Showing 36001 words to 39000 words out of 71576 words
Chapter 13 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt
Dauwaz ta ce, to yanzu shi ke nan muna ji muna gani ga abin da muka zo nema sai dai mu kyale shi?
Maruful Dauwaz ya sake yi ma ta rada a kunne a karo na biyu ya ce, "Ke yarinya ce kin cika gaggawa, ki tsaya mana mu jarraba dabarunmu na manya. Ai ita Saniya sai da shafa ake tatsar nononta.
Gama fadin hakan ke da wuya sai suka ji Jarumi Shaddadu ya tuntsure da dariya. Lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa ya dube su ya ce, Tabbas yau ne na yarda cewar idan Kere na yawo, Zabo ma yana yi, wata rana dole a hadu.Yau ramin karya ya kure babu ta inda za a bulle. Babu zancen бuya ko sauya siffa. Kun sani, ni ma na sani farautar juna muka fito, don haka yanzu sai a yi ta ta kare ko ni ko ku!
Koda jin wannan batu sai Ziya'ul Hak ta tari numfashin Shaddadu ta ce, "Kai tsohon munafuki dan munafuka karyarka ta sha karya. A yau din nan zan yanke burin mahaifiyarka wanda ta dade tana tanadinsa shekara da shekaru.
Yau zan kwatowa mabaifina 'yancinsa da karagar mulkinsa a hannunku. Take anan zan kashe ka sannan na tafi can Birnin Kufa na kashe wannan azzalumar mahaifiyar taka wacce ta yi kwacen karagar mulki".
Kafin Ziya'ul Hak ta gama rufe bakinta tuni Jarumi Shaddadu ya tari num fashinta yana mai daka ma ta tsawa ya ce, "Ke saurara 'yar babban munafuki, Shugaban azzalumai na duniya. Idan ba ki san tarihin waye ubanki ba to ki koma wajensa ki nemi sani.
Ina mai sanar da ke cewa mahaifinki Laffaru a da can lokacin da yai Sarauta a Birnin Kufa babu wani Sarki da ya fi shi zalunci a Nahiyar gabadaya, kuma babu wanda ya fi shi karfin dantse da jarumta.
Mahaifin ki ne ya kashe mini Kakannina da dukkan zuri'arsu, kuma shi ne ya yi wa mahaifiyata fyade har aka sami cikina. Kin ga ke nan ke 'yar uwata ce amma a yau babu wadda na tsana a doron kasa sama da ke".
Koda Shaddadu ya zo nan a zancensa sai kwallar takaici ta cika masa idanu har hawaye ya subuto masa daga cikin kwayar idanunsa bai sani ba.
Sa'adda Ziya'ul Hak ta ji wannan jawabi sai jikinta yai sanyi ta fara tunanin cewa hakika mahaifinta bai kyauta ba.
Koda Aljani Maruful Dauwaz ya fahimci cewar wannan batu na Shaddadu na neman karya zuciyar Ziya'ul Hak sai ya kira sunanta, ta waigo ta dube shi sannan ya ce, "Ya ke abar kaunata, kada ki yi amfani da kalmomin abokin gabarki ya yaudare ki da su ya hallaka ki a banza. Ina mai tabbatar miki da cewa har abada makiyi, makiyi ne ba zai taɓa zama masoyinki ba."
Maruful Dauwaz ya dubi Shaddadu ya ce, "Kai yaro, ka yi sani cewa abin kunya ne ni da Ziya'ul Hak mu hada karfi mu yake ka tunda ni ba sa'anku ba ne, Ziya'ul Hak ce daidai da kai saboda haka duk ku ajiye sihirin tsafinku a gefe daya ku yi karon batta da tsagwaron karfin dantsenku domin ku fid da raini a sami daya daga cikinku ya kawar da kishirwar gabar da ke tsakaninku tun ta iyaye."
Lokacin da Jarumi Shaddadu yaji wannan batu sai ya tuntsure da dariya ya ce, "Kuna son ku raina mini hankali ne. Babu wata dabara wacce za ku zo mini da ita ko yaudara ku sami nasara a kaina kawai kowa dabararsa ta kwace shi".
Kafin Aljani Maruful Dauwaz ya Rara fadin wani abu tuni Ziya'ul Hak ta zare Takobinta ta falfala da gudun tsiya kuma gudun tsafi izuwa kan Shaddadu.
Ai kuwa shima sai ya daga Mashin Galilul Haras ya ruga izuwa kanta.
Cikin dimaucewa Aljani Maruful Dauwaz yai sama izuwa kan Ziya'ul Hak domin ya sure ta don kada ayi wannan gumurzu.
A daidai wannan lokaci ne Shaddadu ya kawo wa Ziya'ul Hak mummunan duka aka da Mashin Galilul Haras, ita kuma ta kai masa suka a gefen kirjinsa.
Cikin bakin zafin nama Maruful Dauwaz ya dauke Ziya'ul Hak Mashin bai same ta ba amma sai ya sami kafadar Maruful Dauwaz, nan take kashin kafadar tasa ya karye, ya kwarara wani uban ihu mai tsananin firgitarwa ya fadi kasa sumamme.
Shi kuwa wannan wawan suka da Ziya'ul Hak ta kaiwa Shaddadu ya yi kokarin kaucewa sukar da cikakken zafin namansa amma duk da haka sai da kaifin Takobin ya farka rigar jikinsa ya yanke shi a dantsen hannunsa jini ya yi tsartuwa, ya kwalla ihu kuma Takobin tata ta buge Mashin nasa.
Ai kuwa sai Mashin yai tsalle sama ya fada can kasan wani rami mai tsananın zurfi da fadi wanda karshensa ruwan korama ne yake gudu.
Cikin tsananin bakin ciki Jarumi Shaddadu ya yunkura zai ruga ya fada cikin ramin don dauke Mashinsa na Galilul Haras amma sai Ziya'ul Hak ta daka tsalle ta sha gabansa suka sake kacamewa da azababben Yaki
a lokacin ne ya yi wuf ya zare wadansu gajerun adduna guda biyu suka rinka kai wa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta. A daidai wannan lokaci ne wadannan Dakan guda arba'in wadanda suka sume sakamakon Aljani Maruful Dauwaz suka farfado.
Koda suka ga irin masifaffen Yakin da ake yi tsakanin Shaddadu da Ziya'ul Hak sai suka cika da tsananin al'ajabi domin ba su taɓa ganin Jarumai masu irin wannan Jarumta ba kuma Har i zuwa wannan lokaci Aljani Maruful Dauwaz bai farfado ba.
Nan fa su Shaddadu suka ci gaba da BAKIN ARTABU. Duk sa'adda makamansu suka hadu sai dai ka ga tartsatsin wuta na tashi. Sai da suka shafe sa'a uku da rabi suna wannan bakin gumurzu. Da kyar da sidin goshi shi ma Shaddadu ya samu nasarar yankar Ziya'ul Hak a cinyarta, take wajen ya dare jini yai tsartuwa ta durkusa kasa tana mai kwalla ihu. Ba tare da ta yi yunkurin tsai da jinin ba ta daka tsalle sama cikin tsananın fushi domin ta fillewa Shaddadu kai.
Ai kuwa shi ma sai ya daka tsallen sama suna haduwa suka gwara fuskokinsu. Take kowannensu hancinsa da bakinsa ya fashe suka rikito kasa a cikin wani irin mugun yanayi mai kama da gushewar hankali, ba su san Sa'adda suka saki makaman Yakin da ke hannunsu ba. Ai kuwa sai makaman suka gangara izuwa cikin wannan rami mai zurfin gaske wanda Mashin Galilul Haras ya fada.
Lokaci guda duk su biyun suka mike zumbur
Suka tsinci kansu daf da bakin wanna rami. Suna lekawa kasan ramin sai Shaddadu ya hango Mashinsa akan ruwa yana tafiya. Nan take ya daka tsalle izuwa kasan ramin ba tare da jin tsoron zurfin ramin ba da kuma duwatsun da ke cikinsa.
lta ma Ziya'ul Hak sai ta daka tsallen ta bi shi zuwa kasan ramin domin ta hana shi samun damar dauko Mashin saboda ta san cewa da zarar ya dauko Mashin take zai sami ikon hallaka ta.
Shi da ita sai suka kama kwala ihu sakamakon razanar da suka yi bisa ganin zurfin ramin da suka yi kudunbalar faďawa.
Tun kafin su isa kasan ramin, karamin jiri ya fara dibarsu. Ai kuwa suna isowa cikin koramar da karfi ji kake fanjam! Sai suka nutse kasan ruwan.
Ta ke duk su biyun kawunansu ya bugu da duwatsu kowannensu ya sume, kasancewar jikinsu ya sandare sakamakon sun nutse izuwa ruwan sai suka taso izuwa saman ruwa.
Nan kuwa igiyar ruwa ta raba su. Shaddadu ya yi yamma, ita kuma Ziya'ul Hak ta yi gabas, ruwa ya yi ta tafiya da su.
A daidai wannan lokaci ne Aljani Maruful Dauwaz ya farfado daga dogon suman da ya yi Koda ya yunkura domin ya mike zaune sai ya ji ya kasa sakamakon kashin kafadar tasa da ya karye.
Cikin tsananin juriya ya kama kashin da ya karye wanda lankwashewa ya yi kasa ya dagoshi sama yana mai tsandara uban ihu saboda tsananin zafi da zogin da ya ji. (Maza gumbar dutse)
Wannan uban ibu da ya yi ne ya sa wadannan Dakaru suka sake zubewa kasa sumammu a karo na biyu saboda tsananin dimaucewa.
Aljani Maruful Dauwaz ya mike tsaye a dimauce ya kama dube-dube da waige-waige a wajen amma bai ga gawar Ziya'ul Hak ba ko ta Shaddadu.
Al'amarin yal matukar dugunzuma hankalinsa ke nan kuma zuciyarsa ta kama tafarfasa saboda fishi
Nan take ya cika da mamakin yadda aka yi ya sume nan take saboda an doke shi da Mashin Galilul Haras. Haka kuma ya tuna alkawarin da ya daukarwa iyayen Ziya'ul Hak cewar zai kare lafiyarta amma kuma ga shi ya kasa.
Maruful Dauwaz ya tuno da irin tsananin jarumtakarsa da tsananin karfin dantsensa amma yau duk sun zama na banza tunda ga shi yaro karami ya yi masa kwaf daya. Nan take takaicì ya rufe shi har kwallar bakin yi ciki ta zubo masa.
(Kamar ya manta da tasirin mashin GALILUL HARAS)
Cikin matukar karfin hali Maruful Dauwaz ya mike tsaye ya bude fuka-fukansa yai sama yana leken kasa, ai kuwa sai ya hango Hular karfen da Ziya'ul Hak ta sa akan saman ruwan wannan korama yana tafiya da ita. Cikin gaggawa ya sauko kasa-kasa daf da ruwan koramar ya fara shawagi yana neman Ziya'ul Hak kuma yana kwalla mata kira amma bai ganta ba kuma bai ji duriyarta ba.
Al'amarin da ya kara dugunzuma hankalinsa ke nan kuma ya daďa dimaucewa, ya sauko ya fada cikin ruwan ya yi nutso izuwa karkashin ruwan koramar yana dube-dube ko zai ganta.
Su kuwa Dakarun Sarauniya Zubaina lokacin da suka farfaďo sai suka sake firgicewa a karo na biyu, suka dubi gabas da yamma, kudu da arewa ba su ga Aljani Maruful dauwaz ba sai suka mike tsaye suka cika wandunansu da iska suka durfafi fada domin su kai labarin abin da ya faru.
****
Lokacin da Jarumi Shaddadu ya suma a cikin wannan ruwan korama sakamakon buguwar kansa a dutse har ya taso sama igiyar ruwa ta tafi da shi. sai da ruwan ya yi tafiyar kimanin sa'a daya da rabi da shi sannan ya kawo shi daf da bakin gaɓar wani kogi ya tunkudo shi waje.
Ashe tun lokacin da aka fito farautarsa daga fada tare da saurayin mafarauci mai Kare labari ya riski karuwa Yaldisa.
Koda jin wannan labari sai hankalin Yaldisa ya dugunzuma domin tun bayan rabuwarta da Shaddadu ta kasa samun sukuni sakamakon kamuwa da tsananin sonsa da begensa a cikin zuciyarta.
Ai kuwa tana jin wannan labari ta fito da gudu daga cikin gidanta ta zo kofar fada ta labe. A gaban idanunta mafarauci mai Kare tare da Dakaru arba'in suka fito daga cikin gidan Sarautar a guje suka nausa cikin gari.
Ai kuwa sai ta bi su da sauri tana buya ba tare da sun sani ba har suka iso wajen bishiyar nan inda Jarumi Shaddadu ya bayyana aka kama fafatawa.
Duk wannan gumurzu akan idanunta aka yi shi tana laɓe a bayan wata bisiya tana kallo. Koda ta ga Jarumi Shaddadu da Jaruma Ziya'ul Hak sun fada cikin wannan rami mai zurfin gaske sai hankalinta ya dugunzuma ta fara kuka domin a tunaninta Shaddadu ya mutu. Da ma a wannan lokaci Dakarun Sarauniya Zubaina da Aljani Maruful Dauwaz duk suna kwance a sume.
Abin ka da dan gari, koda Yaldisa ta hango Shaddadu ya fada wannan rami sai ita ma ta juya da aya ta bi wata hanya dabam da gudu.
Tana gudun tana kuka har ta iso cikin wata gangara mai kwazazzaɓai da ruwa. Ta cikin ruwan ta bi da gudu, ai kuwa sai ga shi ta bullo karshen wannan rami mai zurfi wanda su Shaddadu suka fado. Idonta a rufe kuma ba tare da shakkar komai ba ta daka tsalle ta fada cikin koramar ta kama iyo a cikinta tana neman Shaddadu
Sai da ta shafe kusan rabin sa'a a cikin koramar har ta je bakin gaba ba ta ga Shaddadu ba. Ga shi a wannan lokaci ta gaji ainun tana haki da numfarfashi sama-sama kamar ranta zai fita. Tana durkushe a gaban koramar ruwa ya kado gangar jikin Shaddadu dai-dai inda take.
Koda ta yi arba da shi sai ta kara kanta a kirjinsa. Take ta ji alamar numfashi dan kadan. Cikin tsananin murna ta yunkura ta mike tsaye kuma ta sunkuce shi ta dora a kafadarta ta runtuma da gudu izuwa cikin daji.
Lokacin da aljani Radiyan ya zo nan a labarinsa sai yayi shiru ga barin zance mai dadi saboda gajiyar surutu. Cikin tsananin damuwa gimbiya Hursiyya ta dubeshi tya ce haba ya kai Radiyan, saboda me zaka katse mani wannan labari mai dadin sauraro, mai dauke da abubuwan al'ajabi gami da ban tsoro a daidai lokacin da dadinsa yayi yawa kuma aka zo daidai inda za raba gardamar gaba ta shekara da shekaru, wai shin ma ya ya akayi kasancewa dan uwana sarki dujalu ya soma bani wannan labari na mazan jiya kuma har kasan daidai inda ya tsaya a labarin nasa ka dora.
Lokacin da aljani Radiyan ya ji wadannan tambayoyi guda biyu sai ya bushe da dariya sannan ya ce tsananin bincike nane a hallarar tsafina yasa naga dukkanin binda ya faru tsakaninki da dan uwanki sarki dujalu, sannan ni yanzu na gaji da surutu ne shiyasa na yanke maki wannan labari yanzu.
Koda jin haka sai Hursiyya ta sake duban aljani Radiyan cikin tsananin damuwa kamar zata yi kuka tace ina mai rokonka da ka yi mani alkawarin cewar zaka karasa mani wannan labari har izuwa karshensa, in ya so idan muka isa sansanin yaki na iske dan uwana sarki dujalu a raye sai ya bani labarin Sadauki Hulkas na Birnin Romaniya bayan an kammala yaki.
Kod jin wannan batu sai aljani Radiyan yayi ajiyar zuciya sannan y ce Tabdijan lallai dan adam da buri ya ke, yanzu ke har kina sa ran cewa dan uwanki zai rayu a wannan masifaffen yuaki da ake yi? To bari kiji ni kaina yanzu na karamin ganganci nayi ba, dana karbi kwangilar kawoki wannan tsubiri na kogin bahar sufiya, abune mawuyaci duk wanda ya rabi wannan kogi ya iya tsira d rayuwarsa.
Hursiyya tayi guntun murmushi sannan ta ce ina farin ciki zan mutu a kusa da dan uwana sarki dujalu maimakon na mutu a hannun makiyansa wato fadawansa, wadanda a halin yanzu kokari suke yi suyi masa juyin mulki.
Cikin tsananin mamaki aljani Radiyan ya dubi Hursiyya ya ce yaya aka yi kika san wannan al'amari?
Hursiyya ta yi murmushi a karo na biyu ta ce ai kasan an ce ba idone kadai yake gani ba hankali shime ke masa jagora wajen gani.
Tunda aka dawo dani daga sansanin yaki na zuba ido akan fadawan sarki dukkan wani motsi nasu in sane da shi, koda ta zo nan a cikin bayaninta sai ta yi ajiyar zuciya sannan ta cigaba da cewa ya kai wannan boka ni a yanzu na gaji da zama a cikin wannan wawakeken kunnnen aljanin, in bukatar na wasa kafafafuna a bisa turba mai dauke da iska da korayen ganyayyaki.
Kafin Hursiyya ta gama rufe bakinta sai kawai suka ji aljani Raugatul Agwan ya saki fuka-fukansa ya sauko lasa luuu daga can kololuwar sama, kfin cikar dakika dari da ashirin sai gashi ya dira bisa turba.
Nan take boka sadusa haryal da shalbirat suk sauko daga kansa suka tsinci kansu a cikin wani kyakkyawan daji mai yawan ni'ima, domin yana dauke da bishiyu iri-iri, da kuma koramai, dabbobin daji ma gasu nan manyansu da kanana.
Koda muggan dabbobi sukaga su boka sadusa sai suk tarwatse suk bar dajin gaba daya, hatta tsuntsaye dake kan bishiyu sai da suka yi kaura daga dajin gabadaya suka kama guje-guje kai kace wata annoba ce ta barko cikin dajin.
Nan take aljani Raugatul Agwan ya samu guri mai yalwatacciyyar ciyawa ya kwanta domin ya dan huta.
Cikin tsananin mamaki boka sadusa ya dubeshi yace da shi kai dai ka cika lalaci, yanzu yar wannan tafiyar da muka yi shine sai ka kwanta ka huta? To wai shinma wannan wane daji ne haka kazo ka ajiyemu a cikinsa?
Koda jin haka sai aljani Raugatul Agwan ya dubi boka sadusa cikin takaici da mamaki yace hakika ni dai a rayuwata ban taba ganin mahaluki mai rainin wayo kamar biladama ba, yanzu wannan tafiyar da mukayi ta tswon kwana casa'in da uku a cikin abinda bai wuce sa'a bakwai ba shine kake kiranta da yar tafiya, kai fa yanzu ko yankaka za a yi ba zaka iya kawomu nan ba a cikin shekara guda koda kuwa da karfin sihirin tsafinka ne, to ka sani cewa rabon da nayi doguwar tafiya ta rabin sa'a ma yau shekara goma sh tara kenan, tinda na sato kyakkyawa Shalbirat sa'ad dana kawota dajina na darul hushushil maut, game da tambayarka akan wannan dajin kuwa nima ban san kowane daji bane tunda ban taba jin an kirashi da wani daji ba, amman dai abinda na sani shine daga nan zuwa kogin bahar sufiya ba zai wuce tafiyar sa'a uku da rabi ba jal ba,in mai dada yi maku tuni da cewa ni ba zan kaiku har bakin kogin bahar sufiya ba, sai dai na ajiyeku da tazarar zira'i dari daga tekun.
Boka Sadusa yayi dariya sannan ya ce ai mun san da haka, amman dai kada ka manta da cewa mun taho da kai ne domin ka yi mana leken asiri kuma ka gano mana matsayin da yakin ke ciki.
Aljani Raugatul Agwan ya ce na san da haka amman dai ni bazan yarda naje inda za a iya hangoni daga can sansanin yakin ba, yanzu dai zan kwanta bacci na tsawon sa'a bakwai kada wanda ya tasheni har sai wannan lokaci ya cika sannan sai na debeku na tafi da ku can din, lallai zamu isa can a lokacin da dare ya fara, sannan za muje a lokacin da yafi dacewa sa'ad da duhun dare ba zai bari a hangomu ba.
Koda gama fadin haka sai aljani Raugatul Agwan ya kishingida, kwanciyarsa keda wuya sai bacci yayi awon gaba da shi ya kama shara uban minshari tamkar ya kwana arba'in yana bacci.
A sannan ne Boka Sadusa, Halyal da shalbirat suka shiga kokarin kafa tanti, bayan sun gama kafa tantin sunyi shimfida sai suka fito da abincin guzurinsu suka ci, abinka da gajiyayyu nan da nan suma bacci sai ya sace su.
Ashe duk abinda ke faruwa Boka Radiyan da Gimbiya Hursiyya na gani domin sun zo kofar kunnen Raugatul Agwan suna