Showing 48001 words to 51000 words out of 71576 words

Chapter 17 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt

dauki takobinsa ya nufi bakin tekun bahar sufiya kai tsaye ba tare da shakkar komai ba, har ma yana ji a cikin ransa cewa cikin kankanin lokaci zai iya karar da duk aljanin da suke cikin wannan teku kuma ya dauko takobin Saiful Lujara.
Nan dai y shiga cikin tekun ya nutse can cikin karkashinta.
Faruwar hakan keda wuya sai Sarki Maharaz ya dubi jarumi Hasnalu cikin murmushi ya cw da shi ya kai wannan babban jarumi mai daraja, wanda ya fitar damu daga cikin duhu izuwa haske, maza ka shigar damu 2annan addini naka mai daraja, kamar yadda ka shigar da Hursiyya.
Kafin jarumi Hasnalu ya bude bakinsa sai kawai suka ji wata irin iska mai karfi ta taso masu har tana neman wujijjigasu, sai da takai cewa sun rike hannayen juna dan kada iskar tayi sama da su, katsam kuma sai guguwar ta rikide ta zama wani gwabjejen aljani wanda girmansa ya ninka na aljani Raugatul Agwanu sau bakwai, gangar jikinsa ta rufe gabas gabadaya.
Koda sarki Maharaz yayi arba da wannan aljani sai ya kamu da tsananin tsoro ya durkusa a kasa bisa gwiywoyin, ba wani bane wannan aljani face aljani darbuza, gunkin da ake bauta mawa acan birnin sarki Maharaz.
Darzuba ya dubi sarki Maharaz a fusace ya daka masa tsawa ya ce ashe yanzu duk taimakon da muka dade muna yi maka tsawon shekara da shekaru ya zama na banza, mune muka doraka akan karagar mulki, muka baka arziki mai yawa, kuma muka daukaka amman kuma shine yanzu zaka yi mana butulci kadaina bauta mana ka koma bautar wani...?
Kafin aljani darzuba ya karasa kalmar dake bakinsa tuni jarumk Hasnalu ya tari numfashinsa ya daka masa tsawa yana mai cewa kai tsohon kafiri, babban matsafi kuma mayaudari kayi sani cewa kai ba komai bane face bawan ubangijin musulunci domin shime ya halicceka, shekara da shekaru kana yaudarar sarki Maharaz da jama'arsa kana shiga cikin gunkin da suke bauta mawa kana magana da su a matsayin ubangijinsu, to ka sani cewa yau dubunka ta cika, kuma asirinka ya tonu, ina mai kiranka daka tuba ka daina kiran kanka a matsayin ubangiji ka mika wuya ga ubangijin musulunci wanda shine ubangijin komai da kowa.
Koda jin wannan batu sai aljani Darzuba ya bushe da wata mahaukaciyar dariya wacce ta cika dajin gaba daha da amsa kuwwa, dan haka dole kowa ya rinka toshe kunnuwansa. Lokaci guda kuma darzuba ya tsuke fuskarsa yana mai daka wa jarumi Hasnalu tsawa yana mai cewa kai karanin kwaro, karyarka tasha karya, fiye da shekaru dubu ina fafawa da ire-irenka amma basu taba samun nasara akaina ba, saboda haka kalma yanzu zanyi maka kisan gilla a gaban wadannan mutane, domin su zama sheda akan cewa nine abin bauta mafi cancanta.
Gama fadin hakan keda wuya sai aljani Darzuba ya wangame katon bakinsa ya frsa wa jarumi Hasnalu wata irin gagarumar wuta. Cikin bakin zafin nama Hasnalu ya daka wawan tsalle ya bar inda yake yana mai neman taimakon Allah, aikuwa sai wannan wuta ta zuba akan wata katuwar bishiya, wacce kaurinta ya kai kamu arba'in, tsayinta kuwa ya kai zira'i saba'in.
Nan take bishiyar ta nake ta zagwanye kamar an tsom alumin a cikin ruwa, sai tiririn hayaki kawai aka gani na ruburbushin bishiyar.
Koda aljani Darzuba yaga jarumi Hasnalu ya tsallake annan mugun hari nashi, sai ya taso masa a fusace da dukkan karfinsa, aikuwa shima Hasnalu sai ya tare shi rike da takobinsa suka kacame da azababben yaki mai tsananin ban tsoro, a duk sa'ad da takobin Hasnalu ta hadu da takobin aljani Darzuba sai kaji kara kal! Kal!! Tamkar karfe da karfe ne suka hadu, kuma tartsatsin wuta ya tashi, nan fa Imnal, Hursiyya, Maharaz da Mulaifa suka cika da tsananin mamaki bisa ganin irin jarumtakar Hasnalu, domin kwanjin aljani darbuza guda daya ma ya kai kaurin bishiyar katuwar kuka guda uku, amman duk sa'adda ya kai wa jarumi Hasnalu naushi ya kauce tofa duk abinda ya samu walau dutse ko bishiya take suke ragargaje, haka idan ya kai mashi sara ko suka da mugayen faratan hannayensa masu tsananin karfi da tsini kamar zabira to kome suka samu sai dai kaga abin ya dare gida biyu kamar an yanka tsakiyar tuffa, ko kuma kaga abin ya huje tamkar an hujeshi da mashi.
Nan fa suka tayar da hankalin dajin gabadaya, kasa ta kama girgiza wuta ta dinga fallatsa tana dira a wurare da dama tana haddasa gobara, su kansu su Imnal sai da suka gama guje-guje suna neman wajen buya, saboda masifar takai masifa, amman duk da haka basu fasa leken su aljani Darzuba ba domin suga abinda ke wakana. Haka dai aka cigaba da wannan bakin artabu tsakanin jarumi Hasnalu da aljani Darzuba, har dare ya raba sosai amman daya daga cikinsu bai samu nasarar koda lakutar jikin dya ba, da kansu suka ja da baya suk yi cirko-cirko suna haki gami da harar juna. Shi dai aljani Darzuba mamaki ne ya kamashi ainun yadda har aka yi yau ya hadu da shu'umin biladama alhalin tsawon shekara da shekaru yana cin karensa ba babbaka, duk mahalukin da suka yi gaba da gaba da shi walau mutum ko aljan, tofa a cikin abinda bai fi dakika goma ba yake gamawa da shi komai karfin damtsensa dana sihirinsa kuwa, amman yau gashi dan tatsitsin biladama ya gagareshi a kusan sa'a bakwai suna gumurzu.
Shikuwa jarumi Hasnalu tunda suk fara wannan gumurzu addu'a yake yi a zuciyarsa ta neman tsari, dan haka a yanzu sai ya fra karanta addu'ar neman sa'a akan abokin gaba, a daidai wannan lokacin ne aljani Raugatul Agwanu ya iso bakin tekun dauke da boka Sadusa, Halyal da Gimbiya Shalbirat ya dauka a bayan wani katon dutse inda su Imnal suka buya, su duka sai suka fara leke suna hango inda ake wannan gumurzu, abinda suka iya hangowa kawai shine aljani Darzuba da jarumi Hasnalu a tsaye sun fuskanci juna suna kokarin sake kacamewa dda wani sabon fada.
Su jarumi Imnal kuwa sun buyan wasu fogyen bishiyu dake nesa kadan da inda ake wannan fafatawar, suna masu kallon abinda zai faru.
Koda su aljani Raugatul Agwanu suka hango aljani Darzuba da Jarumi Hasnalu su biyu kacal a bakin kogin bahar sufiya sai suka cika da tsananin mamaki, aljani Raugatul Agwanu ya jinjina kai cikin alamun tsoro ya dubi su Sadusa ya ce Tabdijan lallai yau abin babbane, tunda har takai cewa saura manyan mazaje kafai a filin dagar, shin ko kunsan wancan wane aljani ne a tsaye kuwa?
Boka Sadusa ya dubeshi cikin ashin sani yace wane ne? Kuma wane ne biladaman dake fuskantarsa?
Raugatul Agwanu yayi ajiyar zuciya sannan yace ai wancan aljanin shine sarkin sadaukai na dukkan aljanun duniya, kuma shine ubangijin da mutanen sarki Maharaz suke bauta mawa, kimanin shekaru dubu ashirin baya an taba yin yakin duniya na aljanu, wannan sarki na aljanu shine kadai ya baro filin daga a raye, amman sai da gabadaya mayakan sama da aljanu dubu dari tara suka mutu, a tarihin sadaukai da mayaka na duniya ba'a taba samun jarumi kamarsa ba, shi kuma wancan bil'adaman ban taba ganinsa ba, kuma ban taba jin labarinsa, ku duba da kyau gabadaya filin yakin can ciccike yake da gawarwaki, daga nan ma ina iya hango ruburbushin sassan jikin aljanu dukkaninsu sun kone, ai kawai ina ganin cewa mu tsaya anan mu cigaba da kallo domin muga yadda wannan fada zai kasance tsakanin Darzuba da wancan shaidanin biladama, na tabbata duk akan takobin Saiful Lujara suke fadan, babu mamaki suyi ragas mu kuma mu tsinci dami a kala.
Koda jin wannan batu sai tunanin boka Sadusa ya sauya, shi dai burinsa kawai yazo yaga sarki Dujalu ya mutu ya koma can kasarsa ya sanar wa da yan majalisarsa a bashi babban mukami a masarautar, amman kuma yanzu da yaji batun samun takobin Saiful Lujara a saukake sai ya fara tunanin ya za'ayi ya mallaketa shi kadai, ya shammaci aljani Raugatul Agwanu ya halakashi tunda ya fahimci cewar shi sokone, nan dai ya kudurce a ransa cewa ya saurara yaga yadda karshen wannan gumurzu zai kasance tsakanin aljani Darzuba da bakon jarumin da baisan ko wane ne ba.

Acan karkashin tekun bahar sufiya kuwa lokacin da sarki Dujalu yayi nutso zuwa cikinta yana mai jin tsananin karfi a jikinsa, yana ji tamkar zai iya yakar duniya kaf sai y kama lalube, nan fa ya dinga tafiya irin ta kifi a cikin tekun, da yayi tafiyar tsawon rabin sa'a yaga baiga alamar takobin Saiful Lujara ba, sai ya dawo da baya yayi yamma, haka dai ya cigaba da lalube har ya nufi bnagaren karshe na arewa, aiko yana cikin wannan gudu ne ya hango dandazon wadannan aljanu masu gadin Takobin Saiful Lujara a gaban wata katuwar akwatu ta zinare sunyi mata kawanya a sama da kasa.
Koda sarki Dujalu ya hango ttsananin yawan aljanun nan da kuma kirarsu ta girma da sadaukantaka gami da irin mugayen makaman da suke dauke d shi sai zuciyarsa ta buga karfin gaske yaji tsoro ya darsu a cikin zuciyarsa, amman daya tuna irin shekarun daya bata yana shirye-shirye akan mallakar annan takobi ta Saiful Lujara da kuma tsananin wahalar da ya sha a wannan yakin har yakai ga wannan nasara ta matakin karshe, sai yaji dukkan tsoro ya gushe daga cikin zuciyarsa, yace ai rai ba a bakin komai yake ba muddin akwai biyan bukata, dan haka sai yayi kukan kura y ruga izuwa kan mugayen aljanun da nufin ya tsarwatsasu ya fasa wannan akwatu ta zinare ya dauko takobin Saiful Lujara daga cikinsa, a maimakon aljanun su taso masa gaba dayansu, sai guda daya ne jal ya taso masa suka kaure da zababben yaki, aikuwa suna fara yakin ne sarki Dujalu ya gane kuransa domin tsananin zafin naman ljanin da karfin damtsensa gami da na sihirinsa ya ninka nasa sau bakwai, sai da takai cewa sarki Dujalu baya iya kaiwa aljanin hari sai dai kokarin kare kai kawai d yake yi, gashi dai duk sa'ad da aljanin ya sari jikin Dujalu makamin baya tasiri amman fa jikin nasa yan tsami dan yana shan bugun tsiya. Koda wannan aljanin yaga Dujalu baya jin sara d suka amman yana fahimci yana jin bugu sai ya fara yi masa lugudun naushi a fuska, nan da nan ya hada masa jini da majina sai ga idanun Dujalu sun kunbura sunyi suntum har ma ya fara gani dishi-dishi.
Kaico! Hakika tsananin wuya da wahala ita kw sa yaro ya gudu da kafarsa, ganin cewa zai iya rasa ranshi ne yasa sarki Dujalu ya juya baya da gudu ya taso izuwa saman tekun yana haki kamar ransa zai fita, a sannan ne yayi arba da aljani Darzuba tare da jarumi Hasnalu suna kafsa mummunan yaki a karo na biyu. A wannan karon kowannensu yana iya kare harin kowa gami da mayar da martani cikin tsananin zafin nama na gaban kwatance, saboda wannan bala'in gami da masifa ne yasa dajin ya rikece ya kama girgiza a duk sa'ad da jelar aljani Darzuba ta daki kasa, da kum irin wutar da yake fesowa waje daga cikin bakinsa, sarki Dujalu yayi tunani a cikin zuciyarsa yace Tabdijan yanzu wai nan aljani darzuba ne yake son ya kashe jarumi Hasnalu domin ya samu damar dauko wannan takobi, ni gashi har na samu damar shiga karkashin wannan teku kuma na gano inda takobin take, aiko ya zamar mani dole nayi duk yadda zanyi naga n dauko wannan takobi tun kafin aljani Darzuba ya samu nasarar kashe wannan yaro Hasnalu, koda ya zo nan a zancen zucinsa sai ya sake yin nutso a karo n biyu izuwa karkashin tekun ya nufi inda wannan mugayen ljanun suke a guje cikin tafiya ta yanayin tafiyar kifi, koda aljanun suka sake ganinshi ya durfafosu sai daya daga cikinsu ya sake tararsa, nan fa aka cigbaa da bakin yamutsi, aikuwa sai sarki Dujalu yaji aljanin ya rufeshi da luguden duka ta ko'ina har ma a wannan karon ya kasa karewa, suna cikin wannan hali ne aljanin ya gabza masa wawan naushi a baki, Dujalu ya kurm wani uban ihu gami da kururuwa, take hakoransa na gaba guda uku suka yi fitar burgu daga bakin nasa tare da wani gudan jini.
Cikin rudewa da dimaucewa bisa jin radadin zafi sarki ya juya da baya a guje ya bar wajen, da kyar da sidin goshi ya samu ya taso saman tekun, yayin da yaji kansa ya kumbura yayi suntum gashi jini na yoyo a bakinsa kuma numfashinsa na sarkewa, hakika wuya bata da sabo, bisa dole sarki Dujalu yayi ninkaya ya dawo bakin gabar tekun ya cigaba da numfashi da kyar kamar ransa zai fita, a lokacin ne kuma ya cigaba da zuba wa su aljani Darzuba idanu yana kallon bakin gumurzun da suke yi, har izuwa wannan lokaci su jarumi Imnal suna can sama kan bishiya sum suna hangen gumurzun da ake yi.
Haka suma su aljani Raugatul Agwanu suna nan a labe a bayan wannan dutse suna kallo.
Bayan aljani Darzuba da Jarumi Hasnalu sun sake shafe kimanin sa'a biyu sun wannan fafatawar sai suka ja da baya a karo na biyu suna haki da kallon juna saboda gajiya, nan fa kowannensu ya fara tunanin hanyar da xai bi domin ya samu nasara akan dan uwan gaminsa, a daidai wannan lokacin ne jarumi Hasnalu ya fara yi wa Allah kirari a cikin zuciyarsa yana mai cewa:
Ya Allah kaine sarki kuma mabuwayi gagara misali, Allah kaine mai daukakawa da kuma kaskantawa, kuma kaine kayi gaskiya da karya ka tabbatar da bambancinsu, wanda duk ya bika ya tsira wanda kuma ya kaucemaka to ya tabe, ya Allah idan har jihadin nan da nake dominka ne to ka gaggauta bani sa'a akan wannan shaidanin aljani na halakashi gama fadin hakan keda wuya sai jarumi Hasnalu yaji wani irin gagarumin karfi ya shigeshi wanda bai taba jin kamarsa ba a iya rayuwarsa ta duniya, kawai sai yayi wurgi d takobin hannunsa ya tunkari aljani Darzuba ba tare da shakkar komai ba.
Al'amarin da yayi matukar baiwa Darzuba mamaki kenan, ya fara kyalkkyala dariyar mugunta da kuma murna, dan haka shim sai ya tunkareshi da nufin ya kamashi yayi filla-filla da sassan jikinsa, aikuwa suna haduwa sai aljani Darzuba ya kaiwa Hasnalu cafka da hannunsa ya matse wuyansa da dukkanin karfinsa, amman sai yaga Hasnalu kikam ko motsi baiyiba, kamar ba bai taba shi ba.
Darzuba ya tattaro karfinsa ya gabza wa Hasnalu naushi a fuska, take yan yatsun na Darzuba suka kakkarye ya kwalla ihu gami da durkushewa kasa yana mai yarfar da hannunsa cikin tsananin mamaki.
Cikin zafin nama Hasnalu ya kama dayan hannun na Darzuba ya cisgeshi da karfin tsiya daga jikin kafadarsa, aikuwa sai Darzuba ya sake kwarara wani gagarumin ihu fiye da na farko ya zube a kasa magashiyan, sai ga jini irin nasu na aljanu yana bulbulowa daga cikin dungulmin kafadarsa, Hasnalu yazo kan aljani Darzuba ya daga hannunsa sama ya dunkuleshi sannan ya gabza masa naushi a gadon baya, saboda karfin naushin sai da gadon bayan darbuza ya burme yayin da hannun Hasnalu ya shige ciki, zaro hannun nashi keda wuya sai ga kayan cikin aljani Darzuba suna sulalowa kasa.
Darzuwa ya kwarara wani uban gunji wanda yasa dajin gurgiza gabadaya, sannan ya kama shure-shuren mutuwa, yan dakiku kadan jikinsa ya sandare ya daina motsi.
Koda ganin wannan gagarumin bajinta wadda jarumi Hasnalu yayi sai su Imnal suk sakko daga kan bishiyu da suka hau, suna masu rugowa gareshi cikin tsananin murna suna kuma yi masa jinjina.
Nan take Imnal, sarki Maharaz da Mulaifa suka karbi addini musulunci, Hursiyya ta ruga da gudu izuwa bakin gabar teku inda sarki Dujalu yake kwance magashiyan, koda ta isa gareshi taga yadda kansa ya kumbura sannan ga hakoransa uku sun fita sannan ga jini nan male-male a kan kirjinsa wanda ya zubo daga bakinsa kuma taga yadda idanunsa sukayi luhu+luhu kawai sai ta gashe da kuka tare da fadawa saman kirjinsa suka rungume juna tana mai cewa ya kai dan uwana shin yanzu abinda ya sameka da kuma abin al'ajabi da ka gani da idanunka bisa jarumtakar da Hasnalu yayi da taimakon ubangijin musulunci basu isa hujjar da zasu sa ka karbi addinin Musulunci ba?
Sa'ad da sarki Dujalu yaji wannan tambaya daga bakin yar uwarsa Hursiyya sai ya janye jininsa daga jikin nasa suka fuskanci juna sannan ya danyi guntun murmushi irin na manyan kafirai masu taurin zuciya ya ce haba yake yar uwata ai haryanzu sharadinmu bai cika ba, domin kuwa sai naga Wannan jarumin ya shig cikin wannan taku ya dauko takobin Saiful Lujara sannan zan bayar da gaskiya ga addininsa.
Koda jin wannan batu sai jarumi Hasnalu ya dubi sarki Dujalu ya ce idan har ka amince zaka karbi addinina tabbas yanzu zan shiga wannan taku na dauko takobin daga gagareku dauko da izinin ubangijina. Gama fadin hakan keda wuya sai jarumi Hasnalu ya juy tare da fadawa cikin wannan teku yayi nutso izuwa karkashinta yan mai karanta addu'o'in samun sa'a da neman tsari.
Allahu Akbar yardar Allah tafi ta kowa, wanda duk Allah ya yarda da shi tofa babu mai iya ture shi ko yaga bayansa, sannan kuma babu irin matsayin da bazai iya kaiwa ba, shi kansa jarumi Hasnalu lokacin da yayi nutso izuwa karkashin wannan teku sai ya cika da dumbin mamaki bisa yadda yaga ya cigaba da numfashi tamkar a bisa turba ya ke ba a karkashin ruwa ba, sannan kuma yaji ana tafiya da shi tamkar wani ne ke masa jagora bashine ke sarrafa gangar jikin tasa ba, kuma gudu ake da shi a tsaye tamkar gudun tauraruwa mai wutsiya, cikin dakiku kadan ya hango rundunar wannan miyagun aljanun masu gadin akwatin zinare wacce aka sanya takobin Saiful Lujara a cikinta.
Koda wadannan aljanu suka hango jarumi Hasnalu ya durfafosu cikin wata irin tafiya mai ban al'ajabi, sai suka taso masa gabadaya tare da barin akwatin ita kadai maimakon aljani daya ya raineshi kamar yadda suka yi wa sarki Dujalu. Aikuwa suna haduwa da jarumi Hasnalu suka raina kansu, domin kasu ya rinkayi da karfin tsiya yana kakkaryasu, nan fa aljanun suka rinka wani irin mugun ihu gami da ruri, hatta su jarumi Imnal da suke a can wajen takun sai da ihun aljanun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login