Showing 69001 words to 72000 words out of 100703 words
Chapter 24 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt
ganeki sannan kika sake samun guri kika yi bake bake a cikin zuciyata.
Shiyasa In zaki tuna da kyar na iya seseta kaina na fito…..
Arshaad is my brother and best friend
that is why i did what i do to you
that very day saboda a ganina ya zame min dole in yakiceki
In kuma saka miki k’iyayya ta a rai saboda gudun kar ma zuciya ta rud’eni
In so kaina in zo miki da nawa zancen
saboda a wannan lokacin ina k’ok’arin tursasawa zuciyata In samu Inga na hak’ura da ke
amman kwakwalwata da tunanina suna nusar da ni
a kan
Ba fa zan iya hak’urin nan in barwa Arshaad ke ba!.
And yadda na ga Arshaad yana sonki as his big brother
hak’ura da ke is the best thing to do
tunda na ga kema shi kike so!
Shiyasa na yi k’ok’arin zama bad guy a idon ki
har Anty Maryam (and still Ina jiye wa Abba a wannan ranar shiyasa abun ya zama biyu na aikata mata abunda na yi ranar a asibiti.)
Amman kuma sai abun ya gagara
dan
no mattaer how i try
tun ranar da na ganki
har kawo yanzun nan
I don’t think k’aunarki ta ragu dede da kwanyar zarra
a cikin zuciyata!
A ko da yaushe k’aruwa kawai take yi….
Har d’an k’aramin hauka na yi da aurenku ya matso!
Gashi Mommy ta hanani guduwa…
Zakkah sadaka da sallar dare
su suka taimaka Ubangiji ya ji k’aina ya mallaka mini ke a lokacin da ban tab’a tunani ba.
Na tabbatar da ace ban aure ki ba to
It’s either in k’are
a asylum ko kuma mak’abarta…”
Ya k’arashe maganar yana mai cupping face d’inta kafin
ya d’ago fuskar tata yana kallonta
a hankali ya yi kisssing idanuwanta da ta lumshe
sannan ya ce
“I love you Hudan!
Bawai sai da na aureki na fara showing intrest ba,
noo, not at all! Tun kafin in dawo Nigeria nake
So da Burin
inga na aureki.
You are my happiness
my everything
my whole heart
kin shiga kin kanainaye
ke kawai nake gani
ke nake So da Burin in mallaka
in rayu da har k’arshen rayuwata…..
Na san ba lalle ki soni ba a yanzu but please dan Allah kar ki k’i ni Hudatie try
and find a place for me in your heart i promise you won’t regret it!
Just a tiny place,
please my love.”
Ya k’arashe maganar a hankali.
Hawaye ya ga ya fara bin k’uncinta dan haka ya jata ya yi hugging nata ya ce
“Sorry..
Amarya bata kuka
Shikenan a bar maganar in dai zata saka ki kuka.
Let’s pray.......”
A hankali ya cikata ya sunkuya ya d’auki sallaya ya wuce
ya shimfid’e.
Nafila ya ja suka yi.
Ya dad’e yana addu’oi
kafin ya juyo ya dafa kanta ya yi addua. Sannan ya shiga jero mata tambayoyi
game da addini…
Ya ji dad’in sanin da ya ji tana da.
Daga nan ya ce “itama ta yi masa tata tambayar..”
Kasawa tayi dan haka kawai yayi murmushi ya ja hannunta suka mik’e…
Shi kansa yunwa yake ji
amman a yadda yake jin sa sam! Ba zai iya jira a sha ko da ruwa ba!.
Da kyar dan sai da yayi da gaske tukunna ya zare hijabin nata.
..……………..
Tabbas Hudan ta ga
ikon Allah!
Tsaurin ido!
Tsantsar rashin kunya
da kuma k’arfin hali a wajen Aslam.
Tun tana tirjiya har ta d’an fara sakin jiki dan salon nashi babu sauk’i. Kafin daga baya kuma ta ji an d’auki wata hanya daban mai cike da rad’ad’i wahala da azaba na fitar hankali’
Tun tana kuka a hankali tana d’an dauriya saboda rok’o da magiyar da yake ta yi mata
har ta zo ta fara tirjiya sannan ta ware murya ta fara ihu tun k’arfinta dan taga abun nashi ba na wasan Yara bane ba.
Babu wanda Huda bata kiraba har K’asimu sai da ta kira!
Indai Huda ta sanka to tabbas a wannan dare ta kira ka tana magiyar ka zo ka kawo mata d’auki.
Tun tana ganin daidai ta zo ta fara ganin dishi dishi!
Tsananin azaba ta sanya
daga k’arshema ta shak’i numfashi ta sume ba tare da oga Aslam
ya san inda kanshi yake ba ballantana ita...........
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
70
Mikiya Writers Association.
Kamar a cikin ruwa take jinta!
Sai kuma muryarsa sama sama yana d’an shafa mata ruwan a fuska yana tapping kumatunta a hankali yana
kiran sunanta
a d’an rikice.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta samu ta bud’e idanuwanta da suka yi mata nauyi.
A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya ce
“Alhamdulillah!! Sannu
sannu sorry sannu”
Da kyar ta iya had’a idanu da shi, wani haushinsa ta ji a take
sannan duk kyawun fuskarshi yau sai ta nema ta rasa!
A hankali ta kawar da kanta gefe ta sa kuka….
Cikin rashin jin dad’i yace
“Sorry mana, yi hak’uri please, na ce sorry fa”
Cikin kukan ta ce
“Ka fita.”
Zai yi magana ta sake cewa
“Allah ka fita!”
A hankali ya mik’e ganin
kamar ma bata son kallon fuskarshi ya sanya ya ce
“Ki kirani kafin ki fito,
kar ki fad’i”
D’aga masa kai kawai ta yi
shi kuma ya sa kai ya fita daga cikin bathroom d’in….
Duk da baya son ganin ta a wannanan halin da mood d’in
amman sai ya tsinci kanshi da sakin wani k’ayataccen murmushi….
Yana fita ya ga wayarsa tana haske dan haka ya k’arasa ya d’auka da d’an sauri.
Ganin Aaima ya sa ya d’auka cike da ishashshen kuzari ya ce
“Auta ya aka yi?”
Sai da ta gaidashi tukunna ta ce
“Yaya na zo ne”
Ajiyar zuciya ya sauk’e
kafin ya kashe kiran
ya k’arasa ya zaro jallabiya ya zura akan gajeran wandon jikinsa ya fita.
Da baskets nik’i nik’i ya ganta
na break fast.
Bayan sun sake gaisawa ta ce
“Gashi inji Mommy”
Murmushi ya yi ya ce “ki ce mata mun gode. But akwai cook a nan itama ta huta
dan na san wannan da kanta ta girka.”
“To” ta ce, ga mamakinsa sai ya ga ta wuce shi ta nufi hanyar sama.
Da sauri ya ce “Ina za ki je?”
Ba tare da ta juyo ba ta ce
“Zan d’an je mu gaisa da Anty Huda ne”
Gani ta yi ya biyota da sauri sannan ya kamo hannunta ya dawo da ita bakin k’ofa ya ce
“Ki bari ba yanzu ba!
Bacci take yi.”
K’asa k’asa Aaima take danne dariyarta kafin ta ce
“Ya Aslam akwai important maganar da nake so mu yi da ita. D’an matsa dan Allah in wuce.”
Ganin ya saki baki cike da shock yana kallonta ya sanya ta kasa daurewa ta saki dariyar da take ta k’ok’arin dannewa…
Sai yanzu ya gane me take yi mishi dan haka ya yunk’ura
Ita kuma ta juya ta wuce da gudu tana dariya.
Sai da ta b’acewa ganinsa
tukunna ya girgiza kai
ya mayar da k’ofar ya rufe.
Ya shiga kitchen ya d’auko plate da cups ya had’a da baskets d’in ya nufi sama.
Har Aaima ta k’arasa gida tana murmushi da mamakin
yadda ta ga Aslam d’in yayi wani irin haske na ban mamaki
sannan ga wani nutsatsen kyau da annuri cike da fuskarsa.
A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya a fili ta ce
“Hmm”
Kawai, daga nan ta yi gaba.
Yana komawa ya tarar da Huda ta fito a wanka tana takawa da kyar za ta isa kan gadon…
Ajjiye kayan hannunsa yayi nan bakin k’ofar sannan
da sauri ya k’arasa ya d’auketa chak! Yana mai cewa
“ba na ce ki jira ni ba?
Taurin kai ko?”.
Bata kula shi ba, haka ya kaita kan gadon da ya shimfid’awa sabon bedsheet ya kwantar,
a hankali ya yi mata light peck a goshinta kafin ya zauna a gefenta ya kamo hannunta
yana d’an matsawa a nashi ya ce “Ya Aslam bai kyautaba!
He is sorry.
Yanzu kam na san kafin a samu a bani amsa ta ta jiya sai na garu.
Nima dai inbanda ni da karambani na
ta yaya zan yi wannan aikin In sake b’allawo kaina ruwa?
Ni da ban gama samun matsugunni ba…”
Turo baki tayi
ta d’an juyar da fuskarta kad’an.
A hankali ya yi murmushi
ya kawo hannunta setin bakinshi ya yi kissing kafin ya ce
“Thank you Hudatie,
thank you so much!
Ban san ta yaya zan fara yi miki godiya ba..
I just want you to know that
You are everything that I need to be happy and more..
Tnx a lot, I love you.”
A hankali ta lumshe idanuwanta…
Tabbas maganganun shi sun yi mata dad’i amman yadda take ji a jikinta ji take yi
kamar ta yi ta kwarara ihu!.
A hankali ya mik’e ya d’auko baskets d’in ya kawo ya zuzzuba abincin.
Naciii da threats
d’in da ya dinga yi mata ne
suka sanya ta ta ci da d’an dama dan ita kam ko a mafarki bata buk’atar wata had’uwar tasu ita da Ya Aslam!
Ita ta san waye shi
Ita ta san azabar da ta sha.....................
A hankali Sakina take bud’e idanuwanta..
Da sauri Ummu ta ce
“Alhamdulillah! Ta farka.”
Sannan suka yo kanta da sauri ita da Mama suna jera mata “sannu”
Daga nan suka kamata suka zaunar da ita..
Wani irin abu take ji yana yi mata yawo a cikin kanta!
Daman tun jiya da ya toshe mata hanci da baki da wannan handkerchief d’in a take ta ji kamar an zuba mata tsutsotsi a cikin kanta kafin ta sume
to yanzun ma tana farkawa ta cigaba da jin hakan, sosai kuma da k’arfi! Shi ya sanya ta shiga shafa kanta
har ta kaiga tuje d’ankwalin ta hau jan gashinta da k’arfi
kamar wata shahararriyar mahaukaciya!….
Idanuwa kawai ta ga su Ummu sun zuba mata. Sai a lokacin ta lura da yadda idanuwansu suka yi jaaa
duk su biyun
da alamun sun ci kuka.
Tana shirin yi musu magana idanuwanta suka sauk’a a kan Ashraff! Wanda ya tunkaro gadon shima.
Cikin tsanannin tashin hankali da b’acin rai ta ce
“Ashraff!
Ashraff ne..
Kar ka k’araso, Ummu kidnapping d’ina ya zo zai yi
wallahi
Ashraff ne”
Duk ta rikice ta gigice
dan a tsorace take.
A hankali taga ya fara zubda hawaye yana sa hannu yana gogewa.
Gani ta yi Mama ta juya ta fita
Ummu kuma ta sunkuyar da kanta.
Bata gama tunanin abunda yake wakana ba
Mama ta shigo tare da Doctor.
Yana shigowa ya nufeta ya hau dubata kafin ya ce
“Me kike ji
yanzu?”
A tak’aice ta ce masa
“Tsana da tsoro!
Na wanchan bawan Allahn,
ka ce masa ya fita
Allah in bai fita ba zan illatashi”
Ta k’arashe maganar tana dukan tsakiyar kanta saboda yadda take ji abu na yi mata yawo a ciki.
Ajiyar zuciya Likitan ya sauk’e
kafin ya juya ga su Mama ya ce
“Results d’in sun fito!
Gaskiya ta bugu sosai a kan nata shi yasa dole za take misbehaving…
Kar ku biyeta
kawai ku yi addua nima akwai magungunan da zan d’aurata a kai
In sha Allah za a dace.”
Cikin tsananin tashin hankali Sakina ta ce “inna lillahi wa inna ilahirrajiun”
Tana mai d’aura hannunwanta duk biyu a ka!
Za ta yi magana
kawai Likitan ya kama hannunta su Ummu suka taimaka masa wajen rik’eta dan har ta fara bubbuge hannunsa tana tirjiya da surutai, bai yi wata wata ba
ya danna mata allurar
da ko gama shiga cikin jijiyoyin ta basu yi ba
Jikinta ya sake gaba d’aya
ta tafi luu
ta zube a nan kan gadon jinyar.....
Kuka kawai Ummu da Mama suka saka hankalinsu a mugun tashe.
Da sauri Ashraff d’in ya matso ya fara lallashinsu
kafin ya ce
“Akwai wani Doctor d’in da na sani a New York! Dan irin haka
ta tab’a faruwa da wani cousin d’inmu….
Basket ball ne ma shi wani ya buga masa a ka wanda muna a
filin ball d’in fad’a ya had’osu.
Mama ni har ga Allah tsakani na da Allah nake son Sakina!
Ba hauka ba
ko me ne take yi na ji na gani zan aureta in rayu da ita.
A yanzu idan kuna so
tsaff zan iya booking appointment da Likitan
in fitar da ita domin samun lafiyarta.”
A hankali Mama ta ce
“Haka kurum ta fara?”
Cikin share hawayensa ya ce
“Suna buga mata dutsen suka gudu. Ni kuma ban samu na bisu ba tunda naga kamar a buge suke sannan ga itama a kwance.
Muna zuwa asibitin nan bayan taimokon gaggawa ta farfad’o,
abunda ta fara ce min shine
‘Ta bawa Aaima labarin Suhaila!
Allah ya isanta, na cuceta ba zata aure ni ba’.
Ganin da na yi she s not making any sense ne yasa kawai na yanke shawarar In kiraku.”
Ya k’arashe maganar cikin karyewar zuciya da zubar hawaye.
A hankali Ummu ta ce
“Shikenan Ashraff mun gode.
Bara in kira Baban nasu
na ji har yanzu shiru.”
Tana shirin fara dialing numbersa suka shigo shi da Abba! Sai da suka d’anyi kallon kallo shi da Mama
tukunna aka gaisa
kafin Ummu ta hau zaiyyano musu bayani dalla dalla….
“Gaba kura baya damusa”
Baban Sakina ya fad’a a ranshi
dan yanzun nan yana shirin shigowa asibitin
Abba ya kirashi ya ce yana buk’atar ganinshi urgent!
Shi ya sanya ya jirashi
sai da suka gama tattunawa tukun suka shigo
duba Sakinar dan shi Abban ma bai san tana kwance ba!
Ya zo mishi ne akan maganar Auwal…..
Tabbas sun san cewa bai kamata ba amman maybe a san abun yi
dan Auwal tun shekaran jiya
an kasa gane kanshi kwata kwata! He’s not even responding to treatment,
gaba d’aya jikin nashi sai a slow, hankalin Daddy a mugun tashe yake
shiyasa suka yanke shawarar zuwa su sameshi ko akwai wani taimakon da za su yi musu, duk da kuwa ba su ga way out ba
amman dai gara a gwada……
A hankali Abba ya ce
“Bacci take yi ne?”
“Eh” Ummu ta bashi amsa.
Yana shirin yin magana
Ashraff d’in ya ce
“Bara in kira Doctor d’in
Idan anyi sa a yana nan ma
ko a yau za a iya wucewa…”
A hankali Ummu ta ce
“Sannu Ashraff”
Yana fita Baban Sakina ya nema waje ya zauna ya dafe kanshi, bai san abun yi ba!
Har ga Allah.
Cikin sanyin jiki
Ummu ta yi mishi bayanin Likitan New York….
“In dai zata samu sauk’i
kuma zamanta a haka zai iya janyo matsala!
Tou why not kawai ya d’aura musu aure tunda an riga an gama bincike akan shi Ashraff d’in, in ya so sai ya tafi da matarshi ya yi jinyarta a chan
tunda ya nuna zai yi d’in
kuma zai biya makudan kud’ad’e a nema mata lafiya da komai”
Baban Sakina ya aiyyana hakan a ranshi.
Dede nan Ashraff d’in ya dawo
ya ce
“Yana nan!
But zuwa nan da next week zai bar k’asar zuwa wani important aiki and ba lalle ya samu ganin mu ba idan aka kai next week d’in.”
A hankali Baban su Sakina ya mik’e ya ce “Ina zuwa bara in yi waya da brother d’ina”
Dafa shi Abba yayi ya d’an kalleshi kafin ya juya ya cewa Ashraff d’in
“Za ka iya wucewa
kawai, za mu san abun yi
kar ka damu”
Zai yi magana ya ce
“ ka je kawai an gode”
Sai da Ummu ta ce
“Ashraff ka je za mu
nemeka, mun gode”
Tukunna ya juya ya fita da kyar.
Da mamaki Abba yake kallonsu yana ganin yadda duk suka rikice
Yaro k’arami ya na raina musu hankali.
Cikin son gasgata zarginshi ya nemi Ummu da ta yi mishi ishashshen bayani....
....Tana dire aya
ya zaro waya ya danna kiran Aaima…
Da kyar Aaima jikinta na karkarwa jin Abba ya ji abunda k’awarta ta aikata a school ta
shiga koro mishi bayanin tiryan tiryan…
Har zuwan da Ashraff d’in ya yi estate a jiya.
Tana dire aya
Abba ya kashe wayar
ya kallesu ya ce
“Me kuka fahimta
a lamarin su su uku?”
Bai jira jin me za su ce ba ya ce
“Ni na fahimci
K’arya
Yaudara
Da tsoro
a lamarin Ashraff.
Inaso ka zo mu je mu samu Mahaifinsa
a nan na tabbatar in dai mutumin kirki ne
to gaskiya za ta fito k’arara!
But first
sai na fara kulle asibitin nan da mai asibitin tunda karb’ar cin hanci ya maida sana’a”
Bai gama rufe bakinshi ba
Likitan ya shigo!
Sai da ya kallesu one by one
tukunna ya k’arasa inda Ummu take ya shiga yi mata bayani akan wasu takardu da ya shigo da su yanzu….
“Case d’in Sakina fa is severe!
In ba a fitar da ita
a yau ko gobe ba
tou tabbas
za a samu babbar matsala!
Shima sai yanzu ya ke ganin wannan result d’in bayan ya tsananta bincike…..”
Kasa magana Abba yayi
tsabar mamaki da takaici
dan haka kawai ya turawa commisioner of police message
tare da adress d’in asibitin daga nan ya cewa Baban Sakina “ya zo su je..”
Suna fita ya ce mishi su wuce gidansu Ashraff.
A motar Abba ya yiwa Baban Sakina k’arin haske akan abunda ya fahimta game da Ashraff d’in kuma aka ci
sa a Baban Sakinan ya fahimceshi.
Ba Baban Sakina ba hatta Abba sai da ya cika da mamaki
da suka k’arasa k’ofar gidan
suka tarar da tafkeken masallacin juma’an dake a jikin gidan cike da jama’a
anata shige da fice.
A hankali da kamala suka kutsa kai suka shige ciki, sakamokon hango Mahaifin Ashraff ya gilma ciki sanye cikin shiga ta alfarma.
Ba su gama tunanain meke faruwa ba
suka ji a loudspeaker ana
“An d’aura auren Ashraff Muhammad Bashir
Da Suhailat Yusuf Tanko
a kan sadaki naira dubu d’ari uku
lakadan ba ajalan ba.”
Kallon kallo suka hau yi
kafin su hau kallon jamaar one by one…
Chaan! Suka hango Baban Ashraff d’in da suka biyo cikin masalllacin, yana ta fara a yana gaisa wa da wasu Abokanayen sa na jiki jiki
waenda suka samu damar halartar d’aurin auren gaggawan da aka gaiyyacesu.
Yana ganin Baban Sakina hankalinshi ya d’an tashi! Dan a iya saninshi
bai gaiyyaceshi
besides auren ma ai secret aka yishi to
me kuma ya faru?!
Bai gama dawowa dede ba
suka k’arasa wajen shi da Abba suka zauna a kusa da shi.
Abba ne ya iya bashi hannu suka yi musabaha
Baban Sakina kuwa da kyar ya iya ce mishi
“Barkanmu..
Dan Allah d’an yi min elaborating abunda na ji an fad’a
yanzu.”
Sai da Baban Ashraff d’in ya d’an kalli gefe da gefen shi
tukunna ya mik’e ya ja su gefe
ya fara magana k’asa k’asa
“Kasan me ya faru ne?
Yaron yanzu sai a hankali wallahi….”
Sai kuma ya d’an yi shiru kafin ya fesar da numfashi ya ci gaba da cewa
“Shi Ashraff an d’an samu matsala ya je ya yaudari wata Yarinyar oga na
wanda shi ya siya min takardar kujerar sanatan da nake