana mai tunkaro inda suke yana tangadi. Su duka sai suka zuba masa idanu sai da ya kara matsowa kusa da su sosai sai sukaga ashe sarki Maharaz ne, a wannan gabadaya ya rine da jini, koda Imnal ya shaida cewa sarki Maharaz ne sai ya mike tsaye da kyar ya tafi zuwa gareshi, suna haduwa suka rungume juna tare da durkuwa a kasa.
Cikin matukar karfin hali sarki Maharaz ya bude baki ya ce yayi magana a cikin kunne Imnal ya ce masoyiyyarka na can baya gawarwaki sun danneta, bani da tabbacin tana raye ko ta mutu.
Koda jin haka sai Imnal ya saki Maharaz ya sake mikewa da kyar ya kara gaba. A lokacin ne sarki Maharaz ya yanke jiki zai fadi, kawai sai ga jarumi Hasnalu ya karaso gareshi a guje ya tallaboshi sannan nan take ya shiga ƙoƙarin ceto rayuwarsa.
Imnal ya cigaba da tafiya yana tangadi sannan yana dube-duben inda gawarwaki suka danne gimbiya Mulaifa.
A wannan lokacin gimbiya Hursiyya tana ta kokarin danne sarki Dujalu domin so yake ya mike tsaye ya je ya cigaba da yakar jarumi imnal, koda taga ya dage lallaı sai ya je ya kashe imnal din sai ta daka masa tsawa a karon farko a rayuwarta da shi.
Cikin tsananin mamaki da takaici sarki Dujalu ya koma ya zauna a kasa dirshan sannan ya dubeta sa'ad da hawaye ya zubo masa ya ce yake yar uwata, yanzu yau kece da kanki kike daka mani tsawa akan ina son na kashe makiyinmu, ashe kin manta da duk irin halaccin da nayi maki kenan a baya, kuma kin manta da duk irin kaunar da na nuna maki, shin bakya kishin birninmu gami da jama'armu kenan, ko kuma kin makance ne baki ganin miliyoyin rayukan da muka yi asara da kuma dunbin duniyarmu data salwanta a filin yakin nan, yanzu kina nufin shikenan sai dai burina nason mallakar wannan duniya ya rushe, tabbas d dai haka ta faru gareni gwara ku kyaleni na mutu dan banga amfanin ceto rayuwata da kuka yi ba, wane ne wancan bakon jarumin dana ganshi a tare da ke, kuma ya aka yi kika dawo wannan filin alhalin nasa aljani Balzaru ya shammaceki ya daukeki ya tafi dake can birninmu?
Hursiyya ta dubi sarki Dujalu a lokacin data share hawayen dake kan fuskarta ta ce ya kai dan uwana kayi sani cewa kayi mani tambayoyi masu yawa, amman kayi hakuri duk zan baka amsoshinsu nan bada jimawa ba, abinda yasa nayi maka tsawa a yau shine, a yau ne na gane da kai sarki Maharaz duk kuna kan tafarkin bata ne mabayyani, kuma kuna wannan yaki ne bisa zalunci da son zuciyarku kawai, gashi kun janyo anyi asarar miliyoyin rayuka ba tare da dayanku ya samu nasara ba, a yau kai da Maharaz zaku gasgata zancena cewar duk kuma kan hanyar bata domin a gaban idanunku wancan bakon jarumin zai yi abinda kuka kasa aikatawa da taimakon ubangijin gaskiya, koda ta zo nan a zancenta sai suka jiyo Imnal yana kwalla masu kira yana neman taimako.
Hursiyya ta mike tsaye zumbur kawai sai ta hango Imnal yana ta kokarin ture wasu gawarwaki domin ya zaro gimbiya Mulaifa amman sai ya kasa, shi kuma a wannan lokaci jarumi Hasnalu nata kokarin ceto rayuwar sarki Maharaz.
Koda ganin haka sai Hursiyya ta ruga da gudu izuwa inda Imnal yake, ta taimaka masa suka ture gawarwaki dake kan Mulaifa suka zarota, aikuwa sai suka isketa a raye tana numfashi kadan-kadan, cikin hanzari Hursiyya ta shiga ƙoƙarin ceto rayuwar Mulaifa ta fara tsayar da jinin dake zuba a jikinta ta hanyar saka masa magani, sa'ar m da aka yi shine babu manyan raunika a jikinta masu zurfi da yawa.
Koda Imnal yaga Hursiyya ta dage tana kokarin ceto rayuwar masoyiyarsa gimbiya Mulaifa sai ya cika da tsananin mamaki bisa ganin kanwar babban abokin gabarsa ce take kokarin ceto masoyiyarsa. A wannan lokacin ne Imnal ya gama dawowa cikin hayyacinsa, ya juya baya ya hango sarki Maharaz a raye tare a jarumi Hasnalu kuma ya hango sarki Dujalu gefe daya zaune yana kallonsu, bayan kamar sa'a guda lokacin an gama yi wa kowa magani, aka samu nutsuwa sai gaba dayansu su shidan suka taru a waje guda, a lokacin ne Hursiyya ta kwashe labarinta ta zayyana masu, tun daga lokacin da ta hada baki da kuyangarta lazimat taje ta samo mata aljani Radiyan ya fito da ita daga gidan sarauta, kawo izuwa sa'ar da suka shiga cikin kunnen Aljani Raugatul Agwanu ya cigaba da tafiya da su har yazo dajin da suka hadu da jarumi Hasnalu, da dukkan abubuwan mamakin da jarumi Hasnalu yayi akan hanyarsa ta zuwa bisa taimakon Ubangijin musulunci, kawo izuwa lokacin da itama ta karbi addinin musulunci a hannun Jarumi Hasnalu har suka karaso bakin tekun.
Lokacin da Hursiyya ta gama bada wannan labari sai jikin Mulaifa, Imnal da sarki Maharaz yayi sanyi, zukatansu suka yi sanyi suka fara ayyanawa cewa lallai wannan addini na Hasnalu shine addinina gaskiya.
Shikuwa sarki Dujalu sai ya fashe da kukan bakin ciki, kuma cikin tsananin takaici ya ce yake yarbuwata hakika kin tarwatsa mani dukkanin shirina, yanzu duk irin tsananin wahalar dana sha ta tsawon shekara da shekaru ina shirye-shiryen mallakar duniya ina kuma mai yin tanadi ya zama na banza kenan? To bari in fada maki ni ban yarda cewa wannan addini shine n gaskiya ba, dan haka ina nan a kan bakana na cigaba da wannan yaki har sai na kashe abokan gabata na shiga cikin wannan teku na dauko takobin Saiful Lujara.
Kafin Hursiyya ta kara budar baki ta ce wani abu sai sarki Maharaz ya tari numfashinsa ya dubi Dujalu ya ce ya kai wannan sarkin abokin gabata, ka sani cewa komai da yarjejeniya muke yinsa, mu yanzu mun janye maka wannan yaki mun hakura mun bar mka takobin Saiful Lujara, idn har zaka iya daukota to ga fili nan ga mai doki sai ka jaraba daukota mu gani, amman bisa sharadi guda Sharadin kuwa shine idan har ka kasa daukota kuma jarumi Hasnalu ya shiga ya daukota zaka bada gaskiya ga addininsa kamar yadda zamu bada gaskiya ga addininsa yanzun nan.
Sa'ad da sarki Dujalu yaji wannan batu sai yayi shiru ya fada cikin kogin tunani, daga can kuma ya dubi sarki Maharaz ya ce na amince da wannan sharadi.
Yana gama fadin haka sai ya mike tsaye ya dauke takobinsa sannan ya dubi sarki Maharaz ya ce kafin na karbi addinin wannan bakon jarumin inason ka taimakeni na dawo da dukkan sihirin tsafina domin da shine zan iya shiga cikin wannan teku na yaki ljanun dake karkashinta masu gadin takobin na daukota.
B tare da gardamar komai ba sarki maharaz yayi murmushi ya ce nasan cewa inba da taimakona ba babu yadda za'a yi sihirinka tsafinka ya dawo, lallai zan taimakeka b tare da naji shakka ko tsoron komai ba domin ni yanzu nayi imani cewa addinin Musulunci shine addinin gaskiya, kuma na yarda cewa kai ba zaka iya dauko wannan takobiba sai dai jarumi Hasnalu ya daukota.
Koda jin haka sai Sarki Dujalu ya bushe da dariyar mugunta yana mai cewa aikuwa sai ka yi nadama kuma ka gane cewa kayi babban kuskure tunda har zuciyaka ta yarda da hakan, ina mai tabbatar maka da cewa indai sihirin tsafina ya dawo jikina to sai na samu nasarar dauko takobin Saiful Lujara, kuma kaine mutum na farko da zan kasheshi da ita.
Sarki Maharaz yayi murmushi sannan ya ce na amince d hakan. Gama fadar hakan kedawuya sai sarki Maharaz ya mike tsaye shima sarki Dujalu sai ya mike tsaye suka tunkari juna, saura bai fi taku daya ba su hadu sai cikin sauri Hursiyya ta shiga tsakaninsu ta dubi sarki Dujalu idanunta na zubar da hawaye ta ce ya kai dan uwana na rantse da girman iyayenmu ko tsafinka ya dawo ba zaka iya dauko wannan takobiba...
Kafin Hursiyya ta gama rufe bakinta tuni sarki Dujalu ya hankadeta ta fadi can gefe guda, kawai sai ya dubeta a fusace yana mai cewa kin bani kunya d har kika zabi abokin gabarmu kika gujeni, to kisani cewa har abada bazan yada Addinin iyayye da kakanni ba domin shine abin kunya na karshe da zanyi a rayuwata.
Yana gama fadin hakan ne sai ya karasa jikin sarki Maharaz suka manne da juna, faruwar hakan keda wuya sai wani irin haske mai karfi ya lullubesu, aka fara wata irin gagarumar iska mai karfi gami da taawa da walkiya a sararin samaniya, kawai sai sarki Maharaz ya janye jikinsa daga jikin na Dujalu tare da komawa gefe daya. Take wani irin jan haske ya taho daga sararin samaniya ya rinka shiga jikin sarki Dujalu har saida ya gama shigewa kaf, a sannan ne sarki Dujalu ya ji wani irin azababben karfi ya shigeshi, irin wanda bai taba jin irinsa a duniya ba, dan ji yake tamkar idan aka yi masa gammo zai iya daukar wannan duniyar a ka ya kuma yi tafiya da ita.
Nan take sarki Dujalu ya kwarara uban ihu kuma y sunkuya kasa ya