Showing 51001 words to 54000 words out of 71576 words
Chapter 18 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt
gami da rurinsu ya dimautasu, suka ji kamar su arce da gudu, amman sai suka tsaya suna masu toshe kunnuwansu da hannayensu suna masu cigbaa da kallon tekun domin suga abinda zai faru.
Aiko ba a jima b suka fara ganin sassan jikin aljanun yana tasowa saman ruwan, kafin a jima saman takun ta cika makil da sassan aljnun, sai bayan kamar dakiku dari da sittin sannan suk ga jarumi Hasnalu ya fito daga cikin tekun yana mai rike da akwatin zinare.
Koda ya iso bakin gaba sai Hursiyya ta ruga da gudu ta tareshi cikin tsananin farin ciki ta rungumeshi tana mai yi masa jinjina.
Sarki Maharaz, Mulaifa da Imnal ma sai suka tareshi suka kama dariyar farin ciki, nan take Jarumi Hasnalu yayi bismila ya kama kwadon dake jikin akwatun ya balleshi da karfin tuwo, take marfin ya balle, koda aka yi arba da abinda ke ciki sai kowa ya cika da mamaki, domin ashe ba wai iya tabokin Saiful Lujara ce kadai a cikin wannan akwatu harda mashin Galilur Haras tare da hular lamsara.
Hasnalu ya debo wannan kayan yakin guda uku ya zo gaban sarki Dujalu ya zubesu a gabashi sannan ya dubeshi yace ya kai wannan sarki yanzu gashi n dauko abinda ya gagareku daukowa, saboda haka sai ka cika alkawari ka karbi addinina.
Koda jin wannan batu sai sarki Dujalu ya takarkare ya bushe da dariya, al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan, lokaci guda kuma sai ya turbune fuska yake idanunsasuka ciko da kwalla har hawaye ya fara zubo masa a lokacin da ya kura wa yar uwarsa idanu, Dujalu ya kauda kai ga barin kallon Hursiyya ya dubi Hasnalu ya ce ya kai wannan gawurtaccen jarumi kayi sani cewa hakika a yanzu addininka shine na gaskiya, to amman fa b zan iya karbar addinin naka ba, saboda burina shine na mutu akan irin tafarkin da iyaye da kakannina suka mutu a kansa,abin kunya ne a gareni ace irin tsatson gidanmu ya kauce daga turbar gado, babban abin bakin cikina shine zan mutu ba amfana da kayan yakin mazan jiya ba yadda labarina zai bazu a ko'ina a cikin wannan duniya, har ya zamana cewa ba za a taba mancewa da ni ba.
Hursiyya ta kalli dan uwanta sarki Dujalu ta ce saboda yasakake cewa mutuwa zaka yi alhalin gaka a raye kana magana muna sauraronka.
Kayi sani cewa mu duka mun dawo daga rakiyar tsafi gami da aljanu, mun gano cewa duk karya ce, tunda gashi ma munga takobin Saiful Lujara a waje daya da hular lamsara da kuma mashin galilur haras, alhalin an bamu labarin cewa a wajaje daban-daban suke.
Lokacin da sarkk Dujalu yaji wannan batu sai hawaye ya sake zubo masa a karo na biyu ya ce ya ke yar uwata kiyi sani cewa wannan mugun duka da aljanu suka yi mani a karkashin wannan teku sa'ad da nake kokarin dauko takobin Saiful Lujara ba karamar illa yayi mani ba, domin ta kai cewa sun tara mani jini a jikina, tabbas wannan duka shine zai zamo sanadin ajalina tabbas ba zan tashi ba. Hakika inda nasan zan rayu tofa ba zan karbi addinin Musulunci ba sai dai na karbi wadannan kayan yaki na mazan jiya domin na cika burina, shin wani ya cigaba da baki labarin Mazan Jiya kuwa daga inda na tsaya maki ko kuwa baki samu wanda ya baki ba?
Hursiyya tayi ajiyar numfashi sannan tace tabbas aljani Radiyan ya cigaba da bani labarin hikayar sadauki shaddadu har yazo inda ya hadu da jaruma Ziya'ul hak sukayi gagarumin yaki wanda takai cewa su duka sun fada cikin wani rami mai zurfi, wanda kasansa cibiya ce ta ruwan wata korama, a cikin koramar ne ma mashin galilur haras ya fada ruwan ya tafi da shi.
Koda Hursiyya ta zo nan a zancenta sai sarki dujalu ya dakatar da ita da hannunsa a lokacin da yayi tari gudan jini ya zubo daga cikin bakinsa.
Al'amarin daya firgita Hursiyya kenan ta sake fashewa da matsanancin kuka tana mai kankameshi a jikinta, su kuwa su jarumi Imnal dukkaninsu sai suka kamu da tsananin tausayi musamman da sukaga gashi sarki dujalu yana kan gangarar ajali, amman ga dukkan alamu bashi da rabo na musulunta.
Cikin matukar karfin hali sarki dujalu ya janyo Hursiyya daga kan kirjinsa ya dubeta a lokacin da hawaye ke zuba daga cikin idanunsa ya ce ya ke yar uwata bani da wata nadama a wannan duniya face guda daya, itace zan tafi na barki a cikin begena, amman kuma ina farin ciki da naga kin samu masoyi wato wannan bakon jarumi, ko ba komai nasan zai iya debe maki kewar rashin dan uwa da kuma dangi, kuma zaki samu iyali a tare da shi, yanzu zanyi kokari kafin rai yayi halinsa na karasa maki labarin jarumi shaddadu inda halima na baku labari Sadauki Hulkas na birnin Romaniya mai hular lamsara. Game da wannan kayan yakin na mazan jiya kuwa da kuka gansu yanzu a tare a wannan akwatu, abin ya samo asli tunda daga lokacin da kowanne jarumi daga cikin mazan jiyan ya rabu da makaminsa, shidai mashin galilur haras daga lokacin da ya fada wannan korama sa'ar da shaddadu da Ziya'ul hak suka yi yaki to fa bai sake ganinsa ba har izuwa karshen rayuwarsa, kuma aljanu ne suka dauko mashin a cikin wannan korama suka dawo da shi nan cikin tekun bahar suffiya suka sanya shi a cikkn akwatin da aka sanya takobin Saiful Lujara, ya ke yar uwata anan gaba zaku ji yadda kayi itama hular lamsara tazo tekun bahar suffiya.
Yake yar uwata yanzu sai ki saurara da kyau domin kiji karashen hikayar sadauki shaddadu.
Sarki Dujalu ya sake yin tari hudan jini ya zubo, al'amarin da ya sake jefashi cikin mugun yanayi kenan kamar ma ba zai rayu ba, amman sai ya daure ya cigaba da bayani kamar haka: "Lokacin da karuwa yaldisa ta sunkuci jarumi shaddadu ta sabashi a kan kafadarta ta ruga da gudu izuwa cikin daji sai da ta yi tafiya mai dan nisa dauke da shi sannan ta iso bakin wani Kogon dutse.
Kai tsaye ta kunna kai izuwa cikin Kogon ta shimfide Shaddadu a gefe daya sannan ta je ta karyo reshen bishiyoyi ta hada itatuwa ta kunna wuta a cikin Kogon ta fara kokarin dinke katon ramin da ke kan Shadaddu sai da ta gama dinke raunin ta shafa masa magani jini ya daina tsattsafowa sannan ya farfado.
Koda Shadaddu ya bude idanunsa ya yi arba da Yaldisa zaune a gabansa sai ya cika da tsananın mamaki ya kama waige-waige da dube-dube.
Nan take ya yunkura da nufin ya mike zaune amma sai Yaldisa ta danna kirjinsa ta mai da shi kasa kwance ta cé, Kada ka tashi ya kai masoyina domin kuwa ba za ka iya yin tafiya ba yanzu don na san kana jin jiri, dole sai ka huta sannan lafiyar jikinka za ta dawo.
Cikin tsananin rudewa Shadaddu ya dubi Yaldisa ya ce, Ina Mashina?
Yaldisa ta ce, ban tsince ka tare da Mashinka ba, kai kadai na gani a bakin gabar koramar a cikin mugun hali mai kama da suma ko mutuwa. Ni kaina hankalina bai kwanta ba sai a yanzu da na ga ka farfado daga wannan dogon suma.
Koda jin wannan batu sai hankalin Jarumi Shadaddu ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe a rayuwarsa ya fara tunanin cewa, ya bai wa mahaifiyarsa kunya kuma shi ke nan har abada ba zai sami nasara ba akan abokin gabarsa Sarki Laffaru, muddin wannan Mashi na Galilul Haras ya koma hannun Ziya'ul Hak.
Nan fa zuciyarsa ta kama wasi-wasin inda Mashin yake a halin yanzu domin ba shi da tabbacin cewar yana hannun su Ziya'ul Hak.
Cikin alamun tsananin damuwa ya dubi Yaldisa ya ce, ya ke wannan ma'abociyar karame a gare ni hakika kin yi mini taimakon da ba zan taba mantawa da shi ba a rayuwata don haka, na yi miki alkawarin zan yi miki babbar sakayya a nan gaba.
Koda jin wannan batu sai Yaldisa ta murmushi ta ce, ba na bukatar ka biya ni abin da na yi maka da dukiya, amma ni akwai alfarmar da zan nema nan gaba a wajenka.
Shaddadu ya dubi Yaldisa cikin mamaki ya ce, Ke kuwa wacce irin alfarma ce wannan za ki nema a wajena?
Yaldisa ta yi murmushi ta ce, Ka yi hakuri ba zan iya fada maka ba a yanzu sai a lokacin da za ka biya ni ladan da ka yi niyya.
Yanzu dai na san hankalinka a tashe yake saboda rashin ganin Mashinka. Abin da za a yi shi ne, zan bar ka a nan cikin wannan Kogon dutse domin ka huta, kuzarinka ya dawo. Ni kuma zan koma can gidan Sarauta.
A can ne zan samo labarin inda Mashinka yake saboda na fuskanci cewar wadannan abokan gaba naka sun hada kai da Sarauniyarmu domin a ga bayanka.
Sa'adda Shadaddu yaji haka sai ya kamu da murna ya ce, maza ki je ki aiwatar da hakan lallai zan kasance mai zuba idanu don ganin dawowarki.
Yaldisa ta yi murmushi mai taushi a gare shi ta ce, zan yi kokari na dawo da wuri kuma ka kwantar da hankalinka babu abin da zai same ka muddin kana cikin Kogon nan.
Tana gama fadin hakan sai ta juya ta fice da sauri ta ruga da gudu ta nufi hanyar da za ta fitar da ita daga cikin dajin gaba daya.
******
Al'amarin Aljani Maruful Dauwaz sai da ya shafe kusan sa'a guda yana neman Jaruma Ziya'ul Hak a saman wannan korama da karkashinta sannan ya hango ta a kwance ko alamar rai babu a tare da ita.
A dimauce ya duro kasa ya dago ta zaune sai ya ga ashe da ranta domin tana numfashi sama-sama, sannan ga katon rauni a kanta wajen ya dare jini na zuba. Cikin hanzari ya dinke mata wannan rauni sannan ya tofa mata wadansu dalasimai na tsafi akan raunin amma sai ya ga sihirin tsafin ya ki yai tasiri. Al'amarin da ya yi matukar dugunzuma hankalinsa ke nan. Bisa dole ya je ya samo wadansu ganyayen bishiyoyi ya dandaka su sannan ya shafa akan raunin. Jaruma Ziya'ul Hak ba ta farfado ba sai bayan tsawon sa'a daya da rabi. Idanunuta na budewa ta mike tsaye zumbur! Cikis kuzarinta tamkar babu abin da ya same ta ta dubi gabas da yamma, kudu da arewa ba ta ga abokin fadanta ba sai Aljani Maruful Dauwaz. Cikis kaduwa da damuwa ta dubi Maruful Dauwaz ta ce, ina abokin gabar tamu yake?
Maruful Dauwaz ya yi ajiyar zuciya cikin alamun takaici ya ce, ban gan shi ba. Ke ma ban gan ki ba sai da na sha wahalar nemanki a cikin wannan korama. Ya ke abar kaunata, ki yi sani cewa, yanzu babban tashin hankalina shi ne sihirin tsafina da na ki gaba daya sun daina tam kuma ban san dalili ba.
Ina sa ran cewa shi ma Jarumi Shadaddu nasa sihirin tsafin ba zai yi aiki ba amma fa idan har ya ga Mashin Galilul Haras Shirin nasa zai dawo.
Tabbas ba wani abu ba ne ya janyo lalacewar sihirin tsafin namu ba da nasa face haduwar makaman Yakinki da Mashinsa na Galilul Haras.
Koda Aljani Maruful Dauwaz ya zo nan a zancensa sai ita ma Jaruma Ziya'ul Hak halinta ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe ta rasa abin da ke ma ta dadi a duniya.
Ziya'ul Hak ta dubi Maruful Dauwaz cikin alamun tsananin damuwa ta ce, to yanzu mene ne abin yi?
Maruful Dauwaz ya ce, ba mu da wani zabi wanda ya fi mu bazama neman Jarumi Shaddadu da Mashin Galilul Haras a cikin wannan kogi.
Idan ba mu gansu ba sai mu koma izuwa gidan Sarautar Sarauniya Zubaina mu sake neman taimakonta tun da dai da dan gari akan ci gari. Ita ce za ta iya sanin duk inda za a iya zuwa a ga Shaddadu. Ni kam ina zargin cewa akwai wanda yake taimakon Jarumi Shaddadu a cikin garin nan!
Ziya'ul Hak ta numfasa ta ce, tabbas Biri ya yi kama da mutum, domin in da babu wanda yake boye shi da babu yadda za a yi mu neme shi mu rasa haka, duk da cewar Sarauniya Zubaina tana ba mu taimakonta.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba Aljani Maruful Dauwaz ya rankwafa kasa Ziya'ul Hak ta hau kansa ta zauna sannan ya bude fuka-fukansa ya yi sama suka ci gaba da kewaya wannan korama suna neman Jarumi Shaddadu tare da Mashin Galilul Haras amma sai da suka duba ko ina ba su gansu ba.
A sannan ne Maruful Dauwaz ya sauko kasa bisa turba, Ziya'ul Hak ta sauko daga kansa ta dube shi cikin tsananin damuwa ta ce, yanzu ta yaya za mu iya komawa gidan Sarautar Sarauniya Zubaina alhalin sihirin tsafinmu ya daina aiki, ba za mu iya rikiɗewa ba izuwa siffar Mafarauci da Karensa?
Maruful Dauwaz ya jinjina kai ya ce, "Tabbas zancenki dutse ne, to amma ba mu da wani zabi face ki je ki gaya wa Zubaina cewa, kin fito ne farautar wani abokin gabarki mai suna JARUMI SHADDADU kuma ki siffanta kamanninsa. Tun da masu gadin kofar sun gan shi kuma tabbas sun sanar da Zubaina kamanninsa. Tana jin bayaninki za ta aminta da ke kuma za ta ba ki hadin kai. Ki sani cewa ita ma Sarauniya Zubaina gawurtacciyar matsafiya ce idan na bi ki muka je tare za ta farke mana laya tunda mu yanzu namu sihirin tsafin ba ya tasiri, zan ci gaba da zama a nan dajin har zuwa sa'adda za ku sake fitowa farautar Jarumi Shaddadu.
Fatana kawai shi ne a ce Shaddad ba ya tare Mashinsa na galilul Haras, in dai ba ya tare da shi tabbas wannan karon za ki sami nasarar hallaka shi."
Koda jin wannan batu sai Jaruma Ziya'ul Hak ta kamu da tsananin farin ciki. Nan take ta yi wa Aljani Maruful Dauwaz sallama ta tafi i zuwa cikin gari
***
Sarauniya Zubaina na zaune a fadarta ana tafiyar da harkokin fadar sai ga wadannan Dakaru da suka tafi farautar Jarumi Shaddadu tare da mafarauci sun shigo da gudu.
Da zuwansu gaban karagar Zubaina sai suka zube kasa suna haki, aka rasa wanda zai ce kala. Cikin fushi Zubaina ta daka musu tsawa ta ce, ina wannan Mafaraucin yake? Ku ba ni labarin abin da ya faru, shin an kamo wannan tsageran Jarumin?
Koda jin wannan tambaya sai daya daga cikin Dakarun ya dubi Sarauniya sannan ya sake risinawa a gabanta ya ba ta labarin duk abin da ya faru iyakar abinda suka gani da idanunsu.
Koda jin wannan labari sai hankalin Sarauniya haina ya dugunzuma ainun ta mike tsaye tana ma kai kawo cikin tsananin damuwa.
Alamarin da yai matukar bai wa fadawanta mamaki kenan. Wazirinta ya dube ta ya ce, ya shugabata, wai shin mene ne dalilin da ya sa kika yi matukar damuwa ne akan lallai sai kin kama wannan bakon Jarumi? Ni ina ganin cewa tunda dai an yi iya kokari akan a kama shi abu ya gagara ya kamata a hakura haka domin idan aka ci gaba da matsawa za a iya asarar rayukan Dakarunmu da dukiyarmu.
Koda jin haka sai Zubaina ta dubi Waziri a fusace ta ce, akwai abin da nake son na karba a hannunsa wanda ya fi rayukan Dakarunmu da dukkan dukiyarmu daraja da amfani. Tuni na yi bincike a cikin hallarar tsafina na gano cewa wannan bakon Jarumi yana tare da wani Mashi wanda ake yiwa lakabi da MASHIN GALILUL HARAS. Duk wanda yake tare da wannan Mashi zai iya yakar duniya gabadayanta domin komai yawan mayaka zai iya hallaka su shi kadai.
Koda jin wannan batu sai gaba dayan mutanen da ke fadar suka cika da tsananin al'ajabi. Waziri ya ce, yanzu ta yaya za mu iya zuwa mu kamo wannan bakon Jarumi alhalin ba mu san inda yake ba, kuma idan har yana tare da Mashin ai ba za mu iya kama shi ba. Koda jin wannan batu sai jikin Sarauniya Zubaina ya yi sanyi ta rasa abin da za ta ce.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai suka ji an ce, nii zan iya taimakawa a ga inda wannan bakon Jarumi yake har a kamo shi! Cikin kaďuwa kowa ya waiga baya aka dubi bakin kofar shigowa fadar, sai aka yi arba da Jaruma Ziya'ul Hak a tsaye.
Cikin mamaki Sarauniya Zubaina ta dubi Ziya'ul Hak ta ce, ke kuwa wace ce kuma daga ina kika fito?
Da jin wannan tambaya sai Ziya'ul Hak ta risina ta kwashi gaisuwa sannan ta dago kai ta ce, ni sunana BADI'ATUL LAUMARA. kuma na fito ne daga can Nahiyar kasashen da ke gabashin taku. Na baro gida ne saboda farautar babban abokin gabata JARUMI SHADDADU wanda a halin yanzu yana nan a cikin Birnın nan naki ya buya bisa taimakon daya daga cikin mutanen garın nan.
Ina son mu hada KARFI DA KARFE ni da ke domin mu sami nasarar kama wannan azzalumin Jarumi mu yi masa kisan gilla saboda ina da labarin irin barnar da ya yi a cikin wannan Birni naki sannan ya karya miki doka.
Sa'adda Ziya'ul Hak ta zo nan a zancenta sai Sarauniya Zubaina ta bushe da dariya. Al'amarin da la bai wa kowa mamaki ke nan a fadar har da ita kanta Ziya'ul Hak. Sarauniya Zubaina ta ce, haba ya ke Ziya'ul Hak 'ya ga Sarki Laffaru na Birnin Kufa a da, saboda me za ki boye mini kanki alhalin na san ko wace ce ke kuma na san abin da ya baro ki daga gida? Ni da ke zani ce ta tarar da mu je mu. Na sani cewa ke ba ki da wani buri wanda ya fi ki kashe Jarumi Shaddadu sannan ki je ki kamo mahaifiyarsa a raye ki kai ta wajen mahaifinki ku yi mata kisan wulakanci.
Ni kuma ba ni da burin da ya fi na mallaki Mashın Galilul Haras da ke hannun Shaddadu, sabo da haka na amince mu hada KARFI DA KARFE domin kowannenmu ya cika burinsa.
Idan kin amince yanzu sai ki bi ni izuwa cikin Turakata domin mu zauna mu tattauna ke ma ki ci abinci ki huta.
Yayin da Sarauniya Zubaina ta zo nan a zancenta sai Ziya'ul Hak ta yi murmushi ta ce, na amince.
Nan take Sarauniya Zubaina ta ja Ziya'ul Hak i zuwa cikın gidan Sarautar