Showing 81001 words to 84000 words out of 100703 words

Chapter 28 - So da Buri Book 3 Hausa Novels by HUMAIRA BULAMA.txt

25 Sep 2025

4368

rusuna tukunna ya karb’a takardun da Granpa ya gama dubawa
ya fara magana..
“Granpa ya mallaka min Mt
duk da na san kowa ya sani a nan a yanzu, wanda maganar ta fito ne ta wajen Mammy da ta ga copies d’in takardun a d’akin Arshaad, shi kuma na san a mota ta ya ga takardun
ranar da ya d’auka ya fita ya ce tasa ta lalace.
A ranar da ya bani gida a UK a ranar ya bani had’e da MT.
Ba yadda ban yi da shi ba
amman ya ce
‘yana so yayi komai ya gama
ya gaji da cases
kuma daman shi ni ya shirya bawa.’
Na yi godiya tabbas na kuma yi farin ciki amma a ranar na fara working akan nima nawa decision d’in………
Arshaad, mun yi magana da kai a kan kana so ka bar k’asar nan shiyasa na baka na Uk!
Hope you are happy.”

Da sauri kowa ya zuba mishi ido.

Murmushi ya yi
ya d’aga musu kai alamun tabbatarwa
Sanann ya ci gaba da magana
“Auwal kuma na bashi na Abuja, ni kuma na d’auki na Kano”

A hankali ya juya inda Granpa yake ya ce
“Granpa ba wa ban ji dad’i akan kyautar da ka yi mini ba
No
I really appreciate it
but this has been my wish since..
It was your wish ka mallaka min MT ni kuma wish d’ina shine mu rabashi a tsakaninmu brothers uku.
I hope ban b’ata maka rai ba
sannan kayi farin ciki da decision d’ina.
Ban yi tempering da wish d’inka na passing MT from generation to generation ba
Instead na sake fad’ad’a wish d’in naka ne
Na tabbatar duk mu uku zamu zage kwazo wajen kular maka da MT in sha Allah
kowa zai kula da nashi
sannan za mu yi passing d’in shi each to our capable child just like you wanted
sannan zamu rubuta mu ajjiye
y’ay’an mu suma su
bawa capable jikan mu each suma kuma jikokin namu
su bawa capable d’ansu…
A haka dai har illa masha Allah.

I hope ban sab’a maka ba.”
Ya k’arashe maganar yana sunkuyar da kanshi
ganin yadda Granpa ya kafeshi da idanuwa.

A hankali Granpa ya mik’e ya sauk’o daga kan kujerar tashi
ya dogara sandarshi ya k’arasa inda Aslam yake tsaye ya shafa fuskarshi a hankali
yana jin tsantsar k’aunar jikan nashi tana sake shiga cikin zuciyarshi, a hankali ya ce
“I wonder why
mutane suke jin haushi
Idan nace kaine favorite jikana.”
Yana gama fad’in haka
ya ce “Allah ya yi muku albarka
I’m very happy with your decision, thank you.”
Daganan yasa kai ya wuce side d’inshi yana dogara y’ar sandarshi Gramma itama ta mik’e ta mara mishi baya.

A hankali Dad ya k’arasa ya yi hugging Aslam sai kuma
ya jawo Arshaad shima ya had’asu duk su biyun ya rungume.

Murmushi Abba yayi
shinda su Shuraim waenda suka koma kusa dashi tun d’azu da za a tafi da Mammy suka mak’ale masa.

Haka shima Daddy
yana d’an murmushi idanunshi tap kwallah ya ce
“Inama ace inada super powern da zan yi using in ganni a tsakiyanku”

Dariya duk suka yi har Mommy.

A hankali ya ke kallonsu
kafin ya ce
“Sai mun dawo in shaa Allah..
May this smile never fade away a fuskokinmu”

Duk had’a baki suka yi wajen cewa “Ameen”
Daga nan su Daddy suka yanke kiran.

BULAMA ✍️



So da Buri
Free Book
72.


A parlourn k’asa Aslam ya tadda Huda tanata faman safa da marwa…
Duk yadda taso kasa rik’e kukanta tayi dan haka kawai sai ta sakeshi ta taho tana zuwa ta fad’a jikinsa.

A hankali yana sauk’e ajiyar zuciya ya shiga lallashin ta
yana rad’a mata wasu maganganu a kunne.
Cikin d’an murmushi da kuka at the same time ta kai mishi duka a k’irji.
A hankali ya ce “auch!!”
Yana shafa kanta.......


Washe gari da sassafe
Arshaad ya zo. Aslam bai tashi ma akan sallayar da ya gama karatu ba ya ga call d’insa..tunaninsa kuwa yake yi dama
yana rayawa a ranshi dalilin da ya sanya bai ganshi a masallaci ba.

Yana d’auka ya ji ya ce masa
‘yana k’asa gidansa,
ya zo ya bud’e masa.’

“To” kawai ya ce daga nan ya mik’e ya cewa Hudan
“Ina zuwa”
ya fita.

A hankali ta bishi da kallo har ya wuce ya fice tana jin yanayin da takan tsinci kanta a gameda shi yana sake nunkuwa.

Masu aikin su duk ba anan suke kwana ba shiyasa sai da Arshaad ya jira Aslam ya bud’e mishi tukunna ya shigo.

Da murmushi suka yiwa juna sallama kafin Arshaad d’in ya ce “sorry, na tada ku da sassafen nan ko?”

Ajiyar zuciya kawai Aslam ya sauk’e sanann ya ce
“Bismillah”
Yana me bashi hanya.

Suna zama ba tare da b’ata lokaci ba Arshaad ya ce
“Sallama na zo yi muku”
Yana d’an murmushi.

Da mamaki Aslam d’in yake kallonshi kafin ya ce
“Tun yanzu?”

Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce
“I have to, sanann inaso in fara aiki da wuri..you promised Granpa ba za mu yi letting nashi down ba
so bana son in baku kunya
da kai da shi.
Sannan tun a jiya bayan mun rabu da na kira Daddy
yake cemin akwai aiki gaskiya
a company d’in.”

A hankali Aslam ya ce
“So this is it?”

“It’s just a good bye na d’an wani lokaci, zan dinga zuwa in sha Allah kar ka damu.”
Arshaad d’in ya fad’i hakan cikin tarar numfashin shi.

Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e ya sunkuyar da kanshi yana kallon k’asa sai kuma ya fara wani kalar murmushi tukunna ya fara magana
“This Life is very funny!
Difficult! Harsh! And way too upside down
A ko da yaushe it’s very hard ka ga mutum ya samu all that he ever wished for
ko da ace kuma zai samu d’in to sai kaga ya samu late
ko kuma ya samu opposite
ko dai ma ya rasa gaba d’aya….
Tun tasowarmu
ba ni da burin da ya wuce
Inga mun rayu cikin farin ciki gaba d’ayanmu a inuwa d’aya
Ni Kai Aaima Dad Mommy Mammy
har da su Auwal
this has been my wish since childhood
amma
It turns out
ba wai ga ni kad’ai ba ga yawancin mutane za ka ga dukkannin abunda kake so shi yake zame maka jarrabawa.

Hak’ik’a Ubangiji yana jarabtarmu ne domin ya gwada imaninmu, yana jarabtar mafi soyuwa a cikin bayinsa da abunda ya san sun fi tsananin so da kwad’ayin samu….i have accept my destiny, i have accepted the fact that
rayuwar da na so in yi da ku baki d’aya a inuwa d’aya ba zata tab’a yiwuwa ba.
Although i was and I’m broken amma
I’ll heal and embrace it with time.”
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya d’ago ya kalli Arshaad wanda tunda ya fara magana ya kafeshi da idanuwa, a hankali ya ce
“Ina yi maka fatan alkhairi
Allah ya sanya albarka a cikin dukkannin alamuranka
Allah ya baka sa’a ya kare ka a duk inda kake.
Arshaad inaso ka sani
you will forever be my best friend, bani da da d’an uwa who stood by me through my worst times irinka
shiyasa nake ji a raina inama ace Ina da dama to da ba zamu so mace d’aya ba.”

Murmushi Arshaad ya yi ya had’iye wani yawu mai tauri kafin ya ce
“Na gode Aslam,
Allah ya k’addara saduwarmu.
Kar ka damu ko da ace bama kusa I’ll make sure ban baka chance d’in da za ka yi missing d’ina ba daga kai har su Mommy zamu dinga waya video call sannan zan dinga zuwa time to time
In sha Allah”
Cikin sanyin murya ya ce
“Ubangiji ya azurta ni da family masu matuk’ar sona dole in dinga lek’o su”
A hankali yana murmushi yana kallonsa ya ce
“Especially ma you Aslam..
Ina takaicin yadda na bari soyayya da takaicin ganin an mallaka maka MT suka kaini
na kusa in halaka ka!
A tunani na
ina ganin maybe if I have the company zan iya mallakarta ta hanyar power!
Hak’ik’a
So da Buri ya kusan kaini ga matakin da za a iya saka ni a mazaunin the most ungrateful and selfish being a duniya!”
Numfashi mai matuk’ar zafi ya fesar sannan ya ce
“Babban darasin da na fahimta na d’auka shine
‘Wayo! Dabara da kuma k’arfin iko ba su Isa su baka abunda Allah ya riga ya k’addara ba naka bane ba!
Shi ne kad’ai mai bayarwa kuma mai hanawa a duk lokacin da ya so ya kuma ga dama, bawa bai Isa ya kwatar wa kanshi abu ba Allah kad’ai ne yake wannan, shine kad’ai yake kwata ya bawa wanda ya so ya ga dama a duk lokacin da ya so ya kuma ga dama’.”
Shiruu ya yi kafin ya sauk’e numfashi yana mai kallon k’asa a hankali ya ce
“Na yi wayo, na so kaina, na kawar da duk wani negative Abu da nake gani a kan hanyata da ka iya kawo min tangard’a wajen mallakarta, na take gaskiya, na cutar da Junaidu kaima na so in kawar da kai amma duk da haka….”
Shiruu yayi ya kasa ci gaba da magana sai kuma ya d’ago ya kallesa sosai ya ce “Aslam dan Allah please forgive m…”

Da sauri Aslam ya ce
“Arshaad mun wuce wannan wajen..
Idan akwai abunda zan rok’eka ka yi min a zaman ka na Uk shine
ka goge komai..
Duk abunda ka ga yafaru it was already written tun kafin a haife mu dan haka ya faru ya wuce na manta kaima ka manta kar ka bari ya dameka…
Bana duba abunda ka yi min dan bana ganinshi ma
Iyaka abunda na sani nake gani
shine
‘You are my best Man Arshaad’
Shine kuma abunda zan rik’e har abada.
Ina rok’on Allah ya bar mana zumunci mu.”

A hankali Arshaad ya ce “Ameen”
Sannan ya mik’e ya ce “bisssalam”

“Bara in kirata ku yi sallama”
Aslam ya ce yana k’ok’arin juyawa.

Da sauri Arshaad ya ce
“A’a barta.
Kawai ka ce mata na wuce”

Da “to” Aslam ya bishi,
daga nan ya yi mishi rakiya har bakin mota.

Already sun yi sallama da su Dad da Granpa da kowa
dan haka ya shiga..
Driver na k’ok’arin ja a hankali Arshaad d’in ya kalleshi ya ce masa
“Ka kula mana da Aaima,
tana wajen Mommy.”

A hankali Aslam ya ce
“I’ll.”
Sai kuma kamar wanda baya son yin maganar ya ce
“G’bye Arshaad”.
Yana kallo driver ya yi reverse daga nan ya ja suka fice….

Yafi minti biyar a tsaye ya zubawa inda motar ta bi ta fice ido kafin a hankali ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya
ya juya ya shige ciki
idanuwansa jazur!. ..................


….24 HOURS AGO!….
Jirginsu yana Landing
Daddy ya na shirin d’aukar drop ya ji Mom ta dafa shi
ta ce “Daddy”.
A hankali ya juyo suna had’a ido ya d’an b’ata fuska ya ce
“Ke da ba y’ar gari ba Adama Ina ke ina zuwa d’aukar mu??”

Murmushi kawai ta yi ta ce
“Sorry” sannan ta wuce ta isa inda Sakina take tsaye
tanata kame kame dan tun tasowarsu
take fargabar ya zata kasance mata ita da Mom d’in.
Ga mamakin Sakina Mom tana zuwa kawai sai taga ta yi hugging d’inta
a hankali ta ce
“Welcome dota”
Sannan ta ja hannunta da d’an k’aramin trolley d’inta suka yi gaba.

Murmushi Daddy ya yi
dan ba k’aramin dad’i ya ji ba.
Cikin sigar zolaya shima ya nufi motar da suka nufa yana jan nashi trolley d’in yana cewa
“Wato ni ko In taho ko In zauna a nan ba damuwarki bane ba ko?
Tunda kin samu y’arki”.

Murmushi kawai Mom d’in ta yi
a haka suka isa bakin motar.

Suna zuwa drivern ya fito ya karb’i akwatunan ya saka a booth, suka shiga
driver ya jasu suka wuce.

Ga mamakin Sakina sai ta ga an kaisu hotel!
So take tayi tambayar ‘Ina Auwal d’in’ dan in akwai wanda tafi buk’atar gani ta ga lafiyar shi a halin yanzu tou Auwal ne..so take ta yi magana amman kuma kunyar su sai ta hanata dan haka kawai ta bi bayan Mom wadda take ta wani lallab’ata har suka isa k’ofar wani d’aki.

Wanda ya d’aukar mata akwati yana ajjiyewa
Mom ta bud’e d’akin ta ja suka shige bayan ta mik’awa Daddy makulli.

Suna shiga Mom ta rufe k’ofar kafin ta kamo hannun Sakina duk biyun ta rik’e, a hankali ta ce “Dota ki huta ki ci abinci
daga nan sai ki je asibiti wajen Auwal ko?”
Sai kuma ta d’an yi shiru
chan ta ce
“Ki yi hak’uri akan abunda na yi miki ranar birthday d’in su Shuraim, ki yafe min”.

A hankali Sakina ta ce
“Ba komai Mom ya wuce,
ki daina bani hak’uri dan
Allah”

A hankali Mom ta saka hannu ta yi hugging d’inta.
Sun d’an jima a haka kafin ta cikata ta juya ta fita tana cewa
“Yanzu za a kawo miki abinci,
ki ci ki yi wanka
sai mu zo mu wuce gaba d’ayanmu.”

Da “to” kawai ta iya binta dan ita har ga Allah so take kawai ta ji ance ta zo su wuce wajensa.


Ba yadda ta iya haka ta daddannna abincin ta yi wanka duk ranta a jagule.
Allah yaso su Mom basu wani d’auki time ba ta ji ana knocking..
Ta san sune
dan ta gansu ta jikin d’an TVn dake jone da cctv camera d’in gaban k’ofar, dan haka gudun ma kar a sake yin wani jinkirin
ta d’auko har handbag d’inta ta sak’ala akan bak’ar abayar da ta chanja dama ta yi rolling
ta nufi k’ofar ta bud’e ta fita.
Suna ganin ta a shirye chap suka ce “su wuce kawai”
Mom na y’ar dariya k’asa k’asa
tana yaba tsantsar k’aunar da Sakina take yiwa d’anta
tana jin k’aunarta na shiga zuciyarta. Tun d’azu ta lura da yadda Sakinar take ta rawar k’afar son zuwa ta ga Auwal d’in……
Da wannan tunanin
suka k’arasa mota
Drivern jiya shi ya ja su ya kaisu har cikin tafkeken asibitin.

Tunda suka fara takawa cikin asibitin gabanta yake mugun fad’uwa! Had’e da wani sanyin farin ciki da ya lullub’eta.

Suna shiga dakin ta fashe da kuka, duk da kuwa Aaima dama ta gaya mata halin da yake ciki amman bata yi tunannin samun shi da oxygen har yanzu ba.

Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin ya k’arasa wajen ya tsaya a dede kanshi yana kallon shi..
Ya rame ba kad’an ba
ya yi haske sosai.

A hankali ya shafa kanshi ya ce “Son”

Tun lokacin da suka shigo yake d’an jinsu sama sama. So yake ya bud’e idanuwan nashi amman ya kasa
dan haka kurum suna shigowa gabansa ya yanke ya fad’i.

A hankali ya samu ya bud’e idanuwan nashi
da suka k’ank’ance..
Suna had’a idanu da Daddy ya sakar masa d’an murmushi.

Murmushi Daddyn shima ya yi masa kafin ya ce
“I’ve a surprise for you”
Ya yi maganan yana mai juyawa ya yafito Sakina.

A hankali ta k’arasa inda suke.
Tunda ta taho jikinshi ya bashi,
yana cikin tunani
kawai ya ganta a tsaye a kanshi!

Mutumin da ko iya motsin kirki baya yi kawai su Daddy suka ga ya yunk’ura da sauri
zai tashi sai kuma ya ce “auch!!”
Yana dogarar da guiwar hannunsa a kan gadon for sopport
dan da mugun ciwo
k’irjinsa wuyansa kafad’unsa da kansa suka sara!
Sai kuma ya fara juwwa.

Da sauri Daddy ya tareshi yana mai zama a bakin gadon ya maida shi kwance
ya ce
“careful mana”
Sai kuma yasa dariya ya ce
“har ka warke kenan?”

Sai a lokacin kunya ta rufe Auwal….A hankali ya d’auke idanuwansa a kan fuskar Sakina ya mayar ya lumshe…..
Tsananin farin ciki ya ji da ya ganta by surprise
dan ji yayi kamar an tsundumashi a aljannah!
Sai kuma a take batun
Aurenta da Ashraff ya fad’o masa dan haka take lokaci guda ya ji wani tsananin tashin hankali
sanann k’irjinsa ya hau zafi.
Muryar Daddy ce ta katseshi jin yana cewa
“Auwal ba komai mutum yake sa rai kuma ya samu ba!
Kar ka ga ka mallaki Sakina ka yi tunanin duk wani abu idan ka sa rai nan gaba zaka samu.
Ubangiji shi ya baka ita ba wai saboda nacin ka da rashin lafiyarkaba.
An d’aura muku aure jiya kai da ita sakamokon matsalar da ta b’ullo a alamarin
Aurenta da Ashraff.
Amana ce Yarinyar nan
Mahaifinta yayi mana kawaici da mutunci
Dan Allah kar ka bamu kunya.”

Tunda ya fara magana Auwal ya k’ame! Ya kasa motsi sam!
Ji yake yi ma kamar iskar oxygen d’in bata isarsa………

A hankali Daddy ya yi wani sassanyan murmushi ya ce
“Dota idan kuna buk’atar wani abun ga waya chan….idan Likita kuke so za ki ga digits d’in a gefe
idan kuma abinci ne
shima digits d’in suna gefe.
Mu bara mu wuce ko?
Yana da number mu
duk abunda kuke buk’ata ku kira.
Allah ya yi muku albarka.”

A hankali Sakina ta ce “ameen” tana mai sunkuyar da kai.

Da kyar ya iya bud’e idanuwanshi ya ce
“Thankyou Daddy”
A hankali dan shi kad’ai ya san luguden da zuciyarsa take yi masa.

Murmushi ya yi daga haka suka juya shi da Mom suka fice
tare da alk’awarin ‘zuwa anjima za su dawo’
Bayan Itama Mom d’in ta yi musu addua sun amsa......


A hankali ta ga ya mik’o mata hannunsa yana kallonta.

Cikin nutsuwa ta k’arasa ta sa hannunta a cikin nashi.

Still yana kallon fuskarta ya zaunar da ita a gefenshi.

Da kulawa ta ce
“Ina wuni”
Tana kallon bakinshi ya amsa da “Alhamdulillah”
a hankali.
Daga nan ya ja hannun nata ya d’aura a gefen fuskarsa saman kumatunshi ya had’a da nashi hannun ya runtse
kafin ya maida idanunsa ya rufe…
Ko minti uku ba a yi ba ta ji
yanayin rik’o da ya yiwa hannun nata ya sauya
alamun ya yi bacci, bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba..
Kallon shi kawai take yi tana sakewa..ya d’an tara k’asumba har da gemu, tabbas ta so
ta tarwatsa rayuwarta da hannunta dan bata jin akwai wanda zata iya so ta zauna ta rayu ta yi farinciki da shi idan ba Ya Auwal ba. Bata tashi sanin zazzafar soyayyar da take yi mishi ba sai da ya kwanta ciwo….

Sun fi 40 minutes a haka
gaba d’aya hannunta ya k’age amman bata so ta motsa gudun kar ya farka dan
ta lura baccin nashi mai dad’i ne yake yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali
kamar ma murmushi taga yana yi.

Sai da ya yi 1 hour yana baccin tukunna ya farka. Yana bud’e ido da fuskarta ya fara tozali
Itanma shi take kallo dan haka ya sakar mata wani tsadadden murmushi. Sai kuma ya d’an gyara ganin kamar a takure take kafin ya ce mata “call the Doctor” a hankali.

Ta fahimci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login