Showing 3001 words to 6000 words out of 100703 words

Chapter 2 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

4470

yafi farin ciki sannan hankalin shi yafi kwanciya da Aslam d’in
dan bakiga irin farin cikin da yake yi ba a lokacin da aka goya mishi baya aka kuma d’aura auren. To who are we to reject?
Besides
Ni a ganina ma it’s for the best
In sha Allah
Tunda kullum zab’in Ubangiji muke nema
shi ya shirya hakan.
Dan haka sai mu runguma mu kuma gode mishi mu bita da fatan alkhairi.

Banaso inji wata magana ta taso! Ku saka a ranku kawai Arshaad ba shine Allah ya tsara zai zama Mijin Huda ba
Aslam ne!.
Sai kuyi mata nasiha
ku shiryata,
Yahaya yace min k’arfe biyar na yamma za su zo su tafi da ita in sha Allah..
Allah yayi muku albarka gaba d’ayanku.”
Yana gama fad’in haka ya mike suka fita shi da Baba Bashir.

A hankali sautin kukan Mama ya fara tsananta a cikin d’akin....
Ganin Huda ta mik’e ta nufo inda take tana kuka ne
ya sanya Maman ta mik’e da sauri ta fice daga d’akin tana kuka.

A tsakar d’akin Huda ta zame ta zauna ta fashe da wani kuka mai ban tausayi

Shuwa ce ta umarci Ummu da “ta je ta d’auko mata laffayar da za a nad’a mata
Sannan ta taho da turarukan wuta da kasko”

Ummu na fita Shuwan
ta k’arasa inda Huda take zaune itama ta zauna sannan ta kamo hannunta duka biyu….
Nasiha mai ratsa jiki tayi mata
wanda ko Maman iyakar abunda zata gaya mata kenan!
Duk wani abunda ya dace sai da Shuwa ta fahimtar da ita dalla dalla.

A haka Ummu ta shigo ta samesu
dan haka itama ta nemi waje ta zauna ta d’ora mata da nata darussan…,
Ita dai Huda zuwa yanzu muryarta ta disashe,
hawayene kawai yake fita daga idanuwanta, sai
faman sauk’e ajiyar zuciya take yi, a ranta
tana tunanin
‘Tayaya zata fara zama da mutumin da ba ya sonta bata sonshi?
Mutumin da ta lura ko inda take baya son zama...’


Umartarta suka yi da ‘ta mik’e’
Tana mik’ewa suka hau shiryata..
Suna mata ruwan turarurruka
Khumra da na wuta...............





A gigice Anty Zainab ta k’arasa gidan Baba.
Tana shiga ko sallama bata yi ba ta fad’a d’akin Umma.
A kan gado ta sameta ta bararraje tana shan lemo da bredi da gyada
Ya Ja’afar kuma yana gefe a kwance yana bacci.

D’auke bredin tayi ta jefar
Umma na shirin yin magana Anty Zainab ta katseta ta hanyar cewa
“Jiya! Sai da nace miki kar ki k’arawa mutumin nan kud’i
yaudarar mu zai kuma yi amma da yake kunnen k’ashi gareki kika d’auki mak’udan kud’ad’e kika bashi saboda kinji Jalila duk ta rikice tana kuka ko?
To albishirinki kice mini goro!
Ga Huda chan ana shirya ta
In sha Allah nan da k’arfe biyar za azo a tafi da ita gidan Arshaad!
Aure kam ya d’auru, ba d’an borin da yayi nasarar lalatawa.”

Kwarewa Umma tayi da d’an ragowar bredin bakinta wanda bata gama had’iyewa ba.
Da kyar ta dawo dai dai
Cikin tsananin tashin hankali tace
“Innalillahi wa innailaihirrajiun!
Wacce iriyar masiface ni kam ta fad’amin?
Ni sadiya ina zan saka kaina?
Yanzu mutumin nan ya kyauta min kenan?
Tsofai tsofai da shi amman ya karkace yayi ta faman gilla mini k’arya?
Kin san tun yaushe muka sanshi kuwa? An dad’efa ana tare.
Haba dan Allah
Allah ya isa kud’ina da lafiyata.
Kiga fa jiya cikin dare muna barin asibiti haka muka je wajen shi.
Har da cewa ko dan halin da nake ciki zai yi mini aiki mai zafi!
Shege ashe yaudarata ya kuma yi ya saka min rai
Allah sai ya saka min wallahi”
Ta k’arashe maganar tana fashewa da kuka..

Duk sai tausayinta ya lullub’e Anty Zainab,
a hankali tazo ta zauna a gefenta kafin tace
“Yanzu menene abun yi?
Kuka ba zai kawo mana solution ba.”

Hawayenta ta goge sannan ta mik’e tace “komawa za muyi!
Ai ta inda aka bi aka hau tanan ake sauk’a.
Wallah ko dai ya lalata auren kafin ta tare ko kuma ya biya ni kud’ina”
Ta fad’a haka tana mai yafa mayafinta wanda ta d’auka yanzun.

Da sauri Anty Zainab ta mik’e ta tsaya a gabanta sannan tace
“Sadiya ki nutsu dan Allah.
Na tabbata kafin mu k’arasa wajen nan mai uban nisa Huda ta riga ta shak’i iskar gidan Arshaad.
Yanzu ni dai indai zan baki shawara ki d’auka to ki hak’ura da raba auren nan!
Kinga fa yadda muka yi ta k’ok’arin rabawarnan yak’i rabuwa to maybe wani babban rabo ne a tsakaninsu
Allah ne ma yake son mu shiyasa ya barmu da ranmu,
kar muje mu sake yin wani yunk’urin, muje garin neman gira mu rasa idanuwanu.”

Cikin tsananin b’acin rai Umma tace
“To matsoraciya!
Kin san Allah wallahi sai dai duk abinda zai faru ya faru
amman aure kam na raba shi na gama billahilazim!
Ai In na barsu ma
To
Maryam taci riba kenan!
Idan zaki ci gaba da taimaka min to na gode, idan kuma ba za ki ci gaba ba
to kina iya yin tafiyarki
dan ni nan kin ganni wallahi sai inda k’arfina ya k’are!
Na tabbatar inda ace Khadija ce take cikin halin da Jalila take ciki da kema sai inda k’arfin ki ya k’are!”.

Anty Zainab taji zafin maganar
amman kawai sai ta basar
duba da halin da Umman take ciki kwana biyu..Jafar a haukace! Junaidu ya b’ata!! Baba ya gudu!!! Jalila kuma gata chan itama sai a hankali,
sannan duk fad’in duniyar nan ita kad’ai Umman ta gayawa Jalilan cikine da ita
amman har Laraba bata sani ba Umman tace ‘In ta fad’a mata tana iya gayawa su Hansai, daga nan su kuma
su yayata ayi ta munafurci a cikin unguwa da dangi’
Waennan dalilan su suka sanya itama Anty Zainab d’in tayi sticking by her side take taimaka mata sannan
tana tsananin jin tausayin k’awartata, shiyasa yanzu ma
Mta kaawar da haushin da taji tace
“Sadiya yadda na d’auki Jalila haka na d’auki su Khadija.
Ki kwantar da hankalinki ki nutsu kar muje muyi ba daidaiba cikin rashin sani.”

Da sauri Umma tace
“Hankali na ba zai tab’a kwanciya ba Zainab!
Ina cikin tsananin tashin hankali..
Jiya da Jalila ta kira ni gaya miki ne ban yi ba dan kaina ya d’au chaji ba kad’an ba!
Cikin jikinta ya zube, garin
haukarta taje ta fad’o daga matattakala.
Kinga yanzu shi Yaron Auwal babu maganar karb’ar kud’i a hannunshi
kuma na tabbatar nan da kwana kad’an uwar nan tashi mara mutunci itama tsayayyiyar kanta
zata auno Jalila gidan nan!
Ni na ma yi mamakin da ta barta har yanzu dan
kwata kwata ba shiri suke yi ba!
Gashi ke kin san yadda Jalila take matuk’ar k’aunar Arshaad
sannan a haka kike tunanin zan bar Huda taje ta zauna tare da Arshaad a gaban idon Jalila?
Tana ji tana gani?
Da wanne Yarinyar nan za taji saboda Allah?
Sannan ni kaina
me nayi ne haka a rayuwa da mugayen abubuwa suketa fad’o mini haka?”
Ta k’arashe tana mai fashewa da mugun kuka.

Rungumeta Anty Zainab tayi ta shiga lallashinta
Sai da taji tayi shiru tukunna tace
“Sadiya ki nutsu ki bani hankalinki dan Allah mu yi magana”

Kamar wata k’aramar Yarinya haka Umma ta hau share hawayenta tana d’aga kai
duk ta rikice, ta manta rabon da ta shiga kwatankwacin tashin hankali irin wannan.

Sai da ta nutsu sannan Anty Zainab tace
“Anjima idan na dawo daga raka Huda zan zo mu koma wajen mutumin nan,
akwai wani ma shima za muje wajenshi.
I’m sorry to say amma raba auren Huda da Arshaad ba zai yiu ba Sadiya tunda an riga an d’aura.
Yanzu mu bar Huda
mu ji da Jalila
duk bala’i idan za muyi yawo tsirara mu san yanda za ayi a sati mai kamawa a aurawa Arshaad Jalila.
Ke kin san wacece Jalila da kuma yadda take son Arshaad
da taimakonta da taimakonmu
na tabbatar Huda ba zata yi wata biyu a gidan Arshaad ba.
Na tabbatar hakan sai yafi yiwa Maryam zafi akan yanzu a fasa kai Huda gidanta kai tsaye!.
Yanzu ki cewa Jalila ta daure ta jure ta kauda kanta, za mu yi
nasara in shaa Allah.”

BULAMA ✍️




So da Buri
Free Book
56



Sakina ce ta yi knocking aka bata izinin shiga, tana
shiga tace musu
“Masu d’aukar Amarya sun zo, suna k’asa.”

Dumm!!
Haka k’irjinsa ya buga hatta Shuwa.
Cikin dauriya Ummu ta cewa Sakinan “ta je, ga su nan zuwa”
Kallon ta Hudan tayi da idanuwanta da suka k’ank’ance suna zubar hawaye, da sauri ta juya ta fita
tana share tata kwallar..

Shuwa na hannun damanta Ummu kuma ta ruk’ota ta gefen hannun hagu,
a haka suka sakata a tsakiya suka sauk’o parlourn da ita fuskarta a lullub’e.

Kauda kai Mommy ta yi
ta share kwallar farin cikin data zubo mata!
A hankali ta mik’e
ta k’arasa wajensu ta kamo hannun Huda ta kawota kan kujerar da take akai gefenta ta zaunar da ita sannan itama ta samu waje ta zauna kusa da ita.

Ummi ce ta mik’e itama ta isa 3 seater da suke zaune su biyu ta zauna a kusa da Huda ta kamo hannunta tana murmushi (ya zamana sun sakata a tsakiya ita da Mommy )

Tsakin da Mom ta yi sai da ya d’an fito fili ba tare da ita kanta ta san zai fito d’inba!
Da sauri ta wayance ta sake yin wani sound kamar wadda abu ya mak’alewa a hak’ori
sannan ta shiga gaida su Shuwa tana mai
k’arewa gidan kallo!
Dukda cewa gidan yana da girma gashi mai bene amman hakan bai hana Mom yiwa gidan kallon k’ask’anci ba.

Gaggaisawa aka shiga yi cikin barkwanci da mutunta juna,
daga nan aka damk’awa su Mommy amanar Huda
suka amsa hannu bibbiyu suna masu farin ciki…

Mik’ewa aka fara yi da niyyar tafiya amman Amarya furr! Ta k’i mik’ewa..
Da kyar Ummi tasa hannu ta d’agota sannan ta jawo ta jikinta ta rungume ta shiga lallashinta tana cewa “muje mana dota.
Yi hak’uri kinji, kowa da haka ya fara.”

Cikin kuka, da muryarta wadda ta dad’e da dishashewa ta cewa Ummin
“Ban yi sallama da Mama ba.
Dan Allah ku kaini wajenta.
Zan biku amman sai na fara yiwa Mama sallama.”

Lumshe ido Ummi tayi tana jin yadda k’irjinta ya fara bugawa da sauri da sauri…
A hankali ta juya ta sanarwa su Mommy abunda Hudan tace

Murmushi Shuwa tayi
kafin ta cewa Ummu “ta tashi ta kamata su kaita mota.
Za suyi sallamar a waya.”

Sai da suka yi da gaske kuwa tukunna suka iya janyeta.
Tana kuka tana komai haka suka fitar da ita aka sanyata a mota Ummu da Ummi suka sakata a tsakiya
Ummi sai faman lallashinta take yi.....


Inda Mama take Mommy ta tambaya bayan fitar su.
Sakina ce ta kaita har d’akin sannan ta juya ta fita dan itama tana so ta raka Amarya.
Mota guda suka yi ita da k’awayensu su hud’u waenda suka zo rakiyar Amarya.


A zaune Mommy ta sami Mama a bakin gado
tana ta sharar hawaye..
Sai da ta k’arasa inda take ta dafa kafad’arta tukunna ma Maman ta san mutum ya shigo!
Murmushi Mommyn tayi ta zauna a gefenta sannan
tace
“Ai gara da Hajiya tace a tafi da ita ba sai kun yi sallama ba
dan na san daa ta shigo ta ganki a haka to da sake tab’arb’arewa al’amarin zai yi”

Kukan Mama ne ya tsananta a hankali ta juyo ta kama hannunta tana sheshshek’a tace
“Mommy, ga amanar Huda!
Dan Allah ki kular min da ita.
Ina tausayawa Huda dan
ban san ya zaman nasu zai kasance ba saboda na san duk su biyun basa k’aunar juna
amman kuma idan na tuna ke ce surukar ta sai hankalina ya d’an kwanta na san at least
ko da ace bata samu soyayyar Miji ba na san zata samu ta Mahaifiyarshi
Hakan zai d’an rage mata rad’ad’i da damuwa.

Naso ace Huda ta auri mai k’aunarta amman kuma k’addara ta riga fata.”
Ta k’arashe maganar tana mai fashewa da kuka.

Murmushi Mommy tayi kafin tace
“Share hawayenki, ki d’ago ki bani hankalinki.”

Da kyar Mama ta iya tsayar da kukan nata sannan ta d’ago tana mai kallon Mommy da idanuwanta da suka k’ank’ance sukai jaa.

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin tace
“Ki daina cewa Aslam ba ya k’aunar Huda!
Dan zan iya rantse miki ko shi kanshi Arshaad d’in ba ya yi mata kwatankwacin son da Aslam yake mata.”

D’an zaro ido Mama tayi tana kallonta da alamun mamaki.

“Kwarai kuwa”
Shine abunda Mommy tace
sannan ta d’aura da cewa
“Tunda na warke, although ban zauna da Aslam ba
ban kuma san yanayin shi sosai ba amman tashi d’aya na fahimci yana cikin matsananciyar damuwa!
Kullum yana fama da zazzab’i da hawan jini, anyi anyi da shi akan ya fad’i damuwar shi amma yak’i fad’awa kowa.
Sai da yaga yana shirin mutuwa tukunna ya zo ya samemu ni da Dad
yace mana ‘yana neman alfarmar mu barshi ya tafi uk
ya d’an yi y’an kwanaki’
Mu kuma ganin rashin dacewar hakan ne ya sanya muka hanashi tafiya.
Bayan Dad ya fita ne
na lallab’ashi akan ya fad’amin damuwarshi..
Da kyar ya iya gaya min
dan shi har ga Allah kunya yake ji…
‘He knows he’s selfish ta ko wanne b’angare
amma ya rasa yadda zai yi ya yakice soyayyar Huda a cikin zuciyarshi.’
Yace min ‘tun ranar da ya fara ganinta tun ba yanzu ba
Allah ya d’aura masa matsannciyar soyayyarta!
Kuma dede da rana d’aya k’aunarta bata tab’a raguwa a zuciyarsa ba
instead k’aruwa ma take yi.
Baya iya bacci baya iya yin komai cikin nutsuwa idan
ba hotonta ya saka a gaba ba yayi ta kalla.’
A ranar yace min
‘Muddin muka barshi aka d’aura auren Huda da Arshaad a gabanshi tou tabbas zai iya rasa ranshi!
Dan haka shiyasa yana ganin gara yayi nesa sosai kuma yana rok’ona ko da an d’aura auren to kar In fad’a mishi,
ko ya tambayeni kawai ince mishi nima ban sani ba’.

Naji matuk’ar tausayin Aslam a wannan lokacin tabbas, ba na so ya zama coward shiyasa na hana shi tafiya
na rok’esa Allah da Annabi ya zauna..idan yayi facing ya tabbatar da ta sub’uce mishi forever hakan will make him stronger and zai cire hope yayi moving on.

Ya yarda zai zauna bayan ya tabbatar min idan bai mutu a ranar ba to zai iya samun heart attack!
Ni kuma na duk’ufa gayawa Ubangiji
Ya saka mishi sassauci da dangana sanann ya zab’awa
Hudan Arshaad da Aslam dukkan nin abunda yake alkhairi ne a rayuwarsu.

Tun jiya na hango silver lining.
Shiyasa yau na tilasta mishi yaje d’aurin auren!
Idan an d’aura auren Huda da Arshaad a gabanshi na san hakan zai taimaka mishi
akan ace ya gudu daga reality da nauyin hope!
Idan kuma an d’aura da shi to falillahil hamdu.”
Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ci gaba
“Tunda har Aslam ya iya kawar da komai ya cire kunya ya furta mini cewa yana son Huda to tabbas na san ba k’aramin so yake yi mata ba!

Ki duba kiga yadda suke shi da Arshaad da kuma kawaici irin nashi amman ya kasa hak’ura!

Na san Aslam tun yana Yaro k’arya ba abunda ya iya baneba besides why will he even lie?
All that I’m trying to point out miki anan shine
Hudan ta tafi gidan wanda yake k’aunarta matuk’a!
Ki kwantar da hankalinki ki bisu da fatan alkhairi.........”


Direct MT estate aka wuce da ita...
Already Mommy ta saka masu aiki sun share sun goge side d’in Aslam sai tashin k’amshin turaren wuta yake yi.
Ba abunda babu na fannin furnitures, duk ragowar d’akuna ukun akwai gadaje masu kyau!
Parlourn ma yana d’auke da duk wani abun buk’ata.

Motocin suna gama yin parking aka fara firfitowa.

Tun a gate na estate d’in Anty Zainab taji inama bata zo ba!
Gashi mata y’an Maiduguri da suka shigo mota d’aya tare da su sai faman zuzutawa suke yi suna
“Ma shaa Allah! Huda kam Allah ya bata duniya” ita kuma tanajin kamar ranta zai fita!
Sannan kanta ya d’an juye
dan cewa aka yi gidanta ita kad’ai ce yanzu kuma taga an kawota nan!.
A haka dai tana ji kamar zuciyarta zata fashe ta biyewa jamaa akai ta washe baki da ita, ta bari akan In sun koma zata bugi cikin Khadija ta ji komai dan ta san idan ba bugar cikin nata tayi ba to ba zata tab’a gaya mata ba!
Sun sha yin fad’a da ita Khadijar ba sau d’aya ba akan su Hudan.

Ummi da Ummu ne suka ruk’ota, suna zuwa main door na shiga gidan suka umarceta da ta shiga da bismillah da k’afar dama, haka ma k’ofar side d’in Aslam da tazo shiga!
Yadda suka ce hakan take yi da fuskarta a rufe cikin laffaya tanata kuka.

Sai da suka kaita bakin gadonta sannan suka ajjiye ta da bismillah.

Bayan an d’an ragu a d’akin
Ummu ta k’ara mata da nitsatsiyar nasiha!
Basu wani dad’e ba suka fara shirin tafiya hatta gifts da abincin da Dad ya shirya musu ma mota kawai aka kai
dan suna idar da sallar Magrib suka fara zuwa suna yi mata sallama suna ficewa……
Jama’a da friends d’insu in banda santin estate d’in da side d’inta ba abunda suke yi,
a haka kowa ya watse.
Aka barta ita da su Sakina da Khadija da friends d’insu guda biyu da suka zauna dan ragowar cewa suka yi ‘za su wuce saboda basa so su yi dare’…..
Da kyar da sid’in goshi Huda ta d’an tsayar da kukan nata, bayan dogon lallashi daga su Sakina ta yi shiru
ta bud’e fuskarta.
Tana jinsu suna ta hira ana shewa amman ta kasa tanka musu
Istigfari kawai take tayi
saboda sam! Tunanin Arshaad yak’i fita daga ranta.

Daga masallaci direct gida Aslam da Dad suka wuce side d’in Mommy.
Suna zaune ita da Gwaggo Asabe da alamun magana suke mai muhimmanci su Dad d’in suka shigo.
Mik’ewa Gwaggo Asabe tayi zata fita Dad yayi saurin cewa “ta dawo ta zauna
Nasiha za su yiwa Ango!”….
Sun kusan 1 hour suna yi masa Nasihar
daga nan Dad ya mik’e yayi musu sai da safe.

Kana ganin Mommy da Gwaggo Asabe ka san suna cikin farin ciki.

Mommy ce tace
“To ka tashi ka je kuyi siyan bakin mana.
K’awayenta fa kai suke jira su tafi”

Kamar zai yi kuka yace
“Mommy siyan baki kuma?
Kin san fa a yanda auren nan yazo. Ki barshi kawai su yi tafiyarsu,
Ina son ganin Arshaad
first.”
Ya fad’a yana mai mik’ewa zai fita.

“Baya nan”
Yaji muryar Mommy.

Da mamaki ya juyo kafin yace
“Ina ya je?”

“No body knows”
Mommy ta fad’a tana mai mik’ewa ta k’araso inda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login