Showing 39001 words to 42000 words out of 100703 words

Chapter 14 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

4398

ya wuce gaban mudubi.
Sai a lokacin ta samu damar d’aukar y’ar mitsitsiyar hair dryer d’in da take buk’ata ta mik’e ta nufi bakin gado da kayan da ta ware…

Tsaff ya shirya ya shafa mai kad’an ya fesa turarurruka ya gyara gashinsa, sannan
ya d’auki kwalin ya nufi inda take zaune har yanzu ko kwance kan bata yi ba ballantana ta busar
Ita ala dole jira take sai ya fita tukunna.

Yana zuwa ya d’aura mata akan cinyarta ya nemi waje ya zauna a gefenta.

D’agowa tayi ta kallesa, da gira yayi mata alamun ta bud’e!
A hankali ta shiga warware bow d’in da yake nan a saman kwalin wanda an yi amfani da igiyar ne wajen d’aure kwalin,
tana kwancewa ta d’an d’aga ta zareshi gaba d’aya a jikin kwalin ta ajjiye
kafin ta kama gefe da gefen ta d’aga shima ta ajjiye murfin a gefe.
Bata san lokacin da tace
“woow!” Ba.
Wata had’add’iyar riga ce a ciki, duk da a nunke take ta fahimci princess gown ce dan gata a jikin wata a gefe an manna da alamun anaso masu siya su san yanda take ba tare da sun bud’e ledar sun warwaretaba.
Gefe guda kuma y’an kunne ne masu kyau da bracelet da anklet, sai takalmi shima an yi mishi gurin ajiyar sa daban mai matuk’ar kyau kalar y’an kunnen da kayan
RED!.

Chan k’asa kuma wani d’an k’aramin lipstic ne an yi rapping d’inshi da leda garai garai da alamun gift ne shi aka bayar.

Banda murmushi tana kallo tana sake kallon katon kwalin,
ba abunda take yi.

A hankali ta ji yace
“Do you like it?”
Murmushi tayi mai d’an had’e da dariya kafin ta juyo ta d’aga masa kai tace
“Yes, na gode sosai”

Kallon idanunta yake yana hango farin cikin da take ciki
a hankali ya jinjina kai ya d’an motsa bakinsa yace
“Welcome”
Sannan ya mik’e ya karb’a dryer d’in hannunta ya bud’e ya mak’ala comb d’in ya jona a socket. Har zai kunna sai kuma ya koma gaban dressing mirrow ya d’auko hair cream ya dawo. Takalmansa sau ciki ya cire ya bar iya safar ya hau kan gadon ya tsugunna ata bayanta sannan yace “ta mik’o mishi dryer”
Juyowa tayi da d’an mamaki a fuskarta kafin tace
“Me zaka yi?”
Tana d’an zaro ido.

“Bani sai ki gani, ko?”
Ya fad’i hakan yana k’ok’arin b’alle murfin hair cream d’in da ke hannunsa.
“Ko kina buk’atar cuddling ne sannan ki mik’o?”
Ya fad’i haka yana zare towel d’in da ta nad’e gashin da shi.

Tun kafin ya ida rufe bakinsa tayi sauri ta mik’a masa dryer.

Karb’a yayi yana dariya k’asa k’asa sannan ya d’an d’ebo man ya mulke mata jik’ak’k’en gashin nata da shi ya fara busarwa yana tajewa.

Hudan, ba k’aramin mamaki ta sha ba game da yadda
akai ya iya gyaran gashi dan
har wani massage yake mata da taji tana shirin fara barci.

Gyaran gashin yake yi
amman cikin nutsuwa da aji.

Kasa hak’ura tayi tace
“A ina ka koyi gyaran gashi?”

Sai da yayi murmushi tukunna yace
“Internet.
I always dreamt of making my wife’s hair..gashi
is one of the things da nayi ta adduar Allah ya sa matata ta kasance tana da shi, I love it!
Sai gashi Allah ya amsa adduar tawa.”
Ya fad’i haka yana me kashe dryer dan har ya gama.


Dariya Huda ta fara ganin yadda ya dawo gaban gadon yana haki kamar wanda yayi race.

Hararar ta yayi ya b’ata rai
tukunnan yace “ba thank you sai dariya ko?”

A hankali tace “thank you”

Sai da ya gama hutawa tukunna ya tashi ya d’auko rigar ya cire a leda ya ware ta
ya kama hannunta ya mik’ar….
Da sauri tace
“Ya Aslam kai fa kai kad’ai ka shirya”

“Bari tou In cire nima sai ki tayani, ko?”
Yayi mata tambayar yana k’ok’arin kwance belt d’in wandon jikinsa.

Da sauri ta rik’e hannunsa tana turo baki sannan ta sunkuyar da kanta k’asa…..

Zip d’in rigar har kusan chan k’asa ne dan haka ya zuge shi duka tukunna ya kawo ta wajen kanta ya zura mata sannan ya saki rigar.

Ganin yana k’ok’arin sa hannu ya kwance mata bathrobe d’in ta ciki yasa tayi sauri ta matsa ta kwance ta zame hannuwan kafin tayi k’asa da ita duka sannan ta jaa hannun rigar ta saka threequater hannun
ta fara k’ok’arin zuge zip d’in….
Ganin bazata iya ba ya sa
duk turjewarta haka ta tsaya ya ja mata…..
Kwalliyarma da kyar ya barta ta shafa powder ta saka mascara da eye liner
amman y’ankunne bracelet anklet takalmi da
red lipstic duk shine ya saka mata!
Tayi kyau kuwa sosai…,

A hankali ya ajjiye lipstic d’in yana kallonta….
Ganin kallon yayi yawa ya sa ta wuce taje ta d’au ribbom d’inta ta yi parkin, ta d’auko
wani tauban cap na chantily mai stones red ta saka
ta d’auko vail black medium ta rufa a kafad’a…….

Aslam, gaba d’aya jikinsa yayi sanyi dan Huda ba k’aramin tafiya tayi da imaninsa ba..duk
inda tayi kawai binta yake yi da idanu.

A hankali ya d’au wayarsa ya k’arasa inda take ya jaa hannunta suka nufi gaban dressing mirrow suka tsaya…
Ta tsaya a gabanshi shi kuma a baya ya rik’e waist d’inta yayi musu hoto.
Sun yi kyau kuwa ba kad’an ba
kuma sun fito sosai.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya gyara mata mayafin nata ta hanyar maidashi saman kanta kafin yace
“Can we talk?”
ya fad’a hakan yana me juyo da ita suka yi facing juna
kafin ya d’aura hannayensa a kan kafad’unta ya fara magana
“Next week, in shaa Allah inaso mu wuce UK!
Mun riga mun gama magana da su Abba tun last 2 weeks jiya kuma har su Ummi na gayawa a wajen dinner, yanzu
ke kad’ai ya rage baki sani ba.
Za ki bini?”
Ya k’arashe maganar a hankali.

“Um um”
Tace tana mai
ja da baya ta d’an sunkuyar da kanta kafin tace
“Mai yasa za mu tafi?
Me su Ummin suka ce?”

Sai da ya lumshe idanuwanshi ya bud’e kafin yace
“Arshaad is morethan comfortable!
Infact da farko shi ne ma daa zai tafi saboda yace zaman mu under same roof ba zai yiu ba, sai da na yi masa bayani d’azu
akan
already daman akwai plan d’in tafiyar ta mu tukunna shi ya yarda zai zauna a nan.”


Sai da ta gama jin bayanin nasa tukunna tace
“Nifa ba saboda Ya Arshaad bane nace A’a ba.”

A hankali yace “mai yasa to ba zaki bini ba?”

Cikin tarar numfashinsa tace
“Ya Aslam kamata fa yayi mu yi focusing akan yadda zamu warware wannan auren!
Kar mu bawa su Abba false hope d’in wata rana za mu so juna..”
Ta k’arashe maganar tana jin wani nauyi yana sauk’a daga zuciyarta.

Janyo ta kawai taji yayi yai huggging d’inta…
Sun d’an jima a haka
kafin a hankali yace
“Za mu tafi UK next week
It’s an order”

Shiruu, tayi tana mamakin yadda k’irjinsa yake bugawa da kuma yadda gaba d’aya jikinsa yake karkarwa,
gashin sai sake rik’eta yake yi da kyau kamar wanda akace za’a kwace ta.

So take ta motsa ta gaya mishi itafa ba inda zata je amman kuma kamar wadda aka rufe waa baki, kwata kwata
sai ta kasa.

Sun jima a haka suka ji ana knocking......



Mommy, tunda tazo take baza ido, so take kawai taga ta Ina za su fito..
Duk da Aslam yana zuwa kullum wajen ta idan ya tashi a office wani lokacin ma kafin ya fita sai ya je
amman so take yi kawai ta gansu especially Hudan…
Hak’urinta ne ya k’are dan haka ta cewa Ummi “ta je ta kira mata su, da wurwuri
take son tafiya su fito su gaisa kafin ta tafi.”
Dariya Daddy yayi yace
“A’a Mommy ki dai fad’i gaskiya…y’ay’anki kawai kike son gani.
Tun d’azu fa nake ganin ki kinata zullo kina lek’en ta Ina za su fito”
Ai kuwa gaba d’aya aka saka dariya
banda Mammy da Mom
Arshaad kam murmushi kawai yayi.

Mik’ewa Ummi tayi zata wuce
dai dai nan su Shuraim suka sauk’o…
Suite d’insu milk masu asalin tsada sai belt da takalmi brown. Ba k’aramin kyau suka yi ba.
Wajenta suka fara zuwa suka yi hugging d’inta!
Bata san daliliba kawai sai taji hawaye ya zubo mata. A hankali ta
dafa kawunan su ta ce “Allah ya yi muku albarka”
Daga nan tayi saurin wucewa dan bataso tayi kuka.

Nan suka k’arasa inda Dad Mommy Abba Arshaad Mammy Mom da Daddy suke..
Aka fara hotuna bayan an yi wishing d’insu Happy Birthday kowa ya basu gifts d’in da ya shirya musu.

Knocking kawai Ummi tayi ta juya dan ta raba kanta da shiga d’akinsu Aslam ita kam......


Bata yi minti d’aya da zama ba suka fito..
Kowa a parlourn zuba musu ido kawai yayi, ba
k’aramin kyau da dacewa da juna suka yi ba.
Kallo d’aya Arshaad yayi musu ya d’auke kai da sauri
Mammy kam tana ganin fitowarsu ta juya kan ma gaba d’aya ta sake tamke fuska.

Ba yadda Hudan bata yi da shi akan ya saki mata hannu ba
amman fur!! Ya k’i.
Haka nan duk sai taji kunya ta lullub’eta especially da suka had’a ido da Mommy wadda take ta zuba murmushi kamar an mata albishir da gidan aljannah…
Suna k’arasowa ta mik’e ta kamo hannun Hudan
ta fara k’ok’arin janta dan ta zaunar da ita a gefenta.

D’agowa tayi suka had’a ido da Aslam! Sai da ta d’anyi dariya tukunna tace
“Cikata mana, ko?”

Shima kuma sai yaji kunyar Abba da su Dad ta rufeshi dan haka a hankali ya cikata ta zaunar da ita itama ta zauna Aslam ya zauna a gefnta
Tun kafin ta fad’a Shuraim ya shiga yi musu hotuna…
Abba da Dadddy da Dad ma suka shiga, haka ma Ummi.
Ranar dai anshan hotuna kala kala bibbiyu uku uku,
daga nan su Shuraim suka fita saboda friends d’insu duk suna waje.


Sai wajen 9 su Sakina suka zo, murna a wajen Hudan ba a magana.
Suna gama gaisawa da su Abba suka fita compound suka nemi waje suka zauna.
Basu dad’e da zama ba
aka fara gudanar da program of event.

Suna cikin hira su biyu
dan Sumayya har ta yi k’awa wata Khairat sun ja gefe anata iyayi da manyance, suka ji
an jawo kujera an jona da table d’insu an zauna a gefen su.
Tana d’agowa suka had’a ido
a take gabanta yayi wani irin mahaukacin fad’uwa!
So take ta cire idanunta a nashi amman ta kasa…..

“You came.”
Yace
yana mai kallon cikin idonta.

A hankali tace
“Yes”
Sai kuma ta mik’e da sauri tace
“Hudan muje ki rakani bathroom”
Tana mik’ewa ta yi gaba…..

Da sauri ya kalli Hudan yace mata
“A minute please”
Sannan ya mik’e ya bi bayan Sakina wadda tayi hanyar falon su Hudan da sauri.


Kwarewa Mammy ta yi, da sauri ta kamo hannun
Mom! Tana juyowa ta nuna mata su, tace
“Kinga
Auwal da Cousin d’in Huda wadda suka zo d’azu
Hudan take ta murna d’innan.”

Babu abunda yafi d’aga musu hankali irin yadda Auwal yake kiranta yana d’an gudu
amman ko alamun zata juyo ma bata yi ba...


Tana shiga shima yana shiga!
Sai a lokacin ta lura da Huda bata biyo su ba. Da sauri ta had’e hannuwanta biyu waje guda alamun rok’o, tace
“Dan girman Allah Ya Auwal ka rabu da ni! Ka fita a harka ta.
Me kake so in yi maka?
An saka ranar aurena!
Nan da 5 month in sha Allah Ina gidan wani me kuma zaka ce min yanzun
me kake buk’ata a....”
Maganarta ce ta katse sakamokon hawayen da ta ga sun tsinke masa lokaci guda kamar fanfo sai kace wani k’aramin Yaro.

A hankali ya durk’usa a gabanta ya had’e hannuwanshi duka biyu shima, yace
“Sakina dan girman Allah
ki san yadda za kiyi da ni!
Wallahi ban san halinda nake ciki ba, ba laifina bane ba,
na san na takura ki da yawa
amman ba laifina bane ya kamata ki gane.
Ya kike so in yi?
Wallahi na yi na yi In cire ki a raina amman kullum sonki da k’aunarki k’aruwa kawai suke yi!
Ki taimaka kar ki auri wani
wallahi zan iya mutuwa.

Na ji zan baki time zan baki space amman kar ki auri wani na dan girman Allah.
Sannan ki san yadda za kiyi da ni, ki yi min abunda zan ji kin fita a raina. In kikayi min haka kin gama min komai.

Na san ba a neman aure cikin aure amman na kasa hak’ura da ke! Ba zan iya ba ki san yadda za ki yi dani dan Allah.

I know I’m not making any sense here
I can’t loose you
kuma tunda kince bakya so na
i can’t force you to love me
so I can’t love you
saboda ni
happiness d’inki shine abunda nake so
amman fa kar ki ce za ki auri wani.
Wallahi rabona da bacci tun shekaran jiya!
Inaga haukacewa zan yi, bana gane komai bana gane kowa sai ke!
Ki fita a raina sai in barki
Ki fita a zuciyata sai in...........”
Kukan da ya taho mishi fiye da na farkon da yake yi ne ya sanya ya kasa ci gaba da magana.

Ita kanta Sakina
kukan da take ta k’ok’arin rik’ewa ne ya samu nasarar kufce mata.

“Innalillahi wa innailaihirrajiun!!”
Suka ji muryar Mom da Mammy a bayansu har da wata k’awar su,
suna salati suna tafi.

Da sauri Sakina ta share hawayenta ta d’an matsa
saboda Auwal d’in ya tashi ya basu damar shigowa
amman ko gezau bai yi ba.

Wani kallon tsana Mom take watsa mata, kafin cikin tsananin b’acin rai tace
“Yanzu ku jinin Madu ashe ba zaku tab’a jin tsoron Allah ba?
A haka za ku k’are?
Wato Maryam ta yi
shine kema zaki biyo ki haukatamin d’a??
To billahilazim na fi k’arfinki!
Duk surk’ullen da kika je kika yi ki koma ki je ki wargaza tun kafin In tashi biyowa ta kanki!.

Saboda Allah Mammy ku kalli yadda Yarinyar nan ta maida Auwal! Auwal fa!!!
Wai yau shine a gaban mace yake kuka haka wiwi da hawaye kamar wani sakare?

Wallahi Allah sai yayi mana hisabi da mu da family d’in Madu ranar gobe k’iyama.
Wanne irin jarababben abu ne yake yawo a jininku sai kace mayu?”
Tayi maganar tana kallon Sakina cikeda tsana
wadda itanma ta zuba mata nata dara daran idanuwan da suka rine sukai jaa.

Za tayi magana kenan Auwal ya mik’e da kyar ya juya gareta yace
“Haba Mom,
abubuwan da suke kai na already sun yi yawa
Dan Allah kar ki zo kiyi haka
kar ki saka ta k’ini completely!
Ki koma waje dan girman Allah
Magana muke yi, maganar da ta shafemu iya mu biyu tak!
Ba wanda ya gayyotoki ke da k’awayen ki nan”
Ya k’arashe maganar tari yana kufce masa…”

A rikice tace
“Auwal na rantse da Allah zan yi maka abunda baka tab’a zato ba!
Karankatakaf fad’in duniya ace ka rasa macen da za ka so sai jinin Maryam Jikar Madu da Shuwa?
Kasan su waye su kuwa?”

Kuka kawai Sakina ta saka
ta fara ja da baya…
Da sauri Auwal ya juya ya fara binta yana magana yana tari
“Ki tsaya..
Don’t mind her..
let’s talk..
Dan Allah..

Sai a sannan Mom ta samu damar shigowa ita da su Mammy.
Kamar ma tangad’i Auwal d’in yake yi dan haka suka samu suka wuceshi suka yi kan Sakina!

Mom tana zuwa, ta shak’ota tace
“You must mind me!
In dai kina da hankali kuma kin san darajar uwa a wajen d’anta
to ki sani ba zan tab’a barin Auwal ya aurenki ba wallahi!
Dan haka ki hak’ura.

Ina fatan Huda ta zame miki lesson a rayuwa…..amma idan
mahaukaciya ce ke to ki so Auwal ki aureshi dan Allah, wallahi nayi miki alk’awarin sai na lahira ya fiki kwanciyar hankali”
Tana gama fad’in haka tayi cilli da ita wanda har ya kaita ga kaiwa k’asa.

Kasa motsi Auwal yayi dan zuwa yanzu ya fara ganin dishi dishi, tabbas ya san halaiyyarsa da kuma Granpa su suka hana Sakina yarda ta auresa amma ya san tana sonshi wanda hakan ne ma yasa ta sanya aka kawo kud’in aurenta da wuri!
Duk ya fahimci hakan.
Yanzu kuma ga Mom!
Ya tabbatar ta gama wargaza masa d’an
guntun chance d’in da yake hangowa….
Duk da baya ganinta amman yana iya jiyo setin inda take kuka, dan haka ya fara yunk’urin d’aga k’afarsa domin ya k’arasa wajenta.
Yana motsawa kuwa kamar jira ake jiri yace bismillah!
Gaba d’aya ganinshi ya d’auke in banda duhu babu abunda yake gani, ga wani mahaukacin juyawa da kanshi yake yi……
Da sauri yasa hannu ya dafe kan nashi yace “wash!!”
Da d’an k’arfi.
Sai a lokacin hankalin Mom
da Mammy da k’awar tasu waenda suka k’arasa suka cigaba da tsigale Sakina suna kiranta da ‘talaka, kwadayayyiya’ Ya koma kan Auwal.

Da sauri Mom ta nufesa ganin yana shirin zubewa k’asa
amman kafin ta k’arasa har ya fad’i k’asa sumamme..

Dede nan su Daddy Abba da Ummi suka shigo
dan dama Ummi kamar ta d’an jiyo hayaniya sama sama…

Ba karamin tsorata Mom tayi ba ganin Auwal a k’asa kamar matacce.

A haukace ta juya ta koma kan Sakina da take nan durk’ushe tana kuka, ta sake shak’ota ta mik’ar tsaye ta hau magana kamar tab’b’abb’iya
“Waenna irin mutane ne ku?
Baku da tausayi ne?
Dolene sai an so ku?
Wallahi na rantse da Allah ko a Birnin sin kika yi mishi asiri yau sai mun je yanzu ba sai gobe ba kin warware shi.”
Ta fad’i haka tana k’ok’arin fara janta.

Sakina kam banda tari ba abunda take yi gaba d’aya ta fice a haiyyacinta dan ba k’aramar shak’a Mom tayi mata ba.

“Adama!!!!”
Suka ji muryar Dad cikin tsawa a bayansu.

Juyawa Mammy da k’awar tasu suka yi ita kuma Mom ta cika wuyan Sakina ta durk’ushe a wajen ta fashe da kuka.

Dede nan Aslam da Huda suka shigo!
Da gudu Hudan ta k’arasa inda Sakina take…

Cikin tsananin b’acin rai Daddy ya k’arasa inda suke ya d’agota ya fara magana
“Baki da hankali ne?
Me yake damunki?
Wachche irin kwakwalwa ce da ku ne wai?
She’s our guest for crying out loud!!
Ga babanta chan a waje ya dawo d’aukar su
a haka kikeso a fitar mishi da ita ko yaya?”

Cikin kuka Mom tace
Kallafa Auwal”
Ta nuna masa Auwal
wanda Abba da Aslam suka ciccib’a za su fitar,
cikin kukan taci gaba da magana
“Asiri tayi mishi
Irin wanda Maryam ta yiwa Abba bani da tantama!
Daddy a k’asa fa nazo na tarar da Auwal durk’ushe gaban wannan k’ask’antacciyar yana rok’onta ta soshi ta aureshi yana kuka kamar k’aramin Yaro
In ba aikin asiri ba tayaya zaka yi tunanin Auwal zai so wannan k’ask’antacciyar?”
Tayi maganar tana nuna Sakina a wulak’ance.

“Tayaya aka yi na so ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login