Showing 57001 words to 60000 words out of 71576 words

Chapter 20 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt

maka cewa raina da jikina duk na sallama su a ceton taka rayuwar. Hakika ni ma yanzu na gane cewa ba mu da wani zabi wanda ya fi mu tunkari masifar tun gabannin ta tunkaromu.

Abu daya kawai da ma nake shakka, kuma ba wani abu bane face karfin sihirin tsafin Sarauniya Zubaina, to amma a yanzu haka ma wata dabara ta fado mini zan san abin da zan yi akan hakan.

Ai Sarauniya Zubaina ta yi sake Dan Zaki ya girma, domin ta raini ajalinta da hannunta.
Tun da na fara girma na yi hankali kuma na gano cewa Sarauniya Zubaina abokiyar gabata ce ba masoyiya ta ba na shiga bincike akan sanin sirrinta. Ban san dukkan sirrinta ba, amma na san wadansu da yawa.

Baya ga wannan, ina mai tabbatar maka da cewa zan yi matukar ba ka mamaki a wannan Yaki da za mu je mu yi a gidan Sarautar tamu.
Yanzu dai sai mu gaggauta shiryawa domin mu san abin yi.

Nan take suka fara shirya kayan Yaki. Yaldisa ta sake komawa cikin gari a cikin bad-da-kama ta shiga kasuwa ta siyo Kwari da Baka gami da wadansu irin sinadarai na kayan Yaki wadanda ita ta san abin da za ta yi da su, sannan ta siyo wa Jarumi Shaddadu riga da wando na karfe gami da garkuwa ta karfe, ita ma ta siyowa kanta kayan karfen sannan ta sake komawa can dajin cikin wannan Kogon dutse.

Shi kansa Shaddadu da ya ga irin kayan Yakin da Yaldisa ta siyo musu sai da ya yi matukar mamaki domin da yawa daga cikin irin kayan Yakin ko a gidan Sarautar Birnin Kufa bai taba ganin irin su ba tun daga yarintarsa har izuwa girmansa.

Sai da Yaldisa ta shafe sama da sa'a guda tana koyawa Shaddadu yadda za su yi amfani da wadannan sinadaran na kayan Yaki.

Bayan nan ne suka sanya wadannan kayan Yakin na karfe a jikinsu, Shaddadu ya rataya Takobinsa a baya kuma ya zuba wukake a jikinsa gami da Adduna guda biyu kuma ya goya jakar sinadarin kayan Yakin a bayansa.

Ita kuwa Yaldisa wannan Baka ta rataya a bayanta gami da jakar Kwari wacce ke dauke da kibiyoyi masu yawan gaske.

Ita dai wannan Baka ta Yaldisa Baka ce ta musamman wacce ta kasance katuwar gaske kuma zaren jan ta mai matukar tauri ne da kauri, sai kato ya cika kato sannan zai iya tabe ta.

Hakika duk wanda ya ga Jarumi Shaddadu da Yaldisa a wannan shiga dole ne ya razana domin shigar ta kara musu kwarjini ainun, musamman ma shi Jarumi Shaddadun wanda kirarsa ta kasance ta sadaukai, kuma kirar ta sake bayyana a fili karara.

Bayan sun gama kintsawa sai suka yanke shawarar su sauya wuri a cikin dajin su je su nemi wani wuri mai duhuwa su biya sai dare ya tsala Sannan su kai MAMAYAR BAZATO izuwa gidan Sarautar.

Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin Jarumi Shaddadu da karuwa Yaldisa bayan ta ceto rayuwarsa a daji sakamakon masifaffen Yakin da ya faru tsakaninsa da Jaruma Ziya'ul Hak.

****

Al'amarin Aljani Maruful Dauwaz kuwa, lokacin da ya rabu da Jaruma Ziya'ul Hak. ya ga cewa ta tafi ta ci gaba da wanann Yaki ita kadai ba tare da taimakonsa ba sai hankalınsa ya dugunzuma ya shiga sake-saken zuci da tunani

Koda ya tuna cewa da shi da Ziya'ul Hak yanzu duk ba su da sauran karfin sihirin tsafi a jikinsu tunda shi ma an doke shi da Mashin Galilul Haras har ma an balla masa kashin kafadarsa kuma ba shi da tababcin cewa Jarumi Shaddadu na tare da Mashinsa sai hankalınsa ya dugunzuma kuma zuciyarsa ta karaya da sa ran samun nasara akan Shaddadu.

Nan take ya yanke shawarar ya koma can. dajin da suka baro Sarki Laffaru da matarsa ya sanar da su halin da ake ciki domin idan suna da wata dabarar da za a yi a cim ma buri su fada masa.

Ai kuwa nan take ya bude fuka-fukansa ya tashi sama ya luluka a cikin gajimare yana mai tsala azababben gudu na gaban kwatance domin ya isa can dajin akan lokaci.

Kash! Rashin sani ya li dare duhu. Inda Aljanı Maruful Dauwaz ya san gaibu da bai taba yin wannan ganganci ba na komawa dajin da su Sarkı Laffaru suke domin ya sanar da su halın da 'yarsu Ziya'ul Hak ke ciki ba.

**
A can Birnin Kufa kuwa, tun daga ranar da Jarumi Shaddadu ya bar gida sai Sharlisa ta rinka yin mugayen mafarkai a kansa tana yawan ganinsa a cikin garari da tashin hankali amma a duk sa'adda ta tuna cewa ai yana tare da Mashin Galilul Haras sai hankalinta ya kwanta don ta san cewa babu wani tsautsayi da zai taba lafiyarsa ko rayuwarsa.

Lokacı da ta ci gaba da yin irin waďannan mugayen mafarkai ba kakkautawa sai hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa sukuni saboda haka sai ta dauko madubin tsafinta ta shiga bincike.

Ai kuwa nan take ta ga duk abin da ya faru ga Shaddadu tun daga farkon tafiyarsa kawo izuwa saukarsa a Birnin Sarauniya Zubaina da irin bakin artabun da ya yi da Ziya'ul Hak da kuma halin da ake ciki na yanzu cewar, ya yi shirin Yaki shi da YALDISA su biyu kacal! Za su je su Yaki Sarauniya Zubaina da Ziya'ul Ilak a cikin dare.

Koda gama ganin wannan alamari sai hankalin Sharlisa ya dugunzuma ainun, bakin ciki ya turnuke ta, nan fa ta yanke hukuncin ta tashi ta yi shiri ta tafi izuwa Birnin Sarauniya Zubaina domin ta kai wa danta dauki.

Amma babban tashin hankalin shi ne, karfin sihirin tsafinta ba zai iya kai ta garin ba a cikin yıni daya ba dole sai ta shafe kwana uku tana tafiya, ke nan kafin ta je komai zai iya faruwa, ma'ana za a iya kashe mata da a ruguza ma ta dukkan shirinta da burinta.

Nan take ta aiyana a ranta cewar kamata ya yi ta fara biyawa ta jejin da su Sarki Laffaru suke ta yake su ta kashe su shi da matarsa kawai domin ta fara rage takaici, amma kuma da ta tuna cewa ba za ta iya shiga dajin da suke ha sai ta sake kamuwa da tsananin bakın ciki. Babu ma abın da ya fi daga mata hankali sama da batan Mashin Galilul Haras.

Nan take Sharlisa ta shiga cikin dakin halwar tsafinta ta yi gagarumin shirin Yaki da tafiya sannan ta fito ta hau kan wani sabon Tsuntsun tsafi ya tashi da ita sama suka luluka a cikin gajimare.

***

Lokacin da Aljani Maruful Dauwaz ya isa dajin da su Sarki Laffaru suke, koda suka hango shi yana saukowa kasa shi kadai babu Jaruma Ziya'ul Hak a tare da shi sai hankalinsu ya dugunzuma ainun nan take suka mike tsaye zumbur! daga bakin bukkarsu suka rugo izuwa gare shi suka tambaye shi ina 'yarsu take, a cikin hadin baki. Koda jin wannan tambaya sai Aljanı Maruful Dauwa ya sunkui da kansa kas cikin alamun tsattanin damuwa ya kasa cewa komai. Al'amarin da ya dugunuma hankalin Laffaru da matarsa ke nan suka fara tunanın ko Ziya'ul Hak ta mutu ne. Cikin fushi Sarki Laffaru ya dora hannunsa a kan kafadar Marutul Dauwaz ya daka masa tsawa ya ce, ya kai Sarkin Jaruman aljanu, yaya za mu ba ka amanar yarmu amma ka dawo ka yi mana shiru ba ka sanar da mu halin da take ciki ba? Da jin wannan batu sau Aljani Maruful Dauwazya dago kai ya dube su ya ce, yarku tana nan a cikin Koshin lafiya kuma a raye, amma tana cıkın TSAKA MAI WUYA. Ni kaina na hadu da tashin hankali wanda ya fi Karfina.

Nan take Maruful Dauwaz ya kwashe labarin duk abin da ya faru a can Birnin Sarauniya Zubaina ya shaida musu, har da irin BAKIN ARTABUN da aka yi tsakanin Jarumi Shaddadu da Ziya'ul Hak, har aka buga masa Mashin Galilul Haras a kafada kashınsa ya karye ya zube kasa sumamme, kawo izuwa lokacın da Sarauniya Zubaina da Ziya'ul' Hak suka hada kai domin su hallaka Shaddadu amma duk da haka babu tabbacin Shadaddu yana tare da Mashinsa ko baya tare da shi.

Koda jin wannan batu sai hankalin Sarki Laflaru da na matarsa ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe suka rasa abin da ke musu dadi.

Nan dai Laffaru da matarsa suka koma gefe daya suka shiga yin shawara a tsakaninsu inda Ramlatul Siyam ta dubi Sarki Laffaru cikin tsananın damuwa sa'adda Kwalla ta cika idanunta ta ce, ya kai mijina, ka yi sani cewa idan har yarmu ta kasa hallaka wannan yaro Shaddadu bisa taimakon Sarauniya Zubaina to fa shi zai sami nasarar hallaka su, da zarar ya hallaka su kuwa zai nemi duk inda muke ya zo, kuma tunda yana tare da Mashin Gaililul haras zai iya zuwa har nan ya yi mana kisan gilla ko kuma ya kama mu ya kai mu har can Birnin Kufa gaban Sarauniya Sharlis ta yi mana kisan wulakanci. Da dai haka ta faru gare mu gwara mu bi Aljani Maruful Dauwaz i zuwa Birnin Sarauniya Zubaina a yi-ta-ta-kare a gaban idanunmu.

Ni kam a yanzu na sami nutsuwa guda daya da ya zamana cewa sihirin tsafin Shaddadu da na Ziya'ul Hak duk sun daina tasiri. Fatana kawai shi ne ya zamana cewa Shaddadu bai ga Mashinsa ba, babu mamaki ruwa ya batar da Mashin a cikin Tekun.

Lokacin da Ramlatul Siyam ta zo nan a zancenta sai Sarki Laffaru yai shiru yana tunani har izuwa lokaci mai dan tsawo daga can sai ya baro wajen Ramlatul Siyam ya je wajen Aljani Maruful Dauwaz ya ce, to yanzu ka zo ka sanar da mu halin da 'yarmu ke ciki kuma ka sani cewa babu wani taimako da za mu iya yi mata tunda har yanzu ni ba ni da karfin jikina.

Na rasa jarumtaka tun daga lokacin da Sharlis ta sihirce ni kuma na rasa dukkan karfin sihirina na tsafi. Kai wanne hukunci ka yanke wa kanka? Shin ka dawo ke nan ba za ka ci gaba da tsare lafiyar 'yata ba?

Koda jin wannan tambaya sai idanun Maruful Dauwaz suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa ya dubi Sarki Laffaru ya ce, ya kai wannan Sarki, ka yi sani cewa muddin ina numfashi a doron kasa ba zan iya nisantar 'yarka ba domin a dalilinta ne kadai na yarda na ci gaba da rayuwa a doron kasa saboda tana matukar kama da masoyiyata.

Babban abin bakin cikina wanda zan mutu da shi a cikin raina kuma wanda shi ne burina na karshe shi ne rashin sanin inda wasiyyar masoyiyata take. Inda zan ga wannan wasiyya ta isa ta debe mini kewar rashin masoyiyata domin zan koma Kogon Darul Ikisina na karasa rayuwata ya zamana cewa kullum dare da rana ba ni da wani aiki sai karanta wasiyyar tata har izuwa ranar da wa'adina zai cika. Tun da dai yanzu ban ga wannan wasiyyar ba dole na ci gaba da rike alkawarina na kare lafiyar 'yarka da rayuwarta iyakar karfina koda a sanadın hakan ne zan sadu da ajalina.

Ina so ka sani cewa na zo ne na sanar da ku halin da ake cíki a matsayinku na iyayen Ziya'ul Hak don kada mu riski ajalinmu ni da ita ba ku san abin da ya faru ba a gare mu, sannan kuma na yi tunanin cewa ku bil'Adama kuna da hikima da basira irin wacce mu aljanu ba mu da ita, babu mamaki kuna da wata dabarar wacce za ta iya tserar da mu daga sharrin Jarumi Shaddadu.

Lokacın da Aljani Maruful Dauwaz ya yo nan a zaneensa sai Sarki Laffaru ya sunkui da kansa kas ya shiga tunani mai zurti har izuwa lokaci mai dan sawo daga can sai ya dago kai ya dubi Aljani Marutul dauwaz ya ce, Masu ya magana sun ce faduwar gaba asarar namiji ce, sau tari idan masifa ta tunkaro mutum to bai kamata ya zauna jiranta ba gwara ya je ya tare ta domin idan ya bari ta zo ta riske shi har inda yake za ta yi masa kwaf daya ne.

Tabhas yanzu zan yi amfani da shawarar matata, kuma akwai wata dama guda daya wacce idan har na same ta a cikin gıdan Sarautar Sarauniya Zubaina to ta karfin dantsena da na sihirina zai iya dawowa.

Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Maruful Dauwaz ya ce, yanzu kai dama ka san hanyar da za ka iya dawo da martabarka amma ba ka bi ba tun tuni?

Sarki Laffaru ya gyada kai cikin alamun takatci har kwalla ta zo masa sannan ya ce, da ma Boka Muzaffar ya sanar da ni cewa hanya biyu ce zan iya bi na sami waraka daga sharrin Sharlis.

Hanya ta farko ita ce, ta auren Ramlatul Siyam mu haifi 'yar da za ta iya kashe Shaddadu da mahaifiyarsa. Hanya ta biyu kuwa ba zan taba samunta ba face a wajen mashahuriyar Sarauniya wacce ta kasance gagarumar matsafiya mai mulkin babban Birni wanda ya kai Birni na Kufa.

Bisa labarin da ka ba ni na Sarauniya Zubaına na fahimci cewar duk tana da wadannan abubuwa wadanda Boka Muzaffar ya siffanta mini.

Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube Aljanı Marutul Dauwaz ya ce, ai kuwa idan karfin dantsenka da na sihirinka suka dawo shi ke nan mun tsira daga sharrin Sharlis da danta, musamman idan ba sa tare da Mashin Galilul Haras. Ka sanar da ni hanyar da za ka bi ka dawo da komai naka domin na san irin taimakon da zan iya ba ka.

Koda jin wannan batu sai Sarki Laffaru yai ajiyar zuciya yace, ai da zarar na furtawa wani al'amarın komai ya rushe domin ka'idar sihirin ke nan.

Yanzu dai bari mu yi shiri ni da matata mu zo ka kai mu can Birnin Sarauniya Zubaina domin a yi ta-ta kare. walau mu sami nasara akan makiya ko kuma su sami nasara akanmu kowa ya huta da fargaba.

Koda gama fadin hakan sai Sarki Laffaru ya juya ya nufi inda Ramlatul Siyam take ya sanar da ita cewa ta shiga cikin Bukka ta dauko musu kayansu domin su tafi i zuwa can inda 'yarsu take. Koda jın haka sai farinciki ya lullube Ramlatul Siyam ta ruga i zuwa cikin Bukkar tasu ta debo musu kayansu ta fito.

Ba tare da bata wani lokacı ba suka hau kan Aljani Maruful Dauwaz ya tashi da su sama ya luluka a cikin gajimare yana tsala azababben gudu.

***
A can Birnin Sarauniya Zubaina kuwa, Jarumi Shaddadu da Yaldisa na labe a cikin duhuwar wadansu ciyayi da ke nesa kadan da gidan Sarautar suna hangen Dakarun da ke kai kawo a kofar gidan don tabbatar da tsaro, suna tunanin hanyar da ya kamata su bi su samı nasarar shiga cikin gidan Sarautar a lokaci guda farat daya.

Bayan sun shafe 'yan dakiku suna tunanı sai dabara ta fado wa Jarumi Shaddadu ya dube ta ya ce, abin da za mu yi yanzu kawai shi ne, mu yi fitar burgu da gudu mu afkawa wadancan Dakarun da ke bakin kofar gidan Sarautar.

Da zarar mun tarwatsa su zan dawo da baya ki tsaya a gaban kofar gidan Sarautar ni kuma sai na rugo da gudu, ki hada tafin hannayenki biyu a waje guda na taka su da kafa daya ke kuma sai ki cilla sama na haye katangar gidan na fada ciki, ina fadawa zan tarwatsa masu tsaron bakin kofar daga ciki ki shigo ciki, a sannan ne za a fara wannan gagarumin Yaki.

Koda jin wannan batu sai murna ta kama Yaldisa. Nan take su biyun suka mike zumbur! A lokacı guda suka zare makamai suka ruga da azababben gudu izuwa kan masu gadin da ke kofar gıdan Sarautar.

Kafin daya daga cikin masu gadin ya dauki wata katuwar guduma ya doka akan wani babban Bandiri tuni Yaldisa ta daka tsalle sama ta doki fuskarsa da guiwarta. Nan take yai sama ya fado Kasa sumamme.

Shi kuwa Shaddadu sai ya afkawa sauran masu gadin wadanda adadinsu ya kai goma sha daya a lokacin da suka yi masa rubdugu. suna kawo masa sara da suka ta ko ina.

Maimakon shu ma ya yake su da makami sai ya rinka kaucewa harin nasu cikin wani irin bakın zafin nama na al'ajabi ya rinka gabza musu naushi. Duk wanda ya nausa sau daya sai ka ga ya zube kasa sumamme, Kafin cikar dakika ashirin sun gama bazar da Dakarun gaba daya

Faruwar hakan ke da wuya sai Shaddadu ya koma da baya ya rugo da gudu ya taka hannayen Yaldisa ta cilla shi sama sai ga shi ya haye katangar gidan Sarautar ya dirga ciki. Yana dira ya tarwatsa masu gadin yai sauri ya bude kofar Yaldisa ta shigo da sauri ta fara harbo Dakarun da ke sama da kibiyoyinta suna fadowa kasa suna ihu, shi kuma Shaddadu ya ci gaba da gudu yana sara da sukar Dakaru a lokacin da Dakaru suka fara tuttudowa ta ko ina. Nan fa gidan Sarautar ya hargitse ya yamutse da haniniya, ihun Dakaru gami da karafkiyar karafa.

Dabarar da su Shaddadu suka yi ita ce, ba su yarda sun tsaya a waje daya ba, suna Yakin ne suna gudu suna durfafar can gidan Sarautar suna tarwatsa Dakarun da karfin tsiya ba su yarda sun tsaya a waje daya ba.

A wannan lokaci ne Jarumi Shaddadu ya cika da tsananin mamaki bisa ganin irin gagarumar jarumtakar da Yaldisa ke yi.

Nan fa kansa ya daure ya kama zancen zuci yana mai cewa, yaya aka yi Yaldisa ta zama gagarumar mayakiya haka alhalin tana rayuwa ko yaushe a gidan abincin Sarauniya Zubaina kuma ba ta kasance daya daga cikin manyan garin ba?

Haka dai Yaldisa da Jarumi Shadaddu suka ci gaba da ragargazar Dakarun gidan suna daďa kutsawa can ciki, kuma Yaldisa ce akan gaba tun da ita ce ta san hanyar da za a bi a isa har can inda turakar Sarauniya Zubaina ta ke. Da ma tun kafin su shigo cikin gidan Sarautar Yaldisa ta gargadi Jarumi Shaddadu akan cewar kada ya kuskura ya bari a kama su a tare ko kuma su yi arba da Zubaina a tare tunda za ta iya hallaka su farat daya da karfin sihrin tsafinta.

Bisa wannan dalili ne Jarumi Shaddadu ya rinka bayar da 'yar tazara tsakaninsa da Jaruma Yaldisa, burinsa kawai shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login