Showing 42001 words to 45000 words out of 100703 words
Chapter 15 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt
har
na aureki?”
Muryar Daddy ta katse mata maganar da ta yunk’uro za ta ci gaba.
Da sauri ta juyo tana kallonshi cike da shock!
Cikin tsanannin b’acin rai yace
“Adama na gaji na gaji da rashin tunanin ki da shirmen ki da son zuciyarki!
Na gaji wallahi..
Tsabar idonki ya rufe daga ganin gaskiya
you don’t even realize the fact that Auwal ya nutsu tunda ya had’u da Yarinyar nan.
Kar ki bari In chanza miki wallahi ba zaki ji dad’ina ba dan kin kaini bango!.”
Ya k’arashe maganar cikin tsananin fushi.
Dede nan Aslam wanda ya dawo daga kai Auwal ya dafa Daddy yace
“Daddy dan Allah ka yi hak’uri.”
A hankali Arshaad wanda ya shigo yanzun
shima ya k’araso inda suke yace
“Akwai mutane a gidan Daddy,
Abba kai yake jira ku kai Auwal asibiti suna mota.”
Kallon Mom yayi wadda ta k’ame tun lokacin da ya fara magana..
Kamar zai ce mata wani abun sai kuma kawai yayi tsaki ya juya ya fita ranshi a mugun b’ace.
Yana fita Mammy ta k’araso ta dafa ta tace
“Zo mu je”
Daga nan ta ja hannunta suka nufi wani d’akin a nan k’asan ita da k’awarta..
Suna shiga kamar jira Mom take ta fashe da kuka tace
“Akan Yarinyar chan Daddy ya gaya min wannan maganar??
Waenna irin mutanene su Maryam wai ni Adama…”
Cikin katseta Mammy tace
“Saboda haka baki ga ta zama ba!
Ko kuma ince ba muga ta zama ba har sai mun cire ta a zuciyar auwal!.
Sannan akwai wani abunda ya faru na tashin hankali d’azun nan nima na gani
amman kar ki damu dama na gama tsara mana mafita tun kafin in zo
Sannan itama wannan sai mun yi da gaske tukunna zamu cireta a rayuwar Auwal.
Da sauri Mom tace
“Kina ganin ciretan zai yiu?
Kina gani fa Arshaad bake kad’ai ba har ni d’innan gaba yake yi da ni.
In ba asirin aka karya ba ba zamu samu sukuni ba.”
Ajiyar zuciya Mammy ta sauk’e kafin tace
“Adama Allah ya jefomu cikin wasu kalar family masu zuciya mai naci dan haka sai mun yi
da gaske saboda su na fahimci
weakness d’insu mace ce!
Ki duba kiga har shi kanshi Granpa d’in
duk abun shi kina ga yana yiwa matarsa?”
Cikin kuka Mom tace
“Kullum addua ta d’aya kar Auwal ya fad’a kaidin mace kamar iyayensa
sai gashi rana d’aya ya fad’a, ni Adama ya zan yi?
Shi kad’ai gareni!
Ita kad’ai fa yake gani
ko maida hankali kwana biyun nan na lura ba yayi akan aiki
ashe ita ce sila!
Kiji Daddy tsabar rashin sanin ciwon kai wai har da ik’irarin Auwal ya nutsu! Shi a ganinshi nutsuwa ce wannan
an haukatamin kwakwalwar d’a amma shi yana ik’irarin ya nutsu…”
Ta k’arashe maganar tana durk’ushewa a wajen.
A hankali Mammy ta k’arasa ta hau lalalshinta, sai da
taga tayi shiru tukunna ta matsar da bakinta dede kunnenta ta shiga rad’a mata waensu maganganu.
Aslam da Hudan ne suka raka su Sakina har bakin mota
bayan sun lallasheta ta yi shiru da kyar!
Har da Arshaad.
Sanann suka tsaya suka kira Sumayya a wajen k’awarta suka wuce tare.
Hudan maganganu ne fal a ranta take so tayi da Sakina
amman ganin halin da take ciki kawai yasa suka yi musu godiya ta bari akan In komai ya lafa za suyi chatting.
A parlourn suka tarar da Mom Mommy da Mammy da Ummi
Dad ya had’asu gaba d’aya da alamun fad’a yake yi musu.
Suna shiga
Aslam ya cewa Hudan “taje ta had’o masa Coffee mai zafi please”
Daga nan ya wuce ciki bayan ta amsa masa da “to” ita kuma
ta nufi kitchen d’in direct.
Arshaad ma ya wuce d’akinsa.
Arshaad yana shiga d’akinsa Mammy ta mik’e ta nufi d’akin
dan they have to talk, ta lura in ta biye shi gaba zai yi da ita.
D’azu sau biyu tana zuwa d’akin nasa bata sameshi ba.
Tana shiga su Dad suka gama zaman nasu suma aka mik’e kowa ya kama gabansa.
Ta gama had’awa kenan ta d’auko flask za ta juye wayarta ta fara k’ara!
Tana dubawa taga sunan Sakina dan haka tayi saurin amsawa ta kara a kunnenta.
Ko sallamarta Sakinar bata amsa ba tace
“Hudan d’anyi sauri ki fito kinga akwai sak’on da zan baki ashe na manta.”
“Ok”
Hudan tace sannan ta kashe wayar ta ajjiye flask d’in ta rufe had’in nata ta fita.
Tana fita wani mutum ko wata mata ta/ya shigo ta k’ofar baya sanye cikin bak’ak’en kaya kamar irin na leda d’innan na tare ruwa an rufa har hular saman fuska.
Ta chan ciki a fuskar da mask bak’ik’irin, baka ganin komai hatta idanuwan a rufe suke da bak’in glass.
Tafin hannu da k’afa kuma duk da bak’ak’en socks…..
Wani ruwa aka zaro a cikin syring aka bud’e had’in coffe d’in da Hudan ta gama had’awa aka b’alle kan syringing kamar za a matsa sai kuma aka tsaya aka yi shiruuu!
Da alama mutumin ko matar is having second thoughts.
Ahankali aka ja wani d’an siririn tsaki aka mayar da murfin aka rufe aka ajjiye syringing a gefe kamar ana tunani…
Motsin mutum ya ji ko ta ji
dan haka aka yi saurin d’agowa ana kallon k’ofar bayan ta inda aka shigo
ai kuwa aka ci sa’ar ganin giftawar inuwar mutum!
Lalle kuwa ko waye ya gifta to ta/ya san ya ganshi ko ya ganta! Dan haka da sauri aka
bud’e k’ofar bayan aka bi Inuwar da aka gani amman ko da wasa babu alamar mutum a wajen…
Har bayan compound sai da ya/ta zazzagaya amman ba kowa.
Ya/ta dad’e a tsaye tana/yana tunani kafin chan ya/ta nufi hanyar kitchen d’in da niyyyar d’auke syringing da ta/ya manta akan kanter kitchen d’in kusa da tray da coffe d’in da ya/ta had’a.
Tana/yana zuwa tayi/yayi saurin ja da baya
sakamokon hango Huda da Ummi a cikin kitchen d’in!
Hudan tana juye coffe d’in a cikin flask Ummi kuma ga wani abu a hannunta tana sha suna d’an hira..........
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
64
Mikiya Writers Association.
Da d’an saurinta ta fita ta nufi gate saboda ta ji Sakina tace mata ‘ta yi sauri’ Kuma ta ji muryarta dishi dishi
sannan kamar maa fa ba muryar Sakinar ta ji ba!
Gidan ba kowa shiruu, bak’in duk an watse kasancewar kowa da motarsa yazo wasu kuma drivers ne suka kawosu suka tsaya suka jira su
shiyasa ana gamawa kowa ya kama gabanshi.
Sai da ta kusan kaiwa gate tukunna ta danna kiran Sakina.
Bugu uku ana hud’un ta d’auka, tana d’auka Hudan tace
“In fito ko za ki shigo?”
Da mamaki Sakina ta zare wayar daga kunnenta ta kalli sunan sanann ta mayar tace
“Ki fito Ina?
Ina zan shigo?”
Turuss!
Haka Hudan taja ta tsaya
itama ta zaro wayar ta kalli sunan kafin ta mayar tace
“Sak’on fa da kika ce za ki bani?”
Cikin rashin fahimta Sakina tace
“Wanne sak’o?”
Ahankali Hudan ta sauk’e ajiyara zuciya tace
“Dan Allah Sakina bar wasa, yanzun nan ki ka kirani kika ce in fito kin manta sak’o in zo in karb’a da sauri…”
Cikin katseta a d’an firgice Sakina tace
“Hudan yi sauri ki koma gida
maza maza yanzun nan!
Inaga kidnappers ne suka yi hacking wayata
sun ga yau kuna taro.
Yi maza ki koma ciki da sauri
kar ki sake fitowa.”
Da sauri kuwa Hudan ta juya k’irjinta yana dukan uku uku!
Har da d’an gudu ta shiga had’awa da shi.
Parlourn ba kowa shiruu, nan ma duk an watse….
Haka nan ta wuce kitchen d’in jikinta yana karkarwa tana salati.
Tana shiga taga kamar an fita ta k’ofar baya!
Dan haka tsoronta ya sake nunkuwa.
A hankali ta shiga takawa tana kallon k’ofar da aka bi aka fitan dan gani take yi kamar har yanzu ana tsaye jikin k’ofar ba a matsa ba!
“Huda”
Ummi wadda ta shigo yanzu taga tana sand’a ta kira sunanta.
A mugun tsorace tace “wayyo Allah!!” Sai kuma ta juyo jikinta yana karkarwa.
Dariya Ummi tayi kafin tace
“Matsoraciya!!!
Ai kuwa gara tun wuri ki yakice wannan tsoron saboda gidan da za ku zauna a UK inaga ya kusa rabin wannan…
D’azun Dad yake gaya mana
Granpa although yana fushi da Aslam akan ki
amman ya kasa jurar fushin da yaji labarin zaku koma UK
ya bashi kyautar gida da mota a chan.
A hankali ta kalleta kamar za tayi magani sai kuma ta sunkuyar da kai kawai
kafin ta juya ta nufi inda ta ajjiye had’in coffee d’in Aslam.
Murmushi Ummi tayi,
ganin kamar Hudan bata son maganar yasa itama ta kawar da zancen ta hanyar cewa
“Yauwa coffe d’innan na biyo!
Gaba d’aya drinks d’in nasu na yau zak’iii sosai kaina har sarawa yake yi idan nayi sipping.
Allah yasa baki saka sugar da yawa a wannan ba, bana
son sake saka wani abu mai sugar sosai a baki na.”
A hankali Hudan wadda duk jikinta yayi sanyi daga fitarta zuwa yanzu tace
“Eh.
Naga kamar shima baya so sosai shiyasa dama zan
ajjiye mishi a gefen tray d’in in yana so sai ya k’ara.
Murmushi Ummi tayi sannan tace
“To za a zuba min inshaa ne
ko sai na jira an fara kai mishi ya d’iba?”
Ta k’arashe tambayar cikin sigar tsokana.
Murmushi mai had’e da y’ar dariya Hudan tayi
kafin tace
“Haba Ummi”
Tana mai juyawa ta d’auko cup mai d’an girma, ta dawo ta hau tsiyaya mata.
Sai da ta kusan cika kofin tukunna Ummin tace
“Okay tam ya isa haka na gode dota, Amaryar Aslam.”
Sunkuyar da kai Hudan tayi…Ta lura Ummi so take sai taga ta saka ta tayi walwala
shiyasa kawai ta d’an sake
suka hau hirar yadda birthday d’in ya kasance, suna hirar tana juye coffe d’in a cikin flask……..
Ummin kuwa daman hakan take so dan ita kunyar Hudan ma take ji akan abunda aka yiwa Sakina yau gashi saboda su Shuraim takanas ta zo
shiyasa ta dinga janta da wasa har sai da taga ta d’an sake
tukunna ta shirya bata hak’uri akan abunda ya farun!
A lokacin Huda har ta juye
ta had’a tray ta d’aura cup da spoon da sugar tana shirin d’auka Ummi tace
“Amm Huda
iwant to apol....”
Kamar an mak’ale ta haka maganar tata ta tsaya cak!
Da sauri Hudan ta ajjiye tray d’in ta nufeta saboda yadda tana juyawa taga Ummin ta damk’i wuyanta kamar zata shak’e kanta sannan ta runtse idanuwanta.
Da kyar Ummi ta iya cewa “ya subahanallah!”
Sai kuma ta zube a wajen ta fara tari…..
“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Hudan ta ambata a firgice da k’arfi!
Sakamokon ganin jini yana fitowa daga bakin Ummi wadda take nan k’asan tiles d’in kitchen d’in kwance tanata tari.
Da sauri ta durk’usa ta hau jijjigata tana “Ummi! Ummi!! Ummiii!!!
Abbaaa! ya Aslam!
Ya Arshaad!
Ummi ki tashi..”
Kuka take tana ihu tun k’arfin ta dan tun lokacin da ta durk’usa akan Ummin ta ga ta daina motsi sannan jikinta ya sake.
Da gudu ta mik’e ta nufi k’ofa da niyyar fita ta kira jama’a azo a kai Ummi asibiti…
Tana gudu tana juyowa tana kallon Ummi
bata yi auni ba taji ta fad’a jikin mutum!
Da sauri ta d’ago tana kallon Arshaad wanda shima ita d’in yake kallo bakinsa yana d’an rawa da alamun magana yake son yi amman ya kasa.
Cikin kuka ta hau juyawa tana nuna mishi Ummi wadda ke nan kwance a k’asa kan tiles!
Sannan ta juya da gudu ta nufi Ummin tana cewa
“Harda jini! Tama daina motsi”
tana mugun kuka.
Da kyar Arshaad wanda gaba d’aya ilahirin jikinsa ya d’au karkarwa tun lokacin da ya ga Ummin nan kwance, ya taka ya k’arasa inda Hudan da Ummin suke.
Da sauri ya durk’usa a wajen a mugun rikice yace
“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Kawai kuma sai hawaye ya biyo ta idanunsa.
Da sauri Hudan tace
“Ya Arshaad dan Allah kar ka ce ta mutu!
Wallahi bata mutu ba!
Bata mutu ba!!
Ka kaita asibiti zata farfad’o.
Dan Allah ka kaita asibiti..
Ummi ki tashi!
Abbbbbaaaa!!!”
Ta sake kwala kiran Abba dan taga Arshaad d’in yak’i motsi kwata kwata so ba lalle ya iya tab’uka komai ba,
da alamun ya yi mugun firgita da ganin Ummin.
A rikice Aslam ya afko cikin kitchen d’in sanye da bathrobe a jikinsa da alamun ma bai gama wankan ba dan har da y’ar kumfa a gefen kumatunsa.
Ganin Ummi yasa shima ya k’araso ciki da mugun gudu ya durk’usa a inda suke
dai dai nan su Shuraim suma suka k’araso cikin kitchen d’in.
Sai ga Mom itama ta shigo tana cewa
“Ife ifen me nake ta ji ne wai hak……?”
Muryarta ce ta katse sakamokon kitchen d’in da taga cike da jama a a nata ihu ana kuka!
Dan su Shuraim suma suna shiga suka yi kanta sukai joining Hudan a kukan.
Da sauri ta k’arasa tana cewa “waye ba lafiya ne mai ya far..”
Maganarta ce ta katse sakamokon had’a ido da tayi da Aslam! Sanye cikin bathrobe…
Da mamaki take kallonsa har da y’ar kunfar sa a gefen fuska, har zata yi masa maganar fitowar dayayi half naked dan bathrobe d’in bata da wani tsayi sosai sai kuma kawai ta shareshi dan jin dalilin kukan da take ji ne priority yanzun.
D’auke kanta tayi ta maida inda su Hudan suke durk’ushe….
Dishi dishi ta fara gani
sakamokon Ummi da ta gani kwance bakinta duk jini!
A hankali jikinta na mugun karkarwa tace
“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Sai kuma ta tafi luuuuuuu ta sume a wajen…
Sudais da Shuraim ne suka fara k’ok’arin ciccib’ar Ummi
dan haka Hudan ma ta sa hannu suka d’auketa.
Aslam yana ganin haka ya bisu a baya duk ya rikice…
Da gudu ya wuce su ya shiga d’aki ya d’auko mukullin
motarsa ya mik’awa Huda yace “su jira sa”
Sannan ya koma ya zura jallabiya mai kauri daman already ya saka boxes a k’asan bathrobe d’in! Ya
fito ya bi bayansu.
Yana zuwa ya kunna motar already sun gama shiga
suka yi gaba kowa hankalinsa a tashe sai kuka su Hudan suke yi.
Da kyar Arshaad ya iya mik’ewa ya d’auko ruwa a fridge ya shiga yayyafawa Mom……
Har ya d’an fara tsorata dan da farko k’in farkawa ta yi, kafin
daga baya kuma ta farka a firgice tana salati sai kuma ta tashi ta zauna ta fashe da kuka!
Kallon inda taga Ummi d’azun tayi ganin ba kowa sai d’an ragowar jini jinin da aya zuba a k’asa ne yasa a rikice ta juyo tana kallon Arshaad
kafin tace
“Tana Ina?”
Bai ce mata k’ala ba!
Dan kanshi a mugun d’aure yake ‘jini, Ummi, how?’
Sune abubuwan da suka taru suka hautsina mishi kwakwalwa.
Mik’ewa kawai yayi ya wuce d’akinsa ya d’auko key ya cire rigar suite d’in jikinsa ya rage daga long sleeve sai dogon wando da belt, ya fito ko cover shoe d’in k’afarsa bai tsaya chanjawa ba.
A parlourn ya tarar da Mom tanata faman safa da marwa
Yanzun ma bai kulata ba ya wuce ita kuma ta bi bayanshi da sauri suka fice.
Sai da suka shiga motar ya kunna tukunna ya kira Aslam.
Shuraim ne ya d’auka, nan yake tambayarsu “suna Ina?”
Cikin kuka yace
“Basu riga sun k’arasa asibiti ba amman duk wanda suka samu mai kyau nearby nan za su je”
Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e daga nan ya katse kiran ya tada motar ya fice daga gidan.
Driving kawai ya hau yi towards asibitin da ya san yana a kusa dasu mai kyau….
Kamar had’in baki kuwa
yana shiga ya hango motar Aslam nurses suna d’aura Ummi a akan gado.
Yana k’arasawa yayi parking suma suka fito suka
d’unguma gaba d’ayansu suka rufa musu baya.
Da kyar aka iya tsayar da su Shuraim da Hudan daga shiga investigation room d’in…haka nan suka dawo in banda
kuka ba abunda suke yi.
Da sauri Mom ta k’arasa ta jawo Sudais da Shuraim ta rungumesu itama tana kuka.
A hankali Aslam ya k’arasa inda Hudan take tsaye tana kuka, ya juyo da ita ya rungumeta a hankali ya shiga bubbuga bayanta.
Da sauri Arshaad ya tashi ya fita a wajen waya kare a kunnensa. Dad, yana amsa wayar ya fad’a masa halin da ake ciki daga nan
ya nemi waje ya zauna a harabar asibitin..
BAYAN MINTUNA TALATIN.
Cirko cirko haka kowa yake tsaye sun cika wajen
Dad Daddy Aslam Abba Mom Mammy Gramma Mommy Arshaad Sudais Shuraim da Hudan!
Kowa ka ganshi ka san hankalinsa a tashe yake dan
ko zama ba wanda ya iya yi.
K’arar bud’e k’ofar inda aka shiga da ita suka ji, dan
haka duk suka juya suka zubawa Likitan da ya fito ido.
Yana kallonsu ya yi saurin sunkuyar da kanshi
kafin ya zare glasses d’insa yad’an murza idanunsa sannan ya mayar ya d’ago ya kalli Aslam yace masa “follow me”
A hankali ya zame hannunsa a cikin na Hudan ya bi bayan Likitan..
BAYAN MINTUNA BIYAR.
A hankali Aslam ya bud’e k’ofar office d’in ya fito, kamar
wanda aka zarewa laakka a jiki haka yake taku, sai da ya kusan k’arasawa corner da in ya shiga zai gansu tukunna ya zaro wayarsa ya danna kiran Granpa!
Yana karyo kwana suka yo kanshi gaba d’ayansu suka hau tambayarsa….
Kallonsu kawai yake yi da waya kare a kunnensa, sai ya
bud’e baki kamar zai yi magana sai kuma ya kasa.
Jijiyoyin kansa sun yi rud’u rud’u! Gashi idanuwansa sun kad’a sun yi jaaa!
Wanda hakan ba k’aramin sake gigita ahalin yayi ba.
Sai da wayar ta kusan katsewa tukunna Granpa ya d’auka!
Jin shiru yasa yace
“Talk to me Aslam”
A hankali bakinsa na rawa yace “Granpa, its Ummi!
Incase you have something to say to her…
Likita yace she has less than 1 hour.”
“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Shine abunda kowa ya hau maimaiitawa a zuciyarsa dan
k’amewa k’am! Gaba d’ayansu suka yi kamar an d’auke musu numfashi haka wajen yayi tsit!.
A hankali kukan Gramma ya fara tashi followed by na Mom da Mommy sai su Sudais da Huda…
Tashi d’aya kuma sai wajen ya hautsine! Masu hawaye nayi masu kururuwar kuka ma suna yi.
Da kyar Abba ya iya k’arasawa ya dafa Aslam yace
“What happened to her?”
Jikinsa yana mugun karkarwa.
A hankali da kyar ya iya cewa “poision ta sha!
Ya tsinkamata gaba d’aya hanjinta
The Soctors where even shocked! Ta yadda take numfashi har yanzu.”
A rikice Abba yace
“Poison kuma?
How? A ina?
Wa ya bata poision?”
D’agowa yayi ya na kallon Hudan yana son tambayar ta ‘ya aka yi?’
Ganin yadda gaba d’aya hankalin jama’ar wajen ya koma kanta ne
ya sa kawai ya d’auke kai.
A hankali yace
“Ihun Hudan kawai na ji, ina
zuwa na ganta tana tarin jini.
Ba mu san a ina ta sha ba.”
Da sauri Mammy ta matso tana matsar hawaye tace
“Ta ya zaka ce