Showing 51001 words to 54000 words out of 100703 words

Chapter 18 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

4499

had’uwarsu da irin kalar warning d’in da yayi mata!
Sai yanzu ta gane dalilin tambayoyin Abba Madun
da kuma dalilin damuwar da ta hango shimfid’e akan fuskarsa.

“Shigo mana Mama”
Muryar Kaka ta katse mata tunani…
A hankali ta taka ta k’arasa cikin parlourn k’irjinta na dukan uku uku!!!

A k’asa kan kafet ta zauna gefen kafar Madu,
muryarta na d’an rawa tace
“Ina wuni Daddie”

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e, kafin ya ja wani yawu ya had’iye
sanann ya d’ago ya zuba mata idanuwanshi yace
“Alhamdulillah, Maryama”

A hankali ta sake cewa
“Ya hak’uri”
Bata jira jin amsarshi ba
dan bataso maganar tasu tayi tsayi kar ya ga zak’ewarta kuma bataso ya kasance batayi mishi gaisuwa ba dan ta san yanda yake da Ummi d’in,
dan haka tace
“Allah ya gafarta mata yasa Aljannah ce makoma”

“Ameen” ya ce.

A hankali Aslam ya gaidata cikin girmamawa, da
kulawa ta amsa
kafin Granpa yace
“Marigayiya ta bani sak’o wajenki”

Da sauri Mama ta d’ago kai tana kallon shi..
Shima itan yake kallo kafin yace “A ranar da zata rasu tace ‘In sake nema mata yafiyarki’.”

Da sauri Mama tace
“Na riga na yafe mata
tun ba yau ba mun gama wannan maganar da ita.
Mun yafe mata daga ni har Huda fatan mu Allah ya ji k’anta da rahama”

A hankali Granpa yace
“Ameen”
Sannan yad’an sake muskutawa ya gyara zamanshi
kafin yace
“A ganina ya dace ace nima na zo na nema yafiyarki tun kafin azo a nema min”

Ba Mama ba hatta su Kaka da Aslam
Granpa suka kalla fuskokinsu d’auke da tsananin mamaki!

Bai damu da yadda suke kallonshi ba yace
“Shekaru 29 ko ace 30 baya!
Na san na baku wahala ke da Abba…
Ban san halinda za ku shiga ba
na biyewa b’acin rai da zuciya na turaku chan wata k’asa sannna bayan shekaru goma duk irin shak’uwar da kuka yi ban duba ta ba na sa Abba ya sake ki!
Ki yi hak’uri….”
A hankali ya kalli su Madu yace
“Kuma ku yi hak’yri ku yafe min abubuwan da na aikata muku”

Da kyar Madu wanda ya shiga shock yace
“Ba komai ya wuce Allah ya yafe mana gaba d’aya.”

“Na gode” Granpa yace,
sannan ya maida idanuwansa kan Mama wadda ta kasa cewa komai.
Ganin ta yi shiru yasa ya sake cewa
“Ki yi hak’uri Maryama ki yafe min dan Allah....”

Da sauri Mama
wadda sai yanzu ta dawo haiyyacinta tace
“Daddie dan Allah ka daina bani hak’uri..
Gaba d’aya am not comfortable with you apologizing.
Ka yi hak’uri dan Allah ka daina bani hak’uri.
Na hak’ura na yafe na manta komai, mu yafewa juna
muma mun yi laifi ni da Abba dan kamata yayi ace dole muma mun tsaya mun bi zab’in iyayenmu…
Ku yi hak’uri ku yafe mana”
Ta yi maganar tana kallonshi sanann ta juya ta kalli su Madu.

Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin yace
Na gode Maryam
amman in dai da gaske kin yafe min ke da iyayenki
To
a yanzu Ina so mu d’aura aurenki da Abba!”

This time around k’amewa Mama tayi k’am!
Hatta numfashinta sai da ya kusan d’aukewa….

Ganin ya sake yunk’urowa zai yi magana yasa kawai ta fashe da kuka sai kuma ta tashi da sauri ta fita a parlourn
tana kuka sosai.

Da sauri modu ya mik’e zai bita
Granpa ya hanashi ta hanyar cewa
“Barta, kyaleta.
Dawo ka zauna mu k’arasa magana.”

Ahankali ya koma ya zauna
jikinsa duk ba laka.

Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin yace
“Ka lallab’ata.
Na san dama dole ba lalle ta amince lokaci guda ba.
Amman yau! Ni, a matsayina na Mahaifin Yakubu
na zo nema mishi auren Maryam.
Ina fata za a bamu.”

Tun kafin ya rufe bakinsa Kaka yace “na baku, za ku jimu nan ba da jimawa ba in sha Allah.”

A firgice Abba Madu ya juya yana kallonshi yana shirin yin magana Kaka ya mik’e tsaye
yace
“Mun gode kwarai Granpa.
Ba ka san yadda maganganun ka na yau suka sanyani cikin tsananin farin ciki ba!
Allah yasa ka gama da duniya lafiya
In sha Allah ni da kaina zan samu Maryam mu yi magana da ita, daga nan zan tsayar da rana kawai a d’aura aure”
A hankali ya kalli Aslam yace
“Ina so ka yiwa Abba albishir d’in
Baba Bashir ya sake bashi Maryam a karo na biyu!
Sannan ba zai yi k’asa a guiwa ba wajen ganin ya mallaka mishi ita cikin sauk’i.”
Daga haka ya kallesu yace
“Bara in je gida na barku lafiya”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fita yana share wasu hawaye da shi kanshi bai san dalilinsu ba.

Kana ganin Madu ka san yana cikin tsananin rud’ani!
A hankali ya koma ya gyara zamanshi da kyau ya hau kame kame
kafin ya daure yace
“Mun gode Granpa..
Kwarai za ku jimu in sha Allah”
Ya fad’i haka wani gumi yana keto masa.

Tashi d’aya Granpa ya fahimci akwai wani abun a k’asa
haka ma Aslam,
amman ganin da suka yi
tunda har suka b’oye kuma ga abunda suka gaya musu sai kawai suka bari akan
bara kawai suma su bisu a hakan. Dan haka Granpa ya dogara sandarshi ya mik’e tsaye sannan yace
“Na barku lafiya”
Daga nan ya juya ya kama hanyar fita.

A hankali Aslam ma ya mik’e ya yi wa Madu sallama ya fice.
Har ya isa mota ya bud’ewa Granpa ya shiga ya rufe mishi sannan shima ya zagayo ya shiga ya tada motar kansa a d’aure yake!
Ga dai abun farin ciki,
abunda yana d’aya daga cikin abubuwan da yake mafarkin son ganin sun tabbata
amman kuma Allah yasa babu wata matsalar da zata kunno kai ta b’angaren su Madu
dan nan kam a b’angaren su Granpa ya gama gyara komai.............


Mama tana shiga ta tarar da Shuwa a yadda ta barta, suna
had’a ido ta sake fashewa da kuka ta k’arasa inda take ta tsugunna a gaban kujerar da take ta d’aura kanta akan cinyarta.

Shafa kanta Shuwa tayi kafin tace
“Lafiya Maryam, mai ya faru?
Nifa daman yadda naga Abban ku ya shigo na san akwai matsala.
Mai ya faru?”
Tayi mata tambayar cike da fargaba.

A hankali Mama ta share hawayenta ta d’ago tace
“Hajiya matsalar ba daga kowa bane ba, daga mu ne!
Matsalar daga ni da Abba ne!
Faith d’inmu a baibai yake
duk lokacin da muke so ko ya dace mu kasancewa da juna sai a samu matsala ta yadda indai muka zamo tare wani sai ya k’untata…
Mai yasa farin cikin mu yake tahowa a tare da bak’in cikin wasu?”

BULAMA ✍️



So da Buri
Free Book
66


Mikiya Writers Association.

39 DAYS AGO!
Gandun Albasa.
Gidan shiruuu, gaba d’ayansu
suna zaune kowa yayi jugum!
Kamar anan ake zaman makokin.

A hankali Shuwa ta juya ta kalli Ummu kafin tace
“Gaskiya fa Mama ta fad’a Ummu, ku je kawai ke da Sakina..
Ai ta ce ta kirashi ko?”.
A hankali Mama ta d’aga kai alamun ‘eh’.
Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e kafin tace
“To shikenan Hajiya.
Sakina taso mu je,
Babanku yana waje.”
A hankali Sakina ta d’an kalleta sai kuma ta d’auke kai tace
“Ummu, dan Allah ki je kawai ko da Sumayya ne
bana son zuwa gidan wallahi”.
D’an k’ura mata ido Ummu tayi
kafin tace
“Taso mu je!
Ba na son shirme..
Ba zaki yiwa su Abba da Aslam gaisuwa ba ko me??”.
A hankali Mama tace
“Ummu barta kawai
ku je ke da Sumayya.”
Shiruu Ummun tayi kamar za tayi magana sai kuma tace
“Sumayya mu je”
Ta fad’i hakan tana mik’ewa ta d’au mayafinta ta nufi k’ofa
da alamun ranta ya b’aci.

Suna fita ita da Sumayya Hajiya Shuwa ta mik’e ta fita tsakar gidan don yin zagaye
saboda kumburin da k’afafuwanta suke yi idan ta zauna shiru.

A hankali Mama ta mik’e ta koma kan kujerar da Sakina take zaune 2 seater..

Tana ganin ta dawo kusa da ita ta tashi ta zauna da kyau sannan ta d’an sunkuyar da kanta a hankali tace
“Bara inje d’aki in kwanta”
Tana shirin mik’ewa Mama ta kamo hannunta ta rik’e.

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta sunkuyar da kanta k’asa.

Sai da Mama ta gama k’are mata kallo ta gama nazartar ta tukunna tace
“Nima b’oye min za ki yi?”

Da sauri Sakina ta d’ago tana kallonta kafin ta juyar da kanta tace
“Me ne zan b’oye miki Mama?”
Tana k’ok’arin danne kukan da taji ya taho mata.

A hankali Maman ta sa hannunta ta juyo da fuskarta
sannan ta ce
“Tun ranar da kikace kin bawa Ashraff go ahead ya turo Sakina har yau ban ga walwala a kan fuskarki ba!
In akwai wani abun ki yi magana a samu a gyara
Idan mai gyaruwa ne..
B’oye b’oye ba abunda yake janyowa sai dana sani a rayuwa.
D’azu Ina jinki a band’aki ke kad’ai kinata kuka!
Meye ne yake damunki?
Ko na tashi daga Mama na koma wata daban wadda ba zaki iya gayawa damuwarki ba?”

Duk k’ok’arin Sakina na ganin ta tsayar da kukanta kasawa tayi, tashi d’aya ta hau ambaliyar hawaye ta shiga kuka tsakaninta da Allah..

Janyota Mama tayi zuwa jikinta ta rungumeta.
Sai da tayi me isarta
tukunna ta yi shiru da taimakon lallashin Mama
kafin a hankali ta fara magana
“Daman akan Ya Auwal ne cousin d’in su Hudan............”
Tun ranar da suka fara ganin juna har kawo yanzu
ba abunda Sakina ta b’oyewa Mama…

Kallon ta Maman take yi tana sake wa kafin
a hankali ta ce
“Sakina wa ya gaya miki ana aure saboda a yakice soyayyar wani daga cikin zuciya?”
Bata jira jin me zata ce ba
tace
“to bari kiji in gaya miki..
Shekarata goma sha takwas tare da Ya Usman matsayin mata da miji amman har yau ba abunda ya shiga zuciyata game da shi ta fannin soyayya
sannan ba abunda ya ragu a cikin soyayyar Abba a zuciyata.”

Da sauri Sakina ta d’ago tana kallon ta sai kuma ta fashe da kuka ta ce
“Mama dan Allah kar ki yi min fatan in yi dakon soyayyar Ya Auwal haka har k’arshen rayuwata!
Wallahi tallahi In dai yadda nake ji akanshi haka zan ci gaba da ji har abada bayan bana tare da shi tabbas mutuwa zan yi”
Ta k’arashe maganar tana kifewa akan cinyar Mama tana sakin wani sabon kukan.

A hankali Mama take shafa kanta….
Sai da taji ta d’anyi shiru tukun tace
“Sakina ba zan b’oye miki ba,
kin yi mistake!”

A hankali ta d’ago tana kallon Mama da dara daran idanuwanta da suka rine sukayi jazir.

Jinjina kai Maman tayi alamun tabbatarwa.

Cikin share hawaye Sakina ta ce “Mama kin ji fa abunda Mom da Mammy suka yi min
still in aureshi?
Daman ni saboda family d’insa shiyasa na k’i tun farko
bana san issues
sannan…”
Sai da ta d’anyi k’asa da kanta kafin tace
“Sannan womanizer ne
shi ne ya yiwa Jalila ciki fa”

Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e kafin tace
“Sakina Ubangiji ya halicci bayinshi kowa da irin yananyin tashi k’addarar!
Idan Allah yayi wannan ce k’addararki kina ganin kina da wayon da za ki kufce?.

In dai Auwal yana sonki tsakani da Allah to zai daina abubuwan da yake yi, za ki iya gyarashi
besides
ai Auwal d’in ya shiryu
ke kanki kin ce Arshaad tun ba yau ba ya cewa Hudan ya ga changes a tare da shi
sannan kin ce Mahaifinsa shima yace ya shiryu!
Ni a ganina
zaki iya sake gyarashi tunda yana son ki wanda Allah kad’ai ya san d’umbin ladan da za ki samu.
Tabbas ban so ki aura irin Miji mai halinshi ba ko da ace ya shiryu amman in dai haka Allah ya tsara
yana sonki
kema kuma kina son abunki
to ya za ai?.
Kuma Mahaifinsa ma baya k’in ki yana son ki wanda shi ne
yake da say a gidan!
Tabbas Mom matsala ce
amman ni a ganina zugar Mammy ce…yadda
kika ce tanata kuka ta rikice a lokacin da ya suma
na tabbatar inda ba a kawo kud’in auren ki ba to da tuni yanzu tazo nan gidan saboda farin cikin d’anta dan tana tsananin sonshi
wanda hakan shi zai sakata ta sauk’o ta so ki
In sha Allah.

Yanzu kam ba abun yi sai dai hak’uri…
But by any chance kar ki sake yunk’urin toshe hanyar da za ku bi ku mallaki juna ke da Auwal! Ko da wasa, tunda
kuna son juna.”

Kukan da Sakina take ne yasa Mama ta janyo ta jikinta,
a hankali ta shiga lallashinta kafin tace
“Ki yi hak’uri
Allah ya zab’a miki mafi alkhairi.
Ku yi ta addua
Allah ya zab’a mafi alkhairi.”

Da kyar Mama ta samu ta lallab’ata ta yi shiru
dann ita kam ta san inba wani tsananin rabo ba to
Auwal yayi mata nisa!
Ta riga ta datse duk wata igiyar da zata k’ullasu su kasance tare k’ark’ashin inuwa d’aya da hannunta….



A Cikin kwanakin da ba su kai wata d’aya ba da Anty Zainab ta yi da Sadiya tabbas ta fahimci ba zaman amana take yi da ita ba!

Mamaki k’arara take yi game da yadda Abotar tasu take k’ok’arin juyewa ta koma wani abun na daban.

Haka nan ita za ta yi musu girki da kud’inta saboda duk wani ragowar gari ko abun dafawa da suke da shi Umma ta tattare tace “babu ya k’are!”
Sai ta fita aiki ita da Jalila su dafa su ci. Tun bata gane ba har tazo ta fara fahimta..
Ga shegiyar k’azanta daga Umma har Jalilan
sannan wani lokacin Jalila har yada mata da magana take yi wai ‘anzo an zaune musu a gida!’ Sannan Ya Ja’afar kwata kwata basa kula da shi
dan wani lokacin wandonshi har tsutsa ne suke binshi
gashi kullum cikin datti
kacha kacha
especially gashin kansa sak mahaukacinsa!

Haka nan zata tartare kitchen da band’aki dan idan zai yi tsutsu ba za su gyara ba!
Sannan ta gyara Ya Ja’afar ta fita aiki ta je ta dawo ta dafa kuma su ci tare.

Ana cikin haka Junaidu ya dawo… Ranar suna zaune a d’aki suna d’an tab’a hira kawai suka ganshi ya shigo!
Da farko Umma tsorata ta yi dan ihu ma ta yi,
fahimtar da tayi ba ita kad’ai ce take ganinshi ba yasa ta tashi ta k’arasa ita da Jalila inda yake.
Sai da suka d’an tab’a fuskarshi da jikinshi suka tabbatar da shi d’inne tukunna suka rungume shi a tare suka fashe da kuka…
Tabbas shima yayi matuk’ar kewar gida shiyasa bai san lokacin da hawaye suka wanke mishi fuska ba.
Da taimakon Aanty Zainab aka samu suka yi shiru
ita ma ta rungume shi tana d’an nata hawayen sannan suka nema waje suka zazzauna.........


Tun daga lokacin duniya ta dawowa Umma da Jalila sabuwa!…. Hankalin Junaidu ba k’aramin tashi yayi ba ganin halin da Ya Ja’afar ya ke ciki.
Bai yi k’asa a guiwa ba haka suka kinkimeshi shi da Jalila suka sa a mota suka nufi asibiti…
Bayan y’an dube dube Likita ya basu sunan asibitin da ya kamata a kaishi.

Ba abunda ya fi bawa Jalila mamaki irin kyan asibitin
da mak’udan kud’ad’en da Ya Junaidun ya bayar
daga nan suka amshi Ya Ja’afar d’in.
Kusan kamar gidan mahaukata haka wajen yake
amman ana basu kulawa da treatment mai ma’ana.

Suna dawowa washegari
ya fara da case d’in Baba shima wanda tun ranar da ya dawo yaje ya ganshi a gidan Kaka don tun dawowarshi a wajen Baba talatu yake.

To anan ma an kashe kud’i wajen bincike da ragowar abubuwa, duk kuma tare
ake zuwa da Jalila wadda babu abunda tafi sakawa ido irin aljihun Junaidun
dan haka tana dawowa gida take sayarwa da Umma Jarida! Nan kuwa suka maidashi atm….
Tun abun yana burge Anty Zainab har yazo ya fara bata tsoro saboda yadda Junaidu yake wasa da kud’i
ya kamata a bincikesa.

Ita kuwa Umma ba abunda ya dameta, da Anty Zainab tayi mata maganar ma cewa tayi
“Kar su yi mishi magana
yayi tunanin zarginshi suke yi ya rage basu kud’in”
Tun daga nan Anty Zainab taja bakinta tayi shiru bata k’ara magana ba.


Su Umma duniya ta dawo sabuwa! Hatta shinkafa basmati ake ci a gidan
Kaji kuwa ba a magana..
Wani zubin ma da daddare sai dai a siyo tsire ko pizza da fresh milk aci a kwanta.

Har gidan su Kaka da Abba Madu junaidu bai bari ba
alkhairi na yau daban na gobe daban…


Tabbas zama da Sadiya sai mutum mai d’ankaren hak’uri!
Dan wannan duniya da jin dad’in da ta samu
sai ta mayar da Anty Zainab kamar wata bola!
Idan an kawo kaji sam ba zata bari ta tab’a ba ma, ita da kanta za ta gyara ta soya su d’ibar mata dan wulak’anci a nata kason kai da k’afa suke fitowa, sam basa la’akari da ‘shi Junaidun nephew d’inta ne itama’
Idan ya zo fita suka ce suna buk’atar kud’i har da na Anty Zainab yake ajjiyewa amman sai su hanata!
Abubuwa kala kala haka ta dinga fuskanta wanda daman ance ba a gane asalin halin mutum sai an zauna tare ko an yi yunwa…
Gashi wani abun mamaki
sam Umma tak’i yarda su koma wajen malaminsu tare!
Kullum sai sun bari ta fita aiki sai su je ita da Jalila, idan ta dawo sai ta tarar sun je sun karb’o mata sak’o. Gashi kullum ita ke bada kud’i su basa bada ko sisi
wannan watan tun kafin wata ya zo k’arshe an bita bashi
ba dan Khadija da Yayarta sun aiko mata kud’i ba to da bata san ta ya zata dinga zuwa aikin ba ma.

Haka kurum yau taji bata yarda da bayanin su Umma ba dan agaskiya so take a san yanda za ai ta koma gidanta!
Shiyasa tana tashi a aiki ta wuce wajen mutumin da kanta.

Hankalinta ba k’aramin tashi yayi ba da taji bayanin mutumin….tabbas ashe shiyasa ko waya idan tace su kira a gabanta sai suce an sace wayar mutumin bashi da waya yanzu.
Jiki ba kwari haka ta yi mishi sallama dan ita kasa ma yi mishi bayanin komai tayi
ta mik’e kawai ta tafi......

A tsakar gida ta samesu
Suna gashin zabi akan abun gashi, gaba d’aya gidan ya d’au k’amshi.

A hankali ta k’arasa ta zauna a kan tabarmar da suka shimfid’e a tsakar gidan ta kalli Jalila ta ce
“Auta dan Allah d’an kawo min ruwan sanyi a fridge d’in Junaidu in akwai”

Ba tare da ta kalletaba tana chattn a wayarta tana nan kwance akan tabarmar bata motsa ba tace
“Babu!”

Ajiyar zuciya Anty Zainab ta sauk’e kafin tace
“Je ki duba”
Ta yi maganar cikin d’an tsare gida.

Banza Jalilan tayi da ita.

“Hmmm”
Umma wadda take zaune akan kujerar tsugunno a gabn abun gashin tace sannan ta juya ta kalli Jalilan tace
“Auta dan Allah je ki duba mata mana.”

Tsaki tayi ta ajjiye wayar sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login