Showing 66001 words to 69000 words out of 100703 words

Chapter 23 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

4444

ayyuka da dama akanshi.

Tana shirin tura gate d’in gidan ta ji ya ce
“Sakina”
Da sauri ta juyo!
Daman taga kamar motarshi a parke d’an gaba kad’an.

Ganin sa d’in ne kuwa yasa ta had’e fuska tamau! Kafin ta ce
“Naam, Sageer.”

A hankali ya k’araso inda take, sai da hasken globe d’in k’ofar gidan nasu ya haska fuskarshi da kyau tukunna ta lura da abun mamaki..
Gani tayi yana
kuka wiwi
fuskarshi har ta kumbure da alamun ya dad’e yana yi.

Tana shirin yin magana shi ya rigata ta hanyar cewa
“Sakina komai Aaima ta fad’a muku gaskiyane
nine Sageer!
Amman asalin sunana Ashraff.
Ba zan b’oye miki ba…
Har ga Allah tun farkon had’uwata da Yarinyar na ji ina sonta
amman ba so na aure ba
sha’awace kawai irin wadda shed’an kan saka a zuk’atan waenda ya yi nasara.
Na san Abbakar Abokina ne tun Yarinta. Muna barin gurin ya tambayeni ‘dalilin b’oye mata asalin sunana da na yi’
Ban b’oye mishi ba
na fad’a mishi k’udurina a kanta!
Ya ji ba dad’i kuma yaso nusar da ni amman da yake
shed’an ya riga yayi galaba a kaina yasa sam ban ji ba.”

Matsowa ya sake yi kusa da ita
wanda hakan yasa ta d’an ja baya.
Cikin kuka kamar Yaro ya ce
“Sakina na yi laifi, na san
na yi laifi!
Amman dan Allah ki fahimceni
ki fahimci k’aunar da nake yi miki ta tsakani da Allah ce.
Ki duba kiga yadda ita na fad’a mata fake adress fake suna and everything
Ke kuma na fad’a miki komai nawa! Har waya kuke yi da Mamana.
Dan Allah kar ki bari a rabamu,
ki toshe kunnuwanki, fight for our love! Ko wanne d’an Adam ajizi ne
ni ga nawa mistake d’in
dan Allah ki fahimceni
kin ga gashi
na fad’a miki komai ban b’oye miki ba,
ki yi min adalci Sakina.”

Girgiza kai kawai Sakina ta yi sannan ta share hawayenta ta ce
“Meyasa ka zab’i ka gaya min yanzu?
Saboda an kira Maman ku ko?
Kuma ka san dole case zai taso…
Bara ka ji Ashraff
magana d’aya kawai zan iya gaya maka
saboda at this stage ba zan ma iya tolerating ganinka ba! Saboda abubuwan da ka yi sunada yawa ban san ta Ina zan iya farawaba…
Abunda nake so ince kuma nake so ka fahimceni da kyau
tunda naga kana da sharp brain
shiine
Ba zan aureka ba!”

A gigice ya d’ago yana kallonta.

“Kwarai!!
Babu wannan maganar.
Ga responsibility d’inka chan ‘Suhailat’
Ka koma gareta
ka nemi yafiya
ku haifi d’anku
ku zauna lafiya
ku reneshi a tare!”
Tana gama fad’in haka ta juya zata shige gidan ya yi saurin ruk’o hannunta.
A mugun fusace
ta juyo bata yi wata wata ba ta d’auke shi da wani irin mahaukacin mari
jikinta har karkarwa yake yi ta ce
“Na rantse maka da Allah idan baka bar nan ba
zan iya yi maka illa!
Dan duk abunda na raruma sai na maka ma
saboda raina ya kai k’ololuwa wajen b’aci!
Audacity d’inka shi yafi komai d’aga min hankali Ashraff!
Ka ma raina min hankali wallahi!
How kake tunanin.....”
Shiruu ta yi ta kasa ci gaba da magana chan kuma ta ce
“Kaga! Just go, kama
gabanka. Like i said
Idan na ce zan yi maganar abubuwan da ka yi da renin wayon da ka zo da shi yanzu to
ba zan iya jurar ganinka k’alau akan k’afafuwanka ba!
So just leave!!!!”
Ta k’arashe maganar cikin tsawa sannan ta juya ta tura zata shige cikin gidan
ta ji ya ruk’ota!
Za ta yi magana ta ji ya toshe mata baki da hanci da wani handkerchief....



Sai dare tukunna Granpa ya tara su Dad da Gramma ya fad’a musu d’aurin auren Maryam da Abba
next week in sha Allah.
A ranar Abba kasa bacci yayi
yadda ya ga rana haka ya ga dare!
Daga k’arshema ma ji yayi cheecks d’inshi sun fara ciwo tsabar murmushi. Tun ba ma da ya kira Mama ta kula shi sosai ba.


Kaka ma ya samu Madu,
babu alamun wasa a fuskarshi yace
“In dai har yanzu
yana yi mishi kallon Mahaifi a wajen Maryam
to ya sani ya saka ranarta!
Rana ita yau su Granpa za su zo a d’aura aure. Kuma dan girman Allah kar ya tambayeshi dalili ko ya yi mishi musu indai yana buk’atar Abotar su ta d’aure har k’arshen rayuwarsu.”

Murmushi kawai Madu yayi
kafin ya ce
“Kaka ai Abotar mu har aljannah in sha Allah
ba abunda zan bari ya shiga tsakani
dan haka duk abunda ka yanke na goyi bayanka
blindfolded….duk da ban san dalilinka ba
amman i trust you kuma zan yi sopporting d’inka d’ari bisa d’ari!
So dan Allah kar ma ka sako
maganar lalacewar Abotar mu
Allah ya kaimu ranar asabar d’in da rai da lafiya.”
Ya k’arashe maganar yana murmushi.

Duk fushin da Kaka ya kwaso daga gida sai ya ji gaba d’aya ya kau. Dan haka yad’an sake suka shiga tattauna abunda ya shafi alamuransu
mostly a kan Jalila. Kafin daga baya ya nemi ganin Mama itama….
Same yada ya yiwa Madu itama haka yayi mata
kafin ya d’aura da cewa
“Indai ta d’auke shi a matsayin uba har yanzu tou kar ta yi mishi jayayya
kawai yanaso ta amince da abunda ya zo da shi”
Daga anan ya d’aura mata da Nasiha akan ‘kar ta rik’e Abba a ranta komai ya wuce
su zauna su yi rayuwarsu kamar farko
Allah yayi musu albarka.’

A hankali ta ce “ameen” sannnan ta yi mishi godiya
daga nan ta mik’e ta fita.

Wata nannauyar ajiyar zuciya Kaka ya sauk’e yana jin wani nauyi yana sauk’ar mishi
tun kafin ya kai ga sauk’ewa gaba d’aya…….


Tana zaune a kan darduma ta idar da sallar isha kenan
Gwaggo Asabe ta shigo
da akwati sai kuma Mommy da ragowar masu aiki mata
duk da akwatuna…
Tun tana iya irga su har ta hak’ura ta tsaya kawai a tsaye
bayan ta mik’e ta gaidasu cikin girmamawa.
Sai da aka jere akwatunan tukunna suka yi mata sai da safe suka juya suka fita suka barta nan a daskare.

Ta fi minti uku
kafin ta samu ta k’arasa bakin gadon ta zauna still idanunta a kan akwatunan.

Da sallama ya turo k’ofar ya shigo! Da leda a hannunshi.

Da sauri ta sunkuyar da kanta ta ja hular alkyabbar ta rufe fuskartata.

Murmushi yayi kafin ya k’araso inda take nan bakin gadon ya zauna ya kamo hannunta cikin nashi ya rik’e ya d’an murza kafin ya ce
“Sai na yi siyan fuska shima?”

Dariya Hausar tashi ta bata dan haka ta d’an saki murmushi wanda har sai da ya jiyo sautin shi.

A hankali ya ajjiye ledojin dake nan rik’e a hannunshi
kafin ya sauk’o gabanta yad’an durk’usa tukunna ya sa hannu ya janye hular alkyabbar.

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace
“Ma sha Allah”
Sai kuma ya sake cewa
“Kukan me kika yi?”

A hankali ta girgiza kanta alamun ‘ba komai’
Tana jin bugun zuciyarta yana kara tsananta!.
Cikin son ya tashi a gaban ta ta ce
“Akwatunan menenen wannan?”

Murmushi yayi yad’an sunkuyar da kanshi k’asa ya ciji lips d’inshi kafin ya d’ago da kanshi yana kallonta tukun ya fara magana
“Ai dama sai da na cewa Mommy ta yafe min a barni ba sai na yi ba
amman ta saka ni kashe uban miliyoyi akan lefe!
Yau kusan wata biyu kenan tana ta tatsemin aljihu.
Ga shi ke kanki bama ki so ba ko?
Mu mayar mu karb’o kud’in mu?”

Sai yanzu ta d’ago ta kalleshi
“Ma sha Allah” ta fad’a a ranta..
Tunda ya shigo dama ta lura da fararen kaya ne a jikinshi kaftan, sai yanzu taga ashe har hular kansa itama fara ce tas! A ranta ta ce
“Manyan kaya sun fi yi maka kyau”

Cikin katseta ta ji ya ce
“Kwalliya ya biya kud’in sabulu kenan!
Tunda gashi har an saki baki ana kallona”
Ya fad’a yana murmushi gefen baki da d’age mata gira.

Da sauri ta d’auke idonta da kyar.
Cikin son kawar da zance
ta ce
“Ya Aslam wasa wasa fa kanada rowa, tun ba
yau ba na fuskanci haka”

Dariya sosai yayi kafin ya ce
“Ai kin fini rowa!
Tunda gashi ana ta yi
mini rowar zuciya.”
Ya fad’i maganar yana k’ok’arin yin zaman dirshen akan kafet d’in gaban gadon ( a gabanta)

Yana zama, bata san lokacin da ta yi sauri itama ta sauk’o ta zauna a gabansa ba
har guiwowinsu suna gogar juna.
Sai kuma ta fara k’ok’arin janyewa…
Hannuwanshi ya saka ya rik’e cinyar tata ta yadda ba zata iya motsawa ba!
Yana jin wani yanayi na daban ya na shigar shi…
A hankali yana d’an murmushi ya ce
“I love this respect
da kike min Hudatie,
Thank you.”

Sunkuyar da kanta ta yi kawai ta kasa cewa komai.

A hankali yana kallonta ya ce
“Baki ce komai ba.
Akan maganar mu da muka fara a d’akin Gramma”.

Da sauri ta ce
“Ya Aslam dan Allah ka daina bana son maganar.
Kuma ni dai ka d’auke hannunka.”

Gefe ya kalla yayi wani murmushin gefen baki..
Bata gama fahimtar murmushi da jinjina kan me yake yi ba
ta ga ya mik’e tana shirin yin magana ya sunkuya ya d’auketa!

Sai da ya k’arasa wajen sofa tukunna ya zauna ya d’aura ta a kan cinyarshi kafin ya ce “Bud’e idon sannan ki ja numfashi
Matsoraciya kawai…
In kika sake yi min musu ko kika ce kar In tab’aki Allah sai na nuna miki matsayina a wajenki.”

A hankali ta bud’e idonta tana kallon k’asa.. Hankalinta In yayi dubu tou ya tashi!

Tanajin yadda jikinsa yake d’an rawa kad’an kad’an
ga zuciyarshi tana iya feeling bugunta!

A hankali ta ji ya ce
“Unhm ina jinki.
Say something anything…
i told you how I feel.
Let’s talk about us,
Um??”
Yayi maganan yana ruk’o hannunta.

Zuwa yanzu kam Huda ji ta yi ba zata iya jurar wannan torture d’in ba dan apart from heart d’inta da yake over racing!
Ta rasa fahimtar meyene game da hannun Aslam
da yake sanya touches d’inshi suke zautar da ita.

D’igar hawayenta ya ji
dan haka ya sauk’e ajiyar zuciya ya mik’e da ita a jikinshi ya ja hannunta…
Sai da suka je inda ya ajjiye ledojin d’azu tukun ya d’auki wata ledar bag y’ar babba mai zip lock mainkyau sosai
ya bata ya ce
“Gashi ki shirya ki sa wannan kayan ki yi alwalah..please ki saka rigar ciki”
Har zai juya sai kuma ya ce
“If not”
Ya matso da bakinshi kusan kunnenta ya fara magana…..
Da mugun sauri ta juya ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta jikinta na karkarwa.

“Kisa rigar kin ji, pls”
Ya fad’i maganar kamar ba shi ya gama zuba mata maganganu a kunne ba yanzun nan.


A hankali ta ce “tou” dan ita Allah Allah take ya fita ya bata guri ta samu ta shak’i isashshiyar iska.

Yana fita ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tana dafe k’irji sanann ta nemi waje ta zauna akan gadon.

Ta jima a haka kafin kawai ta mik’e ta fad’a toilet dan daman wanka take son yi tun kafin ya shigo:

Ta d’an jima tukun ta fito bayan ta yi wanka da ruwan turarrukan da Ummu ta jere mata a toilet d’in, da brush duk sai da ta yi sannan ta fito.

Rigar, dan kyau ta yi kyau sosai
sai dai spaghetti hand ke gareta. Ba wani rashin d’a’a a rigar dan doguwar gown ce har k’asa
Slim mai bin jiki
sai wasu stones masu shek’i na azaba k’anana a saman edge d’in wuyan rigar
da kuma dede k’asan boost
sai kuma chan k’asan edge d’in rigar shima an zagaye da stones d’in.
Ko bra bata saka ba dan rigar irin me bra d’innan ce ta ciki.
Sai da ta saka rigar ta zuge zip d’in da kyar tukunna ta ga rashin d’a’ar rigar
dan kusan rabin k’irjinta a waje ne sannan bayanma gaba d’aya ashe akwashe yake dan ma Allah ya taimaka gashinta ya rufe kusan rabi.

Da sauri ta fara k’ok’arin zuge zip d’in domin ta samu ta chanza rigar kafin ya shigo.
Bata kaiga zugewan ba kuwa ya shigo! Sanye cikin jallabiya
fara tass! Mai k’aramin hannu.
Suna had’a ido da shi bata san daliliba kawai sai ta fashe da kuka.

Da sauri ya k’araso gaban madubin dan shi a tunaninshi
yadda ya ga ta rik’e wajen zip d’in ta na jaa
ya d’auka had’ewa ta yi da fatarta.

Sai da ya duba ya ga ba komai tukunna ya sauk’e ajiyar zuciya ya juyo da ita ya fara lallashinta yana dariya k’asa k’asa dan sai yanzu ya fahimci dalilin kukan nata.

Da kyar ta yi shiru tana sauk’e wasu tagwayen ajiyar zuciya
tana nok’ewa:

A hankali yake binta da wani irin kallo kafin ya tattara gaba d’aya gashin nata ya zubo mata shi ta gefen fuskarta suka fad’a a kan k’irjinta gefe d’aya.
Tunda ya fara kallonta har ya gyara mata gashin kan nata
ta sunkuyar da kanta k’asa.

A hankali ya zaro wata red rose
ya sak’ala mata a jikin gashinta ta d’an saman kunnenta
kafin ya zaro wani tsadadden pendant necklace
d’an mitsitsi mai shape d’in heart ya ware shi ya bud’e ya kara mata a wuyanta
sannan ya matso sosai ya lek’a ta baya ya manne mata sark’a ya saketa ya gyara mata gashinta.

A hankali ya na nan a yanda yake dan baya son motsawa daga position d’insa ya ce
“Open it”

Da kyar ta iya bud’ewa hannunta na gogar k’irjinsa…
Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba
Right side d’in an rubuta
‘Y’
Left d’in kuma
‘M’.
A hankali ta mayar ta rufe sark’ar tana d’an murmurshi.

Jin yayi shiruu yasa ta d’an motsa sai kuma ta tuna ashe a jikin madubi ta ke!
Da sauri ta juya ta katseshi daga k’are mata kallon da yake..
Dariya ya yi ya ce
“To ai nan d’in ma zan ganki”
Da sauri ta koma ta kanannad’e shi ta baya ita ala dole kar ya sake ganinta.

Ganin tana shirin kunce mishi lissafi yasa ya ce
“Tsaya In d’auko miki hijabi mu je mu yi sallah”

Da kyar ya samu ta sakeshi ya k’arasa wajen akwatunan ya bud’e wanda yake kyautata zaton akwai hijabin a ciki..
Cikin sa’a kuwa ya samu ya d’auko harda darduma ya dawo ya mik’a mata hijab d’in ya ce “Ungo, saka”

A hankali ta karb’a ta saka
tana sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya..
Daga nan
ya ja hannunta ya ce “mu je,
i have a surprise for you.”
Yana rik’e da hannunta suka fito suka nufi d’akinsa…
Yana bud’ewa! A hankali ta ce
“Woow..”
Tana murmushi.
Sai da ta k’arasa shiga cikin d’akin tukunna ta fahimci
abunda ya rubuta da y’an k’ananan candles d’in da ya kunna a tsakiyar d’akin
I
Love
You
Hudan!.

Kan gadon ma wanda ke nan shimfid’e da white bedsheets
haka ya rubuta da wasu k’ananan red roses.

Murmushi kawai take yi tana kallon yadda d’akin ya k’awatu
matuk’a! Ya burgeta sosai.

A hankali ta ji yayi hugging d’inta ta baya sannan ya ce
“Do you like it?
Ya yi kyau?”.

Murmushi ta yi a hankali ta ce
“Ya yi kyau”.

Juyo da ita ya yi ya d’an b’ata yayi kalar tausayi fuska abun dariya ya ce
“Ya yi kyau but you don’t like it ko?
Y?”

Sai da ta yi k’asa da kanta tukunna ta ce
“Ni Ya Aslam kana confusing d’ina ne
idan na ji ka ce you love m me”
Ta k’arashe maganar da d’an inda inda.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce
“Y?”

Cikin runtse idanunta ta ce
“Ya Arshaad fa k’anin ka ne!
Amman kuma how kake sona
bayan ka san shi zan aura?
Idan kuma ba haka ne ba to tayaya zaaka ce ka fara sona ana d’aura auren mu?
Tunda na lura tun lokaci ka fara nuna intrest.”
Ta fad’a tana sake sunkuyar da kanta sosai.

Ya ji zafin zancen Arshaad da ta kawo amman sai ya basar, ya ce
“Dole ki sunkuyar da kai ai”
Ya fad’i hakan yana d’an jan hancinta, kafin ya sa hannu ya sake jawota jikinshi tukunna ya fara magana
“Hudan!
That day
da muka fara had’uwa
ranar da Arshaad ya ce in zo mu je yayi min introducing d’inki mu ga juna
Wasn’t the first time i saw you.”

Da sauri ta d’ago tana kallonshi.

Lumshe kyawawan idanuwanshi yayi ya bud’e su sannan ya jinjina mata kai alamun tabbatarwa.
“Banso gaya miki haka ba
na so ace na saka soyayya ta a cikin zuciyarki a hakan
in ya so daga baya ki sani
amman zancen Arshaad da kika kawo
wanda na fahimci it’s like kina tuhuma ta da betraying d’inshi,
shi ya sanya zan fad’i miki..
...Akwai wani competition da kuka yi,Tournament,
Mathematics..
I think a time d’in kina ss 2 ne.

A cikin makarantun akwai wata makaranta ta y’an labanoon wadda sister d’in wani employee d’ina
d’an labanoon ta yi representing.
A chan uk yake min aiki a company d’ina,
muna shiri sosai da shi.
Ke kika zo first ntic
Sistern nashi kuma ta zo second Labanoon school.

Employee d’in nawa ne ya turomin full video d’in
yana me tambaya ta
‘Dama inada sister bayan Aaima?’
Na ga resemblance d’in sosai nima amma ba wannan ne matsala ta ba
dan a tashi d’aya kika shiga raina.

Sai da ta kai ta kawo bana iya bacci idan har ba hoton ki da wannan video d’in na gani ba.

Inada waenda na sani suke koyarwa a school d’inku
dan haka na sakasu suka nemo min sport, prep da duk wani pictures d’inki da wasu information a kan ki!
Tabbas hankalina ya tashi sosai da na ga a scholarship kika je school d’in
dan zuwa wannan lokaci
soyayyarki ta riga ta yi min kyakkyawan kamu!
Sanin da na yi tabbas za asha gwagwarmaya da Granpa! Ne ya yi matuk’ar d’aga mini hankali, duk da inada tabbacin idan na lallab’ashi na shawo kanshi maybe ya iya yarda.

Har ranar graduation d’inku sai da na saka aka yi min video d’inki kina bada speech
special
aka turomin ke kad’ai. Zuwa wannan lokacin
na san in dai ban sameki ba tou tabbas akwai matsala, dan ni kad’ai na san me nake ji……

Na shirya akan zan dawo In karb’i adress d’inki In samu Granpa in yi mishi bayani
idan yayi aproving In je in sameki dan
no matter how much i love you
I don’t think zan iya yarda in jefa ki a irin halin da Anty Maryam da Mommy suka shiga ciki, ba.

Ina shirin dawowa
Arshaad ya kirani akan wai Auwal yayi framing d’inshi har an kaishi Kotu!
Bani da kamar Arshaad
shiyasa
tun kafin In dawo na maida case d’in shi priority
tukunna in samu Granpa
tukunna in sameki.

Ana cikin case d’in nashi kuma
ya ce ‘in zo mu je In ganki’

Ba k’aramin tashin hankali na shiga ba ranar Huda!
Don a take Ina ganinki na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login