Showing 42001 words to 45000 words out of 71576 words

Chapter 15 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt

su bi, domin su cigaba da tafiya, amman sai yaga hanya daya ce jal dole ne sai sunbi ta wani katon kogon dutse mai duhun gaske.
Nan fa Hasnalu ya ji a jikinsa cewa lallai baza a rasa wani mugun abu ba a cikin kogon, kuma gashi duhune dundum a ciki, suna shiga abinda ke ciki zai iya cutar da su ba tare da sun ganshi ba, nan fa Hasnalu ya fara tunanin dabarar da zai yi yasa duk abinda ke cikin kogon ya fito waje ayi gaba da gaba.
Nan take kuwa dabara ta fado masa ya daga kansa sama yana mai wangame bakinsa ya kwala kabbara da karfi, aikuwa take dajin ya kama amsa kuwwa, duk wani abu dake wannan daji sai da ya razana tsuntsaye suka kama tashi sama suna sauya sheka, dabbobin dake wannan daji suka kama fitowa suna karo da masu kokarin shiga saboda rudewar da suk yi, aikuwa a sannan ne suka ji cikin wannan kogon dutsen ya rude da wani irin gurnani mai yawa da karfin gaske, al'amarin da yayi matukar razana aljani Radiyan da Hursiyya kenan, kafin kiftawar ido sun ruga da baya izuwa cikin duhuwar bishiyoyi suna masu leken jarumi Hasnalu domin suga abinda zai faru gareshi. Shikuwa Hasnalu sai ya kara rike takobinsa da hannu biyu yana mai gyara tsayuwarsa alokacin da wannan mugun gurnanin yake dada karuwa, gami da wani irin takun sawaye tamkar giwaye ne ke shirin fitowa daga cikin kogon dutsen wanda har sai da ya fara haifar da yar karamar girgizar kasa.
Sai dai hakan bai sa jarumi Hasnalu ya razana ba ko kuma yayi yunkurin ja da baya ba, kwatsam sai ga rundunar wasu burirrika manya manya masu tsananin tsawo da kaurin gaske gami da tsananin muni, su dai wadannan burirrikan adadinsu ya kai kusan dari, suna da zara-zaran farata a hannunsu, masu kaifi da tsini kamar wukake, duk da cewar jarumi Hasnalu yana da dakakkiyar zuciya amman sai da zuciyarshi tayi rawa yayi tunanin cewa lallai fa yau ya gamu da gamonsa.
Al'amarin su Hursiyya da aljani Radiyan kuwa lokacin da suka hango wadannan burirrika a take suka firgice suka kwanta a kas cikin duhuwar ciyawa, kuma suka dauke numfashinsu tamkar marasa rai.
Lokacin da wadannan munanan burirrikan sukaga biladama guda daya jal a gabansu yana rike da makami, sannan babu alamar tsoro a tare da shi sai suma suka tsaya cak suna kallonshi cike da tsantsar mamaki, ba wani abu ne yasa suke mamaki ba face shine kadai mutum na farko daya taba yin arba da su ba tare da ya sume ko kuma ya haukace ba.
Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin burirrikan da jarumi Hasnalu har izuwa tsawon yan dakiku, a duk sa'ad da yayi arba da jajayen idanun burirrikan masu ban tsoro da tsananin ja tamkar an gasa dan bida a cikin wuta sai yaji kamar jiri na dibarsa.
Nan take Hasnalu ya fara karanto addu'o'i na neman tsari domin ya fuskanci cewar burirrikan suna da kofi a tare da su.
Sannu a hankali burirrikan suka fara rarrabuwa suna yiwa Hasnalu kawanya, shi kuwa sai ya cigaba da tsayuwa a inda yake ba tare da ya motsa ba, kawai kuma sai ya rufe idanunsa tare da daga takobinsa sama sosai tsininta na kallon sararin samaniya. Al'amarin da ya dan tsorata burirrikan kenan yasa suka kasa afka masa farat daya, suka rinka kusantarsa da kadan kadan.
Hursiyya da aljani Radiyan dake boye suna ganin dukkanin abinda ke faruwa, kawai sai suka sake cika da dumbin mamaki musamman ganin dakewar zuciya irin ta jarumi Hasnalu, kuma suka cigaba da zuba ido dan suga irin gumurzun da xai yi tsakaninsa da wadannan birirrikan.
Kamar hadin baki sai kawai birirrikan suka yunkura gaba dayansu tare da afka masa a lokacin guda da nufin suyi gutsu-gutsun da sassan jikinsa kowa ya ja rabonsa, aikuwa sai suka kaiwa isk sara da suka domin kuwa tuni Hasnalu ya daka tsalle sama tamkar daga cikin baka aka harba shi, kafin su dga kawunasu sama yayi alkafira a saman kawunasu ya dawo kasa hannunsa na rike da takobinsa, a sannan ne ya shiga gididdiba su yana sare masu kawuna, koda ya dira kasa kuwa sai ya cigaba da daukar rayukansu cikin bakin zafin nama irin wanda dan adam bai taba gani ba, yana saransu da sukansu yana hadawa da kabbara, sai dai kaga sassan jikin birirrikan na shawagi a sama ko kuma kaga hanjin cikinsu na bullutsowa waje suna faduwa kasa matattu.
Koda birirrikan suka ga Hasnalu yayi masu mummunar barna kuma ga shi a tsakiyatsu amman sun kasa koda warzanar jikinsa sai suka fusata ainun kuma suka haukace suka rinka jijjigo bishiyoyi daga karkashin kasa suna masu kai masa duka ta ko ina, a hakan ne daya daga cikinsu ya samu nasarar kwada masa bishiya a kirji, saboda karfin dukan sai da Hasnalu yayi sama bayansa ya gwaru da jikin wata bishiya take yayi aman jini, kuma tsinin reshen bishiyar ya sokeshi a gefen hakarkarinsa na hadu, nan fa Hasnalu ya kwala kabbara a lokacin da ya subuto sakamakon tsananin zafi da zugin da ya ji, a matukar galabaice ya fado kasa aikuwa sai birirrikan suka yo masa ca domin su cinye namansa danye, a lokacin ne hankalin gimbiya Hursiyya ya dugunzuma ainun bisa mamaki sai kawai ta ji hawaye ya subuto mata dan ganin Hasnalu zai hallaka.
Ba zato ba tsammani sai kawai taga Hasnalu ya mike tsaye zumbur ya na mai cigaba da yakar burirrikan yana gididdibasu da takobinsa yana mai cigaba da yin kabbara, a wannan lokacin ma sai karfinsa gami da zafin namansa ya ninku fiye da na baya duk kuw da cewar har wannan lokacin jini na zuba a hakarkarinsa inda wannan reshe ya sokeshi.
Wohoho! Nan fa kasuwar daukar rai ta bude, duk inda jarumi Hasnalu yasa gabansa sai dai kaga birirrikan na zubewa kasa matattu, lokacin da wuya tai wuya sai birirrikan suka ga cewar Hasnalu ya kusa karar da su saboda haka sai suka fara ja da baya dan su tsira da rayukansu amman sai jarumi Hasnalu ya rinka kure masu gudu yana rafkesu, sai ga shi girman birirrikan gami da karfinsu duk si ya zama na banza, daman ance in kaji ana ki gudu to fa sa gudu ne bai zo ba.
Nan dai Hasnalu ya cigaba da saran birirrikan sun masu ihu gami da kururuwa suna kum faduwa kasa mattatu a haka dai sai da ya karar da su gaba dayansu, ya zamana cewa ko daya bai tsira da rayuwarsa ba.
A sannan ne jiri ya kashe shi ya fadi kasa sumamme, ai kuwa sai gimbiya Hursiyya ta yi wuf ta fito daga inda take boye ta ruga da gudu izuwa kan Hasnalu, shima aljani Radiyan sai ya fito daga maboyarsu yana waige-waige cikin alamun tsananin tsoro dan gani yake kamar akwai sauran wadannan birirrikan a boye a wajen.
A lokacin ne kuma jarumi Hasnalu ya farfado daga dogon suman da yayi, ko da ya farfado sai ya tsinci kansa bisa cinyar Hursiyya idanunta cike da kwalla, a firgice ya mike zaune zumbur yana mak kallonta cikin mamaki sannan ya dubi raunin dake hakarkarinsa, yaga an samasa magani kuma an daure wajen da kyallen rigarta.
Koda Hursiyya taga Hasnalu ya mike tsaye sai ta kamu da tsananin farin ciki ta dubeshi cikin murmushi mai taushi ta ce godiya ta tabbata ga ubangijinka wanda ya baka nasara da sa'a akan wadannan mugayen burirrika.
Kada jin wannan batu sai jarumi Hasnalu yaji gabadaya tsigar jikinsa ta tashi, nan take a karon farko ya ji a rayuwarsa wata ya mace ta burgeshi saboda dalilai guda biyu; dalili na farko kuwa shine ganin kwalla a cikin idanun Hursiyya a lokacin daya farfado daga dogon sumar d yayi wanda hakan ya tabbatar masa da cewa tana cikin tsananin damuwa bisa halin d ya shiga, dalili na biyu shine tunda ya shigo wannan nahiyoyi tsawon shekara guda da rabi ya ratsa ta cikin birane da garuruwa amman bai taba haduwa da wanda yayi yabo ga ubangijinsa ba face gimbiya Hursiyya kawai sai Hasnalu yaji kaunar Hursiyya ta shigeshi farat daya, abinda ko a mafarki bai taba faruwa a kansa ba.
Cikin murmushi Hasnalu ya dubi Hursiyya ya ce madalla da wannan yar sarki wacce ta ceto rayuwata, hakika bna an irin godiyar da zanyi maki ba, domin n lura da irin jinin d ya zuba a jikina mai yawa ne, kuma inba dan kin tsaidashi ba da wata kila yanzu na dade da mutuwa.
Koda jin haka sai itama ta maida mashi da martanin murmushi ta ce ai asarar irinka guda daya a cikin al'umma gwara ayi asarar gari guda. Da farko dai kaga kai kyakkyawa ne irin wanda sai an tara kyawawa dubu ba'a samu kamarka ba, kai gwarzo ne a cikin jarumai mai jarumtakar da sai an tona, domin na fahimci cewar ko dan uwana sarki dujalu iyakar jarumtakar da zai iya kenan, ga dukkan alamu ma sai k fishi tunda kai ka dogara ne da zallar karfinka baka tsafi. Ya kai wannan jarumi kayi sani cewa kaine saurayi na farko daya taba burgeni a rayuwata, kuma in banda dan uwana sarkk Dujalu babu wani namiji da jikina ya hadu da nasa, ni kaina nayi matukar mamaki bis yadda aka yi har naji na aminta da kai tamkar ka kasance dan uwana na jini.
Duk wannan hira da su Hasnalu ke yi aljani Radiyan na zaune a gefe daya a bayansu, yana mai kallonsu da sauraronsu amman zuciyarsa sai faman tafarfasa take tamkar zata kone, saboda ya fahimci cewar da sannu jarumi Hasnalu zai ja ra'ayin gimbiya ta karbi addininsa, kuma akwai alamun cewa zasu iya fadawa cikin tarkon soyayya.
Nan fa hankalin aljani Radiyan ya dugunzuma ainun ya fara tunanin hanyar da zai bi ya lalata wannan alaka tasu, ko kuma ya dauke Hursiyya su bace wa jarumi Hasnalu.
Hasnalu ya dubi gimbiya Hursiyya ya ce yake wannan yar sarki kiyi sani cewa nima kece mace ta farko da jikinta ya taba haduwa da nawa, wanda yin hakan haramun ne a addinina kasancewarki ba muharramata ba, babu wani dan adam ko aljan daya taba ceton rayuwata sai ke, a gaba daya nahiyoyin dake nan kece mutum ta farko da tayi yabo ga ubangijina. Yanzu dai abinda nake so ki sani shine duk wannan gagarumar jarumtaka da kikaga nayi har na samu nasarar kashe wadannan birirrikan ba wai tsagwaron karfin damtsena bane ko dabarata ba face taimako daga ubangijina. Shin yanzu kin gamsu cewa ubangijina shine na gaskiya ko kuwa har sai na cika sharadi nayi abubuwa al'ajabi guda uku kamar yadda kika bukata a baya?
Sa'ad da gimbiya Hursiyya ta ji wannan tambaya sai ta juya da baya ta dubi aljani Radiyan shi kuma sai yayi mata nuni da idanunsa kar ta ce ta gamsu.
Hursiyya ta juyo ta fusknaci Hasnalu cikin murmushi tace da shi mu bi dai a sannu a hankali har ka cika ragowar sharadin. Koda jin haka sai Hasnalu yayi murmushi sannan yace yake gimbiya ki kasance mai ra'ayin kanki ba wai ra'ayin wani ba, kuma ki tabbatr kinyi aiki da gaskiya ba da son zuciya ba, yanzu sai ki tashi mu cigaba da tafiya.
Koda jin haka sai Hursiyya ta dubi Hasnalu cikin yanayin tsoro ta ce da shi ai abune mai hadari mu cigaba da wannan tafiya a haka, kana tare da danyen ciwo a jikinka, akwai bukatar ka yi jinya koda na tsawon sa'a goma sha biyar ne.
Koda jin haka sai Hasnalu yayi murmushi sannan ya ce yanzu kina nufin kice idan na cigaba da tafiya da wannan ciwon a haka wani abu zai taba lafiyata kenan?
Hursiyya tace ai bama abinda zai taba lafiyarka ba ma, idan har ka cigaba da tafiya a haka zaka ma iya rasa rayuwarka gabadaya.
Koda jin haka sai Hasnalu ya sake yin murmushi a karo na biyu sannan ya karanta wata addu'a ya tofa akan raunin nasa sannan ya mike ya dubi Hursiyya da aljani Radiyan ya ce to ni dai zan cigaba da tafiya, ko dai ku tashi mu tafi tare ko kuma ku sameni a gaba, yana gama fadar hakan sai ya kama hanya ya nausa cikin wannan kogon dutsen mai duhu wnada wadannan birirrikan suka fito daga ciki.
Koda ganin haka sai aljani Radiyan da Hursiyya suma suka tashi da sauri suka bi bayanshi. Sai da suka shafe rabin sa'a suna tfiya a cikin wannan kogon dutsen amman basu hadu da komai ba face kwarangaloli na sassan jikin biladama wanda wadannan birirrika suka kashe, a sannan ne suk gane cewa ashe wannan kogon dutsen gari ne guda na birirrikan. Suna fitowa daga cikin kogon sai kuma suka tsinci kansu a wani dajin daban ba wancan ba, kawai sai suka hango cibiyar tekun bahar sufiya ruwana nata fanjam-fanjam kamar zai zo inda suke ya shafesu.
Nan take kuma suka rinka jiyo ihu gami da kururuwar mazaje acan kasa-kasa alamar cewar har yanzu fa ana kafsa wannan azababben yakin acan bakin tekun. Koda iyo wannan sauti sai Hasnalu ya waigo da sauri ya dubi Hursiyya kawai sai yaga ta tsugunna a kasa tana haki saboda gajiya, shi kuwa aljani Radiyan ya koma gefe daya ya zauna harma ya fada cikin kogin tunani.
Hasnalu ya matsa kusa da Hursiyya ya dubeta y ce ga dukkan alamu dai muna daf da riskar inda ake yin wannan yaki, dan haka sai kuzo mu karasa da sauri.
Koda jin haka sai Hursiyya ta dubeshi cikin alamun tsananin mamaki tace wai kai wane irin mutum ne wanda baya gajiya, ni abinda ma yake bani mamaki game da kai shine yadda ka kasa sarewa alhalin cewa kana dauke da rauni a jikinka, koda ta zo nan a zancenta sai ta dubi raunin nasa take kuwa ta sha mamaki, domin kuwa raunin ya kame harma ya bushe kai kace dama ya dade a jikinsa ba sabo bane.
Al'amarin da yayi matukar girgiza Hursiyya kenan, ta dubi jarumi Hasnalu ta ce yaya aka yi wannan raunin naka ya warke da gaggawa haka, tamkar ma ba yau ka same shi ba?
Koda ya ji wannan tambaya sai Hasnalu yayi murmushi ya ce wannan shine iko irin na ubangijina, dan haka yanzu na cika sharadi na biyu da ke tsakaninmu saura sharadi na uku wanda daga shi sai ki karbi addinina kamar yadda muka yi alkawari.
Hursiyya ta maida mashi da martanin murmushi tace tabbas zancenka dutse ne.
Lokacin da aljani Radiyan ya ji wannan batu sai hankalinsa ya kara dugunzuma ya tabbatar da cewa lallai dan bai dauki matakin gaggawa ba akan jarumi Hasnalu to fa duk shirinsa sai ya tarwatse.
Hasnalu ya zauna daf da Hursiyya ya dubeta ya ce ina ganin dai cewa yanzu tafiyar da ta rage mana mu riski bakin tekun nan da ake wannan yaki baya wuce ta rabin sa'a ba, tunda daga inda muka baro zuwa kin tekun kunce mani tafiyar sa'a guda ce kuma gashi mun shafe kusan rabin sa'a a iya tafiyar da muka yi.
Jin hakan ne yasa Hursiyya ta yi murmushi sannan tace tabbas gama babbar alama na muna iya jiyo sautin ihun mazaje daga can filin dagar gami da karafkiyar karafa, sai dai fa abinda ya bani mamaki shine ban ji karaji gami da rurin aljanu ba wanda shine ya kamata yafi amsa kuwwa da cika kunne.
Koda jin wannan batu sai Hasnalu ya jinjina kai sannan ya ce aikuwa indai akwai aljanu a wannan yaki kuma ya zamana cewar bama jiyo rurinsu gami da karajinsu to babu mamaki an kashesu gabadayansu.
Hursiyya ta jinjina kai ta ce kwarai kuwa na yarda da zancenka, idan kuwa haka ne kaga kenan yakin yazo da sauki tunda yanzu ya rage tsakanin mutane kawai, kuma lallai ana daf da kareshi don haka zaifi mana kyau mu tashi mu karsa can din da sauri.
Koda jin wannan batu sai aljani Radiyan ya takarkare ya bushe da wata mahaukaciyar dariya, al'amarin da yasa Hasnalu da Hursiyya suka juyo da sauri kenan suna masu kallonshi cike da mamaki, Hursiyya ta ce da shi ya kai Radiyan ina dalilin wannan dariya taka ?
Maimakon Radiyan ya bata amsar tambayarta sai ya sake bushewa da dariya a karo na biyu, lokacin guda kuma ya murtuke fuska ya ce yanzun nan nima nayi bincike a cikin madubin tsafina naga cewa lallai an kashe gaba daya aljanun da suke a wannan tsibiri na kogin bahar sufiya, a halin yanzu babu sauran aljani a wannan daji gabadaya face ni da kuma Aljani Raugatul Agwanu, yanzu kuma gashi zan riga Raugatul Agwanu zuwa bakin wannan teku, tunda shi yana can yana bacci bai farka ba, tunda a halin yanzu sihirin tsafi ya daina aiki acan filin yakin babu wanda ya isa ya ganni, kunga kenan zan iya zuwa na shiga cikin takun salin alin ba tare da wani ya ganni ba na lalubo inda takobin take, da zarar na daukota shikenan na zama sarkin duniya kuma yanzu zan bace maku da gani babu yadda zaku yi da ni.
Babban burina na biyi shine na mallakeki ki zama abar debe mani kewa kamar yadda shalbirat ta debe wa aljani Raugatul Agwanu kewa tsawon shekaru gom sha bakwai, kinga idan na mallakeki babu mai iya rabamu har abada sai dai ajali tunda na mallaki takobin Saiful Lujara na zama sarkin duniya.
Sa'ad da aljani Radiyan yazo nan a zancensa sai takaici ya lullube gimbiya Hursiyya har idanunta suka ciko da kwalla, ta dubeshi tace ashe daman yaudarata ka yi kenan, wannan shine burinka a cikin wannan tafiya ban sani ba, hakika ka cika maci amana shugaban azzaluman duniya.
Koda jin haka sai aljani Radiyan ya cigaba da kyalkkyala dariyar mugunta.
Ita kuma gimbiya Hursiyya sai ta kama kukan bakin ciki, kawai sai ta ji jarumi Hasnalu ya kira sunan aljani Radiyan yana mai daka masa tsawa gamk da cewa ya kai Radiyan kayi dukkan abinda kaga dama amman ka sani cewa da izinin ubangijina ba zaka samu nasara ba.
Koda gama fadin haka sai Hasnalu ya zauna a kasa dirshan gaban gimbiya Hursiyya kuma ya lankwashe kafafunsa sannan ya runtse idanunsa ya kama karanta wata addu'a ta neman taimakon Allah a cikin zuciyarsa.
Shiko aljani Radiyan sai ya cigaba da kyalkkyala dariyarsa ta mugunta, a lokacin ne kuma hankalin gimbiya Hursiyya ya dugunzuma ainun, tsoro ya baibayeta kuma jikinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login