Showing 9001 words to 12000 words out of 100703 words

Chapter 4 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

4480


ya sanya kawai yace mata “ta huta” dan shi tunaninshi bashi yayi gajiyar biki ce take d’awainiya da ita.

Tana ajjiye wayar Khadija na shigowa, nan ta tusa ta gaba da zancen Auwal…
“Ta soshi mana, yana da hankali daga gani, ga
kyau, gashi zata zauna kusa da Huda…
Waye waye”

Ita dai Sakina k’arshe juya mata baya tayi, tayi mata banza kamar tayi bacci, ganin
haka yasa Khadijah kashe fitila, abunku da mai k’aramin ciki tuni tana kwanciya bacci yayi awon gaba da ita!
Sakina kuwa yadda taga rana haka taga dare
Wani abun mamakin shine
duk wani labari da plans da Ashraff ya gama gaya mata na bayan aurensu yanzun
she can’t help it but to picture it ita da Auwal!
K’ok’ari take yi ta danna k’iyayyar shi a cikin zuciyarta
sai dai abunda bata saniba
ta riga ta makara dan
already zazzafar soyayyarshi ta riga ta rinjayi y’ar guntuwar k’iyayyar da take k’ok’arin dannawa zuciyarta ta k’arfi da yaji.....

BULAMA ✍️



So da Buri
Free Book
57


Da kyar Aslam ya iya mik’ewa bayan fitar su Auwal.
A hankali yana jin yadda zuciyarshi take bugawa da mugun k’arfi ya isa bakin k’ofar d’akin da ya ga su Sakina sun fito daga ciki.
Da kyar ya iya d’aga hannunshi ya fara knocking….

A hankali kamar mai kuka yaji tace
“Sakina shigo mana”
Dan ita har ga Allah ta yarda da Sakina wadda tace mata ‘bara su je su yi siyan baki ta dawo
Ai ita a nan ma zata kwana yau’.

A hankali ya lumshe idanuwasa ya bud’e
kafin ya murza handle d’in ya tura k’ofar ya shiga da sallama.

Da sauri ta d’ago jin muryar Namiji!…
Duk da su Sakina sun ja mata mayafinta kafin su fita amman tana iya hangoshi!
Har yanzun shadda ce a jikinshi abunda bata tab’a ganiba kenan. Sai taga yayi mata mugun kyau!
Tsayi kamala surar jikinshi ta cikakkaen lafiyayyen Namiji ta fito sosai…
A take zuciyarta ta hau bugawa da sauri da sauri.....

Takowa yake yi izuwa bakin gadon wanda hakan da yake yi ji take kamar a kan zuciyarta
yake yin tafiyar..
Duk taku d’aya sai taji tamkar numfashinta zai d’auke ne!
Hakan yasa ta fara ja da baya..
Yana matsowa ita kuma tana ja baya.
Aslam shi bai ma lura da yadda take ja da bayan ba
har sai da yaga sun kai edge d’in gado tana neman mik’ewa,
dan shi har ga Allah
ba abunda idanuwanshi suke gane mishi sai ita, ruhinta!
shiyasa sam bai lura da movement d’inta ba…
Yana isowa dab da ita, ya jaa ya tsaya a bakin gadon.

Ita kuma sai k’ok’ari take ta mik’e amman k’afarsa da side drawer sun tokare ta gashi
har ta kai jikin fuskar gadon
so ba daman ci gaba da matsawa…

A hankali taga yana d’an sukuyowa….ji take yi kamar ta bud’e murya ta kurma ihu!
Ko kuma ta tashi ta yi tsalle ta fad’a tsakiyar gadon daga nan ta samu ta sauk’a ta d’ayan side d’in…
Ita har ga Allah tun farkon had’uwar ta da shi, sam! Bata k’aunar zama a kusa da shi (Aslam) Saboda muddin suna tare no matter how she tries kwata kwata zuciyarta bata barin wannan mahaukacin gudun data rasa dalilinsa!
Gashi bata san dalilin da ya sa yaketa matsowa kusa da ita ba..
Ita fa yanzu abunda ya kamace su shine
su nutsu su yi tunanin ya za suyi da rayuwarsu da wannan auren da aka k’ulla musu
shiyasa duk a rud’e
sannan a rikice take kuma gashi yanzu ya zo ya sake rikitata……

Tana cikin wannan tunanin
ta ji fuskarsa daff da tata!
A hankali taji yasa hannu ya yaye lullub’in laffayar fuskarta..
Had’a idanu suka yi!
Da k’arfi zuciyoyinmu suka buga a tare!

Sai da ya lumshe idanunsa ya bud’e kafin ya sak’ale kwayar idanuwanshi da tata sannan yace
“Assalam alaiki, Maryama.”

Da mugun k’arfi ta runtse idanuwanta sannan
dai dai nan hawayen da bata san dalilinsu ba suka b’alle mata a take.

A hankali ya hau yi mata kallon k’urilla….
Cikakkiyar minti d’aya ya d’auka yana kallon fuskarta
kafin da kyar ya samu ya iya kokawa da zuciyarshi ya d’auke idanunsa yana mai lumshe su..

Wata zazzafar ajiyar zuciya ya sauk’e wadda itama bata san lokacin da ta sauk’e tata siririyar ajiyar zuciyar ba
sakamokon numfashinsa mai d’umi da dad’in shak’a da ya ziyarci hancinta wanda
har zuciyarta sai da ta amsa!
Hakan ne kuma ya haifar mata da sauk’e ajiyar zuciyar da bata shirya wa ba…

A hankali ta ji sauk’ar wani lallausar tafin hannu kamar na jarirai mai mugun taushi
a kan kumatunta!
A mugun zabure ta bud’e idanuwanta da suka k’ank’ance suka yi jaa ta zuba masa su..
Bai damu da kallon da take yi masa ba! Kallonta kawai yake yi yana goge mata hawayen nata…
Idanuwansa da ya zuba mata ya kafeta da su ne ya sanya ta runtse nata idanuwan jikinta na wani mugun rawa!.

Wata ajiyar zuciyar kawai ya sake sauk’ewa...yana gama goge hawayen ya mik’e da sauri dan ba k’aramin kokawa yake yi da zuciyarsa ba tun lokacin da ya shigo!

Sai da ya lumshe ido na some seconds tukunna ya bud’e yace
“Ki taso mu je kici abinci”
Kafin ya rufe bakinsa tace
“N na na k’oshi”
Tana mai jan numfashi
har yanzu jikinta bai daina rawa ba.

Be ce mata komai ba, ya sa kai ya fice a d’akin.
Minti kad’an ya dawo
da ledojin da Auwal ya shigo da su..
Gefenta ya nema waje ya zauna a bakin gadon!
A hankali ya bud’e ledojin ya d’aura akan stool
kafin yace
“Oya, gashi ki ci.
Akwai wani abun da kike buk’ata?”

Da sauri ta girgiza kai alamar ‘a’a’.

A hankali ya mik’e
yace
“Sai da safe”

Tun kafin ya rufe bakinshi tace
“Allah ya kaimu”
Don so take ya fita.

Shima
lura da hakan da yayi ne dama ya sanya kawai ya mik’e d’in.
Ajiyar zuciya ya sauk’e kamar zai ce wani abun sai kuma kawai yace
“Allah ya tashe mu lafiya”
Yana mai juyawa ya fita daga
d’akin gaba d’aya”

Yana fita ta sauk’e wata wawiyar ajiyar zuciya…
Har ta d’an zauna sai kuma ta mik’e da sauri ta isa bakin k’ofar ta murza key ta zare ta taho da shi ta ajjiye a kan side drawer tana ta tunani….
Ta dad’e bata sha mamaki irin na yau ba!
Yadda yake yin abu kan sa tsaye sannan kamar bashi da wata damuwa abun yayi mugun d’aure mata kai!
Dubafa yadda ya wani zauna a kusa da ita sannan har da wani share mata hawaye..
Ita tana tunanin sai ta yi kusan kwanaki ma bata ganshiba
daga nan ya bata takarda yace taje ta auri Arshaad d’inta
Amman kalli abunda yayi tun yau..
Ba abunda yafi d’aure mata kai irin siyan bakin da aka yi
sai kace waenda suka yi auren soyayya…

Harga Allah yunwa take ji
sosai ma kuwa
amman d’aurewar da kanta yayi ne ya sanya ta mayar da kajin cikin ledarsu ta had’a da ledar drinks d’in ta saka a d’an k’aramin fridge d’in data gani a d’akin.

Da kyar ta lallab’a ta yaye laffayar jikin ta ta ninke,
ta shiga toilet ta d’auro alwala tazo ta nemi waje ta zauna
dan
already sun yi sallolinsu Magrib da Isha ita da su Sakina.

A ranta ta gama ayyanawa
tabbas idan aka yi d’an kwana biyu taji Aslam bai yi mata wata magana ba
to ita kam zata tareshi da zancen ya saketa!
Idan ma Mahaifiyar Ya Arshaad ta hana aurensu
to zata hak’ura ta rungumi k’addara tayi facing karatunta
idan Allah ya fito mata da wani ta yi aurenta
amman ita kam ba zata iya zama da wannan murd’ad’d’en mutumin da bashi da alk’ibla ba!
Infact tayaya ma zata zauna da mutumin da kullum in dai suna tare sai taji zuciyarta tana barazanar fashewa
haka kurum salon yaje ya fasa mata zuciya a banza ya yiwa Mama da Abba da su Sakina asara,
Inaa ba zai yiu ba!

Da wannan tunanin ta kwanta akan lallausan gadon tana mai lumshe ido…
Nan kuma ta fad’a tunanin Arshaad!
Tana yi tana istighfari amma sam ta kasa dainawa.
Tabbas sai ka rasa abu kake gane yawan son
da kake yi mishi!
A lokacin da take tare da Arshaad bata san tana sonshi haka ba sai yanxu da ta san In ba da kyar ba to ta rasa shi kenan har abada!
Dan muddin Mahaifiyarsa bata basu go ahead ba to ita kuma tayi alk’awarin ko sonshi zai kasheta ba zata tab’a aurensa ba tare da albarkar ta ba!
Besides sai ma ta fara nemo mafita akan wannan auren!
She has to do something fast
saboda taga take taken Aslam kamar shi zai iya hak’ura ya zauna da ita don ya faranta ran su Abba
Kuma ta tabbata idan hakan ta faru to haka za su k’are rayuwarsu
ba soyayya
tunda ita dai zuciya d’aya Allah ya bata kuma ta riga ta damk’awa Ya Arshaad
shima kuma Aslam d’in ta tabbata bai ya k’aunarta
sai dai ya kawai ya zauna da ita saboda ba yadda ya iya
To Ina riba?
Garama shi Namiji ne
anytime idan ya had’u da wadda yake so zai aura
Ita fa?
An cuceta an cuci Ya Arshaad d’inta..how she wish she can see him now..tana so
taga halin da yake a
ciki, bawan Allah d’azu ba kalar zargin da batayi mishi ba
ashe fin k’arfinsa aka yi….
Bata san lokacin da wani mugun kuka ya kufce mata da k’arfi ba.……

Tunani da kuka basu barta ta rintsaba sai around 2:00am
tukunna
bacci ya kwasheta
wanda bata yishi cikin dad’in rai ba.
Kafin asuba ta farka
sakamokon mugun ciwon kan da ya rufar mata,
da zazzafan zazzab’i
ko idanuwanta bata iya bud’ewa sosai in banda rawar sanyi ba abunda take yi.....

Tanaji ana kiran sallah
k’ok’ari take yi ta samu ta tashi amma sam ta gagara....


A b’angaren Aslam shima bai samu yayi ishashshen bacci ba
kusan kwana yayi yana nafila..
A nan kan daddumar ya samu bacci ya saceshi.
Kiran sallar farko da aka maka a masallacin cikin estate d’in ne ya farkar da shi, dan
haka ya mik’e ya shige bathroom…
Sai da yayi wanka ya d’auro alwala sannan ya fito ya d’an
kimtsa ya zura jallabiya ya gabatar da fajr nafl, ya zauna karatu.

Yana idarwa ana tada sallah
dan haka a gurguje ya fice ya nufi mosque..
Ya so ya duba Huda
amman gudun kar ya makara yasa ya fita da niyyar ana idarwa zai dawo ya duba ta.

Azkar kawai yayi daga nan ya fito daga masallacin.
A k’ofa suka had’u da Dad
dan haka suka jera yana d’an yi mishi nasiha har suka iso gidan..
Jan hankalinshi yake sake yi akan ya rik’e amana dan Allah kar ya wulak’anta matar da suka zab’a masa, ya
taushi zuciyarshi ya bata dukkan hakkin ta da kulawa
wata rana zai k’aunaceta in sha Alla…

Shi dai Aslam da ‘to’ ‘in sha Allah’ kawai yake ta binshi
dan ya rasa dalilin da yasa zuciyarshi taketa faman azalzalarshi akan yaje ya dubata..
Sam ya kasa sukuni ballantana ya samu ya bawa Dad d’in hankalinshi..

Da kyar ya samu Dad ya barshi ya wuce side d’inshi,
bayan yace mishi “ya tabbatar sun je sun samu Granpa”…
..saboda ta watsapp yaji yace mishi zai nemeshi tun jiya amman har yau shiru,
kar aje ko fushi yayi
shi kuma har ga Allah baya so ya je ya sameshi gudun rigimarshi yake kuma bai san a wanna mataki ya saka maganar auren Aslam d’in ba
gara idan Aslam d’in yaje da kanshi maybe abun yazo da sauk’i…

Da ‘to’ Aslam ya amsashi
sannan suka yi sallama
ya wuce side d’inshi
yana dariya da mamakin Dad d’in
k’iri k’iri ya hango tsoro a tartare da shi..wato sun yi abu amman kuma suna tsoro
shine bara su tura shi..
Da wanna tunanin ya Isa bakin k’ofar d’akin da Huda take ciki ya d’anyi knocking sannan ya murza handle d’in da niyyar turawa amman k’ofar sai ta k’i motsi, a hankali yad’an sake yin knocking amman still yaji shiru…
Yayi mata knocking yafi sau biyar amma yaji shiru
dan haka ya d’an sassauta murya ya matsar da fuskarshi jikin k’ofar ya fara kiran sunanta…

A take gabanshi ya yanke ya fad’i! Dan in dai kunnuwanshi sun ji mishi dede to
kamar sheshshek’a da jan numfashi yake jiyowa yana tashi daga d’akin!

Da mugun sauri ya koma d’akinsa ya d’auko spare key
sannan yazo ya zura ya murza ya tura da sauri ya shiga

A k’udundune ya hangota a kwance tana rawar sanyi
Da sauri ya k’arasa ya d’agota ya zaunar sannan ya fara shafa goshinta wanda ya ji ya d’auki zafi ba na wasa ba.
A firgice yake kallonta,
gaba d’aya ta jik’e da gumi kamar an watsa mata ruwa,
pillow ya jawo ya kwantar da ita sannan ya mik’e ya nufi toilet ya jik’o towel ya fito..

Hannuwanta da tafin k’afarta sai saman goshinta ya shiga shafawa towel d’in amman kamar k’ara mata zazzab’in ma yake yi dan haka kawai ya
mik’e ya je d’akinsa ya d’au waya ya kira Doctor tukunna ya dawo ya ci gaba da goga mata… ji yake kamar yayi kuka gani yake yi duk laifinshine dan inda a d’aki d’aya suke da tun farkon zazzab’in nata zai yi noticing ya san abun yi…..

A hankali ya ga tana bud’e idonta, da sauri ya matso yace
“sannu ya jikin?”

A hankali ta shiga motsa bakinta a lamun magana take son yi..

Hannunshi yasa a a gefen kumatunta yana kallonta kafin yace
“me kikeso? Tell me.
Yanzu Doctor zai zoo kin ji, sannu” ya k’arashe maganar
a hankali yana kallon bakinta da take k’ok’arin yin magana..

Murmushi ya ga ta fara
kafin yaji tace
“Ya Arshaad!
yaushe ka zo?
Ina ka tafi ka bar ni?”
Tana mai kallon cikin idanunsa.

Da sauri sannan da mugun k’arfi Aslam ya runtse idanuwanshi.....

Magana take yi amman ba ya fahimta, babu abunda yake iya ji sai
‘Ya Arshaad’ d’in da take ta ambata a duk k’arshe ko farkon maganarta!…..

Ya so ya zauna ya cigaba da shafa mata jik’akk’en towel d’in a samu fever d’inta ya sauk’a amman sai ya kasa!
A hankali ya mik’e tsaye daga kan gadon yana ganin dishi dishi…,

Ji yayi kawai ta fashe da kuka
sannan ta fara k’ok’arin ruk’o hannunshi, cikin kukan tace
“Dan Allah kar ka tafi,
mu zauna a cikin mafarkin nan da nake yi
ni da kai har abada,
kar ka tafi ka barni
bana so in farka
idan kuma zan farka to sai ka yi min alk’awarin zaka dawo gar....”

Wucewa yayi da sauri ya fice a d’akin ya barta nan tana ta faman surutai..

Da kyar ya iya kai kanshi d’aki
yana zuwa ya dafa bango da d’ayan hannunsa d’ayan kuma ya dafa goshinsa yana jin
yadda zuciyarshi take harbawa da tafarfasa tamkar zata fashe!
Sunayen Allah ya hau karantowa sannan ya fara k’ok’arin controlling kanshi…
Tabbas ya san zafin zazzab’i ne ya sanya ta take
hallucinating amman hakan bai hanashi jin kamar zai mutu ba!
Da kyar ya samu ya zaro waya ya kira Mommy yace mata “ta zo Hudan bata da lafiya”
Daga nan ya lallab’a ya koma bakin gado ya zauna ya jingina bayanshi a fuskar gadon ya lumshe idanuwanshi.....



Kamar yadda su Umma suka tsara!
Yau da sassafe k’arfe 7:00 na safe Anty Zainab ta biyo mata suka kama hanya…
Tafiyar awa uku ce ta kaisu d’an k’aramin k’auyen da za su je wanda tsaf In ka tsaya zaka iya k’irga gidajen wajen kaff d’insu.
Wani gida isolated a chan nesa suka nufa, a dai dai hanyar gidan akwai wata y’ar majalisar wasu matasa a k’asan wata k’atotuwar bishiyar mangoro dai dai suna zuwa za su wuce wani a cikinsu yace
“Ga wasu b’atattun yau ma sun zo”
Sarai sun ji sa
ba wannan ne a gabansu ba dan haka suka wuce suka yi cikin gidan….

Sai da suka d’an jirashi ya karya sannan ya samu damar ganinsu. Suna shiga suka nemi waje suka zauna.

Da kyar Umma ta iya ce mishi “Ina kwana”
Bata jira amsawar shi ba
ta hau zuba…
Har da cewa da ya san ba zai yi aikin ba tun jiya da bai ce ta k’ara mishi kud’i ba!
Sai da Anty Zainab ta d’an zungureta tukunna aka samu ta yi shiru.

Gyaran murya Anty Zainab d’in tayi sannan tace
“Ni a ganina yanzu aikin gama ya riga ya gama,
tunda har ta tare.
Yanzu abunda muke so shine a tabbatar da auren Jalila da shi Arshaad d’in
sannan a san yadda za a yi a taimakawa Jalila ta fitar da Huda daga gidan!”

Shiruuu, mutumin ya d’ab yi ya lumshe idanuwanshi..
Chaan! Ya bud’e, ya kalleta yace
“Na riga fa na yi abunda zan yi!
Kun tabbatar anyi auren ita Huda da shi Arshaad d’in kuwa?
Dan ni gaskiya bincikena bai nuna min an yi ba.”
Da sauri Umma tace
“Shirme kenan!
To bari kaji..
Jiya ma a gidanshi ta kwana k’arshen magana kenan.
Kuma na tabbatar idan aka bincika ma yanzu haka ciki gareta!
In dai binciken tsakani da Allah za a yi”.

Murmushi kawai yayi
kafin yace “shikenan.
Ku d’an jira ni”
Daga nan ya mik’e ya
fita.
Kamar minti biyar haka
ya dawo…

Wata bak’ar laya kawai
ya mik’o musu bayan ya zauna
Anty Zainab ce tasa hannu ta karb’a dan ita Umma in banda tura baki da kumbure kumbure ba abunda take yi.
Sai da ta karb’a sannan yace
“Ku nutsu! Ku bani dukkan hankalinku!
Dan kunga wannan abun da na baku shine kankat!
Amman muddin kuka yi ganganci aka samu matsala
to abun zai dawo kanku ne!
Kun amince?”

“Eh”
Suka had’a baki duk su biyun.

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya sake cewa
“Shawara itace..
Ku sake bincikawa
ku tabbatar an yi auren
dan in dai basa tare kuma
akayi wannan aikin mai zafi to
idan ya tafi bai samesu ba kan ku zai dawo! Bi ma’ana
Auren d’aya daga cikinku ne zai mutu.”

Murmushin takaici Umma tayi
kafin tace
“Mallan”
Yace “Na’am” tace “fad’a mana yadda za ayi amfani da ita kawai!
Maganar tare kam
Huda da arshaad suna tare.”

“To shikenan.
Aikin ba mai wani wahala bane ba, ita wannan abar dana baku
cikin dare za a tashi a k’ona ta k’urmus! Shikenan
Ko wanne irin kalar aure aka k’ulla musu
sai sun rabu!
Rabuwa ta har abada, idan har kinga sun dawo sun zauna
to sai dai in za a iya maida layarnan ta koma dede yadda take kafin a k’onata!.
Sannan shi kuma wannan” yayi maganar yana basu wani turare
kafin yace
“Ita Jalilar za ki bawa ta shafa a jikinta, ta tabbatar shi Yaron ya shak’a da Mahaifiyarsa da Mahaifinsa da duk wani wanda zai iya shige

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login