Showing 21001 words to 24000 words out of 71576 words
Chapter 8 - MAZAN JIYA Littafi Na 4 Rubutawa Madakin Gini.txt
cikin dajin cikin sauri shalbirat
ta kama hannun Halyal suka taja shi suka bi
bayan boka sadusa::
Haka dai su boka sadusa suka yi ta yawo a
cikin dajin Darul HusHushul Maut; Shalbirat ta
wucce gaba tana yi musu jagora har suna
mamaki yadda ta lakanci hanyoyin dajin:
Ai kuwa sai suka yi ta ganin abubuwan al ajabi
wanda basu taba tsamamanin zasu gani ba:
Abinda suka gani kuwa shi ne gaba daya
bishiyoyin dajin na yan yan itatuwa ne iri iri
sannan kuma bishiyoyin da ruwa ke zuba daga
cikinsu mai haske da dadin dandano:
Page 115
gaba daya dajin a cikin ni ima yake kuma
kowanne wuri irin tasa ni imar dabam data
gaba:
Duk inda mutum ya shiga ba zai ji zafi ba kuma
ba zai ji sanyi ba sannan a duk inda zaka
kwanta wata irin ciyawa ce a lullbe mai
tsananin laushi kuma hankalo kwance mutum
zai yi kwanciyarsa babu tunanin wani kwaro zai
cijeshi ko kuma wata muguwar dabba zata
kawo masa hari::
Nan take sadusa Halyal da shabirat suka tsinko
yayan itatuwa kala kala masu dadi suka sami
wuri suka zauna suka kama ci suna hira har sai
da suka koshi sannan suka mike suka cigaba
da yawo abinsu:
Shalbirat Dai a wannan rana ji ta yi taamkar an
tsamota daga cikin gagarumar wuta an sanyata
a cikin ruwan sanyi sbd farin ciki::
Haka dai suka wanzu suna yawo har suka gaji
suka kwanta suka kama barci:
Al amarin aljani Raugatul Aguwanu kuwa tunda
ya sha wannan giya yayi tatul kama barci bai
farka ba sai da dare ya raba:
A firgice ya farka zuciyarsa na dukan uku uku:
Cikin hanzari ya mike tsaye ya dauko
madubinsa na tsafi ya shafeshi:
Nan take yaga Hoton Shalbirat Sadusa da
Halyal a cikin dajin a kwance suna ta shara
barci::
koda yaga Shalbirat a cikin cikakkiyar surarta:
ta mutum sai ya razana ainun ya kuma tabbatar
da cewa lallai boka sadusa ya cika hatsabibi
domin shi a tunaninsa baza a taba samun
bokan da zai iya karya wannan asirin ba:
Page 116
Nan dai zuciyarsa ta kama sake saketana mai
gaya masa cewa:
AI KAWAI YANZU TUNDA SU BOKA SADUSA
BARCI SUKEYI YAJE YA KASHESU YA DAUKE
SHALBIRAT YA SAKE MAI DA ITA YAR
MITSITSIYA YA SATA A CKIN KEJINTA:
wata zuciyar kuma sai ta ce da shi::
TO IDAN KUMA KA KASHE WANNAN BOKA
WAYE ZAI TSERAR DA KAI DAGA SHARRIN
SARKI DA ZAI MALLAKI KAYAN YAKIN MAZAN
JIYA?
TABBAS IDAN KA BIYEWA SON ZUCIYARKA
ZAKA YI CIN DARE DAYA NE KUMBURIN CIKI:
ZAI FI KYAU KA TSAYA KA GA IYA KOKARIN
DA WANNAN HATSABIBIN BOKA ZAI YI
MAKA:
haka dai aljani Raugatul Aguwanu yayi ta wasi
wasi acikin zuciyarsa har dai daga karshe ya
yanke shawarar ya jira abinda zai faru a gaba:
Kashe gari da sassafe su boka sadusa suka
farka daga barci kawai sai suka ga aljani
Raugatul Aguwanu
zaune a can gefe daya ya zura masu idanu:
koda suka tashi zaune sai Raugatul Aguwanu
ya risina ga boka sadusa yai gaisuwa sannan
ya dubi shalbirat ya sake duban sadusa yace ya
shugabana anya kuwa bakayi mini gaggawa
ba?
Ai ina ganin cewa bai kamata ka ai da shalbirat
izuwa ainahin siffata ba tun yanzu tunda ban
gamsu da cewar za ka iya warware mini
matsalata ba::
Page 117
zidane kd::
koda jin wannan batu sai boka sadusa ya
murtuke fuska tamkar an aiko masa da sakon
mutuwa ya dakawa Raugatul Aguwanu harara
yace shin kaine ka fini sani abinda yafi dacewa
muyi ko kuwa nine?
Raugatul Aguwanu ya sunkui da kansa kas ya
ce ka gafarceni ya shugabana mantawa nayi::
boka sadusa yai murmushi yace yanzu nake
son ka daukemu mu ukun nan domin mu tafi
izuwa can sansani yaki wato can baki kogin
bahar sufiya :
koda jin haka sai idanun Raugatul Aguwanu
suka zazzaro ya kamu da tsananin tsoro yace
haba ya shugabana ya ya zaka ce na kaimu
izuwa inda ajali yake?
Ina mai tabbar maka dacewa masifar da ke
bakin kogin bahar sufiya a yanzu babu kamarta
a ko ina a cikin duniya::
koda jin haka sai boka sadusa yayi murmushi
sannan yace ai ba wai ina nufin muje har inda
ake yakin bane zaka sauke mu ne acan bayan
kogin bahar sufiya nesa da inda ake fafata
yakin sannan kaje kayi mana leken asiri bisa
abinda ke faruwa::
abinfa nake bukata kawai shine nagane
bangaren da suke samun nasara:
Da zarar na gano hakan akwai a sihirin da zanyi
daga inda muke mu dauko Takobin SAIFUL
LUJA RA a karkashin kogin ba tare da su sarki
dujalu sun sani ba mu bace daga wajen::
kaga kenan sun sha wahalar banza kuma sun
kashe junansu a banza wato kura da shan
bugu gardi da kwashe kudi::
koda boka sadusa yazo nan a zancesa sai
aljani Raugatul Aguwanu ya kura masa idanu
cikin
alamun rashin yarda yai shiru yana tunani da
nazari::
Page 118
daga can sai ya ce kai boka nifa ina ganin cewa
kazo mini da zance na rainin hakali:
Yaza ai kace zaka iya dauko takobin saiful
lujara da karfin sihirinka alhalin wadanda suka
fika karfin sihirin nesa ba kusaba sarki dujalu
da sarki maharaz tuntuni sun kasa daukota?
Koda ma dayansu ya sami nasarar wannan yaki
sai ya sha bakar wahala kafin yagano inda
takobin take acikin karkashin tekun:
Kai ni ga yadda mana sami tarihi cewa aka yi
tsaron dake inda takobin take yafi gaban
hasashen mai hasashe sai dai abinda ido ya
gani kawai::::::::::
ANAN ZANDAKATA SAI KUMA IN ALLAH
YAKAI MU GOBE ZAMU CIGABA:
NAKU HARKULLLU SULEIMAN ZIDANE KD:::
KUYI COMMENT::MUNASON HAKAN:::::
Page din mu....
gawadan da basu karanta farko littafe ba kuzi
yarci wannan page Mai suna Duniyar masoya
littafan yaki only..
👇👇👇👇👇👇👇
Aslm yan uwa ga page dinnmu sai kayi kokari
shiga domin samun Littafe Kala Kala cikin blue
dinnan Na kasa..
Duniyar Masoya Litattafan yaki only
Home of Littafan Yaki And Hausa Novels
Matan Arewa Special Group
Zauren Muslims
MAZAN JIYA 4
littafe na hudu 4
part 20
typing: suleiman zidane kd:
::
Koda ma dayansu ya sami nasarar wannan yaki
sai ya sha bakar wahala kafin yagano inda
takobin take acikin karkashin tekun:
Kai ni ga yadda mana sami tarihi cewa aka yi
tsaron dake inda takobin take yafi gaban
hasashen mai hasashe sai dai abinda ido ya
gani kawai::::::::::
koda jin wannan batu sai boka sadusa ya
murtuke fuskarsa yace to shikeanan idan har
baka aminta da abin danake gaya maka ba sai
ka yankewa kanka hukunci :
kofa dai yanzu my yaki juna ni dakai wandaya
kashe dayan yayi abinda yaso: ko kuma
murabu salin alin kowa ya kama gabansa:
amma kasani dace idan muka rabu salin alin
har abada ka rabuda Gimbiya Shalbirat kenan
baza kasake mallakarta ba:
lokacin da boka sadusa yazo nan a zancesa sai
hankali aljani Raugatul Aguwanu
ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe yarasa
abinda ke masa dadi a duniya:
nan fa ya kasa zaune ko tsaye ya rinka kai
kawo :
daga can sai ya dubi sadusa yace ka bani sa a
uku na koma can kogona nayi bincike:
Page 119
da tunani tukkunna:
sadusa yai murmushi yace jeka nabaka tsawon
sa a biyar ma:
nan take aljani Raugatul Aguwanu
ya bace bat tamkar kiftawar ido:
A Sannan ne shalbirat ta dubi boka sadusa
cikin alamun tsoro tace yakai abul halyal anya
kuwa kana ganin cewa Raugatul Aguwanu zai
amince ya daukemu yakaimu bakin kogin bahar
sufiya?
To wai shin ma meye hikimarka ta zuwanmu
can din alhalin kasan cewa sansani ne na
mutuwa?
Sadusa yai ajiyar zuciya sannan yace kiyi hakuri
yake wannan yar sarki:
Ki tuna cewa mu bamu baki labarin mu ba
kamar yadda kika ban mu naki sakamakon
cewar babi isashen lokaci na yin haka:
Page 120
zidane kd:
Ni dai kawai abinda na sani shine sau tari sai ka
tari aradu da ka sannan kake fita daga cikin
wata masifar:
akwai abin da ya baromu da kasarmu kuma
bukatarmu ba zata biya ba face mun dangana
da bakin tekun bahar Sufiya inda ake yin
wannan yakin:
kuma ki rungumi kaddara har izuwa sa adda
zamuje can dinko bakomai dai gwara ki mutu
acan sansanin yakin da dai ki mutu a hannun
wannan azzalumai alajni:
kodajin wannan batu sai shalbirat ta jinjina kai
tayi shiru bata kara cewa komai ba::
* * *:
BIRNIN SARKI DUJALU:
ACAN gidan sarautar sarki dujalu kuwa
tundaga ranar da kunyaga lazimat ta tafi
neman hanyar da Gimbiya Hursiya zata sami
damar komawa sansanin yaki a cikin kwanki
kadan bata dawo ba har kwanaki biyu da aka
dirba mata suka cika:
A dare kwana na biyun ne hankalin Gimbiya
Hursiya ya dugunzuma ainun ta kasa zaune ko
tsaye:
fara zubar da hawaye domin ta saddakar da
cewar har abada baza ta sake ganin dan
uwanta ba sarki dujalu ba:
Page 121
babu abinda yake kara fusatata facw a duk sa
adda ta leka wajen turakarta ta cikin taga sai ta
hango aljani barzaru yana shawagi a saman
turakae yana kewayeta don tabbatar da tsaro
wato dai ta san cewa gadinta yake yi babu
yadda za ayi wani ya iya zuwa yatafi da ita
batare da yagani ba:
Gimbiya Hursiya na cikin wannan hali ne ta jiyo
alamar takun sawu an nufo kofar turakar
Ta kawai sai ta zuba idanu akan kofar
shigowar:
abinda ta sani shine koma wanane ya taho in
dai bai kasance daya daga cikin kuyangitaba ko
bayinta aljani barzaru ba zai barshi ya shigo ba:
Ashe ba wani bane ya durfafo turakar ta ba
face kuyanga lazimat rike da wani jan fure mai
kamshin gaske fisa faranti:
yayin daya rage bai fi saura taku biyar ba
tsakanin kuyaga lazimat da kofar turakar
gimbiya sai kawai taga aljani barzaru ya fado
juf a gabanta;
ko Gezau batayi ba ta dubeshi a fusace yace
meye haka zaka sha gabana alhalin kasanni na
sanka ko kuwa ni bakuwa ce a gidannan?
Aljani barzaru ya daka mata tsawa wacce tasa
hanjin cikinta ya kada hannunta yakama
karkaewa har farantin dake hannunta ya fadi
kasa tayi sauri daukeshi:
Barzaru yadubi wannan fure dake kab faranti da
kyau sannan ya dubi kwayar idanun lazimat ko
zai ga alamun rashin gaskiya a tare da ita
sanna ya ce: ke tsohuwar makira: ni fa ban
yarda dake ba ina kyautata zaton cewa akwai
wani kullin boye da kuke shiryawa ke da
gimbiya:
page 122
shin baku san cewa ina lura da dukkan motsi
ku ba? Yau kwanaki biyu kenan rabonki da
turakar gimbiya alhalin kullum kuna tare baku
taba rabuwa ba sai sa adda sarki ya tafi da
gimbiya bakin tekun bahar sufiya: lallai akwai
alamar cewa ta turaki ne kiyi mata aikin ne don
haka ban yarda da wannan furen da kika kawo
mata ba:
bani shi na koneshi:
Har aljani Barzaru ya yunkura zai dauke fure sai
ya jiyo muryar gimbiya Hursiya tana mai daka
masa tsawa; ba shiri ya janye hannunsa: nan
take Hursiya ta dako kofar turakarta ta fito
waje cikin tsananin fusata ta dubi aljani barzaru
tace au sbda samun dama shine zaka wuce
gona da iri a cikin aikin naka na gadinna?
Shin ka manta ne cewar tun ina yarinya karama
babu abinda nakeso sama da jan fure?
Ka sani cewa labari ne yazo mini cewa an sami
sabon samfarin jan fure a can birnin zandal shi
ne na aikata taje ta siyo mini shi kuma ka san
cewa dole ne mutum ya shafe kwana biyu kafin
yake birnin zandal ya dawo ::
ka dubi wannan fure da kyau kaga ni zaka ga
cewa yasha bamban da irin sauran janjayen
furen da ake kawomini:
page 123
suleiman zidane kd:
Koda jin haka sai aljani barzaru ya kurawa
wannan fure idanu nan take kuwa ya ga lallai
fure ne dabam domin bai kasance ja zallah ba
akwai ratsin ruwan dorawa a jikinsa:
koda ganin hakan sai ya zube kasa a gaban
Gimbiya ya kama tuba;
ko kallinsa Gimbiya batayi ba ta kama hannin
kuyanga lazimat taja izuwa cikin turakar suka
rufe kofa suka kulle:
A sannan ne aljani barzaru ya mike tsaye ta
bude fuka fukansa yai sama yana mai cigaba
da shawagi yana kewaya saman turakar ta
gimbiya don tabbatar da tsaro:
ABINDA BAI SANI BA SHINE AN KULLE KOFA
DA BARAWO KUMA BAWANI BANE BARAWON
FACE WANNAN JAN FURE WANDA KUYAGA
LAZIMAT TA SHIGA DA SHI CIKIN TURAKAR
GIMBIYA:
Lokacin da Gimbiya Hursiya ta ja kuyanga
lazimat izuwa cikin turakarta sai suka shige har
can cikin daki barcinta:
Suna shiga sai lazimat ta rufe dakin gami da
tagogi sannan ta fiddo wani turare wuta na
tsafi daga cikinAljihun rigarta:
take turarren wuta ya kunna kansa hakinsa ya
cika dakin gaba daya tamkar hazo ne ya shigo
dakin:
faruwar hakan ke da wuya sai wannan jan fure
da ke kan faranti wanda lazimat taxo dashi ya
rikide ya zama wani dan wadan aljani mai
kwalelen kai wanda tsawonsa bai wucce kamu
biyu ba:
page 124
Zidane kd:
tunda gimbiya Hursiya ta zo duniya bata taba
ganin mitsitsin wada kamar saba sai kace yar
tsana:
yana da kwala kwala idanu kamar na mujiya
hancinsa kuwa wakakeke ne kamar na a zura
kwai a ciki:
yana da dan mitstsin baki tamkar kwallon
dabino bazai iya shigewa ba:
kafafuwansa kuwa yan dugul dugul ne kaman
na agawagi:
koda bayyaynar wannan aljani sai gimbiya
Hursiya ta fadawa kainun taja da baya cikin
sauri tana mai fadawa kan gadonta kamar za ta
kwalla ihu:
cikin tsananin razana ta dubi kuyanga lazimat
tace sabda me zaki jeki nemo mini wannan
aljani n mai ban tsoro haka?
Koda jin ewannan tambaya sai kuyanga
lazimata tayi murmushi sannan tace ya
shugabata wannan aljani ba mai cutarwa bane
kawai dai halittarsa ce haka:
nantake dan wadan yadaka tsalee daga fartanti
dayake ya dure kasa daf da gadon Gimbiya yai
sujadda agareta yace sunana boka RADIYAL
IBN ZAILUR: INA zaune a can nahiyar da ke
kudanci taku ne sako ya riskeni cewar kina
neman wanda zai kaiki can sansanin yaki na
teku bahar sufiya shiyasa na taso da kaina
nazo domin na biya miki wannan bukata amma
bisa sharadi guda:??
ANAN ZANDAKATA SAI KUMA IN ALLAH
YAKAIMU GOBE DASAFE DAFATAN ZAN IMIN
AFUWA NAKWANA BIYU DA AKAJENI
SHIRU::COMMENT:::
MAZAN JIYA 4
Littafe na Hudu
Part 21
Typing: Suleiman zidane kd:
in baku manta ba mun tsaya:
INA zaune a can nahiyar da ke kudanci taku ne
sako ya riskeni cewar kina neman wanda zai
kaiki can sansanin yaki na teku bahar sufiya
shiyasa na taso da kaina nazo domin na biya
miki wannan bukata amma bisa sharadi
guda:??
Cigaba:
Page 125
Koda jin wannan jawabi sai Gimbiya Hursiya ta
tashi zaune tana ;mai gyara zama sannan ta
dubi boka Radiyan ciki murmushi tace ina
sauraronka ya kai wannan babban boka:
Radiyan yayi gyaran murya sannan yace a halin
yanzu nayi bincike na gano cewa a duk fadin
duniya babu wani aljani dazai iya zuwa bakin
kogin bahar sufiya a cikin yan kwanaki kadan
kafin a gaa gagarumin yaki da ake fafatawa
acan face aljani daya wanda ake kira da suna
Raugatul aguwanu wanda ke zaune a cn dajin
darul Hushshul maut:
Dajin ne wanda sama da shekaru bakwai baya
mutane aljanu dabbobi da tsuntsaye da kwari
suka daina shiga ko wanzuwa a cikinsa amma
a halin yanzu wani takadarin boka dake nan
garin mai suna sadusa ya karya kofin da ke
dajin ya shiga har ya sadu da aljani Raugatul
aguwanu zai daukeshi a gobe su tafi izuwa
bakin kogin na bahar sufiya:
zan iya kaiki can dajin Darul Hishushul maut a
yau dinnan acikin abinda wuce sa a biyar ba
kuma zamy shiga ne a sirrance ba tare da mun
bari su aljani Raugatul aguwanu sun ganmu ba
ko suji motsinmu ba:
Nida ke zamu shiga cikin kunnen aljani
Raugatul aguwanu ne muyi zamanmu a ciki a
lokacin da yake barci:
Ba zai taba sanin da zamanmu ba a cikin
kunnen nasa muddin zamu jure yi masa susar
kunne domin a duniya babu abinda yake sa shi
yamanta da koai face susar kunne:
Page 126
zidane kd::
A haka za a tadi dau izuwa bakin tekun bahar
sufiya ba a sani ba:
Sharadin dake tsakanina dake shi ne ba zan
yarda na kaiki inda aljani Raugatul aguwanu
yake ba face kinyi alkawari cewar idan dan
uwakinki sarki dujalu ya sami nasarar cin yaki
kuma ya dauko takobin Saiful Lujara zaki sa ya
maisheni daya daga cikin manya fadawansa na
hannun dama:
lokacin da boka radinya yazo nan a jawabinsa
sai hankalin gimbiya Hursiya ya dugunzuma
tayi shiru tana tunani da nazari al amarin ta
rasa abinda zatace:
daga can sai ta dago kai ta dubi boka radiyan
tace yakai wannan boka kayi sani cewa ina da
wadansu yan tambayoyi a gareka kafi na
aminta dakai:
da farko dai ina son kaga mini dalilin da yasa
boka sadusa yaje ya hada kai da aljani Raugatul
aguwanu domin yaje sansanin yaki?
Tambaya ta biyu itace ta ya kake tunanin zaka
iya fitae dani daga cikin gidan sarautae nan har
ka kaini dajin darul hushushul maut alhalin
aljani barzaru na shawagi a saan turakata yana
gadina?
Tambaya ta uku wacce itace ta karshe yaza ayi
muyiwa aljani Raugatul aguwanu susa a
kunnensa ba tare da yagane cewa akwai baki
hallitu a cikin kunnen nasaba?
Page 127
zidane kd:
Sa adda boka radiyan yaji wanna tambaya sai
ya bushe da dariya lokaci guda kuma ya hade
rai ya ce yake wannan yar saki kiyi sani cewa
hakika aiki sai mai shi:
Dangane da tambayarki ta farko am . Sarta
itace fadawan dan uwanki suna son su gaje
karagar mulkinsa idan har yazamana cewa bai
sami nasarar yaki ba a bakin tekun bahar sufiya
domin su ke suga halin da ake cikin a sansanin
yaki ne boka sadusa ya nemi hadin kan aljani
Raugatul aguwanu tunda shi kadaine xai iya
zuwa can din:
dangane da tambayarki ta biyu kuwa itace sa
adda na shigo gidan nan ba tare da aljani
barzaru ya ganni ba taha kema zaki fita :
sai tambayarki ta uku wacce itace ta karshe
amsarta itace duk jikin aljani Raugatul aguwanu
babu inda yafi girma da nauyi sama da
kunnunwansa guda biyu don haka idan muka
shiga cikinsu tamkar a dauki yar karamar
tsakuwa ne a jefa cikin RIJIYA GABA DUBU:
bazai ji sa adda zamu shigaba kuma dazarar
mun fara yimasa susa zai sami cikakkiyar
nutsuwa da zai yi azabbaben gudu a sararin
samaniya har mu isa bakin kogin bahr sufiya
cikin sa o i kadan:
Yanzu dai kin shirya zamu tafi cikin murna
Gimbiya Hursiya tace aini bani da wani shiri sai
naka:
page 128:
kafin ta gaa rufe bakinta tuni boka radiya yayi
nuni da hannunsa na hagu gareta:
lokacin guda shi da ita suka rikide suka zama
wannan jan fure guda daya kawai sau kuyanga
lazimat ta sunkuya ta dauki wannan fure ta
dorashi akan farantin ta fita daga cikin turakar
gimbiya Hursiya rike da faranti:
Tana fitawa sai taga aljani barzaru tsullu
agabanta fuskarsa a murtuke babu alamar
annuri nan take ya daka mata tsaya ta firgita
ainun har ta saki fitsari a tsaye bata sani ba:
hunnunta yakama karkawa farantin dake
hannunta ya rinka jujjuyawa kamar zata
sakeshi ya fadi::
aljani barzaru yadubi wannan jan fure da ke
hannunta sannan ya dubeta cikin alamun
rashin yarda yace ina ma anar fitowa da
wannan jan fure yanzu alhalin dazu nan kika
shiga dashi?
Kuyanga lazimat ta budi baki muryata na rawa
tace ai gimbiya ce tace batason wannan kalar
sai dai mai dashi na canjo da irin wanda aka
saba kawo mata:
page 129:
barzaru ya ce tome yasa kuke gudanar da
wannan al amari yanzu a cikin wannan dare
maimakon ku zarta dashi da safe?
Lazimat tace ai ka sani cewa yanzu duk abinda
gimbiya takeso shi takeyi tunda sarki baya nan:
Duk umarnin da ta bayar shi akebi a gidannan :
kodajin haka sai alajni barzaru ya gyada kai
yace Tabbas kiyi gaskiya amma dai ni yanzu
ban zan amince da keba facce mun koma tare
dake cikin turakar gimbiya na ganta da
idanuna:
koda jin wannan batu sai hankalin kiuyanga
lazimat ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe
alamomin tsoro da rashin gaskiya suka
bayyana kururu akan fuskarta:
koda ganin haka sai aljani barzaru ya tukuda
keyarta suka koma cikin turakar gimbiya suka
wuce kai tsaye izuwa cikin dakin barcinta:
zidane kd::
WHATSAPP 09064179602
koda suka tura kofar sai suka ui arba da
gimbiya hursiya kwance akan gadonta tana ta
shara barci:
al amarin da yai matukar daurewa aljani
barzaru kai kenan yacika da tsananin mamaki:
ita kuwa kuyanga lazimat sai ta sami nutsuwa
takama murmushi;
Nan take suka juyo da baya kafin su fice daga
cikin dakin tuni gimbiya hursiya wacce ke
kwance a kan gado tanaBarci ta rikide ta zama
ha yaki yashige cikin wannan jan fure dake
hannun lazimat ba tare da aljani barzaru ya lura
ba:
PAGE 130
ZIDANE KD:
WANNAN SHINE ABINDA YAFARU A BIRNIN
SARKI DUJALU BAYAN GIMBIYA HURSIYA TA
SAMI HANYAR DA ZATA SAKE KOMAWA