Showing 27001 words to 30000 words out of 100703 words
Chapter 10 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt
ya zamana hannuwantane kawai akan nasa ko motsasu bata yi…..
A hankali take jin fad’uwar gaba da kuma wani sanyi da nutsuwa a yayin da take kallon cikin idanunsa…ta fad’a a yau kuma ta sake tabbatar wa
‘babu wanda ta tab’a gani mai kyawun idanuwa kwatan kwacin na Ya Aslam’
A ranta tace
“tubarkallah ma sha Allah”
Cikin muryar bacci taji yace
“Good morning wifey!”
A hankali ta lumshe idanuwanta a ranta take tunanin
‘Anya wannan ba aljani bane ba kuwa?
Kallafa yanzunnan ya tashi a barci amman idanuwansa basu yi ja ba
sai ma wani kyalli da taga sunayi sannan bakinsa kamar
ma sweet ya sha dan in dai
taji da kyau tou k’amshin mint taji……….’
D’umin numfashinsa ne taji yana k’ara bak’untar fuskarta!
A hankali take sauk’e ajiyar zuciya tana sake rik’e hannunwansa…..
Chan! Kamar wadda ta tuna wani abun, tayi saurin bud’e idanuwanta tarr!! A d’an zabure….dai dai shi kuma ya samu nasarar d’aura lips d’insa a kan nata........
A mugun firgice ta sanya dukkannin k’arfinta ta turesa
amman ko gezau! Bai yi ba.
Wani rikitaccen kuka ta saka masa!
Dan haka yayi saurin sakinta ya d’an jaa baya yana kallonta.
Tana jin ya saketa, ya bata iska ta bi ta kansa da wani irin sauri ta sauk’a daga kan kujerar!
Mayafinta da yake lullub’e a jikinta wanda ya fad’i yanzun kawai ta samu damar d’auka
daga nan ta nufi k’ofa………
Tana jinsa yana kiran sunanta
amman tayi banza da shi ta fice da mugun sauri....
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
62
Mikiya Writers Association.
Chan sama ta nufa.
tana tafe tana adduar
‘Allah yasa side d’inta a bud’e yake’.
Tana isa ta tura, cikin sa a ta tarar a bud’e dan haka ta shige ta saka key!
Tana zuwa ta zauna a kan kujerar parlourn tana haki kamar wadda tayi gudun famfalak’i…
Ta dad’e a nan zaune, jin
an shiga masallaci ya sanya ta mik’e tana tunanin komawa d’akin dan ta samu ta d’au hijabi ta yi sallah.
Kamar aslam d’in ya biyota
haka ta d’an bud’e k’ofar kad’an ta lek’a!
Ganin babu kowa a dogon corridorn ya sanya ta sauk’e ajiyar zuciya ta fito tana sand’a…..
Sai da ta kai tsakiyar parlourn taji muryar Ummi a bayanta
“Hudan”
Runtse idanunta tayi a hankali kafin ta bud’e sannan ta juyo, ta shiga k’ok’arin k’ak’alo murmushi…
Kallonta Ummin tayi from head to toe sannan ta nufota, tana zuwa “me ya kawoki nan?”
Kame kame ta fara…chan! Da kyar tace
“Daman zuwa nayi In karb’i Qur’ani a wajen Shuraim
kuma d’akin nasu ma a kulle ne “
Had’e fuska Ummi tayi kafin tace
“Yaushe kika koyi k’arya?
Ina d’aki fa Ina karatu naji an hawo
Ina lek’owa naga wucewarki d’akinki tun d’azu!
Mai ya faru??”
Tayi maganar tana tsareta da idanuwa.
A hankali ta sunkuyar da kanta
batai auni ba kawai taji hawaye sun zubo mata.
Sarai daman Ummi ta so ta fahimci wani abun…murmushi
kawai tayi a ranta
tana mamakin Aslam!
Kafin ta jawo Hudan zuwa jikinta cin son sake fahimtar lamarin tace
“Yi shiru, shikenan.
Bara in d’auko miki Qur’anin a d’akina sai ki wuce kije ko?
Kar Aslam d’in yaga kin dad’e, yau ma na san da wurwuri za su fita.
Kiyi sauri kije ki tayashi shiryawa, ko?”
Kuka kawai taji Hudan ta kece dashi kamar wadda akace za a yankata! Cikin kukan tace
“Ummi dan Allah karki bari in koma, Allah ba zan iya had’a ido da shi ba, baki san meh....”
Kamar kuma wadda aka datse harshenta sai ta
tsaya da maganar chak! Tana mai ci gaba da kukanta.
Murmushi Ummin tayi
ranta fess. Tace mata “to shikenan
jeki ki yi alwala ki yi sallah
ki daina kuka haka.
Anjima sai muyi magana ko?
Muje d’akina.
Tayi maganar tana jan hannunta.....
Bayan, Ummi ta gabatar da sallar Asubah, ta yi azkar,
ta zauna ta hau nazari…
Wani sanyi da dad’i take ji a ranta..ta san Huda Arshaad take so amman tabbas kamar yanda su Dad sukace
‘Ko bayan auren Mammy bazata barta ta zauna lafiya ba’
Aslam shine wanda take gani zai bata cikakkaiyar kula da soyayyar da take buk’ata,
bayan haka
sun yi mugun dacewa
sannan ita daman ta d’an fahimci kamar Aslam d’in yanas son Huda!
In dai kuwa hakanne
Allah Ubangiji ya barsu tare ya k’ara musu k’aunar juna
ya sanyasu farin cikin da basu yi tun tasowarsu ba……
A zaune taga Huda ta fara gyangyad’i dan haka tace mata “ta tashi ta kwanta a kan gado”
Da sauri kuwa Hudan ta mik’e
saboda daman addua take tayi kar Ummi tace mata taje ta had’awa Aslam breakfast.
Tana kwanciya bata dad’e ba bacci ya kwasheta
Ummi kuma ta mik’e ta fita dan had’a musu breakfast d’in..
Tana cikin bacci taji muryar Abba yana kiran sunanta,
a hankali ta bud’e idanuwanta.
Zaune ta ganshi a gefenta yana mata murmushi
dan haka itama ta d’anyi murmushin sannnan ta mik’e ta zauna tace
“Abba Ina kwana”
“Lafiya, Alhamdulillah.
Kin tashi lafiya?”
“Alhamdulillah”
Tace
Mik’ewa taga yayi tsaye kafin yace
“Zamu wuce UK ni da Daddy.
Urgent tafiya ya taso,
akwai abunda kike buk’ata?”
Murmushi kawai tayi tace
“Ba komai.
Allah ya kiyaye ya tsare hanya ya dawo daku lafiya”
A hankali ya d’an matso ya shafa kanta yace
“Ameen princess,
take care.
Sai mun dawo ko”
Yana gama fad’in haka ya juya ya nufi hanyar fita, har ya kama handle d’in sai kuma yaga rashin kyautawarshi
dan haka ya juyo ya kalli Ummi dake gefe a tsaye yace
“Na tafi.
Zan saka miki kud’i ta account ko akwai abun buk’ata.
In akwai wani abun you can call me”
Wani kalan murmushin farin ciki ne ya baiyyana a kan fuskarta, tana murmushin tace
“Nagode.
Sai kun dawo”
Murmushin daya mayar mata ne ya bata kwarin guiwar binsa a baya domin tayi mishi rakiya.
Hudan ma taso ta rakasa
amman ganin sun fita da Ummin ya sanya ta bari kawai,
dan ta barsu su samu alone time su biyu.
Kallon agogo tayi taga har 10 ya d’an gota. Ta san by now Aslam ya fita dan haka ta sauk’e ajiyar zuciya ta zuro k’afafunta k’asa tana
tunani da mamakin guts! Kalar na Ya Aslam….mai yasa yayi mata hakan? Ya san ba sonta yake yi ba mai yasa zai dinga yi mata wasu abubuwan kamar waenda sukayi auren soyayya!?
She definitely has to stay very far away from him
har sai ta gano inda relationship d’insu ya dosa da ita kanta dan
gaba d’aya Aslam ya juya mata lissafi kwana biyun nan kanta duk ya d’aure
It’s like bama ta san me take so ba! Tabbas ta san tana son Ya Arshaad sannan tana son rabuwa da Ya Aslam
Amman kuma when ever she’s with him
she feels complete and safe!
Da farko bata fahimci hakan ba sai a jiya da yayi hugging d’inta ta kasa kwace kanta daga k’arshema bacci ya kwasheta………..’
Ajiyar zuciya ta sauk’e, a chan k’asan ranta tace
“A complicated marriage is enough!
I can’t deal with complicated and confused relationship.”
Tun d’azu idan ta tuna da moments d’insu na tsakanin jiya da yau da safe sai taji tana feeling somehow…bata k’aunar wannan feeling d’in at all
bata son abunda zai na janta garesa shiyasa gara tun
kafin ta gama zama confuse tabbas ya kamata ta d’au mataki….
A haka Ummi ta shigo ta sameta.
“Tunanin me kike yi?”
Taji muryar Ummin.
A hankali ta d’ago ta kalleta
sai kuma ta maida kanta k’asa tace
“Ina kwana”
Murmushi kawai Ummin tayi tace
“Lafiya” sannan tace
“Oya tashi ki shirya mu yi sauri mu tafi ko?”
Ai tun kafin Ummi ta ida rufe bakinta Hudan ta sauk’a ta fita daga d’akin cike da d’oki.
Murmushi kawai Ummin tayi itama ta hau nata shirin…
Sai pass 11 sannan suka shirya suka fito
Hudan bata wani yi kwalliya sosai ba, Abaya ce a jikinta nude colour mai kyau sosai, tayi rolling ta d’an saka lipstick, sai zobe da bracelet a hannunta.
Ummi kuma lace ne mai kyau da tsada a jikinta peach da farin mayafi da jaka da takalmi.
Suna baya suna d’an tab’a hira driver yana jansu, haka suka kama hanya…
A wani babban mall Ummi ta cewa drivern “yad’an tsaya”
Dai da suka fita tukunna ta bawa Hudan kud’i, tace
“D’azu Aslam yace abata ta yi siyayyan tsaraba ta kai gida”
“Angode” kawai ta iya cewa
daga nan suka shiga sukayi y’ar siyayayr tsarabar suka fito
Ummi tana lura da yadda mood d’in Hudan ya chanza tun daga lokacin data ambato sunan ‘Aslam’
So take ta fassara yanayin nata amman ta kasa
a haka driver yayi parking a kofar gidan Madu....
Fita suka yi,
Driver ya tayasu kai kayan har bakin k’ofar parlour
daga nan suka sallameshi
bayan sun yi da shi akan 3:00pm zai dawo ya d’auke su.
A parlourn k’asa suka tarar da Mama tana zaune tana kallo.
Sallamar su ce ta sanya ta maida hankalinta bakin k’ofar, kamar a mafarkin haka taji
nan take wani farin ciki ya lullub’eta.
Cikin farin ciki Huda ta ajjiye ledojin hannunta a farkon parlourn ta k’arasa da gudu ta fad’a jikinta ta yi hugging d’inta.
Tabbas Mama tayi farin cikin ganin d’iyar tata
amman sai ta maze ta zarota daga jikinta ta fara yi mata fad’an ‘mai yasa ta fito?
Dududu yaushe ma aka kaita?”
Ummi ce ta k’araso inda suke tace “Ayi hak’uri Mama ni nace sai ta rakoni”
Murmushi Maman tayi
dan ita ta ma manta Hudan tare take da bak’uwa hakan
yasa ta d’anji kunyar barinta da sukayi a tsaye ita kad’ai.
Cikin fara a tace
“Bismillah ki zauna.
Yi hak’uri wannan ta gudo ta barki bama ta tsaya kun k’araso tare ba”
Murmushi Ummi tayi
sanann ta k’arasa ta ajjiye ledar hannunta a gefe tukun ta zauna a kan d’aya daga cikin setin kujerun da Maman tayi mata nuni da.
Tana zama Mama tayi kitchen..
Sai da ta cika mata gabanta da kayan kwalama da su lemuka tukunna ta nemi waje ta zauna tana raba d’ayan biyu
‘Ko dai babar Auwal ko kuma matar Abba!
Amman anya kuwa matar Abba zata yarda tazo kuma tana mata fara’a haka sosai?’
“Ina su Hajiya? Na ji gidan shiru”
Muryar Huda ta katse mata tunani.
Sai da ta d’anyi jimm!
Tukunna tace
“Tana gidan Baaba Talatu,
Baba ne aka dawo da shi
wai bashi da lafiya sosai”
“Allah ya bashi lafiya”
Shine abunda Huda tace kawai
dan jiya ma sai da suka yi maganar ita da Sakina
A yanayin take taken Baaba Talatu so take ta fake da rashin lafiyar Baba a maida Mama gidanshi.....
“Kafin ku tafi ya kamata ki shiga ki dubo shi”
Hudan taji muryar Mama.
“Tam”
Kawai tace kafin tace mata
“Sakina fa?
Jiya tace min tana nan”
Cikin sigar zolaya Maman tace
“Amarya dai zaki ce!
Ta tafi. Gobe suka ce za suje gidan dangin Babanta
da shi da Yayansa
Babansu yayi tafiya.
Nan da sati biyu kuma in sha Allah za su koma har da su kawunnansa da Mahaifin nasa a saka rana”
Murmushi suka yi daga Huda har Ummi, a tare suka ce “Allah ya tabbatar mana da alkhairi”
Kafin Ummi ta d’an nisa tace
“Dota d’an bamu guri, ko?”
A hankali Hudan ta mik’e ta wuce sama ta bar su su kad’ai a zaune.
Gyaran murya Ummi tayi suka d’an sake gaisawa kafin tace
“Maryam ni ban ma san ta Ina zan fara ba!
Abu biyu
ne yake tafe dani
wanda duk biyun alfarma ce nazo nema daga gareki
amman inaga gara in fara dana farkon dan shi yafi hanani sukuni a rayuwata.”
Tabbas tun lokacin da taji ta kira ‘Huda’ da ‘dota’ ta fahimci Zainab ce!
A hankali Mama ta gyara zama ta fuskanceta da kyau kafin tace “Ina saurarenki,
Allah yasa zan iya taimokonki”
“Za ki iya
In sha Allah”
Shine abunda Ummi tace
kafin ta cigaba da cewa
“Sunana Zainab, na san
kin sanni a bad’ini a zahiri kuma yau gani a gabanki.
Da farko ina mai neman alfarmarki
Maryam dan dan Annabi
ki samu ki yi creating space a zuciyarki ki yafe min laifin da nayi miki shekarun baya
sannan ki yafe min laifin da nayi ta maimaitawa Ina nanatawa duk akan Abba kar ya dawo gareki!
Ba dan ni ba, tare da taimokon su Adama to da tuni tun a karon farko lokacin da kika tura mishi da sak’o na san
da kun koma kun ci gaba da zaman ku cikin kwanciyar hankali da k’aunar juna, amma
biyewa zuciya da son kai
suka kaini ga aikata makircin da wallahi ni kaina idan na tuna kunyar kaina nake ji!…,
Na san I’m asking for a lot,
na san da wuya ki yafe min, na san ko da ace kin yafe min to ba lalle ki daina ganina da abun ba….”
A hankali Ummi ta share hawayen da suka zubo mata sannan ta d’an zamo daga kan kujerar ta durk’usa….
Da sauri Mama itama ta sauk’a akan kujerar tace
“Dan Allah kar ki yi haka!
Already ni kam na dad’e da yafe miki besides ba kece kika saka Abba ya sakeni a wannan ranar ba kawai dai kun had’amu fad’a ne wanda yanzu ya riga da ya wuce,
komai ya wuce!
Dan haka
na yafe miki
Ubangiji ma ake masa lefi anemi gafara kuma ya yafe mana
ballantana ni?
Ki manta da komai
ki saki ranki
In dai dan ta ni ne inaso kisa a ranki kamar komai bai faru ba!
Dan Allah. Sannan
ki daina d’aura laifin da ba naki ba a kan ki ke kad’ai dan Allah.”
Ummi bata san lokacin da ta fashe da kuka ba!
A hankali Mama ta rungumeta
Itama tana nata hawayen da bata san dalilin sa ba.
A hankali ta share hawayen nata sannan ta cika Ummi ta gyara zaman ta ta hau lallashinta…..
Da kyar Mama ta iya lallashinta
aka samu ta yi shiru.
A hankali
Ummin ta kamo hannuwanta duka biyu a cikin nata tace
“Na gode kwarai!
Sai alfarma ta biyu….
Ina rok’on ki
ki daure! Na ji kuma na san yadda Abba yake ta faman biko amman kin k’i amincewa!
Na san kina da gaskiya ta wani b’angaren amman kuma duk inda akaje aka dawo Abba ya fiki gaskiya.
Ki yi hak’uri ki daure
ki koma gidanki na farko
na tabbatar har yanzu kina son Abba kuma a cikin shekaru goma sha taran nan da nayi da shi a matsayin Miji na fahimci zuciyarsa ba tawa bace ba taki ce!
Ba zan tab’a mallakar abunda ba nawa ba
kuma indai bakya tare da shi to ba zai samu nutsuwar da ni kaina zan samu koda ace 1/10 d’in kulawar da ya kamata ya bani ba.
Ki daure, kar ki cuci kanki ki cuce ku. Ki dawo kusa da y’arki
kusa da masoyinki
ku k’arashe rayuwar ku just like it was soppose to be…
Kar ki damu da kowa
ke dai kawai ki yi abunda zai sanyaki farin ciki,
dan Allah.”
Da sauri Mama tace
“A’a zainab
gaskiya wann.....”
Cikin katseta Ummi tace
“Na san alfarma nace Ina nema a wajen ki
amman In kikai duba zakiga kamar a cakud’e take da shawara! Shawarar da duk wani masoyinki na gaskiya zai baki.
Sanann idan kikai haka za ki sanya mutane da yawa farin ciki..
Kinga na farko ‘Abba’
Ta biyu ‘Huda’
Sannan ta uku ‘Ni’.”
Da mamaki Mama take kallonta.
Murmushi Ummi tayi sannan tace “tabbas!
Dan ni gani nake yi ma ko Abba ba zai kaini farin ciki ba saboda kinga na farko
Zan ganshi cikin farin ciki Sannan zai daina blaming d’ina akan na rabaku
sannan idan ba gani nayi na gyara abunda na b’ata ba to
wallahi har abada har In koma ga mahaliccina ba zan iya samun nutsuwa ba!
Ganin ku tare a yanzu
living together happily
zan iya ce miki shine abunda nake da kwad’ayin gani a yanzu fiye da komai a rayuwata”
Zuwa yanzu Mama kam tama rasa bakin magana…
A hankali Ummin tace
“Ki yi tunani mai kyau.
Dan Allah Maryam”
A hankali Mama ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya
tana kallonta kawai..
Sai a lokacin Shuwa wadda shigo tun d’azu tayi musu sallama.
D’agowa sukai suna kallonta, itanma su take kallo har ta k’araso tsakiyar parlourn inda suke, jikinta duk a sanyaye.
Cikin mutuntawa Ummi ta shiga gaisheta, Itama ta amsa mata cikin karramawa da kulawa kafin ta k’araso ta nemi waje ta zauna
tana tambayarta “ya mutan gidan?”
Sun d’an jima kafin Huda ta sauk’o.
Shuwa na setin staircase dan haka da ita ta fara tozali!
Salatin da ta rafka sai da ya firgita su Mama dan
haka suka juya suna kallon inda sukaga tana kallo
Ita kanta Huda sai da ta tsorata.
Tun kafin ta k’araso ta rufeta da fad’a!
“Dan mai yasa za ta fito? Aslam d’in ne ya bata izini saboda shima sakare ne irinta!
Ko dai satar hanya tayi ta fito?”
Da kyar ta iya tsayawa ta amsa gaisuwarta daga nan tace “su kama hanya maza maza su koma gida!
Wannan shirmen ba da itaba..
Ita tunda uwarta ta kawota duniya bata tab’a ganin amaryar da ta fito bata yi sati biyu ba!”
Da kyar ta yarda suka d’an jira driver bayan sun kirashi
amman da cewa tayi ‘bara ta yiwa Abban Ya Jamilu magana ya maidasu
Ai bai dad’e ta kawo Baba ba akwai mota shima a hannunshi.’
Ba a wani dad’e ba
Drivern nasu ya k’araso:
Ba yadda Hudan ta iya ta fara k’ok’arin tafiya ba dan taso ba
haka nan ta yi wa Shuwa sallama ta basu tsarabar da Aslam ya bata kud’i suka tsaya suka siya daga nan
ta cewa Mama za suyi waya anjima dan da akwai maganar da itama ta shirya za suyi da Maman.
Har mota Maman ta rakasu,
haka nan ta tafi tanata kumbure kumbure..
Sai da Shuwa taga fitarsu tukunna hankalinta ya kwanta,
yadda tabi ta d’aga hankalinta zaka ce Huda wani gagarimin laifi tayi…
Mama tana dawowa daga rakasu ta zo ta nemi waje ta zauna a gefenta kan 3 seater tace
“Kiyi hak’uri Hajiya nima sai da nayi mata fad’a wallahi.
Wai Ummi ta rako ne shiya sanya. Kin san su family d’in nasu boko ta ratsa su da yawa basu wani damu da al’ada ba
amman duk da haka na san inda ace a waje d’aya suke da Mommy da ba zata barta ta fito ba.”
Ta k’arashe maganar tana d’agowa ta kalli Hajiya Shuwa wadda tunda ta fara magana ta tsareta da idanu.
A hankali taji ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace
“Maryam”
“Naam” Maman ta amsa a hankali.
Wata ajiyar zuciyar Hajiyan ta sake sauk’ewa sannnan tace
“Naji duk abunda Ummin tace miki yanzu shigowa ta”
Wani yawu Mama ta had’iye kafin tace
“Hajiya na gama deciding tun tuni
Ba zan koma wa Abba ba!
Ba kuma zan komawa Baba ba!
A barni kawai, itama Ummin
dan tak’i yarda ta saurareni ne
da abunda na shirya